Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 48

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 48

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 48: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 48. Miƙewa ta yi tsam tare da ɗaukan Bag ɗinta ta ce.

3,352 words

Miƙewa ta yi tsam tare da ɗaukan Bag ɗinta ta ce.

"Let's go to the class kinga har time ɗin Madam Rozy ya kusa cika kada ta riga mu shiga kinsan halin ta."

Daga haka ta shashantar da zancen suka tashi suka koma lecture hall ɗin.

******

Gidan Alhaji Mas'ood kuwa, sun riga sun gama shirin tafiya gabaɗaya ahlin gidan wanda Mukarram ne kaɗai yace ba zai je ba kuma matar shi Aysha itama bai amince taje ba.

Haka suka shirya washe gari sai Gusau, gidansu dake Damɓa suka sauka wanda tun barin su garin basu ƙara zuwa ba sai yau amma dai Mubarak da Yaa Muhammad duk wanda ya zo yana sauka a nan.

Sosai abubuwan da suka faru a baya suka shiga dawo musu musamman Ammie da take ganin komai a idon ta kamar jiya ne yake faruwa.

Bayan sun huta sun ci abinci ta ɗauki Rabi'a ita da Yaa Amina da Na'ima suka wuce da ita gidan mahaifinta wanda suna shiga tun a harabar gidan Umma ta kece da wata irin guɗa tare da rugowa tamkar wata ƙaramar yarinya ta rungume Rabi'a tana ta yi mata kirari tana zuzuta ta tana taɓa habaici iri-iri wai ita ma ta nunawa su Ammie cewa ita ma fa Rabi'a ta samu mai kuɗin wanda duk ƙaryar Haisam bai yi wa Na'ima kayanda aka yi wa Rabi'a ba.

Kallonta Mummy Jamila ta yi ta girgiza kai cike da baƙin ciki ta ce.

"Shi dai mutum idan aka ce ya samu matsala to tabbas ya riga da ya same ta har abada. Allah ya shirye ki Umma..."

Hannaye ta ɗaga sama tana wani irin murmushi ranta fes ta ce.

"Ameeennnn Jamila! Ai ni yanzu bani da lokacin fushi ko lokacin ɓatawa ga ire-irenku domin na wuce da sanin ƙaramin ajinki. Da ne ake yi min kallon rai ni kallon wacce ba ta da shi, to amma yanzu ƙaryar mutum wallahy sai dai ya bi ni..."

Wani kalar murmushi Ammie ta yi wanda ita kaɗai tasan abun da take nufi sannan ta ce.

" Ai mu haka muke so Hajiya Umma, ubangiji Allah ya ƙara rufa mana asiri baki ɗaya..."

Daga nan suka tafi kowa ya ci gaba da abinda yake gabansa. Daman gobe ita ce ranar sa lalle hakan yasa yau ta kasance ranar shirye shirye a gare su wanda.

Duk wanda ya kalli Rabi'a sau Ɗaya sai ya ji ta burge shi domin Ammie ta sa an yi mata gyara na musamman wanda babu algus, kuɗi ta zuba aka shiga gyarata ciki da waje wanda komai hassadar ka idan ka kalle ta sai ka yaba ta.

Magrib na yi Ammie ta wuce gida ita da su Yaa Amina suka kwana sai washe garin sa lallen suka zo misalin sha biyu na rana.

Wani irin feleƙe ne Umma ta shiga yi wanda duk yanda zaka kalle ta sai ka ji ta baka dariya wai Ita nan surukar masu kuɗi.

Ammie na zaunawa Parlournta ta zo tace Ammien ta tashi ita kaɗai ake jira a wuce wurin gyarawa Rabi'a gida. Saboda haka ta tashi su tafi kuma bata ɗaukewa kowa ba.

Haushi ne ya kama Na'ima ganin yanda Umman take ta wani magana in a commanding tune kaman ta ajiye mutane. But sai Ammie ta ce mata ta yi haƙuri domin lokacin ta ne, bata taɓa aurar wa sai yanzu, saboda haka su yi haƙuri a samu a rabu lafiya.

Mutane ne da yawa Umma ta gayyata tun daga en uwa har zuwa abokai maƙota kowa ta gayyato azo aje wurin jeren ɗakin Rabi'a. Mutane kowa mamaki yake irin mutanen da ta tara wanda sun san cewa yanzu ba jere ake ba kawai dai ana zuwa a gyara ne kuma baya wuce mutum uku highest mutum biyar.

Koda su Ammie suka je gidan sun tarar an gama saka gadaje, daman 3bedroom ne with 2parlour wanda kowane an cika shi da kaya waɗanda Abbah, Yaa Muhammad da Naseer suka siya. Kitchen ma guda biyu take da shi kuma duk an zuba uban kaya a ciki. Gidan ya burge ba kaɗan ba. Mutane kowa sai santin shi suke suna kiran Rabi'a ta yi sa'a ta samu miji mai kuɗi.

Sun yi event yakai uku wanda aka kashe kuɗi aka kama Hall aka yi shagali aka yi rabon kayayyakin soveniers na alfarma.

*******

Alhaji Gimba ne a zaune yana waya a ɗakin Maimuna ita kuma tana tsaye tana saurarensa wanda jira kawai take ya sauke ta furxa mishi abinda yake ranta.

Yana gama wayar ya ajiyeta a gefe ransa a ɓace ya ce.

"Can you imagine wai ni Alhaji Sambo zai kira wai yana mini barka da arziki?"

Taɓe baki ta yi ta ce.

"Ah ah to! Wannan irin dukiya da suka ga ana darzaza ai dole su ɗauka da son ranka ake komai. Dukiya an narke ta a banza ko Ince ana kan narka ta sai ka ce bai san zafin yanda ake wahala wurin nemanta ba..."

Kallonta yake sai kuma kawai yaga ya ta fashe da kuka taci gaba faɗin.

" Shi ke nan ka sakar musu komai suna ta yanda suka ga dama ita da ɗanta wurin auren da ma yaƙi ya yi maka biyayya. Kada ka manta ni ma fa ina da haƙƙi kuma ni ɗin ba juya bace ballantana kace ba zan haihu, watarana nima 'ya' yan nan zan haifa maka su. Kuma ita guda ɗaya kawai ta baka amma ni zan haifa maka maza da yawa da yara mata, to a lokacin idan sun gama ƙarar da dukiyar mu muyi yaya kenan? Baka ga ko ranar kai lefen nan ba yanda iyayenta ke ta alfahari suna faɗin sun samu abin banza dukiya ta zo..."

Cikin kalaman rarrashi ya ce.

"Ya isa Maimuna! Ki yi haƙuri kuma wallahy daga shi har uwar ta sa ƙarya suke yi. Zan nuna miki ƙarfin iko na da kuma isa ta. Ai gwanda ke da za ki haifa min yara da yawa to ita fa? Ɗa guda ɗaya tal ne kamar idon Besfa wanda gashi ya zamo min jarrabawa. Saboda haka zan yi maganin su na faɗa miki."

Daga haka ya miƙe ya je sashen Hajiya Salamatu wacce ya tarar a zaune saman sallaya tana lazimi bayan ta gama sallah.

Rabon shi da ya shigo sashenta tun ranar da Faris ya shigo gidan nan. Yau ma daga yanayin fuskarsa shi ya tabbatar mata da cewa ba Lafiya ba.

"Ina ɗan ki yake? Duk inda yake kice na ce yazo ina nemansa yanzu-yanzu."

Cikin wani irin farin ciki ta ce.

"Yanzu kuwa zan kira shi ya zo."

Baiwar Allah jiki na rawa ta ɗauko wayar ta ta kira shi amma sai aka ce mata a kashe, ita duk tunanin ta wata ƙila ya yafe masa ne tunda taga cewa yau daren ɗaura auren ne gobe za'a ɗaura da sha biyu na rana wata ƙila ya karbi shawarwarin mutane ya haƙura zai yafe masa.

"Miye kika tsaya kina yi? Ki kira sa na ce."

"Wayar ce Alhaji ba ta shiga...."

"Ki tabbatar kin same shi cikin daren nan kin ji na faɗa miki." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 58*

Na'ima na zaune a ɗaki tana breastfeeding Khalifah sai ga Kiran Anaam ya shigo wayanta. Da sauri ta yi picking ta ce.

"Hmm! Ke yanzu haka kika dawo ko? Daga mijinki sai mijinki?"

Dariya ta fashe da ita ta wani girgiza kai tamkar suna ganin juna ta ce.

"Kai Yaa Na'ima wannan sharri ne kawai kike min idan ba shi ba wacce ke school a Abuja miji na Lagos a ina ta ganshi?"

"Ni dai ai na yi shiru,amma duk su Yaa Amina shaida ne yanzu duk kin share kowa kin kama mijinki..."

"Yaa Na'ima ya buki?"

"Lafiya lau buki ana ta gwarama."

"To Allah yasa albarka. Ina My son?"

"Ga shi nan ya yi bacci, tun ɗazu ma yana wurin Ammie sai da za su wuce ta kawo min shi..."

"To ke kina ina?"

"Ina gidan Baba, bai jima ba da suka wuce ita da Yaa Amina, kin san gobe ɗaurin aure shi ne Ammie ta ce na zauna a nan kinsan halin su abun laifi baya kaɗan gare su."

"Uhm! Haka ne, Allah yasa a watse lafiya."

"Amin."

"Mu ma dai muna nan muna shirye-shirye, 7days suka rage ayi taron ƙaddamar da sabbin ma'aikatansu da suka horar wanda shi ne Jagora..."

"Shi wa?"

Wani wawwara ido ta yi kamar tana ganin ta sannan ta ce.

"Yaa Na'ima bana son wulakanci. Mijina Maheer nake magana..."

"Iyyehhhh..."

Dariya Anaam ɗin ta yi ta ce.

"Ah to naga ai rashin kunyar da kike so ki ji na yi kenan."

"Hmm! Tau ya yi,Allah ya nuna mana rai da Lafiya."

"Amin. Wai yaushe za ki koma gidan Dr. Haisam Yaa Na'ima?"

Wata dariyar ta yi ta ce.

"Sai na gama wanka.."

"Wallahy Yaa Na'ima ki ji tsoron Allah, tau ya yi."

Tana gama fadar haka ta yanke kiran wanda a daidai lokacin ne Rabi'a ta turo ɗakin ta shigo hannayenta ɗauke da kula da wani kofi.

Komai ba ta ce mata ba har ta zauna ta buɗe kula ɗin wanda lokaci ɗaya ƙamshin Kazar Magani ya daki hancin Na'ima ta girgiza kai ta ce.

"Duk ba wannan ba Rabi'a. Ke dai ki yi addu'a Allah ya haɗa hankalinku wuri ɗaya ya baku zaman lafiya..."

Ɗan ɓata rai ta yi sannan ta zame hannun ta ta kalli Na'imar ta ce.

"Yaa Na'ima baki son zaman lafiya a rayuwa, tun da na shigo ɗakin nan ban ce miki komai ba, saboda haka ki zuba ido ki kalle ni. Kuma in sha Allahu mugun fatan ki babu abinda zai mini, yanda kike zaune lafiya da mijinki cikin rayuwar jin daɗi ke da Anaam ni ma haka zan zauna. Itama da take da baƙin tabo kuma ta samu miji take jindadi ballantana ni da nake ɗanyata shakaf..."

Miƙewa Na'ima ta yi ta saɓa Khalifah a kafaɗanta ta fice ta bar mata ɗakin. Tabbas ba don ta ɗaukarwa Ammie alƙawari ba wallahy da babu abinda zai hana ta faffasa mata baki akan wannan magana da ta yi, amma barin ɗaki shi ne masalaha domin idan ta tsaya komai na iya faruwa.

******

Hajiya Salamatu kwana ta yi tana neman Layin Faris amma ba ta samu ba, koda ta kira Layin Hajiya Luba kuma sai ta sanar da ita cewa itama gabaɗaya a ranar bata sanya shi a ido ba.

Shi kuma Faris ɗin daman yana gidan Alhaji Ridwan dake Gada biyu tare da ɗansa Raihan wanda dawowar sa daga kenan daga Birnin Sin.

Duk abubuwan nan da ake har yau iyalansa basa ƙasar suna China wanda sai dai shi ya zo ya yi abinda zai yi ya koma duk abinda ya faru sai dai su yi ta Waya.

Raihan ɗin ma abokin Faris ne tun yaranta hakan yasa ya biyo mahaifin nasa suka taho wurin hidimar.

A tare suka shirya har Alhaji Ridwan ɗin misalin ƙarfe sha ɗaya na safe suka wuce gidan Alhaji Mas'ood dake Damɓa inda a can ne za'a ɗaura auren Rabi'a.

Suna zuwa ba ɓata lokaci aka hau shirye-shirye sha biyu na rana na bugawa aka ɗaura auren na su.

Kowa sai murna yake yana taya shi murna amma shi sam ya ma kasa gane a wanne hali yake. Wani lokacin sai ya riƙa jin kamar ma ya haƙura da auren domin duk abinda iyayenka suka ce basa ciki ai bashi da daɗi. To a yanxun ma haka yake ji, ji yake gabaɗaya komai ya fice daga kansa.

Sai da aka kambala komai Alhaji Ridwan ya kwashe mutane a matsayin sa na uban ango suka wuce gidansa aka ci abinci aka yi komai gwanin burgewa.

Bayan mutane sun rage sosai Faris ya koma gefe ya kira mahaifiyarsa jiki a sanyaye ya gaishe da ita. Shiru suka yi na ɗan lokaci sannan daga karshe ta ce.

"Faris dai da ka yi auren nan ko? Tun jiya ya kamata ace ko ni ka kirani munyi magana amma ka mayar damu tamkar waɗanda ba su da wani amfani a gareka..."

"Mum please ki yi min addu'a ki yi min fatan alheri dan Allah..."

"Shi ke nan! Allah yasa albarka."

Lumshe idanunsa ya yi a hankali yana mai jin wani sanyi ya ce.

"Amin Mum. Ina Daddy?"

"Tun daren jiya yace na nemoka a waya duk inda kake ka zo amma kuma sai ban sameka ba, saboda haka ka zo yana neman ka."

"In sha Allahu zan zo."

******

Maheer ne tsaye a ɗakin Grandpa ɗinsa wanda ke kwance da oxygen mask a fuskansa.

Daman tun daren jiya ne Maami ta kira sa tana kuka sanar masa cewa jikin Abiyh ya sake ta shi. Hakan yasa ya kwantar mata da hankalin ta tare da bata assurance cewa idan gari ya waye zai zo.

A waya ya sanarwa Anaam cewa zai je amsa kiran gaggawa a ofishin su dake Oman wanda zai iya spending 2days kafin ya dawo. Da haka suka yi sallama ya wuce wanda koda ya shiga gidan gabaɗaya kowa ya yi tsit kamar ba kowa.

Yana gama gaishe da su Uncle Ameed ya wuce inda mahaifiyarsa ke tsaye kusa da window tana kallon waje.

Sosai yanayinta ya bashi tausayi domin yasan cewa tana going through alot kasancewar ta rasa Mijinta na tsawon lokaci sannan yanzu tana tsoron ta rasa mahaifinta wanda ya kasance bangon jinginar ta.

"Maheer baya gane kowa a yanzu..."

Ta kowa ya yi a hankali ya yi hugging ɗinta cike da tausayi ya ce.

"He will be fine Maami, mu ci gaba da yi masa addu'a babu abinda zai same sa..."

Wasu sabbin hawaye ne suka sake zubo mata a hankali ta girgiza kanta ta ce.

"Idan na rasa Abiyh ina zan kama Maheer?"

"Maami please ki daina faɗin hakan,.."

Wani raunataccen kallon ta bi shi da shi sannan a hankali ta ce.

"Ina so ka kasance a kusa dani,wannan nisan da ka yi dani yana cutar da ni Maheer...aikinka kake ni kuma uwa ce kawai mai son kasancewa a tare da ɗanta a kowane lokaci. Please ka yi min alƙawarin cewa ba za ka sake karɓan aiki irin wannan ba...Ina so ka yi aure,idan ka yi aure ka haihu ko baka nan atleast idan matar ka tana a kusa dani da grandchild ɗina zan ji sauƙi sosai..."

Wani irin abu ne ya ga ya wuce masa akan idonsa mai tsananin duhu wanda ya sanya shi runtse idanunsa ba tare da ya shirya ba. Sosai zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfi jin kalaman ta da suka kasance barazana da tashin hankali a cikin rayuwarsa.

Janyewa ya yi a hankali ya yi excusing kansa ya taka ya wuce ɗakin Naana ya kwanta a gadon ta domin ji ya yi lokaci ɗaya wani irin mugun zazzaɓi ya lulluɓe shi.

Mi zai yi ya samu ƙwarin gwiwa har ya iya faɗawa Maami cewa shi yanzu mijin aure ne yana da mata a tare da shi? Ta ina zai fara yi mata bayani ta yanda zai gamsar da ita har ta yarda da shi. Tsoro ne fal yake gani a cikin idanunta saboda bata so ta rasa mahaifinta and shi ma duk ganin take kamar ta rasa shi. Hakan yasa take ganin kamar idan ya yi aure komai zai dawo yanda take muradi.

"Maheer..."

Ya ji Naana ta kira sunansa.

Miƙewa ya yi ya zauna a hankali tana ci gaba da kallonshi ta ce.

"Are you sick?"

Girgixa kansa ya yi ya ce.

"No Naana kin san wurin aikina a yanxu is too stressful shiyasa nake Ji na sai a hankali."

"Okay to, ka fito a sama maka wani abun, kaman ma Sabiƙa tana kitchen, ask her to make something for you."

Yana fita ya zarce gidan Maami bai ko bi ta kan abincin da Naanar ta yi magana ba kawai ya ciro wayarsa ya kira Anaam. Cikin lokaci ƙanƙani ta mantar da shi damuwar sa suka sha love ɗin su sannan ya Kashe ya shiga wanka ya fito ya shirya ya sake komawa gidan.

******

Suna dumfaro ƙofar gidan yace Raihan ya ajiyesa ya tafi idan ya gama zai kira shi a waya.

Bai san dalilin kiran sa da mahaifin nasa ya ce yana yi ba, but hankalinsa a matuƙar tashe yake.

Gidan tsit babu komai kamar ba auren ɗan su ɗaya tilo ake ba wanda bayan shi ba su da wani ɗan.

A harabar gidan ya tarar da shi zaune akan doguwar kujerar hutawa yana zaune riƙe da wayarsa a hannunsa.

Duƙawa yaje yi da nufin gaishe da shi but sai ya miƙe tsaye tare da ɗaga masa hannu alamar ya dakata.

"Tsaya a yanda kake? Ba na son gaisuwarka domin ba ta da wani amfani a gare ni.."

Tsaye Faris ɗin ya yi tare da zuba idanu yana kallon sa kurum ba tare da yace komai ba.

"Kasan dalilin kiranka?"

Girgixa kansa ya yi ya ce.

"No..."

Hannu ya miƙo masa ya ce.

"Na ji duk labarin yanda ka wulaƙantar min da dukiya ka yi son ranka. Tambaya ɗaya nike da ita zuwa gareka. Shin lokacin da na sha wahala na nemi dukiya ta tare da kai na neme ta?"

Girgixa kansa yayi ya ce.

"A'a..."

"To ina so indai kai kana da zuciya kuma kai ɗin nan ba shege bane ka dawo min da duk abinda yake nawa ne, kamar yanda nasha wahala na tara tunda har kace ban isa da kai ba to kai ma kaje ka nemi kuɗin daga baya sai ka yi yanda kake so."

A wani irin gigice ya shiga kallon mahaifin nasa jin wasu irin kalamai waɗanda ko a mafarki bai yi tsamnanin cewa za su iya fitowa daga bakin sa ba.

" Ka tsaya kana wani kallo na! Duk abinda kasan nawa ne da dukiya ta ka yi shi ban yafe ba ka yi amfani da shi, idan har kana da zuciya a ƙirjinka duk abinda yake nawa ne ka dawo min da shi kaje ka nemi naka kaman yanda na yi. Sannan a tunanin ka wai zan ji wani abu don ka auri jinin Mas'ood Galadima? Babu abinda nake ji sai tsantsar nadamar haihuwar ka da na yi, domin ba ta mini rana ba... "

Idanunsa har suna rufewa tsabar baƙin ciki haka ya fice daga gidan a gigice ya je ya ta tari abun hawa ya je sabon gidan da za'a kai Rabi'a ya kulle gidan gabaɗaya ya ɗauko Keys sannan ya wuce ya ɗauko motar sa ya dawo gidan, a bakin gate ya tsaya ya yi masa transfer na dukkan kuɗinda yasan cewa suna da alaƙa da mahaifin nasa sannan ya kira Rabi'a wacce ke can tana ta shirin zuwa gidan miji yace ta dawo mai da 5M ɗinnan da ya tura mata yana jiran ta shaf-shaf, ita kuma ba tare da ta kawo komai a ranta ba ta tura mai sannan ta ci gaba da abunda take.

Yana kambalawa ya shiga gidan ya wuce ɗakinsa ya tattara duk wasu document da yasan suna da alaƙa da baban nasa. Yana cikin birkice ɗakin Hajiya Salamatu ta shigo hankalinta a tashe ta shiga tambayan shi abinda yake faruwa.

Komai bai ce mata sai da ya gama haɗa komai sannan ya kalle ta cikin tsananin ɓacin rai ya ce.

"Mijinki ya ce ya yanke duk wata alaƙa dani, to ki ji Mum me too as well bani da wata alaƙa da shi. Ya ce wai shi ne wanda ya nemu kuɗinsa bayan yasan cewa na kwashe shekaru ana neman kuɗin da ni nima..."

"Faris!! Faris...."

Fuu haka ya fice ya je ya tarar da shi zaune a parlour ya ajiye komai akan center table ya ce.

"Ba zan yi mamaki ba domin ba ni na na farko da ka taɓa butulcewa ba, amma kuma abun da tsoro sosai ace har ɗan cikin ka za ka iya butulce masa Daddy."

Maimuna wuri ta samu ta laɓe domin tsoro ya gama kamata gabaɗaya, idan har ta bari ta haɗa fuska da shi to tabbas zai iya karya ta ganin irin wutar balbalin bala'i dake tafasa a cikin idanunsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull