Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 7

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 7

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 7: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 7. Wani matashi ne tsaye a gefen control zone Wanda zai kai shekaru…

3,364 words

Wani matashi ne tsaye a gefen control zone Wanda zai kai shekaru talatin da biyar a ƙalla. Sanye yake cikin navy blue safety coverall Mai ɗauke da tambarin Al-noor maritime and shipping LLC. A kansa akwai white safety helmet wato hular bada kariya, yayin da wuyansa ke maƙale da ID card ɗin aikinsa da kuma Tag ɗinsa mai ɗauke da sunansa a gefen ƙirjinsa ɓangaren dama. Digital handheld radio ce a hanunsa na dama yayin da ɗayan hannun ke riƙe da wata ƙaramar tab da yake aiki da ita.

Digital handheld ɗinda ke hannunsa ce ya ɗaga a hankali ya fara magana cikin sautinsa na zaƙaƙurin ma'aikaci yana faɗin.

"Crane 3,slow down...Reduce speed by 5percent...i repeat, reduce speed by 5percent."

Wasu dogayen jiragen ruwan ne masu fili sosai domin ɗaukar containers suka matsa zuwa inda waɗan can manyan jiragen ke tunkarowa, ya yin da ma'aikata waɗanda ke aikin sauke kayan suka wuce da sauri sanye da kayan aikin suka jera suna jiran a basu umarni.

Har yanzu idonsa na kan jiragen ba tare da ya ɗauke ba na tsawon mintuna sannan daga ƙarshe ya ɗaga hanunsa mai ɗauke da tuta yana yi musu alama tare da yin magana a handheld ɗinsa ya ce.

"Hold it there..."

Cike da ƙwarewa suka aika ta abin da yace nan take.

Ƙara matsawa ya yi yana jinjina kai ya ce.

"Perfect! Secure the container, I repeat secure the container..."

Ƙarar na'urori ce ta karaɗe wurin tare da ƙarar chains ɗinda ke rirriƙe da containers ɗin da kuma wasu engine ɗin da ke can cikin ƙasan ruwan.

Handheld ɗinsa ce ya ji ta ɗauki ƙara da faɗin.

"Dear Supervisor...incoming message from Singapore requesting docking clearance...i repeat..requesting docking clearance..."

Jinjina kai ya yi tare da mayar da amsa ya ce.

"Clearance approved...proceed to Dock..supervisor MAHEER TAHAMEER ALEE...I ordered. Clearance approved."

Abin da ya yi ta maimaitawa kenan har sai da aka kambala sauke kayan gabaɗaya sannan ya yi signing documents ɗin kayan daga ƙarshe ya koma zuwa office ɗinsa bayan ya tabbatar babu wani sauran aikin da ya rage masa a yanzu dai.

Sallar azahar ya gabatar, bayan ya kambala ya janyo wayarsa dake ta faman ringing ba tare da ta saurara ba har sai da ya kammala sallar.

Lumshe ido ya yi a hankali tamkar wani mai jin bacci duk da a wani gefen rashin bacci ya yi tasiri sosai a wani ɓangaren na rayuwarsa a wannan lokacin.

A hankali ya kai wayar saitin kunnensa tare da faɗin.

"Maami..."

Ajiyar zuciya ta sauke daga can ɓangaren sannan ta girgiza kai tamkar yana a gabanta ta ce.

"Maheer where are you?"

A sanyaye ya ce.

"Maami Ina wurin aiki na fa..."

"Are you sure?"

"Oh Common Maami trust me mana.."

Jinjina kai ta yi sannan ta ce.

"Uhm! OK to! Allah ya tsare ya taimaka ya kuma dawo da kai lafiya."

Murmushi ya yi na gefen baki sannan ya ce.

"Amin yah Allah Maami. Thank you so much. Bye"

Lumshe idonsa ya yi tare da resting bayansa jikin kujerar da yake zaune a gefenta ransa fal da tunanin irin yanda Maamin tasa ta ɗauke sa tamkar wani ƙaramin yaron goye a yanzu, sam ba ta barin sa ya yi nisa, daga zaran ta ji shiru na en awanni za ta fara kiransa tana tambayar a ina yake.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 10*

Har ya ƙara so cikin parlourn ta kasa ɗauke idonta a kansa, ganin yan da yake ta wani farin ciki yana washe haƙora kamar gonar auduga.

"Ya ki ke mini wani kallo haka ne kamar yau ne kika fara ganina Salamatu?"

Ya faɗa yana mai tsatstsare ta da ido ganin irin kallon da take masa tamkar yau ne ta fara ganin sa ɗin da gaske.

Jin irin maganar da ya jefa mata yasa ta girgiza kai ta ce.

"A'a! Mamaki kawai na ke. Shi Faris ɗin ne ka nemowa aure?"

Girgiza kai ya yi ya ce.

"A'a. Ko ɗaya Hajiya Salamatu. Uban Faris dai ne ke shirin gwangwajewa ya angwance kwanan nan..."

Cikin zallar mamaki ta wani kalle sa ta ce.

"Aure Alhaji?"

Jinjina kai ya yi yana mai ƙara gyara zamansa da kyau saman kujerar da yake zaune ya ce.

"Ƙwarai kuwa."

"Auren Lafiya Alhaji? Aure fa ka ce?"

"Miye ki ke wani zare ido to kamar na faɗi wani babban zunubi? Aure zan yi next week idan Allah ya kai mu..."

Duk yanda Hajiya Zaliha ta so ta nuna juriya ta kasa aikata hakan, domin wani irin tsoro ne ya shige ta lokaci ɗaya tare da jin yanda zuciyarta ta hau wani irin lugude akan tsantsar mamaki da al'ajabi.

Jiki a sanyaye ta kalli mai aikin ta ta Ramatu wacce ke zaune kanta a sunkuye ƙasa tana jiran umarninta ta ce.

"Ramatu ta shi ki je, iya abin da za ki siyo min kenan."

Miƙewa Ramatun ta yi tana faɗin.

"Tau Hajiya."

Bayan ta fice ne Hajiya Salamatun ta sake mayar da kallon ta gun Alhajin wanda ya wani daddage yana ta danna waya da alama akwai abin da yake mai muhimmanci.

"Yanzu Alhaji muna zaunenmu zaman lafiya hankalinmu kwance za ka takalo wani aure kuma?"

A hankali Faris ya ƙarasa saukowa ƙasan yana mai gyara zaman necktie ɗinsa da kyau ya kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ya kalli kayan da ke jere tsakar parlourn na su ya ce.

"Ya naga kaya haka? Kuma Na ji kina zancen aure Mom, waye zai yi aure? I hope ba ni ba ne?"

Wani kallon uku saura kwata Mahaifin nasa ya yi masa sannan ya ce.

"Waye yake ta taka? Ai sai ka yi ta zama nan har mahadi ya bayyana Farisu. Kuma wallahy idan za ka yi shekarun ƙasa har abada ba zan taɓa amince maka da ka auri Anaam ba..."

Ajiyar zuciya Hajiya Salamatu ta sauke tana mai furzo da zancen da ya fiye mata ta ce.

" Shi ne fa nan goɗai-goɗai da shi wai aure zai yi.. "

A mamakance Faris ɗin ya kalle ta sai kuma ya kalli Dadyn nasa ya ce.

" Aure? Daddyn ne zai yi aure?"

Jinjina kai Alhaji Gimba ya yi cike da confidence ya ce.

"Ƙwarrai kuwa! Ni ne nan zan yi aure. Idan kuma akwai ubana a cikinku ko kuma uwata sai a samu mai hanani in gani..."

Cike da wani sabon takaicin ta ce.

"Amma dai Alhaji Wallahi ka ji kunya! Wane irin aure muna zamanmu lami lafiya, ka ɗauko mana fitina, gaibu ka kawo. Gidanmu mai zaman lafiya zai dawo gidan tashin hankali..."

Miƙewa ya yi tsaye yana mata wani kallon kin ma rainawa kan ki hankali ya ce.

" Wai dawa za ki yi tashin hankalin Salamatu? Na ce dawa za ki yi tashin hankalin? Ba dai da amaryata ba ko? Na rantse da Allah duk na kawo Maimunice gidan nan wani ya ce zai ɗaga mata hankali sai na yi mai rashin mutunci. Shi kenan gidan nan kullum ni kuke juyawa baya? Wai ki koma kina goyon bayan maƙiyina kai kuma har da cewa sai ka auri 'yarsa..."

Girgiza kai Faris ɗin ya yi yana kallon Daddyn na shi jiki a sanyaye ya ce.

" Noo Daddy please Dan Allah kar ayi haka. Ka barmu mu ci gaba da zamanmu a yanda muke...."

"Na rantse da Allah Farisu sai na yi wannan auren! Ai dole ma na yi sa ko Uwar taka za ta shiga hankalinta. Shi ke nan ni kullum ba'a kan daidai nake ba? Komai na yi sai ta ce ba haka ba, komai na yi sai ta ce na yi kuskure, wato ita ga 'ƴar masani ko?"

"Daddy please za ta canja..."

Hannu Hajiya Salamatu ta ɗagawa Faris ɗin alamar ya dakata ta ce.

"Faris dakata. Wai ma akan me ka ke ta wani roƙonsa? In dai akan dalilin faɗa maka gaskiya da nake ne kace za ka yi wannan auren kaje Allah ya baka sa'a..."

Hannu ya ware alamar oho yana mai yi mata wani kallon ya ce.

"ai ba waɗan nan dalilin kaɗai ba ne. Ina da dalilai na masu yawa da yasa nake so na yi wannan auren, domin ke ɗin gabaɗaya kina da wani baƙin hali ne da mugun nufi a kaina...."

"Ohh! Duk tsawon shekarun da muka share ni da kai ba ka taɓa sanin ina da wata matsala ko kuma wani aibi ba sai yanzu? Saboda ka cika butulu? Bayan neman auren naka duk bai ishe ka ba sai ka haɗa da ci mini fuska da tozarci...."

"Shin yanzu za ki shirya aje kai lefen nan dake ko kuma su Hadiza su zo su ɗauka?"

Girgiza kai ta yi cike da baƙin ciki tace.

"Ba zan je ba Alhaji. Allah ya baka sa'a ya sanya alheri...."

Wani murmushi ya yi ya ce.

"Ameeennn! Sai yanzu ki ka yi magana Hajiya Salamatu..."

Daga haka ya kara waya a kunnensa ya nufi hanyar waje yana faɗin.

"Halo Alhaji Sama. Kaga katin gayyata ko?....eh ni ne zan yi aure wani sati idan Allah ya kai muna rai..."

Kallon fuskar mahaifiyar tasa ya yi cike da damuwa ya ce.

"Wai dan Allah Mom da gaske Daddy yake yi ko dai wasa? Aure fa Mom?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"Hmm! Faris babu zancen wasa a cikin wannan maganar da yake. Mu zuba masa ido kuma mu yi ta addu'a Allah yasa auren ya zama shi ne mafi alheri."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.

"To Amin Mom. Ki yi haƙuri..."

Daga haka ya taka ya nufi hanyar waje. Ƙwala kiransa ta yi ganin ya bar briefcase ɗinsa ta ce.

"Ga fa Briefcase ɗin ka ka manta."

Dawowa baya ya yi yana mai jan guntun tsaki sannan ya ce.

"Kin ga ni wallahy har yasa duk na ruɗe. Tun ɗazu na aiki Shuraihu a ɗan ɗaure mini abu a mota kinga sai yanzu ya dawo, ashe da rabon dai sai na ga wannan abun baƙin cikin sannan zan fita....tukunna...wai ma wace ce wannan ɗin da zai aura Mom? Budurwa ce ko kuma Zawara?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

" Wallahy ban sani ba Faris. Yanda fa ka tsinci zancen nan a yau nima haka na tsinta. Sai da ya shigo da kayan ne yanxu yake faɗamin. "

Girgiza kai ya yi ya ce.

" Allah ya kyauta. Ni na wuce Mom sai an jima."

*******

Tahameer Alee Residence, Al Najhar Residential Quarters, Al Wusta Governorate, Oman.

Kwance yake akan doguwar lallausar kujerar da ke ɗakin sa, duk da cewa ya jima da yin bacci, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar cewa wannan baccin ba na daɗi bane a garesa, domin ya takure sosai tamkar wani baƙo a wurin da bai saba ba.

A hankali wata mata wacce za ta kai a ƙalla 52 to 53 a shekaru ta turo ƙofar ɗakin ta shigo.

Kallon sa ta yi tun daga sama har ƙasa sannan ta girgiza kai tare da zura hannu a hankali ta zare frame ɗinda ke rungume a ƙirjinsa ta ɗan kalla na few seconds haka, sannan daga ƙarshe ta je a hankali ta ajiye akan wani table wood Wanda ke ɗauke da abubuwan amfanin sa.

Dawo wa ta yi ta bubbuga handle ɗin Cushion ɗin a hankali wanda a zaton ta za ta jima tana yi ba tare da ya farka ba. Sai dai ga mamakinta tana yin ɗaya zuwa biyu sai gashi ya yi firgigit ya buɗe ido tare da miƙewa zaune tamkar wanda yake mummunan mafarki aka tashe sa.

Ido ta zuba masa tana observing ɗinsa sannan daga ƙarshe ta jinjina kai ta ce.

"ina jiranka a dining area."

Shiru ya yi ba tare da ya amsa ba wanda ido kawai ya zuba yana kallonta har ta fice sannan daga ƙarshe ya lumshe idanunsa a hankali waɗanda suka yi masa nauyi sosai sannan ya buɗe ya tashi ya shiga toilet.

Ya jima a toilet ɗin tsawon lokaci sannan bayan ya kambala duk buƙatar sa ya ɗaura towel ɗinsa ya fito.

Ko bayan ya fito ya jima yana shiri sannan daga ƙarshe ya shirya cikin simple white Shirt da black 3 quarter.

Ya jima a bakin ƙofar da za ta sada shi da Mamin tashi wacce shi yana iya hango ta sosai ya yin da ita kuma bata san ma ya fito ɗin ba.

Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da sai ta kansa sosai ya zo ya zauna kusa da kujerar da take zaune tana pressing phone a hankali ya ce.

"Good morning Maami..."

"Daga ina ka ke?"

Ta jefa masa tambayar ba tare da ta kalli inda yake ba.

"Ina wurin aik.."

"Ba ka wurin aiki Maheer. Tsawon kwanaki uku baka nan...where have you been?"

Yanzu kam kallonta yake kamar yanda itama ta zuba mishi idon tana kallon shi cike da mamakinsa na waɗan nan sabbin abubuwan da ya tsiro da su kwanan nan.

"I'm sorry Maami! I visited a friend?"

Da mamaki ta jinjina kan ta ta ce.

"A friend? Where?"

Girgiza kai ya yi tare da runtse idanunsa ya ce.

"Here you go again...always thinking negatively..."

"Maheer!"

Ya ji ta ambaci sunan nasa a hankali tana mai ƙara tsatstsare shi da ido.

Haɗiye sauran maganar tasa ya yi tare da zuba ido yana kallonta ta ce mishi.

"I'm scared! Waɗan nan sababbin ɗabi'un da ka tsiro da su kwanan nan suna ba ni tsoro. Is not that wai ina takura ka ko wani abu...please you have to understand my fear. Ko Jiya Abieh ya zo neman ka. (cewa da kakan sa mahaifinta) Meeting na uku kenan akayi baka nan, and no any genuine reason..."

Hannunta ya kama tare da saukar da muryarsa a hankali ya ce.

"don't be scared please. Kawai ki yarda dani, ba zan taɓa aikata wani abin da bakya so ko kuma abin da zai ɗaga hankalinki ba...and again Maami ni fa ba yaro ba ne..."

"Yes I know! I know that you are not a kid anymore....but to me you are still a kid Maheer. Saboda haka, daga yau za ka baro Maritime ka dawo gida gabaɗaya, idan yaso sai ka riƙa zuwa kana dawowa...."

"But Maam..."

"Shhh! That's my order. Haka za'a riƙa yi."

Daga haka ta janyo abincin da ta haɗa da kanta ta zuba mishi sannan ta ajiye a gabanshi tana faɗin.

"You most finish the food, saboda na san ka jima baka ci abinci da yawa ba."

Jinjina kai ya yi tare da ɗaukar spoon yana murmushi ya ce.

"And I also miss the taste. Thank you so much my Maami."

Daga haka ya fara cin abincin a hankali. Sosai ya dage yana zuba abincin a cikinsa amma ba don ya na jin daɗin sa ba. Abincin Maamin sa ƙarshe ne but a kwanakin nan har na ta sam baya masa daɗi.

*******

Gefen Anaam kuwa, tun da suka dawo gida taƙi yarda ta kalli ko hanyar inda ɗakin ta yake.

Baccinta ma sai ya dawo ragagge ba kamar na lokacin da suna India ba.

Yau ma, tun da ta ji shigowar Mama Hanne da kuma Matar Baba Salisu Hajiya Umma Kishiyar Mahaifiyar Na'imatu ta shige ɗakin Ammie ta yi shiru tamkar ba ta gidan.

Suna nan suna ta fira Rabi'atu ɗiyar Hajiya Umma da suka zo tare wato 'ƴar Uwar Na'imatu wacce suke babansu ɗaya ta miƙe tana kallon Ammie ta ce.

"Ammie Anaam fa?"

"Anaam ina ga tana ɗakina Rabi'atu. Idan kin je please ki ce ta fito ta gaishe da su Hajiya. Tun ɗazu nake saka ran fitowar ta shiru."

"Tau Ammie...bari na dubo ta na gani."

Wucewa ta yi ta nufi ɗakin Ammien ta shige kai tsaye. Kwance ta cim ma Anaam ɗin akan gadon Ammie ta yi rubda ciki tana kallon wani littafi dake gabanta wanda ta ajiye tun ɗazu domin ya ɗebe mata kewa amma kuma daga ƙarshe ta ajiye ba tare da ta buɗe shi ba.

Ta ji motsin shigowar mutum sarai, amma ba ta ɗago ba kuma ba ta yi alamun cewa ma ta ji ɗin ba.

"Anaam!"

Rabi'atun ta ambaci sunanta a hankali tana mai samun wuri daga gefen gadon inda take kwance ta zauna tana kallonta.

A hankali ta miƙe ta zauna tare da kallon Rabiatun da ɗan murmushin yaƙe ta ce.

"Rabi'a..."

"Uhm Anaam! Sannu da dawowa, ya jiki?"

Wannan kalmar ta ya jiki da suke ambatar mata, da sun san yanda ta tsani wannan kalmar da sun haƙura sun daina ambatar mata ita.

Wani irin kallon ƙurulla ne ta shiga jefa mata tamkar wacce taga wata baƙuwar hallita sannan daga ƙarshe ta girgiza kai ta ce.

"Ai komai jindaɗin da kike ciki Anaam wallahy dole ki rame. Ba'a barka da baƙin cikin abin da ya dame ka ba, sannan mutane sun ɗauke ka suna ta yaɗawa a duniya ina daɗi..."

Wani kallon ban fahimce ki ba Anaam ta yi mata tana faɗin.

"Kamar ya kenan?"

Ɗan ƙara muskutawa ta yi ta gyara zamanta da kyau tana mai kallon fuskar Anaam ɗin ta ce.

"Ina nufin yan da hoton ki da labarin ki ya je viral ko'ina tsawon lokaci ba daɗi duk inda ka duba social media tamkar yanzu ne abin yake faruwa. Kin san halin mutane ba tsoron Allah ne da su ba. Hatta Daddy Gimba kin ga irin firar da ya yi da kafafen Jarida cewa wai maza goma sha biyar ne suka yi miki fyaɗ..."

A gigice ta zaro ido laɓɓanta har suna harɗewa tsabar yanda ta ruɗe ta shiga tambayar Rabi'atu har sai da ta kamo mata komai a waya ta nuna mata.

Gani ta yi kawai ta fasa wata irin ƙara tare da zubewa ƙasa lokaci ɗaya babu numfashi a tare da ita.

Na'imatu wacce shigowar ta kenan bayan ta dawowa daga unguwa ne ta yi saurin shigowa ɗakin a gigice ta shiga tambayar Rabi'atun abin da ya samu Anaam ɗin.

Kafin ta gama jefa mata tambayar har su Ammie su ma sun shigo a ruɗe suna tambayar Rabi'atu, musamman Ammie domin tasan cewa ita ce wacce ta shigo ɗakin tun ɗazu.

Itama Rabi'atu a tsorace ta shiga zare ido tana faɗin.

"Ni fa ba abin da na yi mata. Kawai dai na jajanta mata ne, shi ne tace bata san abinda yake faruwa a social media ba dangane da ita shi ne na yo search na nuna mata...."

Cikin wani irin zafin nama Na'imatu ta iso gabanta kai tsaye ta watsa mata wani marin da sai da ta kifa bata shirya ba.

Daga haka ta sake shaƙo wuyan rigar ta ta shiga zabga mata mari da bugi a duk inda ta samu.

Ganin hakan yasa Hajiya Umma isa wurin da sauri ta ƙwace 'ƴar ta a fusace, sannan ta ɗaga hannu ta wanke fuskar Na' imatu da mari na jin haushin yanda ta shiga jibgar mata 'ya kamar ta samu Jaka.

Haba! Kafin ma ta gama janyo Rabi'atun tuni Hajiya Hanne ta wankawa Hajiya Umma na ta marin ranta a ɓace ta kalle ta ta ce.

"Saboda an nunawa 'ƴar ki kuskurenta shi ne za ki mare ta. Ai gwanda da ta jibgi 'ƴar banza munafuka mai fuska biyu..."

Itama Hajiya Umma cike da ɓacin rai da kuma jin zafin Marin da Hajiya Hannen ta yi mata ta ce.

"Miye abin munafurci a nan ɗin da za ta wani kama mini yarinya tana duka? Ƙarya ta yi ba haka a kayi ba.? Ko kuma ita ce ta aikata mata hakan?"

Fuska Hajiya Hanne ta karo saitin Hajiya Ummar ta ce.

"Ko za ki rama ne Umma?"

Girgiza kai ta yi ta ce.

"Ba zan rama ba Hajiya Hanne,na barki da sarki Allah shi ne wanda zai saka mini...ke kuma munafuka..."

Cewa da Na'imatu.

"Wacce xuciyarta ta mutu, kin baro gidan ubanki kin zo kin tare gidan uban wasu kina bauta musu alhali ko daraja ki basa yi, ba su ɗauke ki da muhimmanci ba. Saboda baki san ciwon kanki ba, har za ki daki 'ƴar uwarki akan zancen da ke kanki kin san an yi shi ba ƙazafi ba ne ko ƙage a ciki...."

Girgiza kai Ammie ta yi tana mai share hawayen da suka zubo mata ta kalli Hajiya Umma ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull