Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 40

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 40

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 40: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 40. Hannu ta shiga ɗaga mishi tana faɗin.

3,359 words

Hannu ta shiga ɗaga mishi tana faɗin.

"Alright! Bye-bye...please take care."

Tunda ya shigo jirgin har ya sauka tunanin Maryam bai bar shi ya huta ba ko na second ɗaya.

Sai da ya shiga gidan sannan ya duba wristwatch ɗinsa yaga ƙarfe ɗaya na dare ne da mintuna ashirin cif. Ba lallai ace tana farke ba. Hakan yasa ya shiga ɗakinsa ya ajiye kayansa ya yi wanka sannan ya fito kai tsaye ya shiga ɗakinta a hankali cikin sanɗa tamkar wani ɓarawo.

Kan sallayah ya ganta zaune ta jingina bayanta da gefen gado ga ƙur'ani a gabanta da alama shi take karantawa.

Kallo ɗaya tayi mishi sai kawai ta ji gabanta ya faɗi wanda bata san dalilin hakan ba. Ba ta ji ta damu ma da ganin sa ɗinda ta yi ba, but how comes zuciyanta marar adalci za ta shiga bugawa fiye da ƙima?

"Welcome..."

Kalmar da ta furta kenan tare da saukar da idonta ta ci gaba da kallon ƙur'an ɗinda yake gabanta.

Shiru ya yi tare da samun wuri kan Sofa ya zauna na tsawon lokaci tare da zuba mata ido yana kallonta wanda take ta ji gabaɗaya ma ta rikice, hakan yasa ta rufe Alƙur'anin sannan ta miƙe ta kaishi wurin da ta tanadar masa na musamman sannan ta ninke sallayan ta cire hijabinta ta fita waje.

Iyaka 10mnt sai ga ta ta shigo ɗauke da wani wooden tray mai bala'in kyau wanda ta jero cups guda biyu, ruwa da kuma lemu ta ajiye masa a gabansa ta ce.

"Ban sani ba ko kana da buƙatan abin ci? Ko na girka maka wani abu ne?"

Wani irin abu ne wanda ba zai ce ga ko minene ba ya ji ya ratsa tun daga tsakiyar brain ɗinsa har zuwa tafin ƙafarsa. Gabaɗaya ta ruɗar da shi ta sa ya shiga wani irin yanayi. Tun a hanya yake hasaso tsananin fushi da borin da za ta hau yi masa, but unfortunately sai ya same ta ba yanda ya za ta ba. Gaskiya haƙurinta ya yi yawa. Shi yasan tana da haƙƙi a kansa amma kuma sai bata nuna ba. Wannan abun da ta yi ya yi matuƙar girgiza shi ya kaɗa masa zuciya.

Hakan yasa jiki a saɓule ya janyo hannunta a hankali ya zaunar da ita gefen shi tare da kamo hannun da ya saba riƙewa a darare yace.

"I'm sorry Maryam..I'm very sorry da yanda nake behaving....Tabbas na aure ki ne domin rarrashi da kuma baki duk wani farin cikin da kika yi deserving, na aure ki ne da nufin kawar da dukkan wata damuwar ki da baƙin ciki da ƙuncinda da kika fuskanta a baya wanda...wanda ina mai matuƙar baki haƙuri..."

Maganar ce ta kakare masa a maƙoshin shi ganin irin yanda ta zuba ido tana kallon shi ko ƙyaftawa babu. Lokaci ɗaya ya ji zuciyar shi na bugawa da sauri fiye da yadda ya saba ji a duk lokacinda ya tuna da mummunan yanayin da ya kasance da ita a shekarun baya wanda duk wani ƙuncinta da baƙin cikinta shi ne sila.

He thought he has all the courage...he thought he has all the good words ɗinda zai iya amfani da su yanzu wurin bata haƙuri da kuma faɗa mata gaskiya domin ya lura tunanin ta da zuciyarta sun zurma sun tafi ga abinda baya tunanin zai ci gaba a tsakaninsu ballantana ya ɗore.

He wants peace hakan yasa ya shiga yaƙi da zuciyarsa tare da ƙoƙarin kawar da abunda zuciyar tasa ke neman ruɗin shi da shi a kanta. He don't want any regret Saboda haka ba zai bari wannan ya yi nisa ba. Mace baka iya tsere mata ko waye kai musamman wacce take ganin kai ɗin halal ɗinta ne. Idan ka zame mata ka ƙaura ce mata za ta shiga damuwa da ganin cewa ka tauye mata haƙƙin ta.

Wannan abun da ta yi yanzu yayi matuƙar girgiza mishi zuciya wanda ba zai taɓa bari wani abun kunyar ya sake faruwa ba a tsakaninsu a karo na biyu ba.

To amma kuma ya kasa..ya ji gabaɗaya ƙwarin gwiwa da karsashin da ya ji a farko gabaɗaya ya suranye. Daman duk wanda ya saɓawa Allah ya tsallake dokar Allah yana tare da kunya. Ya aikata laifi so yake yanzu ga ta a gaban shi ya faɗa mata gaskiya domin su fahimci juna ya roƙeta ta yafe mishi amma kuma lokaci ɗaya ya ji wata irin matsananciyar kunya ta lulluɓe shi wanda ya ji kuma ba zai iya ba.

"Yanzu kenan ka fahimta ka gane cewa we didn't deserve each other right?"

Ta ambata tana mai zubo da ruwan hawaye masu tsananin ɗaci da baƙin ciki.

"Ka ƙi ka kaini wurin familynka, sai guduna kake kana ta bani excuses waɗanda na san cewa you are just doing it just to avoid me. And yanxu kuma so kake ka faɗamin cewa ka haƙura da ni? Na ɗauka cewa zan jure domin na yarda da duk wata ƙaddara mai kyau ko akasinta, but miyasa duk wani neman Matan da za ka yi idan ma yi kake ɗin idan ka gama ba za ka dawo gida ba?...."

Sake fashewa ta yi da wani irin matsanancin kuka ta ƙwace hannun ta tana girgiza kanta ta ce.

" Please just do it! Idan har so ka ke ka rabuda ni please ka yi hakan kada ka damu,wallahy zan fahimce ka kuma I promise you to accept my faith Domin ba wannan ne farko ba. Na shiga rayuwa da baƙin cikin da ya fi wannan kuma na take saboda haka yanzu ma kada ka damu, damuwa da baƙin cikin da zan kasance a cikin su na ɗan lokaci ne. Ni na san cewa ba ka so na...baka so na Maheer because har zuwa yau ko sau ɗaya ban taɓa ji ka furta kalmar so a gare ni ba koda da wasa ne. Ban san manufarka a kai na ba amma na jima da ji a raina cewa ba ka so na ba ka jin soyayya ta..."

Da sauri ya matso tare da janyo ta amma sai ta zille tare da miƙewa tsaye tana mai girgiza kanta tana ta wani irin kuka tana faɗin.

" Don't touch me...don't! Kai ɗin kyakkyawane ajin farko, kai ɗin mai kuɗi ne, ni kuma...baƙa ce kuma mummuna, sam babu ta inda muka dace domin rayuwarka da rayuwata sun yi hannun riga. A karon farko da akace min kace kana so na kana so ka aure ni na yi mamaki because ni a karan kai na ko kaɗan banga dacewar mu ba domin akwai mata a duniya da suka wuce ni a komai amma kuma ka zo ka ce kana so na. Daga aurenmu zuwa yanzu I have discovered alot of things waɗanda suka tabbatar min cewa you are just using me ga wata buƙata ta ƙashin kanka. Da ace ba daga familynsu aunty Dinaratu ka fito ba wallahy da nace wani bokan ya baka laƙani dani domin biyan wata buƙata da ƙashin kanka. And ko yanzu ina ji a jikina, kaman yanda mutane da yawa a yanxu ba abin yarda ba ne haka nima nake ji a yau cewa ban yarda da kai ba. Please idan har akwai wani nufi a ranka dangane dani I beg you for the sake of God dan Allah ka fice daga rayuwata. Da zuciya ɗaya iyayena suka aura maka ni, da zuciya ɗaya na amince na aure ka, ya rage naka ka ji tsoron Allah domin idan ka cutar dani wallahy Allah ba zai taɓa barin ka ba. Ka ji tsoron Allah! Manzon Allah (S.A. W) ya tabbatar mana a cikin hadisin sa ingantacce cewa: a lokacin da alƙiyama ta tsaya dukkan wasu halittu dake rayuwa a doron duniya Allah ya yi alƙawarin zai narkar da su su dawo turɓaya tamkar ba'a taɓa hallitar su ba,amma wallahy saboda girman haƙƙi da son Adalci daga wurin ubangiji mai rahama ya ce kafin a mayar da su turɓaya hatta dabba wacce ta zalunci er uwarta dabba sai Allah yace ta rama sannan daga ƙarshe a mayar da su turɓayar. Wannan ga wasu ababen halittu kenan wanda Allah ya yi alƙawarin cewa babu su a zaman wuta ko Aljanna. Amma mu kuma da muke en Adam da Aljanu..wallahy al'amarinmu mai girma ne da ban tsoro a wannan yinin. Duk wanda ya cutar da ɗan uwansa Musulmi ya zalunce shi ya yi masa zamba cikin aminci..."

A gigice ya taso da gudu ya wani ƙanƙameta da ƙarfin da ba za ta taɓa iya ƙwacewa ba ya shiga girgiza kansa da hawayen tashin hankali yana faɗin.

" Please I'm sorry...I'm sorry Maryam..."

Kicaniyar ƙwacewa ta shiga yi tana ta yi masa borin da ya ƙara ɗaga masa hankali wanda sai da ya yi da gaske sannan ya matse ta tare da kai bakin sa a hankali ya haɗe da na ta na tsawon minti ɗaya sannan ya janye kaɗan a hankali ba tare da ya janye fuskarsa daga ta ta ba.

Ji ta yi gabaɗaya lokaci ɗaya duniyar ta shiga kewayawa da ita da jin wani abun da bata san ya yake ba.

Kallon idanunta ya yi, sai ya gansu a rufe gam amma jikin nan nata gabaɗaya ya yi relaxed tamkar batir ɗinda cajinsa ya ƙare. Saitin kunnen ta na dama ya kai soft lips ɗinsa a hankali ya ce.

"I love you Maryam..."

Tamkar wacce ya furtawa wasu sababbin kalmomin da bata taɓa ji ba a rayuwar ta haka ta buɗe idanunta tana kallon shi.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 48*

Cikin wani yanayi na ruɗani da firgici Maryam ta tsaya cak tana kallon sa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi fiye da kowanne irin lokaci domin ji ta yi kamar nema yake ya gigita tunanin ta.

"I love you Maryam…"

Ta sake nanata kalmar a cikin kanta domin tantancewa ko za ta samu ta fahimci abinda yake nufi. So! Wane irin so kenan yake nufi? So na yaudara kenan ko me? Ita tasan cewa bai taɓa son ta ba, kuma baya son ta. Yau ma kalaman yaudarar da ya saba furta mata ne yake so ya yi amfani da su domin ya mamaye ta? Idan yana sonta ba zai dinga gudunta ba. Idan yana son ta ba zai riƙa yi mata ƙarya ba. Ta ci abinci? bata ci ba? Ya ta kwana? Ya ta tashi? Bai sani ba. Tana farin ciki ba ta farin ciki bai sani ba. Daga auren su zuwa yanzu babu abinda ta samu sai damuwa da baƙin ciki. Ya tafi tsawon kwanaki sannan sai da ya ga dama ya dawo shi ne yake so ya ƙara rai na mata hankali kaman yanda ya saba. Wannan ba so ba ne! Ba so ba ne!

Daga haka ta saka hannayenta duka biyu ta wani tura shi da ƙarfi tana girgiza kanta tana kuka ta ce.

"Ni ka ƙyale ni! Ƙarya ka ke yi ni na san ba ka so na! Ka daina min wasa da zuciyata sannan ka daina min wasa da hankali....."

"Maryam please..."

Sake matsawa baya ta yi tana mai ɗaga masa hannu cikin ɗaga murya ta ce.

"Babu wata kalma da za ka iya amfani da ita domin ka yaudare ni. Na daina yarda da kai, ba na sonka a kusa dani. I don't want be with you anymore..."

Muryarsa na wata irin rawa ya ce.

"Maryam dan Allah!! Dan Allah ki saurare ni...wallahy tallahy ina son ki..."

Cike da taratsi ta ce.

"Ba za'a saurare kan ba! Kuma ni ba na son ka! Kai ɗin mayaudari ne kuma maƙaryaci! You are just pretending kana wani kamar ka damu da ni! To ba za'a saurare kan ba kuma ni wallahy sai ka bani takandan Saki na domin ba zan zauna da kai ba. Idan kuma ka ce a'a zan faɗawa su Yaa Dina da su Yayyuna domin su karɓa min da kansu. Kuma kafi kowa sanin cewa ni ɗin ƙanwan Maza ce,...kada ka bari wannan labarin ya kai gare su musamman Yaa Mukarram..."

Wani irin super ya yi wannan karon ya saka ƙarfinsa cikin tsananin ruɗewa ya wani rungumeta gam tamkar wani zararre yana faɗin.

"Please don't do that to me! I promise not to do it again...please forgive me..ba wai bana son ki ba ne...I'm just afraid of so many things Saboda bana so na cutar da ke a karo na biyu...."

Jin ta kasa ƙwacewa daga irin riƙon da ya yi mata yasa ta sake fashe masa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ta katse shi da faɗin.

" You are lying! Duk cewa da kake za ka tsaya dani ba za ka taɓa bari na yi kuka ba duk wannan Ƙarya ne domin na yi kuka sau ba adadi and you didn't care.."

"Ki yarda dani please! Don Allah ba don ni ba ki saurare ni. Ki tuna ni mijinki ne kuma ɗaga murya da kike a kaina haramun ne. Na sani na yi miki laifi amma ina roƙon ki don Allah ki sake bani wani daman...na yi alƙawarin gyara komai ki yarda ni. Kada ki fallasa mana sirrinmu na roƙe ki ki bari mu gyara wannan a tsakaninmu. Idan har na sake maimaita miki wani kuskuren na yarda ki ɗauki duk wani matakin da ya dace.."

Tana jin hakan sai ta yi laƙwas tamkar ruwa sun cinyeta tana mai jinjina zancen nasa a ranta. Ji take kaman ta sake yarda da shi ta bashi dama kaman yanda ya roƙi alfarma amma kuma wani ɓarin na zuciyarta yana gargaɗinta akan kada ta yarda da shi domin babu wata gaskiya a zancensa sai son zuciya.

Shi kuwa, Mamaki, tsoro da kuma wani irin al'ajabin ta ne suka kama shi. Wani irin bugawa zuciyar shi ta shiga yi tamkar za ta fasa ƙirjin shi da ta fito tsabar yanda ta gigita tunaninshi ta birki ce lokaci ɗaya tamkar wacce ta sha ƙwaya. Faɗi yake a ransa cewa Anya kuwa wannan maryam ce? Maryam matarsa mai haƙuri wacce ta gama tarban sa a yanzu kaman bai yi mata wani laifi ba? Maryam ɗinda take shanye komai wacce ko fushi ta yi daga zaran ya rarrasheta za ta saurare shi ita ce take iƙirarin neman saki? Wait...to idan ma ta kai zancen nan gaban Familynta ya ce musu me? Gaskiya bai shiryawa wannan ba. Tsoro ne da kuma fargaban abunda zai faru ne yasa yake baya-baya amma shi ya san cewa yana son ta. Yana matuƙar son ta musamman ranar farko da ya ganta gidan Dina tana zubo da ruwan hawaye. A lokacin ya ji tsananin ɓacin rai da takaicin hawayen da ya gani a idanuwanta. Ya ji yana yi mata wata irin ƙauna a ranar Rabi'a ta shiga aibata ta a gaban shi. Ranar da aka zarga igiyoyi uku a tsakanin su a daren ranar ya ƙara tabbatar cewa yana son ta. Yana kauce mata ne domin a duk lokacin da suka kasance a tare yi yake yana rasa nutsuwar sa. Baya so ya yi wani kuskuren a karo na biyu, hakan yasa yake avoiding ɗinta...

"Ni bacci nake ji ka ƙyale ni.."

Ta ambata tare da ƙoƙarin ƙwacewa a karo na biyu.

Bai yi ƙoƙarin hana ta ba a wannan karon. Hakan yasa ya janye hannayensa daga jikinta yana mai ƙure ta da ido har ta fice daga ɗakin.

Runtse idanunsa ya yi gam tare da faɗawa jikin gini yana mai jin yanda duniyar ke yin sama ƙasa da shi. Ya zai yi kenan? Miye ya kamata ya yi? Waɗan nan su ne tambayoyinda suka sarƙafe tunaninsa da zuciyarsa domin abubuwa yake gani masu yawa a gaban sa.

A haka dai ya ɗauki dogon lokaci a tsaye ba tare da ya samu wata makama ba wanda hakan yasa ya taka a hankali ya matsa inda ta kwanta wanda yana hango yanda ta ƙudundune duk da cewa yasan cewa ba bacci take yi ba.

So yake ya zo kusa da ita, so yake ya rarrashe ta ya ba ta haƙuri amma kuma tsoro yake kada ta sake yi mishi irin borin da ta yi mishi ɗazu.

Hakan yasa ya koma kan Sofa ya zauna yana ta nazarin rayuwa wanda har lokacin sallahn asuba ya yi bai samu ya runtsa ko na second ɗaya ba.

Itama kamar yanda bai samu bacci ba haka ta kwana ranta na mata wani irin zafi da takaicin halin da ta kasance a ciki sanadiyyar wannan ƙaddararren auren da ya haɗa ta da shi. A yanzu ko kallon inda yake bata so ta yi hakan yasa ta ƙi ta buɗe idonta tsawon lokaci ballantana tasan Allah ya yi ruwan shi a wurin.

Tana jin ya fita ta miƙe tana mai murza idanunta da suka gama yi mata nauyi tsaban kukan da tasha ta shige toilet ta yi duk wata buƙatar ta sannan ta yi wanka sanadiyyan yanda take jin Jikinta ba daɗi ta yi alwala ta fito ta shimfiɗa sallaya ta yi sallah a natse sannan ta ɗauko Alƙur'ani ta buɗe ta fara karantawa.

Iya ka in ta yi shafi ɗaya sai ga shi ya shigo ɗakin ɗauke da sallama a bakinsa mai cike da nutsuwa tamkar ba shi ba ya zauna a bakin Gadon ya kalle ta ya ce.

"Good morning..."

Amsa masa ta yi da kalmar ina kwana ba tare da ta ɗago ma ta kalle shi ba.

Cikin rashin jindaɗin yanayin da ta nuna masa ya sake kallonta yace.

"Ki shirya za mu je Abuja yanzu.."

Sai yanzu ta ɗago ta kalle shi sau ɗaya ta kawar da idonta jin abinda ya ce.

"Allah ya kai mu."

Ta amsa tana mai ci gaba da karatunta a zuciya.

Ya jima a zaune amma tamkar takardar tsiren da ta gama amfani haka ta watsar da shi tamkar bata san da akwai wani Maheer a wurin ba. Ganin hakan yasa jiki a saɓule ya miƙe yana kallonta ya ce.

" Zan je Base na yi reporting, zuwa 10am zan dawo kafin Sannan kin shirya sai mu tafi."

"Allah ya kai mu."

Ya so jin kalmomin nan na ta masu daɗa da sanya shi alfahari a duk lokacin da ta ce mishi Allah ya tsare gabanka da bayanka. But yau kuma ko kallon arziki bai samu ba ballantana ya samu wannan kyakkyawar addu'ar daga bakin ta.

Yana fita taci gaba da karatunta wanda sai da ta yi kusan shafuka biyar sannan ta ajiye ta yi azkhar ɗinta sannan ta miƙe ta koma kan gado ta kwanta wanda bata farka ba sai misalin ƙarfe tara da wani abu.

Kitchen ta shiga ta sulala indomie ta tsaya a nan ta cinye sannan ta fito. Tana shigo parlourn suka haɗa ido da shi wanda yana zaune akan kujera yana zaman jiranta domin ya ji motsinta hakan yasa ya zauna zaman jiran breakfast.

Sai da ga mamakinsa kallo ɗaya ta yi masa ta kawar da kai tamkar mai ciwon ba ki a daƙile ta ce.

"Welcome..."

Jikinsa ne ya yi sanyi ganin yanda ta wuce bata ma jira ta ji ya amsa ba ko a'a.

Yana nan tunanin ta ya ishe shi domin ba ƙaramin shayar da shi mamaki ta yi ba daga jiya zuwa yau.

Yi yake yana ƙara duba agogo time to time kasancewar lokacin da aka bashi daga wurin aikin nasa ɗan taƙaitacce ne hakan yasa ya ga ta jima bata fito ba.

Ita kuma da gangan ta yi zamanta tana ta shiririta wanda bata fito ba sai Misalin sha biyu na rana sanye cikin riga da wandon da suke matuƙar burgeshi a duk lokacin da ya ganta cikin su.

Jiki sanyaye ya miƙe ya shiga ɗakinsa ya fito sannan suka fito tamkar wasu baƙin juna suka kama hanya.

Har suka Abujan babu wanda ya yi yawa wani magana musamman ita da take ta wani kakkauda kai tana yin kaman wacce aka yi wa tilas.

Suna sauka ya tafi ya ɗauko motar sa da yasa Anasi ya kawo masa tun kafin su iso sai ya janyo ta ya kawo ta shiga suka kama hanya.

Ɗagowa ta yi ta kalle shi lokacin da idon ta ya yi tozali da gate ɗin Al-mufidah Specialist hospital.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull