Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 43

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 43

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 43: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 43. Aikin ta ta shiga yi a hankali wanda tana yi tana ta tunani…

3,354 words

Aikin ta ta shiga yi a hankali wanda tana yi tana ta tunani iri-iri wani mai amfani wani kuma marar amfani. Tana nan ta ji Phone Vibration wanda ta ɗauki tsawon lokaci ta na ji ba tare da an daina ba.

Fitowa ta yi sai ta hango wata waya keypad ajiye a ƙarƙashin throw pillow dake kan one seater.

Matsawa ta yi ta ɗauki wayar ta shiga kallon sunan da ke kan screen ɗin wanda har yanzu ake ci gaba da kira ba tare da an daina ba.

"My Maami..."

Sunan da ta gani kenan ya yi appearing wanda take ranta ya bata cewa wannan ɗin wata ƙila mahaifiyarsa ce.

Ta ɗauki lokaci mai tsayi tana kallon kiran sannan daga ta ajiye.

Sai da ta kai bakin ƙofan kitchen ɗin sai kuma ta juyo ta dawo ta sake ɗaukan wayan tare da receiving a darare ta kara ta a kunnunenta cike da mamakin dalilin irin wannan kiran hakan.

"Maheer!...Hlo Maheer are you hearing me?.....Abiyh was on admission tun around 2am and his condition is getting worst this time around..."

Wannan shi ne sautin da ya shiga kunnuwanta wanda ta ji muryar wata Mace wacce bata san kowace ce ba.

A hankali ta kai hannu ta yanke kiran tare da shiga ta goge amsa kiran da ta yi sannan ta ajiye ta a yanda take ta koma kitchen da sauri ta ci gaba da aikin da take.

Shi kuwa yana can masallaci bai dawo ba sai da haske ya ɗan fara sannan ya shigo shaf-shaf ya wuce ɗakinsa ya shiga neman wayar wanda sai daga baya ya tuna cewa tana parlour tun daren jiya sannan ya dawo ya ɗauka. Miss calls ɗin Maami su ne abin da ya gani rututu wanda ba shiri ya kira ta hankalinsa a tashe.

"Maheer wai miye abinda yake damunka ne a 'yan kwanakin nan? Yanzu ba daman mutum ya kira ka sau ɗaya ka yi picking dole sai ya yi ta kira sannan za ka ɗaga? Your attention was derived away by something else wanda ban san mine ne ba..."

"I'm sorry Maami! Koda kike kirana ina masallaci sai yanzu na dawo..."

Cike da ɓacin rai ta dakatar da shi da faɗin.

"Ko daren jiya na yi maka almost 5miss calls but no response..."

"Please Maami I'm sorry, in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, kin san lokaci kaɗan ne ya rage na kambala assignment ɗina so I'm working so very hard ta Yanda zan kambala komai na cikin tsari da ma'ana. Shi ne kawai, but bayan wannan babu wani abu kuma... "

Yana jiyo sautin yanda ta sauke ajiyan zuciya a hankali sannan ta ce.

"Shikenan! Allah ya taimaka ya bada sa'a, Allah ya taimake ka ya sanya albarka a cikin wannan aikin."

"Amin Maami. Good morning..."

"Good morning! Daman Abiyh ne aka yi admitting na shi around 2am Kuma condition ɗin masa har yanzu sai a hankali.."

Ido ya zaro a hankali ya ce.

"Subhanallah! Baya shan maganinsa ne ko me?"

"Yana sha daidai kuma akan Lokaci,Allah ne ya kawo masa wannan ɗin."

"Allah sarki! I wish him speedy recovery..."

"Amin yah Allah, thank you."

"Ahm...I'm sorry Maami, kwanakin nan ina da ayyuka sosai wanda bani da wata daman da zan ɗaga na bar su, but In sha Allah zan zo idan na samu chance.."

"Ba damuwa, ai daman idan aski ya zo gaban goshi yafi zafi. Allah ya taimaka ya nuna min kambala ka dawo gida wallahy hankali sai yafi kwanciya."

Cikin faɗuwar gaba ya amsa da Amin Maami amma kuma can ƙasan ransa Anaam ce kawai yake tunani. Har yanzu bai hasaso yanayin ba sai yanzu da Maamin ta furta masa waɗan nan kalamai.

Lokaci kaɗan ne ya rage masa ya kambala, ta yaya ta ina zai fara?

Jin yanda hankalinsa ya tashi yasa ya yi saurin kawar da wannan tunanin a cikin ransa ya wuce direct ya yi wanka ya shirya ya fito ya shiga ɗakinta. All his thoughts tana nan tana bacci,amma kuma sai ya tarar bata nan hakan yasa ya fito ya tarar da ita a dining area tana gyara tana arranging table ɗin.

Fuska ba yabo ba fallasa ta ɗan kalle shi cikin shirinsa na uniform wanda yake ƙara fito da shi a kullum ta ce.

"Good morning..."

Murmushi ya yi tare da jinjina kansa ya ce.

"Good morning,...Ahm..na ɗauka kina bacci ne?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"A'a. Nasan za ka fita da wuri shi ne nace bari na sama maka wani abun.."

Zaunawa ya yi cikin nuna farin ciki ya ce.

"Thank you so much."

Ciki ta koma ta yi wanka ta shirya cikin wani material doguwar riga da hula ta fito wanda hakan ya yi daidai da tashin sa domin wucewa.

Kallonta ya yi daga sama har ƙasa yana murmushi ya ce.

"Komai kika saka yana miki kyau."

Shiru ta yi tare da kawar da kanta daga barin kallon shi sannan ta ji ya ce.

"Zan tafi Base Maryam. Ina da meeting idan muka gama training, but in sha Allahu zuwa 3pm zan dawo."

"Allah ya tsare ka ya bada sa'a ya kuma dawo da kai lafiya."

"Amin Ya Allah, na gode."

A nan suka yi sallama ba tare da ta rakashi zuwa waje ba kaman yanda ta fara a can baya. Yana fita ta zauna taci abinci sannan ta ɗauko wayarta inda itama ta tarar da miss calls din su Ammie da Su Na'ima da yawa wanda sai daga baya sannan ta bi su ta kikkirasu.

Bayan ta gama ta koma ɗaki ta kwanta a hankali maganganun wannan matar wacce ya rubutawa Maami suna dawo mata. Wace ce Maami? Mahaifiyarsa ce ko waye? Waye kuma Abiyh?

Tambayoyinda ta shiga yiwa kanta kenan na tsawon lokaci wanda tasan cewa ko kwana za ta yi tana tunani ba za ta taɓa samun wannan amsar ba sai dai idan ta tambayeshi domin shi ne kaɗai wanda zai iya warware mata wannan.

Da wannan ƙudurin a ranta ta zauna tana ta saƙa irin tambayar da take so ta yi mai, sai yanxu ne ma take na damar miyasa tun farko ba ta tsaya ta yi copying number matan ba? Shirme da yaranta. Ta faɗawa kanta tare da miƙewa taje ta yi masa girkin rana mai rai da motsi sannan taje ta yi wanka ta shirya cikin wata Atamfa riga da skirt masu bala'in kyau ta zauna zaman jiran shi. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 51*

Knocking ɗinda ta ji shi ne abinda ya katse mata tunanin da ta nutsa a ciki na tsawon lokaci. Da sauri zuciyarta ta yi wani irin bugawa wanda hannunta ya kai kan chest ɗinta tayi saurin dafe gefen zuciyar ta ba shiri.

Ido ta zuba tana jiran taga shigowan shi but sai ta ji kuma ya ci gaba da knocking wanda hakan yasa ta miƙe a ranta tana faɗin yau kuma wane irin iyayi ne da sabon salo? Mutumin da ke turo ƙofa ya shigo duk sanda ya so shi ne zai wani tsaya saboda iyayi yana wani knocking sai ka ce wani baƙo.

Guntun tsaki ta ja daga can cikin zuciyar ta sannan a hankali ta lumshe idanun ta tare da ƙoƙarin daidaita nutsuwarta sannan ta miƙa hannu ta murɗa handle ɗin ta buɗe.

Wani irin skipping zuciyarta ta yi tare da zaro ido cike da tsananin mamakin ganin wanda yake tsaye.

"Ko na juya na koma ne Anaam?"

Mutumin ya ambata yana mai yi mata murmushi.

Ita kuma jin hakan yasa ta yi saurin girgiza kanta tare da matsowa da sauri ta rungume shi ta ce.

"Oyoyo Yaa Muhammad..."

Janyewa ya yi yana dariya ya ce.

"Ya kike Anaam?"

Hannunshi ta ja da sauri ta kai shi tsakiyan parlourn saitin kujera ta ce.

"Yah Muhammad dan Allah ka zauna."

A tare suka zauna ta wani kamo Hannunshi tamkar wani baƙonta ta ce.

"Wallahy na yi matuƙar mamakin ganinka. But na yi farin ciki kuma.."

Murmushi ya yi ya ce.

"I miss you Anaam ɗin Yaa Muhammad. Aure kaɗai ya kai can ya rabaka da ɗan uwanka wanda sai dai idan hidima ta tashi ko dai wani dalili sannan za ku iya haɗuwa. To wataran koda dalilin ma sai kika ga haɗuwan ta yi wuya tunda gashi you spend almost a week a gida ba tare da mun haɗu ba. Hakan yasa na ji ba zan iya daurewa ba na ce sai na biyo na ganki kafin na wuce gida."

"Allah sarki Yaayana..thank you so much..taso..taso kaci girkin gidana yaa Muhammad."

Ta ƙarashe maganar tana mai janyo hannunsa zuwa table ɗinda ta gama shiyarwa Maheer ɗin.

Dariya ya yi cike da tsokana ya ce.

"Yanzu wannan duk na mijin Anaam ne shi aka shiryawa?"

Rausayar da kanta ta yi tare da kwaɓe fuska ta ce.

"Kai Yaa Muhammad harda kai ko?"

"Yi hak'uri wasa nake, ina ganin kaman komai a mafarki."

Ita dai shiru ta yi ta ci gaba da serving ɗin shi sannan bayan ta kambala ta zauna tana ta mishi fira har da ɗaukan waya ta kira su Yaa Mubarak vedio call suka yi ta fira suna dariya har ya kambala sannan ya tashi yana faɗin.

"Ni zan tafi..."

Raurau ta yi da ido tamkar za ta yi kuka ta ce.

"Haba Yaa Muhammad dan Allah! Tun yanzu?"

Hannun ta ya kama yana kallonta ya ce.

"To Anaam mi zan jira? Na haɗu da mijinki mun gaisa mun ɗan jima ma a tare muna fira, ashe yana aiki a nan shi ma but yace min bai ji ma ba..."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Haka ne, ya ce min aikin ne ya burgeshi sai Hamad ya mishi hanya."

"Haka fa. Ina fata dai kina lafiya kuma ba wata damuwa right?"

Jinjina kai ta yi alamar ba komai duk da cewa har yanzu wani kallon take yi wa Maheer ɗin na daban.

"Okay...and again na san dai baki da matsalan kuɗi?"

Sake jinjina kai ta yi ta ce.

"Bani da Yaa Muhammad, ko ranar da na dawo sai da yaa Mubakar ya turomin 500k yace min in ji Abbah."

"okay. Ki yi ta haƙuri kin ji ko? Haƙuri shi ne gaba da komai, but a matsayina na Yaya kuma Uba ta wani fannin kada ki yi haƙurin da zai zama cutarwa a gareki...."

Ganin irin kallon da take yi masa mai nuna buƙatar ƙarin bayani ya yi saurin girgiza kai ya ce.

" No Maryam kin gane? Akwai haƙuri wanda an san rayuwan gidan aure ta yau da kullum daman haƙurin yafi yawa kuma shi ake so, but haƙuri na cutarwa wanda zai iya sanyaki a wata damuwar da za ta ma iya illata miki zuciya kaman yanda na faɗa miki a baya kada ki taɓa yarda da wannan. Allah ya ƙara muku haƙuri ya baku zaman Lafiya."

"Amin, na gode ya Muhammad. Allah ya tsare, ina gaishe da su Yaa Amina."

Yana fita ta koma kan kujera ta zauna tare da lumshe ido tana jin kaman ta tashi tabi bayan shi ta koma gida.

Sai da ta kambala sallar Asr sannan ta ji shigowanshi wanda har mind ɗinta ta gama bata cewa ko yau wata ƙila ba zai dawo ɗinba sai wani satin ko fiye da haka ma because 3pm ya ce mata zai dawo gashi har 5pm ta kusa.

A hankali ta ji takun takalmin shi har zuwa cikin ɗakin ta wanda a hankali ta ɗago ta kalle shi ta ce.

"Sannu da zuwa..."

Zaunawa ya yi a bakin gado yana murmushi ya ce.

"Ya gida Maryam?"

"lafiya lau."

Miƙewa tayi tana faɗin.

"Abinci yana parlour...."

Hannunta ta ji ya riƙo kawai ya janyota jikin shi a hankali ya kai fuskarsa saitin wuyan ta ya goga fuskarsa sannan ya gangaro zuwa fuskanta a hankali ya ɗago ya kalli idanun ta waɗanda ta rufesu gam tamkar mai jin tsoron kallon wani abu tana jin yanda tsikan jikinta yake tashi ba daɗi.

"Sai da na zauna na ci abincin nan sannan na shigo, thank you..."

Hannunta ya kamo yayi twisting a nashi sannan ya ɗago yana kallon lallen hannunta wanda aka yi musu a daren suna ita da Yaa Na'ima ba tare da yace komai ba.

Ganin ya yi ta zame a hankali ta sauka daga kan ƙafafunshi tare da ɗan matsawa gefe kaɗan.

Hannun shima ta shiga neman yanda za ta yi ta ƙwace but sai taji ya ƙara riƙewa tare da kafeta da ido a hankali ya ce.

"Miyasa kike guduna? Ba zan taɓa cutar da ke ba ki yarda dani. Kodai akwai wani abu ne.?"

Girgiza kanta tayi alamar a'a sannan ta ɗan ɗago ido ta kalle shi kaɗan zuciyar ta cike da fargaba ta ce.

"Ahm...daman..daman..."

Sai kuma ta yi shiru ganin yanda ya zuba ido yana kallonta ba ko ƙyaftawa.

"I'm all ears...feel free and talk to me kin ji? Daman me?"

Girgiza kanta ta yi da sauri tana mai kauce wa kallonsa ta ce.

"Ba komai.."

Cike da mamaki ya ce.

"ba komai kuma?"

Shiru ya yi ya zuba ido yana mai ci gaba da kallonta sannan daga ƙarshe ya miƙe ya ce.

"Zamu iya fita shopping? Are you interested?"

Jinjina kai ta yi alamar eh, sannan ya ɗauki excuse ya fita. Yana fita ta wani girgiza kanta tare da runtse idanun ta ta buɗe tana faɗin.

"Oh no...this is so stupid of you Anaam! What's wrong with you? Miyasa baki tambayesa ba?"

Ji ta yi gabaɗaya ta kasa yi masa ko tambaya ɗaya daga cikin tambayoyinda ta tsara za ta mishi. Gabaɗaya ji ta yi zuciyar ta na gargadinta akan cewa ta ƙyale shi tunda har baya so ya sanyata cikin al'amarin familyn shi. Tunda itama tana da na ta to kowa ya riƙe abinda yake da shi. Idan taci gaba da magana zai ga kaman ta cika shishshigi.

Tana jin kaman alamar motsin shi ta tashi da sauri ta je ta shirya suka fita. Siyayya yayo mata wacce mafi yawa duk kayan da take yawan sakawa ne na riga da wando da kuma riga da skirt su ne ya kwaso mata masu matuƙar tsada, plus there veils na rolling da kuma bags ɗinsu. Sai kuma tulin kayan chocolate da ya siyo Wanda hannunta yana cikin na shi duk inda suka sanya ƙafa har suka gama.

Suna shigowa ta yi sallar magrib da Isha sannan ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando masu santsi wanda wandon ya kasance bakin gwiwa ɗinta da kuma rigar sa da hannunta ya tsaya bakin gwiwan hannunta shima wanda suka kasance ba masu nuna tsiraici ba.

Parlour suka koma tana ta shan ice cream ɗinta da sauran kayan shiririta tana kallo a TV shi kuma yana ɗayan kujerar yana aiki a system wanda bata san abinda yake ba domin ba kusa da juna suke ba.

*******

Gidan Alhaji Gimba kuwa, tun da Maimuna ta dawo daga fitan da ta yi a ranar ta fahimci cewa kaman ba lafiya. Dalilin daren ranar da ya kasance kwanan Hajiya Salamatu ne amma kuma ya dawo Sashenta ya kwanta a parlour.

Dole tasan akwai abinda yake faruwa wanda idan ba wani abu ba yanda zai yi ya dawo sashenta sai dai ma ya shige nashi Part ɗin duk ya ƙyale kowa.

A haka dai taga ya shafe kwanaki ko kallon inda Hajiya Salamatu take baya yi ko miye sai dai yace ita Maimunan ta yi wanda daga ƙarshe ta ji wani irin daɗi da farin ciki sun gauraye mata zuciya. Sai wani rawar ƙafa take tana yi masa iyayi. Taso ta ji abinda yake faruwa kaman me amma ba ta ga fuskar tambaya ba hakan yasa dole ta ja baki ta yi shiru.

Yau kuma tana gama wanka bayan ta fito ta shirya da nufin fita can ta jiyo hayaniya ta tashin hankali a parlournsa.

Lallaɓawa ta yi tazo ta tsaya jikin ƙofar a hankali ta laɓe tana saurarensu.

Alhaji Ridwan ne a ciki, sai Yayarsa Hadiza da kuma wani ƙanin baban shi Baba Sa'idu da kuma Hajiya salamatu.

"Na rantse da Allah ba zan taɓa hari Faris ya auri jinin Galadima ba. Duk abinda za ku yi saidai ku yi, idan kuma ya ce sai ya yi to sai dai yaje babu ni babu shi...maƙiyinki har abada maƙiyinka ne, babu wani abin da za ka yi masa ka burge shi ko kuma shi ya burgeka... "

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Suka karɓa lokaci ɗaya jin wani irin ɗanyen hukuncin da yake neman yankewa.

Baba Sa'idu ya girgiza kansa ya ce.

"Wai kai Gimba wane irin mutum ne? Wane irin mutum ne kai wanda ba ya jin magana a rayuwa? Gabar da ke tsakanin ku da iyayen yarinyar nan da ban shi kuma aure zai yi..."

"To ni da wannan auren dai wallahy gwanda ya je ya ɗauko min karuwa wacce ta jima gidan bariki yace min ita zai aura bisa ga ɗiyar gidan Galadima..."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*BOOK ONE* *PAGE 52*

"Subhanallah!"

Hajiya Salamatu ta furta cikin tsananin mamaki da firici sannan ta sake cewa.

"Amma dai ko Alhaji baka da ɗabi'a ta ƙwarai domin wannan magana da ka faɗa ba ƙarama bace… ya kamata ka tsaya ka saurari kanka fa tun kafin mafita ta kuɓuce maka.."

Wani kallon uku saura kwata ya yi mata sannan yace.

"Ke har kina da bakin magana? Duk abunda ya faru ai kece sila domin kece kike hure masa kunne domin kun jima kuna goyon bayan Alhaji Mas'ood tun ba yau ba. Kuma wallahy Allah ya isa tsakanina dake tunda har kike goyawa Faris baya don kawai ya bijire min... "

Wani irin numfashi ne mai nauyi Alhaji Ridwan ya sauke yana girgiza kai cike da takaici ya ce.

" Alhaji Gimba… ka daina ɗaukar awa kanka wahala, Wannan ba abun faɗa bane aure ne wanda yaro da yarinya suna son juna..."

" SO?"

Alhajin Gimban ya katseshi da wata irin dariya mai cike izgili sannan ya ci gaba da cewa.

"Wane irin so? Wai har akwai Son da Faris zai iya yiwa wata Mace wanda zai sa ya raina ni ya nuna ban isa ba? Ni ne nan wanda ya raine sa, ya bashi abinci da tarbiyya, sutura, wurin kwana, makaranta, kuɗin magana! Ni da na yi masa duk wannan idan shi ɗan kirki ne har akwai wata Macen da ta isa ta sa ya bijirewa Umarnina?"

" Ba raini bane Alhaji Gimba. "

Baba Sa'idu yace yana mai gyara zamansa cikin nutsuwa yaci gaba da cewa.

" Faris yaron ne kirki ne mai biyayya wanda yasan abin da yake. Kawai dai kasan yaran nan zamanin nan idan suna son Mace rufe musu ido yake, sannan kada ka manta kai ma fa ka yi naka lokacin Kamar shi"

Saurin girgiza kansa ya yi ya ce.

"Ni ban taɓa saɓawa mahaifina ba! Na san cewa ina da rashin ji amma kuma ina da gudun zuciya wani lokacin..."

Girgiza kai Hajiya Hadiza ta yi tana kallon shi ta ce.

"Uhm! Gimba kenan! Ka dai manta ne amma abin da kayi ai ba ƙarami ba ne,Ya kamata ka tuno halayenka lokacin da ka ke saurayi wanda kai kanka na san idan ka tuna wani abun sai dai ya baka mamaki..."

A zabure ya miƙe tsaye cike da bala'i ya ce.

"To me kike nufi Hadiza? Wasu shekaru kika bani masu yawa da har kike tunanin kema bansan irin ƙurciyar da kika yi ba da ni kike so ki kwayemin baya?"

Kwantar da murya ta yi tana mai girgiza kanta ta ce.

"A a! Ni fa ba wani abu nake nufi ba, nidai ina nufin ka tausayawa ɗanka tilo ƙwallin ƙwal da kake da shi a duniya, tunda yarinyar nan ba wani halin banza ke gare ta ba don Allah na roƙeka ka bari ayi auren ka daina duk wannan abun,farin cikin ɗanka ai shi ne naka ko ba haka ba?"

Hajiya Salamatu ta amsa da cewa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull