Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 38
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 38: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 38. "Kin san yanzu duniyar nan ta lalace Maryam, hakan yasa ake so…
3,350 words
"Kin san yanzu duniyar nan ta lalace Maryam, hakan yasa ake so mutum ya zama yana ɓoye sirrinsa wanda ba komai ne za ka riƙa bayyanawa ba, Rayuwa sirri ce. Shi wannan ɗin Companyn da Hamad yake aikine kin san cewa abokina ne, shi ne wanda ya samo min aikin kasancewar na taɓa faɗa masa cewa aikinsa yana burgeni. To yanzu haka akan assignment nake wanda ni ne nake bawa wasu daga cikin sababbin ma'aikatanmu horo na musamman. Idan na kambala na nutsu in sha Allahu zamu tafi Zaria sai ki gaishe da kowa. "
Jinjina kai ta yi cike da yarda da shi ta ce.
" Allah ya taimaka. Allah ya bada sa'a ya tsare..."
Cikin jindadin addu'arta ya ce.
" Amin amin. Thank you."
Juyawa ta yi ta kwanta tare da lumshe idanunta ta yi shiru.
Kallon bayan ta yake yana mai jin wani abu a ransa dangane da ita. She's always good and smells nice. Mace ce mai fahimta da kuma matuƙar haƙuri. Sai dai kuma yana so tunaninta ya canja, yana so ta daina jin cewa wai idan ya yi mata wani abun don bata cancanta ba ne. Ya aure ta ne domin ya kawar mata da baƙin cikinta, ya aureta ne domin yasa ta ji cewa ita ɗin fa itama mace ce. But ya lura idan har yana so wannan mafarkin na sa ya tabbata dole sai ya kula da ita na musamman.
******
Washegari da wuri ta fito sanye cikin wata rantsatstsiyar doguwar Abaya baƙa wacce ta ɗauko daga cikin kayan lefenta, rolling ne a kanta da kuma Black shade Wanda ya ƙara fitowa da ita. She looks beautiful even though cewar ita ɗin baƙa ce sai dai kuma baƙin mai shining ne da yake ƙara mata ƙwarjini. Shi sam bai ga munin da Rabi'a ta kira ta da shi ba.
Shi ma dai shirye yake cikin white long sleeve shirt mai tambarin kamfaninsu na maritime, da black trouser. Yau kam kansa babu wannan P-cap ɗin wacce ke burgeta a duk lokacin da ya sanyata. Amma kuma duk da haka black hair ɗin nan nasa a kwance yake luf wanda yasha gyara ya yi kyau.
"You ready?"
ya tambayeta ganin kamar ta fara tsarguwa da kallonda yake mata.
Jinjina kai ta yi alamar eh sannan ya saƙala hannunsa a na ta karon farko da abin ya bata mamaki.
Anasi shi ne wanda ya kaisu Airport ɗin tare da yi musu fatan sauka lafiya.
Wani kallon Hamad ya bi su da shi domin har yanzu hannunsa yana cikin na ta bai janye ba wanda hatta wasu tsirarrun mutane da hankalinsu ke kansu sai da suka yi ta gulmarsu, lamarin mutane da ba'a iya musu, wasu sun burgesu sunga dacewarsu wasu kuma sunga rashin dacewar su ta yanayin launin fata da kuma kyaun fuska wanda Maheer ya wuce ta nesa ba kusa ba.
Mamakin Hamad ya kasa ɓoyuwa da ganin Anaam domin bai taɓa jin yace masa zai kai ta Lagos ba koda wasa, amma kuma gasu a tare tamkar wadanda suka shekara goma.
"Ina kwana.?"
Ya ji ta ce masa wanda shi ne abinda ya dawo da shi cikin hayyacinsa.
Murmushi ya yi mata ya ce.
"Lafiya ƙalau Maryam ya gida?"
"Alhamdulillah! Shi ne tun biki ba ka dawo gidana ba?"
A ba zata suka ji maganar ta ta wanda ya sanya Maheer ɗin shima juyowa ya ɗan kalle ta.
Hamad na murmushi ya ce.
"Ki yi haƙuri ban samu zama ba ne. But In sha Allah zan zo."
"To Allah ya yarda. Idan ma ka zo Abuja ba ka zo gidana ba zan ji daga wurin Yaa Dina."
Dariya ya yi yana jinjina kansa ya ce.
"Zan zo Amarya kada ki damu."
Saida suka gama komai ta shiga ta zauna sannan Hamad ɗin ya kalli Maheer yana girgiza kai ya ce.
"Maheer..."
Saurin tariyar numfashinsa ya yi yana kallon sa ya ce.
"Hamad yarinyar nan ta kambala exams ɗinta. Zaman gida ita ɗaya zai iya cutar da ita. Idan tana tare dani a can ko motsina kaɗai take ji zai fi da ace ita ɗaya ce a nan."
"But Maheer za ka cutar da Ita da yawa..."
Cike da jin haushi yace.
"Hamad ka fitar da kanka cikin al'amarin iyalina..."
"Iyalinka? Macen da za ka saka ba jimawa ita ce kake wannan iƙirari a kanta? Kada ka manta kai ne ka faɗi hakan ba ni ba..."
"And idan kuma ban saketan ba fa? Ni fa a wasu lokutan sai inga kamar kana mini baƙin ciki......"
Cike da jin wani irin shock Hamad ya zaro ido tsabar mamaki ya ce.
"Maheer ni kake cewa ina maka baƙin ciki?"
"eh mana, tun farkon auren nan har zuwa yau kullum ba ka faɗin alheri sai dai sharri wanda hakan babu kyau."
Daga haka ya wuce shi ya hau jirgin ya zauna a gefenta ransa a tafashe domin sam Hamad ba ya masa adalci.
******* Gidansa da yake zaune a ciki ne wanda companynsu na maritime ya tanadar masa na temporary ya kai ta. Gidan yana nan a tsare komai gwanin sha'awa sai dai kuma bai kai kyaun gidansu na Abuja ba.
A yinin ranar gabaɗaya abincin waje suka ci. Domin tun da suka sauka a tsaitsaye yake bai samu ya zauna ba, sai dai kuma da dare ya yi bai wani jima a wajen ba ya dawo wanda ita kam har ta gama shirinta na kwanciya bacci a wannan lokacin.
Gefe ya zauna yana ta aiki har ta yi bacci bai kambala ba.
Washegari tun 6am ya shirya cikin complete uniform ɗinsa. Kallon Tag ɗinsa take ta yi tana ƙara maimaita sunan a brain ɗinta wanda ita tasan ba haka ne a katin auren su ba.
"Ko za ki rakani mu je?"
Tambayar da ya yi mata kenan wacce ta ɗauke hankalinta daga tunanin da ta fara.
Jinjina kanta ta yi tana murmushi ta ce.
"Idan kana ra'ayi.."
Murmushin ya mayar mata ya ce.
"I will wait..."
Komawa ta yi ta shirya cikin wasu Turkey dress, Army green Riga da wando ne wanda rigar ta sauko mata har gwiwa ta yi rolling da black veil.
Dressing ɗinta yana burgeshi, ta iya saka kaya yanda ya dace da ita. Komainta na manya babes take yi waɗanda suka san abinda suke.
Bag ɗinta ta ɗauko black tare da saka heels ɗinta waɗanda suma suka kasance same colour with her Bag da kuma sunglasses da ya daɗa fitowa da ita kaman jiya. hakan sai yasa ya ji ta ƙara burgeshi. Ita ɗin wayayyiya ce wacce tasan kanta. Daga jiya zuwa yau dressing ɗinta ba ƙaramin tafiyar da shi ya yi ba.
Hannun ta ya sake kamawa ya riƙe har suka iso sannan bayan sun fito mota ya sake hannun na ta gudun zargi domin babu wanda yasan cewa ya yi auren.
Ma'aikatan wurin na ganin sa suka taho suna gaishe shi cikin girmamawa.
"Good morning sir…"
"Morning everyone…"
Ganin shi a tare da wata mace for the first time yasa itama suka shiga gaishe ta. Office ɗinsa suka shiga ya ɗauko wasu documents wanda ya turo aka yi masa printing domin submitting ya fita yaje office ɗin shugabansu ya yi signing sannan ya miƙa masa ya fita.
A bakin wasu tsayayyun jiragen ruwa suka tsaya inda ya samar mata wata rumfar shaƙatawa a kusa da shi ya shiga da ita yace ta zauna ta bashi one to two hours zai Dawo.
Sosai take iya hango shi da jiyo yanda yake musu bayani cike da ƙwarewa yana faɗin.
"Today we will start with safety procedures…"
Daga haka ya saka helmet ɗinda take hannunsa Sannan ya ce.
"Safety is the first rule in maritime....ba za ku taɓa zama cikakkun ma'aikatan tashar jirgin ruwa ba without proper safety knowledge."
Wani Box dake gaban shi ya buɗe ya shiga ciro kayan da ke ciki one after the other yana faɗin.
"This is called Life jacket, this is Safety helmet...Communication radio..Emergency kit..."
Murmushi ta ke ta yi wanda charting ɗinda suke ita da Na'ima shi ne abinda ya ƙara mata nishaɗi.
Wayarta naga ta ɗaga tayi masa short video daga nesa ba tare da ya sani ba, sannan ta dawo da fuskar wayar tana ɗaukar kanta na en wasu mintuna sannan ta katse ta tura mata ta rubuta mata.
"Tare dani ya taho wurin aikinsa Yaa Na'ima...har yanzu mamaki nake!"
Emojin dariya ta turo mata sannan ta ce.
"ki riƙe wuta ƙanwata,kafin hutun ki ya ƙare ki tabbata kin gama da shi, kada ki yarda ki bashi rata kada ki bashi sarari.... Ki tabbatar masa da cewa ba zai iya rayuwa ba idan ba ke a kusa da shi...."
Ita dai dariya kawai take aika mata da ita wanda ya ɗan so ya ɓatawa Na'ima rai ta ce.
" Ina miki magana mai muhimmanci kina dariya ko? Wallahy da gaske nake miki, ni wallahy har asibiti nake bin Haisam mu kwana kuma ba don ina rashin lafiya ba a'a, saboda ba zai iya ba sai da ni a kusa da shi, wannan shi ake kira mutual bonding between husband and wife. Ke da kike da irin wannan mijin masha Allah idan ba ki kame shi ba ai wallahy kina tare da ciwon zuciya domin kema kin san dole mata sai sun bibiyesa.. "
Sosai ta ji zuciyarta ta buga a wannan lokacin duk da cewa ita ta san ba son shi take ji ba. Ƙara ɗago kai ta yi ta kalle shi wanda ita kanta tasan mai kyau ne. Kyaun da a wasu lokutan ko tunowa tayi da shi sai ta ji zuciyarta ta amsa. Aure ne ke tsakanin su, auren da babu wata macen da ta isa ta kira shi da sunan Mijinta sai ita.
Hakan yasa ta nutsu sosai a wannan karon ta yi ta ɗaukar maganganunta tana yi musu register a ƙwaƙwalwarta.
A haka dai suka shafe tsawon kwanaki takwas tana ƙara jinjina zancen Na'ima a ranta. Duk yanda taso tayi wani yunƙuri ta kasa, gabaɗaya hankalinsa ba'a kanta yake ba 24hours yana kan aiki kamar wani Engine.
Yau ma koda ya shirya yace mata ta shirya sai kawai yaga ta girgiza kai ta ce.
"Yau dai a gida zan zauna, ina so in dafa mana abinci da kaina domin na gaji da na kasuwan nan..."
Kallonta ya yi da mamaki ya ce.
"Do you know how to cook?"
Wani kallon kama raina wayo na ta yi masa sannan daga ƙarshe ma ta yi wata 'ƴar dariya ta ce.
"Ta ya ya za ka yi tunanin ban iya girki ba? Na iya mana."
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Ni kuma ban iya ba..."
Murmushi ta yi ta ce.
"Ba laifi ba ne don baka iya ba domin Allah bai ɗora maka ba, sai mu Mata da ya kasance aikinmu ne."
"Uhm! So, In sha Allah zuwa an jima za'a kawo miki komai da kike buƙata..."
Hannunsa ta riƙe har zuwa bakin ƙofa tana murmushi ta ce.
"Allah ya bada sa'a. Allah ya taimaka ya tsare gabanka da bayanka..."
Da amin ya amsa yayin da ya bi ta da wani kallon har ta juya ta koma ciki.
Yana fitowa ya duba yaga kiran Maami har guda biyu wanda yana sane yanzu yake saka wayan a silent Domin baya so ya zama Anaam ta fara zarginsa domin ya lura tana da matukar wayau da saurin fahimtar abu.
*******
Faris yana tsaye cikin office ɗinsa yana haɗa kayansa domin tafiya gida sai ga Rabi'a ta turo ƙofa ta shigo.
Da mamaki yake kallonta har ta ƙaraso wanda daga ƙarshe ya ɗauke kansa.
Jiki sanyaye ta tsaya a ɗan nesa da shi ta ce.
"Please ka yi haƙuri dan Allah! Zuciyata a wahalce take da tsananin dakon kewarka..."
Waigowa ya yi ya kalleta tare da katse mata maganar ta ya ce.
"Haka kawai kika guje ni, na kira-na kira but you refuse me...saboda auren Anaam kika yanke alaƙa dani kina jin tsoron nuna ni a matsayin wanda zai aure ki...."
"Haba Faris dan Allah...."
Hannu ya ɗaga mata alamar ta yi shiru sannan ya ci gaba da cewa.
"Ni ba shashasha ba ne da zan dinga hanging around with you. Ba zan ci gaba da ɓatawa kai na lokaci ina bibiyar ki ba. Tun tuni na so ayi auren nan ki ka ce ke a'a mudai jira, to jiran me zamu yi? Ni nake da ra'ayi na ba wani ba,babu wanda ya isa ya tilasta min abinda ban yi niyya ba, sannan ga abinda nake muradi kuma, to babu wanda ya isa ya hanani...if you are not ready, I will find someone Domin ba zan ci gaba da zama kina ɓata min lokacina ba. Ina so in yi aure ko don yanda iyaye na suka damu..."
Jinjina kai ta yi tare da share hawayenta ta ce.
" Ni ma Baba ya take min gidan wuta ya ce dole sai na fito da miji, saboda haka na amince kuma na shirya ka turo iyayenka."
"Miye ya kawo ki Gusau?"
Tana ƙara share hawayenta ta ce.
"Na dawo gida ne sanadiyyar wata 'ƴar matsala da ta faru."
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Okay. Ki je zan zo."
Fitowa ta yi da bala'in jin haushinsa a ranta, yanzu yana nufin ba zai iya rarrashinta ba ne ko ya ya? Sannan ga mota maimakon ya zo ya kaita gida shi ne zai wani ce wai taje zai zo.
Koda ta shiga gida ta tarar da Baba Salisu a harabar gidan inda yake kishingiɗe bisa tabarma da pillow yana sauraren Redion da ya kamo ya baza muryarsa ko'ina ana ji rarara.
A duniya wannan rayuwar ta Baba tana bata baƙin ciki. Shi kawai harakar tsofaffin mutanen ƙauye Ita kaɗai ya iya a rayuwa.
"Rabi'atou..."
Zuwa ta yi ta tsuguna ta ce.
"Gani Baba."
"Daga ina kike?"
Duk da irin yanda zuciyarta ke wani irin bugawa, hakan bai hana mata buɗe baki ba ta ce.
"Baba Faris ne yace zai turo iyayen sa domin a saka mana ranar aure..."
Gyara zamansa Baba ya yi da kyau yana kallonta cike da neman ƙarin bayani ya ce.
"Faris..wane Faris ɗin?"
"Baba Faris dai na gidan Alhaji Gimba Taunau..."
Shiru ya yi na wani lokaci yana ƙara jaddada maganar a ransa sannan daga ƙarshe kwatsam ta ji saukar wata babbar sandar da ke gefen sa a gadon bayan ta wanda ya sanyata rugawa da gudu a gigice ta shige cikin gida wurin Umma tsabar yanda dukan ya shigeta.
Ko takalmi babu a ƙafar sa ya tashi afujajan yabi bayan ta yana faɗin.
"Ni za ki rainawa wayau Rabi'a? Ni za ki ciwa mutunci ki tona min asiri? Ɗan Gimban ne saboda baki da kunya za ki kalli tsabar idona ki ce wai za ki aure shi...Mutumin da bai da mutunci bai san darajar tare ba. A gabanki ya ci mana mutunci ya toxar tamu ya tozarta mutuncin 'ƴar uwarki a idon duniya, shi ne saboda baki da mutunci ki ce min shi za ki aura? Azzaluman mutane maha' inta su kike so na haɗa iri da su... "
Cikin yanayin fushi Umma itama ta fara faɗa tana faɗin.
"Alhaji ita fa soyayya ba ruwanta da wannan. Yara kuma Allah ne ya haɗa su..."
"Ummu-Salma.!!"
******
Sai misalin ƙarfe shida da rabi na yamma ya shigo gidan wanda a yau shirin gidan na musamman ne ta yi shi domin yasha bambam da sauran ranaku.
Lumshe idanunsa ya yi tare da samun kujera ya zauna ya fara cire takalmin sa yana mai jin yanda ƙamshin gidan ya gauraya da sanyin Acn ya bada wani ƙamshi na daban.
Fitowar ta shi ne abinda ya dakatar da shi yasa komai ya tsaya masa cak, wani abu ya ji ya fara circulating brain ɗinsa lokaci ɗaya.
She look beautiful! And her dress too looks very crazy...
Shi ne abun da ya ambata a ransa yana mai bin ta da kallo tamkar idanun sa za su fito waje. Sosai numfashinsa ya shiga yin sama da ƙasa domin shigar ta ba'a magana. To wai yau rigar kunyar ta ta cire ta ajiye gefe ta yi irin wannan shigar ko me?
Tamkar vex marar amfani haka yake ganin jikinta musamman saman ƙirjinta da ya kasance a buɗe duk rabin boobs ɗinta a waje duk da cewa ba wasu manya ba ne. Da wannan rigar da babu ita duk ɗaya.
"Welcome..."
Wani abu ya ji ya wuce masa a maƙoshinsa da ƙyar sannan ya jinjina kansa alamar ya amsa domin harshensa da yawun bakinsa sun kasa bashi haɗin kai wurin tattaro kalaman da ya dace ya furta mata a yanxu.
Wannan yarinyar ashe bata da kunya bai sani ba? Yana ganin kaman ba ruwanta.
"Are you okay?"
Shaking ɗin kansa ya yi tare da runtse idanunsa ya buɗe da ƙarfi tamkar mai jin jiri ya ce.
"Maryam miye haka kuma?"
Duk da cewa a tsorace take, hakan bai hana ta buɗe baki ba ta ce.
"Miye ya faru? Sannu da zuwa. Please zo ka ci abinci..."
Kallon dirarren bayanta ya shiga yi wanda ya kasance a buɗe sanadiyyar wannan shaiɗaniyar rigar da ta saka bayan ta juya zuwa Dining table wanda sai da ta sake juyowa sannan ya kawar da idon sa gudun abun kunya.
Tahowa ta yi ta kamo hannunsa tana murmushi wanda a take ya ji kwanyarsa ta shiga hautsinawa sanadiyyar wani mashahurin ƙamshinta da ya daki ƙofofin hancin sa wanda ya sanya shi lumshe ido ba shiri.
A shagwaɓe ta ce.
"Uhmm! Ta so mana please...wannan fa shi ne girkina na farko. I assured you it will taste better..."
Wai da gangan take duk wannan ɗin ko kuma a rashin sani ne? Ko dai wai wasu aljanu ne suka shige ta yau bai sani ba?
Da kanta ta yi serving plate ta ɗora mishi a gabanshi sannan ta zuba mai lemun fruit da ta yi grinding ta haɗa shi da kanta ta yi mai murmushi wanda idonsa ya sauka akan lips ɗinta da ke ta glowing suna sheƙi gwanin burgewa sanadiyyar lip glow ɗinda ta Shafa.
"I'm coming..." Ta ambata tana mai bashi baya.
Briefcase ɗinsa ta ɗauka da takalminsa a karon farko ta shige ɗakin sa kai tsaye.
Mamaki take da al'ajabin yanda taga gabaɗaya ya ruɗe kamar wani magani. Tabbas Yaa Na'ima ta yi gaskiya da tace ta jaraba wannan yau ta gani. Tsoro take ji tare da jin faɗuwar gaba, amma kuma da ta tuna cewa tana so ta samu lokacin Mijinta sai ta ji ta samu ƙwarin gwiwa.
Ita kanta a takure take da wannan rigar,sai da ta yi kamar tana yi sannan ta samu ta lallaɓa zuciyarta har ta ba ta wannan haɗin kan wanda da alama kamar ta fara yin nasara.
To idan ya ga kaman tayi rashin kunya fa? Only one month ne suka yi spending kada ya za ta ko ya yi tunanin wai she need something daga wurin shi. She only needs his attention right now Bayan shi babu komai a mind ɗin ta.
Tana ajiyewa ta matsa gaban wani table dake gefe ta shiga kallon ƙananun frames guda uku waɗanda ya jera su tare da juna.
Ɗauka ta yi ɗaya bayan ɗaya ta shiga dubawa wanda sai da ta gama duba su ta fahimci cewa duk mutum ɗaya ne, kuma suna kama da mutumin.
Bayan wani ƙaramin akwatin glass dake gefen table ɗin ta sake ɗauko wani frame wanda ta ganshi lokacin da yake ƙarami tare da mutumin wanda suna dariya aka yi hoton. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 47*
A darare ya kai one spoon a bakinsa ya shiga chewing a hankali tamkar Wanda aka cewa akwai wani poison a cikin abincin.
Girkin Maami, girkin gidan Naana, girkin da yake ci a mabanbanta Eatry da kuma girkin Hamad duk kowane da taste ɗinsa, Na Maami has different taste because ya sha bambam da sauran wanda bai sani ba ne ko don shi ne abincin da yafi yawan ci a rayuwarsa, but this one too...the aroma is something else wanda har ga Allah ya yi masa daɗi sosai a baki.