Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 50
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 50: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 50. Towel ɗinda ya cire ta ɗauke da nufin kai wa ta yi hanging kawai…
3,367 words
Towel ɗinda ya cire ta ɗauke da nufin kai wa ta yi hanging kawai ta ji ya riƙo hannunta ta faɗo jikin shi ya sake rungumeta sosai kaman ɗaxu da ya iso.
Shiru ta yi tare da kwantar da kai a ƙirjinsa na dogon lokaci wanda daga ƙarshe ta ɗago ta kalli cikin idanuwansa da suka gama rinewa tsabar damuwa hankalinta a tashe ta ce.
"Babe...miye yake damunka?"
Tamkar zai fashe da kuka ya ce.
"Komai ma damuna yake Noori! I'm not okay.."
Ganin ta yi ya kamo hannunta ya riƙe yana mai bin ta da wani irin karyayyen kallo ya ce.
"Please ki yi min alƙawarin cewa komai zai faru ba za ki bar ni ba..."
Ido ta zuba tana kallon sa tare da nazarin irin halin da yake ciki. Definitely he's not okay kaman Yanda ya faɗa. Gabaɗaya baya cikin nutsuwarsa, fuskansa da idanunsa sun nuna damuwa wanda ita kanta a yanzu ta gama fahimtar hakan.
"Noori...."
Lumshe idanun ta tayi ta buɗe a hankali tana kallon shi jin yanda kalmomin sunan suka daki har tsakiyan kanta. kallon shi take kaman yanda yake kallonta softly ya ce.
"Do you love me?"
Jinjina kanta ta yi alamar eh wanda da gaske take ta amsa har cikin zuciyarta cewa tana son shi.
"Ki faɗamin in ji da kunnena Noori ki faɗamin domin zuciyata ta ji cewa kin amsa ke ma kina so na kina ƙauna ta kaman yanda nima nake son ki. Kunnuwana su na so su ji yanda kike ji game dani..."
A hankali ta kai cute lips ɗin nan na ta da ba sa rabo da ƙyalli ta haɗe bakin su wuri ɗaya ta shiga kissing ɗin shi romantically. Gabaɗaya ji tayi dukkan wata jijiya dake jikinta ta amsa tare da gaɓɓan jikinta jin irin kalaman da yake furta mata. She is burning in love a yau domin kalamansa sun shiga kowace gaɓa ta jikinta ba kaɗan ba.
Cikin wata irin zazzafar ƙauna ta shiga sarrafa kanta daga lips ɗinsa zuwa wuyansa kaman yanda yake rikita ta idan ya tashi. Ta sani cewa ita ce wacce ta katange shi da cika sunnar su ta aure domin ganin take kaman ba za ta iya ba. Gani take kaman za ta cutu hakan yasa take jin tsoro kuma take ta ƙoƙarin hana masa Kanta wanda har yau bai taɓa yi mata complain ba ko ya nuna mata cewa ran shi ya ɓaci. Lokaci ɗaya ta shiga unbuttoning ɗin yaloluwar rigarta da ke da wasu maɓallai guda uku a gaba waɗanda da su da babu su duk ɗaya. Tana gama zare buttons ɗin ta sake manna jikinta da na shi tare da kai lips ɗinta ta sake locking bakinsu wuri ɗaya.
Gabaɗaya ta gama rikita shi ta gama ruɗar da shi. Wani irin shock yake ji wanda ke shigar sa tun daga tsakiyan kansa har zuwa tafin ƙafar sa. Wata irin wuta yake ji tana ci ko'ina na jikinsa ta yanda duk yanda ya so ba zai iya hana kan shi ba a yau.
Lokaci ɗaya suka faɗa kan makeken Bed ɗin nasa wanda ya yi mata rumfa yayin da idanunsa suka sauka akan tsayayyun breast ɗinta wanda komai ya zo masa a ba za ta.
Ya kiɗime, ya ruɗe ya gigice gabaɗaya ya fice daga hayyacinsa. Ba wannan ne buƙatansa ba a yanzu. Amma kuma ta riga ta zurma shi, ta riga ta kwance masa notukan da bai isa yace zai ɗaure kansa ba.
Itama ɗin she's just doing it Saboda Kawai ta bashi comfort na irin damuwa da tashin hankalin da ta ganshi a ciki. A yau ta miƙa masa wuya domin ta bashi tabbaci akan cewa ta amsa kalamansa kaman yanda shi ma ya amshe ta da hannu biyu. So take a yau ta mayar da shi namiji kamar sauran mazajen da suka yi aure kaman shi. Ta sani cewa ba za ta iya bashi ɗa ba, amma kuma duniyar nan da kowane namiji yake mafarki da burin kasancewa a duk lokacin da ya ji ransa ya amsa nan take so ta samar masa mafaka ta har abada. A yau ta sadaƙar ta kuma yarda har cikin zuciyarta cewa duk zafi, duk raɗaɗi za ta jure domin kawai ta ba shi haƙƙin sa da ya rataya akan wuyanta. Da hakan ta kafe zuciyarta tare da runtse idanun ta ta yi shiru tana jin yanda yake sarrafa kowace irin gaɓa ta jikinta.
Daren ta na yau ya bambanta da wancan daren da ya kasance mummunan dare a gare ta. Domin yau cikin ɗakin aurenta take tare da Mijinta wanda yake taɓa ta a hankali tamkar yana taɓa ƙwai sabanin wancan lokacin da ta shiga azabtuwa tamkar wanda ya samu dabba.
Komai haka ta shiga jinsa kaman a mafarki wanda ba ta ji ta raina kanta ba sai da ta ji ya yi addu'a ya ɗauki hanya. Ruɗewa ta yi gabaɗaya ta shiga ture sa amma kuma ta riga ta makara domin gabaɗaya ya fice daga hayyacinsa abin kawai ya ke ji da gani.
"Babe..please stop...."
" Relax kin ji Noori tah! Ki dai na jin tsoro kin ji, ba zan cutar da ke ba, ba zan yi miki da zafi ba I promise...idan har wani abu ya same ki har abada ba zan yafewa kai na ba..."
Cike da soyyaya da tausayawa ya tafiyar da wannan daren na su cikin wata irin zazzafar ƙauna mai tsaya a rai.
Bambancin da ta ji daga waccan ranar zuwa wannan shi ma haka ya ji. Wancan ke ta haddi ne ba bisa yarda ba wanda a wancan ranar gabaɗaya baya cikin hayyacinsa saɓanin yau da ita ce ta amince masa kuma da yarda ta kamar yanda yake cikin hayyacinsa shi ma.
Kukanta yake ji can ƙasan zuciyarshi tamkar ana watsa masa ruwan zafi, hakan yasa ya rungumota tare da sake jan Duvet ya rufa su da shi. A hankali ya kai yatsanshi ya shiga goge hawayenta tare da saka ɗayan hannun yana bubbuga bayan ta a hankali alamar rarrashi sannan daga ƙarshe ya buɗe bakinsa muryar nan a narke ya ce.
"I'm sorry mah Noori."
Fuskanta ta kai a hankali ta goga akan faffaɗan ƙirjinshi ta share hawayenta sannan ta kwanta luf tare da ƙara ƙanƙame shi tana sauke ajiyan zuciya.
A hankali ya ji yanayin numfashinta ya shiga sauyawa wanda hakan shi ne ya tabbatar masa da cewa bacci ta yi.
Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya buɗe yana mai jin yanda komai ya shiga dawo masa bit by bit. Ji yake komai kamar ya na yi masa tamkar a mafarki, maryam ce ta sakar masa jikinta tare da ba shi yarda akan ya tara da ita a matsayin domin su kasance abu ɗaya. Ya nemi kalaman soyyayarta da baki ita kuma ta gamsar da shi da ruhi da gangar jikinta. Haƙiƙa ta riga ta gama masa komai a rayuwa wanda yanzu yake ji duk abinda zai faru ba zai taɓa iya rabuwa da ita ba.
Ya ɗauki tsayin dare yana ta tunani kala-kala wanda daga ƙarshe ya janyo wayarsa ya duba time. Ƙarfe huɗu saura minti bakwai abinda agogon wayarsa ya nuna masa kenan.
A hankali ya zame ta zuwa lallausan pillow ɗinda yake kai sannan ya ƙara lulluɓe ta da kyau ya sauka ya shige toilet ya yi wanka ya fito ya shirya cikin jalabiya ya shimfiɗa sallaya ya hau jera nafila yana addu'ar mafi alheri da kuma Alkairan da ke cikin auren gabaɗaya. Fatansa da addu'arsa shi ne duk abin da zai je ya dawo ta fahimcesa, matukar ta amince da shi to duk wani tashin hankalin da zai riske sa mai sauƙi ne.
Haka ya jima akan sallayar wanda duk wani motsinta akan idon har aka gama kiran sallahr asuba.
Stroking ƙafanta ya shiga yi a hankali yana hura mata iska a ido zuwa cikin kunnen ta.
A hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka gama yi mata nauyi tsabar kukan da ta sha ta kalle shi sai kuma ta kawar da kanta.
Ji ta yi ya tallafo ta gabaɗaya sannan ya zare Duvet ɗinda ke lulluɓe da ita ya shige toilet da ita. Kawar da kanta tayi tare da saka hannayenta ta kare ƙirjinta ta ce.
"ni dai ka fita.."
Waje ya yi bai ce mata komai ba ya wuce masallaci.
Ruwan zafi ta haɗa a bathtub ta shiga tana mai lumshe idanunta jin yanda zafin yake ratsa ta a hankali. Haƙiƙa ko yau ta ji zafi, amma bai kai kaman na waccan ranar ba domin bata san ma a wace duniya take ba wancan, amma yau zafin kaɗan ne.
Ta jima tana gasa kanta wanda tunanin maganganunsu Yaa Amina ne ke ta dawo mata na wannan ranar da suke ta bata tabbataci a kai. Ga shi komai ya faru kaman a mafarki.
Sai da ta gama duk bukatunta sannan ta yi alwala ta fito ta yi sallah, tana cikin yin azkhar ɗinta wani bacci mai nauyi ya sake kwashe ta tsabar kasala da gajiyar da ta tarar mata.
Yana shigowa ya ganta kawai ya ji tausayinta ya kama shi. A hankali ya ɗuƙa ya ɗauko ta sai gashi ta buɗe ido ta kalle shi.
"Good morning Wife...."
Sake kawar da kanta ta yi wanda a yanxu wata kunya take ji dangane da irin abinda ta aikata a daren jiya.
Gefen gadon ya ajiyeta sannan ya kwaɓe jalabiyarsa ya bita suka Kwanta suka sake komawa bacci wanda bai farka ba sai misalin ƙarfe tara na safe. A hankali ya sauko gudun kada ya sake tayar da ita ya koma parlour inda ya yasar da kayayyakin tafiyarsa tun a daren jiya, ciki har da wayoyinsa wanda ya tarar da miss calls da yawa har da Maami ta kira shi da Hamad.
Maamin ya fara kira wanda sai yanzu ya tuna da wata Nazli ganin kiran Maamin tasa. Wallahy gabaɗaya ya manta da wannan auren nan nasa da aka ɗaura masa daren jiya.
Tana yin picking ya gaishe ta amma sai ya ji muryanta can ciki ciki alamar tana fushi.
"Maami kina fushi ne?"
"Eh,.."
"I'm sorry..."
"Yanzu Maheer ya kamata ka tafi ba tare da ka tsaya ka yi magana da Nazli ba? Maheer don't complicate things please.! Yanda iyayen yarinyar nan suka yi accepting you have to accept it too matuƙar dai kana son farin ciki na..."
"I'm Sorry Maami, but ina ƙoƙarin yanda zan yi na iya sarrafa kai na ne a wannan maganar. Maami I don't want to do anything stupid da zai sa abubuwa su je yanda bai kamata ba, ki yi haƙuri..."
"Na san cewa gobe ne rananka ta ƙarshe. Idan ka kambala zai ɗauke ka zuwa yaushe ka kambala komai ka dawo gida?"
Dum-dum! Haka ya ji zuciyarsa ta buga lokaci ɗaya. Wannan fa abu ne mai yiyu ba kai tsaye ace yabar Nigeria wai har abada. Ba zai taɓa iya barin maryam ba har abada...
" Maheer magana fa nake..."
"It can take me a month Maami."
"A month??"
Ya ji ta ambata a mamakance domin ita kanta ta ji abin a ba za ta. Wata ɗayan lafiya?
"Maami wasu abubuwan har yanzu ba su kambala ba..."
"Maheer a tsarin da management ɗin Maritime suka gabatar min babu wani additional month a ciki. Is only 12month and gobe kuma wa'adin zai cika..."
"haka ne Maami but ni ina da wani kasuwancin da na yi investing wanda zai iya ɗauka ta a month kafin na gama handling komai na dawo."
"Na ji! To ita Nazli fa?"
"Maami to ai ba ta sa ran cewa ma za'a yi mata wani aure a jiya ba ballantana ta saka rai da wani jiran namiji kawai ta zauna sai na dawo..."
Cike da jin tsabar mamakin da ya kusa kashe ta zaro ido tamkar suna ganin juna ta ce.
"Maheer..."
"Maami ina busy yanzu, idan na kambala abinda nake zan kiraki."
*******
Daga Ammie sai Abbah da kuma shi Faris ɗin suka san abinda yake faruwa. Hatta kayan gadonta da aka rufe da su aka kai wa Alhaji Gimba makulli Abba cewa ya yi a ƙyale shi a nemo mata wani, daman ko banza idan aka ce a ɗauko kayan to wannan gidan da ya kama haya ya yi musu kaɗan domin ɗakunan ba su yi girman waɗan can ba.
Umma na can tana ta gayyato mutane kamar wata mahaukaciya wai su zo raka Rabibinta gidan Mijinta Allah ya kai ta.
A parlourn Baba Salisu Abbah ya saka a kai masa ita a hankali bayan ta zauna ya kira sunanta.
Amsawa ta yi kanta a ƙasa ba tare da ta ɗago ba ya ce.
"Wane ne ya zaɓo miki Faris?"
Sai da ya maimaita kusan sau uku sannan ya ce.
"Rabi'a tambayarki fa nake?"
Sai yanxu ta amsa murya can ƙasa ta ce.
"Abba ni ce."
"Ke ce kika kawo sa kuma kika ce kin amince da auren sa ko?"
"Eh Abbah..."
"To abinda zan faɗa miki shi ne, rayuwar aure gabaɗayanta hak'uri ne, kuma idan kana son mutum babu inda ba za ka iya binsa ku zauna ba. Daɗi baya zama kullum haka zalika rashin daɗi baya zama kullum. Faris namiji ne wanda ya san abinda yake ki bi mijinki sau da ƙafa ku zauna lafiya. Idan kuma wani abu ya biyo baya na wulaƙanci ko na take haƙƙi to ki sanar dani in sha Allahu zan yi abinda ya kamata. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuriya dayyaba."
Ba tare da kawo komai a ranta ba ta amsa da amin suka fito. Ammie ta so ya fito fili ya yi mata bayani domin ya ja mata kunne don ta san halin ta amma sai ya ce ta ƙyale ta Mijinta shi zai fahimtar da ita.
Haka suka fito hannunta cikin na Aunty Shema'u suka shige mota suka tafi.
Unguwar ko ita ba laifi tana da dama dama, amma daga shiga unguwar zuwa cikin gidan da 'yan kai amaryar suka shiga daga nan zance ya sauya sai gulma ta kacame tamkar filin wunin buki. Shima gidan ƙaramin gate ne sai matsakaicin harabar gida. Parlour ne da bedroom a haɗe Wanda ke da toilet ciki, sai kuma wani single room dake waje shi ma daban da aka sanya mata wani gado a ciki.
Sai kitchen a waje da kuma toilet ɗin tsakar gida. Gidan ba laifi domin tiles ne a parlour sai breaking tiles a tsakar gidan.
Hankalinta ne ya ta shi ganin ɗakin da aka shigar da ita ga maganganun mutane dake tashi a kunnen ta ɓaro-ɓaro ta na ji.
A ruɗe itama Aunty Shema'u ta ce.
"Kutumar uba! Rabi'a miye haka nake gani? Ya naga wani gidan ba wancan aljannar duniyar ba?"
Yaye mayafin kanta ta yi tare da miƙe tsaye ta fashe da kuka tana kallon mutane ta ce.
"Nima abinda na gani kenan Aunty Shema'u. Miye abinda yake faruwa haka?"
Leƙowa Mummy Jamila ta yi ta ce.
"Ku fito jama'a mu tafi dare yana ƙara yi.."
Mayafinta suka ga ta figa itama tana faɗin.
"Wallahy tallahy ni ma ba za'a bar ni a wannan gidan ba, wallahy gida zan koma.."
Zaro ido Aunty Shema'u ta yi tace.
"Ki rufa min asiri Rabi'a ki yi hak'uri ki zauna, ki jira idan mijin ya dawo sai ya sanar dake abinda yake faruwa. Idan kin ga wurin zama ki zauna. Idan kuma ba ki gani ba sai ki san inda dare ya yi miki. Amma Mukam ba za ki barmu da mummunan tarihi ba ace mun kawo amarya mun koma da ita. Ko kuwa jama'a na yi laifi?"
Ta ƙarashe maganar tana mai kallon mutanen da suke ɗakin.
Komi Mummy Jamila ba ta ce musu ba, daman su Yaa Na'ima suna shigowa suka juya suka koma abin su.
A haka suka zame suka barta ita kaɗai tana wani irin kuka mai ban tausayi. Tana ganin sun fice ta ɗaga waya tun kafin su isa ta kira Umma ta shaida mata halin da ake ciki.
Bayan ta kashe wayar ta sake Leƙowa waje ta shiga ƙarewa tsakar gidan kallo, Generator ɗinda ta hango yana aiki shi ne abin da ya ƙara baƙanta mata zuciya ta sake rushewa da kuka. Babban Gen ɗin wancan gidan ta tuna wanda yake da ɗaki mai zaman kansa tsakar gida mai interlock da abubuwan more rayuwa shi ne zai yi mata baƙin ciki ya kawo ta nan.
Tunda 'yan rakiyarta suka fita bata zauna ba har ta ji an buɗe ƙofar an shigo.
Wani kallon banza ne ta watsa masa mai cike da takaici da baƙin ciki.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 60*
Wani irin kallo Faris ya tsaya yana yi mata, kallon da yake cike da zallar mamaki ganin irin tarbon da ya samu. Kowace amarya ta duniya yasan cewa a lulluɓe take tana jiran angon ta ya zo gare ta. To amma saɓanin hakan ya tarar a wurin Rabi'a.
A hankali ya rufe ƙofar bayan ya shigo gaba ɗaya, jingina bayansa yayi jikin gini yana kallonta yadda take tsaye tana kuka kamar wacce aka zalunta da gaske.
"Rabi’a…"
Ya kira sunanta a hankali murya ƙasa-ƙasa yana mai jin tsoron ƙara tayar mata da hankali domin bai san abinda take yiwa duk wannan ba.
Sai dai kuma kalmar tasa kamar ma ƙara fusata ta tayi.
"Kar ka kira sunana!"
Ta faɗa da ƙarfi tana share hawayenta da bayan hannu tana wani cika tana batsewa.
Lumshe idanunsa ya yi na ɗan lokaci, yana mai ƙoƙarin haɗiye abinda yake ji a ransa na tsananin ɓacin rai da takaicin ta.
A hankali ya baro jikin ginin ya tako gaba kaɗan yana kallonta ya ce.
"To… me kike so na kira ki?"
Wani irin kallo ta watsa masa ta ce.
"miye wannan ka aikata min? Da gaske kai ne ka kawo ni nan ko kuma mafarki nake? Ina gidanmu da muka je na gani, ina gidanmu wanda aka jere min kayana a ciki? Don Allah Faris bana son wasa. Wannan irin wasan sam ba ta kamata ba a irin wannan lokacin da ya kasance daren amarcinmu..."
Girgiza kansa ya yi yana kallonta ya ce.
"Babu wani abu makamancin wasa a nan Beeyh...duk abinda kike gani da gaske ne yake faruwa, wannan shi ne gidan aurenmu a yanzu, wanda ko shi ba mallaki na bane haya ce na kama mana. Daddy ya karɓe komai nasa wanda na mallaka da sunan sa, mota, gida, kasuwanci, kuɗi, komai ya karɓe Beeyh. saboda haka yanzu zamu fara sabuwar rayuwa..."
Wani irin tsalle ne ta ji zuciyarta ta yi tsabar mamaki da tsananin kaɗuwa. Anya Faris yana cikin hayyacinsa kuwa? Kodai daman can yana shaye-shaye ne ba tare da ta sani ba? Wannan ai maganar hauka ce da renin hankali. A gidan ubanwa hakan zai faru ace a daren auren su ubansa zai karɓe komai na sa?
"Beeyh ki nutsu dan Allah, komai ya yi tsananin sauƙi yana tafe in sha Allah..."
Wani irin zabura ta yi da ƙarfi ta wani cire ɗankwalinta ta ɗaure a waist ɗinta tana mai yi masa wani kallon banza a tsawace ta ce.
"Allah ya isa tsakanina da kai Faris! Ka yaudare ni, ka ci amana ta. Kuma wallahy sai Allah ya saka min. Faris...wannan gidan? Wannan ne kake tunanin ni Rabi'a na rayu a ciki?"
"Tabbas wan can ne gidana a baya, but abubuwa sun canja Rabi'a kwana biyu da suka wuce? Yanzu ma bai kamata ki karaya ba, zan jajirce, zan tsayu wurin neman na kai na wanda in sha Allahu watarana za ki samu rayuwar da kike so..."
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"Never wallahy! Ni ban zo gidan ka domin na wahala ba! Ban san ta ba don ban taɓa rayuwa a cikinta ba, kuma wallahy tallahy ba zan fara a nan ba. Ba haka na zaɓawa kai na ba, rayuwar jindadi da morewa ita na tsara. Rayuwar yawo ƙasashen duniya ita na tsara. Babu ta yanda za'a yi Yaa Na'ima, Anaam da kowa ace yana cikin rayuwar hutu ni na ƙare a irin wannan makararren gidan mai kama da sheƙar tsuntsaye. Kai hatta Sa'adah da nake ganin Mijinta ba kowa ba wallahy gidansa ya ninka wannan sau dubu. Ni za ka rainawa hankali?"