Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 51
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 51: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 51. Jikinsa ne ya yi sanyi ya tsaya tsawon lokaci yana kallonta. Duk…
2,718 words
Jikinsa ne ya yi sanyi ya tsaya tsawon lokaci yana kallonta. Duk wannan gwagwarmaya da ya ɗauki tsawon lokaci yana yinta duk yana yi ne saboda ita. Bai taɓa tunanin cewa Rabi'a za ta iya yi masa irin wannan wulaƙancin ba.
Jin ta yi shiru tana ta ciccika yasa ya sake kallonta ya ce.
"Rabi'a I never expect this from you...duk wannan kina yinsa ne saboda kin samu na aure ki. Kada ki manta ke ce wacce kika fara cewa kina so na. Da gaske kika ce kina so na kuma kin shirya rayuwa dani a kowane irin yanayi. Ke ce kina so na saboda na baki tausayi akan guduna da Anaam ta yi da kuma wulaƙancin da en uwanta suka min. Ashe kenan duk wannan Ƙarya ne?"
Wani irin kallon ta yi mishi cike da mamaki ta ce.
"To da nace ina sonka ba gashi na aure kan ba! Da ni da kai yanzu waye ya ci amanar wani?"
"Saboda na kawo ki wannan gidan kike kiran hakan da cin amana? Abu ɗaya ne zuwa biyu yasa na dage da auren ki, na ɗaya shi ne da kika ajiye girman ajinki a matsayinki na mace kika ce kina so na, na biyu domin na nuna wa Mukarram cewa bai isa ya hana ni auren ɗaya daga cikin ku ba, na jure na shanye komai saboda ke amma abinda za ki saka min da shi kenan..."
"Wallahy komai za ka ce ni bai dame ni ba, kuma sai ka sake ni na faɗa maka..."
"Waye zai sake kin?"
"Kai mana!"
Ta faɗa a tsawace tamkar wata mai shafar aljanu.
"Wallahy ka ji na rantse maka da Allah sai ka sake ni. Idan kuma baka sake ni ba zan je wurin Abbah ya karɓa min da hannunsa. Ai yace kada na ɗauki wulakanci ko cin zarafi, daga zaran naga wani abu makamancin wannan na je na sanar masa."
Ɗakin ya barta ya je ya buɗe single room ɗin nan da ke waje ya shige ciki ya kwanta shiru yana nazarin rayuwa.
Ganin ya fita yasa ta faɗa kan kujera ta sake fashewa da kuka tana ta ƙara tsine masa a ranta shi da iyayen sa.
Yanda taga rana haka taga dare. Ta saƙa ta warware ta saƙa ta warware abinda ta kwana yi kenan har gari ya waye.
A bakin famfon tsakar gida taje ta yi alwala ta zo ta gabatar da sallar asuba, tana nan a zaune tana duba lokaci har shida da rabi na safe ta buga. Hakan yasa ta ɗauki gyalenta da jakanta ta fito da nufin tafiya.
A bakin Generator ta tarar da shi yana ƙoƙarin kashewa tunda gari ya waye. Cike da mamaki ya kalle ta ya ce.
"Ina za ki je haka?"
Wani kallon sama da ƙasa ta yi mai sannan ta ce.
"Gidan iyaye na zan tafi, daga nan sai su nemo ka su karɓar min takardar sakina."
Gefe ya koma ya bata hanya. Ledar da ya yasar tun a daren jiya ta kalla ta taɓe baki sannan ta ja ƙofa ta buɗe ta tafiyar ta.
Ita ba ta ma san a wace unguwa take ba sai da ta tare mai mashin ta tambayeshi sannan ya faɗa mata cewa a unguwan Shado take.
Damɓa direct ta ce ya kaita wanda bata dire ko'ina ba sai ƙofan gidan Alhaji Mas'ood. Mai gadi na ganinta ya buɗe mata ƙofa cike da mamaki ta shige.
Na'ima ita ce wacce ta fara ganinta kasancewar Khalifa da ya farka tunda sassafe yana ta yi mata rigima.
Cike da tsantsar mamaki ta kalle ta ta ce.
"Rabi'a?!"
Wasu sabbin hawayen da ta ji sun silalo mata ne ta share sannnan ta ce.
"Da Abbah nake son Magana."
Jinjina kai ta yi tare da ɗaga waya ta kira Ammie ta sanar mata sai ga shi nan take ta sauko a ruɗe tana kallon Rabi'a ta ce.
"Lafiya Rabi'a?"
"Ammie ni bana son shi, a kira min Abbah ya kira sa yace ya bani takarda ta."
Shiru Ammie ta yi tare da zuba ido tana kallonta na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta ja numfashi tana jinjina kanta ta ce.
"Okay..."
Sama ta haura ba jimawa sai ga Abbahn shi ma ya sauko.
Kuka ta fara ƙasa-ƙasa ta buɗe bakinta ta ce.
"Abbah ina kwana..."
Saurin ɗaga mata hannu ya yi alamar ta yi shiru sannan ya ce.
"Riƙe gaisuwarki Rabi'a, na gode. Miye abinda ya fito dake daga gidan mijinki?"
Yanzu kam cikin ɗaga sauti ta shiga faɗin.
"Abbah ni bana son sa, Faris ya yaudare ni ya ci amana ta. So nake ka karɓa min takarda ta Abbah."
"Akan wane laifi? Yaudara wace iri?"
"Abbah bai faɗamin cewa bashi da komai ba yanzu sai daren jiya yake sanar da ni...."
"Shi ne dalilin da yasa kike son saki?"
"Eh Abbah.."
"Rabi'a..."
"Na'am Abbah"
Ta amsa ba tare da ta ɗago kanta ba.
"So nake ki ɗago ki saka idanunki cikin nawa."
Ɗagowan ta yi ta kalle shin zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi ya ce.
"Kin san halina kuwa Rabi'a? Kin san yanda nake idan raina ya ɓaci? Bani da daɗi ko kaɗan,. Ke da kika yi aure domin neman yardar Allah ina ruwan ki da wani ƙyalƙyalin rayuwa? Komai ɗan a hankali ne, idan kana son mutum babu inda ba za ka iya bin shi ku zauna ba. Saboda haka ki tashi ki kama hanya kaman yanda kika wanko ƙafa kika zo to ki ƙara wanke ta ki koma gidan mijinki. Idan kika ce ba haka ba to sai dai ki nemi wani gidan uban amma ba nan ba ko gidan ɗan uwana. Idan kika ce ba haka ba kije ki nemi wasu dangin uban amma ba mu ba,kuma idan har kika sake na ƙara ganin ki tabbas sai na karya miki ƙafafu. Mutuniyar banza mutuniyar wofi."
Tamkar Kazar da aka tsoma a ruwan zafi haka ta ji ta tsamo-tsamo a cikin wata irin kunya da matsananciyar nadama. How she wish ace duk wannan ɗin mafarki ne? Ina ma ace za ta iya dawo da hannun agogo baya? Da tabbas sai ta canja Faris domin yanzu ta gane cewa su ɗin ba su dace da juna ba.
Abbah bai san yanda take ji ba bai kuma san halin da take ciki ba da tabbas ba zai ce mata ta koma ba. Wannan ɗin wai reaction ɗin Abbah kenan, Abban da yana da wahala ka ji shi yana yi wa wani faɗa. To Idan ta koma ga Baba bata san irin hukuncin da zai yanke mata ba saboda haka dole ta nemi mafita, domin wallahy har abada ba za ta amince da zaman wahala ba.
"Za ki tashi ne ko sai na ɗauki matakin da ya kamata Rabi'a?"
Miƙewa ta yi jiki a saɓule ta fice tana wani irin kuka wanda gabaɗaya Idanunta sun rufe har bata san inda take jefa ƙafa ba.
*******
Ƙarfe huɗu na yamma a birnin Lagos ta buga musu inda ya kama musu ɗaki a babban hotel domin kasancewar wannan zuwan na su na musamman.
Iyaka 30mnt ya shirya ya fita ya barta ya tafi base ɗinsu ya tarar da Hamad a gida.
Jiki a sanyaye ya kalli Hamad ɗin ya ce.
"Hamad ina cikin damuwa. Ina neman mafita, na san cewa Maami ta sanar maka da zancen aure na da Nazli. What should I do?"
Ajiyan zuciya Hamad ya sauke a hankali tare da ajiye Laptop ɗinda ke saman jikinsa ya kalle shi ya ce.
"Tunda ba za ka iya sakin Anaam ba. Ka faɗa mata gaskiya idan tana da ra'ayin ci gaba da zama da kai sai ku ci gaba da zama. Sannan ka fadawa mahaifiyarka gaskiya itama, sannan ka yi wa Nazli bayanin ita ce ta biyu idan tana jin za ta iya zama..."
"Hamad magana ta gaskiya ba zan iya zaman aure da Nazli ba, and again Maami ba za ta yafe min ba Hamad.."
"Fyn..."
Daga haka ya ɗauki laptop ɗinsa ya ci gaba da aikin da yake.
Wani kallon Maheer ɗin ya yi masa sai kuma ya miƙe ya bar gidan kai tsaye yana mai jin haushin Hamad ɗin. Har abada Hamad ba zai taɓa kawo masa mafitar da za ta faranta masa rai ba.
Shiru Hamad ya yi yana tunanin irin wannan masifar da abokin nasa yake ciki. Da Maami ta kira shi ta sanar mai zancen auren Maheer ɗin da Nazli sai da ya ruɗe duk da cewa ba shi ne angon ba. Abubuwa da dama yake hangowa wanda duk inda aka shiga aka fita shima ɗin ba zai tsira ba. Da Maheer yana ɗaukan shawarar shi tabbas da yanxu abubuwa ba su kawo haka ba. Ba shi ne a matsalar ba, amma gabaɗaya baccinsa a yanzu rabi da rabi ne.
Tashi ya yi ya shirya ya cim masa office ɗin ya kama masa suka rarrage abubuwa sannan misalin goma na dare suka fito da nufin rabuwa.
Kallon shi Hamad ya yi ya ce.
"Anaam fa?"
"Hotel.."
Cike da mamaki Hamad ɗin ya ce.
"Miyasa?"
"Ra'ayi mana."
Daga haka ya shiga mota ya wuce, sai da ya tsaya ya yi mata siyayyar favorite ɗinta Sannan ya wuce hotel ɗin.
Koda ya shiga ya tarar da ita har ta yi baccin gajiya, hakan yasa ya ajiye ledojin da ya shigo da su a hankali ya canja kayansa shi ma ya sulale gefen ta ya kwanta wanda ba su farka ba sai asuba.
A nan ɗakin suka yi sallah a tare, bayan sun kambala ta kalle shi muryar nan can ƙasa tace.
"Babe..I'm hungry."
"you sleep early yesterday...I'm sorry, ban samu na dawo da wuri ba."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"Na gaji ne sosai har kai na na ji yana ciwo, but Alhamdulillah, I'm okay now."
Fita ya yi iyaka 20mnt ya dawo mata da fresh breakfast ya ajiye mata a ƙasan carpet Sannan ya janyota jikin shi tare da janyo ledan da ya shigo da ita ya ce.
" I will feed you my self.."
Murmushi ta yi tare da jinjina kanta ta ce.
" Your welcome..."
Wayarta ta janyo ta duba time, ƙarfe shida ne na safe da wasu mintuna. Dariya ta fashe da ita ta ce.
"It sound silly eating this early..."
"And that's why I hate it to sleep with empty stomach..."
Ita ce wacce tace tana jin yunwa amma kuma a tare suka cinye komai wanda suna yi a hankali suna fira mai cike da nishaɗi da farin ciki wanda suka kai kusan ƙarfe goma a zaune su na ta nishaɗin rayuwa.
Sai da ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ya shiga daga baya. Koda ya fito har ta gama shiryawa cikin the best outfit ɗinda Idan ta saka su yake jin ta gama burgeshi a rayuwa.
Matsota ya yi tare da saka hannu ya riƙo waist ɗinta a right side ɗinshi ya rungumota yana mai jin yanda wani abu yake fisgar zuciyarsa ya yi kissing lips ɗinta lightly Sannan ya haɗe goshin su wuri ɗaya suna shaƙar iskar juna na tsawon mintuna sannan ya janye ya yi mata murmushi ya ce.
"You look beautiful Noori..."
Jinjina kanta ta yi tana murmushin itama ta ce.
"Thank you Babe.."
Komawa ta yi ta zauna tana amsa chart ɗin su da Yaa Na'ima wacce tun a daren jiya bata samu yi mata reply ba sai yanxu.
Idonta ne ya sauka a kan shi ta shiga kallon yanda ya tsaya yana ɗaura agogo amma ya yi pausing kaman yana tunanin wani abu. Sosai wannan kakin ya yi masa kyau wanda ya sanya zuciyarta bugawa tana mai jin wata sabuwar soyayyarsa na ƙara huda ta.
" Babe…mi kake tunani haka?"
Ta faɗa a hankali tana mai ƙure sa da kallo.
Ido ya ɗan zubo daga cikin mirror ɗin ya kalleta tare da yin wani forced smile ya ce.
"I’m okay… I'm just thinking about the program."
Tasowa ta yi ta ƙaraso kusa da shi ta daura hannunta a ƙirjinshi sannan ta saƙala ɗayan ta bayan shi suna facing juna tana murmushi ta ce.
"Kai ɗin jarumi ne, I trust you, in sha Allah komai zai tafi daidai.."
"I love you Noori...thank you so much..."
"I love u Babe...muje lokaci yana tafiya."
Ta ambata daga ƙarshe tana mai jan hannunsa zuwa waje.
Motar wurin aikinsu ce ta tsaya mai ɗauke da tambarinsu wanda mutum biyu suka fito da wasu kalar uniform ɗin suka sara masa sannan suka buɗe musu motan suka shiga.
Babban Hall ne wanda manyan baki suka hallara daga can Oman da kuma sauran sassan da suke da reshe a can wanda akwai directors, investors, international partners, da sabbin ma'aikatan da suka horar waɗanda suka kasance jere cikin uniform ɗaya gwanin burgewa da tsari.
A first row ya yi mata masauki wanda ya kasance high table na mutane na musamman sannan ya wuce inda aka tanadar masa tare da manyan ma'aikatansu ya zauna.
Yana zaunawa ya ciro Tab ɗinsa ya shiga duba jadawalin da yasa Hamad ya yi masa 'yan gyare-gyare sannan ya sake turo masa. Sai da ya gama duba aikin sannan ya ɗago da nufin kallon inda Hamad yake domin ya tambayesa cewa bai ga wani correction ba kawai idonsa ya sauka akan Maami, Uncle Abdallah, Uncle Ameed sannan Nazli dake gefen Maami tana riƙe da hannun ta.
Wani irin bugawa zuciyarsa ta yi sai kuma ya ji ta yi wani irin tsalle tamkar zai sume tsabar gigita da tashin hankali. Shima Hamad haɓa na yi masa rawa ya yi saurin miƙewa tsaye ya kalli inda Anaam ke zaune sannan ya sake waigawa ya kalli su Maami dake dumfaro cikin Hall ɗin kai tsaye wanda suna tafe suna magana da junansu suna dariya cike da nishaɗi.
Idan har ƙwaƙwalwarsa ba ƙarya take faɗa masa ba tabbas fitsari ne yake a wando.
ALHAMDULILLAH!!! A nan muka kawo ƙarshen BOOK ONE In sha Allah. Sai ku biyo mu a BOOK TWO da zai fara sauka sartuday 9-May 2026.
Mai karatu Tafiyar DUHUN DARE yanzu muka fara, mun hau tudu yanzu za mu fara gangara.
Littafin Duhun Dare ya ƙunshi abubuwa da dama wanda ba nishaɗi ne kawai ba, akwai abubuwa masu yawa da muka ɗauko kuma in sha Allah zamu warware su ɗaya bayan ɗaya.
Wai bahaushe yace rana Dubu ta ɓarawo rana ɗaya kuma ta mai kaya, ga dai Maheer ga Maami da danginta ga Maryam ga kuma Nazli, idan fa kere na yawo zabo na yawo watarana tabbas za'a haɗu. Ko ya za ta kaya a wannan Hall ɗin? Book 2 ne zai warware mana.
Maheer zai iya fahimtar da Maami kuwa? Ko ya za ta kaya tsakanin su da Maryam da Maami and tsakanin Maryam da Nazli?
Anya Maryam za ta yafe wa Maheer duk gadar zaren da ya ƙulla mata har ya kawo ta zuwa nan?
Aunty Dinaratu, Oga Nameer da suka yarda da Maheer su kuma Ahlin Anaam suka yarda da shi saboda su ya za ta kaya tsakanin su idan suka gano gaskiya?
Mun baro baya da ƙura tsakanin Azaan da Oga Jud, shin da gaske an rabu kenan har abada ko kuma dai akwai wata ranar a gaba?
Alhaji Mas'ood Galadima yaga taskon abota kuma yaga rashin halacci, shin miye gaskiyar abunda yake faruwa da ahlinsa tsawon shekarun nan? Da gaske abokin ka amininka da ka sanyawa riga zai iya dawo wa daga baya ya kwaye maka baya?
Alhaji Gimba rigimamme wanda shi tashin hankali ma kamar a jinin sa yake, ya ya tsakanin sa da ɗansa zai kasance? Dukkan su wannan hukuncin da suka yanke zai haifar musu da ɗa mai ido ko kuwa dai akwai buƙatar gyara?
RABI'A...RABIBIN Umma amarya mai capacity. Ta yi auren kuɗi ta ƙare dare ɗaya a gidan Mijinta da ya tsiyace a ranar ɗaurin auren su. Ga Abbah ya shata mata layi, miye mafita a gare ta?
Mai karatu akwai alot alot da muke buƙatan mu warware a gaba. Ku an tayo kuɗinku domin a ci gaba da wannan tafiyan da ku. Na cika muku alƙawarina na yi muku book one a free nima ku cika min nawa ku sayi book 2 a 500 Naira kacal. Ku biya kuɗi kusha karatu. In sha Allahu ba za ku yi dana sani ba.
500 Naira only. Ku biya ta wannan asusun: 3132703269 First bank Ibrahim Amina Sai ku tura evidence of payment ɗinku ta wannan Layin. 08068974831. OUM-AMEER