Kenza eBookz

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 4

Duhun dare book 1 complete novel - Chapter 4

Duhun dare book 1 complete novel Chapter 4: Duhun dare book 1 complete novel Chapter 4. "Kateh kana fa jin maganar banzar shirmen da suke faɗa! Wanda ya yi…

3,312 words

"Kateh kana fa jin maganar banzar shirmen da suke faɗa! Wanda ya yi wa Anaam ɗin haka za'a ce wai ba'a san yanda za'a yi a kama shi ba? Ni nan da zan gansa seconds sun yi yawa na kashe shi..."

Cikin kalaman Ladabtarwa Baba Salisu ya kalle sa ya ce.

"Mukarram ya kamata ka nutsu. Duk abinda kwanciyar hankali bai bayar ba tashin hankali ba zai bayar da shi ba. Ka yi haƙuri ka sassauta."

Miƙewa Alhaji Ridwan ya yi ya kalli DCP ya ce.

"Let's go outside Please."

A tare suka fice Alhaji Ridwan ɗin yana gaba, su kuma jami'an suna bayan sa.

A wata rumfar shaƙatawa ya ja su suka zauna akan tsararrun kujerun da ke wurin.

Jinjina kai Alhaji Ridwan ya yi yana mai kallon DCPn ya ce.

"Ina baka haƙuri DCP... Haƙiƙa suna cikin jimami da tashin hankali shiyasa ka ji Mukarram ya yi magana haka. Amma ni ma a gareni gaskiya wannan maganar ba magana ba ce ku ce wai babu ta yanda za'a yi a gano waɗannan sheɗanun mutanen."

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya jinjina kai ya ce.

" Magana ta gaskiya ranka ya daɗe a yanzu dai, babu wani bayani. But za mu ci gaba da bincike in sha Allah. Ko a ma'aikatan gidan har yanzu bamu samu wata makama ba."

Hannu ya bashi alamar godiya yace.

" Shi ke nan DCP. Mun gode sosai. Allah ubangiji yasa mu dace, Allah ya bayyanasu ko su waye ya tona musu asiri."

Miƙewa su ka yi DCPn yana mai faɗin.

" Amin Yah Allahu. Mun barku lafiya."

Cikin parlourn ya koma bayan sun wuce ya zauna cikin nutsuwa ya fara musu magana musamman Mukarram wanda ya fahimci cewar yafi kowa ɗaukar zafi.

" Dan Allah abin da nake so da ku dangane da wannan abun da ya faru....komai fa da kuke gani muƙaddari ne daga Allah. Duk abinda Allah ya ƙaddaro cewa zai sami bawansa to babu wanda ya isa ya hana. Mu ɗauki wannan abun da ya faru a matsayin ƙaddara. Idan muka ce zamu ci gaba da hakan to har abada zamu ci gaba da ƙuntata a zuwan kowace rana. An rasa rai kuma aka haƙura aka ci gaba da rayuwa ballantana wannan ɗin, mu yi haƙuri,mu maida hankali wurin ceto rayuwarta, su kuma Allah ya tona asirinsu...."

Miƙewa Mukarram ya ƙara yi yana mai kallon Mubarak ya ce.

" Mubarak mi ma kace wannan ɗan daban ya faɗawa Alhaji??"

Jinjina kansa ya yi ya ce.

" Yauwa...cewa ya yi wai su ɗin 'ƴan aike ne right? kuma duniya ta lalace yasan irin abokan hulɗar da zai riƙa mu'amala da su ko?"

Wani irin tafa hannu zai yi yana wani jinjina kai cikin ɗaga murya ya ce.

" To na ma gane kowaye ya aikata mana wannan abun! Alhaji Gimba ne...Yes! Alhaji Gimba... "

" Mukarram ya Isa!!!"

Cewar Yaa Muhammad yana mai yi masa wani kallon da ke nuni da cewa kamar ya fara zaucewa.

Kallon Yayan nasa ya yi yana jinjina kai ya ce.

" Shin wai Kateh mamaki ka ke Ko kuma tantama? Alhaji Gimba kowa yasan cewa shi ne wanda yake takun saƙa da Alaji tsawon lokaci...and bai fi 3month ba da yazo yace a ba wa ɗansa Faris auren Anaam aka ce a'a. To ka gayamin idan ba shi bane waye?? Waye nace ya turo su?"

Ido kowa ya zuba yana kallon sa wanda Abbah ne kaɗai wanda idanunsa suke a rufe har yanzu tamkar baya jin abin da yake faruwa.

Ganin yanda Mukarram ɗin ya juya a fusace yasa Muhammad da Alhaji Ridwan suka shiga ƙwalla masa kira amma sam bai waigo ya kalle su ba.

A zafafe yaje yaja motar kai tsaye ya nufi gidan Alhaji Gimba ransa na masa wani irin tafarfasa.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 5*

Jin yanda Mukarram ɗin ya figi mota a haukace ne yasa Alhaji Salisu kallon su Muhammad ya ce.

"Madu ka fa san halin Mukarram idan ya yi fushi ko kansa baya saurara. Ya kamata ayi wani abun kafin ya je ya aikata wani kuskuren. Idan har wannan zargin ya tabbata akan Alhaji Gimba to lallai nima ina bada goyon bayan a shigar da shi ƙara a tuhume shi...."

Jinjina kai Muhammad ya yi ya ce.

" Ni ma abin da nake tunani kenan Baba,maganar Mukarram tabbas akan hanya take, to amma ta fuskar da yake shirin tunkarar shi Alaji Gimban Sam bai yi ba."

Alhaji Ridwan shi ma ya ce.

" Ba za'a tsaya sanya ba, da zafi-zafi akan bugi ƙarfe. Bari na kira DCP na yi masa bayanin abin da yake faruwa.."

Jinjina kai Yaa Muhammad ya yi ya ce.

" OK, bari na je ni kuma na dakatar da shi Mukarram ɗin nasan halin sa sarai da abin da zai iya. "

*******

Ɗakin Anaam kuwa, tana nan dai jiya wa yau. A yanzu sun yi nasarar ce to ta amma kuma she's still unconscious Wanda tsawon a week yanzu amma babu wani improvement sosai. Hakan yasa suka shiga shirye-shiryen fitar da ita waje kamar yanda Dr. Anil ya basu shawara. Domin ko akan yanda mutanen gidan motsi ɗaya zuwa biyu sai sun tambayi yanayin jikin na ta ya kamata ace an fitar da ita.

Yanzu ma Aunty Aysha ce a ɗakin (Matar Mukarram) ita da Na'imatu suna haɗa kayan Anaam ɗin domin tafiya da ita zuwa ƙasar Indiyar kamar yanda aka tsara.

A hankali Hajiya Nasmah ta turo ƙofar ta shigo wanda itama har yanzu jikin nata ba don ya gama dawowa daidai ba. Ƙarfin hali ne kawai irin na Uwa, tunda ta farfaɗo ta kasa samun nutsuwa, kullum cikin kuka take da salloli tana gayawa Allah akan ya ba Anaam lafiya sannan ya saka mata akan wannan zaluncin da waɗan nan mutanen suka yi mata. Idan sau dubu za ta kalle ta sai ta ji zuciyarta ta karye.

Da sauri Aysha ta miƙe tana mai sakin murmushi ta ce.

"Ammie barka da fitowa."

Murmushi ta mayar mata itama tace.

"Yauwa Aysha. Ya mai jikin?"

Kallon gadon da Anaam ɗin ke kwance tayi sannan ta waiga ta kalli Ammien ta ce.

"Mai jiki da sauƙi Alhamdulillah!"

Wuri Ammie ta samu ta zauna sannan tace.

"Kinga fa daga yin sallahr Azahar bacci ya ɗauke ni, shi ne kuma Amina tana gani amma bata tashe ni ba...sannan ga yaran nan gabaɗaya sun tare wurin Nene sam ko ɗuriyarsu baka ji..."

"Eyyah! Ai gwanda kam da ta barki ki ɗan hutu Ammie."

Murmushi kawai ta yi tare da jinjina kanta,waɗannan surukan na ta guda biyu wato Aysha da Amina, babu abin da za ta yi da ya wuce godiya ga Allah domin yanda suke ƙaunar ta, suke kuma ƙaunar zuri'arta da son zaman lafiya ko itace wacce ta haifesu da cikinta sai haka.

Yara ne masu matuƙar biyayya da haƙuri da kuma son zaman lafiya.

Hannu ta miƙa ta ɗauko wayarta da aka kira wacce ta ajiye yanzu da za ta zauna.

Sunan Hajiya Hanne shi ne ta gani yana yawo gaban screen ɗin wayar,wacce ita ɗin ta kasance Yayarta wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya.

A hankali ta ɗauka ta kara a kunnen ta tare da yin sallama.

Bayan sun gaisa ne, Yaya Hannen daga can ɓangaren ta ce.

"Ya batun tafiya da Anaam ɗin?"

"Goben ne In Sha Allahu."

"To Allah Ubangiji ya kaimu rai da lafiya. Allah ya bata lafiya. Sai na shigo gobe da safen In Sha Allahu."

"Allah ya kai mu Yaya Hanne. Na gode sosai. Ki gaida gidan."

Bayan ta ajiye wayar ne ta kalli Na'imatu ta ce.

"Na'imatu je ki ki kawo min maganin nan dan Allah, sannan fura za ki ɗauko min da Empty cup da kuma ruwa."

Miƙewa Na'imatu ta yi tare da ajiye wayar da ke hannunta ta ce.

"To Ammie."

Tana fita Ammien ta kalli Aysha ta ce.

"Kun gama haɗa kayan Aysha?"

Jinjina kai ta yi tare da kallon kayan ta ce.

"Eh Ammie an haɗa. Har wannan Bag ɗin da kika ce a haɗa ta daga baya an haɗa"

*******

Mukarram na isa ƙofar gidan Alhaji Gimba ya dinga babbaka horn tamkar zai ɓalle ƙofar ya wuce ta ƙarfin tsiya.

Cikin tsoro mai gadi ya zo ya leƙo ta ƙaramar ƙofa yana faɗin.

"Waye wannan?"

Suna haɗo ido da Mukarram ya koma da gudu ya wangale masa ƙofar gate ɗin ya wuce a tsiyace wanda ko gama daidaita parking bai yi ba ya fito direct ya shige gidan ba tare da neman izini ba.

Alhaji Gambo na zaune a dining area matarsa Hajiya Salamatu na serving ɗinsa launch wanda dawowar sa gidan kenan ko ƙwaƙwƙwaran minti goma ba'a cika ba.

Miƙewa ya yi cikin jin mamakin ganin yanda Mukarram ɗin yau ya shigo gidan cike da ruwan rashin mutunci ya ce.

"Mukarram lafiya?"

Sai da ya iso har inda yake sannan ya saka hannu da ƙarfi ya daki table ɗin wanda sai da ya yi sanadiyyar faɗuwar glass cups ɗin da ke jere ya kalle sa cike da masifa ya ce.

"Saboda an hanawa Faris aure shi ne za ka tura 'ƴan daba su yi mata fyaɗe?"

Cike da zallar mamaki ya ce.

"What? Wannan wace maganar banza ce haka Mukarram? Miye kake magana a kai??"

Wata irin shaƙa ya kaiwa kwalarsa yana mai kallon sa cikin ido ya ce.

"Ka sani sarai abin da nake magana a kai Alhaji Gimba ka daina wani pretending...kuma wallahi ka sani sai na ɗaureka...zaka biya nan ba da jimawa ba...Duk abin da kasan ka aikata mana sai ka biya.."

Hannu ya saka ya fisge kwalar rigar tasa da ƙarfi sannan ya ce.

"Ka yi kuskure Mukarram! Ƙaramin yaro kamar kai ya yi kaɗan yace zai ja ni a ƙasa ya zauna lafiya! Da ubanka zan yi domin ni shi ne tsara na...and again...Duk wannan bragging da kake yi ni ban san ma abinda kake magana ba a kai ba..."

Wani irin murmushin kama rainawa kanka wayo Mukarram ɗin ya shiga yi tare da jinjina kansa ya ce.

"Oh! Da gaske! Da gaske baka san abinda yake faruwa ba? Duk yanda labarin nan ya baza gari tsawon sati ɗaya za ka ce baka sani ba? Na yi mamakin rashin zuwan ka wurin yi mana jaje Alhaji Gimba daga kai har iyalinka,bayan kai ne mutum na huɗu ko Ince na uku da yafi kusanci da Alhaji sosai."

Cikin sabon ɓacin rai Alhajin Gimba yana mai ɗaga murya yace.

" And so what!! Don ina kusa dashi shikenan abu ya faru da shi sai kuma ku zarge ni?? "

Ƙara matsowa ya yi kusa da shi sosai suna kallon juna da kyau ya ce.

" Yes! Saboda kai ne wanda yake adawa, hassada da baƙin ciki da Alajinmu wanda duk mun san da wannan tsawon shekaru zuba maka ido kawai muka yi muna kallonka. Hatta wannan tafiyar da ya yi last zuwa China sai da ka nuna hassadarka a fili a gaban kowa kace wai kullum shi yake yin gaba, ya tare komai ya hana taurarinku haskawa..ko ba haka kace ba??"

Babu wani alamar tsoro ko ɗar a kalamansa ya jinjina kai yace.

" Ba a yi wani namijin da Mace za ta tsuguna ta haifeshi ba, ni Alhaji Gimba ace na kasa maimaita magana a gabansa ba. Tabbas na ce, na ce ya tare kowace hanya, kasuwancin ƙasashen waje, kasuwancin gida Nigeria, da ma sauransu waɗanda duk a tare muka fara su tun muna yara, har yanzu ya tare komai duk yanzu kasuwancin namu ba a haɗe yake ba, ya hana taurarinmu haskawa, idan kuna da abin da za ku yi Mukarram ku je ku yi!"

" Haka kace Alaji Gimba? "

Jinjina kai ya yi cike da izza yace.

" Haka na ce Mukarram fitsararre! Kuma ina so in tunatar da kai cewa, ita doka ba mahaukaciya bace, da hujja take aiki, to ina baka shawara, kafin ku yi tunanin shigar dani ƙara ku fara tanadar hujjojin da za ku yi amfani da su a kaina....Now!! Get out of my House. "

Jinjina kai ya yi yana mai jin yanda ransa ke wani irin ƙuna ya ce.

" Zan fita! Amma kai ma ina so daga yau ka fara lissafin kwanakin ka na jindaɗi, domin a kurkuku za ka ƙarasa banzar rayuwarka! "

Daga haka ya fice fuu yaja mota ya fice.

Yana fita Alhaji Gimba ya fito ya ƙwala kiran mai gadinsa cikin ƙaraji ya ce.

"Halu!!"

Da sauri ya zo gaban Alhaji bai ko gama rufe gate ɗin ba yana ta ɗagawa Mukarram ɗin hannu yana faɗin.

"Alhaji Mukarram maliya mai dubun tagagi, angon Hajiya Aysha, Uban Mufid da Mufidah, Yayan Anaam da Mubarak..."

Wani irin zazzafan mari Alhaji Gimba ya kifa masa wanda ba shiri ya dawo hayyacinsa tare da zubewa ƙasa yana mai saka hannayen sa duka biyu ya dafe kuncen domin marin ba ƙaramin shigar sa ya yi ba. Haɓa na rawa ya ce.

"Gani Alhaji, barka da fitowa..."

"Ubanwa yace ka bar wancan ɗan iskan yaron ya shigo min cikin gida kai tsaye yana karanta mini hauka..."

Zaro ido Halu ya yi ya ce.

"Alhaji ka yi mini afuwa, ai na ga Mukarram ne. Mukarram ne fa Alhaji ko dai ka manta?"

Hannu Alhaji Gimba ya ɗaga ya sake zabga masa mari a karo na biyu wanda sai da ya sake riƙe kunce ba shiri sannan ya nuna shi da yatsa ya ce.

"Shashashan banza Sakarai! Ni za ka karantawa hauka kace wai ko na manta da cewa Mukarram ne? Daga yau kada ka sake barin ko ɗaya cikin Ahlin gidan Alhaji Mas'ood Galadima su sake shigo mini gida na, koda mata ne kuwa..."

Cikin sauri ya jinjina kai alamar ya fahimta da kyau yace.

" In Sha Allahu an gama Alhaji, tuba nake. "

Cikin gidan ya koma har yanzu yana mai jin zafin abin da Mukarram ɗin ya shigo har gida ya yi masa.

Kallon sa Hajiya Salamatu ta yi ta ce.

" Alhaji wai lafiya? Miye yake faruwa haka? Mukarram ne fa Mukarram naga ya shigo yana wata magana..."

Girgiza kai ya yi ya ce.

"Ke dai bari Salamatu, amma zan yi maganin su..."

"To miye ya faru ɗin? Miye yake magana akai??"

A zafafe ya wani kalle ta cike da takaici ya ce.

"Ban sani ba! Ban sani ba nace! Ki ɓace mini da gani dan Allah."

Juyawa kawai ta yi ta shige ciki ba tare da ma ta ƙara kallon inda yake tsaye ba.

Yana ganin ta shige ya buga wani uban tsaki sannan ya ciro wayarsa yana wani irin murmushin mugunta ya kira waya.

******

A hanya suka yi clashing tsakanin Muhammad da kuma Mukarram, parking suka yi a gefe kowa ya fito wanda Muhammad ne ya fara yi wa Mukarram magana ya ce.

"Mukarram miye kaje ka faɗawa Alaji Gimba? Tun a hanya nake ta fatan Allah yasa ma ba ka cim masa a gidan ba..."

Cikin ɓacin rai ya ce.

"Na cim masa a gidan fa. Kuma a yanda na tuhume sa ya hau wani haƙiƙancewa wallahi tallahi shi ne wanda ya aikata mana haka..."

Girgiza Kai Ya Muhammad ya yi ya ce.

"Mukarram ni ban so ka je masa ta wannan fuskar ba. Kasan fa idan baka iya kama ɓarawo ba to ɓarawon ne zai kama ka.."

"Kateh! Alaji Gimba da Faris sai sun je gidan yari nan ba da jimawa ba..."

Daga haka ya juya ya shige motar sa tare da bata wuta ya yi tafiyar sa. Kallon motar Ya Muhammad ke ta yi wanda har sai da ya ɓacewa ganinsa sannan ya shiga tashi motar ya wuce.

Ya so ya wuce gidan Alhaji Gimban amma kuma sai wata zuciyar ta gargaɗe shi. Hakan yasa ya juya ya koma suka wuce wurin DCPn kamar yanda Alhaji Ridwan ya tsara.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*D U H U N D A R E* *A 2026 N O V E L* *BOOK ONE*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHEEM* *OUM-AMEER* Arewapen: @Oumameer2671 Wattpad: @Ummu-Amir

*PAGE 6*

Misalin ƙarfe takwas na dare, Alhaji Mas'ood na zaune a parlournsa ya yi resting bayansa jikin kujerar da yake zaune tare da lumshe ido wanda tunda abun nan ya faru,Shi ma ya daina yi wa kowa doguwar magana sai idan ta kama.

A hankali Muhammad ya yi sallama ya shigo hannunsa ɗauke da tray Wanda yake ɗauke da abinci da ruwa.

Center table dake gefe ya janyo ya ɗora abincin a hankali sannan ya zauna a gefen Alhajin ya ce.

"Alaji barka da hutawa!"

A hankali Alhaji Mas'ood ya ɗago ya kalle shi yana mai jinjina masa kai kawai ba tare da ya amsa ba.

Cike da nutsuwa a kalamansa yace.

"Alaji ya kamata ace ka sassauta akan wannan al'amarin da ya faru,gabaɗaya baka hayyacinka, mu fa ka sani, dogaronmu Allah ne sannan kai, idan wani abu ya sameka mu ya sama sannan gidan nan zai rushe ne idan ba kai, Allah ya riga ya hukunto da wannan abun sai ya faru, ka yi haƙuri ka fawwalawa Allah komai. "

Jinjina kai ya yi yana mai kallon Muhammad ɗin ya ce.

" Na gode Madu.. "

" Alaji ba zancen ka gode ba ne. Dan Allah ka ɗauki maganata, yanayin da kake ciki baya mana daɗi at all. "

Daga haka ya janyo abincin ya shiga bashi da kansa yana ci a hankali.

Abinci wannan ba ci yake ba, Muhammad ɗin ne ko Mubarak kaɗai ke saka shi ya ci ko Mukarram, Hajiya kuma tana can tare da Anaam. Gabaɗaya gidan ya zama shiru tamkar gidan mutuwa. Wanda a can baya kafin faruwar wannan abun gida ne mai cike da nishaɗi da zallar farin ciki. Musamman Anaam da ke auta wacce Alhaji Mas'ood ke tsananin ji da ita, haka ma duk mutanen gidan kowa Anaam ta shi ce domin tana da matuƙar shiga rai, ga ladabi da biyayya da cikakkiyar nutsuwa wacce ta samu tarbiyya mai kyau tun daga tushe. Yayyun nan na ta maza guda uku da take da su kowa yana ji da ita na ƙololuwa. Hatta Mubarak da take binsa, duk da cewa suna yawan yin rigima ta mabiyi da mabiyi Suna matuƙar ƙaunar juna wanda idan wani abu ya samu ɗaya to ɗayan ji zai yi tamkar zai yi hauka.

Alhajin Bai wani ci abincin da yawa ba ya kalli Muhammad ɗin ya ce.

"Ya isa Madu, na gode, Alhamdulillah."

Ajiyewa ya yi sannan ya ɗauko magungunansa ya ɓaɓɓalla masa ya shiga bashi a hankali, yana yi masa bayanin tafiyar da za'a yi da Anaam ɗin zuwa ƙasar Indiya a gobe idan Allah ya yarda, yana yi yana tattara kayan ne ya ji wayarsa ta yi ringing.

Yana dubawa yaga sunan babban abokin sa Engineer Saleem. Sai da ya yi kamar ba zai ɗaga ba sannan dai ko me ya tuna kuma, sai ya ɗaga ɗin bayan ya sake kira a karo na biyu.

Yana ɗagawa daga can ɓangaren Saleem ɗin yaj ji muryarsa hankali a tashe yana faɗin.

"Galadima ka kuwa san abinda yake faruwa??"

Da sauri Muhammad ya girgiza kai tamkar yana a gabansa ya ce.

"A'a Engineer! Miye ya faru?"

"Idan kana kusa da TV ka kunna ka kamo gidan TVN Aminta ko kuma ka duba channel ɗinsu a YouTube yanzun nan, kai da ma sauran kafafe..."

Lokaci ɗaya Hajiya Nasmah ta shigo parlourn tare da Mubarak, Aysher da kuma Na'imatu.

Kallo ɗaya za ka yi wa fuskokin su ka tabbatar cewa akwai damuwa wanda su ma da alama akwai mummunan labarin da suke ɗauke da shi.

Muhammad kuwa, kashe wayar ya yi wanda bai ma jira Saleem ɗin ya gama dire zancensa ba, ya tashi ya kunna makeken TVn parlourn ya ɗauki remote control ya kamo tashar.

Lokaci ɗaya idonsu ya sauka akan Alhaji Gimba, yana tsaye ga 'yan jarida sun kewaye shi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull