Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 46
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 46: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 46. "Welcome ma, I'm Kudirat Abdul-Haziz...I'm here to serve you, my…
3,345 words
"Welcome ma, I'm Kudirat Abdul-Haziz...I'm here to serve you, my work is all about kitchen.."
Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.
"Your welcome..I'm Maryam Mas'ood Galadima...Mrs. Mah..."
Saurin girgiza kanta ta yi da sauri tare da runtse idanun ta tamkar wacce ke filin gabatarwar da aka yi wa tilas ta ce.
"No...I'm Anaam. You can call me Anaam If you want. Kina jin Hausa?"
Jinjina kanta Kudirat ta yi ta ce.
"Ina ji Mah.."
"Okay...Mi kike a yanzu?"
Cike da respect ta ce.
"Waiting for you ma, to come and give me order for what to cook now..."
"kin karanci girke-girke ne ko kuma kawai kin tsinci kan ki kina yi saboda yau da gobe?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Yes ma, degree nayi a fannin girke-girke..."
"Wow...congratulations."
"Thank you ma."
Shiru Anaam ɗin ta yi na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta ce.
"While...you can go ahead ki yiwa Mijina breakfast mai daɗi, and please ki yi da wuri ki kambala because he's leaving and Kuma da wuri zai tafi..."
"Okay ma.."
Maimakon ta bar kitchen ɗin ba ta yi hakan ba, wata shiriritar ta shiga yi daban wanda tana yi tana murmushi jefi jefi kuma tana fira da Kudirat.
Aikinta kawai take amma kuma Idonta na can tana kallonta wanda ita kanta bata san miye Anaam ɗin take yi ba.
Bayan ta kambala ta shirya tray ta ɗauka kanta tana kallon Kudirat ɗin tace.
"Please ki hanzarta dan Allah kin ji"
Tana fitowa ta nufi dining table ta ajiye sannan ta taka ta shige ɗakinsa inda ta tarar da shi ya duƙar da kai yana ta rubuta da pen da tarin papers a gaban sa.
Ya ji shigowar ta amma kuma ƙamshinta shi ne abinda ya ja hankalinsa har ya ɗago ido babu shiri ya kalle ta.
Ya salam! Ya furta a ransa ganin irin shigar da ke jikinta wacce rigar ta yi shara shara kuma ba ta sauko mata zuwa ƙasa ba.
Hannunta ta kai a hankali ta zare Pen ɗin tare da yin murmushi ta ce.
"Good morning Mr. Busy..."
Janyota ya yi zuwa jikin shi wanda shi kanshi ba zai ce ga dalilin da yasa ya yi hakan ba.
Muryar shi ta yi very low as always ya ce.
"Good morning my bread and butter.."
Ido ta zaro alamar mamaki ta ce.
"what? Ni ce bread and butter ɗin?"
Hannunta ya riƙe ya sumbata yana murmushi ya ce.
"And why did you call me Mr. Busy?"
Turo baki ta yi gaba tace.
"I'm sorry..."
Ɗayan hannunsa ya kai ya shafo lips ɗin yana dariya ya ce.
"I'm sorry too. How are you?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"I'm good..."
Tana faɗin haka ta yi shiru na ɗan lokaci wanda akwai sauran abin da take so ta ce but jin kaman bai ji dadin kalmar Mr. Busy ɗinda ta kira shi ba yasa ta yi shiru, amma kuma ai miye shi ɗin idan ba Mr. Busyn ba? Always ba shi da wani aiki sai aikin Maritime, ba shi da lokacin kansa kullum dai aiki kullum aiki.
Kamar wanda yake magana da zuciyar ta haka ta ji ya bata amsar tambayar da take yi wa kanta ya ce.
"I'm sorry Maryam...ni na san cewa I haven't been fair to you dalilin wannan aikin nawa, but I promise you cewa daga zaran na kambala wannan assignment ɗin za mu samu kyakkyawan lokaci da juna. Wannan aikin ma da kika ga ina yi yanzu nasan cewa zan yi submitting na shi cikin kwanakin nan, but ban san cewa yau ake buƙatan shi ba sai da Chief Odev ya kira ni ɗazu...."
Lumshe idanunta ta yi zuciyarta cike da tausayinsa ta wani ɓangaren ta jinjina kanta ta ce.
"Ba komai, Allah ya taimaka ya bada sa'a. Allah ya ɗaukaka maka dukkan ayyukan ka ya tsare ka."
Shiru ya yi yana mai jin yanda kalaman ta ke ratsa zuciyarsa tare da sanya masa nutsuwa da jin cewa shi fa ya yi dacen mata domin ko daga yanayin kalaman ta za ka tabbatar cewa ta samu tarbiyya ingantacciyya.
Kiran wayar shi da akayi shi ne abinda ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga wanda yana duba screen ɗin yaga sunan Hamad ya yi rejecting tare da ajiye ta gefe ya kalle ta ya ce.
"Ya kamata na tafi domin na isa da wuri ko Maryam?"
Miƙewa ta yi daga jikin shi tana faɗin.
"Ka zo ka fara cin abincin tun da ka shirya kafin ka tafi."
Biye yake da ita tamkar wani raƙumi da alaka har suka iso wanda koda suka je har Kudirat ta gama shirya komai amma sai ta buɗe mishi tray ɗinda ta fara ajiyewa tana wani kalar murmushi ta ce.
"Bismillah..!"
"Thank you Maryam.."
Sai da ya ɗauki spoon Sannan idanuwansa suka sauka cikin plate ɗin wanda a ruɗe ya ɗago ya kalleta hankalinsa a tashe ya ce.
"Maryam what is this? Oh my God!..."
Dariya ta fashe da ita wacce ta bayyana masa fararen haƙoranta ta ce.
"Ba kace kai komai kana iya cin sa ba?"
Saurin girgiza kansa ya yi yana fadin.
"Oh no! Ba irin wannan ba..."
"Kai fa kace komai ci kake, ko baka ce ba?"
Ƙara kallon cikin plate ɗin ya yi hankalinsa a tashe ya ce.
"Wait...miye ma wannan ɗin kika yi mixing Haka?"
Still tana dariyar ta matso tana kallon cikin plate ɗin itama kamar yanda yake yi ta ce.
"Ba fa wani abu bane, kawai Sphagetti ce, with Beans, Indomie and Macaroni..."
Ƙara zaro ido ya yi tsaban mamaki ya ce.
"Oh God! Haba Maryam For goodnes..."
"Kuma tunda na sha wahala na girka sai ka cinye."
Kallonta yake sai kawai murmushi ya suɓuce masa.
"Ko kana nufin ba za ka ci ba?"
Yana murmushin ya jinjina mata kansa yana kallonta ya ce.
"Zan ci mana wane ni? Ai dole zan ci.."
Daga haka ya ɗauki Spoon ɗin a hankali ya tsakuro hannunsa har yana rawa zuciyarsa na masa wani iri ya kai spoon ɗin bakinsa.
Saurin riƙe spoon ɗin ta yi tare da zaro ido tace.
"Wai ci za ka yi?"
Yana murmushi ya ce.
"Eh mana! Ke ce fa kika dafa min domin farin ciki na..."
Dariya ta yi tare da saukar da spoon ɗin tana girgiza kai ta ce.
"Ni ba zan barka ka ci ba...ga wanda Kudirat ta girka."
Hannunta ya kamo ya sumbata yana mai wani irin farin ciki ya ce.
"Thank you Luv... Allah ya yi maki albarka ya bar mu tare har mutuwa."
"Amin amin."
Daga haka ta shiga serving ɗin shi wanda duk inda fuskanta ta yi idon shi yana kanta har ta kambala ta samu wuri ta zauna ta jira shi har sai da ya gama wanda bai wani ci sosai ba akan tsabar farin cikin da ta sanya shi, abinda ya faru yau har abada ba zai manta da shi ba a tunanin shi, because sun samu good time ɗinda bai taɓa sanin ko tunanin cewa zai faru ba.
Bayan ya kambala ya shiga ya shiryo itama ta shiga ta shirya cikin Abayah ta yafa veil ɗin ta fito ta rako shi har bakin mota.
Sai da ya saka Kayansa sannan ya waigo ya kalle ta yana jinjina kansa da murmushi muryaarsa a hankali ya ce.
"Thank you Maryam...thank you so much for making my day. I will miss you. I love you.."
Lumshe idanunta ta yi tana mai jin yanda kalmominsa ke ratsa ta masu neman zauta tunanin ta kawai ta ji ya janyo ta tare da jan hannayenta ya ɗora akan wuyan sa suna facing juna wanda hakan yasa ta buɗe ido ba shiri yana mata murmushi ya ce.
"Can I try something?"
Zuciyarta na wani irin pumping tamkar mai tsoron magana ta ce.
"Kamar na me?"
Ƙara matso da fuskarsa ya yi dab ta ta tare da ƙara riƙo waist ɗinta da kyau suna mai jin wani iri tamkar an saka igiyoyi an ɗauresu tsabar yanda zuciyoyinsu suke bugawa numfashinsu na gauraya da juna.
A hankali ya matso da lips ɗinsa Wanda hakan yasa ta lumshe idanunta tana mai jin tamkar ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukar ta ba tsabar yanda take ji kawai ta ji saukar lips ɗinsa akan cute lips ɗin nan na ta da ke matuƙar ɗauke hankalin sa ya haɗe bakinsu wuri ɗaya.
Wani irin shock suka ji lokaci ɗaya wanda ya sanyasu yin baya tamkar za su zube jin wani irin sabon yanayi da ya bugi ƙwaƙwalwarsu.
Wani irin abu ne, mai sanyi, daɗi da garɗi yake ratsa brain ɗinta tamkar zai zautar da ita.
Da ƙarfi ta saka hannayenta ta riƙe colar ɗinsa domin ji ta yi kamar ba za ta iya ci gaba da tsayuwa ba.
A hankali ya janye wanda a lokacin idanunsa har sun gama canja kala tsabar abinda yake ji na musamman yana harɓawa a ƙwaƙwalwarsa zuwa zuciyar sa.
Cikin wata irin muryar da ta ƙara rikita tunanin ta ta ji ya ambaci sunanta wanda ko shi daga ji kasan yana cikin wani irin yanayi ya ce.
"Diyanah..."
Sai yanzu ta buɗe idanunta tamkar mai tsoron kallon wani abu ta kalle shi ba tare da tace komai ba.
"I love you."
Ya furta mata, daga haka ya janye jikin sa ya shiga mota wanda sai a lokacin ya ji siririyar muryarta tamkar za ta yi kuka ta ce.
"When are you coming back?"
Buɗe motar ya yi ya fito ya riƙo hannunta sannan ya jingina jikin motan a hankali ya ce.
"I will spend only 2weeks kin ji ko? And Anasi will be taking you to school when ever you have lectures. Please ki kula min da kan ki kin ji?"
"Allah ya tsare..."
Daga haka ta juya kawai ta koma gida. Tafi awa a zaune wanda ta rasa abinda yake mata daɗi sannan ta janyo wayarta ta kira Yaa Na'ima murya a ƙasa suka gaisa sannan Na'ima cikin damuwa ta ce.
"Anaam...lafiyanki kuwa? Miye ya same ki na ji muryanki ya yi low? Are you sick?"
Lumshe idanunta ta yi a hankali ta ce.
"I'm fine Yaa Na'ima. Daman zan faɗa miki ne cewa na zo ina Abuja tun jiya..."
"Me? Lallai ma? Ina mijin na ki?"
Turo baki ta yi tamkar tana a gabanta ta ce.
"Ya koma yanzu.."
Wata irin dariya Na'ima ta fashe da Ita sannan ta ce.
"Lallai ma Anaam ɗin nan! Kin zo Abuja tun jiya baki sanar mana ba, kina nan kina ta shan love da miji, yanzu ya koma shi ne kika kirani kina min fushi...."
Cikin jin wasu irin hawaye ta ce.
"To ni dai kawai Yaa Na'ima idan ba za ki zo ki ganni ba sai ki faɗamin in cire rai..."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 55*
Katse kiran ta yi jin da gaske Yaa Na'ima neman ƙara mata zafi take akan wanda take ci sannan ta kai hannu kan lips ɗinta tana shafawa a hankali abinda ya faru a tsakaninsu na ƙara dawo wa a ƙwaƙwalwarta. Haƙiƙa wannan abin ya shige ta ba ka ɗan ba. Ji ta yi gabaɗaya duniyar na juyawa da ita.
Daga jiya zuwa yau abubuwa da yawa sun faru waɗanda suka bata mamaki kuma suka sanyata jin cewa Maheer wani mutum ne na daban. He's very gentle and nice also.
Kamar yanda yace yana sonta tabbas itama a yau soyayya ta ke ji, soyayya take jin tana yi masa ta musamman. Yanayin da take ciki daga jiya zuwa yau ta tabbatar mata da cewa yafiye mata lokutan baya farin ciki wanda take ji a ranta cewa ina ma ace lokaci ya tabbatar da su haka? But hakan tasan cewa ba zai faru ba because yanayin aikin nan nasa yana ɓata mata rai a halin yanzu.
Wani tunanin na daban kuma zuciyarta ta ɗarsa mata na cewa ko yana ina a yanxu? Miye yake yi? Oho!
Tana nan tana ta tunani iri-iri ƙarshe taje ta kunna TV ta zauna tana kallo ko za ta samu ya rage mata kewar da ke damun zuciyar ta.
Tana nan har sai da lokacin sallah ya yi sannan ta tashi ta shige ta yi sallah. Tana kambalawa kiran Friendy ɗinta ya shigo wayanta. Tana ɗagawa ta ce mata tana bakin gata. Da kanta taje ta shigo da ita Na'ima Hassan sai santin ta take tana cewa ta canja sosai ta yi kyau.
Suna shiga Friendy ɗin ta kalle ta ta ce.
"Result Alhamdulillah! Have you checked yours?"
Dariya ta yi ta girgiza kanta ta ce.
"Ina fa,ba abin da na duba, har Yaa Mubarak nace ya karɓi details ɗina ya dubamin yace ba zai yi ba kinsan halin sa..."
"Bari mu dub..."
Saurin dakatar da ita ta yi ta ce.
"No! Kada ina zaune zaman jindadina ki ɗaga min hankali..."
"Wane irin ɗaga miki hankali nima fa na duba."
"To ke kika ce, ai ke kinsan abinda kikayi to ni fa?"
Jinjina kai friendy ta yi ta ce.
"In sha Allahu ma you made it, I trust you."
Wata dariyar Anaam ta yi sai kuma ta ja hannun ta ta ce.
"You trust who? Abeg zo muje mu ci abinci muyi firarmu, bana son zancen school ki bari sai jibi idan mun koma. Ya Mum da Pa?"
"Lafiya lau suke Alhamdulillah, sun ce in gaishe da ki."
"Allah sarki na gode. Ina samarin ki?"
Taɓe baki ta yi ta ce.
"Babu, kema kin san ba bu.."
"Uhm! Wai ke haka za ki yi ta zama?"
"Noo! Ba haka bane, ban isa dai yanzu a 100level ba in kai wani gidanmu, Pa zai kashe ni ina faɗa miki, but zuwa 300level to 400level wannan duk zan iya ya yi."
"OK, Allah Ubangiji ya baki nagari amin. Ni ma fa ƙa'idan Abbah a can baya ba zai aurar damu ba sai mun gama degree, to sai gashi kana naka Allah yana shi, sai ga ƙaddararmu ta sauya daga ni har Yaa Na'ima..."
Firar su suka sha har zuwa ƙarfe biyar sannan drivernta ya dawo ya ɗauke ta suka tafi.
Tana nan ta cika ta batse akan rashin zuwan su Yaa Na'ima kawai ta ji sallamansu. Koda ta fito kamar daga sama ta ga Abbah, Ammie, Yaa Mukarram da matar shi da yaran su, Yaa Amina, Yaa Na'ima, Sannan kuma da Rabi'a.
Cikin ihun murna taje ta maƙalƙale Abbah tana dariya tace.
"Welcome all...welcome...Abbah.."
Muryarsa ta ji yana faɗin.
"Anaam kada fa ki ƙalla min wuyana.."
Dariya suka fashe da ita sannan ta sauka ta shiga gaishe su ɗaya bayan ɗaya, da ta kai ga Rabia ta ce.
"Welcome...ashe kin dawo?"
"eh, sannu da zuwa, an ce kema jiya kika dawo?"
"yeah..."
Parlour ta kai su sannan ta kira Kudirat ta ce ta kawo musu ruwa da komai sannan ta shirya musu abinci. Kallon ta Abbah ya yi ya ce.
"Maryam na ji kina cewa a shirya abinci, yanzu fa za mu koma..."
Wani irin marairaice fuska ta yi ta ce.
"Kai Abbah dan Allah..! Gaskiya kuna nan sai kunci abinci sannan, ai baku taɓa cin abincin gidana na... Ammie dan Allah ki ce ya tsaya kada ya tafi."
Dariya suka fashe da ita sannan Ammien ta ce.
"Muna nan Auta sai mun ci abinci kin ji ko? Ina mijin ki?"
Kallon Yaa Na'ima ta yi sai kuma ta sake kallon Ammie ta ce.
"Ya koma ɗazu da safe."
"okay. Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Amin amin."
Fira suka sha wanda saida suka ci abinci sannan suka tashi zuwa salloli, a ɗakin da ta kai su Yaa Amina ta tsaya ta yi sallah inda a nan Rabi'a ganin babu wanda ya yi zancen aurenta har suna batun tafiya sai ta ciro IV daga bag ɗinta ta miƙawa Anaam ɗin tana faɗin.
"Kamar baki san da zancen aurena ba ko? Ga kati, saura 2weeks yanzu.."
Hannu Anaam ta saka ta karɓa ba tare da tace komai ba.
"Kina da labarin cewa Faris zan aura? Ɗazu ma ya tura min 5M domin na fara business idan mun yi aure kin san Baba ya hanani karatu..."
Idon ta ta ɗauke daga katin ta zuba su tana kallonta kamar yanda su Yaa Amina su ma suka shiga kallonta cike da tsantsar mamaki da al'ajabi.
Ganin kaman zancen ya ɗan girgiza su yasa ta saki wani murmushi cike da gadara ta yi wani war-war da ido tace.
"Yaa Amina shin duk kuma baku da labari ko? Wallahy ɗazun nan ya turo min su. Lefena ma yana hanya."
"Allah ya sanya alkairi..."
Abinda Anaam ɗin tace kenan tare da miƙa mata Invitation Card ɗinta.
"Sai naga kaman baki yi farin ciki da wannan labarin ba Anaam..."
Wata irin tsawa ce Na'ima ta daka mata tare da yi mata wani kallo cike da takaici ta ce.
"Wai Rabi'a miye haka? Wane irin iskanci ne wannan?"
Itama Yaa Amina girgiza kanta ta yi ta ce.
"Rabi'a bakya son zaman lafiya a rayuwa. Ta ya za ki iske mata har cikin gidanta kice za ki ci mata fuska."
Aunty Aysha ta karɓe da cewa.
"To miye ma zai sa Anaam ta nuna rashin jindadi tun da ba saurayinta ba ne, abu ɗaya zai sa in yarda da zancen ki shi ne za ki auri ɗan mutumin da baya son iyayenki yake neman ganin bayan su...mutumin da ya sace yayanki, ya cutar da 'ƴar uwarki da ahlinki ai dole ta yi baƙin cikin za ki aure shi..."
Turo ba ki ta yi tana mai jin haushin kalaman Aunty Aysha ta ce.
"Aunty Aysha baku da wata hujja akan hak..."
Ji ka yi Tas! Na'ima ta ɗauke ta da kari wanda sai da ta bawa kowa mamaki a ɗakin sannan ta ce.
"Waye za ki yi wa rashin kunya a nan wanda yake tsaran ki?"
Girgiza kai Anaam ta yi ta ce.
"Ai da ba ki mare ta ba Yaa Na'ima. Ki bar ta indai surukuta da Alhaji Gimba ne za ta gani ga ƙwaryar shanta.."
Tana dafe da kunce ta cika ta batse tamkar za ta fashe ta ce.
"In ga Alheri wallahy. Kuma wallahy Yaa Na'ima wannan ya zama shi ne na ƙarshe domin wallahy idan kika sake marina daga yau zan baki mamaki."
Daga haka ta wuce ta fice gabaɗaya taje jikin mota ta tsaya, daman Abbah yace daga sun gama sallah za su wuce.
Ajiyan zuciya mai ƙarfi Na'ima ta sauke sannan ta ce.
"Rabi'a har abada ba za ta yi hankali ba..."
Yaa Amina ta ce.
"Namiji ne kuwa zai gyara mata zama."
Khalipah Anaam ta saɓa a Kafaɗanta suka fito suka tarar da su Ammie daga nan ta rakosu har bakin mota cike da kewa ta yi musu sallama. Babu wanda ya koma kan Rabi'a har suka bar gidan.
******
Cikin azama Hajiya Salamatu ta fito parlour inda Ramatu mai aikin ta tace Faris ya shigo yana can zaune a parlour ya ce ta zo.
Wani kallon ta bishi da shi na tsawon lokaci wanda shi ko a jikinsa. Bayan ta gama kallon shi da kyau ta gane shi ɗin ne dai ba wani ba kawai ta hau shi da masifa abinda bata saba yi ba. Faɗa sosai ta yi mai sannan daga ƙarshe ta ce.
"Ni ma na goyi bayan mahaifinka ba za ka auri Rabi'a ba..."
Hankalinsa a kwance ya kalle ta yana girgiza kai ya ce.
"Mum ki daina biye mijinki. Yanzu dan Allah time ɗinda ya auro wannan yarinyar mu a son ranmu ya auro ta? Yarinya fitsararra haka ya auro ta ta yi ta wulaƙanci tana haɗamu da shi kuma muka yi haƙuri shi ne ni zan yi aure saboda kawai wani son rai na shi na banza yace ba zan aure wacce nake so ba... "
" Faris... "
"Mum sai na auri Rabi'a...ga Invitation card nan ki raba Mum idan za ki raba, amma dole zan auri Rabi'a..."
Maimuna dake laɓe tun shigowan Hajiya Salamatu tana sauraren su ta koma ciki ta iske Alhaji Gimba dake kwance yana baccin safe ta tashe shi ta ce.