Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 6
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 6: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 6. Gyara zama mubarak ya ƙara yi sannan ya kalli Alhaji ya ce.
3,294 words
Gyara zama mubarak ya ƙara yi sannan ya kalli Alhaji ya ce.
"Alhaji ka yi haƙuri, ba don ina so in ƙetare maganar ka bane da kace a rufe wannan maganar. Alhaji zuciyata ta kasa samun sukuni da nutsuwa akan wannan wanda aka kira da JAK na cewa wai ya ɗauki fansar sa. Har da cewa wannan dama ce a gare sa...hankalina a tashe yake, da yanzu ka mutu Alhaji bayan shi JAK ya hana ɗan uwansa ya kashe ka...Ina tsoron kada su sake farmakarka ko su sake dawowa gidan nan watarana..."
Cikin zallar mamaki Mukarram ɗin ya ce.
" What?"
Jinjina kai Mubarak ya yi sannan ya ce.
" Na ga komai da idona Yaa Mukarram. Shi ne wanda ya ture ɗayan bayan ya harɓi Alaji, wannan dalilin ne yasa harbin ya sauka a hannun sa maimakon wani wurin mai hatsari a jikin sa..."
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke a hankali sannan ya kalle su ya ce.
"Mukarram, kai ne kaɗai baka tare dani, kana can Indiya wurin aikin likitancinka, amma kai Madu da kuma Mubarak daku nake kasuwanci na, komai tare daku nake yinsa, kunsan kaso saba'in na daga cikin mutanen da nake mu'amala da su, a iya sani na bani da abokin faɗa, bani da abokin gaba, bani da wani wanda faɗa ko tashin hankali ya taɓa shiga tsakanina da shi, Gimba ne kaɗai wanda ko shi bai taɓa fitowa kai tsaye ya yaƙe ni ba sai dai ya yi ta abubuwansa cikin habaici da sauransu. "
Jinjina kai Muhammad ya yi ya ce.
" Wannan haka yake Alaji. Wata ƙila an samu kuskure ne ma'ana ya kuskure daga abin harin sa ya za ta kai ne, wata ƙila sai daga baya ya gano cewa ba kai bane hakan yasa ya fasa kuma ya hana a kashe ka ɗin..."
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke a hankali ya ce.
" Touh! Muna fata Allah yasa haka ne, Allah ya kyauta ya tsaremu daga sharrin maƙiyyanmu."
"Amin amin Alaji."
"To a ta shi a yi haramar tafiya."
Jinjina kai mukarram ya yi yace.
"In Sha Allahu Alaji. Allah ya baka lafiya mai amfani, yasa wannan abun ya zamto kaffara. Amin. Amma kuma ace har da Common award! Idan ba na kusa da kai mai yin hassadar ka ba waye zai yi maka haka?"
Sai yanzu Hajiya ta girgiza kanta da mamaki ta ce.
"Hmm! Duniya kenan! Ai ni wannan al'amarin ya yi matuƙar bani mamaki da al'ajabi. Allah dai ka ci gaba da bamu kariya daga sharrin mutum kowane iri ne, domin wallahy mutum bai shi da kyau, duniyar ce ta riga ta gurɓace da abubuwan zaluncin wanda a yanzu sun fi yawa a cikinta. Hassada da baƙin ciki da ƙyashi ya taru ya yi wa zuciyar wasu katutu, wani fa ko wata alaƙa ba shi da ita da kai amma kuma haushinka yake ji. Shiyasa yawaita sadaka yana da kyau kuma yana fa'ida, domin manzon Allah da kansa yace mu yawaita yin sadaka, domin sadaka tana maganin masifa. Allah ya kyauta ya sa mu dace."
Da amin suka amsa sannan suka tashi suka je suka shirya inda Muhammad ya nufi Abuja su kuma suka kama hanya gabaɗaya ahlin gidan zuwa ƙasar Indiya har da Alhaji Mas'ood bayan ya tabbatarwa su Baba Salisu cewa lallai su janye kowace irin ƙara su manta da komai, kawai abin da yake so shi ne su tayashi addu'a.
******
Alhaji Gimba kuwa, yana zaune a parlournsa Faris ya shigo wanda shi ne kaɗai ƙwallin ɗan da yake da shi a duniya.
Cikin farin ciki ya ce.
"Daddy da gaske ne iyalin Alhaji Galadima sun janye ƙarar da suka shigar?"
Miƙewa ya yi tsaye daga zaunen da yake yana mai fuskantarsa ya ce.
"Haka na ji! Daman na san ba za su iya ba. Kuma ni hakan nake jira, saboda haka ni zan shigar da ƙara a yanxu..."
Da sauri Faris ya girgiza kansa ya ce.
"Noo Daddy please! Kamar yanda suka fasa please kai ma ka manta."
Cikin wata irin tsawa ya yi mishi wani kallo ya ce.
"Akan me zan manta? Shin ba ka ji irin wulaƙanci da tozarcin da mukarram yazo har gidan nan ya yi mini ba?"
"Duk na ji komai daddy, please ka yi haƙuri, ko su nasan fushin zuciya ne yasa haka, and again kuma ni har yanzu gaskiya Ina son Anaam..."
Wani irin gigitaccen mari ne Alhaji Gimban ya sauke masa wanda hatta Hajiya Salamatu dake tsaye jikin ƙofar shigowa parlourn daga ɓangarenta sai da ta razana. A fusa ce ya nuna shi da yatsa ya ce.
" Ashe kai mahaukaci ne ban sani ba? Shashasha wanda bai san ciwon kansa ba? Ragin ɓarayin ce kake iƙirarin cewa kana so?"
Shima Faris ɗin a zuciye yace.
"Ni babu ruwana! A haka nake sonta. Ai kai ne wanda ya goya mini baya daga farko kuma ka yi mini alƙawarin cewa zan same ta..."
"To na janye maganata, kuma na soke wannan soyayyar. Because there's no way zan barka ka kaje ka auro wacce en daba suka gama da rayuwarta gabaɗaya. Miye ya rage wanda za ka samu a tare da ita har ya sanya ka yi farin ciki da aurenta??"
Girgiza kai ya yi ya ce.
" wannan ya rage naka kuma! Matuƙar za'a bani Anaam to tabbas sai na aure ta, duk abin da za ka yi sai dai kayi. Kuma ina baka shawara da gargaɗin ka akan kada ka sake tada wannan maganar ballantana har kace za ka shigar da su ƙar..."
Cikin wani irin tashin hankali Hajiya Salamatu ta daka masa tsawa da cewa.
" Faris!! Kana cikin hayyacinka kuwa? Mahaifin na ka kake faɗawa irin waɗan nan kalamai??"
Idanunsa ya sauke akan mahaifiyar ta shi a hankali waɗanda suka rine sosai suka canja launi tsabar ɓacin rai, kamar zai yi magana sai kuma ya girgiza kai kawai ya juya ya fice daga gidan.
Juyawa Alhaji Gimban ya yi ya kalli matarshi tashi na tsawon sakanni sannan ya girgiza kai daga ƙarshe ya ce.
"Na sani! Na san cewa kema goyon bayan ɗanki za ki yi. Daman kin fi son fiye dani. Tun da har yace na janye ko na ce ba zan janye ba za ki iya kema ki ga laifina. Alhali a gaban idon ki Mukarram ya zo har cikin gidan nan ya ci mini mutunci tamkar ni ɗin ba ubansa ba ne..."
Ƙasa ta yi da muryarta sosai ta ce.
" To ai Alhaji gaskiya ce baka so. Amma ni ma da za ka ji shawara ta da ka ƙyale su sun je sun ji da abinda ya dame su..."
"Miye ya dame su ɗin? Na ce miye ya dame su ɗin da har za ki goyo musu baya ki bar ni mijin ki? Ni da suka maƙalawa sharri har za ki bi bayan su ko?"
Parlourn ta bar masa itama ta koma ciki domin ba za ta iya da wannan fitinar ta sa ba a yau.
Shi kuma sai mi ta yake ci gaba da yi yana ƙara ɗaga murya yana faɗin.
"Wannan wace iriyar masifa ce? Waje baka ji daɗi ba haka ma gidan ka baka ji daɗi ba. Kai ba za ka dawo a tarairayeka a lallashe ka! Sai dai a barka da baƙin cikin da ka ƙunso daga waje ya yi ajalinka? Yanzu a gabana take tausayin Galadima da iyalinshi ni kuma na faɗi na mutu kenan? Wallahi aure zan ƙara. Na rantse da Allah auren da bakya so shi zan ƙaro. Yarinya zan samo 'ƴar shala wacce za ta saka na manta da komai ke kuma ta shiga gasa miki aya a hannu. Daman ai shi ne bakya so, kice da girman ki an auro miki 'ƴar cikin ki."
Daga haka ya ƙwafa ya haura ɗakinsa.
✍️ OUM-AMEER ✍️
*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 8*
Wata ɗaya suka kwashe a Kaduna suna aikin neman Azaan ƙarshe da suka gaji, Bash ya ce musu ya kamata su koma su faɗawa Oga Badru halin da ake ciki.
Hakan yasa suka juya suka koma gida. Oga Badru na yin tozali da su bai ko bari suka zauna ba ya fara rarraba ido yana faɗin.
"Ina Azaan ɗin? Ko kun kashe shi tun a can ɗin kun yasar da gawarshi?"
Kallon kallo suka fara domin an rasa waye zai fara masa bayani. Ashu ganin da gaske su Daniel ba bayanin za su mishi ba yasa ya girgiza kansa murya cike da zallar karaya ya ce.
"Oga Azaan ba Azaan ba ne kamar yanda ka sani."
Wata uwar harara ya dalla masa sannan ya ce.
"Wannan wace maganar shirme ce kake faɗamin? Ban gane Azaan ba Azaan ba ne..."
"Eh to! Gabaɗaya informations ɗinda ya bamu dangane da kansa duk bayanan Ƙarya ne, a wannan gidan da ya taɓa nuna mana Ƙarya yake bai san ma su waye a gidan ba kamar yanda su ma basu san wani Azaan ba. Babu wani ma mai kama da shi a duk inda muka je neman sa. Bayanan wurin aikinsa da yace a kamfanin Royal constructives yake aiki nan ma Ƙarya ne, babu wani ko mai kama da shi a kamfanin. Duk inda ya kamata mu bincika mun bincika Oga har inda ma ba'a ce ba..."
A ruɗe Oga Badru ya ce.
" What! To amma wannan tsohuwar da muka taɓa gaisawa da ita fa? Wacece? "
Girgiza Kai Bash ya yi yace.
" Muna ɗaukar shi a matsayin hamago, ashe shi ne wanda ya ɗaukemu hamagawa. Ni wallahy tun zuwansu na farko a cikinmu na ji a raina ban yarda da shi b.."
Wasu irin tagwayen marora Oga Badrun ya kifawa Bash a lokaci ɗaya sannan ya ce.
"Ni za ka kawowa maganar rainin hankali? Miyasa tun a ranar da ran naka ya ji bai amince da shi ba ka ƙi ka faɗamin? Yanzu kasan a irin jafa'in da zai jefamu a ciki?"
"A huce Oga! Amma nasan a wannan lokacin ko na faɗa maka ba yarda za ka yi da zance na ba."
A hargitse ya kalle su ya ce.
"Bamu ga ta zama ba fa! Tun da har ya bar nan akwai babbar matsala."
Ya faɗa yana mai girgiza kai cike da jimami ya ci gaba da cewa.
"Tun farko ma da mun sani da mun kashe yarinyar daga ƙarshe da yanxu hankalinmu a kwance yake..."
Prince ne ya kalli Oga Badrun ya ce.
"To yanzu Oga miye abun yi?"
"While! Dole a yau ɗin nan zamu bar wannan State ɗin na har abada, koma mu tsallaka kawai mu bar ƙasar kafin ƙura ta lafa, don billahillazy akwai babbar matsala gagaruma...saboda haka kowa ya shirya a gaggauce mubar wannan gidan ma tun yanxu..."
Ba su fi 2 hours ba suka shirya kayansu na buƙata suka fito cikin motocin su na alfarma da shigar mutanen kirki kamar yanda suka saba idan za su shiga mutane kamar ba su ba.
Suna fita gate Oga Badru ya ce su tsaya, sai da ya ƙare wa gidan kallo tsab sannan ya girgiza kai cike da baƙin ciki ya ce.
"Azaan kenan! Lallai ka ƙara koyar dani wani darasin rayuwar...amma kuma ka sani! Wallahy ba zan manta ba, kuma ba zan yafe ba."
Waigawa ya yi ka kalli Daniel rai a ɓace ya ce.
"Daniel ka kira wannan Alajin ka faɗa masa halin da ake ciki, saboda haka ya an kare domin komai na iya faruwa. Ni wallahy ji nake ma kamar na je ka sheƙe shi, domin shi ne marar sa'ar. Tun daga lokacin da mukayi wannan aikin nasa har yau bamu sake samun bacci mai daɗi ba, kullum a tsoro da zullumi. Sai ka ce wasu karnuka."
Jinjina masa kai Daniel ɗin ya yi Sannan ya ce.
" Zan kira shi kuwa na faɗa masa, amma ni shawara ta kawai a barshi kada a kashe shi, idan har Azaan ya koma wurin wannan yarinyar Kaga shi kenan nan za ta ƙare a tsakanin su."
*******
Shanti Devi International Institute Of women's Health and Trauma Care. Vasant Kunj Extension, New Delhi, India.
Suna isa babbar asibitin wacce ƙwararru ke ciki aka Shirya yi mata surgery na gaggawa bayan sun yi reviewing case ɗinta wanda sai da ya sake ɗaukar ta tsawon lokaci kafin suka samu ta farfaɗo bayan sake yi mata aiki a karo na biyu.
Haƙiƙa tasha matuƙar wahala wanda sam ba su yi zaton cewa za ta rayu ba.
Tun da ta farka tsawon kwanaki uku kenan taƙi buɗe Idanunta kuma taƙi ta yiwa kowa magana. Duk wanda zai zo ya yi mata magana yi take kamar tana bacci wanda sai idan likita ya shiga take buɗe ido tana kallon sa da sauraren duk abin da yake faɗa mata.
Abbah ne ma idan ta ji muryar shi ta kan zubo da ruwan hawaye amma ta kasa haɗa ido da kowa a cikin su, juyin duniya sun yi amma taƙi ta saurare su.
Lokaci ɗaya hakan ya sa Alhaji Mas'ood sake shiga cikin wani sabon tashin hankalin. Daman abun da yake ta gudu kenan tun tuni. Kullum da wannan tunanin yake kwana a ransa da shi yake tashi na ya za ta yi idan ta farfaɗo.
Yau ma misalin ƙarfe uku na dare, Ammie tana zaune akan Sallayah bayan ta farka daga bacci ta yi nafila sannan ta zauna da carbi a hannunta tana ja.
Kamar a mafarki ta ji sautin kukan ta a hankali yana ratsa cikin kunnunwanta. Kallon inda Na'imatu ke kwance tayi taga tana ta sharar baccin ta hankali kwance.
Miƙewa ta yi tazo ta zauna kan kujerar da ke dab da gadon tare da miƙa hannu ta janyo hannunta ta riƙe a cikin na ta.
Anaam kuwa, jin hannunta cikin na Mahaifiyar ta ta sai ya ƙara karyar mata da zuciya wanda sosai sautin kukan ta ya ƙaru.
A hankali Ammie ta takai ɗayan hannunta ta ɗora akan goshinta ta shafa tana mai matso hawayen da suka cika mata ido ta ce.
"Anaam! Shin har zuwa yaushe za ki ci gaba da kasancewa a haka? Na sani cewa an cutar dake, an cutar da ke an zalunce ki,but wannan ƙin buɗe idonda ki ke da ƙin magana da kike yi is not the solution Anaam. What happened to you is not your fault, yes! Yana daga cikin ƙaddarar ki. Abinda Allah ya rubutawa bawan sa babu wanda ya isa ya kauce masa..."
Ta ƙarashe maganar tana mai share guntun hawayenta tare da jinjina kai ta ci gaba da cewa.
" Komai zai same ki a rayuwar nan, baki da iyayen da suka wuce mu, haka zalika ke ce kaɗai 'ƴar da muke da ita a duniya bamu da wata bayan ke. Komai zai same ki, mu iyayenki ba za mu taɓa gudunki ba kuma ba za mu taɓa juya miki baya ba. Duk abin da ya same ki a rayuwa mu ya sama walau na daɗi ko kuma akansi sa."
A hankali Daddy ya turo ƙofar ya shigo fuskar nan ɗauke da damuwa kamar ko yaushe.
A ɗan nesa da su da ya tsaya na 'yan wasu daƙiƙu sannan daga baya ya taka a hankali ya isa gefen gadon tare da kama ɗayan hannunta cike da damuwa ya ce.
" My princess!"
Wani abu ta ji ya motsa har can ƙasan zuciyarta jin maganar Abban ta mai cike da zallar karaya.
"I'm here. Duk da na san cewa ba za ki kalle ni ko ki yi mini magana ba...ina mai baki haƙuri domin na kasa kare ki a wannan daren...and the pain...will stay with me for ever because I fail...."
Jinjina kai Ammie ta yi ta ce.
"Yes Anaam! Gabaɗaya mu iyayenki da 'yan uwanki har abada wannan raɗaɗin da ciwo ba zai taɓa barin zukatanmu ba. Ya kamata ki duba ki yi wa kan ki uzuri..."
Abbah ya ce.
"And with all this...muna nan a tare dake har abada ba za mu taɓa barin gefen ki ba...muna son ki muna ƙaunar ki, en uwanki ma haka. Please ki yi haƙuri ki yi ƙoƙarin manta bayanki tare da fuskantar sabuwar rayuwa..."
A hankali ta shiga buɗe idanun ta tana mai kallon su ɗaya bayan ɗaya tamkar wata wacce ta samu taɓin ƙwaƙwalwar da ba ta gane komai na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta fasge da wani irin mugun kuka mai tsuma rai.
Lokaci ɗaya jikinta ya hau wata irin jijjiga tana mai jin komai kamar yanzu ne yake faruwa da ita. Gabaɗaya ta fige ta lalace ta zabge tamkar ba 'ƴar gayu Anaam ba.
Sai da ta jima sosai tana kuka ba tare da ɗaya daga cikin su ya dakatar da ita ba sannan daga ƙarshe ta buɗe idonta ta kalle su ɗaya bayan ɗaya tana ci gaba da kuka ta ce.
"Abbah! Do you know how it feels?"
Ta furta cike da karyewar zuciya tana mai bin sa da wani irin raunataccen kallo.
"Na yi fatan mutuwa sau ba adadi sannan na yi nadamar kasancewa a cikin wannan duniyar! Na yi ta addu'ar Allah ya ɗauki raina kafin na iya buɗe idanuwana na kalle ku, domin komai ya ƙare mini a wannan duniyar. Kunyar kai na nake ji kamar yanda nake jin kunyar ku. A kowace rana da za ta zo ta wuce mutuwa nake yi Abbah! Rayuwa ta ba ta da wani amfani a gareni...wallahy gwara na mutu.."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Cewar Ammie tana mai ƙara matsawa dab ita sosai ta shiga share mata hawaye itama da hawayen a idanun ta ta ce.
"Haba Anaam! Shin ashe ba za ki zamto mai yarda da ƙaddara ba?"
"Ammie! To be touched without your consent is...is.."
Wani irin sabon kukan ne ya sake sarƙeta tamkar za ta shiɗe tare da ɗaga hannu tana nuna saitin zuciyarta wacce take jin tamkar za ta fashe tsabar baƙin cikin da take ciki.
Jinjina kai Ammie ta yi itama tana mai ƙara sautin kukanta ta ce.
" Na fahimta! Wallahiy na fahimce ki because I feel your pain...ni uwa ce Anaam. Dole abin da yake damun ki nima ya dame ni.."
Girgiza kai ta yi tana mai jan wani kalar numfashin wahala ta ce.
"I feel dirty! Daga ta ciki na da waje na ina mai jin kunyar kaina sosai Ammie...I'm alive but I am not Okay...har abada ba zan dawo daid...."
"Na sani. But ki daina cewa ba za ki dawo daidai ba..."
"Macen da aka ketawa rigar mutunci Ammie...har abada ba za ta taɓa yin daidai da sauran matan duniya ba."
Cikin jin wani irin sabon tausayinta ta ce.
"Anaam! Kowace irin mace a duniya da kalar ƙaddarar ta. Kin ga duk da irin wannan abun da ya same ki? Wallahi idan ki ka ji tarihin wasu matan ke a aljanna ki ke...ki karɓi wannan ƙaddarar ta ki hannu biyu sannan ki kama Allah. In Sha Allahu rayuwa za ta dawo miki kamar komai bai faru ba muddin kika ɗabbaka haƙuri...Muna tare dake har abada ba damu da sauran en uwanki..dan Allah ki yi haƙuri Anaam ɗinmu."
Tashi tayi ta zuro ƙafafunta a karon farko ta faɗa jikin Ammien ta sake fashewa da kuka.
*******
Port of Duqm special Economic Zone, Dock 5, Maritime Operations sector, Duqm Coastal Highgway. Al-Wusta Governorate, Oman.
Babbar tashar jiragen ruwa ce wacce ke ɗauke da manyan jirage iri-iri kowane da kalar da kuma abin da yake ɗauke da shi a bakin babban tekun Oman. Wasu jiragen suna nan a tsaye wuri ɗaya, wasu kuma an gama musu lodi domin tafiya yayin da wasu ke dab da isowa gaɓar ruwan.
Ma'aikata ne birji waɗanda kowane da kalar kakin su da kuma kalar aikinsu domin yin komai cikin doka da tsari.
Bayan su kuma, akwai mutane iri-iri wanda kowa da abinda yake gabansa na hada-hadar rayuwa.