Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 9

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 9

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 9: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 9. Hannu Maamin ta kai akan goshin sa zuwa wuyansa, aiko nan take ta…

3,311 words

Hannu Maamin ta kai akan goshin sa zuwa wuyansa, aiko nan take ta ji wani irin zafi sosai, hakan yasa ta sake waro ido ta kalli Ziyadah sai kuma ta kalle shi ta ce.

"Ya Allah! Maheer wannan zafin ya yi yawa! Wai miye yake damunka?"

zaunawa tayi a kusa dashi ta janyo kanshi zuwa jikinta tamkar wani ɗan ƙaramin yaro a tausashe ce.

"Maheer mi yake damunka?"

ƙara kwantar da kansa ya yi akan ƙafarta yana mai lumshe ido ya ce.

"Ki ci gaba da tayani da addu'a Maami kamar yanda kika saba..."

"Na san cewa tabbas mutuwa ba ta da sabo, musamman da kuka rayu tsawon lokaci ku biyu kaɗai har ka yi wayau da shi, ban isa na hana ka damuwa ba, but ka sassauta ka yi ta yi masa addu'a. Kai ne farin ciki na, kai ne ƙwarin gwiwa ta bayan iyayena da nake da su Maheer, idan wani abu ya sameka ban san ya zan yi ba...."

Kamar yanda Maamin ta share hawayenta haka itama Aunty Ziyadah tayi lokaci ɗaya tana share hawaye tana murmushi ta jinjina kanta tana kallon su ta ce.

" Ko ranar Aunty Shahida sai da ta tayar mana da firar rayuwar Doctor Tahameer da Maheer, wallahy soyayyar ɗa da mahaifi sai Allah. Allah dai ya gafarta masa ya ƙara jaddada rahamarsa a gare shi Ameen.."

Murmushi Maami tayi idon ta akan Ziyadahr ta ce.

"Tau Ameen....let me took him to hospital,zafin jikin ya yi yawa, kada ya zarce zuwa wani ciwon kuma."

Ganin da gaske bai da niyyar buɗe baki ya yi mata magana yasa suka shirya a gagauce ta kai shi private asibitinsu mai suna Tahameer Crescent Private Hospital dake nan kusa da su wacce ainahinta ta mahaifinsa ce wacce ya gina a nan da kuma Nigeria tun kafin ya rasu ya buɗe ta yake aiki a ciki, bayan ya rasu daga baya ta dawo gida taci gaba da gudanar da ita through ita da wasu dangin ta da kuma mutanen da ta ɗaura a kai.

Suna shiga nan take aka wuce da shi ɗaki na musamman inda ma'aikatan asibitin suka hau bashi kulawa yanda ya kamata.

Office ɗinta dake cikin asibitin suka wuce bayan sun tabbatar cewa ya samu bacci bayan an gama bashi treatment. Daman ita ɗin likita ce kamar tsohon Mijinta Doctor Tahameer Alee amma ba ta kama aiki a asibiti ba sai bayan da ya rasu.

Suna shiga bayan sun zauna ta kalli Ziyadah cikin damuwa ta ce.

"Ina cikin damuwar halin da Maheer yake ciki a 'yan kwanakin nan Ziyadah...tun da wurin aikinsa suka turasa zuwa Nigeria ɗin nan gabaɗaya ya canja tamkar ba Maheer ɗina ba, and na bibiyi rayuwarsa sosai a can ɗin sosai domin ko wurin dangin mahaifinsa bai je ba kamar yanda ya yi mini alƙawari...."

Cikin son fahimtar abinda take faɗa mata yasa Ziyadahr ta ƙara gyara zamanta tana mai fuskantar ta da kyau ta ce.

" Kamar ya kenan? Ina nufin miye kika gani a tattare da shi da har yake ɗaga miki hankali?"

" Hmm! Bana ce ina da wani reason kai tsaye ba, but abubuwa da yawa Ziyadah...domin gabaɗaya ya sauya, a duniyar da Maheer baya taɓa yi min Ƙarya no matter how...but yanzu idan ya faɗa mini magana ko yayane sai na samu ɗaya wacce ba gaskiya ba, sannan sai ya dinga tafiye-tafiye any how yana satar hanya, yana iya kwana biyu ko uku baya Oman ɗin nan Ziyadah. Har ta kai ta kawo Abiyh sai da ya ajiyesa ya tambayesa but still ansar sa ɗaya ce ta ba komai..."

Girgiza kai Ziyadah ta yi tana mai jan numfashi a hankali ta furzar sannan ta Kalli sistern ta ta tace.

" Aunty Laylah! Kada fa ki manta cewa Maheer yanzu ya kai matakin da zai iya handling kaso casa'in na daga cikin al'amarun rayuwar sa, because he's not a kid anymore....beside ke kanki kin fi kowa sanin irin tarbiyyar da ya samu da irin nutsuwarsa, at wannan stage ɗinda yake ciki, he has a personal issues ɗinda bai kamata ace kina interfering ba..."

Cike da mamaki Hajiya Laylahr ke kallonta baki buɗe ta ce.

" Ziyadah Maheer nawa yake gabaɗaya? Har akwai wani abu da zai iya fuskanta a duniyar nan ace wai ba zan iya interfering ba?"

" Aunty Laylah ina faɗa miki gaskiyar ne. Ke za ki riƙa ganin hakan kamar ba komai ba domin kece kika haife shi, kina ganin kamar jiya ne, but the truth is, he need some privacy now da yasa yake buƙatar ya yi handling wasu abubuwan personally...watarana aure zai yi Aunty Laylah..."

Still cikin rashin yarda da maganar Ziyadahr ta girgiza kai ta ce.

" Duk abinda Maheer zai zama Ziyadah, to me....shi ɗin yaro ne and dole na dinga bibiyar rayuwarsa...ko aure ya yi dole yana da buƙatata a cikin rayuwarsa..."

" Haka ne kuma Aunty Laylah. Yanzu dai duk mu bar wannan tukun, lafiyarsa ita ce gaba da komai. Allah ya bashi lafiya ya ci gaba da tsare mana su a duk inda suke...bari na tashi haka...."

"Amin Ziyadah, na gode. Allah ya tsare."

Har ta kai ƙofa sai kuma ta juyo tana faɗin.

"Yauwa....Da kina ciki na manta ban faɗa miki ba, Na kira Abdallah na ce mishi ya faɗawa Abiyh cewa Maheer yana asibiti."

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Ok to ba damuwa, na gode, sai an jima ki gaida gidan da su Ameer."

*******

Iyayen Anaam sun kasance 'yan asalin jihar Zamfara ne wanda shi Alhaji Mas'ood ya fito daga garin Bunguɗu ya yin da Mahaifiyarta Hajiya Nasmah take 'ƴar asalin cikin garin Gusau.

Alhaji Mas'ood ya taso a hannun iyayensa a garin Bunguɗu da shi da yayansa Salisu. Ya yi primary ya yi secondary daga nan ya fara bin Yayan sa Salisu zuwa tafiye-tafiyen kasuwanci. Shi Salisu a lokacin ya kasance yana sana'ar dabbobi daga Zamfara zuwa Lagos, yayin da shi kuma Mas'ood ya fara siyo kayan gini, irin su siminti, katako, ƙusoshi da sauransu.

Ya shafe tsawon shekaru uku yana zuwa yawon saye da siyarwa a Lagos ɗin, wanda a hankali Allah ya buɗa masa shima ya fara samu, daga nan sai janyo abokansa kuma amininsa tun a secondary wanda suka kasance garinsu ɗaya, Ridwan, Gimba da kuma Bala Kimba. Kai tsaye ya tallata musu kasuwancin sa sannan ya neme su da idan suna da sha'awa su zo su riƙa yi a tare. A lokacin kowa ya kawo kuɗin sa domin haɗaka amma Gimba shi kaɗai ne bai kawo ko biyar ba domin gidansu sun kasance sai a hankali, su Ridwan ɗin sun so a batse shi amma Mas'ood ya tsaya kai da fata yace lallai sai an yi da shi domin su ɗin sun zamo ɗaya. A haka suka tsunduma kasuwancin wanda biyu daga ciki suke zuwa Lagos biyu kuma suke tsayawa Gusau suna siyar da kayan.

A kwana a tashi kasuwanci ya shiga bunƙasa har suka buɗe shago na kansu a Gusau wanda a lokacin ne Mas'ood ya yi musu tayin su ci gaba da karatu domin samun ci gaban rayuwa amma a wannan lokacin duk suka ce a'a, su kwalin secondary school da suka yi ya ishesu. A haka suka ci gaba da gwagwarmaya wanda shi Mas'ood ɗin ya ci gaba da kasuwanci da karatu har sai da ya ci kusan shekaru biyu sannan Ridwan ya yi joining ɗinsa a haka suka samu suka kambala wanda Mas'ood ɗin ya riga shi kambalawa.

A kwana a tashi kasuwancinsu ya daɗa bunƙasa wanda a lokacin ne suka sake buɗe wasu manyan shaguna a nan Gusau ɗin da Bunguɗu, sannan suka ƙara samun hanyoyi a Lagos wanda a wannan lokacin ne Mas'ood ya kawo musu shawarar gwada zuwa China kamar yanda wani abokin kasuwancinsa Moses ya bashi shawara. A lokacin da yazo musu da shawarar duk sai suka ƙi amincewa, domin ganin suke kamar akwai haɗari idan suka ce za su gwada zuwa ƙasar da ba su san kowa ba, suna ganin kamar ma za'a iya cutar su gabaɗaya kuɗin kasuwancinsu su shige ciki su dawo ba su da ko sisi.

Daƙyar ya samu yayi convincing na su musamman Gimba da ya kafe yace lallai shi sam bai amince ba domin farar fata ba abun yarda ba ne. Kuma sai da suka yi rubutu cewa duk wata matsala ta faru da shi ko kuma aka samu wata asara to fa su babu hannun su a ciki kuma dole ya biya su kuɗin su.

Da haka suka amince amma daga cikinsu babu wanda ya yarda ya bishi zuwa China ɗin, Ridwan ne ma yaso ya tafi amma sai su Bala ɗin suka zuge shi yace ya fasa. shi kaɗai ya yanki ƙaddara ya tafi inda bai san kowa ba, bai iya yarensu ba, sai dai sauƙinsa ɗaya yana tare da Moses wanda shi ya saba ba zuwan sa na farko kenan ba.

Sai da ya shafe tsawon watanni shida cikin na bakwai sannan ya dawo bayan yasha gwagwarmaya ya wahala sosai,daga can ya yo sarin kayayyin wutar nepa, kayan gine-gine wanda basu yawaita a nan ba da sauransu ya dawo da su.

Bayan ya dawo suka shiga yin kasuwa sai ga shi nan take aka siyar da komai suka samu ribar da basu taɓa samun irinta ba. Sai murna suke suna ta saka mishi albarka amma duk da haka Alhaji Gimba shi sai ya riƙa ganin kamar ba shi kaɗai ya cancanci yabo ba tunda tare suke tafiyar da kasuwancin.

Komai na rayuwarsu a lokacin ya kasance ɗaya, su ɗin aminai ne, abokai ne en uwan juna. Komai za su yi sai sun yi shawara da juna. Sun yi aure a mabanbantan lokuta amma kuma babu wata tsera sosai a tsakaninsu. Bayan auren Mas'ood ne ya shirya ya koma China da zama ya shiga tafiyar da kasuwancin na su kamar yanda suka buƙata cewa ya tafi can ya zauna domin shi ya fi su shige-shige da iya mu'amala da mutane.

A kwana a tashi ci gaba sai samuwa yake, Ridwan yana Lagos yana kula da kasuwancinsu na can, Bala da Gimban suna nan Gusau suna kula da kasuwancinsu na nan shi Mas'ood yana China yana kula da kasuwancin can yana aiko musu da kaya, kwatsam watarana Alhaji Gimba ya tsiro da zancen cewa ya kamata ace wani daga cikin su shima ya gwada tafiya China sai Mas'ood ɗin ya dawo gida. Ganin yanda sunansa a hankali yake tashe yana zaga Nigeria su kuma babu wanda ya san su, kuma kasuwancin nan tare aka fara shi saboda haka ya dawo shi sai ya tafi. A wannan lokacin Hajiya Nasmah tana goyon Mukarram, Muhammad kuma yana primary.

Gudun rigima yasa suka tattaro suka dawo Nigeria shi kuma Gimba ya tafi amma ba don ran Hajiya Nasmah ya so ba. Suna nan sai aka fara samun matsala domin shi bai san yanda hulɗar ke tafiya a can ba. Daga can China ɗin sai suka yi rejecting ɗinsa domin yana da wuyar sha'ani kuma bai da cikakken ilmi akan wannan kasuwancin na su,nan suka ce idan Mas'ood bai dawo ba sai dai a rufe kasuwar ko kuma su nemi wasu mutanen amma ba su ba. hakan yasa ba yanda ya iya ya dawo tamkar zai mutu akan baƙin ciki.

Maimakon Mas'ood ɗin ya koma suka ce lallai sai dai Ridwan ya tafi, haka ya tafi shima aka yi ba daɗi ya tattaro ya dawo dole dai Mas'ood ɗin ya koma.

Wasa-wasa sai gashi abubuwa sun fara ɓaci tsakaninsu ganin yanda ake samun ci gaba, kuma cigaban nan duk tare suke samun sa na kuɗi, amma wai ba kuɗin suke yiwa ba, don mi sunan sa zai yi sama bayan tare suke komai amma su ba bu wanda ya san su. Komai dai Mas'ood Galadima komai Mas'ood Galadima, duk wani taro sai dai shi a gayyace shi ko kuma wata gamayyar kasuwa sai dai a neme shi.

Suna nan dai a haka, watarana suka samu wasu containers na farko da suka fara zuwa waɗanda suka zo kowa da sunansa, ma'ana kowa ta shi ta ƙashin kanshi wanda Alhaji Mas'ood shine ya tsara hakan yace su sauya salo wannan karon kowa a kawo masa kaya shi ka ɗai idan aka sayar kowa ya ɗauki kuɗin. A gwada wannan tsarin a gani. Domin yana so su sauya salon kasuwa, idan Allah yasa komai yaje daidai to kowa zai riƙa samun damar hulɗa da wanda ransa yake so, kuma kowace ƙasa suke so su tafi za su iya zuwa domin kasuwancin su. A wannan karon Kowa ya yi na'am da shawarar domin kuɗi ne za'a samu ba ƙanana ba,sai dai kuma....a wannan lokacin ne suka samu jarabawa wanda kwatsam labari ya same su cewa kayan gabaɗaya sun nutse a ruwa sai container ɗaya ce aka samu nasarar ceto wa amma sauran sai dai ayi haƙuri.

Da wannan suka samu matsala suka fara tashin hankali har ta kai ga Alhaji Mas'ood ɗin duk haƙurin sa sai da ya yi fushi yace a raba komai shi zai koma gefe ya ci gaba baya buƙatar kowa, daman duk laifin shi suka ɗauka suka ɗaurawa cewa laifin sa ne. Ga shi ta wannan dalilin containers ɗin ne har ta kai ga Alhaji Bala ya rasa ransa domin ya kasa jurewa har zuciyarsa ta buga ya mutu.

Bayan sun raba kasuwanci ne ya tsallake ya koma China ya shafe tsawon shekaru biyar sannan ba su sake jin labarin sa ba sannan daga baya ya dawo gida Nigeria ya buɗe kamfaninsa na farko mai suna Mas'ood Global Trade and Energy Ltd. A nan Gusau.

Haka rayuwa ta ci gaba tafiyar masa ya dawo yin gwagwarmaya shi kaɗai,sai dai shi da su Alhaji Ridwan akwai mutuncin nan, abotar nan da kuma aminantaka kamar ko yaushe, saidai Alhaji Gimba ya zame masa Ƙarfen ƙafa domin kullum cikin faɗa masa baƙar magana da habaici yake a duk inda suka haɗu. Ga mutanen duniya ko ba su san yanda al'amari yake ba, za su shiga fassara shi ta yanda ya yi musu daɗi. Zagi kam ko a wurin mutane Alhaji Mas'ood yasha shi ba kaɗan ba, domin ganin suke shi ne yaci amanar su ya kwashe musu dukiya sannan ya juya musu baya yaje ya haɗa baki da wasu ya cigaba da kasuwanci.

Shi kuma Sam bai damu ba, kullum tunanin sa ta ya ya zai juya taro ya dawo sisi ne haka yaci gaba da rayuwa.

Tun daga wannan abun da ya faru bai ƙara yarda da kowa ba, shi kaɗai ya kafa kamfaninsa yake ta gwagwarmaya har su Muhammad suka fara girma ya ɗora su a kai, musamman Muhammad wanda secondary school kawai ya kambala shima ya tsunduma shi a ciki wanda yana cikin kasuwancin kuma yaci gaba da karatu.

Mukarram ma ya jima a kasuwar ana komai tare da shi, sai bayan ya kambala karatun likitancin sa ya samu aiki a Indiya ya wuce.

A haka suka ci gaba da tafiyar da kasuwancin tsakanin Alhaji Mas'ood, Muhammad, da Naseer ɗan gidan Alhaji Salisu, sai wasu daga cikin danginsa mutum Uku da kuma Nameer yaron yayan Hajiya Nasmah Alhaji Yaƙub.

Bayan Mubarak shima ya kambala secondary ya tsunduma a ciki, a haka suka ci gaba da gudanar da kasuwanci wanda suka samu ɗaukaka sosai suka bunƙasa.

Duk da cewa kasuwancinsu ba'a tare suke yinsa ba, Alhaji Gimba ransa ya kasa yi masa daɗi. Kasuwanci kala ɗaya suke yi har yanzu domin da shi suka saba da shi suka yi wayau. Amma kuma har kwanan gobe ganin yake Alhaji Mas'ood ya tare komai domin ya fisu kuɗi ya fisu samun ɗaukaka. Ya samu contact da ƙasashe da dama ya yi suna wurin shigo da kayan wuta, kayan gine-gine da solar da sauransu, ya yin da yake ƙera wasu kayayyakin a kamfaninsa wanda a yanzu yana da branch a Abuja, Lagos, da kuma Kano wanda suke aiki dare da rana. Duk a cikin garuruwan nan, ya fi son zama Gusau domin ita ce tushen komai na sa.

Ci gaban labari.....

Shawarar Dr. Anil ba wai yana ƙinta ba ne, barin garin ne ya zame masa babban tashin hankali domin bai san yanda zai fara rayuwa a wani wurin ba bayan ya kafa daular sa a nan garin Gusau ɗin bayan ya gama gwagwarmaya. But daga ƙarshe da ya gama dogon nazarinsa kuma sai ya ga cewar farin cikin 'ƴar sa da walwalarta ta ya fiye masa komai da duk da abinda ya mallaka. Anaam ita kaɗai ce 'ya mace da ya mallaka a duniya, saboda haka matuƙar hakan shi ne abinda zai ba ta sabuwar rayuwa to ya shirya tafiya. Ba zai iya zama ba tare da ita a kusa da shi ba, da sun ce ta koma hannun Muhammad ko Mukarram ko wani ɗan uwa nasu, but ba zai iya bari ta yi nisa da shi ba, saboda haka ya shirya tafiya duk inda ya dace da rayuwarta.

Tun da suka tattauna da Dr. Anil kusan kwana uku kenan bai cewa kowa komai ba. Bayan Mukarram ya iso ne ya tarar da shi a ɗakinsa bayan sun gaisa ya ce.

"Alhaji Mi zai hana ka bani ita na koma da ita India, Aysha ba mace ce mai matsala ba, za ta kula da ita na sani, and kuma suna da kyakkyawar alaƙa da juna..."

Jinjina kai Alhaji Mas'ood ɗin ya yi yana kallon sa yace.

"Na sani,Aysha Mutuniyar kirki ce, kuma tabbas za ta iya kula mana da ita, itama Amina za ta iya kula mana da ita. Amma dai na fi son ta kasance a kusa dani Mukarram...daman bayan dogon nazari da nayi, na yanke komawa Abuja da zama. Kasuwancin mu gabaɗaya a nan yake, a nan yafi ƙarfi, saboda haka zamu ci gaba da zama a nan. Na yi waya da Dr. Anil na faɗa masa abin da na yanke kuma yace Abujar ma ba laifi..."

Cike da girmamawa ya ce.

" shi ke nan Alhaji, Allah yasa shi ne mafi alheri."

"Amin. Ya ya iyalin naka?"

"Lafiya lau, suna gaishe da ku."

"Muna amsawa. Mun gode."

Tea ya shiga haɗawa Wanda suna yi suna taɓa fira har su Mubarak ɗin suka yi joining na su.

Muhammad bayan ya kammala wayar da yake ya kalli Alhajin na su ya ce.

"An shirya komai Alhaji, gidan ya kambala..."

Mubarak ne ya kalle shi ya ce.

"Amma dai ina fata duk ma'aikatan da ke nan ba'a buƙatar su a can?"

Mukarram ya ce.

"Ko ɗaya daga cikin su ba za'a je da shi ba, Nene ce kaɗai za'a tafi da ita. Ni daman gabaɗaya ma'aikatan gidan nan ban ɗauke zargina akan su ba gameda shigowa gidan nan da akayi har yanzu...."

Jinjina kai Yaaya Muhammad ya yi ya ce.

"Daman ban tsara da su ba. Kuma tun da har Allah yasa ka iso...Gobe in sha Allahu sai mu tattara mu tafi.." ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 14*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Gidan Alhaji Gimba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull