Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 5
Duhun dare book 1 complete novel Chapter 5: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 5. "No, kun gane? Ni na tara ku ne domin in faɗa muku gaskiyar abin da…
3,374 words
"No, kun gane? Ni na tara ku ne domin in faɗa muku gaskiyar abin da yake faruwa tsakanina da Alhaji Mas'ood Galadima. Ance ni ne na tura wasu mutane suka ke ta DUHUN DARE suka shiga gidansa suka harbeshi sannan suka yi wa 'yarsa Fyaɗe, mummunan fyaɗe wanda ya yi sanadiyyar yanzu haka ta samu mummunar matsalar da sai an fita da ita zuwa waje domin jinya, domin ance gabaɗaya mutanen sai da suka yi lalata da ita kusan su goma sha biyar... Wanda ni magana ta gaskiya har yau ban san abin da yake faruwa ba kuma bansan abinda ake zargina a kai ba, sannan abu mafi ban mamaki a ciki shi ne: ni ban amsa kiran wata hukuma ba, daga sama kawai ɗan sa Doctor Mukarram Wanda yake zaune a ƙasar Indiya yazo har cikin gidana yana tuhuma ta alhali shi ɗin ba jami'in doka ba ne. Bai da wani hurumin da zai zo har cikin gidana ya ci zarafi na sannan ya yi mini barazana domin ban aikata ba...."
Wata 'ƴar jarida ce daga cikinsu ta ɗaga hannu sannan ta ce.
" Alhaji Gimba! Dangantakarku da Alhaji Galadima ta daɗe wanda kowa yasan ku a tare, tun ƙurciya kuke aminta, to amma miyasa wannan alaƙar take cike da rashin jituwa kamar yanda duniya ke jin Jita-jita?"
Jinjina kai ya yi yana murmushi tare da kallon inda take tsaye da microphone a hannunta ya ce.
" Mu ɗin aminanai mu huɗu, ni, Alhaji Ridwan, Alhaji Galadima da kuma Alhaji Bala Kimba Allah ya ji ƙansa da rahama. Kinga mu huɗun nan da na lissafa? Mu ɗin aminai ne kuma abokan kasuwanci, tare muke gwagwarmaya wacce har yau bamu daina ta ba. Babu wata rashin jituwa a tsakaninmu, domin mu ɗin kasuwanci muke, kuma dole akwai ƙalubale a cikin kasuwa kowace iri ce, a duk lokacin da ya kawo shawara naga cewar ba ta yi mini ba, ina da right ɗinda zance ni ban amince ba, duk yanda za'a yi sai dai ayi, shi ma kuma haka, wanda kasuwanci ya gadi haka domin ba za ka so kai da gumin ka akace kuma kana cutuwa ba. Amma ni babu wani abu makamancin haka a tsakaninmu. Dole zama akwai saɓani, domin duk wanda yace zo mu zauna to fa lallai yace zo mu saɓa. Ni ɗan kasuwa ne ba ɗan daba ba, ba zan taɓa aikata haka ba. "
Wani daga cikin su ne ya sake jefa masa tambaya da cewa.
" Shin ka taɓa yin barazana ko kuma iƙirari akan ɗaukar fansar wani abu akan shi Alhaji Galadima?"
Wani murmushin ya sake yi sannan ya girgiza kai yace.
" Yanzu fa na gama yi muku bayani. Waɗan nan kalmomi ma da ka ambata kowa ya ji yasan cewa ba kalmomi ne na ƙwarai da za'a riƙa furtasu kai tsaye ba, domin duk mutumin kirki sam waɗan nan kalaman bai dace ace ana jin sa a bakin sa ba. A kasuwa ana faɗin abubuwa masu yawa, amma ban taɓa wuce iyaka ba. Ban taɓa yi masa barazana da shi da iyalan nasa ba, na kan je gidansa dani da iyalina a duk lokacin da muka so, haka zalika shi ma ya kan zo gidana da shi da iyalinsa a duk lokacin da suka so, kai in taƙaice muku zance har ɗana na nemawa auren 'yarsa Anaam wacce aka yi wa fyaɗe yanzu, to amma Allah bai nufa ita ɗin rabon sa ba ce face rabon ' yan daba. Ina fata Allah ubangiji ya bata lafiya yasa ayi mata aiki cikin nasara. "
" Amin. Tambaya ta ƙarshe Alhaji Gimba Taunau...shin za ka amince a bincike ka kai tsaye akan wannan zargi da familyn Alhaji Galadima suka ɗora a kan ka? "
" Why not? Ban aikata komai ba, saboda haka ba zan ji tsoron wani bincike ba. A shirye nake duk sanda suka so ina nan ina jiran su, har tafiya nake da ita, amma kuma ku ji da kyau cewa na ɗage ta har sai sun gama bincika ta. To amma kuma ina so su kwana da cewa, idan har aka gama wannan binciken, matuƙar dai basu kama ni da kowane irin laifi ba, to nima zan shigar da su ƙara domin doka ta ja mini haƙƙina akan ɓata mini suna da suka yi da kuma zuwan da Doctor mukarram ya yi har cikin gidana ya yi mini barazana tare da jan mutunci na a ƙasa. Sannan hatta ita Anaam ɗin da aka yiwa fyaɗen, zan so su shirya mini zama da ita kamar haka, sai ta faɗi kamannin mutanen da ta gani, idan ta ganni a ciki ko ni ko ɗana Faris, na yarda a zartar mana da duk wani hukuncin da ya kamat..."
Ƙitt! Haka Muhammad ya kashe TVn yana mai jin yanda zuciyar sa ke wani irin ƙuna da baƙin ciki akan wannan abun da Alhaji Gimba ya yi.
Waigawa ya yi ya kalli yanda Hajiyarsa da su Na'imatu suke ta kuka. Yanzu sirrin wannan yarinyar da suke ta ɓoyewa suna kaffa-kaffa shi ne ya fito da shi yana maganganu na tozarci a gaban idon mutanen duniya?
Suna nan sun yi shiru kowa ya rasa abin cewa kawai suka ga Alhaji Galadima ya faɗi ya suma.
Da gudu suka yi kanshi cikin tashin hankali suna ta faman kiran sunansa.
Sallamar Mukarram ita ce ta ja hankalin Muhammad ya ɗago cike da wani irin ɓacin rai ya tarbeshi tare da wanke masa fuskarsa da wani irin azababben marin da sai da ya dafe kunce ba shiri.
Da wani irin maɗaukakin mamaki ya shiga kallon yayan nasa wanda zai iya cewa tunda ya taso ya girma ya fara sanin ciwon kansa, har zuwa yau ba zai iya tuna lokacin da yayan nasa ya taɓa ɗaga koda yatsarsa ce ya ɗora a jikin sa da sunan hukunci ba.
Su ma su Hajiya hakance ta faru a ɓangaren su, musamman matar Mukarram ɗin Aysha wacce ta zaro ido da tsananin mamaki domin tunda take gidan tsawon shekaru tara kenan bata taɓa ganin wani abu makamancin hakan ba.
A raunane Mukarram yana kallon idon Muhammad ɗin ya ce.
"Kateh!"
Cikin wani irin ɓacin rai Muhammad ɗin ya jinjina kansa yace.
"Yes! You deserved it Mukarram! Duk wannan abun da ya faru kai ne ka janyo shi. Sai da na hana ka, amma kai da yake kana da taurin kan tsiya da zafin zuciya sai ba ka saurare ni ba. Ina ji ba ni ba, hatta su Baba Salisu sai da suka yi maka magana. Da ace baka je gidansa ba, da ya isa ya yi mana wannan tonon asirin ya fallasa mu a duniya? wanda bai san abin da ya faru ba, ga shi yanzu duniya duk ta ji, wannan yarinyar Sam ba ka yi mata adalci ba... "
Wasu irin hawaye ne masu matuƙar zafi suka gangaro masa akan kumatunsa. Girgiza kai ya yi cike da nadama ya ce.
" I'm sorry! Ban taɓa zaton cewa zai fuskancemu ta wannan hanyar ba..."
Jinjina kai Muhammad ya sake yi yana faɗin.
" Ai abin da nake ta jiye maka kenan! Ba za ka taɓa haɗa wayonka da na Alhaji Gimba ba Mukarram...shi ɗin mutum ne mai wahalar zama wanda idan ba ka iya shi ba, to za ka kasance ne a damuwa da baƙin cikinsa har abada. Yanzu ga abin da ka janyo...ka faɗamin ina amfanin hakan?"
A zafafe cikin ɗaga murya ya shiga mayar masa da martani cewa.
" Ni ma Yayan Anaam ne kamar yanda ka ke Kateh! Matsayin mu ɗaya ne a gare ta,uwa daya uba ɗaya muke, ban yi don cin zarafi ko kuma wulaƙanci a gareta ba, kai ma kasan ba zan taɓa yin wani abu makamancin wannan ba..."
"Ga shi kuwa ka yi! Da ka bar zancen a lulluɓe kamar yanda muka tsara da yanzu babu wanda ya ji.."
Juyawa ya yi a fusa ce kawai ya bar parlourn ya fice daga gidan gabaɗaya. Yana matuƙar girmama yayan nasa da mutuntashi, idan yaci gaba da musayar yawu da shi a yanda yake jin zuciyar sa tabbas komai zai iya faruwa.
A hankali Aysha ta ɗora kanta akan kafaɗar Ammie ta sake rushewa da kuka ganin wannan abun da ba ta saba da shi ba a gidan surukan na ta.
Ammie na hawaye ta kalli Muhammad ɗin a ɗan tsorace ta ce.
"Madu kana gani fa yanda ya fita a zuciye..."
Cikin ɓacin rai ya kalle ta ya ce.
"Hajiya ƙyale shi kawai, duk abinda zai yi yaje ya yi...ni ban ga amfanin da zuwan nasa ƙasarar nan ya tsinana mana ba. Duk inda zai tafi ya daɗe."
*******
Gefen su Oga Badru kuwa, tun daga wannan ranar Azaan ya fita a harkarsu. Yana nan a gidan tare da su amma tamkar baya nan, ya ɗauke kansa ba ya yiwa kowa magana. Kamar yanda suke sabgar su shima haka yake yin tasa.
Duk da haka hankalin Oga Badru ya kasa kwanciya, hakan yasa ya saka su Prince cewa su sanyawa duk wani motsinsa ido, sannan wayoyinsa da computersa su ma Aroun yana nan bibiye da shi da duk wani motsinsa 24hours.
A daren jiya ma da suka shirya tafiya ƙasar Yola sai da Oga Badru ya tabbatar masa da cewa a tare za su tafi idan gari ya waye,domin suna gudun kada su bar shi bayan sun tafi ya je wurin familyn Alhaji Galadima, idan kuma har hakan ta kasance to kuwa lallai akwai babbar matsala musamman ga Alajin da ya basu wannan aikin.
Suna nan suna ta shirin su, bayan sun kambala misalin ƙarfe goma sha biyu na rana suka fito domin tafiya. Sun jima suna jiran fitowar Azaan ɗin amma kuma shiru bai fito ba tsawon lokaci. Sai da suka gaji da jira sannan Oga Badru ya kalli Aroun ya ce.
"Ka tabbata Azaan yana cikin gidan nan kuwa Aroun? Ni fa tun daren jiya da na fito ban ji alamunsa ba."
Jinjina kai ya yi alamun ba shi tabbaci ya ce.
"Yana nan cikin gidan nan,...Bash ko za ka dubo shi ne?"
Fita motar Bash ya yi ya tafi ɗakin sa, sai dai ga mamakinsa bai gan shi a ɗakin ba wanda har toilet sai da ya duba tunanin sa ko yana ciki.
Yana kowa yace masu baya nan. Sake kallon computer Aroun ya yi na ɗan lokaci sannan ya ɗago ya kalle su ya ce.
"Yana cikin gidan nan har yanzu...na'urar biyar diddigi ta tabbatar yana cikin gidan nan..."
A tare suka koma ɗakin su shida, sai dai abin mamaki shi ne, wayoyinsa guda biyu da yake amfani da su da kuma laptop ɗinsa suna nan ya ɗaga pillow ya ɗora a kai amma shi baya ɗakin.
Nan suka hau binciken ɗakin inda suka ga ya ɗauke komai na shi mai muhimmanci ya fece daga gidan.
Sun Sha matuƙar mamaki da irin game ɗin da ya buga musu, musamman Aroun da yake ganin duk yafi su basira da wayau a cikin su.
Wani kallon Oga Badru ya yi wa Aroun ya ce.
"Aroun ba bu zancen tafiyarka zuwa ƙasar ka har sai mun nemo Azaan mun kashe shi sannan..."
Daga haka ya waiga ya kalli su Daniel ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce.
"Ai shi ɗin cikakken ɗan Kaduna ne kuma mazaunin cikinta, ina ga ya manta da cewa ya bani bayanansa. Saboda haka...wannan operation ɗin an ɗage shi har sai mun kamo Azaan mun kashe shi, a wannan karon ba zan saurara masa ba tun da har shi bai san kawaici ba. Rasa ransa da zai yi, ya fiye mana alheri fiye da bala'o'an da zai jefa mu a ciki. Ban fara sana'a ta don na daina ba, sannan ba zan bari wani ƙaramin ƙwaro ya zamo mana barazana ba. "
Jinjina kai Prince ya yi ya ce.
" Bari kawai mu je Kadunar Oga Bad, .kai ka zauna gida ka huta kawai....Ai duk wanda yace uwar wani ba za ta yi bacci ba, to shima tashi uwar ai bai kamata a bar ta ko gyangaɗi ta yi ba."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir
*PAGE 7*
Misalin ƙarfe biyu na dare. Ammie ce zaune akan sallayah ɗakin Anaam tana addu'a wanda ta jima bayan ta kambala nafila tana addu'ar, ƙarshe ta miƙe da carbi a hannunta ta je a hankali ta buɗe window ta leƙa.
Sosai garin ya ɗinke da duhu sanadiyyar dare da Allah ya sanya ya zamo mahuta a wurin bayinsa.
Mamaki take har yanzu da al'ajabi yanda wasu suka lalata rayuwarsu da mugun nufi da zalunci. Ubangiji da kansa yace ya haramtawa kansa zalunci sannan ya sake cewa ya haramta zaluncin a tsakanin bayinsa. Duk da wannan amma wasu suke keta iyakar Ubangiji ba tare da tsoro ko tunawa da cewa akwai mutuwa, akwai hisabi, kwanciyar ƙabari da kuma tsayuwa domin hisabi ba.
Duk mutanen da za su iya keto DUHUN DARE su shigo gidan mutane kai tsaye ba tare da laifin komai ba su yi wa yarinya fyaɗe, su ƙwace dukiyar da ba su ne suka sha wahala wurin nemo ta ba sannan har da yin yunƙurin kisan kai ai al'amarin waɗan nan mutanen ya ɓaci. Babu Allah Sam a cikin al'amarin su, kuma wallahi da sannu ko a gidan duniya ko kuma lahira za su girbi abin da suka shuka.
Hawayenta ta share a hankali tare da girgiza kai ta janyo windown a hankali ta rufe daga ƙarshe sannan ta koma gefen Anaam wacce ke kwance da bututun iska har yanzu a baki da hancinta ta shiga tofa mata addu'a a hankali tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta sumbaci goshinta idonta cike da ruwan hawaye ta miƙe tana gyara mata duvet ɗinda yake lulluɓe da jikinta.
Ta ka wa ta yi a hankali ta kalli Aysha wacce ke kwance a saman matress a ƙasa, sosai ta ji wani sabon tausayinta tuna yanda hankalinta ya tashi a ɗazu ganin yanda Mijinta Mukarram da kuma Yayan shi Muhammad suka so yin rigima bayan ga halin da familyn yake ciki.
Hasken fitilar ɗakin ta rage musu sannan ta fita ta ja musu ƙofar a hankali ta nufi ɗakin Alhaji Galadima.
Tsaye ta cim mishi jikin window ya buɗe ta yana kallon waje da tarin damuwowi a cikin ransa.
Jin alamun shigowa ya sanya shi waigowa a hankali sai suka yi ido biyu.
"Alhaji! Kana nan har yanzu baka kwanta ba? Ya kamata fa ka riƙa samun baccin yanzu kamar yanda likita ya faɗa maka..."
Jinjina kai ya yi yana mai kallonta ya ce.
"Hajiya Nasmah ke ce zan faɗawa haka. Ya kamata ki riƙa hutawa idan dare ya yi..."
Wasu sabbin hawayen da suka silalo mata ne ta share tare da matsawa a kusa da shi a hankali ta ce.
"Bana iya bacci Alhaji...Wallahy bana iya bacci."
Jinjina kai ya yi yace.
"Ina jin tsoro Hajiya Nasmah...abubuwa da yawa sun faru ko Ince suna kan faruwa. Ina jin tsoron kada na wayi gari ace na rasa Maryam. Idan MARYAM (Anaam) ta mutu ta barni a duniyar nan ban san a wane hali rayuwa ta zata kasance ba, sannan idan kuma ta ci gaba da rayuwa ina jin tsoron halin da za ta kasance a ciki na baƙin cikin wannan abun da ya faru da ita. Tana da buri, tana da mafarkai da yawa, amma waɗan nan azzaluman mutanen sun shigo rayuwarta da mummunan giɓin da har mutu ba za ta manta ba. And again ki kalli gidana Hajiya Nasmah yanda 'ya' yana suka fara rikici a tsakaninsu, Mukarram har yana iya ɗaga wa Muhammad murya... "
Hannu ta kai a hankali ta ɗora akan kafaɗarshi tana shafawa tare da kwantar murya sosai tana mai ɓoye hawayenta domin ta ƙarfafa shi ta ce.
" yana daga cikin ɗabi'un mumini na ƙwarai yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta. Allah ya kan jarabci bawan sa a duk lokacin da yaso, ya rage ga wannan bawan ya zama mai tawakkali sannan ya rungumi wannan al'amarin hannu biyu ya gode masa domin shi ne Allah wanda baya kuskure. Wanda shi wannan bawan Idan kuma bai yi haƙuri ya zama mai godiya ba, sai Kaga ya taɓe al'amarin rayuwarsa kuma sun taɓarɓare. Allah ya baka yara maza guda uku ya baka mace ɗaya sannan ya shiryar maka da su, ya baka surukai na gari sannan ga jikoki har guda shida, yanzu da ya yi maka wannan jarabawar...Ka yi haƙuri Alhaji, ka mayarda komai a wurin Allah ka yi addu'ar mafi alheri. In sha Allahu komai zai yi daidai, komai zai dawo watarana kamar ba'a yi ba. "
Jinjina kai ya yi tare da kallon fuskarta yana mai jin yanda nauyin da ke ƙirjinsa ya ragu sosai ya ce.
" Haƙiƙa maganar ki haka take Hajiya Nasmah, na gode sosai da wannan tunatarwar...Sai dai kuma, abin da na yi nazari a kai na kuma yanke hukunci shi ne, ina so su Muhammad su janye daga wannan maganar kada su sake zancen Alhaji Gimba har abada indai akan wannan maganar ne, zato ba shi da kyau a musulunci koda ya zama gaskiya, ni kaina ina da abubuwa da yawa da zan iya zargin Alhaji Gimba da su, sai dai ba zan yi hakan ba, domin ko na yi abin da ya faru dani da iyalina ba zai canza ba har abada. Saboda haka duk wani bincike ina so a daina shi, duk wata ƙara da suka shigar ko suke ƙoƙarin shigarwa su janye ta, domin babu wani abin da za ta ƙara janyowa sai matsala da ɓacin suna da zubewar mutunci..."
Girgiza kai ta yi tace.
" To amma Alhaji a haka za ka ci gaba da hulɗa da shi?"
Jinjina kai ya yi alamar eh sannan ya ce.
" Ba komai Hajiya Nasmah, tare muka rayu tsawon shekaru da dama, shi ɗin abokina ne, don abubuwa sun faru haka ba zan daina abota da shi ba, domin bamu da tabbacin shi ne ya aikata mana hakan ko bashi ba ne. Ba komai, mu ci gaba da zamanmu a haka har mai rabawa ta raba watarana."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce.
" Shi ke nan Alhaji. Allah ya kyauta, Allah ya ci gaba da bamu kariya ya ɗoramu akan maƙiyanmu na fili da na ɓoye. Ya kamata ka kwanta haka nan Alhaji..."
Ta ƙarashe maganar tana mai kallon katafaren gadonsa wanda Mubarak ya gama shirya masa a ɗazu ya kwanta kamar da gaske, sai da yaga mubarak ɗin ya fice ya tashi ya zauna.
Tana cikin ƙara kakkaɓe masa gadon ne ta ji muryarsa yana faɗin.
" Za ki tsaya dani a nan ɗin Hajiya Nasmah?"
Ɗagowa ta yi tare da ƙura ido tana kallon sa na 'yan wasu daƙiƙu sannan daga ƙarshe ta jinjina kai tare da yi masa wani lallausan murmushi mai sanyi ta ce.
"Idan haka kake so zan tsaya."
Zuwa ya yi ya kwanta bayan ta gama gyara shimfiɗar sannan taje ta kashe fitilar ɗakin ta dawo ta kwanta a gefen sa.
******
Washegari, suna dawowa daga masallacin Asuba ya aika Mubarak yaje sashen Muhammad da Mukarram ɗin ya kira su zuwa parlourn sa, bayan ya gama faɗa musu hukuncinsa ya kalli Mukarram ya ce.
"Mukarram! Kana da ɗabi'ar yin fushi sosai, wanda na sha faɗamaka ka riƙa ƙoƙarin iya sarrafa fushinka, manzon Allah S. A. W yace: wanda yake da zafin zuciya yake da tsananin fushi, to a duk lokacin da wannan fushin nasa ya motsa ƙaramar hauka ce take kama shi, wanda a nan ne zai riƙa faɗin maganganu waɗanda ba su kamata ba, ta dalilin wannan ne yace hatta alwala idan ka yi ya kamata ka sake yin wata domin akwai wasu lafuzza waɗanda idan aka furtasu cikin fushi suke karya alwala. Saboda haka ka yarda da maganar yayanka cewa ka aikata kuskure..."
Jinjina kai ya yi cike da ladabi ya kalli Alhajin na su sannan ya mayar da kallon su gun Yaya Muhammad ɗin ya ce.
" Haka ne Alhaji, Haƙiƙa na yarda cewa na aikata kuskure, don Allah ina neman afuwarku da ku yafe mini, Kateh ina neman alfarma da ka yi haƙuri..."
Jinjina kai Muhammad ɗin ya yi yace.
"Ba komai, Allah yasa mu dace. Allah ya bata lafiya amin."