Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 47

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 47

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 47: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 47. "To sai ka tashi Alhaji. Ga Faris can ya shigo yana ta faɗin…

3,369 words

"To sai ka tashi Alhaji. Ga Faris can ya shigo yana ta faɗin maganganu marasa daɗi yana zaginka yana faɗin wai kai baka isa ka hana ya auri wacce yake so ba, ko kamawa ta yi ya yanke alaƙa da kai zai yi hakan matuƙar barunsa zai cika. Sai wasu irin maganganu yake babu daɗin ji.."

A ƙufule ya ce.

"Waɗan ne irin maganganu ne yake faɗi Maimuna? Don Allah ki faɗamin.."

"A'a Alhaji. Wace ni ace na haɗa ka da iyalinka. Yana nan a main parlour kaje ka jiyewa kunnenka."

Zuruf haka ya diro tare da janyo jalabiyarsa ya zura ko takalmi bai saka ba ya fito.

Ta bayansa Faris ya jiyo taratsin Daddyn nasa tamkar zai tayar da gidan yana masifa yana ƙarawa yana faɗin.

" Faris ni za ka kunyata? Ni za ka nunawa duniya cewa ban isa ba? Shi ne kaje ka saka wasu waɗanda ban haɗa komai da su ba akan su shige gaba wurin nema maka aure?"

Lumshe idanun sa ya yi ya buɗe a hankali sannan ya girgiza kai ya ce.

"Daddy..."

Hannu ya ɗaga masa da sauri yace.

"Ka yi min shiru! Bana son jin komai daga gareka. Ka janye maganar Auren Rabi'a ka je gidan Alhaji Hamza Salmu 'ƴar sa na nan Ruƙayya yace ya baka ita..."

"I'm sorry to say Daddy....Ni ba ita nake so ba Rabi'a nake so."

"Haka ka ce Farisu?"

"I'm sorry Daddy.."

"Shi ke nan! Shi ke nan Farisu kaje tunda ɗiyar maƙiyana ka zaɓa kaje babu ni babu kai har abada, ka manta cewa ka taɓa sanina a matsayin mahaifi a rayuwar ka..."

Hannu Hajiya Salamatu ta ɗora aka ta fashe da wani irin kuka tace.

"Wayyo Allah ni Salamatu na shiga uku na lallace! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Alhaji miyasa za ka biye shi dan Allah?"

Cikin fushi ya wani kalle ta yace.

"Hajiya Salamatu idan kika sake kiran ko sunan Faris a cikin gidan nan wallahy tallahy a bakin aurenki kin ji na rantse...ya tashi bar min gidana."

Hannun Faris ɗin ta riƙo a gigice ta ce.

"Wai kai Faris wace irin zuciya ce take cikin ƙirjinka? Yarinyar nan tunda ba 'ƴar gwal bace ka haƙura mana kaje ka nemi Ruƙayya. Faris kana iya canja mata amma ba za ka iya canja mahaifi ba. Don Allah na roƙeka ka daina duk wannan..."

Fisge hannunsa ya yi ya miƙe kawai ya fice daga gidan.

Komawa tayi daɓas akan kujera ta zauna ta ci gaba da rusa kuka yayin da Maimuna ta shiga ba ta wani haƙurin gulma amma can ƙasan ranta farin ciki ne kamar ya kashe ta.

Tana ganin Alhaji Gimban ya koma ciki ta zauna a gefenta tare da ɗora hannun ta a Kafaɗanta murya a ƙasa ta ce.

"Hajiya kiyi haƙuri, in sha Allahu wannan duk zai wuce. Kin san mu yaran zamanin nan idan muka kafe, amma don Allah ki kwantar da hankalinki tunda Rabi'ar ita yake so ki bar shi ya aure ta, Alhaji in sha Allahu zai sauko, kema kin san ba zai iya rayuwa idan babu Faris ba..."

Haka dai ta yi ta ba ta magana kaman da gaske har ta samu taji zuciyarta ta yi sanyi. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 56*

Faris na fita daga gidan ya zarce gidan Ƙanwar mahaifiyarsa Hajiya Luba dake unguwar Gwarza.

Yana shiga parlournta ya zauna daɓas tare da saka hannayensa ya dafe kansa dake matuƙar sara masa. Gabaɗaya ya daina samun isasshen bacci a 'yan kwanakin nan. Tunani da damuwa su ne suka taru suka yi wa zuciyarsa yawa.

Duk wannan halin da yake ciki da Daddy zai haƙura da kowace damuwarsa za ta gushe. Ana ango haka? Ango ba farin ciki? Ba ɗoki ba komai tsaban stress!

"Faris..."

Hajiya Luban ta faɗa tare da samun wuri ta zauna tana kallon shi.

Ɗagowa ya yi ya kalle ta muryar nan a raunane ya ce.

"Hajiya ina kwana?"

"Lafiya lau. Hajiya Salamatu ta kirani yanzu ba jimawa akan maganar auren nan naka. Faris ka haƙura da wannan yarinyar dan Allah, gabaɗaya gidanku ya hargitse saboda wannan..."

"Hajiya ba zan haƙura ba. Ba wai Daddy yana ƙin yarinyar nan ne saboda tana da wani aibu ba, kawai yana ƙinta ne saboda takun saƙar da ke tsakaninsa da ƙanin mahaifinta."

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce.

"Shi ke nan. Allah yasa albarka ya daidaita tsakaninku. Mahaifin na ka ne wani irin bahagon mutum Faris. Amma duk da yake haka yi masa biyayya ya zame maka wajibi ya zame maka tilas."

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Na sani Hajiya, ina nan ina iya ƙoƙarina, but ba zan fasa auren Rabi'a ba saboda ba Allah na saɓawa ba. Na san halin sa In sha Allahu zai sauko daga baya."

"To Allah yasa."

"Amin. Daman So nake ku haɗu da su Gaggo Hadiza ku kai kayan Lefen Rabi'a ko zuwa jibi ne."

"Masha Allah! Allah ya kai mu rai da lafiya."

"Amin. Ina sisto?"

"Nabila ta fita wurin aiki tun ɗazu, Nasir kuma yana nan yana bacci indai ba yanxu ya fita ba."

"Okay. Akwai abinci?"

"akwai. Amma dai ɗumamen tuwo ne yau Nabila shi kaɗai tayi mana ta tafiyanta."

Murmushi ya yi kaɗan sannan ya ce.

"Itama sisto idan ta tashi wani lokacin baƙin hali ne da ita. A zubo mun hajiya amma ki saka min man shanu sai ki sako spoon."

Dariya ta yi ta ce.

"Nabila fa itama ta iya. Tana nan ta kawo wani kwanan nan har Alhaji yace ya turo iyayensa..."

Fira suka sha sosai wanda sai kusan ƙarfe biyu na rana ya bar gidan daga nan ya wuce Bunguɗu wurin dangin mahaifinsa.

*******

Yau tsawon kwanaki biyar kenan da tafiyarsa. Kowace safiya sai ya kirata kusan sau biyu ko sau uku kafin ta fita lectures, idan tana can ma sai ya kira, idan ta dawo ma haka.

Yau ma zaune take a table reading ɗinta misalin ƙarfe goma na dare tana karatu. Karatun take amma zuciyarta na can tayi nisa da tunaninsa, duk bayan mintuna sai ta janyo wayarta ta duba ta gani wai ko ya kirata ba ta ji ba, amma har yanzu bai kira ba and Kuma bai yi mata text ba. To ko dai baya nan? Ko kuma yana can yana wani aikin?

Tambayar da ta yi ta yiwa kanta kenan wanda daga ƙarshe ta ɗora kanta a table ɗin bayan ta ƙara rage hasken table lamp ɗin.

Ɗago kanta ta yi da sauri jin kaman ƙamshinsa na shiga ƙofofin hancin ta wanda take jin kaman yana tsaye yana kallonta.

Tsaye yake ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallonta. Sake ware idanun ta yi da kyau ta kalle shi domin ta tabbatar cewa shin gizau ne yake yi mata ko kuma dai shi ɗin ne ya dawo? Mutumin da ya ce mata zai yi 2weeks, how comes za'a ce Kuma shi ne yanzu tsaye a gabanta?

"Ko na koma ne?"

Ta ji ya faɗa cikin muryar nan tasa mai kashe mata jiki tana hautsina tunaninta.

Ware hannayensa ya yi alamar ta zo sai kuwa ta miƙe a hankali taje ta shige jikin sa.

Rungume shi ta yi ƙam tare da goga fuskar ta akan ƙirjinshi a hankali ta sauke ajiyan zuciya har da wani lumshe idanu tana jin wata irin nutsuwa na ƙara saukar mata.

"I miss you..."

Ta ji ya raɗa mata a kunne yana mai ƙara riketa da kyau a jikinsa. Fuskarsa ya sa gefen wuyan ta a hankali ya gangaro zuwa fuskar ta inda ya yi kissing gefen chicks ɗinta.

Sosai al'amarin ya sauya musu yanayinsu wanda hakan shi ya tabbatar musu da cewa sun yi missing Juna.

Jin kaman tsayuwa na neman ta gagare su musamman ga irin riƙon da ta yi masa ta shige jikinsa sai yake jin ƙafafuwansa ma ba za su iya ɗaukar shi ba.

Hakan yasa yaja ta a hankali suka wuce ɗakinta suka zauna shiru akan kujera na tsawon lokaci suna sauke numfashi mai cike da nutsuwa.

Ɗagowa ta yi ta kalle shi muryar nan can ƙasa sosai ta ce.

"Na sama maka wani abin ne?"

Girgiza kansa ya yi yana mai ƙara riƙe ta da kyau yace.

"No,I'm okay. Kewanki ce ta dameni ta hana zuciyata sukuni, for the whole 5days ɗin nan da ƙyar na iya daurewa domin ji nake kaman na rufe idona na ganki a kusa dani...are you feeling the same?"

Jinjina kanta ta yi yayin da ta sauke idanunta ƙasa tana mai jin yanda zuciyarta ke wani irin bugawa da ƙarfi. Da gaske yake matsayinta har ya kai haka? Ya fa kirata ɗaxu misalin magrib. Da gaske ya baro aikin nan nasa saboda kawai ya yi kewanta?

" Ya naga fuskanki ta nuna kaman baki gasgata kalamai na ba?"

Saurin girgiza kanta ta yi ta ce.

"A'a."

Ƙara matso da fuskarsa ya yi kusa da ta ta ya ƙara saukar da muryarsa sosai ya ce.

"Do you miss me? Tell me."

Tana jin ya ƙara riƙota sosai ya matso ta ta yi saurin jinjina kanta cike da jin kunya ta ce.

"I do..."

"How?"

Shiru tayi tare da ƙara kawar da idon ta daga kallon shi domin ta ma rasa miye abinda ya kamata ta yi.

Tana nan duk ta diririce ta ji saukar soft Lips ɗinsa akan nata a hankali ya yi kissing ɗinta lightly ya janye yana mai yi mata wani irin zazzafan kallo wanda ya gama nakasa masa zuciya ya ce.

"Kamar dai haka ko? Kamar haka kuma..."

Ya sake kai bakin sa gefen wuyan ta ya shiga kissing ɗinta zuwa tsakiyan boobs ɗinta har ya gangaro zuwa lips ɗinta.

Nan take dukkan ilahirin jikinta ya ɗauki ɓari ta shiga kakkarwa kaman za ta sume jin wani irin karatun da ya girmewa ƙwaƙwalwarta.

Hawaye ya ga sun gangaro daga idanunta ga shi jikinta sai ciccira yake duk ta wani bi ta ruɗe.

Hankalin sa ne ya tashi ganin yanayin da ta shiga lokaci ɗaya, hakan yasa a hankali ya ɗan ja baya kaɗan yana kallon idanunta dake rufe ya ce.

"Maryam..."

Buɗe idanun ta yi cike da tsoro ta kalle shi wanda hakan ya yi matuƙar karyar masa da zuciya. Miyasa za ta tsoro ta haka? Shi Mijinta ne, ba zai taɓa cutar da ita ba. Wan can ɗin ma ƙaddara ce wanda ya aikata mata kuskuren ne ba cikin hayyacinsa ba. Duk yanda yake ji a ransa har yau ya kasa kwatanta halin da ta kasance a wancan ranar, duk da cewa he's unaware akan yanayinta ya san cewa she went through alot Wanda duk ya tuna sai ya ji nadama ta shige shi.

Yanzu kuma yana so ya bata farin ciki, yana so ya bambanta mata tsakanin waccan mummunan ranar da wannan. Ita ɗin matar sa ce, har abada ba zai cutar da ita ba. Idan tace za ta riƙa jin tsoronsa hakan zai riƙa ƙona masa zuciya.

Neman zamewa da ya ji tana batun yi shi ne abinda ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga.

Ƙara riƙe ta ya yi yana kallon fuskar ta ya ce.

"Relaxed Maryam! Bakya so ne?"

Saukar da kanta kawai ta yi bata ce masa komai ba. Ganin hakan yasa ya kamo hannun ta a hankali ya yi twisting a na shi ya fara mata magana cikin zallar kulawa ya ce.

"Ba zan taɓa cutar da ke ba Maryam. Bana so kina jin tsoro na,ni ɗin nan mijinki ne, har abada ba zan bari wani abu ya same ki ba ki yarda dani..."

Girgiza kanta ta yi a hankali still da hawaye a idon ta ta ce.

"I'm sorry...but I'm just scared. Bab..bana so na ƙara rasa kai na a karo na biyu..."

"I will never let that to happen. Ba zan miki komai ba sai idan ke ce kika amince. Idan kuma hakan Shi ne zai riƙa ɗaga miki hankali to zamu zauna a haka kuma muci gaba da farin ciki. Ke nake so, farin cikin ki shi nake so."

Daga haka ya zame ta gefe ya tashi yaje ɗakin sa ya yi wanka ya shirya cikin kayan bacci sannan ya dawo inda ya tarar da ita har ta ƙundudune a Duvet. Murmushi kawai ya yi ya girgiza kansa sannan a hankali ya saka hannu ya janye Duvet ɗin ya kwanta tare da janyota jikin shi. Sosai kwanciya cikin jikin shi ke yi mata daɗi a yanzu, kwana biyun da baya nan idan ta kwanta sai ta daɗe ta na juyi akan gadon domin ji take gabaɗaya ya yi mata faɗi.

Kalamansa na yau sun ƙara kwantar mata da hankalinta, tabbas ya tabbatar mata da cewa shi ɗin na daban ne a cikin maza. Duk da cewa su Yaa Amina sun tabbatar mata cewa rayuwar auren da za ta yi da Mijinta ba su da nasaba da abinda ya faru da ita a baya, hakan bai sa ta daina jin tsoro ba, kuma yau da ta ji yana yi mata wani abun sai gabaɗaya hankalinta ya gushe. Tana jin tsoron sake komawa turkenta mai taɓo.

A haka dai har bacci ya yi nasarar sace ta wanda sai washe gari bayan ya dawo masallaci suka zauna ya kalleta ya ce.

"Jiya na dawo domin na ganki mu gaisa duk kin bi kin rikitar da ni Maryam..."

Murmushi tayi tana mai tuno abinda ya faru wanda ita kanta yanzu yake bata dariya ta ce.

"I'm sorry..."

Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya buɗe sannan ya ce.

"Is okay. Ya kike ya lectures?"

"Alhamdulillah. Ya aiki? Ya Lagos ɗin?"

"Alhamdulillah."

Kallon shi ta yi cike da fargaba ta ce.

"Yau za ka koma?"

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Eh, satar hanya fa na yi na tsero saboda kawai na ganki..."

Bata san lokacin da ta fashe da dariya ba tana wani kallon shi jin ya yi maganar kaman wani ƙaramin yaro.

"Mamaki kike ko? Zuciyana kasa daurewa ta yi, hakan yasa na gudo, tunda kuma na ganki yanzu in sha Allahu zan juya na koma."

Ganin yanda ta yi da fuskanta yasa ya ɗan matso ta kaɗan ya ce.

"Ko na tsaya?"

Saurin gyaɗa kanta ta yi alamar eh wanda har cikin zuciyarta take nufin hakan domin da gaske take tana so ta riƙa ganin sa a kusa da ita.

"Lokaci kaɗan ya rage na dawo a kusa dake kin ji ko? Kawai abinda nake so ki ci gaba da mayar da hankali akan karatun ki."

Jinjina kanta ta yi tace.

"In sha Allah."

*********

Yau koda suka wayi gari gidan Baba Salisu tinƙis yake da mutanen da Umma ta tara wurin tarbon lefen Rabi'a.

Gabaɗaya ta ruɗe ta gigice ganin irin lefen da Faris ɗin ya danƙarowa Rabi'ar kamar za'a buɗe shago.

Sai wani feleƙe take tana yaɓawa su Mummy Jamila habaici wanda su dariya ma ta ba su. Yayin da kuma ta bawa masu kawo lefe mamaki ganin ta a matsayin uwar Rabi'a kuma tana ta wannan rawar kan cike da rashin arziki.

Itama dai Maimuna dake gefe mamaki ne ya kusa sumar da ita ganin irin tsurar dukiya da aka narka tamkar ba'a san zafin ta ba. Ita da tasan wannan kayan takaicin za ta tarar wallahy babu abinda zai sa ta zo.

Ita a ɗan ƙaramin tunaninta tunda har Alhaji Gimba yace ba hannunsa a ciki ta ɗauka za ta ga kaya a wulaƙance, sai gashi ta haɗu da abinda ya bata mamaki.

Bayan su Shema'u sun gama ƙirge kaya ƙanwar mahaifinsa wato Hajiya Hadiza ta ciro tsabar kuɗi har dubu ɗari biyar ta bayar cewa kuɗin sa lalle da sauransu. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 57*

Maheer na kambala breakfast ya tattara ya koma Lagos ya barta da kewa.

Sosai sabuwar soyayya da wata irin shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. A Koda yaushe matuƙar dai yana free to suna nan maƙale a waya wanda ko yace taje ta ci gaba da karatu sai ta ce mishi ko ta yi bata ganewa sai idan yana a kusa da ita and semester ɗin ma ba ta yi nisa ba saboda haka sai zuwa gaba za ta fara karatu mai yawa.

Duk time ɗinda kuma yake da sarari saidai kawai ta ganshi a cikin gidan tamkar wani walƙiya. Ta sake da shi sosai a yanzu ba kaman can baya ba, sukan zauna su yi ta fira suna dariya wanda hakan yana faranta mata rai ba kaɗan ba. Ko ba komai tasan cewa a yanzu ta yi nasara domin ta dawo da hankalin Mijinta a kanta wanda a yanzu yake bata muhimmanci da lokaci fiye da komai a rayuwarsa.

A yanzu ma idan yazo sukan fita garin Abuja su shaƙato su dawo, wani zubin sukan biya gida ko gidan Yaa Muhammad duk da cewa baya ƙasar a yanxu ko kuma gidan Yaa Mukarram ko ma dai gidan Aunty Dina. Duk abinda yasan cewa idan ya yi shi zai ba ta farin ciki to baya ɓata lokaci wurin yi mata shi, soyayya yake mata ta musamman wanda a duk lokacin da ya tuna da Maaminsa sai ya ji hankalin sa ya tashi sosai. Allah ya sani ba zai iya rabuwa da Anaam ba a halin yanzu and again bai san yanda zai tunkari Maamin da maganar cewa wai ya yi aure kuma ya auri 'ƴar gidan Mas'ood Galadima.

Yanzu gabaɗaya ya daina haɗuwa da Hamad domin Hamad bashi da wani aiki sai na cusa masa baƙin ciki yana aibata auren na shi da har yanzu bai san wata mafita ba.

A haka suka ci gaba da tafiyar da rayuwa har auren Rabi'a ya rage saura 5days.

Tana zaune tare da Friendy a school cafeteria sai ga Kiran Ammie ya shigo wayanta.

Fuskar nan a sake ta yi mata sallama ta gaishe da ita sannan daga can ɓangaren Ammien ta ce.

"Kina class ne?"

Girgiza kanta ta yi tamkar tana a gabanta ta ce.

"A'a Ammie, muna school Cafe tare da Friendy tah."

"Okay, kina ji Anaam? Auren Rabi'a ne ya tashi, wanda nasan cewa kin san da zancen, saboda haka ina so ki nemi izinin mijinki idan yana da Lokaci ya kai ki, idan kuma babu lokaci sai Mubarak ya zo ya kai ki."

Shiru ta yi tana ɗan nazari na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta sauke ajiyan zuciya ta ce.

"Ammie kin san cewa yana Lagos, kuma yanxu aikinsa ya ninka sosai kasancewar wani assignment da yake kai, to kinga abubuwa sun yi masa yawa bana so na ƙara masa wani tension ɗin. Kawai ku je daga baya idan ya samu lokaci zan je na yi musu Allah ya sanya alheri... "

"Amma Anaam..."

"Ammie ko a lectures fa mun yi nisa sosai, saboda haka idan muka yi exams na samu hutu zan je."

Ajiyan Zuciya Ammie ta sauke a hankali sannan ta ce.

"Shikenan, Allah ya bada iko. mu zamu tafi gobe idan Allah ya kaimu..."

Wani irin ɓata fuska ta yi tamkar tana a gaban Ammien ta ce.

"But Ammie shi ne za ku tafi gobe gobe amma sai yau ake faɗamin?"

"To ki yi haƙuri kin san Rabi'ar tana nan dole ni zan je tare da ita ba za'a barta tabi hanya ita kaɗai ba kinsan amarya da tsautsayi."

"Allah ya tsare Ammie. Allah yasa ayi taro lafiya a watse lafiya, Allah ya basu zaman lafiya ya basu zuriya ɗayyaba.."

"Amin amin yah Allah, kema ina yi miki wannan addu'ar Anaam Allah ya baki 'ya' ya na gari masu albarka."

Dariya Friendy ta yi tana mai ajiye bottle water ɗinda ke hannun ta ta ce.

"Kin ƙara ƙiba kaɗan musamman a fuskanki, ga wannan goshin na ki sai wani ƙyalli yake da alama dai mun samu ƙaruwa..."

Bata san lokacin da ta fashe da wata dariya ba tana mai kallon Na'ima Hassan ɗin ta ce.

"Ina ga dai ƙawata akwai abinda kika sha yau da har yasa kike ganina a haka. Ƙaruwa dai? Uhm! Allah yasa mu da ce."

"To wannan amarcin da kuke gurxa ai ba wasa ba ne..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull