Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 39

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 39

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 39: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 39. Da ace bata sanar masa cewa ita ce ta girka ba da ba zai taɓa…

3,375 words

Da ace bata sanar masa cewa ita ce ta girka ba da ba zai taɓa yarda ba because su Zarah da su Arwah yaran uncles ɗinsa dake zaune a gidan Naana kai harda ma waɗanda ke gidan iyayensu da yake tunanin za su iya zuwa sa'anni da ita da suke schooling shi shaida ne da cewa bai san akwai wacce ta iya girki ba a cikin su, sai mutum ɗaya, wato Nazlin gidan Uncle Ameed wacce yasan ita tun tasowarta tana da rayuwar son girke-girke hakan yasa ta cusa kanta har ta iya amma kam sauran aikinsu kawai karatu, ci, sha bacci.

Ci gaba ya yi da cin abincin a hankali wanda yana yi yana ganin wulgawarta a idonsa har ya kambala sannan ya tashi ya koma kan kujera ya yi shiru tare da ƙura idanun sa a TV.

A zahiri za ka ga kamar cewa da gaske kallon yake amma kuma can cikin ransa hankalinsa da tunaninsa basa wurin.

Ƙofar room ɗinsa ya kalla tare da tunanin ko me take a ciki oho! But honestly ta yi matuƙar ba shi mamaki a yau.

Bai kai ga ɗauke idon nasa ba kwatsam ta fito cikin sa'a kuma idanun su suka sarƙe hakan yasa ya kauda kai da sauri yana mai taking deep breaths a hankali tare da ƙoƙarin daidaita kansa. Sai dai kuma ji yake yana so ya gardamawa umarnin zuciyar sa domin idanunsa sun kasa daina kallon cute lips ɗinta da ke sheƙi tamkar an shafa musu zuma.

Gabanta ne ya tsananta bugawa wanda yasa ta ɗan sunkuyar da kanta kaɗan tana jin kunyar kallon da yake mata. Ta lura da yanda idanunsa suka canja sosai yana yi mata wani irin kallon da bashi ta saba gani ba.

"Miyasa ka ke kallona a haka?"

Ta faɗa a hankali tana mai ɗan ƙara komawa baya kaɗan domin gani take kamar ma baya hayyacinsa.

Da ƙyar ya ɗauke idonsa daga fuskarta a wannan karon tare da sunkuyar da kansa yana ɗan murza goshin sa lokaci ɗaya kuma ya runtse idonsa da ƙarfi ya buɗe tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ya ɗago cikin wata irin murya wacce ta nuna alamar laushi sosai ya ce.

"Kina ji Maryam...wannan shigan taki..."

Ya ambata kai tsaye amma sai ya ji ya kasa ƙarasawa.

Girar ta ta ɗage still da wani murmushin ƙarfin hali ta ce.

"Ba tai maka ba ne?"

Kansa ya girgiza da sauri yana mai jin yanda zuciyarsa ke wani irin pumping da Sauri ya ce.

"No... it's not bad. It's... it's just..."

Sai kuma ya sake yin shiru a karo na biyu yana mai neman kalmar da ta dace ya furta mata kada ya je ya kofsa.

Miƙewa taga ya yi ya nufota wanda da gudu ta koma cikin ɗakin sa tamkar wata wacce taga abin tsoro ta lafe a jikin gini ta shiga waro ido tare da jin wata irin nadama a ranta nan take.

Ƙarasowa ya yi har inda take tsaye ita kuma cikin ruɗewa ta ce.

"Please I'm sorry! Dan Allah ka yi haƙuri kada ka...kar ka.."

Ido ya zuba yana yi mata wani kallon mamaki domin ya ma kasa gane abinda take magana a kai. Itama dai maganar ce ta maƙale mata domin bata san mi za ta ce ba kada taje tayi wani shirmen kuma.

" Maryam... "

Idonta ta mayar a kansa ta kalle shi ba tare da ta amsa ba ya ce.

"We need to talk."

Daga haka ya janyo ta suka zauna a bakin gadon ɗakin nasa sannan ya ɗaga hannunsa ya yi twisting a na ta calmly ya fara mata magana da cewa.

"Maryam...you don't have to do all this to me kin ji ko?"

Kallon sa take da mamaki wanda ganin kallon da take masa ɗin yasa ya miƙe domin ya kawar mata da zargi ya ja hannunta suka dawo parlourn ya kalle ta ya ce.

"Kin ci abincin?"

Girgiza kai ta yi alamar a'a sannan ya Jinjina kansa yace.

"Okay...ki ci abincin zan fita sallah kinga time ɗin magrib ya yi."

Kallonsa take har ya shige da mamaki a ranta wanda bata ɗaga nan ba har ya fito sanye cikin jalabiya black as usual ya fice ba tare da ma ya ƙara kallon inda take zaune ba.

******

A gidan Baba Salisu kuwa, kiran Umma ya yi cike da jin wani sabon mamakin ya ce.

"Soyayya? Ta rasa da waye za ta yi soyayya sai Farisu? Wallahy tallahy ko maza sun ƙare a duniya ba za ta aure shi ba..."

Sallamar Mubarak ita ce ta katse shi daga ƙarasa zancen tare da juyowa ya kalle shi rai a ɓace ya ce.

"Mubarak...Ka ji wani zancen banza zancen wofi da Rabi'atu ta isko ni da shi? Da yake ita ɗin mutuniyar banza ce da bata gudun zuciyar iyayenta..."

Girgiza kai Mubarak ya yi wanda dawowarsa daga wurin aiki kenan ya biyo ta nan domin tun safe Baba Salisun ya kira shi ya ce idan ya taso ya zo yana neman sa, to sai gashi kuma ya tarar da wannan abun wanda yasa shi kallon Rabi'ar sannan ya Kalli Baban ya ce.

"Baba miye kuma abinda yake faruwa?"

Kai tsaye Baba ya ce.

"Wai ni Rabi'atu za ta isko tace min wai Farisun gidan Alhaji Gimba za ta aura..."

Wani irin kallon mamaki ne Mubarak ya jefa mata daga ita har Umman sannan ya ce.

"Faris.!!!"

"Tuna mata dai ko za ta shiga hankalinta domin wallahy tallahy ba za ta aure shi ba ko za ta mutu. Mutumin da baya son ƙanin ubanki baya son iyalinsa ke har muma baya son mu ki ce wai za ki auri ɗansa? Mutumin da yasa aka yi garkuwa da ɗan uwanki aka azabtar da shi tamkar wani bawa kike tunanin shiga inuwa ɗaya da ɗansa? To ku zauna ma ta ya ya kenan?"

Ajiyan zuciya Mubarak ɗin ya sauke a hankali sannan ya kalli Baba ya ce.

"Baba...Ka ma kwantar da hankalinka domin wallahy ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba Alhaji Gimba ba zai taɓa bari Faris ya aure ta ba. Saboda haka ka ƙyale ta. Kuma ke..."

Ya waigo ga Rabi'atun wacce ke ta faman sharar hawaye ya ce.

"Ki kiyayi kanki....Faris ba zai taɓa auren ki ba, idan ma ya amince mahaifinsa ba zai amin ce ba.."

Turo baki ta yi gaba tana gunguni ta ce.

"Wallhy Tallahy Yaa Mubarak ni shi nake so, kuma shi zan aura. Daman cewa ya yi na faɗa a gida cewa zai turo..."

Sandar da ke hannun Baba ya sake ɗagawa sai ga shi ta ruga da gudu ta shige ciki tare da turo ƙofa.

Cikin wani baƙin cikin da ya hanawa Umma magana tun ɗazu ta wani mere baki ta ce.

" Ni gaskiya bana son haka! Kowa an aura mata wanda take so, sai ita ce za'a nuna son kai ace ba'a amince da ta aure shi ba saboda ita ba ɗiya ba ce ko me? Miye aibun Faris?"

Jinjina kai Mubarak ya yi ya ce.

"Umma Faris ba shi da wani aibu amma kuma Abinda ke tsakanin mahaifinsa da Alhaji ne za ki duba. Umma sai idan kin so kanki a wannan gaɓar amma kema kin san aure tsakanin su har abada ba zai faru ba."

"To idan kuma Allah ya yi ya nufa matarsa ce banga wanda ya isa ya hana ba."

Daga haka ta juya ta shige ciki ta bar su kowa da mamakin wannan abin da suka ɓullo da shi. Umma ba ta son a zauna lafiya a rayuwar nan.

Kallon Mubarak ɗin Baba Salisu ya yi jiki sanyaye ya ce.

" Yaushe ma ka ce za ka tafi gida?"

" Zuwa friday in sha Allahu, daga zaran Yaa Naseer ya dawo ya iso da kayan zan wuce."

"okay to, zo mu je.."

Hanya ya kama su koma part ɗinsa suka shiga parlour suka zauna still hankalinsa a tashe Baban yace.

"Mubarak don Allah koda ka koma gidan nan kada ka sanarwa Mas'ood da wannan maganan dan Allah. Wallahy abin ma kunya ne abun takaici ace mun bar wannan magana ta kai kunnen sa. Alhaji Gimba Sam ba mutumin arziki ba ne da har za'a nemi a haɗa zuriya da shi..."

"In sha Allah Baba ka kwantar da hankalinka domin wannan auren har abada ba zai faru ba."

"To Allah yasa. Allah ya kyauta yasa mu da ce. Ya can wurin su Maryam kuma?"

"Alhamdulillah! Tana nan lafiya ƙalau, da yake ma kasan mijin ya tafi da ita Lagos wai kafin su fara next semester..."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Haka fa, daman ko Na'ima ta faɗa mini ranar a waya. Allah ya taimaka ya ƙara basu zaman lafiya amin."

Miƙewa ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya ce.

"To Baba bari na ƙarasa gida naga magrib ma ta ƙarato...."

"Haka ne, Allah ubangiji ya bamu alheri amin..."

*******

Anaam tana gama sallar Isha ta sake sheƙa wanka da wata irin nighty wacce tafi ta ɗazu rashin albarka, domin wannan ɗin tamkar net haka ta ke komainta a waje.

Zaunawa ta yi zaman jiran sa wanda bai dawo ba sai da ya tabbatar ta yi bacci sannan ya shigo misalin ƙarfe sha biyu da rabi na dare. Da ƙyar da suɗin goshi ya samu ya yakice ta a tunanin shi saboda haka ba zai yarda ta kai shi ta baro ba. A darare ya leƙo ɗakinta inda ya hango ta a can ƙarshen gado ta takure sosai ta nannaɗe a cikin Duvet tana sauke numfashi a hankali.

Juyawa ya yi koma ya zauna ya ci wani daddaɗan snacks da ta yi wrapping ta ɗora a plate ya ci kusan guda huɗu sannan ya sha lemu ya tashi ya wuce ɗakinsa ya zauna yana ta haɗa bayanai waɗanda zai yi presenting gobe idan ya isa Depot ɗinsu na Maritime da ke Oman.

Ya kai kusan 3am sannan daga ƙarshe ya tashi ya kwanta wanda bai wani jima ba kuma ya tashi ya shirya.

A kitchen ya sameta tana ta uxurin haɗa masa breakfast Wanda hakan shi ne abinda ya sage masa gwiwa a hankali ya kira sunanta tamkar shi ne wanda ya raɗa mata shi tsabar yanda ya saba da sunan a yanxu ya ce.

"Maryam..."

Waigowa ta yi da wani irin kalar murmushi wanda daga ita sai mahallincinta ne kaɗai suka san abinda yake ranta ta ce.

"Good morning..."

Jikinsa ne ya yi sanyi ganin yanayin fuskarta da alama kamar ta yi kuka ma.

"Are you okay?"

Murmushin ta sake yi tare da ƙoƙarin ganin ta kaucewa kallonsa ta ce.

"I'm fine....ka ɗan jira kaɗan yanzu zan kawo maka abincin."

Parlourn ya koma ya zauna a dining room shiru tamkar wanda ruwa suka cinye tsawon lokaci with different thoughts in his mind Sannan can sai ga ta ta iso ta jera masa komai gwanin sha'awa.

Ta juya kenan ta ji ya riƙo tsintsiyar hannunta hakan yasa da sauri ta waigo sai ya ce.

"zamu iya mu ci tare?"

Jinjina kanta ta yi ta ce.

"Yeah...but ka fara kada na tsayar da kai nabar abu a wuta."

Sakin hannun na ta ya yi ta koma kitchen ɗin ba don tana da wani aikin da ya rage mata ba kaman yanda ta ce. Al'amarin sa ne kawai yake ba ta mamaki da al'ajabi. Sai ya yi tamkar bai san tana existing ba a cikin gidannan sai ya yi tamkar bai san wace ce ita ba ko kuma matsayinta.

Kanta ta saukar ta shiga kallon irin shigar kayan da ke jikinta amma ko kaɗan bai nuna alamar hakan ya dame sa ba.

Tana nan a tsaye ya sake leƙowa wanda a yanzu ya shigo har inda take tsaye ya kamo hannunta ɗaya ya riƙe a nashi yana kallon fuskanta ya ce.

"Maryam ko akwai wani abu? Please idan akwai feel free and talk to me kin ji ko?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"Ba komai. Allah ya tsareka ya taimaka."

"Amin. Za ki rakani mota?"

Ba musu ta biyo shi hannunta a cikin na shi har bakin mota inda taga ya ajiye wasu files da kuma wata black Bag a backseat ɗinsa.

"Allah ya tsare..."

Daga haka ta juya ta koma ciki wanda bai ɗauke idonsa a kanta ba sai da yaga ta shige ciki sannan ya sauke wata irin ajiyar zuciya tare lumshe idanun sa ya buɗe sannan ya tayar da motar ya wuce.

Tana shiga ta tarar da miss calls ɗin Ammie hakan yasa ta ɗauki wayan tare daidaita nutsuwarta sannan ta kira ta.

Bayan sun gaisa ne Ammien ke sanar da ita Walimar saukar Fatimar gidan Yaa Muhammad da za'a yi sati mai zuwa. Sosai ta ji daɗin wannan labarin domin ta gama yanke cewa za ta ce ya mayar da ita gida Abuja because a can ɗin ma ya fiye mata farin ciki domin ko ba komai time to time tana ganin en uwanta suna ɗebe mata kewa.

Bayan sun gama wayar ta koma ɗakinta ta kwanta akan gado a hankali sai gashi bacci ya sace ta kasancewar daren jiyan ba ta samu ta yi wani baccin kirki ba tsabar baƙin ciki da damuwa.

Tana nan tana ta bacci bata farka ba sai misalin ƙarfe biyu sannan ta tashi ta yi sallah ta shiga kitchen ta sake girka masa abinci ta jere masa sannan taje ta yi wanka ta saka atamfa riga da skirt da ɗankwalinta waɗanda suka yi mata kyau sosai.

Tana nan har 6pm ta wuce har aka yi sallar magariba bai dawo ba. Mamaki ne ya daɗa kamata wata zuciyar ta ce ta dai ƙara jiran sa ta gani.

Wasa wasa sai ga shi ta kwana ta wuni bai dawo gidan ba sannan kuma bai kira ta ba. Ta so ta kira Hamad ta tambayesa domin tasan wurin aikinsu ɗaya because kullum suna haɗuwa idan ta bi shi suka tafi, but idan ta kira shi miye za ta faɗa masa? Abinda fa ya ji ya gani shi zai faɗawa Yaa Dina. Hakan yasa sai ta kawar da tunanin kiran nasa a ranta.

Haƙiƙa ta shiga cikin wani irin matsanancin baƙin cikin da bata san ma ya za ta misalta shi ba. Zargi ɗaya ta fara a ranta shi ne cewa Maheer neman mata yake. Neman mata yake wanda baya da lokacin ta sai na su da kuma wata ƙil a gare shi sam karenta bai kai tsaiko ba domin bata ishe shi kallo ba. Yana da wasu matan wadanda yake gani da tunanin cewa sun fito komai shiyasa.

Wannan auren a yanxu ji take ya kasance jarrabawa a gare ta. Ahlinta sun zaɓa mata shi sun kuma ɗauka cewan shi ne zai zamto jigo kuma jagoran farin cikin ta. Ashe shi ne sabon tsanin da ta hau ba tare da sanin cewa shi ne zai ƙarasa nakasa rayuwarta kamar can baya. An ce aure rahama ne, aure farin ciki ne, aure nutsuwa yake bayarwa da kwanciyar hankali, duk yanda Amarya take atleast wannan tarairayar da soyayya da kuma ɗokin amarci ta kan same shi ne ko ba yawa, to ita kam ko na kwana ɗaya bata samu ba sai baƙin ciki. Ba komai a cikin zuciyarta daga aure zuwa yanzu sai ƙunci da danasani.

Ta yi nadamar wannan auren a yau kuma har abada ba za ta daina danasani ba. Kowa a danginta kallon mace mai gata da samun soyayya suke mata, amma ba su san cewa da ita da babu ita duk ɗaya suke a wurin miji ba. Bata so ta zama mai yawan complain, bata so ta zama mai yawan ƙorafin gidan aurenta. Yaa Na'imar ma ba za ta sake faɗamata damuwar ta ba ballantana ta ɗaga mata hankali.

Kamar yanda aka saba faɗa cewa kowa haƙuri yake a gidan auren sa kuma kowa da ƙaddararsa, to haka itama take jin cewa ba ta yi aure don ta fita ba, tunda har haka ƙaddarar ta ta zo, to za ta ci gaba da haƙuri,za ta zauna ta yi ta haƙurin har zuwa numfashinta na ƙarshe. Kuma alƙawarin da za ta ɗaukarwa kanta shi ne, za ta cire shi daga cikin ranta ta manta da cewa su ɗin mata da miji ne, a duk lokacin da yaje yawon bin matan sa ya dawo, koda kwana nawa zai yi, ko wata nawa zai yi, ko shekara nawa zai yi ba za ta ƙara nuna cewa ta damu ba, idan yana nan za ta yi masa girki sannan ta rakashi idan zai fita domin biyayyar aure take kaman yanda ta sani wanda kuma ladanta tana a wurin Allah, idan ya yi mata magana za ta kula shi ba tare da nuna wata damuwa ba in sha Allahu. Allah yana sane da ita, waɗanda suke gidan aure cikin jindaɗi ba su suka rubutawa kansu wannan ƙaddarar ba, ita ma kuma da ma wasu ire-irenta dake cikin ƙunci ba su suka zaɓarwa kansu ƙaddarar ba. Saboda haka za ta ci gaba da haƙuri wanda ba za ta ƙara kuka ba.

******

Rabi'a kuwa, gabaɗaya kukan ta yaƙi ya tsaya hawayen ta sun kasa daina zubowa tsabar bakin ciki. Sun fi hour Umma na rarrashinta amma taƙi ta saurare ta.

Ƙarshe ta miƙe tsaye tana wani irin kuka ta ce.

"Ni wallahy gidan zan bari in bar garin gabaɗaya tun da kema kin kasa tsinana mini komai. Ba zai yiwu ace ina gani Yaa Na'ima na zaune gidan hutu gidan jindaɗi ita da Anaam ba sannan ni ace ba za'a bari na auri wanda nake so ba..."

Cikin tashin hankali Ummahn ta ce.

" A'uzubillahy! Haba Rabi'a wannan wace irin magana ce?.."

" To Umma tunda kin kasa ƙwatar min 'yancina tsawon kwanaki kin rabke hannu kin yi shiru ba dole raina ya ƙara ƙone wa ba.."

Riƙo ta ta yi zuwa jikinta tana share mata hawaye ta ce.

"Idan ban cika miki burinki ba miye amfanin rayuwa ta? Ki bar ni yanzu zan kira Shema'u in sha Allahu zamu shawo kan wannan matsalar ba jimawa na yi miki alƙawari."

Jinjina kai tayi alamar yarda da ita sannan daga ƙarshe ta wani karyarda wuya tare da shagwaɓe murya ta ce.

" To Umma Faris da ya ce zai zo an jima ya zan yi kenan tunda Baba yaƙi yarda da zancensa?"

" Ki shirya ki wuce gidan Shema'u ko Binta sai ya same ki a can kuyi firar ku idan kun ƙare sai ki dawo..."

"Umma idan na tafi can yana iya yin fushi ya ce har yanzu kenan tsoron nake aji cewa muna tare dashi..."

Ɗan Jim ta yi kaɗan alamar nazari sannan daga ƙarshe ta jinjina kanta ta ce.

"To ki bar shi yazo nan ɗin, ni nasan mi zan yi."

"To umma na. Allah ya bar min ke."

"amin amin. In sha Allahu Faris kin aure kin gama duk wani ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu, mu ba ruwanmu da gabar da ke tsakaninsu su suka sani can su ƙara ta."

******

Kwana ki biyar ya share a Oman yana ta harkokin gabansa tamkar bai san ya baro wata Maryam a Nigeria ba.

Kwana biyu a gidansu Naana ya yi su tsakanin familyn shi cike da farin ciki sannan ya kwana uku a gidan mahaifiyarsa wacce ke ta ɗoki da lissafin ya kusa kambala wannan aikin ya dawo.

Abun da ya ƙara bashi mamaki shi ne yanda aka tabbatar mai cewa taje har Companyn nasu ta ƙara jaddada musu kada a sake ba shi wani aiki muddin a nigeria ne. Kowace ƙasa a duniya ta yarda yaje amma bata son Nageria daga wannan ɗin. Idan kuma ba haka ba to tana maraba da shaidar sallama kowace iri ce domin hakan ya fiye mata kwanciyar hankali.

Yau ma da zai dawo har Airport ta rako shi kaman yanda ta saba ita da Uncle ɗinsa Abdallah kuma abokinsa wanda ya kasance Ƙanin Maamin tasa.

Bayan sun yi sallama Uncle Abdallahn ya kalle shi yana murmushi ya ce.

"Aunty Lailah ta zuba maka ido ta bar ka babu wani zancen aure a gabanka ko?"

Karɓe zancen tayi tana dariya tare da riƙo hannun Maheer ɗin ta kalli Abdallahn ta ce.

"Aure Lokaci ne Akhiy, kaima baka yi ba sai da time ɗinka ya yi. Saboda haka shi ma watarana zai yi..."

Hannunsa ya zame tare da yin gaba yana faɗin.

"Idan na ci gaba da biyeku I will be late Maami..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull