Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 8

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 8

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 8: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 8. " Yanzu Umma Fitinar da za ki zo har gidana ki kunna mini kenan? "

3,360 words

" Yanzu Umma Fitinar da za ki zo har gidana ki kunna mini kenan? "

" Eh ɗin! Ai kune kuka fara, domin faɗin gaskiya ai ba laifi ba ne...."

Wani kallon banzar Hajiya Hanne ta sake jefa mata tace.

"Faɗin gaskiya ina gaskiyar a nan? Daman dai munafurcin ki ne ya dawo dake kamar yanda kika saba, idan ba shi ba ku da kuka zo shekaranjiya ba biki ba ba suna ba miye kuma ya sake dawowa dake yau..."

"Na ga dama ne Hajiya Hanne.."

"Wallahi idan kika ci gaba da yi mini rashin kunya Umma yanzun nan zan yi ƙasa-ƙasa dake a nan.."

"Haifata ki ka yi Hajiya Hanne? Na ce Haifata ki ka yi?"

Faɗa sosai ya kacame a tsakanin su musamman da ƙanwar su Hajiya Nasmah ta iso Hajiya Nafisa wacce ita ce auta a garesu, sai musayar baƙaƙen kalamai tamkar wasu maƙiyan asali.

Bayan sun jima suna cacar baki suna rashin arziki tamkar za su tada gidan, daƙyar aka samu Mubarak ya shigo ya raba su wanda dawowarsa daga kasuwa kenan. Da roƙo da lallashi da komai ya samu su ka saurara.

*********

Bayan Abbah ya dawo aka kira Baba Salisu, sosai sabon rikici ya ɓarke domin ran Abba ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ganin yanda Anaam duk ta gigice ta haukace ba ji ba gani tamkar wata sabuwar mahaukaciya.

Lokaci ɗaya gabaɗaya hankalin kowa na gidan ya ɗaga ganin irin yanda ta gigice sosai.

Da ƙyar Mubarak, Nasir (Yayan Na'imatu) da kuma Baba suka taru wurin bada haƙuri. Wanda sun ji ma ba su ga fushin Abbah irin haka ba, kai ko a lokacin da abin nan ya faru da wanda Alhaji Gimba ya yi musu bai ɗauki zafi haka sosai ba because a lokacin ba ta ma cikin hayyacinta.

But yanzu Allah ya taimake su sun fara ganin haske a tattare da lamarin ta shi ne za ta zo ta nemi ɗaga mata hankali.

Sun jima parlourn Abbahn suna zaune ba tare da ya ce komai ba.

Ganin hakan yasa Alhaji Salisu kallon Abbahn ya ce.

"Mas'ood ka yi haƙuri! Rabi'atu ba ta kyauta ba."

Jinjina kai ya yi ya ce.

"Haka ne Alhaji Salisu. Da Rabi'atu da Anaam dukkan su nawa ne, kuma duk wanda a cikin su ya nemi cutar da ɗan uwansa ba zan ji daɗi ba. Ta ya ya ace tana matsayin 'ƴar uwar ta amma ace ita ce za ta nemi ɗaga mata hankali...sannan kuma su dawo daga baya su mayar min da gida gidan dambe..."

"Haka ne. Amma ka yi haƙuri, kasan sha'anin mata musamman Ummu Salma, kaima kasan irin haƙurin da nake da ita."

Girgiza kai ya yi ya ce.

"Allah ya kyauta."

Baba Salisu ya ce amin. Sannan ya mayarda kallon sa gun Nasir yana faɗin.

"Magana ta gaba kuma, Nasir ne ya zo da zancen ƙarin aure shi ne nace masa ya zo ya sanar da kai."

Daga Abbah har Mubarak juyawa suka yi suna kallon Nasir ɗin. Wanda daga ƙarshe Abbah ya jinjina kai ya ce.

"ƙarin aure Nasir? Auren ka shekara nawa ne?"

Shiru Nasir ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba wanda sai Mubarak ne ya kalli Abbahn ya ce.

" Shekara huɗu cikin ta biyar ne."

Jinjina kai Abbah ya yi tare da kallon Nasir ɗin ya ce.

"Akwai wata matsala ne tsakanin ka da iyalin naka Nasir?"

Da sauri ya girgiza kansa ya ce.

"A'a Alaji. Babu wata matsala gaskiya, kawai dai ina so na ƙara."

"OK.. Za mu yi magana In Sha Allah .Allah ya yi jagora."

"Amin Alaji na gode sosai Allah ya ƙara girma."

"Amin."

******

Gefen Hajiya Salamatu kuwa, tunda Alhaji Gimba ya zo mata da zancen auren sa bacci ya ƙauracewa idanun ta. Sosai ta tsoro ta da al'amarin domin ba ta san wacce ce zai ɗauko mata ba tana zaman-zaman ta.

Ta jima zaune a gefen gado sannan ta ga ya farka a hankali ya sauka ya je toilet ya dawo.

Zaunawa ya yi ya kalle ta ya ce.

"Wai Hajiya Salamatu lafiyar ki kuwa?"

Girgiza kai tayi murya a karye ta ce.

"Ba zan ɓoye maka ba Alhaji. Maganar gaskiya ina cikin damuwa da zancen auren nan naka. Dan Allah ka fasa auren nan..."

Cikin ɗaga muryar tamkar ba dare ba ya fara bala'i yana faɗin.

"Ai sai ki je ki yi ta yi Hajiya Salamatu, ƙarshe hawan jini ya kama ki, zuciyar ki ta buga ki mutu ki huta. Kuma wallahy ba zan fasa auren nan ba kinji na gaya miki. Idan ma za ki sararawa kan ki ki sarara, idan kuma ba za ki sarara ba ki je ki yi ta yi."

Daga haka ya koma ya kwanta ya juya mata baya. Kallon shi kawai take ba tare da ta ɗauke idonta ba sai kuma taga ya sake miƙewa zaune yana kallonta ya ce.

" Kuma let me give you a sound warning...wallahy kada ki yarda in ji ko in gani cewa wai kin kai ƙarata wurin Alhaji Mas'ood ko Alhaji Ridwan kin ji na faɗa miki. Ban amince ba, ban yafe ba idan kika kai maganata wurin su, idan an yi can a baya yanzu na rufe na datse alaƙar. Idan za ki zauna a haka mu zauna ki zauna, idan kuma kinga ba za ki iya ba, ƙofa a buɗe take za ki iya tafiya..."

Cikin jin wasu irin hawayen baƙin ciki ta kalle shi ta ce.

" Alhaji ni yau ka ke cewa in tafi?"

"Eh to, na ga kamar haka kike buƙata Salamatu. Ko kuma idan naga za ki kawo mini matsala wallahi sai in tattara nawa da nawa in tsallaka wata ƙasa can wanda sai kin shafe shekaru baki ganni ba."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 12*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzartq shiga wannan link.💃💃💃

A razane Alhaji Galadima ya kalli Hajiya Nasmah jin wata irin magana wacce sam zuciyar shi ba za ta iya ɗauka ba. Girgiza kai ya yi cike da karaya ya sake mayar da kallon shi gun Anaam ɗin da ke kwance a jikin Ammie kamar ruwa ya ce.

"Nooo! Hajiya Nasmah Noo....Anaam ba ta mutu ba...taya ma za'a yi ta mutu?"

"Haba Alhaji! Kada ka yi saɓo mana...."

Juyawa ya yi da sauri yz koma ya ɗauko waya ya kira likitansu wato Doctor Anil a gaggauce ya sanar da shi abinda yake faruwa in brief.

Ɗakin ya dawo wanda koda ya shigo ya tarar Na'imatu ta kawo ruwa suna yayyafa mata amma ko alamar motsi ba ta yi ba.

Shi kan shi a gigice yake, but yanayin yanda Hajiya Nasmah ke kuka sai ya ƙara karyar masa da zuciya domin ba ƙaramin tausayi itama ta bashi ba.

Jinjina kai ya fara yana kallon fuskar ta a tausashe ya ce.

"Dr. Anil yana kan hanyar zuwa,...please ki daina kukan nan, in sha Allahu ba ta mutu ba....ki tuna ta shiga halin da ma yafi wannan kuma cikin ikon Allah ta kuɓuta....to ko a wannan ma ina so ki ƙarfafa zuciyarki tare da yi mata addu'ar Allah ya bata ikon cinye wannan jarabawar da ta same ta..."

*****

Dr. Anil na isowa gidan ko gama gyara parking bai yi ba ya fito da kayan aikinsa ya shige ciki.

Ɗaya daga cikin securities ɗin gidan da ake kira Junayd ne ya zubawa Dr. Anil ido yana kallon sa jiki a sanyaye har ya shige cikin gidan.

Tabbas da shi aka haɗa baki har su Jud suka yi nasarar shigowa gidan, but har ga Allah bai san cewa wai za su cutar Madam Anaam ɗin su ba. Ya ɗauka cewa kuɗi kawai za su karɓa su tafi kamar yanda suka yi masa alƙawari,ashe sun san abin da suka shirya na cutarwa ga Ahlin uban gidansa.

Anaam ta kasance mace mai kirki da ba zai taɓa manta alherinta ba. Albashi duk ta kwatanta ko ba su cancanci ƙari ba sai ta roƙar musu Abbahnta cewa ya kamata a ƙarawa wane da wane kuɗi kaza domin suna da iyali waɗanda suke ɗauke da nauyinsu a kafaɗarsu, idan ana ƙara albashi hakan zai taimakesu su samu damar kula da iyalinsu. Ita kanta tasha yi musu alheri ta hanyoyi da dama ga sauƙin kai da sanin ya kamata.

Alhaji Galadima ma mutumin kirki ne wanda yake girmamawa ma'aikatansa yake kuma kula da haƙƙoƙansu daidai gwargwado, amma wai yau shi ne ya haɗa baki da wasu waɗanda bai taɓa sanin su ba, basu taɓa amfanar shi da komai ba ya yi musu hanya suka shigo suka cutar da mutumin da ya yarda da shi. Son zuciyar sa ya kai sa ya barosa. Ga kuɗi sun bashi har million biyar amma ya kasa taɓa ko naira biyar ciki akan tashin hankalin da yake ciki. Bai san ma ta ina zai fara ba, tunda wannan abun ya faru gabaɗaya gidan ya juye sama ƙasa kamar ba kowa a gidan. Gidan mai cikakke zaman lafiya da farin ciki wanda hatta su kansu ma'aikatan gidan ba'a bar su a baya ba wurin samun jindaɗi da walwala da kuma samun girmamawa ga duk Ahlin gidan.

Yanzu wannan abun ina daɗinsa? Ta ina zai fara idan yace yana so ya gyara kuskurensa? Rayuwar da Ahlin gidan suka shiga ta ɗaga mai hankali, baccin kirki ma wannan baya iya yi,ko a gidansa yake baya iya bacci ballantana idan hutunsa ya ƙare ya dawo aiki. Haƙƙin su ya sani...har abada ba zai bar shi ya zauna lafiya ba....to amma yanzu idan ya ce zai yi musu bayani ta ina zai fara? Ina zai samo su Jud waɗanda ko cikakken sunansu bai sani ba, bai san ma daga ina suke ba...kai! Kwaɗayi dai mabuɗin wahala....

Muryar Adam abokin aikinsa na yau da yaji ita ce ta dawo dashi daga mummunan mafarkin da ya shiga na rashin makamar abin da zai yi don ya wanke kansa.

"Junayd wai lafiya?"

Girgiza kansa ya yi da sauri ya kalli Adam ɗin yana mai ƙoƙarin daidaita kansa ya ce.

"Lafiya lau. Mi ka gani?"

Ɗan ware hannu Adam ɗin ya yi alamar ba komai, ya ce.

"No...kawai dai ina ɗan observing ɗinka a 'ƴan kwanakin nan gabaɗaya ka canza....Junayd kodai da kai aka haɗa baki da mutanen suka shigo gidan nan??"

Wata irin zabura Junayd ya yi yana mai yi wa Adam ɗin wani kallo ya ce.

"Subhanallah! Wannan wace irin maganar banza ce Adam? Yanzu ni za ka danganta ga irin wannan mugun aikin mi na maka da zafi haka?"

Da sauri Adam ɗin ya girgiza kai yana murmushi ya ce.

"kai mutumina wasa fa nake...kawai naga duk ka yi wani sukuku ne..."

Wani irin murtuƙe fuska ya yi tare da saurin ɗaga masa hannu ya ce.

"No wannan ba wasa bane Adam! Idan kana zargi na ne kawai ka fito ka faɗamin...amma idan ba shi ba, ta ya ya kawai za ka kalli idona ka ce wai ni na shigo da ɓaray..."

Cikin alamun lallashi Adam ya ce.

"Dan Allah ka yi haƙuri Junayd...wallahy ni da gaske wasa nake maka, naga ka wani ɗau zafi...."

"Ba dole in ɗauki zafi ba! Ni wallahy zan iya ɗaukar wa kowane ne mataki matuƙar yace zai shiga rigar mutunci na. Idan ba shi ba taya za ka jinginani ga irin wannan mummunan laifi..."

Tafiya ya fara yana ci gaba da faɗin.

"Ni wallahy dole ma na kai ka ƙara domin a ja mini haƙƙina na wannan ƙazafin da ka yi min..."

Cike da fargaba Adam ya zabura da sauri ya riƙo hannunsa yana faɗin.

"Dan Allah Junayd ka yi haƙuri...wallahy ni wasa nake maka."

Tsayawa ya yi cak har sai da ya gama sauraren sa sannan ya jinjina kai alamar ya haƙura ya ce.

"Na haƙura tunda ka bani haƙuri, shi ke nan komai ya wuce,amma ka sani daga yau kada ka sake yi min wasa irin wannan na faɗa maka."

*******

Dr. Anil yana shiga ba ɓata lokaci ya shiga duba ta wanda cikin hours ɗinda ba su gaza biyu ba sai ga numfashinta ya dawo jikinta.

Haka ya jera tsawon sati biyu yana zaryar zuwa bata kulawa wanda daga ƙarshe ya wuce parlourn Abbah bayan ya gama duba ta ta samu bacci suka zauna domin tattauna magana kamar yanda yace tare da Mubarak da Yaa Muhammad da ya zo jiya.

Sun jima zaune tsawon lokaci ba tare da Dr. Anil ɗin ya ce komai ba. Hakan yasa Yaa Muhammad ya kalle shi murya a sanyaye ya ce.

"Dr. Anil ka yi shiru tsawon lokaci baka ce mana komai ba....please explain to us gaskiyar abin da yake faruwa da Anaam ɗin..."

Lumshe ido Dr. Anil ɗin ya yi a hankali sannan ya buɗe ya kalli gefen Abbah wanda yake zaune tunɗaxu ya zuba masa ido yana saurarensa ya jinjina kansa ya ce.

" while....i want explain something very important Wanda zai sa ku fahimci halin da 'ƴar ku take ciki sannan har ya baku damar taimaka mata. Magana ta gaskiya Anaam ba wai tana fatan mutuwa ba ne a yanzu....a'a, she's trying to escape pain ɗinda yake cin ruhi da gangar Jikinta....she suffers a lot tun daga wannan ranar da abun nan ya faru da ita har zuwa yanzu...."

Girgiza kai Abbah ya yi idanun nan jajir tamkar zai yi kuka ya ce.

" Doctor Anil na kasa ina ne na yi kuskure....ni sam ban san cewa na taɓa cutar da wani da har abin ya yi girman da zai iya cutar min da yarinya haka ba....na yi mata alƙawarin rayuwar farin ciki da samun duk wani gatan da 'ƴa take samu a wurin mahaifi....but I fail..."

"You didn't fail her as a father Alhaji Galadima....daman kana naka Allah yana na shi, and Allah's plan is the best,duk Bawa bai isa ya kauce wa ƙaddararsa ba. What Anaam needs now Shi ne tsantsar kulawa. Yes...she need more than love..."

Ya ƙarashe maganar yana mai kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya tare da jinjina kansa alamar basu tabbaci.

" Because ga irin abin da ya faru da rayuwarta....she needs a new environment. Yes....tana da buƙatar canjin muhalli. She associate her current environment with shame, fear, and the rape trauma. Every place...i mean, school, kasuwa, gidan ƙawaye buki da sauransu...waɗannan da na lissafo maka, za su ci gaba da tuna mata da komai kamar yanzu ne yake faruwa..."

Jinjina kai Yaa Muhammad ya yi ya ce.

" Yanzu Doctor kana nufin kenan ta canja gida, unguwa, gari baki ɗaya? "

"Honestly speaking Mr. Galadima, idan har ta ci gaba da zama a nan...the healing process will be very low, and akwai high chances na ta yi ta attempting cutar da kanta wanda watarana sai dai a tarar da Ita babu rai....ko kuma ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta wacce za ta iya zamowa sanadiyyar haukacewar ce ta ko kuma wani abu makamancin haka...."

Sai yanzu Ammie dake tsaye jikin ƙofa wacce tunda ta shigo ta tsaya daga can tana saurare ba tare da ta samu ƙarasowa ciki ba ta fashe da wani irin kuka tana girgiza kai tana faɗin.

" Innalillahi wa inna ilaihi! Waɗan nan mutanen haƙiƙa kun zaluncemu kun kuma zalunci wannan yarinyar cuta mai girma. Allah ya isar miki ya isar mana Anaam, yanda kika kasance a baƙin ciki da damuwa tsawon lokaci Allah ya haɗa su da baƙin ciki da damuwar da tafi taki...."

Miƙewa tsaye Abbah ya yi yana kallon Dr. Anil ɗin ya ce.

"Nan fa shi ne gari na Dr. Anil, nan shi ne inda tushen kasuwanci na yake..."

"Idan akwai biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba Alhaji Galadima. Anaam needs a calmer environment,..."

Sai yanzu Mubarak ya ɗago a sanyaye ya ce.

"Doctor School ɗinta fa? Yanzu zuwa school shi ma zai Iya zamanto wa barazana ga lafiyar ta?"

"Makaranta can ne First step da zai iya taimaka mata wurin canja tunanin ta da kuma sanya ta manta rayuwar ta ta baya...because it can become part of her healing especially if the place. Ba lallai ta iya manta abin da ya faru da ita ba. But za ta iya koyon yanda za'a riƙa manta abubuwan da suka faru a baya....right now she's drowning in memories...bad memories. Ku ja ta a jiki, ku nuna mata soyyaya, kada ku taɓa barinta ta zauna ita kaɗai, In sha Allah komai zai yi daidai..."

"Thank you so much Dr. Anil. In sha Allah haka za'a yi. Allah yasa mu dace amin."

*****

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, Maami na zaune parlour ita da wata cousin sistern ta Ziyadah Maheer ya shigo parlourn sanye da simple wears wanda da alama ma daga bacci ya taso.

Wuri ya samu akan kujerar 2 seater ya faɗa tamkar wani ɗan maye tsabar yanda yake jin jikinsa ba daɗi.

A tare suka haɗa baki wurin tambayarsa.

"Are you Okay??"

A hankali ya ɗaga ido ya kalli Ziyadah yace.

"Aunty Ziyadah ina kwana?"

"Lafiya lau Maheer, ya kake?"

Kallon shi Maami ta yi calmly ta ce.

"Na ɗauka ka jima wurin aiki. Why are you home?"

Resting bayansa ya yi jikin kujerar tare da lumshe ido yana mai girgiza kai ya ce.

"I'm sick Maami...seriously sick. Wani abu yana damuna sosai..."

A ruɗe ta wani kalle sa ta ce.

"Mike damunka ɗin? Tell me what's that?"

"something I can't tell..."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 13*

https://chat.whatsapp.com/KgJnAzr5KBoJ9YAa2LxG8w

*Albishirinku jama'a shin ko kuna da labarin katafaren group ɗin mu, da mu ke tura KAYAN KITCHEN da KAYAN ƊAKI, har ma da KAYAN YARA MAZA DA MATA, ba mu tsaya a nan ba duk wasu abubuwan da UWAR GIDA DA AMARYA HAR DA 'YAN MATA masu CAPACITY ke bukata muna turawa, kayan mu na kasashen ketare ne kama daga Kayan kitchen, Kujeru da gadaje har da atamfofi, laces da Abaya, fashion net da bedsheets, hijabs gowns, caps, ribbons duk muna da su akan farashi mai RAHUSA, ga masu sayen ɗaya ko sari muna turawa ko'ina a cikin aminci, mutanen mu na kasashen waje kamar Chadi, Nijar, Kamaru, Ghana duk ba'a bar ku baya ba muna tura muku kaya har kasashen ku. Farashin kayan mu tamkar sari ne zaku saye har ku ɗaura ta ku riba kuma muna discount.

Ga masu bukatar kayan mu sai ku hanzarta shiga wannan link.💃💃💃

Zafi yake ji sosai a ƙirjinsa, zafi mai ƙona dukkan wata gaɓa ta jikinsa idan ya tuna da yanda yaga yarinyar ta wani rikice ta gigice daga yi mata magana, Hakan yana nufin shi abin tsoro ne ko me? Kasancewarta cikin Ƙoshin lafiya shi ne muradinsa a yanzu, idan har bata cikin kwanciyar hankali bai san yanda zai kasance cikin nutsuwa ba shima. Da ace ana iya dawo da hannun agogo baya a rayuwa tabbas da ya aikata hakan ko don gyara kuskurensa na baya.

"Maheer..."

A hankali idanuwansa ke buɗewa da rufewa akan fuskar Maamin tasa wacce ta ɗaga hankalinta sosai jin furucinsa na cewa wai wani abu yana damunsa wanda ba zai iya faɗa ba.

Sosai yake wata irin zufa tamkar wanda Kunama ta harbe shi, hoton Anaam na dawo mishi a yanda ta gigice daga sallama kamar yanxu ne abun yake faruwa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull