Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 49

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 49

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 49: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 49. Hajiya Salamatu na ganin ya fice ta sake fashewa da wani irin…

3,370 words

Hajiya Salamatu na ganin ya fice ta sake fashewa da wani irin kuka wanda gabaɗaya ta rikice ta ma rasa ko a wane irin yanayi take. A rayuwarta bata taɓa ganin yaro mai tsananin fushi da kaushi irin Faris ba. Yanzu da ya ajiye masa komai ta ya ya zai fara rayuwa kenan? Ga shi ita kanta ya ƙi ya tsaya ya saurare ta ballantana ta ji inda ya dosa.

******

Har kusan ƙarfe goma na dare babu masu ɗaukar amarya babu labarinsu. Hakan yasa Ammie ta kira Abbah ta ce ya bincika ya ji miye dalili an gama shirya Amarya tun ƙarfe shida amma ga shi har goma ta yi babu labari.

Da kan shi ya ɗaga waya ya kira Faris wanda bai ɓoye masa komai ba ya faɗa masa duk yanda aka yi.

Yana gama saurarensa ya ce ya zo gida ya same shi yanzu yana jiransa.

Nan da nan ba ɓata lokaci sai ga shi ya zo. Gabaɗaya ya gigice ya fice daga hayyacinsa.

A ƙasa ya zauna wurin ƙafafun Abbah kansa a ƙasa yana mai jin har yanzu yanda zuciyarsa ke wani irin tafarfasa.

"Faris..."

"Na'am Abbah."

Ya amsa yana mai ɗagowa ya kalle shi.

"Ni wannan al'amarin nan naku ban san ma mi zan ce ba, shiyasa tun farko na so ka haƙura Faris tun akan Maryam da ka faro. Domin ni ina hango abu makamancin wannan ɗin. To amma kuma tunda har haka ta faru, sai mu yi addu'ar Allah ya kyauta ya zaɓa mafi alheri. Sai dai kuma ina so ka sani cewa duk yanda abubuwa za su canja shi fa mahaifinka mahaifinka ne, yin gaba da shi ko kuma wani takun saƙa duk baya daga cikin ɗabi'a ta yaran kirki. Saboda haka Idan ya huce dole za ka je ka bashi haƙuri matuƙar kana so ka ga daidai a cikin rayuwarka."

"In sha Allah Abbah zan yi hakan."

"Ahm...In sha Allahu akwai gida da zaku zauna wanda wannan ɗin ba matsala ba ne domin ba ni ba, ko Alhaji Ridwan zai iya baka gidan da za ka zauna a ciki har ƙarshen rayuwarka..."

Girgiza kansa ya yi ya ce.

"A'a Abbah, bana so komai daga wurin kowa, I will stand on my feet domin in tabbatar masa da cewa ni ɗin namiji ne, idan har na tsaya aka bani wurin zama to har yanzu ban cika namiji ba."

"To yanzu miye plan ɗin ka?"

"Zan kama haya da kuɗaɗen da na samu a matsayin gudummawa sauran kuma na fara kasuwa da su mu gani. In sha Allahu na yi maka alƙawarin riƙe ta da yi mata duk wata hidiman ta gwargwadon iyawa ta. Saboda haka a bar ta a bani kwana biyu zan nemo gidan da zan sakata a ciki."

" Shi ke nan. Allah ya zaɓa mafi Alkairi. Bari in sha Allahu zan musu bayani."

Yana fita Abbahn ya kira wayar Ammie ya yi mata bayani amma yace kada ya sanarwa kowa kawai dai tace tafiya ta kama Faris ta uzuri, kwana biyu idan ya dawo sai a kai ta. Rasa ta yi ta inda za ta fara yi wa Umma wanga bayani, hakan yasa ta kira Mummy Jamila ta ce ta yi mata tace itama Alhaji ne ya kira yace a sanar musu.

******

Kwanan sa huɗu a Oman ɗin ya tattara da nufin tafiya bayan yaga yanayin Grandpa ɗin ya sauya domin ya samu sauƙi sosai ba kaman ranar da ya iso ba. Kwana biyu yaso ya yi but yanayin condition ɗin nasa da kuma yanda Maami ta ɗaga hankalinta hakan yasa dole ya dakata na kwana biyu.

Yana shiga parlourn Naana ya tarar da shi zaune akan lallausar kujerar sa ya jingina bayansa tare da lumshe idanunsa tamkar mai bacci.

Ganin su Uncle Abdallah da su Uncle Ameed da su Hanan a ɗakin ne ya yi matuƙar ba shi mamaki.

Aunt ɗinsa ziyadah ce ta kalle shi ta ce.

"Ka zauna mana.."

Wuri ya samu a kusa da Naana ya zauna yana kallon fuskar mahaifiyarsa wacce itama shi ɗin take kallo.

Muryar Abiyh suka ji can ƙasa yana faɗin.

"Maheer ɗin ya zo?"

Uncle Abdallah ne ya amsa sa yace masa yazo.

Jin hakan yasa a hankali ya buɗe idanunsa tare da miƙo hannu alamar Maheer ya matsa kusa da shi. Hakan yasa ya matsa tare da kama hannunsa cike da tausayi ya ce.

"Sannu Grandpa..."

"Maheer mahaifiyarka ta damu da irin sababbin halayen da ka sauya, tun muna ganin laifinta muna ganin kaman tana tsaurara maka har muma muka gane cewa tabbas ka sauya da gaske. Kukanta da tsoron ta a yanzu shi ne kada na mutu baka yi aure ba, tana tsoro kada bayan ƙasa ta rufe idona ka canja fiye da yanzu..."

Hankalinsa ne ya tashi jin kalaman Kakan nasa domin sam bai tsammaci cewa wai wannan zaman an yi sa ne ba saboda shi.

Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya buɗe sannan ya saka ɗayan hannun nasa ya jimƙe hannun Grandpa ɗin ya sumbata a hankali ya ce.

" Babu abinda zai sameka Grandpa..."

"Ai ita mutuwa gaskiya ce Maheer...musamman ga mai irin shekaruna da kuma irin condition ɗina a yanxu mutuwa ta fi kusa da ni. Hakan yasa na yanke hukunci cewa zan aura maka Nazli...."

A gigice ya waro ido ya kalle shi kaman yanda itama Nazli dake dannar waya ta ji maganar kaman a ba za ta. Jin ta ne ya ɗauke lokaci ɗaya na wucin gadi daga ita har Maheer ɗin domin ji suka yi kaman ba su ji abinda yace da kyau ba.

Su ɗin ne yanayinsu ya yi saurin bayyana mamakinsu amma har Su Maami da mahaifin Nazli ɗin wato uncle Ameed da sauran mutanen ɗakin sun kaɗu da jin wannan zance na Abiyh. Babu wanda ya faɗawa babu wanda ya yi shawara da shi daga shi sai Naana suka yanke wannan hukuncin.

"Na so sai ka kambala aikinka ka dawo gida, to amma tsoron kada na mutu ban cika wannan burin nawa ba saboda yanayin jikina shiyasa na yanke nake so a ɗaura muku auren a yau, idan ya so in ka dawo sai ku yi duk wani shiri da za ku yi..." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 59*

Wani irin shiru ne ya ci gaba da ratsa ɗakin na tsawon lokaci. Numfashi ma sai ya zama kamar ana jin sa a sarari tsabar yanda kowa ya nutsu yana nazari akan waɗan nan maganganu na Abiyh.

Maheer ya tsaya cak, idanunsa ƙyam akan Abiyh yana mai ƙoƙarin fahimtar shin anya da gaske kuwa yake yi ko ko dai mafarki ne.

"Grandpa…?"

ya furta a hankali muryarsa har tana cracking, ƙoƙarin yake ya furta masa kalmar A'a amma kuma ya kasa hakan.

"Ameeduddeen Na faɗi abinda na yanke tun kusan shekaru biyu da suka wuce. I waited for the whole 2years Ko zai kawo wata yarinyar da ya ji yana so ya aura, but har yau babu wani labari, hakan yasa a yau na yanke wannan hukunci. Babu wanda yasan gobe sai Allah, ta yi yu ba zan kai gobe ba..."

Nan take ya ji zuciyar sa ta sake bugawa a karo na barkatai. Nazlin ce zai aura a yau? Aure dai sai ka ce wani abun wasan yara? Daga can wani ɓangare na zuciyar shi kuma yaji yana tunasar da shi cewa Kana da mata...Maryam ɗinka, farin cikin ka, you promised her alot kada ka amince da wannan auren domin hakan zai rusa tsakaninku.

Miƙewa suka ga ya yi da sauri yay excusing kansa ya fice daga parlourn ya koma bakin ƙofa tare da ɗora hannayensa akan wani ƙaramin pillar dake zagaye da wasu kyakkyawan flowers ya dafe kansa.

Cikin zafin nama Maami ta tashi ta bi bayansa. Bai ji time ɗinda ta zo wurin ba, sai saukar muryanta da ya ji ta ambaci sunan sa a hankali.

Waigowa ya yi idanunsa cike da tashin hankali ya riƙo duka hannayenta a diririce ya ce.

"Maami..."

Itama cikin tsananin mamakin irin wannan ruɗewa da taga ya yi ta katse shi mishi hanzari da faɗin.

"Wai miye kake haka Maheer? Miye matsalarka?"

"Maami please talk to him..Nazli fa Maami? Maami please ni bana son wannan auren..."

"Okay.."

Ta ambata tana mai jinjina kanta ranta na yi mata babu daɗi. She thought cewa zai karɓi wannan maganan with single minded. She thought har abada ba zai iya ja da umarnin Abiyh ba kowane iri ne a rayuwar nan. Miye matsalan Nazli? Nazlin ce baya so ko kuma dai auren ne baya so?

"Ina so ka faɗamin one single reason da yasa ka ƙin wannan auren?"

Kai tsaye ya runtse idanunsa tare da girgiza kansa ya ce.

"Nazli Maami..."

"Na ji, Miye matsalanta?"

Shiru ya yi tamkar ruwa sun cinyesa ya haɗiye sauran maganansa domin yasan cewa Nazli ba ta da wata matsala.

Muryan Maamin ya ji softly tana faɗin.

"Nazli tana da duk wasu qualities ɗinda ake buƙata wurin auren mace ta gari Maheer. Tana da ilmi na addini da na zamani,tana da tarbiyya, tana da wayewa, ta iya girki,tana da kyau and....abu mafi muhimmanci shi ne kun fito daga family ɗaya, ka san ta ka san iyayenta ba ka da wata fargaba. Maheer ba kawai mata nake so maka ba, ina so maka Uwa mai nagarta ga yaranka, ina so maka bangon jingina a duk lokacin da ka gagara tsayuwa, ina so maka hasken da zai zamto marar gushewa a cikin gidanka."

"Maami Nazli tana da girman kai da jiji da kai, tana da alfahari da jin cewa ita ɗin wata ce. Zamu iya shekara without talking to each other because tana da wani hali na jin cewa ita ɗin kaman ta fi kowa..."

Hannunshi ta ƙara jimƙewa tare da ƙara sassauta murya tana kallon fuskar sa ta ce.

"Maheer...kada ka manta fa ita ɗin mahaifiyarta daga gidan sarauta ta fito! Akwai wannan jinin mulkin da yake gudana a cikin jinin ta da yasa take acting haka. A duniya kowane mutum yana da irin nature ɗinsa da kuma halayyarsa. Ita ɗin mace ce kai kuma namiji, kai ne wanda yake da makullin ƙulla kyakkyawan alaƙa a tsakaninku. Nazli mace ce da ta cancanci a so ta sannan duk wanda ya same ta ya cancanci ayi masa barka. Ita ce Mace amma kuma bata musa da wannan umarnin na kakanta ba, mahaifinta ma bai musa daga umarnin mahaifinsa ba, dan Allah ina roƙonka kada ka kunyata ni a wannan maganan, yanda suka karɓa hannu biyu kai ma ka karɓa ka yi addu'ar mafi alheri a tsakanin ku. Idan har kace ka juya baya to ni ɗin nan ni ka tozarta a cikin dangina ba kowa ba. Ka tuna kana da dangin mahaifi amma kuma nawa dangin su ne suka yi maka komai tun kana ƙarami har zuwa yau, please kada kace za ka yi musu butulci. Idan na isa da kai to ina so ka amshi wannan auren kuma ka tsaya a ɗaura shi a yau. "

Tana gama faɗin haka ta juya ta koma ciki. Ɗakin sa dake gidan yaje ya shige tare da faɗawa kan makeken gadon sa yana jin yanda kalaman mahaifiyarsa ke amsa kuwwa a cikin kunnuwansa. Ta riga ta gama ɗaure shi da igiyar da komai rashin hankalinsa dole ya tsaya ya saurare ta. Wannan wace iriyar bahaguwar ƙaddara ce ta sake shigowa rayuwarsa? Bai gama da matsalan Maryam ba ga shi ya sake faɗowa cikin wani tarkon da bai san yanda zai yi ya fita ba. Miye abinda zai faɗawa Matar sa Maryam wacce ta kasance fitila kuma hasken rayuwarsa a yanxu.?

A gefe guda kuma…

Nazli gabaɗaya lokaci guda ta nemi nutsuwarta ta rasa. Anya Abiyh ya san abinda yake faɗa kuwa? Kodai zafin ciwo ne ya ruɗasa? Ita fa tana da wanda take so ba Maheer ba. Ko kaɗan tsarin rayuwarta da rayuwar sa ba su yi kama da juna ba. Magana wannan idan za su haɗu sau goma bai fi su gaisa sau ɗaya ba. Ta kan ji shi da su Zarah suna fira idan ya so wanda ko shi sai can baka rasa ba. Yanzu ta ya za'a aura mata wannan mutumin sai ka ce ta rasa mai son ta? Gaskiya Abiyh bai duba mata ba. Girman ajinta da alfaharinta sun ƙarfin wannan wulaƙancin da Abiyh ya yi mata.

Muryar mahaifinta ta ji yana faɗin.

"Hakan da kayi shi ne daidai Abiyh, kuma mun yi matuƙar farin ciki. Maheer da Nazli dukkan su abu ɗaya ne, Allah yasa wa wannan aure da za'a ɗaura albarka ya basu zaman lafiya."

Cikin farin ciki Uncle Abdallah da Uncle Ibrahim suka amsa da Amin because ba su yi expecting ba. Sun ɗauka Uncle Ameed zai nuna rashin amincewa domin shi ne yake da ɗan tsauri wani lokaci, but unfortunately sai ga shi ya amince kai tsaye cike da zallar farin ciki.

Nan take abu kamar wasa suka tara mutane wanda duk su ne familyn da kuma familyn mahaifiyar Nazlin domin suna girmama Abiyh suna jin maganar sa. Duk yanda Nazli ta so ta kasa gardamawa Umarnin Abiyh ɗin duk da cewa mahaifiyarta itama bata amince ba kawai dai iyayenta ne da 'yan uwanta suka dakatar da ita amma ba don ranta ya so ba.

Ba za ta ce tana ƙin Maheer ba kai tsaye because ya kai kowane irin namiji da ya cancanci a so shi sai dai babu soyayya kuma ta san babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakanin su and again she will never bow on him Wai da sunan biyayya matuƙar yace zai nuna mata rashin daraja a gidan auren na su. Auren ma da take gani kamar almara kaman wasa kaman kuma mafarki. But tana jin cewa wai da gaske an ɗaura kawai ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da rashin makama.

Arwah da ke tsaye a gefen ta ne ta kalle ta cike da tausayi ta ce.

"I'm sorry sis..."

Cike da wani irin baƙin ciki ta miƙe tsaye jikinta har yana wani irin ɓari ta kalli Arwah ɗin murya cike da kuka ta ce.

"Arwah da gaske ne Abiyh bai ga wacce zai tozarta ya zubar mata da mutunci da irin wannan auren ba sai ni? Sai ka ce ya samu wata ɗiyar Baby? I swear...."

Saurin haɗiye maganar ta yi bayan sun yi ido biyu da mahaifinta.

A hankali Arwah ta janye jiki ta sulale ta yi waje.

Hannun ta Uncle Ameed ya riƙo wanda hakan yasa ta ɗago kanta ta kalle shi. Murya cike da ƙwarin gwiwa ya ce.

"Mahaifina shi ne gaba da komai a rayuwata Nazli, yi masa biyayya ya zamemin dole, and kema yi masa biyayya ya zama dole a gare ki. Na yarda da zaɓin da ya yi miki domin kin samu miji wanda ya dace dake. Da bai cancanta ba Abiyh ba zai taɓa aura masa ke ba. Lailah uwa ɗaya uba ɗaya muke, Maheer kuma ɗan ta ne, kaman yanda kike ke ɗaya tilo a garemu shi ma haka yake ɗaya tilo a wurinta. Zumuncinmu ɗaurarre ne wanda muke da cikakkiyar amana da yarda a tsakaninmu, kada ki bari a samu matsala daga ɓangaren ki domin ba zan taɓa yafe miki ba."

Yana gama faɗin haka ya fice fuu daga ɗakin wanda a hanya ya yi kiciɓis da mahaifiyarta, wani kallon ya yi mata sannan ya ce.

" Rumana kada ki ce za ki turza yarinyar nan kisa ta bijirewa wannan auren. Idan har aka samu wata matsala tabbas ba zan ƙyale ki ba."

A hankali mahaifiyarta ta taka ta shige ɗakin ba tare da ta furta masa komai ba, hannayenta ta kai ta yi curving kyakkyawar fuskanta ta juyota idanun su suka sarƙafe sannan ta jinjina mata kanta ta ce.

"Nazli ko kaɗan ban yi farin ciki da irin wannan auren da aka yi miki na nuna fin ƙarfi ba, a matsayin ki na 'ya ɗaya da nike da ita ace wai auren ki ne ya ƙare a haka dole nayi baƙin ciki. Kuma ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu muddin naga alamar cewa za ki cuta ni ba zan zuba ido ina kallo ba, matuƙar na ga cewa bai amshe ki hannu biyu ba ni kuma ba zan ji fargabar neman a raba auren ba domin farin cikin ki ya fiye min komai a duniya duk abinda zai faru sai dai ya faru. Iyaye na sun riga sun amince kuma sun gargarɗeni akan kada na ce zan nuna rashin amincewa, hakan yasa kika ga dole na yi shiru Nazli, amma wallahy tallahy duk naga wani abunda ban yarda da shi ba daga wurin shi to dole a raba auren nan ko sun ƙi ko sun so."

*******

Zaune yake a jirgi amma gabaɗaya hankalinsa baya jikin sa. Ana gama ɗaura auren ko kallon cikin gidan bai ƙara yi ba kawai ya fito ya wuce abinsa. Har yanxu jin komai yake kaman a mafarki domin babu yanda za'a ƙirƙiri maganar aure cikin mintuna sannan kafin 2hours cikakku su cika ace har an ɗaura kaman wani wasan yara.

Maami ba ta san irin halin da yake ciki ba da ko ance ta karɓi wannan auren ba za ta yi ba. Ya so ya kauce, ya so ya ƙi amincewa amma damar hakan ba ta samu ba, domin ta bi duk wata hanyar da za ta bi domin hana shi magana wanda sai da ta yi nasara sannan hankalin ta ya kwanta. Akwai abubuwa a ransa waɗanda yake neman mafita da su, yaso ace duk abunda ya ɗebo ya tsaya tsakaninsa da mahaifiyarsa ne kaɗai. But yanzu abubuwan da yake fuskanta sun dulmiyo wasu mutane a ciki waɗanda yake hango babbar ɓaraka da za ta janyo rugujewar ahlin mahaifiyar tasa baki ɗaya.

Idan suka ji abinda ya aikata sannan ga auren Nazli da yake kansa a yanxu bai san yanda abubuwan za su kasance ba.

And again Maryam! Ya zai yi da maryam kenan? Mahaifiyarsa da dangin ta gabaɗaya sun san cewa mahaifinta ne ya kashe masa mahaifinsa. And ita kuma She is always thinking of cewa ba da gaske yake sonta ba. A lokuta da dama tana yawan faɗa mishi cewa ita ɗin tasan cewa ba ta kai a kira ta da matar shi ba domin zubi da tsarin rayuwarsu sun bambanta, dole akwai wata wacce yake da wacce ta fita komai wanda watarana zai aure ta ita kuma ya nemi rabuwa da ita.

"Yah Allah!"

Abunda ya furta kenan tare da runtse idanunsa jin wani irin sabon tashin hankalin da ya sake mamaye masa zuciya.

Babu abinda bai zo masa a rai ba har ya sauka garin Abuja wanda duk juyin duniya idan ya yi sai fuskar Anaam ta zo masa a tunanin sa.

Bai ƙara jin tashin hankali ba sai da ya shiga gidan ya ga ta taso cike da farin ciki ta rungumesa a hankali ta kai bakinta saitin kunnen sa kaman yanda yake yi mata ta ce.

"Welcome Babe. Your Maryam misses you so much..."

Ɗagota ya yi ya kalle ta cikin idanun ta yana mai jin yanda zuciyarsa ta karye ganin irin farin cikin da take ciki da ganin sa. Hakan yasa ya sake saka hannayensa ya rungumeta gam a jikinsa tamkar wanda zai maida ta ciki.

Jin kaman jikin shi da zafi yasa ta janye hankalinta a tashe tana kallon sa ta ce.

"Are you sick? Na Ji kaman jikinka da zafi..."

Ta ƙarashe maganan tana mai kai hannun ta akan forehead ɗinsa zuwa wuyansa.

Hannunsa ta ja suka shige ciki ta zaunar da shi akan kujera sannan ta je kitchen ta haɗo mai Tea only ta kawo. Hannu ya miƙa ya karɓa har yanzu ba tare da ya yi magana ba.

Tana ganin ya shanye ta ja shi zuwa ɗakin shi da kanta ta rage mai kayan jikinsa abun da bata taɓa attempting yi ba tun farkon auren su har zuwa yau, sai ga shi kanta tsaye ta aikata tare da jansa cikin toilet ta bar shi ta fito.

Koda ya fito ta ciro masa wasu lallausan sleeping dress na cotton sannan da kanta ta taimaka masa ya saka wanda gabaɗaya ya ji lokaci ɗaya ta ruɗar da shi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull