Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 45
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 45: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 45. Tasowa ya yi ya zauna yana mai banzarar da magananta tamkar bai…
3,375 words
Tasowa ya yi ya zauna yana mai banzarar da magananta tamkar bai ji mi tace ba ya canja da wata magana ya ce.
"You look beautiful..."
Shiru ta yi tare da buɗe warmers ɗin ta duba abinda yake ciki sannan ta yi serving na su tana kallon shi ta ce.
"Kai ba ka da matsala da abinci? Duk wanda ya girka za ka iya ci?"
Jinjina kai ya yi yana mai ɗaukan spoon ya ce.
"Yeah, na saba da ci tun a school, wurin aiki ma ina ci domin ni ko ruwan zafi ban iya dafawa ba, kinga idan na tsaya zaɓe zan sha wahala tunda ba Maami a tare dani...."
Idonta tamkar za su zazzago wurin kallonsa kamar mai jiransa ya ji ta tambaye shi.
"Who's she?"
A darare ya kalle ta na ɗan lokaci kamar yanda ita ma shi ɗin take kallo. Jinjina kansa ya yi tamkar mai tsoron magana ya ce.
"She's my Mum..."
Idonta ta sauke tare da jan spoon itama ta saka a plate ɗinda yake gabanta kawai ta jinjina masa kanta alamar gamsuwa. But a ranta ta sha mamaki ace yana mahaifiya amma bai taɓa kai ta wurin ta ba, itama kuma ba ta taɓa zuwa ba, babu daga relatives ɗinsa ko ɗaya da ya taɓa zuwa. She has alot da take so ta sani but ba za ta mishi magana ba a yanzu. Yau da kan shi ya furta mata sunan Maami, a hankali watarana zai furta Abiyh da ma sauransu.
Kamar yanda ta shiga tunani haka shima ya nutsa lokaci ɗaya ya shiga lissafi da mamaki wannan tambayar da ta yi masa.
Haka suka ƙarasa cin abincin kowa da abinda yake ransa musamman Maheer da fargaba ta cika masa zuciya.
Suna kambalawa ta shiga ciki domin yin brush sai ga kiran Na'ima Hassan, bayan ta fito toilet ta zauna suka sha fira shi Kuma sai ya shirya ya fice daga gidan bai dawo ba sai misalin 11pm.
Har ta kwanta ta ji ya janye duvet ɗinda ya janyota wanda ita ta ma gama sakawa a ranta cewa ya tafiyar sa kenan sai kuma ya ga dama. Idan babu comment zan je hutun kwana biyu....
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 54*
Hasken bedside lamp ne kaɗai Wanda ya kasance Dim light ke haskaka ɗakin, wanda shi ne ya bawa fuskar ta wata kyakkyawar colour da ya ji wani abu na fisgarsa musamman cute lips ɗin nan na ta masu ɗauke mi shi hankali.
Kallon ta yake a hankali yana mai jin yanda zuciyarsa ke wani irin bugawa da sauri, domin ko ba komai tun dawowarsa shi yasan cewa akwai abubuwa da dama da yake ji a ransa dangane da ita.
Mutsu-mutsu ta fara a hankali tamkar mai baccin gaske sannan a hankali ta buɗe lumsassasun idanun ta muryar nan a narke wacce ta ƙara sakar masa wata irin kasala ta ce.
"Ka dawo...?"
Jinjina kai ya yi ba tare da ya ce komai ba jin yanda wani abu ke masa yawo a kwanyarsa jin yanda siririyar muryarta ta shige shi.
Janyota ya yi tare da jingina bayan shi da headboard a hankali cikin nuna kulawa ya ji ta ƙara jefa mishi tambaya da cewa.
"Is Everything okay?"
Shiru ya yi na en wasu sakani sannan daga karshe ya saka hannayensa ya rungumeta ƙam cikin jikin shi wanda ya sa ta ɗan tsorata sai ta ma ji a ranta kaman ta janye amma kuma zuciyarta na faɗa mata cewa ba komai sannan taji ya sauke ajiyar zuciya mai sanyi a hankali ya kai lips ɗinsa gefen kunnenta na dama murya can ƙasa sosai ya ce.
"I'm sorry, I visited a friend...that's why kika ga ban dawo da wuri ba."
Komai ba ta ce ba kamar yanda shi ma bai sake cewa komai ɗin ba,sai dai dukkan su kowa yana cikin wani yanayi na jin sabon abu na kasancewarsu wuri ɗaya a shimfiɗa ɗaya, bargo ɗaya and ga su kuma cikin jikin juna. Wani irin yanayi ne suke ciki wanda babu ɗaya daga ciki da zai iya fassara abin da yake ji.
Tun tana jin kamar ba za ta iya baccin ba saboda wani sabon yanayi mai wuyar fassarawa da take ci, har dai sannu a hankali wani irin mashahurin bacci mai sanyi ya sace ta ba tare da ta yi aune ba wanda bata farka ba ma washegari tsabar yanda baccin yay mata daɗi sai da ya dawo masallacin asuba ya shiga tashin ta.
A hankali ta buɗe idanun na ta wanda caraf ta yi tozali da kyakkyawar fuskan nan ta shi dake saurin rikita tunaninta. Lumshe idanun ta yi a hankali sannan ta sake buɗe su tare da yunƙurawa ta zuro ƙafafunta ta shige toilet zuciyarta cike da tsantsar mamakin abinda ya hana mata farkawa yau da wuri.
Koda ta fito baya ɗakin wanda hakan ya bata daman cire towel ɗin jikinta ta canja zuwa doguwar riga ta yi sallah bayan ta kambala addu'ointa ta shirya cikin wasu fitinannun riga da wando wanda rigar ta kasance mai hannun vex sai guntun wandon da ya tsaya a cinyar ƙafarta.
Fitowa ta yi ta shige kitchen direct inda ta tarar da wata matashiya wacce za ta wuce ta a shekaru sanye da uniform a jikinta wacce daga yanayin fuskar ta ma kamar ba bahaushiya ba.
Kallo ɗaya matar ta yi wa Anaam ɗin sai kuma ta ɗauke kanta sannan ta duƙa ƙasa ta shiga gaishe ta cikin harshen turanci.
Fuskar nan ɗauke da kyakkyawan murmushi ta amsa tare da faɗin.
"Ta shi please, ki daina duƙawa babu kyau..."
Gabadai ta manta da cewa wai akwai wasu masu aiki a gidan domin tun jiyan bata gansu ba sai yanzu.
Miƙewa matar ta yi ta ce.
"Welcome ma, I'm Kudirat Abdul-Haziz...I'm here to serve you, my work is all about kitchen.."
Jinjina kai ta yi tana murmushi ta ce.
"Your welcome..I'm Maryam Mas'ood Galadima...Mrs. Mah..."
Saurin girgiza kanta ta yi da sauri tare da runtse idanun ta tamkar wacce ke filin gabatarwar da aka yi wa tilas ta ce.
"No...I'm Anaam. You can call me Anaam If you want. Kina jin Hausa?"
Jinjina kanta Kudirat ta yi ta ce.
"Ina ji Mah.."
"Okay...Mi kike a yanzu?"
Cike da respect ta ce.
"Waiting for you ma, to come and give me order for what to cook now..."
"kin karanci girke-girke ne ko kuma kawai kin tsinci kan ki kina yi saboda yau da gobe?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Yes ma, degree nayi a fannin girke-girke..."
"Wow...congratulations."
"Thank you ma."
Shiru Anaam ɗin ta yi na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta ce.
"While...you can go ahead ki yiwa Mijina breakfast mai daɗi, and please ki yi da wuri ki kambala because he's leaving and Kuma da wuri zai tafi..."
"Okay ma.."
Maimakon ta bar kitchen ɗin ba ta yi hakan ba, wata shiriritar ta shiga yi daban wanda tana yi tana murmushi jefi jefi kuma tana fira da Kudirat.
Aikinta kawai take amma kuma Idonta na can tana kallonta wanda ita kanta bata san miye Anaam ɗin take yi ba.
Bayan ta kambala ta shirya tray ta ɗauka kanta tana kallon Kudirat ɗin tace.
"Please ki hanzarta dan Allah kin ji"
Tana fitowa ta nufi dining table ta ajiye sannan ta taka ta shige ɗakinsa inda ta tarar da shi ya duƙar da kai yana ta rubuta da pen da tarin papers a gaban sa.
Ya ji shigowar ta amma kuma ƙamshinta shi ne abinda ya ja hankalinsa har ya ɗago ido babu shiri ya kalle ta.
Ya salam! Ya furta a ransa ganin irin shigar da ke jikinta wacce rigar ta yi shara shara kuma ba ta sauko mata zuwa ƙasa ba.
Hannunta ta kai a hankali ta zare Pen ɗin tare da yin murmushi ta ce.
"Good morning Mr. Busy..."
Janyota ya yi zuwa jikin shi wanda shi kanshi ba zai ce ga dalilin da yasa ya yi hakan ba.
Muryar shi ta yi very low as always ya ce.
"Good morning my bread and butter.."
Ido ta zaro alamar mamaki ta ce.
"what? Ni ce bread and butter ɗin?"
Hannunta ya riƙe ya sumbata yana murmushi ya ce.
"And why did you call me Mr. Busy?"
Turo baki ta yi gaba tace.
"I'm sorry..."
Ɗayan hannunsa ya kai ya shafo lips ɗin yana dariya ya ce.
"I'm sorry too. How are you?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"I'm good..."
Tana faɗin haka ta yi shiru na ɗan lokaci wanda akwai sauran abin da take so ta ce but jin kaman bai ji dadin kalmar Mr. Busy ɗinda ta kira shi ba yasa ta yi shiru, amma kuma ai miye shi ɗin idan ba Mr. Busyn ba? Always ba shi da wani aiki sai aikin Maritime, ba shi da lokacin kansa kullum dai aiki kullum aiki.
Kamar wanda yake magana da zuciyar ta haka ta ji ya bata amsar tambayar da take yi wa kanta ya ce.
"I'm sorry Maryam...ni na san cewa I haven't been fair to you dalilin wannan aikin nawa, but I promise you cewa daga zaran na kambala wannan assignment ɗin za mu samu kyakkyawan lokaci da juna. Wannan aikin ma da kika ga ina yi yanzu nasan cewa zan yi submitting na shi cikin kwanakin nan, but ban san cewa yau ake buƙatan shi ba sai da Chief Odev ya kira ni ɗazu...."
Lumshe idanunta ta yi zuciyarta cike da tausayinsa ta wani ɓangaren ta jinjina kanta ta ce.
"Ba komai, Allah ya taimaka ya bada sa'a. Allah ya ɗaukaka maka dukkan ayyukan ka ya tsare ka."
Shiru ya yi yana mai jin yanda kalaman ta ke ratsa zuciyarsa tare da sanya masa nutsuwa da jin cewa shi fa ya yi dacen mata domin ko daga yanayin kalaman ta za ka tabbatar cewa ta samu tarbiyya ingantacciyya.
Kiran wayar shi da akayi shi ne abinda ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga wanda yana duba screen ɗin yaga sunan Hamad ya yi rejecting tare da ajiye ta gefe ya kalle ta ya ce.
"Ya kamata na tafi domin na isa da wuri ko Maryam?"
Miƙewa ta yi daga jikin shi tana faɗin.
"Ka zo ka fara cin abincin tun da ka shirya kafin ka tafi."
Biye yake da ita tamkar wani raƙumi da alaka har suka iso wanda koda suka je har Kudirat ta gama shirya komai amma sai ta buɗe mishi tray ɗinda ta fara ajiyewa tana wani kalar murmushi ta ce.
"Bismillah..!"
"Thank you Maryam.."
Sai da ya ɗauki spoon Sannan idanuwansa suka sauka cikin plate ɗin wanda a ruɗe ya ɗago ya kalleta hankalinsa a tashe ya ce.
"Maryam what is this? Oh my God!..."
Dariya ta fashe da ita wacce ta bayyana masa fararen haƙoranta ta ce.
"Ba kace kai komai kana iya cin sa ba?"
Saurin girgiza kansa ya yi yana fadin.
"Oh no! Ba irin wannan ba..."
"Kai fa kace komai ci kake, ko baka ce ba?"
Ƙara kallon cikin plate ɗin ya yi hankalinsa a tashe ya ce.
"Wait...miye ma wannan ɗin kika yi mixing Haka?"
Still tana dariyar ta matso tana kallon cikin plate ɗin itama kamar yanda yake yi ta ce.
"Ba fa wani abu bane, kawai Sphagetti ce, with Beans, Indomie and Macaroni..."
Ƙara zaro ido ya yi tsaban mamaki ya ce.
"Oh God! Haba Maryam For goodnes..."
"Kuma tunda na sha wahala na girka sai ka cinye."
Kallonta yake sai kawai murmushi ya suɓuce masa.
"Ko kana nufin ba za ka ci ba?"
Yana murmushin ya jinjina mata kansa yana kallonta ya ce.
"Zan ci mana wane ni? Ai dole zan ci.."
Daga haka ya ɗauki Spoon ɗin a hankali ya tsakuro hannunsa har yana rawa zuciyarsa na masa wani iri ya kai spoon ɗin bakinsa.
Saurin riƙe spoon ɗin ta yi tare da zaro ido tace.
"Wai ci za ka yi?"
Yana murmushi ya ce.
"Eh mana! Ke ce fa kika dafa min domin farin ciki na..."
Dariya ta yi tare da saukar da spoon ɗin tana girgiza kai ta ce.
"Ni ba zan barka ka ci ba...ga wanda Kudirat ta girka."
Hannunta ya kamo ya sumbata yana mai wani irin farin ciki ya ce.
"Thank you Luv... Allah ya yi maki albarka ya bar mu tare har mutuwa."
"Amin amin."
Daga haka ta shiga serving ɗin shi wanda duk inda fuskanta ta yi idon shi yana kanta har ta kambala ta samu wuri ta zauna ta jira shi har sai da ya gama wanda bai wani ci sosai ba akan tsabar farin cikin da ta sanya shi, abinda ya faru yau har abada ba zai manta da shi ba a tunanin shi, because sun samu good time ɗinda bai taɓa sanin ko tunanin cewa zai faru ba.
Bayan ya kambala ya shiga ya shiryo itama ta shiga ta shirya cikin Abayah ta yafa veil ɗin ta fito ta rako shi har bakin mota.
Sai da ya saka Kayansa sannan ya waigo ya kalle ta yana jinjina kansa da murmushi muryaarsa a hankali ya ce.
"Thank you Maryam...thank you so much for making my day. I will miss you. I love you.."
Lumshe idanunta ta yi tana mai jin yanda kalmominsa ke ratsa ta masu neman zauta tunanin ta kawai ta ji ya janyo ta tare da jan hannayenta ya ɗora akan wuyan sa suna facing juna wanda hakan yasa ta buɗe ido ba shiri yana mata murmushi ya ce.
"Can I try something?"
Zuciyarta na wani irin pumping tamkar mai tsoron magana ta ce.
"Kamar na me?"
Ƙara matso da fuskarsa ya yi dab ta ta tare da ƙara riƙo waist ɗinta da kyau suna mai jin wani iri tamkar an saka igiyoyi an ɗauresu tsabar yanda zuciyoyinsu suke bugawa numfashinsu na gauraya da juna.
A hankali ya matso da lips ɗinsa Wanda hakan yasa ta lumshe idanunta tana mai jin tamkar ƙafafuwanta ba za su iya ɗaukar ta ba tsabar yanda take ji kawai ta ji saukar lips ɗinsa akan cute lips ɗin nan na ta da ke matuƙar ɗauke hankalin sa ya haɗe bakinsu wuri ɗaya.
Wani irin shock suka ji lokaci ɗaya wanda ya sanyasu yin baya tamkar za su zube jin wani irin sabon yanayi da ya bugi ƙwaƙwalwarsu.
Wani irin abu ne, mai sanyi, daɗi da garɗi yake ratsa brain ɗinta tamkar zai zautar da ita.
Da ƙarfi ta saka hannayenta ta riƙe colar ɗinsa domin ji ta yi kamar ba za ta iya ci gaba da tsayuwa ba.
A hankali ya janye wanda a lokacin idanunsa har sun gama canja kala tsabar abinda yake ji na musamman yana harɓawa a ƙwaƙwalwarsa zuwa zuciyar sa.
Cikin wata irin muryar da ta ƙara rikita tunanin ta ta ji ya ambaci sunanta wanda ko shi daga ji kasan yana cikin wani irin yanayi ya ce.
"Diyanah..."
Sai yanzu ta buɗe idanunta tamkar mai tsoron kallon wani abu ta kalle shi ba tare da tace komai ba.
"I love you."
Ya furta mata, daga haka ya janye jikin sa ya shiga mota wanda sai a lokacin ya ji siririyar muryarta tamkar za ta yi kuka ta ce.
"When are you coming back?"
Buɗe motar ya yi ya fito ya riƙo hannunta sannan ya jingina jikin motan a hankali ya ce.
"I will spend only 2weeks kin ji ko? And Anasi will be taking you to school when ever you have lectures. Please ki kula min da kan ki kin ji?"
"Allah ya tsare..."
Daga haka ta juya kawai ta koma gida. Tafi awa a zaune wanda ta rasa abinda yake mata daɗi sannan ta janyo wayarta ta kira Yaa Na'ima murya a ƙasa suka gaisa sannan Na'ima cikin damuwa ta ce.
"Anaam...lafiyanki kuwa? Miye ya same ki na ji muryanki ya yi low? Are you sick?"
Lumshe idanunta ta yi a hankali ta ce.
"I'm fine Yaa Na'ima. Daman zan faɗa miki ne cewa na zo ina Abuja tun jiya..."
"Me? Lallai ma? Ina mijin na ki?"
Turo baki ta yi tamkar tana a gabanta ta ce.
"Ya koma yanzu.."
Wata irin dariya Na'ima ta fashe da Ita sannan ta ce.
"Lallai ma Anaam ɗin nan! Kin zo Abuja tun jiya baki sanar mana ba, kina nan kina ta shan love da miji, yanzu ya koma shi ne kika kirani kina min fushi...."
Cikin jin wasu irin hawaye ta ce.
"To ni dai kawai Yaa Na'ima idan ba za ki zo ki ganni ba sai ki faɗamin in cire rai..." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*