Farhatul qalbi complete - Chapter 18
Farhatul qalbi complete Chapter 18: Farhatul qalbi complete Chapter 18. _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI…
4,491 words
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞 _NA_
_NANA HAFSATU_ _(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:52_
___
*Kasancewar* asabar ce. Hakan yasa bai fita aiki ba. Yana zaune a parlorn kasa yana kallon wasan kwallon kafar da ake bugawa na Manchester united da Fc Barcelona.
Wayar sace ta fara kara. Kiran waya ne yake shigowa. Daukar wayar yayi kamar ba zai amsa ba. Sai kuma ya dauka ganin me kiran Useey ne abokin sa.
Ya dauka yana sallama. Hade da rage muryar talabijin din da ke yi. Gaisawa sukayi can ya zare wayar a kunnen sa yana kallon screen din wayar. Date ya kalla baki daya ya shafa'a ranar itace wadda suka tsayar kan ziyartar da zasu kawo gidan sa. Ya sosa keyar sa kafin ya ce da useey din.,
"Eh mana maza. Allah ya kawo ku lapia. Bayan sallar la'asar ko? Alright ." Ya katse kiran.
"Ahlam.... Ahlam.."
"Na'am." Ta amsa shi tana mai sakkowa daga matattakalar benen sama.
"Yauwa... " Ya fada yana mikewa tsaye.
"Ya akai?"
"Baki zamu yi...Mai da me zaa kawo?"
"Baki kuma?" Ta tambaye shi idanun ta akan sa.
"Eh... Da hausa nayi magana ai."
"Tab.. Ni wallahi bansani ba. Tambaya Waheedah mana." Ta fada cikin rashin damuwa da koma su wanene.
Ya daga kai ya kalli agogo kafin ya girgiza kai kawai.
"Tana ina?"
"Tana daki mana."
Kai tsaye ya isa kofar dakin ya shiga knocking. Muryar karatun qur'anin da take na tashi ahankali cikin lugga da bil tartil na tajweed. Ya lumshe saboda yadda karatun da qira'ar ke tafiya a sanyaye mai cike da dadi.
Ya sake dan bubbugawa ahankali. Waheedah bata tsaya ba sai data kai karshen ayar tukun sannan ta ajiye qur'anin. Ta mike sanye take cikin rigar atamfa doguwa samfarin A shape marar kamawa ta daura dankwali daurin channel o. Ta janyo hijabin ta ta zura kafin ta bude kofar.
Kamshin jikin ta da nasa suka hadu waje daya suka ba da wani sihirtaccen kamshi mai sanyaya zuciyar duk wanda ya shaaqa.
Kasa cire idanun sa yayi daga kanta. Zuciyar sa na zillo tamkar zata fado daga kirjin sa. Ya lumshe idanun ya sake bude wa.
"Ina kwana?" Ta dan rissina ta gayshe da shi.
Shiru bai amsa ba. Gabansa ya tsananta bugawa da sauri da sauri. Dakyar ya iya sai saita kan sa. Ya ce da ita,
"Ki., Ki zo." Yana karasa fada ya bar wajen da sauri. Ya koma tsakiyar parlorn.
Ita kuwa gambal habaru Ahlam🤣 wayar ta na hannunta tana danne danne. Ta bude wani video a Instagram tana gani.
"Ga ni aunty...." Waheedah ta fada cikin girmamawa.
"Okay ba ka gaya mata ba?" Ahlam ta daga kai tana duban Zayn da ya maida kallon sa kan tv.
Ita dai Waheedah ta zubawa sarautar Allah idanu tana jiran cewar su. Zayn ya sauke numfashi zazzafa kafin yace,
"Zamuyi baqi ne... Abokai na ne zasu zo. Su uku. Kinga ai zaa dan yi musu girkuna ko?"
"Eh..."
"To me da me kike bukata na girkin? Abunda babu sai mu sayo "
"Bari na duba." Ta mike ta shiga kitchen ta dudduba. Biro da paper data ke rubuta abunda babu a kitchen din ta dakko tayi list.
Ta koma parlorn ta mikawa Ahlam
"Gashi aunty."
"Okay... Ga shi babe." Ahlam ta mikawa Zayn
Ya karba ya karantawa kafin ya ce da Ahlam din,
"Ki shirya mu sissiyo abubuwan."
"Kai gaskia babe agajiye na ke."
"Me kikayi da kika gaji?"
"Kuje da ita mana .. Tunda ta fini sanin kan abubuwan."
Ya kada kai kawai yana danne leben sa na kasa.
"Mu je..... Wa... Hee.... Dah.." Ya rarraba sunan nata tamkar dan koyo.
Ta daga kai ta kalle shi tana mamakin dama ya san sunanta? Kafin ta bai wa kanta amsar tambayar ta tuni ya fice wajen bayan ya dauki mukullin motar sa.
Ta juya ta dubi Ahlam da ta tattara tunanin ta da nutsuwar ta akan tv da ke nuna shirin keeping of with the Kardashians.
"Aunty mun tafi."
"Okay Waheedah.... Dan Allah kice masa wai yayi mun renewing data plans dina. "
"Tohm."
Ta juya ta shiga dakinta da ke a matsayin na ta. Ta zura takalmanta ta fita zuwa wajen motocin.
Yana cikin motar ya tasheta already. Tana zuwa ta shiga ya fita daga cikin gidan.
Tanata jujjuya yadda zata yi masa maganar datar. Can dai ta ce.
"Aunty tace.... Wai."
"Wai me ?" Ya tambaye ta kansa akan titi...
"Wai ka mata renewing data plan..."
Cikin zuciyar sa abun ya bata masa rai. Amman baya so ta gane kwarai akwai matsala a tsakanin su. Don haka ya gyade kai kawai kafin yace,
"Okay ...."
Yankaba suka je. Waheedah na zaba yana saya. Suka siyo komai daya danganci fannin abubuwan da zatayi amfani da su a girkin. Daga nan suka biya Sufi mart suka cigaba da siyayya.
Shi ke rike da kwandon siyayyar. Yayin da Waheedah ke dauka tana saka wa aciki. Idan ka kalle su zaka rantse da Allah mata da miji ne irin farkon auren nan. Saboda tsananin yadda suka da ce da juna
Ta dauki wani corn flour tana karanta bayan sa. Zayn ya rankwafa. Tururin numfashin sa na dukan jikin ta. Ji yake inama ace halaliyar sa ce.
"Kina bukatar wani abun? Na ki bana gidah ba.... Uhm?"
Zillewa tayi ta na girgiza kai.
"A'ah..."
Suka wuce wurin biyan kudi aka lissafa kaya ya biya suka fita. Ya bude booth ya saka kayan.
Yaja suka dauki hanyar gidah. Kan ta akan carbin data ke ja. Sai ya juya kamar zai mata magana sai kuma ya fasa a haka suka karasa gidah.
Ko da suka je. Nan da nan Waheedah ta shiga yin aiyukan iya karfin ta. Ya yinda Ahlam ke kame a kujera.
"Baka samun data din ba...."
"Ahlam... Bakya gajiya da danna waya ne? Idan ni ba ki da lokaci na. Ke kan ki ba zaki bawa kanki lokaci ba? Uhm? Har abada kan ki na kan waya? Yanzu da yarinyar nan bata nan wa zeyi girkin eh?"
"Yanzu danna wayar ma matsala ne babe? Danna waya rage kadaici yake. Kuma de favorite hobby na ne.... Sannan batun abinci. Ko ba Waheedah dole zaa kawo me yi. To me ya rage?"
Ya girgiza kai yana tabe baki.
"Ba komai..."
Sai bayan laasar Waheedah ta kammala komai. Daki ta koma ta yo wanka saboda kaurin girki da take. Ta cire kayanta ta dauraye ta shanya. Ta zura wata riga fara me karamun hannu da Nadra ta bata.
Lapiar gado ta bi ta kwanta bayan tayi sallah. Sai sauke numfashi take. Saboda gajiyar da ta yi.
Har ta fara bacci tajiyo budewar kofa. Ahlam ce ta shiga dakin.
"Waheedah..."
"Naam.."
"Kizo kiyi serving dinsu. Akwai drinks a freezer ki hada."
"Toh.."
Bayan fitar Ahlam daga dakin. Waheedah ta mike tana rufe bakinta sakamakon hammar data taho mata. Hijabin ta ta zura. Ko glass bata saka ba tafita.
Kitchen ta shiga daya bayan daya ta shiga kai abincin kan dinning. Dai dai shigowar Zayn da abokan na sa. Useey, Lameen da Awais.
Baki daya suka tsaya kallon ta banda Zayn daya wuce ya zauna.
Ta dakko tray din karshe dake dauke da cups ta ajiye.
"Ina wunin ku....?" Ta fada tana jera komai.
Don taga shigowar su. Amman ba zata iya cewa ga kamar su ba. Tunda bata ganin su sosai.
Amsawa sukai baki a sake. Sun zuba idanu suna kalleta daga sama har kasa. Har sai data kurewa kallon su ta koma daki
A tare suka shiga zubawa Zayn ruwan tambayoyi akan Waheedah. Tun yana daurewa yana amsa su har ya dena. Don wasu tambayoyin na saka zuciyar sa radadi. Du bada shi dinma a nasa bangaren yafu kowanne cikin su kwadaituwa da son kasancewa ko mallakar Waheedan ta zama ta sa.
Suka shiga cin abincin suna zuba santin lalle madam Ahlam ta iya girki. Basu gano dawar garin ba. Sai murmushin yake kawai Zayn ya ke. Ya biye musu akan cewar Ahlam din ce ta girka girkin da suke santi.
Yanata doka mata message ta Whatsapp kan ta sakko su gaysa da abokanan sa. Sai data mula ta sha iska tukun sannan ta sakko tana kukkumbura a yatsine ta gayda su ta juya ta koma sama.
Zayn ya harhada zancen bata jin dadi ne da sauran su. Suka yita mata adduar samun lapia mai dorewa
"Har zamu tafi baka kira mana yarinyar nan ba mun gaysa."
"Ba kun gaysa ba...?" Zayn ya basu amsa yana sakatar hakoran sa da toothpick.
"Maza dan Allah ta shi ka kira ta."
"Itama ba dadin take ji ba. "
"To Allah ya basu lapia baki daya.."
"Amin.."
Play station (ps) suka fara bugawa ta tv. Sun jima suna hirar tasu ta abokai har aka kira sallar magrib suka fita sukayi a masallaci suka dawo .
Sai bayan da akayi ishai suka cinye sauran abincin sunata santin daya ki karewa. Daga fita sallar ishain da suka yi daga nan suka wuce joint dinsu sai kuma kowanne ya tafi gidah.
Awais nata kulaficin naci kan lalle a dole Zayn ya samo masa number Waheedah. Shi da gaske yake yana kaunar ta. So yake ya mallaketa a matsayin matar aure. Wadda zata zamo uwar yaran sa.
Zayn ya dube shi kawai ya watsar. Domin ba shi amsa ma bata lokaci ne. Don ba zai taba hada shi da waheedan sa ba. Don kuwa shidinma kullum cikin adduoin sa sai ya kamo sunan Waheedah ya roki Allah da ya mallaka masa ita a matsayin matar sa ta sunnah idan har alkhairi ne hakan agare su baki daya ..
××××××
Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Kwanakin mu nata karewa. Abubuwa na shudewa.
Karatun su Waheedah na ta tafiya cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Suna kuma gane dukkanin wasu darussa da ake koyar da su.
Ya yinda kaunar waheedan keta ruruwa a zuciyar Zayn. Har ya zamto ya fara zautuwa akan batun nata. Hakurin na sa ya soma gazawa.
×× Yau ma hakan take kamar ko da yaushe bayan ta dawo ranar lahadi daga ziyarar da ta kai gidan su.
Ranar litinin da safe ta shirya ta tafi titi ta hau dan sahu ya biya da ita gidan su Basira da fannah ta dauke su suka wuce makaranta.
Zayn ya kuma samun kansa da bin su a baya turyan tiryan har zuwa makarantar. Bayan yaga shigewar su ajin karatu ya samu wani dalibi ya dan ji cikin sa yasanar masa komai har da gudunmuwar tura wa Zayn time table dinsu ta waya.
Ya koma mota ya zauna na ya na mai nazarin jadawalin karatun na su. Wajen aiki ya wuce. Lokacin da zai kasance free period din su kuma a lokacin Zayn ya koma ciki ya faka motar sa nesa da wajen su Waheedah.
Yaga fitowar ta itada kawayen ta. Ragowar pure water din da ke hannun ta ta shiga wanke fuskar tadashi.
Zayn ya zuba mata idanu yana kallon ta. Tayi kyau kwarai matuka ba glasses dinma. Sannan idan ta saka kara wani kyawun ta keyi. Ya samu kansa da sake janyo wayar sa yayi zooming din fuskar ta. Ya dau hotunanta ta camera yana murmushi.
Sai da lokaci ya cika suka koma class. Sannan ya samu damar komawa wajen aiki shi ma. Bayan an tashi ya biya gidan su wajen mahaifiyar sa..
Inda take sheda masa tayi magana da Abiey din su. professor Adams Nasser . Ta karkare da cewar,
"So Abiey din na ku ya yi wa Ummimi tuni akan abubuwan da suke faruwa tsakanin ka da matar ka Ahlam .. Kuma Ummimi ta amince da dukkanin matakin da Abiey dinku yaga ya dace. So Abiey dinku yace na maka maganar. Ko ka duba acikin dangi idan akwai wadda kake da bukata ka aura... Kar a tauye maka hakki. Ka cigaba da zama da Ahlam din. Amman ka kara aure .... Don kaga yarinyar mutane tunda na ga abubuwan naku gaba suke sake yi. Zan mayar ma iyayen su ita. Tunda ni ba yar aiki na baku ba. Ba zeyiwu ba ta cigaba da zama a karkashin ku ba. . So kaji yadda maganar ta kasance."
Zayn ya sauke numfashi kawai kafin cikin ladabi yace,
"Maa.... Wallahi banason auren zumuncin nan.. Dan Allah kada sanadiyyar hakan ya kara bata zumunci Maa. Ba zan iya kara aure da wata daga cikin family ba Maa. Na hakura."
Haj Hameedah ta daga kai ta dube shi shaqeqe can tace
"Ka taba ganin tsatson ku sun auro bare da ba na gidah ba?"
"No..., Amma dai bana so Maa. "
"To kai a naka ganin ya kake so ayi? Kai din da ba mata kake kulawa ba? Tunda can din Ahlam din ce dai. Duk kuwa da hadaku akayi amman kun dede ta tsakanin ku ai."
Shiru yayi bai ce komai ba. Yanata jujjuya yadda zai fadi zancen Waheedah.
"Kayi shiru.... Ba kace komai ba?"
"Maaa... Ni da Abiey zai amince na auro wata daban... Ya kamata a soke auren dangin nan Maa. Kinga nawa beyi dadi ba kar a maimaita. Ni zan sakewa Ummimi magana..."
Haj Hameedah ta daga kai ta dube shi shaqeqe kafin tace,
"Kanata kawo maganar wata daban. Yar gidan wacece? A'ina take?"
Zayn ya taune kasan leben sa ya saki kafin cikin sosa keyar sa yace,
"Waheedah..... Itace wadda ta mai da ranakun baqin ciki na zuwa FARIN CIKIN ZUCIYAH ta maa.... Maa na waheedah itace FARHATAL QALB dina... Na fara kaunar ta tun farkon gani na da ita. Tun kafin na auri Ahlam... Tun bata kai haka shekaru ba Maa.... *
Baki da kunne Maa ta saki. Tamkar gaula. Dimbin mamaki ya hadu ya tokare makoshin ta. Ta ma kasa magana. Ji take tamkar kunnuwanta karya suke mata na maganganun da Zayn ke fadi. Domin tunda take a fadin duniya bata taba gani ko jin Zayn ko a kawo maganar Zayn akan yammata ba. Bata taba ji ya buda baki yace yana kaunar mace fyace yanzu .Kuma ya kamo sunan wadda ko a mafarki bata taba zato ko tsammani ba. Wai yau Zayn. Mai madaukakin zurfin ciki da adana magana.shi ne ya buda baki yana magana akan kaunar mace. Macen ma Waheedah da yake kiran da ita din ce FARIN CIKIN ZUCIYAr sa...
"Ka ce me?" Ta tambaye shi cikin dimbin mamaki.
"Waheedah dai maa.. Dan Allah kar ki ce a'a.... Ina kaunar Waheedah...Kauna irin wadda gangar jiki ke wa zuciya. Zuciya ke aika sako zuwa ga rai. I loved her, with every fiber of my being....
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_ _(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:54_
*SCHOOL OF NURSING AND MIDWIFERY*
*Waheedah* ta cika da mamakin yadda ya san ina ne faculty din su kai tsaye ba tare da ya tambaye su ba, Yaje har kofar ya faka motar.
Basira da fanna na fita ya sakawa motar lock. Waheedah ta saka hannu zata bude ta jita a datse.
Hakan yasa su Basira shigewa ciki su bar ta.
"Mungode.... Zan sauka."
Shiru bai tanka ta ba. Niimataccen kamshin jikin su daya cakudi waje daya sai kamsasa motar yake yi. Ganin tamkar hankalin sa baya jikin sa yasa Waheedah sa ke cewa,
"Ya Zayn.... Zan fita. "
Juyawa ya yi ya sauke manyan idanun sa akan ta. Ta kasa jure kallon sa tana mai mayarda kan ta gefe,
"Waye wancen yaron da na gan ku tare?" Ya tambayeta cikin isa da iyawa.
Tambayar tasa ta daure mata kai ainun. Ina ruwan sa da wanda suke tare?
"Magana na ke miki..." Ya sake fada hadi da juyawa ya fuskan ce ta sosai.
Da kamar ba zata ce komai ba. Sai ta tuna da yanzun a karkashin kulawar su ta ke. Yana da ikon tambaya tunda yanzun sune tamkar marikanta Ba tare da kawo komai ba ta ce,
"Ya Ibrahim..... "
"Meye alakar ku da shi? U in particular. Uhm?"
Ta danyi jim. Can kuma tace,
"Abokin Yaya nane da ya rasu...."
"Allah ya jikan sa ya gafarta masa "
"Amin.. Nagode."
"Ba wani abunda zaki ce bayan haka? Ba wata alaqa ta daban?"
Ta saka hannu ta tura glasses din ta ciki kafin ta bashi amsa da,
"Yace ya na...."
"Uhm ya ki kayi shiru. Yace yana me?"
"Dan Allah zan fita. Na yi latti wallahi."
"Eh ki gayamun gaskia.."
"Gaskiyar kenan."
Ya kada kai kawai. Ya danna button ya cire mata lock. Ta fice da sauri bata waiwaya ba har ta shige ciki.
Zayn ya samu kan sa da sakin tattausan murmushi. Kafin ya ja motar ya bar cikin makarantar zuwa ofishin aikin sa.
×××××
Da sauri ya rufe laptop din gaban sa yana kallon lokaci a agogon da ke daure a wutsiyar hannun sa.
Yana kammala komai ya dauki wayar sa da mukullin motar sa ya fice daga wajen aikin na su.
Kai tsaye ya shige mota ya nufi makarantar su Waheedah yana mai sharara gudu.
In dai ba an canza musu tsarin lectures din ba. Saura minti 20 a tashe su. Don haka yana karasawa ya samu waje yayi parking.
Ya fito daga cikin motar ya jingina bayan sa. Yayin da hannuwan sa biyu ke zube acikin aljihunan gaban wandon sa.
Ba jimawa sosai kuwa students suka fara fitowa daga cikin faculty. Ya gyara tsayuwar sa yana jiran fitowar ta.
Ita da Basira ne suka fara fitowa sai fannah da ke bayan su. Basira ta bude baki tana,
"Laa kinga ya dawo daukar mu.."
"Yana ina?" Fanna ta tambaya tana leke.
Waheedah na daga kai ta hango shi. Gabanta ya ja yayi turus. Ta kasa gane sabon lamarin da ya tsira.
"Ko dai ko dai ...." Fannah ta fada tana dariya.
"Ai kuwa dai .. Na ga ya fara folawa yasin." Basira ta bata amsa itama tana mai shekewa da dariya.
Waheedah wani tuqwiqwin takaici ga taso ya tokare mata a wuya. Ta dube su tana yamutsa fuska,
"Ku fa banzaye ne wallahi. Abun shirme zaku fara ko dai ko dai. Kaffa ku manta a gidan fa na ke. Maybe Maa ce tasa ya dinga kawo ni yana dakko ni. Yau ne fa kawai ya kawo mu sai wani dashare hakora kuke yi kafin ya ganku ma ya zata farin ciki mu ke dan zai dauke mu."
"Yo ai gaskia abune na farin ciki. Sisi na kudin motar mu yau bai yi ciwo ba. Allah ya saka masa da alheri. Yau fa har dan party zan hadawa kai na. Da kudin motar yau da banyi amfani dashi ba. Zan sayo gurji da kifin salihu. Gefe daya kuma zobon baba larai."
Fannah ta fada tana dariya. Tana direwa Basira ta dora da cewar,
"Kamar kin shiga can cikin zuciya ta fannen mu. Sai dai ni ba zobo a budget dina. Kankarar ruwa zan siya ta foster Clark din shagon ma'aruf. Na korawa makogaro na. Ya kukaji wannan hadin?"
"Superb kawalli. Lamarin zai bada color. "
Duk bikin zancen nan da su ke Waheedah bata cewa komai. Ta shiga tafiya ahankali tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Ita dai inde har Maa ce ta sa Zayn ya dinga kawota ya na kuma mayar da ita gidah idan an tashi gaskia bata so. Da da hali da an soke umarnin.
Haka suka karasa har wajen motar sa. Yan faculty duk sai suka tsaya suna bin su da kallo. Musanman Zayn din da ke da madaukakin kyau .
"Sannun ku da karatu.." ya fada. Hadi da shigewa cikin motar.
Basira da fannah ma suka bude suka shiga . Waheedah ce kadai bata shiga ba. Tana ta raba idanu. Can dai ta bude murfin gaba ta shiga .
Ya tada motar suka fita daga cikin makarantar. Motar shiru ba mai magana. Sai sanyin ac da ke dukan su.
A haka suka karasa unguwar ta su fannah . Ya kai su har kofar gidajen su. Sai kuma ya juya kan mota suka dauki hanyar gidah su ma.
Yana driving yana satar kallon ta.
"Kina bukatar wani abun....?" Ya tambayeta cikin muryar lallashi.
Sam bata ji ba. Don gaba daya ta lula duniyar tunani.
"Waheedah...." Ya sa ke kiran sunan ta.
"Na'am." Ta amsa shi kanta na kallon waje.
"Kina bukatar wani abun?"
"A'ah....."
"Kin tabbata?"
Nanma tayi biris bata ce masa komai ba. Kasan zuciyar ta take kunkunin ina ruwan sa da abunda take bukata? Uban yan kanzagin shisshigi da fadi baa tambaye ka ba. 🤣
Bai sake cewa komai ba. Domin shi kansa mamakin yadda ya ke susucewa akan Waheedah ya ke. Itace mace ta farko da yake bi yana kuma kwadaituwa da son kasancewa da ita ta hanyar halal. Gashi sam baya gaban ta. Shi kadai ya ke shirmen sa.
A haka ya karasa gidah. Tun daga nesa baba mai gadi ya hango motar . Don haka da wuri ya bude gate din. Zayn na zuwa shiga kawai ya yi da motar sa ciki. Yana mai yabawa baba mai gadin shi kuma baban na saka masa albarka.
Knocking tayi. Kafin ta danna door bell. Sai da Ahlam ta mula ta sha iska tukun sannan ta mike ta bude kofar.
Gidan nan tamkar ba dazu da safe Waheedah tayi gyaren sa ba yanata kamshin turare. Yanzun kuwa yadda kasan yara ne sukayi dabdalar damben su a parlorn. Ga ledoji nan na chocolates Ahlam ta sha ta zubar su.
Waheedah ta karewa ko'ina kallo tana kakalo murmushi.
"Sannu da hutawa aunty..."
"Yauwa my dear sis.... Cikina kamar yasan ke ce dawo. Yunwa nake ji wallahi."
"Bara na cire kaya sai na dora abincin."
"Yauwa pls .."