Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 41

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 41

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 41: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 41. Shi dai bai ce mata komai ba har suka shiga suka yi parking suka…

3,371 words

Shi dai bai ce mata komai ba har suka shiga suka yi parking suka fito wanda sai a lokacin ne ya kalle ta calmly ya ce.

"Maternity unit..."

Zaro ido ta yi lokaci ɗaya bakinta na rawa ta ce.

"Yaa Na'ima ce a nan?"

Ta na rufe bakinta suka haɗa ido da Yaa Amina wacce itama Isowanta kenan domin sai da ta tsaya ta gama shiryawa.

Da gudu taje tana wani irin murmushin farin ciki cike da nuna shagwaɓa ta ce.

"Yaa Amina wato haka za ku yi min ku shammace ni ko?"

Dariya ta yi tana faɗin.

"Wallhy Anaam ni ma ban san an yi ba because na kira ɗazu nake tambayan Ammie cewa an sanar miki kuwa, shi ne ta ce wai Na'ima ta roƙi alfarma cewa don Allah kada a sanar miki a bari sai kin iso za ki fi jindaɗi."

Tana wani irin murmushi ta ce.

"Miye aka samu to?"

"Sai kin shiga ki gani..."

Daga haka Yaa Amina ta wani washe baki tare da rausayar da kai ta ce.

"A ahhh! Amarya 'ƴar shagali. Hajiya Anaam mutanen Lagos..."

Dariya ta yi ta ce.

"Kai Yaa Amina dan Allah..."

Daga haka ta shige da gudu bata ko tsaya yi wa little maryam magana ba. Ballantana ta tambayeta sauran yara.

Sai yanzu Maheer ya matso a hankali jiki sanyaye na banza da shi ɗinda Anaam ta yi ya ce.

"Barka da wuni Aunty..."

Cikin sakin fuska ta ce.

"Yauwa Maheer. Barka da yau. Ya aiki ya kuma haƙuri?"

"Lafiya lau Alhamdulillah! Ya su Farouk da su Fatima?"

"Alhamdulillah! Duk lafiya ƙalau suke..."

"To masha Allah, ni zan koma..."

"Aa, miyasa za ka koma? Ka shigo ciki Kaga Baby mana."

"eh, zan shigo sai idan na dawo an jima tukun in sha Allahu zan shiga."

"To Allah ya yarda, Allah ya tsare."

"Amin Aunty, Nagode."

Daga haka ya wuce ya shiga motar wacce ya jima zaune yana tunani sannan daga ƙarshe ya ja ya wuce gida.

So yake idan taga Babyn su juya su koma Lagos ɗin anjima domin ya baro aikin da dole sai ya koma kafin gobe. And time ɗinda aka ɗibar masa shi ma iyakacin yau aka basa saboda haka dole su juya su koma yau idan yaso daren sunan sai ya dawo da ita.

Sai dai kuma baya tunanin cewa za ta amince su koma and shi kuma ba zai iya barin ta ba a wannan karon. Ku matse da wannan ba yawa sosai har zuwa gobe. *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 49*

Tana shiga ɗakin ta wani rungume Ammie dake tsaye gefen Na'ima tana taimaka mata wurin breastfeeding Babyn.

Da sauri Ammien ta tare ta gefe ɗaya tana faɗin.

"Ah ah! Ki yi a hankali Anaam kada ki faɗowa yaron na ki..."

Marairaicewa ta yi tare da langaɓar da kanta gefe tace.

"Eyyah Ammie haka aka yi wa Autar Abbah ko?"

Dariya sukayi sannan Na'ima ta ce.

"Kuma wallahy koda Abbah ya kira kin nan jiya misalin 8pm duk muna asibitin nan. Yaa Mukkaram ne yace kar a sanar miki a bari sai an haihu domin kina iya ki ɗaga hankalin ki, ni kuma sai na ce kada a sanar miki a bari kawai sai idan kin zo ki gani."

Juya ido ta yi tana wani hararenta ta ce.

" To ai ya miki kyau Yaa Na'ima kin kyauta. Ni daman nasan yanzu kin daina so na.."

Ita dai Na'ima cikin yanayinta na masu haihuwa tana jin sai a hankali ta yi murmushi ta ce.

" Sowie sweetheart, kema kin san har abada ba zan daina son ki ba. Sannu da zuwa. "

Gaisawa suka yi sannan ta karɓi babyn ta zauna tana ta santi suna ta farin ciki tana faɗin tasan irin zallar farin cikin da Haisam yake ciki a yanzu.

Suna nan suna ta fira sai ga Yayar Haisam ta shigo wato Barrister Hajara ita da yaranta su uku. Ɗakin ta bar musu har da Yaa Amina bayan sun gama yiwa juna barka ta wuce Office ɗin Yaa Mukarram ta shiga a hankali tana dariya.

Ajiye Wayar hannunsa ya yi bayan sun haɗa ido cike da farin cikin ganinta ya miƙe tare da ware hannayensa ta shige tana dariya.

"Amarya yaushe a gari?"

Ɗago kanta ta yi tana dariya ta ce.

"Kai Yaa Mukarram wane irin amarya..."

"Amarya mana. Ai ke amarya ce, ga ki kuma naga kin yi kyau abin ki masha Allah,.."

"Uhm! Yaa Mukkaram ni dai bana son tsokana. Ina wuni ya aiki?"

"Lafiya ƙalau ya kike? Ina mai gidan?"

Shiru ta ɗan yi tana tunani domin ita kam sam ta ma manta da cewa wai ta baro wani Maheer a waje amma daga ƙarshe sai ta yi murmushi ta ce.

"Yana waje..."

Dariya ya yi ya ce.

"Auta manyan duniya, shi ne za ki zo da mutum ki bar shi a waje? Ko ya shigo yaga babyn ne?"

Girgixa kai ta yi ta ce.

"A'a..."

"Please ki je ki shigar da shi ya ga babyn sannan ki shigo da shi nan, kina ta abu kaman wata marar wayau."

Da to kawai ta amsa ta juya ta fice ta sake komawa ɗakin da Na'ima take tana faɗi a ranta cewa indai sai ta shigo da shi saidai har abada kada ya shigo, sanda yake zuwa yawon sa ita ce take kai shi ko shi ne yake kai kansa. Aikin banza kawai. Hakan yasa ta yi banza da shi tare da ci gaba da sha'anin gabanta.

********

Maimuna kuwa, gabaɗaya duniyar ta juye da ita a lokaci ɗaya. Wannan gatan, wannan soyayyan gabaɗaya ta manta daɗinsu domin dai Alhaji Gimba ya sauya mata gabaɗaya.

Haka ta dawo gidan yanzu ba ta da wata power kaman ba ita ce a baya take ta wulakanci ba.

Yanzu ma zaune suke ita da Aunty Halira wacce ita ce ta kira ta da kanta ta zo har gidan na ta akan ta koka mata irin halin baƙin cikin da take ciki musamman rikicin da suka yi jiya har ya kai ga yi mata saki ɗaya wanda daƙyar Allah ya taimake ma yau yace ya mayar da ita da safe bayan kwana roƙon shi da suka yi ita da Hajiya Salamatu.

Wani kallon Aunty Halirar ta yi mata ta ce.

"Wai wannan wane irin iskanci ne Maimuna? Ta ya za ki kirani in zo kuma ki zauna ki tasani a gaba kina mini Kuka banza kuma ke ba ƙaramar yarinya ba. Mts! Haba!"

Girgiza kai Maimunan ta yi cike da baƙin ciki ta ce.

"Aunty Dole na yi domin ina cikin tsananin baƙin ciki. Yanzu gabaɗaya na dawo banza wofi a wurin Alhaji sai ka ce ba amarya ba."

Taɓe baki ta yi ta ce.

"Uhm! na san daman za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Ai tun farko na faɗa miki cewa zama a irin wannan gidan haka nan babu wani shiri wallahy ba zai yiyu a gare ki ba. Gabaɗaya kwanakin baya auren ko wata nawa ya yi, amma haka ya saka ƙafa ita matar shi da ɗan shi suka yi tafiyar su suka barki kina gadin gida, ƙarshe kuma da kika tafi wulaƙanci ne ya biyo ba... "

" To ai aunty wallahy yanzu abun ya fi yawa ma fiye da baya, ga shegen faɗa idan ya fara tamkar wani uba da ɗansa, zagi ta uwa ta uba, ga bala'in rowa Aunty Halira ga ƙazanta..."

" To ai shi ne nace miki matuƙar waccan matar tana gidan nan biyar bokaye da 'yan tsibbu ba zai taɓa bari ki gane kai nai ba..."

Saurin girgiza kanta ta yi ta ce.

" A'a Aunty Halira...wallahy tallahy Aunty Salamatu ba ta da wani laifi domin haƙurin da take da shi da iya ɗaukar rigimarsa ni ban iyawa. Wallahy tana ƙoƙari kuma tana matuƙar haƙuri da shi. Na aure shi don na huta amma ban ƙarar da komai ba sai baƙin ciki, jiya ma daga maganar arziki na ce ya bani jari in fara saro kaya daga China tunda wurin zuwansa ne shikenan ya hau zagina ta uwa ta uba yana ta cimin mutunci. Ƙarshe da nuna ɓacin rai na fa Aunty Halira sakina ya yi... "

Wani irin dafe ƙirji Aunty Halira ta yi tare da zaro ido waje ta ce.

" Saki Maimuna? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Amma dai wannan Salamatu anyi tsohuwar munafuka..."

"Aunty na faɗa miki fa ba tada laifi wani, wallahy har da ita ta tayani bashi haƙuri wanda sai ɗazu da safe ne na samu ya mayar dani.."

Cike da tsantsar ɓacin rai Aunty Halira ta wani kalle ta ta ce.

"Shashashar banza marar hankali. Ita kishiyar ce kika yarda ta ji sirrinki har ki bari wai ta ji cewa an sake ki? Lallai Maimuna sai yau na tabbatar cewa baki da hankali. Wayyo Allah na tuba ta ina za'a haɗa hankalinta da wayonta da naki? Macen da a haife ma ta haife ki amma shi ne kika zauna kina biye wa makircinta? To wallahy tallahy kin ji na rantse miki da Allah sai kin tashi mun tafi gidan Malam don ubanki. Daga tambayar jari zaa ce saki ya shiga ai kowa ya ji wannan yasan cewa makirci ne. Wannan mutumin mai uban kuɗi za'a ce wai yana rowa?... "

" Uhm! Aunty Halira kenan! Wallahy tallahy mutumin nan ya wuce inda kike tunani, kuɗin sa ba sa ciyuwa... "

" Ƙarya ne! Ni na ce miki Ƙarya ne makirci ne kawai, saboda haka ta shi ki ɗauko mayafinki ki shirya mu tafi yau in sha Allahu sai mun samo maganin wannan matsala. Kuma yau wannan matar sai ta gane cewa ba ta da wayau. Kuma nasan halin ki Maimuna...wallahy ko da wasa kada ki taɓa yarda ki ce za ki faɗawa su Inna wata magana dangane da wannan lamari. Kibar komai a hannuna zan miki maganin su."

Jinjina kai ta yi a wannan karon alamar ta yarda sannan daga ƙarshe ta miƙe yi jiki sanyaye ta shiga ciki ta shirya ta fito suka fito, a main parlour suka tarar da Alhajin yana karin safe wanda tun bayan da suka yi rikici daren jiya ya koma ɓangaren Hajiya Salamatu ya yi kwanciyar sa.

Aunty Halira tamkar za ta kifa haka ta shiga gaishe da Alhaji Gimba wanda ko kallon arziki ba ta samu a wurinsa ba a matsayinta na babbar yayar Maimuna amma haka ya wani amsa a daƙile a ransa yana jira ta yi mai wata magana dangane da rigimarsu ta jiya ya ci mata mutunci. Sai ga shi bayan sun gama gaisawa ta sa kai ta yi gaba.

Kallon shi Maimuna ta yi a ɗan darare ta ce.

"Alhaji Zamu je wurin duba wani ƙanin Babanmu ba shi da lafiya..."

Taɓe baki ya yi ba tare da ya kalle ta ba ta ce.

"Koma dai wurin nemomin asiri za ku tafi wallahy ni nafi ƙarfin ku domin baku iya komai dani. An zo an aure ni domin a ci banza ko? To wallahy ƙwandala ta ba zan iya bayar ba domin a yi sharholiya, idan kuma Macce ta gaji hanya a miƙe take kuma ƙofa a buɗe take. "

Wucewa ta yi gaba tana mai jin wasu irin hawayen baƙin ciki suna wanke mata fuska. Irin cin mutunci da tozarcin da ya yi mata a daren jiya ba ta fata ta sake jin irin sa, hakan yasa ta yi gaba kurum ta ƙyale shi.

Bayan ya kambala cin abincin ne ya dawo parlour ya zauna tare da ɗaukan Remote control ya kamo News Yana kallo.

Yana na nan a zaune sai ga Faris ya fito cikin shirinsa na fita Office ya zauna a hankali ya gaishe da shi sannan Alhajin Gimban yana kallonsa ya ce.

"Ba za ka yi breakfast ba ne?"

Girgixa kai ya yi ya ce.

"No, am good for now, Idan 12pm Idan na isa office zan ci wani abun.."

Ya ƙarashe maganar yana mai ƙara gyara zamansa sannan kai tsaye ya ci gaba da cewa.

"Ahm..Daddy daman I have something important to discuss with you. Matar aure ce na samu wacce last few months ago nace maka Idan mun kai ƙarshe mun yanke zancen aure zan sanar maka domin a tura a nemomin auren..."

Cikin wani irin farin ciki ya tare numfashinsa da faɗin.

"Alhamdulillah masha Allah. Gaskiya wannan labarin ya yi matuƙar faranta min ba kaɗan ba. Daman rashin auren nan naka ya dame ni Faris, don kawai bani da yanda zan yi ne. Amma yanzu tunda Allah ya kawo ƙarshen abun magana ta ƙare. Wace yarinya ce wannan? Su waye iyayenta. "

"Daddy ba wata ba ce, Rabi'a ce ta gidan Alhaji Salisu na Alhaji Mas'ood Galadima..."

A hankaɗe ya bi shi da wani irin kallon wanda duk irin tsaurin idonsa sai da ya ji hantar cikin sa ta kaɗa.

"Wane Mas'ood ɗin?"

"Daddy wane Mas'ood ɗin wanda ya wuce abokin ka wanda kuka taso tun yaranta..."

Wata irin zabura ya yi ya miƙe tsaye yana mai jin maganar ɗansa tamkar a mafarki ya shiga jinjina kansa da mamaki ya ce.

"Mas'ood Faris? 'ƴar gidan Salisu yayan Mas'ood jinin Mas'ood ka zauna a gabana kake faɗamin cewa za ka aure ta? Jinin manyan maƙiyana, abokan gaba na, waɗanda ba sa son ci gabana za ka ce kana so Faris?..."

Wata irin super ya yi tamkar wani mahaukaci ya faɗa kan Faris ɗin dake zaune kan kujera ya shiga kai mishi naushi. Hakan ya yi daidai da fitowan Hajiya Salamatu wanda yasa a gigice ta yi kansa cikin tsananin tashin hankali ta shiga kicaniyar janye shi tana faɗin.

"Na shiga uku na lalace ni Salamatu ni yau mi zan gani haka!!"

Dukansa yake ta ko'ina yana kai mishi naushi cikin tsananin zafin rai yana ta tsine-tsine tamkar wani mahaukaci sabon kamu.

"Alhaji Dan Allah Dan girman Allah ka yi haƙuri ka sake shi, kada fa ka je ka ji mishi ciwo fa...Alhaji ka daina dukansa na roƙe ka san Allah ka daina...miye ya aikata maka da zafi haka da har ya cancanci wannan hukuncin haka?"

Tana rufe bakinta ya taso ya juyo kanta ya kifa mata wani irin mari wanda sai da ya saka ta yin baya-baya tamkar za ta kifa sannan ya ci gaba da zage-zage yana faɗin.

" So kuke kuga bayana da ke da ɗan ki kuma wallahy Allah ba zai bari ba domin na riga na yi muku nisa. Ni za ku kawowa iskanci? Ni za ku rainawa wayau? Ku rasa waye za ku haɗa baki da sunan wacce zai aura sai 'ƴar maƙiyana?..."

Miƙewa Faris ɗin ya yi a tsananin zuciye wanda daga kallon sa za ka fahimci cewa baya ma cikin hayyacinsa tsabar ɓacin rai.

Allah sarki uwa! Duk da irin marin da ta ji ya shige ta, ganin yanda ya miƙe yasa ta sha gaban sa a ruɗe tana faɗin.

" Faris ina za ka je? Wai miye ka aikata masa haka?"

Ta gefen ta ya zagaya ya fice tamkar zai tashi sama kai tsaye yaja mota ya bar gidan.

Sake dawo da kallonta ta yi gun Alhajin ta ce.

"Wai miye abunda yake faruwa ne? Ni kun bar ni a duhu, miye kuke magana a kai?"

Wata hararar ya maka mata sannan ya ce.

"Munafuka kawai! Duk abunda yake ai da sanin ki yake yinsa. Rabi'ar gidan Salisu Galadima ai da sanin ki da izininki yaje neman auren ta kuma wallahy tallahy na rantse da Allah ba zai aure ta ba...ke ko wata ɗiyar da ta taɓa alaƙa da gidan wallahy tallahy ba zai aure ta ba ballantana ɗiyar Salisu. Ɗiyar Ridwan ma ba zai aura ba ballantana jinin Galadima....."

Sake girgiza kai ya yi cike da wani irin raɗadin baƙin ciki yace.

"Wato kun raina ni Salamatu ko! Kun yi matuƙar raina matsayi na, ni da gidana amma kun mayar dani banza. Kun nuna ni ban isa da gidana ba, da ace kun san zafi na kun ɗauke ni da daraja ba za ku taɓa fara tunanin mafarkin haɗa jinina da jinin maƙiyana ba..."

Tijara ce mai zaman kanta ya shiga surfa mata wanda sai da ya saka Hajiya Salamatu zubo da ruwan hawayen baƙin ciki. zagi da cin mutunci sai abinda ya manta sannan daga ƙarshe cike da rashin arziki ya ce.

"Kuma tun da har cin amana ta da son ganin bayana shi ne abinda kuke so to har abada ba za ku taɓa yin nasara ba..."

Girgiza kanta ta ci gaba da yi tare da kama hanya ta shige shashenta ta bar shi nan yana ci gaba da cin mutuncin.

Wayar ta ta ɗauko ta shiga kiran Faris ɗin amma kuma tana ta ringing ya ƙi ya ɗaga wanda daga ƙarshe dole ta haƙura tare da zaunawa a bakin Gado ta sake fashewa da kuka. A ranta faɗin take yaro ne dai ka haifeshi ba ka haifi halin sa ba. Idan ba shi ba taya Faris zai ɗauko zancen auren Rabi'a wai kace bai san abinda ake ciki ba? Sai ka ce bai san takun saƙar da ke tsakaninsu da familyn Galadima ba? Shi yanzu ko a makarfi akace masa ya nemi Rabi'a ai bai kamata ya aikata ba. Kai da suka rufe a cell har ka wuni ka kwana akan laifin da ba su da hujja amma shi ne don rashin zuciya za ka koma daga baya ka ce kana son 'ƴar su? Ga shi kuma da yake shiryayye mutumin wofi ko ita ɗin bai taɓa sanar mata ba, yanzu duk abinda za ta ce Alhaji ba zai taɓa yarda da cewa ba ta san da wannan zancen ba. Kuma ko ita ta goya baya akan cewa ba zai aure ta ba, idan kuma mutuwa zai yi to ya mutu tana jira ta gani.

*******

Suna nan a asibitin ba jimawa aka basu takandan sallama hakan yasa suka ɗunguma suka koma gida.

Kafin ƙarfe shida na yamma su Aunty Aysha da yaransu duk sun cika gidan ana ta farin ciki wanda Anaam ita ce zaune a ƙugun mai jego tamkar ita ce mai haihuwar.

Shigowa Nene ta yi ɗakin da suke ta fira ta kalli Na'ima ta ce.

"Na'ima ki taso an kwashe ruwan zafin ki yi wankan..."

Dariya Anaam ta fara yi mata tana faɗin.

"Miƙo min Babyna ki wuce wurin wankan ki Hajiya..."

Wani kallon ta yi mata tana mai mere baki ta ce.

"Ai kema dai ba jimawa turn ɗin ki zai zo saboda haka ki daina yi min dariya..."

Cikin jin wani iri a ranta tana wani murmushi ta ce.

"To ai ni bana haihuwar ballantana ki zauna jiran wannan lokac..."

A hankali ta haɗiye sauran magananta ganin kiran Maheer da ya shigo yanzu a wayanta wanda ta zuba ido tana kallo har sai da ta gama ringing Sannan ta mayar ta ajiye tare da ɗago babyn da yake hannun ta tana kallo tana ta murmushi.

Zamanta a wurin ya yi mata miss calls ɗinda suka kai talatin wanda ko sau ɗaya bata ji nadamar rashin ɗaga kiran nasa ba domin bata so ma ta yi magana da shi.

Tana nan a zaune har Na'ima ta fito wanka suka ci gaba da firarrakinsu sannan daga baya sai ga Yaa Mubarak ya shigo ɗakin.

Wani irin tsalle ne ta yi ta ɗane dokin wuyansa wanda saura kiris su zube ƙasa sannan ya yi nasarar kauce mata yana dariya ya kalle ta sai kuma ya kalli Na'ima yana mai riƙe baki ya ce.

"Toh! Ashe Na'ima idan mutum ya yi aure ya tafi Lagos zarewa yake shi ne ba ki faɗamin ba?"

Dariya suka fashe da ita sannan Na'ima ta ce.

"Ai kam dai sai dai muyi tayata da addu'a Yaa Mubarak...sannu da zuwa."

Jinjina kai ya yi yana dariya ya ce.

"Yauwa Na'ima. Barka, congratulations, Allah ya raya ya baki lafiya.."

"Amin Yaa Mubarak, na gode."

Kallon Inda Anaam ɗin take ya yi sannan ya ce.

"Mijin ki yana waje tun ɗazu yana jiranki. Da alama kin baro wayan wani ɗaki hakan yasa yake ta kira baki ɗaga ba."

Tana jin haka ta miƙe a hankali ta fito ta zo har inda yake zaune a motar sa ta tsaya a bakin ƙofan motan ba tare da ta yi magana ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull