Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 37

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 37

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 37: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 37. "Yo daman waye zai so wahala Rabi'a? Ai wallahy sai idan mutum…

3,344 words

"Yo daman waye zai so wahala Rabi'a? Ai wallahy sai idan mutum bai samu gidan hutun ba. Musamman idan a dangi babu mai ɗan maiƙo kinga wahala ta shiga..."

Cike da jin wani sabon baƙin ciki Rabi'ar ta ce.

"To ai Umma shiyasa na so in samu Maheer ɗin gabaɗaya. Amma sai ki ka zo ki ka kofsa."

Tana gama faɗar haka ta miƙe ta shige toilet domin yin wanka ta bar Umma tsaye jiki sanyaye domin dai ta rasa abin cewa. Shiyasa bahaushe ya ce da muguwar rawa ƙwamma kin tashi,da tun farko sun riƙe abinda ya zo hannunsu da yanxu yana nan bai suɓuce ba.

But ko yanzu ba za ta zauna hakan nan ba domin idan har ba ta samu Faris ba to kuwa za su zamto abin dariya da zunɗe a cikin dangi. Daman ga Baba ya ce aure zai yi mata domin ta gama karatu har abada. To idan ba su kama faris ɗin ba wa za su kama? Daman su ma ba laifi da kuɗin su saboda haka dole ta shiga ta fita domin su samu Faris.

Tana nan tana ta aikin ta tsakar gida taga Rabi'ar ta fito cikin shirinta ta fice tana ce mata sai ta dawo.

*******

Anaam kuwa abu kamar wasa har ta kusa kambala exams ɗinta tsawon 2weeks da 'yan kwanaki Maheer bai dawo ba. Yana garin zuwa gidan ne baya yi ko kuma barin garin ya yi? Allah ne masa ni. Kuma abin baƙin ciki abin mamaki har yau bai kira ta ba bai kuma yi mata text ba ballantana tayi tunanin tana cikin rayuwarsa.

Ita yanzu gabaɗaya ma ta kasa fahimtar shi ɗin wane irin mutum ne? Ta kasa gane ina ya dosa. Gabaɗaya yanzu ta ji ta kamar zuciyarta na so ta tsane shi, ta lura cewa yafi son kansa fiye da komai. Sai ya gama son ransa sannan ya dawo daga baya yana bata wani haƙurin marar amfani. A yanxu ta yarda cewa duk abinda yake yi yana sane yake yin sa babu wani excuse.

Anasi shi ne a tare da ita kullum ya kai ta ya dawo da ita ya kai ta ya dawo da ita har zuwa wannan lokacin.

Zuwan su Aunty Aysha ya kai sau uku gidan na ta, amma ko kaɗan alamu bai nuna cewa sun san baya garin ba ko kuma baya zuwa gidan ba. Ta so ta kira Aunty Dina ta faɗa mata irin wulaƙanci da cin fuskar da ya yi mata amma kuma wani gefen zuciyarta na kwaɓarta akan ta yi hak'uri ta ƙara jira ta gani.

Tambayar kanta take cewa wannan wane irin aure ne? Wane irin rashin sanin daraja da kimar aure ne? Atleast ya kamata ko ya ya ne ya bata muhimmanci a matsayinta na matarsa. Ya kamata ya sanar mata kafin ya saka ƙafa ya yi tafiyar sa. Idan kuma damar hakan bata samu ba atleast ya turo mata text.

Kafin aure bai taɓa kiranta ba and bayan auren ma fiye da sati biyu kiran Mijinta bai taɓa shigowa wayar ta ba. Anya mutumin nan yana son ta kuwa? Ko auren ƙiyayya suka yi ai bai da ce ya yi mata wannan wulaƙancin ba ballantana cewa akayi ya ce yana son ta. Yes! Cewa akayi ya ce yana sonta domin ita dai har yau kunnuwanta ba su jiye mata komai ba. Hakan yanzu ya fara ɗarsa mata zargi da jin cewa kamar akwai wani abu.

Ita ɗin fa ba amaryar Kara ba ce kuma ba 'ƴar tsana ba ce. Mace ce ita mai zuciya a ƙirji. Mace ce wacce aka ajiye ta da sunan matar aure amma kuma ba ta ga amfanin hakan ba. Ta tsane shi! Wallahy ji take ta tsane shi da auren ma baki ɗaya. Wannan abun yayi mata ciwo sosai a rai. Wallhy ta yi nadamar wannan auren. Yaushe ma aka yi daren ballantana gari ya waye. Bai ɓare cingum ɗin ba bai ma tauna ba ballantana ace ya gama shanye zaƙin ya furzar.

Lokaci ɗaya kuma tunaninta ya harba zuwa ga maganar da suka yi a daren da aka kawo ta. Kada ace ya guje ta ne saboda wannan? Kada ace ƙarya ya yi mata ya ɓoye mata baƙin cikin da yake ciki na jin irin labarin ta? To amma miyasa bai guje mata ba tun a daren ranar? Miyasa ya tsaya ya yaudareta? Daman ta sani, da irin ƙaddarar ta babu wani namijin da zai iya jure zama da ita. Miyasa tun farko ta tsaya ƙauron baki har aka kai ga zarga mata igiyarsa uku ba tare da ta faɗa masa gaskiya ba? Yanzu da ya guje mata miye yake nufi? Ina rayuwarta ta dosa? And kuma miye makomarta?

Wani irin marayan kuka ne ya ƙwace mata wanda ba ta san ina ma za ta tsoma ran ta ba. Kuka ta ke tana mai yin nadama marar adadi wanda ta jima har misalin sha biyu saura na dare sannan daga ƙarshe ta miƙe taje a yanda take ko hijabin sallar ta bata cire ba ta kwanta.

Ta jima a kwance zuciyarta na ta yi mata wani irin tuƙuƙi sannan ga rashin sanin abin yi wanda bata san mi ya kamata ta yi ba, bata san wane mataki ya kamata ta ɗauka ba duk da cewa zuciyarta da tunaninta suna hasaso mata wani abun wanda wani sashen na zuciyarta kuma har yanzu bai amince ma ta ba.

Miƙewa ta yi ta sauko daga kan gadon sannan ta fito ta sauko ƙasa ta shiga kitchen ɗinta wanda yanzu take amfani da shi lafiya lau ta buɗe fridge ta ɗauko bottle Water mai san yi Sosai ta ɓalle murfin ta sha.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana mai jin ta tsani komai a ranta ta fito da nufin komawa ciki.

Kallon shi ta tsaya tana yi wanda gabaɗaya a yanzu zuciyarta ji take ta ma gama bushewa, domin da a duniyar da ne ta ganshi kwatsam tabbas sai ta firgice, amma yanzu ko kaɗan bata nuna alamar tsoro ba sai ma wasu hawaye marasa adalci da ke neman silalo mata.

Ganin yanayinta ba ƙaramin haddasa masa faɗuwar gaba ya yi ba domin gabaɗaya yanayin fuskanta ya sauya.

"Maryam..."

Ya ambaci sunan ta murya a karye domin da ganin ta bata cikin yanayi mai daɗi.

Maimakon ta amsa masa raɓa gefen shi kawai ta yi ta wuce ta haura ɗakin ta.

Faɗawa ya yi jikin gini yana mai jin gabaɗaya yanda ƙwaƙwalwarsa ta shiga hautsinawa tsabar mamakinta.

Abunda bai gane ba shi ne, haushinsa take ji don ya tafi ya barta ko me? He thought zama a kusa da ita will make her to feel uncomfortable. Wannan yanayin ya tuna masa da yanayinta na ranar da ya shigo ɗakinta da safe, ya lura kaman tana fushi for the first place amma kuma daga baya sai bai ga komai ba. Da alama ma kuka ta yi kuma daga yanayin face ɗinta kaman ta jima tana yi.

Jiki a saɓule ya taka daga ƙarshe ya haura tare da tura ɗakin.

A edge ɗin gado ya sameta ta rufe fuskarta da tafin hannunta wanda da alama kamar ma kuka take.

Zaunawa ya yi gefen gadon tare da sanya hannu da nufin Riƙota ita kuma cikin zafin nama ta miƙe tare da girgiza masa kanta tana mai zubo da hawaye ta ce.

"Ni ɗin nan fa I'm a human...ni ba dutsr ba ce! Ni ba 'ƴar tsana ba ce. Ni mutum ce mai zuciya a ƙirji. Ban faɗa maka labarin ƙaddarata don ka ji ka tausayi min ka tilastawa kanka zama da ni ba,na faɗa maka ne domin ka nemarwa kanka mafita. Da ka yi min bayani tun a wannan daren wallahy da na fahimce ka....but leaving me all alone without any excuse breaks me a million times. Na tsani auren Gabaɗaya. I don't want be in it anymore... "

A gigice ya janyota tare da ƙanƙameta cike da danasani ya ce.

" I'm so sorry wife...bansan cewa nisantarki zai sanyaki a cikin irin mummunan ƙuncin ba. I'm sorry...i promise not to do it again.."

Luf ta yi a cikin jikinsa tamkar ba ita ce ta gama sabbatu a yanzu ba. Kalamansa suna kashe ta tare da juye mata tunaninta a duk sanda yake furta mata su,musamman kalmar wife ɗin da ya ambata ya gama gamawa da ita. Da gaske da wannan kalmar ko kuma da wasa?

" Uzuri ne ya kama ni mai matuƙar muhimmanci a wannan ranar, and ban samu sarari ba gabaɗaya sai yau ɗin nan ki yi haƙuri kin ji...."

Shiru ta yi kawai tana sauraren sa ba tare da ta ce masa komai ba tsawon lokaci.

Ganin kamar ta sauka daga fushin yasa ya ɗan motsa tare da zamewa ya ce.

"I'm coming.."

Daga haka ya fita zuwa ɗakin sa ya yi wanka ya fito sannan ya shirya ya dawo ɗakinta ya kwanta a kusa da ita tare da janyota wanda baya tunanin cewa bacci ta yi.

Gabaɗaya tunanin yanda ta yi reacting ɗazu ya hanawa zuciyarsa sakat. Kukanta ba ƙaramin ƙona masa zuciya ya yi ba. Haushin kansa ya ke ji domin laifin duk nasa ne. Ko ba komai tana da haƙƙoƙanta da suka rataya akan wuyan sa. Shi yaje Oman ne domin ya gaishe da Kakansa sannan kuma ya ga Maaminsa, hakan yasa ya bar ta domin ta samu damar fuskantar Exams ɗin ta ashe hakan bai yi mata daɗi ba.

Lumshe idanunsa ya yi yana mai tariyo yanda ya ruɗe gabaɗaya ganin yanda take kuka. Kallon fuskarta ya yi wanda ya tabbatar masa da cewa ta yi bacci a yanzu.

Sake ƙara gyara musu kwanciyar ta su ya yi yana mai lumshe idanunsa kawai ba tare da tunanin bacci ba domin yasan hakan ma ba zai samu ba. Mamakin kansa yake da har ya iya haura gado ɗaya da ita a matsayin matarsa ba tare da sanin mahaifiyarsa ba. Bai so ko kaɗan ya zurfafa, so yake ya Ƙarya ta tunanin Hamad. So yake ya nuna masa cewa yasan abinda yake yi. Yasan tabbas ko giya yake sha bai isa ya kai ta gaban Maami da sunan wai ita ɗin matar sa ce ba. Shiyasa yake baya-baya domin tafiyar ba mai ɗorewa ba ce.

*******

Ta yi mamakin ganinsa a ɗakin lokacin da ta farka wanda shi har ya shirya ya zauna da alama zaman jiranta yake. Bacci sosai ta yi bayan ta gama sallah wanda a lokacin kuma baya ɗakin ya fita.

Saukowa ta yi ta shige ta yi wanka sannan ta fito sanye da hijab ta shiga mutsu-mutsun shiryawa. Yana kallonta sau ɗaya ya kauda kai wanda bai sake ɗagowa ba sai da ya ji ta buɗe ta fita.

Bayanta ya bi da mamaki a ransa ganin cewa ba ta gaishe da shi ba.

Kitchen ya same ta tsaye gaban Gas tana batun kunnawa ya ce.

"I'm sorry....but you may be late. Ki ci Wan can da aka ajiye miki...."

Can ƙasa sosai ya ji muryarta tana faɗin.

"Wannan ɗin nake so, ba zan jima ba."

Jin hakan yasa ya dawo parlour jiki sanyaye ya zauna zaman jiranta har ta gama ta fito. Ko a mota babu wanda ya yi wa wani magana har suka isa Campus ɗin wanda a yau ita ce Last exam da za ta yi.

Yana ajiyeta ya zauna zaman jiranta har sai da ta fito sannan ya ɗauke ta a mota wanda bata saki ranta ba sai da ganta a Layin gidan iyayenta.

Sosai ta yi farin ciki kamar yanda su ma suka ji daɗin ganinta, a nan ta wuni ita dasu Mubarak da Aunty Na'ima wacce suke dakon haihuwarta ko yau ko gobe. Yinin ta a gidan gabaɗaya ya wanke mata ranta ta daina jin kowane irin ɓacin rai. Ta so ta faɗawa Yaa Na'ima abinda ya faru amma kuma sai ta fasa domin har yanzu kalaman ban haƙurinsa su ne suke mata yawo a zuciya da ƙwaƙwalwarta.

Ana gama sallar Isha ta ga kiran wayarsa wanda ya yi matuƙar ba ta mamaki. Sai da ta yi ringing kusan sau uku sannan Yaa Na'imar ta ɗan zungureta tana murmushi ta ce.

"Amarya sarautar ce kuma ta motsa? Har a anguwa ma sai an yi ba'a bari a koma gida?"

"Hmm!"

Shi ne abinda kawai ta furta tare da ɗaukar bag ɗinta ta shige ɗakin Ammie ta yi mata sai da safe sannan ta fito ta shiga wurin Abbah.

Har bakin mota Mubarak da Na'ima suka rakota suna ta musu tsiya wanda shi dai Maheer murmushi kawai yake har suka bar gidan.

Suna fitowa gidan motar ta yi tsit wanda har suka isa gida babu wanda ya sake yin magana. Suna shiga parlour kamar jira yake ya janyota tare da manna bayan ta jikin bango domin su samu support sosai yana mai trapping ɗinta tare da kai fuskarsa saitin ta ta ya kalle ta cikin ido murya a ƙasa sosai ya ce.

"I'm sorry.!"

Saurin kawar da kanta ta yi tare da saka hannu ta dafe gefen zuciyarta domin ji tayi kamar za ta fito tsabar yanda ta shiga bugawa da wani irin ƙarfi tsabar yanda take ji. Gabaɗaya jikinta lokaci ɗaya ya ɗauki ɓari domin ya sanyata a cikin wani irin yanayi wanda ke neman ya zautar da ita.

"Zamu iya tafiya Lagos ki yi hutu?" ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 46*

Runtse idanunta ta yi domin ji ta yi gabaɗaya ba za ta iya ci gaba da kallonsa ba.

Matsawa ya yi baya kaɗan tare da janye hannayensa ganin yanda duk ta diririce ya harɗe su a ƙirjinsa ya ci gaba da kallon cute lips ɗinta waɗanda suke madaidaita.

Jinjina kai ya yi yana mai cigaba da kallonta cikin nutsuwa ya ce.

"I think you need rest....and may be we also need time together."

Kalmar ƙarshe ɗinda ta fito a bakin sa, ba ita ba, hatta shi da ya furta ta sai da ya ji wani iri a ransa domin kalmar ta fito masa ne kamar suɓul da baka. Why did he say that? Ya tambayi kansa yana mai jin haushin irin wannan zaƙewar da ya nuna.

Ita kuwa, wani abu mai sanyi ne ta ji ya rasa mata zuciyarta, duk da cewa har yanzu ba ta ji za ta iya sakin jikinta da shi ba,kalmar sa ta ƙarshe ba ƙaramin dukan zuciyar ta ta yi ba.

"Maryam..."

Ta ji ya ambata wanda hakan ya haddasa mata saurin buɗe idanunta ta kalle shi tamkar wanda ya furta kalmomin bada umarni.

"Ba a nan nake aiki ba, kamar yanda kika ji kika sani wurin aikina yana Lagos ne, a yanzu kuma ana buƙata ta wurin aikina fiye da koyaushe. Ba zan iya ci gaba da zama a nan ba and ba zan iya barin ki ba tunda bakya so..."

Ba na so?

Ta tambayi kanta can cikin zuciyarta domin maganar ta ba ta mamaki. Ba wai bata so ba ne, a'a...yanda ya barta ne ya yi tafiyarsa abin ya ƙona mata rai but idan ta san inda zai tafi ba ta da matsala da hakan.

" We are not going to stay long. Daga zaran break ɗinki ya ƙare I will bring you back."

"Okay…"

ta amsa a ƙarshe sannan ta wuce ɗakinta ta faɗa kan gado. Iya ka 5mnt sai kuma ta diro ta shige toilet ta yi wanka sannan ta fito tayi sallar Isha ta shirya cikin wata doguwar rigar roba pink domin yin bacci da ita, amma idan ka so za ka iya fita da ita ma domin tana ɗan da kauri da kuma rashin nuna tsiraici. Kallon himilin kayan baccinta ta yi da kuma kayan shafe-shafe da sauran kayan sakawa na fannin riguna, skirt, trouser da sauransu ta yi tsaki sannan ta rufe ta zo ta kwanta.

Wayarta ta ɗauka ta kira Yaa Na'ima kai tsaye ta faɗamata abinda ya ce. Shiru Na'imar ta yi na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta ce.

"To miye abin damuwa Anaam? Hutu yace za ki yi and idan hutun ya ƙare sai ku dawo. Ki je kawai Allah kai lafiya ya baku zaman lafiya."

"Amin.."

"To amma na yi tunanin cewa may be ya fara kai ki Zaria wurin family ɗin shi idan kun gaisa sannan ku wuce ko ba haka?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Ni ma nayi wannan tunanin ɗazu Yaa Na'ima, kuma ma ko Ammie sai da ta tambayeni ranar, amma kuma shi bai ce min komai ba."

"To ai kin san wani namijin wani lokaci sai kana yi kana nuna masa muhimmancin wani abun. Musamman idan kika fara yi masa magana da kanki sai ya yi farin ciki domin zai ga kin damu da danginsa kin kula da su,hakan zai ƙara miki matsayi da kuma girma a zuciyarsa."

Jinjina kai ta sake yi cikin gamsuwa da kalamanta ta ce.

" Okay, in sha Allah zan mishi magana Muji..."

" OK to, Allah ya tsare."

"Amin. Yaa Na'ima yaushe ne ma EDD ɗin ki?"

Dariya ta yi ta ce.

"Ba jimawa dai in sha Allah."

"Allah ya kawo mai sauƙi.."

Tana ajiye wayar ya shigo ɗakin sanye cikin shigar jalabiya milk colour ya zauna akan Sofa ya buɗe tab ɗin hannunsa mai tambarin Maritime ya fara aiki.

Kallon shi ta yi sai kuma ta juya ta kwanta tare da ajiye wayar gefe ta lumshe idanunta. So take ta yi mishi maganan zuwa Zaria but mind ɗinta na yi mata kashedi akan a'a Anaam, idan ya so shi da kansa zai ɗauke ki ya kai ki. A haka kuma sai maganar Yaa Na'ima ta dawo mata akan cewa she can ask him Wanda hakan ba damuwa bane.

Sauko da ƙafafunta ta yi ta zauna tana kallonsa murya a darare ta ce.

"Ahmm..."

Ɗagowa ya yi da sauri ya kalle ta yana jira ya ji abinda za ta ce.

"daman cewa na yi ko zamu fara biyawa ta Zaria ne kafin mu tafi?"

Cikin nuna mata muhimmanci ya ce.

"Akwai wanda kike so ki ziyarta ne?"

Wani kallon ta bishi da shi mai ɗauke da mamaki wanda ma ya hanata magana. Ganin bai da niyyan magana yasa ta ce.

"Mu gaishe da iyayenka nake nufi kafin mu tafi.."

Daram! haka ya ji ƙirjinsa ya buga domin gabaɗaya ya manta kwata-kwata cewa mutanen da aka yo masa hayarsu da sunan iyayen sa an ce daga Zaria suke. Ya manta gabaɗaya ya sha'afa.

Cikin mintuna kalilan ya ji nadamar wannan Ƙaryar domin bai san mi zai ce mata ba a yanxu. Dole dai ya zama yana da dangi ko ya ya ne tunda dai ba daga sama ya faɗo ba. But ta ya ya zai fara?

Anaam kam ji tayi wani sabon tsoro ya sake shirgarta domin yanayin sa ya nuna he's not ready to take her to his family. Kenan bai shirya nuna ta ba ko kuma bata cancanta ba ne?

Kallon idon ta ya yi sai kawai yaga tana zubo da ruwan hawaye.

Ya salam! Ya furta yayin da ya ji zuciyarsa ta tsinke. Wai Ita kam abu kaɗan sai ta fara hawaye. Ta ya zai kai ta gidan mutanen bai sani ba. Miyasa ne wani lokacin ta cika neman rigima? Shi ne yake da ra'ayi na kai ta wurin danginsa ba ita ce za ta nuna masa ba.

"Tsoro ka ke ji ne? Tsoro kake kada su ganni su tuna da Labarina da ya watsu a shekarun bay..."

Da sauri ya girgiza kansa ya ce.

"No Maryam...jira na ake a wurin aiki wanda bani da daman da zan tsaya a ko'ina sai Idan na kambala assignment ɗina..."

"Assignment kuma? Kai da kake da company miye ya haɗa ka da wani assignment sai kace ma'aikacin kaki?"

"Ban faɗa miki ba ne but ina aiki da wani Companyn jirgin ruwa dake can Lagos ɗin..."

Tasowa ya yi daga inda yake zaune ya dawo bakin gadon ya zauna tare da riƙo hannunta domin ya samu ya cire mata shakkun da ya fahimci ya gama kama mata zuciya murya a ƙasa sosai ya ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull