Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 44
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 44: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 44. "Wallahi wannan gaskiya ne Yaya Hadiza. Ni ma ina goyon bayan…
3,359 words
"Wallahi wannan gaskiya ne Yaya Hadiza. Ni ma ina goyon bayan tunda har abubuwan sun kasance haka, Faris ya kafe ya ƙi ya saurari kowa to ya kamata ka hak'ura ka barwa Allah.... Yarinyar nan dai ba laifin ta yi maka…"
"Ku Daina!!!"
Ya wani daki table ɗinda ke gaban sa da ƙarfi har sai da suka tsorata sannan ya miƙe tsaye.
"Dukkanku ku fita daga maganar nan! Ni dai na haifi ɗana kuma na gama yanke hukunci! Wannan aure ba zai taɓa faruwa ba. Na rantse da Allah da ya aure ta gwanda ya mutu a yanda yake bai yi auren ba. Sannan kai Baba Sa'idu da kake ta wani kare Alhaji Mas'ood dake Hadiza...ku faɗamin miye ya taɓa tsinana muku a rayuwa? Babu! Amma ni na kai ku Makka, na baku jari, hidima da ta ku da ta yaranku babu wacce ban yi ba, saboda haka dole dai nine naku kuma ni za ku marawa baya. Wannan maganar auren babu ita har abada! Idan kuma wani yace zai yi gigin shiga gaba wallahy tallahy kotu ce za ta rabamu da shi ko waye ko!"
Daga haka ya saka hannunsa ya ɗauki hularsa ya fice daga falon fuuu kamar zai tashi sama.
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu tamkar ɗakin mutuwa tsabar mamaki da baƙin cikin Alhaji Gimba da ya gama cika musu zuciya.
Jiki sanyaye Baba Sa'idu ya ce.
" Uh uhm! Gimba har abada ba zai daina tijara ba. Ni har yau ban taɓa ganin mutum irin sa ba. Bawan Allahn nan ya jaka a jiki ya tsaya maka ya nuna maka hanyar samun arziki wanda Allah ne sanadi shi ne sanadi amma kuma kace babu wanda ka tsana kake takun saƙa da shi sai wannan ɗin! Ina amfanin wannan rayuwa wacce babu amana a cikin ta. Kun taso ku huɗu kun bunƙasa a tare, ɗaya yazo ya rasu, maimakon ku haɗe kanku ku uku domin ku ci gaba da tafiyar da kasuwancinku shi ne kai ka farraƙe kana rashin mutunci..."
Ajiyar zuciya Alhaji Ridwan ya sauke a hankali sannan ya ce.
" Tau! Allah ubangiji ya kyauta mana yasa mu fi ƙarfin zukatanmu amin...magana ta gaba kuma ba za mu tsaya haka ba, ba zamu zauna muyi shiru kuna kallon sa ba, wannan aure dole sai ya faru in sha Allahu. Ku manta da shi, indai yaga an yi auren ai dole ya shafawa kan sa ruwa ya sauko. "
" Allah yasa. "
Cewar Hajiya Salamatu sannan suka amsa da amin suka tashi suka wuce tare da ci gaba da jinjina maganar.
*******
Tun daga ranar ta dawo girka masa abinci kamar can farko da ta fara, sannan za ta yi wanka ta shirya kaman yanda ta saba su zauna da dare yana aikinsa ita kuma tana kallo ko kuma tana chart. Tun da ya fahimci cewa tana son kayan Ice cream da snacks da su chocolate tun daga ranar kullum baya dawo mata empty handed, dole sai ya samu wani abinda ya riƙo mata. Idan kuma za su kai ƙarfe nawa a zaune wuri ɗaya to shiru shi ne abinda yafi yawa a tsakanin su. Lokacin tashinsa daga aiki na yi zai kakkaɓo ya dawo cikin lokaci wanda yanzu har ta rage fargabar cewa zai iya sake yin tafiyarsa ya barta. Bacci ma a ɗakin ta suke yi but saidai tana kan gado yana kan kujera har gari ya waye.
Yau ma yana fita ba jimawa Na'ima Hassan ta kira ta take sanar mata cewa sun koma second semester tun kwana biyu da suka wuce har an fara lectures. Bayan sun sha firarsu sun gama tace mata daga zaran ya dawo daga aiki za ta tuna masa.
Da wannan ta wuni a ranta wanda bayan ya dawo yaci abinci har ya yi wanka ta same shi har cikin ɗakin sa abinda ta jima ba ta aikata ba.
Tsaye ta ganshi da frame ɗinda ke ɗauke da hoton wannan mutumin da ruwan hawaye a idon sa.
Da sauri ya ajiye tare da goge hawayen nasa cikin zafin nama gudun kada ta ganshi but ya riga da ya makara domin ta ganshi kuma ta gane kuka yake yi.
Wani murmushi ya ƙirƙiro yana mai kallonta da mamakin abinda ya shigo da ita ya ce.
"Maryam..."
Daga inda take tsaye kawai ta ce.
"Daman ina so ne zamu yi magana."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Okay...Just 2mnt."
Parlour ta dawo ta zauna tare da ɗaukan remote control ta canja tasha Zuwa Zee world amma kuma gabaɗaya hankalinta baya wurin. Tunani kawai na neman dalilin da yasa yake kallon wannan hoton yana kuka. Wait...ko dai shi ne Abiyh ɗin da ta ji wacce ya rubutawa Maami ta ambata? He's condition is getting worst this time around.
Wannan ita ce maganar da ta tuna wacce ta sanya a ranta cewa wata ƙila kukan rashin lafiyar mutumin ce yake, to amma miyasa wannan wurin aikin nasu suke da tsauri haka? Miyasa ba za su bashi dama yaje ya dubo mahaifinsa ba nan da Zaria?
A hankali ta hango shi yana zuwa wanda shi ne abinda ya katse mata tunanin ta. Kallon shi take har ya ƙara so ya zauna ɗan nesa da ita ya ce.
"Barka da hutawa..."
Wani guntun murmushin ta saki domin maganar ta ɗan bata dariya daban, sai kace wata gimbiya.
"Daman ina so in tuna maka cewa mun koma lectures..."
Jinjina kansa ya yi yana Kallonta ya ce.
"Ba mantawa na yi ba, alƙawarin one week muka yi dake saboda haka sai jibi in sha Allahu zamu koma..."
Wani irin farin ciki ta ce.
"Thank you so much..."
Kallonta yake da mamaki ya ce.
"Ohh! Wato murna ma kike yi ko? Kan ki kawai kika sani.."
Girgixa kanta tayi tana murmushi alamar a'a sannan ya sake cewa.
"zan yi kewanki sosai...zan yi kewan wannan girkin naki mai daɗi plus kyakkyawan murmushin ki da kuma dressing ɗinki..."
"Uhm.."
Abinda kawai ta ce kenan ba tare da ta sake kallon inda yake ba. A ranta ji take duk abinda take ji dole ta yi masa uzuri tunda a gabanta ma kullum cikin aiki yake ba dare ba rana and ga shi har yana da marar lafiya amma kuma sun kasa masa uzuri.
******
Rabi'a kuwa, tana nan tana ta shagalinta tana abinda ranta yake so a gidan Abbah musamman da Yaa Muhammad ya iso suka tattauna kuma suka amince.
Duk da cewa tana gidan, kullum cikin waya take da Umma suna ta shirye-shirye da tsare-tsaren buki wanda sun lissafa event da za su yi yafi guda goma wanda tace a ajiye sauran maganan anko a bari sai Faris ya zo idan suka tattauna za ta yi musu bayani kafin ta koma gida idan buki ya rage saura kwana uku.
Yau tunda ta wayi gari taje ta samu Nene a kitchen ta sanar mata cewa Mijinta yana kan hanya tana so a haɗa mishi kalolin girki kamar guda biyar da drinks da snacks na tarbon babban baƙo.
Yanda ta bada order haka Nene ta zaɓi mutum biyu daga cikin masu aikin kitchen ɗin tace su yi mata duk abinda tace.
Zuwa ta yi tasha wankan ta ta fito ta zauna ta tsara wa kanta kwalliya ta ji da gani sannan ta samu wuri a ɗakin na ta ta zauna zaman jiran shi domin ta yi alƙawarin babu wani ƙaton da zai ga wannan kwalliyar sai Farrab ɗinta habibiyn zuciyar ta.
Tana nan tana chart tana kuma yi tana duba time har sai da taji ya kira ta da cewa ya iso.
Cike da wani irin jiji da kai take tafiya tana wani rangwaɗa tana ƙallewa tana tashi tamkar wata taliya har ta isa bakin motarsa tana masa murmushi.
"Beeyh.."
Ya ambata yana mai fitowa daga motar ya tsaya a gefenta.
Fitowan shi a mota kenan suka yi Ido biyu shi da Yaa Mukkaram wanda in banda mugun kallo da harara babu abinda Mukarram ɗin ke jefa musu ✍️ *OUM AMEER✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*BOOK ONE* *PAGE 53*
Ido Faris ɗin ya zuba yana kallonsa kamar yadda yake kallonsa shi ma har ya ƙara so inda suke tsaye ya tsaya.
Wani kallon ya yi wa Rabi'a sannan ya ɗaga yatsa yana nuna Faris yana jinjina kansa ya ce.
"Wannan dai shi ne kika kafe ke dole sai kin aure sa ko? To ki sani, za ki yi nadama kuma nadama marar amfani, domin wannan da kike gani shi da mahaifinsa ba abun yarda ba ne. Amma da yake ke ɗin mai kunnen ƙashi ce wacce babu wanda ya isa da ita, za ki gane taurin kai ba shi da amfani nan gaba kaɗan."
Daga haka ya kama hanyarsa ya shige cikin gidan wanda har yanzu Faris bai daina kallonsa ba sai da yaga ya ɓacewa ganin sa sannan ya lumshe idanunsa ya buɗe su akan Rabi'ar ya ce.
" Don't mind him Beeyh, kina gani ko gidan na su haƙuri suke da shi. Shiyasa na godewa wanda ya sace shi a kwanakin baya ya yi masa dukan mutuwa, ko banza an rage min takaicinsa..."
Jinjina kai ta yi da murmushi tana mai jin yanda zuciyar ta ta yi sanyi kin cewa abin da mukarram ɗin ya yi masa bai ɓata masa rai ba.
"Ji kike a ranki kaman aurenmu ba zai faru ba ko?"
Girgiza kai ta yi ta ce.
"A'a. Ai na ji Ammie ta tabbatarwa Yaa Na'ima cewa za'a yi auren duk da cewa dai ban ji sun ce an saka rana ba..."
"In ji waye yace miki ba'a yi fixing date ba? Da nan Abuja da Gusau duk gidana a shirye yake ke kaɗai yake jira. Ko su Daddy Ridwan da suka ce a yanke 4weeks naga ya yi min tsawo amma dai kinga ban isa na ja dasu ba..."
Wani far-far ta yi da ido tana wani irin murmushin farin ciki sannan ta ce.
" To ni ban ji ka yi maganan kayan Lefena ba."
"No kada ki damu, zan koma gida daga nan In sha Allah, sai mu yi magana da Mum mu ji yanda za'a ayi..."
Ɗan taɓe baki ta yi murya can ƙasa ta ce.
"Ni fa kaman na ji an ce ita ma Mum ɗinka bata goyon bayan aurenmu tunda Daddynka baya so, idan Kaga itama za ta bamu matsala kawai ka manta da ita ko ni nan zan iya haɗawa kai na lefe..."
"Ke.!!"
Ya ambata a ɗan tsawace wanda sai da yasa Rabi'ar ta ɗan zabura ba shiri tsabar yanda ya yi maganar cike da tsare gida, lokaci ɗaya ya ɓata fuska sannan ya sake cewa.
"Are talking about my mum like that? Kin haukace ne ko miye? Mahaifiyar tawa kike cewa in manta da ita tsabar baki da hankali baki iya magana ba..."
Hannayenta ta harɗe da sauri murya na rawa ta ce.
"I'm sorry please, that's not what I meant..."
Juyawa ya yi da nufin tafiyarsa, jiki na rawa ta kamo hannunsa a diririce ta hau magiyar bashi haƙuri wanda sai da ta yi da gaske sannan ta samu ya haƙura ya tsaya tare da rantse-rsntsen cewa tsautsayi ne ba za ta sake ba.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe idanunsa ya buɗe sannan ya kalle ta ya ce.
"My Mum is my Happiness, Har abada ba za ki burgeni ba idan kika ce za ki yi mata wata maganar rashin kirki domin ita ɗin ba tsarar ki ba ce."
Daga haka ya shiga tafiya a hankali har bakin mota wanda itama jiki na rawa ta taka ta bi bayansa murya tamkar za ta fashe da kuka ta ce.
"Dan Allah ka yi haƙuri mana..."
"Na hak'ura ai. Da ban hak'uran ba ba zan tsaya yi miki bayani ba. Kawai dai I need to go...za mu yi magana a waya."
Kallon shi take da ruwan hawaye a idon ta har ya shiga motar ya tayar ya fice wanda ko kallon inda take tsaye bai ƙara yi ba. Tana nan a tsaye sai ga Yaa Amina ta shigo ita da Aunty Aysha da yaran su.
Saurin share hawayenta ta yi ta yi musu sannu da zuwa sannan ta kamo hannun Faryat tana murmushi ta ce.
"Ɗiyar Aunty Na'ima daga ina haka?"
"Daga buki ko Mummy?"
Feruz ya amsa yana mai kallon fuskar Yaa Amina.
A tare suka koma ciki Aunty Aysha na ta tsokanar ta tana ce mata amarya.
********
Yau da ta kasance ranar tafiyarsu tun da safe ta tashi ta yi masa special breakfast ta jera masa a table tana ta farin ciki. Bayan ta kambala tana cikin gyaran parlourn ya fito cikin shiri a gaggauce ya kalle ta tun daga sama har ƙasa.
Wata vex ce haka a jikinta maroon colour mai ɗan shara-shara da kuma plane zani da net a kanta.
Cikin seconds ta ɗan ƙarewa kanta kallo wanda ko bra babu a cikin jikinta ta yi saurin girgiza kanta ta ce.
"Ban yi wanka ba..."
Murmushi ya yi tare da yin stepping zuwa gabanta ya janyo ta a hankali zuwa right side ɗin shi Sannan ya jinjina kansa ya ce.
"You still look beautiful. And....you always smell nice."
Murmushi ta sakar masa tana mai saukar da kanta ƙasa but har cikin ranta ta ji daɗin yanda ya yabeta ko ba komai yanzu ta fara shiga rayuwar shi kuma ya nuna tana da muhalli a cikin duniyar sa.
"Zan je na dawo zuwa 4pm kin ji, kafin nan you should get ready."
Jinjina kai ta yi alamar ta ji sannan ya je ya zauna yaci abincin bayan ya kambala ta ɗauko mai wani basket ɗin mai ɗauke da white rice and stew tana kallon shi a hankali ta ce.
"Ban sani ba ko kana buƙatan wannan..."
Ajiye briefcase ɗinsa ya yi ya karɓa hannu biyu yana murmushi ya ce.
"Thank you so much."
A tare suka fito har bakin mota sannan bayan ya shiga ta miƙa masa briefcase ɗin ta yi masa sallama ta dawo gida taci gaba da ayyukanta wanda koda 12pm ta yi ta kambala gyaran gidan tsab sannan ta zauna ta gyara kayanta da na shi waɗanda aka kawo musu daga laundry daren Jiya.
Bayan ta kambala ta yi wanka ta ci abinci sannan ta shiga ta kwanta da niyyan bacci amma kuma sam bacci ya gagareta wanda tasan hakan baya rasa nasaba da ɗokin komawa Abuja da za ta yi.
Tana nan tana ta shiririta kala-kala har ya dawo inda koda ya shigo har ta shirya cikin Shigar nan da yace tana burgeshi.
Tayin wani abincin ta yi masa sai ya girgiza kansa yana murmushi ya ce.
"Kina so kisa na koma ƙatoto ko?"
Dariya ta fashe da ita ta wani kalle sa wani siriri da shi tamkar a busa shi ya ƙalle shi ne zai ce wai zai yi ƙatoto. Ƙatoto ta ina?
Kallon yanda take ta dariya yake wanda ya jima ko yace ma tunda yake bai taɓa ganin tana irin wannan dariyar ba.
Ya shagala yana Kallonta kawai ya ji taja hannunsa tana faɗin.
"To Mr. Big idan ba za ka ci abincin ba ka zo ka yi wanka mu tafi lokaci yana tafiya..."
Ji ta yi ya janyota ta faɗo cikin jikin shi sannan ya saka both hands ɗinsa ya rungume ta ya shiga kallon cikin idanunta tamkar wanda zai yi mata wata magana, sai dai kuma komai bai ce ba tsawon lokaci wanda hakan yasa ta zame a hankali tana murmushi ta ce.
"Dare fa ƙara yi yake..."
Yana jin ta faɗi haka ya wuce bai ce komai ba ya shiga ya yi wanka, bayan ya fito ne yaga yanda ta gyara masa kayansa tsab sannan ya shirya cikin Jeans and t-shirt as usual ya sanyo P-cap ya fito.
Idonta na sauka a kan shi ta saki wani irin lallausan murmushi domin har cikin zuciyar ta yana burge ta. Kowace irin shiga idan ya yi ta tana burgeta but irin wannan ɗin ita ce tafi tafiya da ita.
Ji ta yi ya kamo hannun ta ya saƙala a nashi suka fito inda cike da mamaki ta kallon Hamad dake zaune a mota tace.
"Waye wannan?"
Dariya ya yi tare da saka Hannayensa ya kama kunnuwansa ya ce.
"I'm sorry. Na san ni mai laifi ne amma ki yi hak'uri..."
"Hmm! Ka kyauta Yaa Hamad..."
Ta ambata sannan Maheer ɗin ya buɗe mata motar ta shiga shima ya shiga Hamad ɗin ya kai su Airport.
Sai da ya shigar da ita yace ta jira ya yi sallama da Hamad sannan ya dawo wurin Hamad ɗin ya kalle shi ya ce.
"I will be back tomorrow morning in sha Allah.."
Idon sa akan Maheer ɗin ya ce.
"Maheer lokaci kaɗan ne ya rage ma. Abinda yasa Kaga ban taɓa shigowa gidan ka tana nan ba bana so wani abu ya taso ta yi kuka dani duk da nasan cewa ba zan taɓa fita ba duk abinda zai je ya dawo. Nasan za ka ji haushi na a yanxu ko Ince a kullum cikin jin haushi na kake tunda ina faɗa maka gaskiya. Bahaushe yace da muguwar Rawa gwamma ƙin tashi Maheer, wallahy abinda kake ciki a yanzu, yafi wanda za ka je ka tarar a gaba..."
"Hamad komai zai faru ba zan iya sakin Maryam ba..i love her..."
Wani kallon ka ma raina wa kanka wayo Hamad ɗin ya yi masa sannan ya ce.
"Wace Maryam ɗin kake so? Hmm! Don Allah malam ka da ma ka yaudari kanka domin ni kaina nasan cewa Ƙarya kake..."
"Miye kake nufi Hamad? Ban kai na so ta ba ne ko kuma ita ɗin ba ta kai a so ta ba ne..."
"Maryam would never love you Maheer...shiyasa na ga kuskuren ka na yarda da aurenta. Kuskure na biyu shi ne rashin neman yardar mahaifiyarka, wallhy ni ba hassada nake maka ba because tsakanina da kai babu zancen hassada. Amana ce mai girma da aminta take tsakaninmu, you have done so much to me ta yanda duk abinda nasan zai cutar da kai indai zan iya dakatar da cutarwar nan dole na dakatar..."
"Hamad I need to go now..Idan na dawo zamu yi magana."
Abin da ya ambata kenan kawai yasa kai ya yi gaba. Shiru Hamad ya yi na tsawon lokaci tare da zura mijsi yana kallon shi har ya ɓacewa ganin sa. Bai san yanda zai yi wa Maheer bayani ya fahimta ba, but yana hango abubuwa masu yawa a gaba.
*******
Anasi shi ne wanda ya zo ya ɗauke su zuwa gida, koda suka shiga ta tarar an jera musu abinci a table komai an gyara gidan sai zuba ƙamshi yake.
Kallon shi ta yi da mamaki a hankali ta ce.
"Akwai wasu ne a gidan?"
Murmushi ya yi tare da saka hannu ya lakace mata guntun hancinta ya ce.
"Who did you expect?"
Ɗage kafaɗa ta yi alamar oho ta ce.
"No one. Kawai dai naga gidanka, kana da right ɗinda kawo duk wanda kaga dama..."
"No! Babu wanda zai shigo gidanki sai da izininki, wannan ɗin waɗanda za su riƙa taimaka miki ne, kinga za ki koma school and ayyukan da kike yi sun yi yawa, you need time to rest, read, sleep and so on..."
"But I can do it my self...."
Saurin girgiza kansa ya yi yace.
"No Luv...you need and assistants, so don't argue please, just do as I said.."
"Ok.."
ta ambata tare da gyaɗa masa kanta tana murmushi.
Sai da suka gama salloli sannan tayi wanka ta shirya cikin wata nighty wacce ta tsaya a Knee ɗinta, ta Shafa powder da lips glow Sannan ta saka hula ta fito.
A kan kujera ta hango shi da waya yana magana a hankali wanda duk nacinta ta kasa jiyo abinda yake faɗa.
Ganin hakan sai yasa ta tsaya daga inda take domin ba shi time ya ƙarasa. Shi kuwa yana nan yana maganan amma kuma idanun shi na kanta har ya kambala.
"Miyasa kika tsaya daga can?"
Ya tambayeta yana kallon ta har ta ƙara so ta wuce ta zauna a table domin cin abinci sannan ta ce.
"I think you need some privacy that's why..."