Kenza eBookz

Farhatul qalbi complete - Chapter 19

Farhatul qalbi complete - Chapter 19

Farhatul qalbi complete Chapter 19: Farhatul qalbi complete Chapter 19. Zayn da ke sauraron komai yayi Allah wadai da banzar dabi'ar Ahlam abincin da zata…

4,432 words

Zayn da ke sauraron komai yayi Allah wadai da banzar dabi'ar Ahlam abincin da zata zuba acikin ta ma ba zata iya dafawa ba sai Waheedah ta dawo.

Komai kaca kaca taki gyarawa. Takaici yasa ya durkusa ya kwashe ledojin ya zuba su a dustbin. Ya dauki air_freshener ta kamfanin turaren yerwa incense and more. Me kamshin oud oudi ya faffesa a parlorn.

Zama yayi akan kujera. Ita kuma gogar taku ta cigaba da kallon da take. Tana kara volume.

"Ba ni ruwa...." Ya fada yana kallon ta.

"Waheedah.... Kawo ruwa. "

"Waheedah ce zata ban ruwan?"

"Eh to menene aciki? Tana kitchen. Hakama ruwan a kitchen ya ke. "

"Ok." Kawai ya fada. Ya mike ya haye sama kansa na matukar sara masa.

Tunane tunane ne dankare cikin zuciyar sa. Ya rasa ta inda zai kamo bakin zaren.

Bandaki ya shige bayan ya murzawa kofar dakin na sa key.

Saboda yadda kansa ke sarawa. Tamkar zai fado kasa saboda tsananin yadda yake masa ciwo ne. Yasa yana fitowa ya kwanta . Ba tare da bata lokaci ba kuwa bacci ya dauke shi

Bai farka ba sai gab da magriba. Yayi sauri ya shiga bandaki yayi tsarki hade da dauro alwala. Ya sauka kasa don tafiya masallaci

Ahlam bata kasan. Sai Waheedah da ke cikin kitchen tana wanke wanke. Da ke kofar a bude take. Tana tsaye agaban sink tana wanke wanken sanye cikin wata doguwar riga marar nauyi.

Masallaci ya fice yaje yayi magriba. Ya zauna yana lazimi har aka kira ishai. Bayan sunyi ishai a jam'i ne ya karasa yan adduuoin sa sai kuma ya mike ya koma gidah

A parlorn kasa ya zauna yana kallon news a CNN . Waheedah ta kammala aiyukan ta ta shige daki ta saka key.

Har ta shige ciki bai dai na waiwayon kofar dakin ba. Yarinyar na tafiya da nutsuwar sa, Tunanin sa dama gangar jikin sa gaba daya. Ya yinda itace FARIN CIKIN ZUCIYAr sa. Kallonta kawai idan yayi sai ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Ta yaya zai gaya mata abunda ke cikin zuciyar sa akan ta? Taya zai sanar da ita ce FARHATAL QALB din sa? Ta ya ya zai gaya mata itace macen da yake ta dakon soyayyar ta tsawon lokaci? Ya sauke ajiyar zuciya kawai

So ya ke ya samu ko da number wayar ta ne....

"Anya tana da waya ne ma?" Ya tambayi kansa cikin gasgatawa.

Ya cigaba da kallon news har wajen 12 saura na dare. Daga bisani ya haura sama don yin bacci.

Ya nufi dakin Ahlam ya murda yaji a kulle.

"Ki gayawa malamar aji.....Da hausa room) Kunnuwan sa suka jiyo masa maganar aminiyar Waheedah . Da alama waya suke yi. Kuma a handsfree ta sa ka.

Ya girgiza kai kawai ya wuce dakin sa. Ko da ya shiga bandaki ya wuce ya dauro alwala da wanka. Ya zura kayan bacci.

Wayar sa ya janyo ya shiga Whatsapp yaci sa'a kuwa Awais yana online.

"Aboki na...." Ya aika wa Awais ta Whatsapp.

"Ah maza ya ne?"

"Steady kawai.... "

"Yauwa, Na ce wacece malamar aji a bloggers dinnan ne?"

Awais ya aika masa da emojis na dariya da hawaye kafin ya amsa shi da,

"Aisha falke mana. Northern hibiscus. Itace suke kira da malmar aji. "

"Alright... Thanks"

Dai-daita kwanciyar sa yayi akan gado. Ya shiga Instagram yayi searching page din northern hibiscus.

Yana shiga kuwa yaga sabon post da ruwan comments a kasan sa.

"Assalamu alaikum Malama.... Ya kamla da dan mutum? Pls keep me anonymous, Ni amarya ce. Malama miji na ne ko shekara bamu yi da aure ba ya canza. Dama can kafin auren baya kauna ta. Na dauka idan anyi komai zai warware. Wallahi Malama sam bana gaban sa. Bashi da aiki sai chatting da yammata a duk wasu social media handles... Kullum idan na duba wayar sa sai naci karo da abubuwan bacin rai. Tamkar ba miji da mata muke ba, Yanzu ma na bara so a parlorn kasa ni ina daki na a sama. Sai ya kusan raba dare acan yana kallo. Malama da yan aji dan Allah a temaka mun da shawara. I will be in the comment section. Thank you."

Mamaki ne ya mamaye sa. Ganin yadda ta girba zance tiryan tiryan kamar gaske. Comments din ya fara bi wasu na bin bayanta wasu na bin bayan sa. Wasu kuma zage ta suke tas. Kasa cigaba da karanta comments din yayi ya fice daga page din

Ya sa ke searching HausaRoom don ganin wanda ta kai can din. Ya cika da mamakin ganin writeups kala kala har ya zo kan wanda yake da tabbacin natan ne.

"Assalam.. greetings Malama. Hide my ID. I got married to the absolute love of my life some months ago. Dan ko shekara ba muyi da aure ba. Gaba daya na kasa gane kansa ya canza. Sam bana gaban sa. Amarya ce ni amman yadda kika san wadda ta tsufa agidan miji haka na gundure shi. Sam bama having lokacin kan mu ni da shi. Baya shiga harkata kwata kwata. Gashi da yawan kai korafe korafe wajen manya. Da ke ni da shi first cousins ne. Manya sun shiga tsakani sau ba adadi amma gaba daya yaki canza halayen sa. Maganar da na ke miki yana kasa yanzu a parlor yana kallo sai ya raba dare acan. Ya zanyi please? Ku ban shawara. Thank you."

Yana karasa karantawa ya daga kansa sama yana madaukakin mamakin Ahlam lalle ta wuce gaban tunanin sa.

Yan social media ta dauka yan uwa da take zuwa tana fadan matsalar ta. Wani abun takaicin ma ta mayar da lefin ta kan sa. Ya cigaba da bin comments wani ya bashi dariya wani haushi.

"Amarya? Kuma first cousins? Yar uwa baku da manya ne a naku dangin da kika ketare su kikazo bidar shawara a duniyar social media? Ni dai ga dukkanin alamu kece me matsalar ba mijin ba wallahi. Allah wadaran naka ya lalace. Irin wannan matan gaba daya basuda sirri. Mijin poster idan kaga post dinnan kana kuma da raayin kara aure ka neme ni please. Zan baka kanwata. Tanada sirri ba zaa taba jin kan ku ba. .... Allah ya kyauta " Zayn ya karasa karanta comments din wani mutumi daya tankawa writeup din Ahlam.

Mutane da yawa kuma sunyi supporting maganar sa. Kowa ita ya dinga ba lefi. Da wannan Zayn ya kashe data dinsa ya sai ta alarm yayi kwanciyar sa bayan ya yi azkar na kwanciya bacci.... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_

💞

_NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:55_

*Tun* asubah daya tashi bai koma ba har gari yayi haske. Already yayi wanka. Mai ya shafa da dangin su turare ya taje kwantacciyar sumar kan sa.

Ya sauya kaya zuwa manya . Riga da wando na shadda. Kalar toka. Samfarin Bauchi style. Ba kadan ba kayan sun amshi zatin haibar sa.

Fita yayi daga cikin dakin. Ahlam na parlorn sama a zaune. Idanunta sun kawo ruwa sun kumbura. Da alama kuka taci ta koshi. Hakan yaso bashi dariya ya danne.

Ya zagaya ya zauna shima akan kujerar .

"Ciwon idanu kike?"

Kallo ta watsa masa. Ta mayar da idanunta gefe.

"Harara kuma..... Meya faru?"

"Au tambaya kake yi me ma ya faru? Kan babban bala'in can."

Wayar sa ya ajiye a gefe ya koma ku sa da ita ya zauna. Hade da janyo hannuwanta cikin nasa yana matsawa. Yayin da idanun sa ya narkar da su akanta. Duk janye janyen ta sai da ta hakura ta sallama.

Rungume ta yayi a jikin sa yana shafa gadon bayan ta da hannun sa.

"Meya faru .... Uhm?" Ya rada mata acikin kofar kunnenta.

"Ni ka rabu da ni....." Ta shiga tirjewa.

"Sssshhh... Calm down! Ahlam, Yanzu abubuwan da ke faruwa da mu. Bakya ganin maslaha shine mu zauna mu biyu mu kamo bakin zaren? Ba ruwan third party....ki ce wani abu mana... Banason wannan kawar ta ki tana shiga al'amuran mu. Kinji dear wifey.?"

"Kawata ce ta rai da rai... Wani baren na gayawa? Kai ma kasan kai ne mara gaskiya. Kana treating dina kaman wata baare. "

"Ahlam... Meyasa ba zaki amince ke me laifi ba ce.? Okay fine! Ni na yadda nima me lefi ne. Allah ya baki hakuri. To me zai hana ke ma ki fito ki bada hakurin? Ki sauya halayen ki. Ki rungumi igiyoyin auren da ke tsakanin mu? Eh Ahlam... Why ?"

Ya ki ce jikin ta tayi daga nasa. Tana hura hanci.

"Ni babu wani laifi da na ke da shi. Kai ne me laifi. Don haka kai zaka canza. Ba ni ba. Atoh."

"Haka kika ce?"

"Eh..."

"Okay fine..." Ya fada hade da mikewa ya koma cikin dakin sa ya janyowani dan box ya dauki abunda zai dauka ya zura a aljihu.

Har zai sauka sai kuma ya juya ya dube ta,

"Akwai wani abun da kike bukata babu? Ko na abinci haka?"

"Subscription dina na Netflix za kayi renewing. Sannan data plan dina ma has exhausted ... Sai ka mun renewing. "

Wayar sa ya duba ya yi renewing mata dukkanin abunda ta fada. Sai kuma ya zaro dubu biyu ya ajiye agaban ta.

"Gashi ko zaki bukaci wani abun daban. Na fita aiki "

Ba godiya baare Allah ya dawo da kai gidah lapia. Ta cigaba da danna wayar hannun ta. Girgiza kai kawai ya yi. Ya karasa sauka .

Su kayi kicibus da Waheedah da ke gyara zaman sandal din kafarta zata fita

"Ina kwana...?" Ta gayshe da shi cikin zazzakar muryar ta mai dadin sauraro da dimbin ladabi.

"Alhamdulillah... Kina lapia?" Ya amsa. Ya kuma ji dadin gayshe da shi da take yi. Ya manta yaushe rabon da Ahlam ta gayshe shi tun satin biyu farko na auren su.

"Alhamdulillah....." Ta amsa shi. Hade da bude kofar.

Ya fita. Ita ma ta fice. Cikin zuciyar ta tanata kwarara adduar Allah yasa ba zai dauke ta ba. Bata karasa adduar ba tajiyo shi yana cewa,

"Muje ko? Motar awaje nayi parking tun asubah."

Ta kasa cewa komai. Tamkar ta fasa ihu saboda takaici. Ta daga hannu tana nuni da yatsan ta cikin gidan.

"A...an..abincin safe." Ta samu kanta da amsa shi da haka.

"Oh abinci ko. Ko zaki mun packaging ?sai na tafi dashi office. "

"Toh.." Ta fada, Hade da juyawa ta koma cikin gidan.

Ta harhada komai ta saka acikin kwando . Komai tsaf tsaf. Kamshi sai tashi yake yi.

Already ya fita yana jikin motar sa awajen .

"Gashi .."

"Alright... Thank you! "

Ya shiga motar ya tashe ta.

"Shigo mana..."

"Okay .."

Shiga tayi . Kanta a kàsa sai murda yatsunta take. Ta rasa madafa.

Har sun hau kan titi ya juya ya kalleta. Kafin ya zaro wayar da ke aljihun gaban rigar sa.

"Rike.... Naga ba ki da waya ko?"

Ta daga kai alamun eh. Kafin ta danyi jim kuma. Can ta ce,

"A'a ka bar shi.."

Ya danyi murmushi. Kwarai matuka yana kaunar halayen Waheedah. Yarinya mai nutsuwa da cikar kamala. Ga ladabi da biyayya.

"Ni ba yayan ki ba ne?"

"Shi ne..."

"Tohm dan Yayan ki ya baki waya wani abune?"

"A'ah."

"To saboda emergency issues haka dai bama fata. Amma ai ya kamata ace da waya a hannun ki. Ko dan saboda pdfs na books da assignment haka na school. Ko?"

"Eh..."

"Yauwa to rike."

Karba tayi da hannu biyu. Waya ce Samsung mai kyau purple color. Daga gani kuma sabuwa ce.

"Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara yalwar arziki."

"Aamin Amin. Ban kuma ce kije kina yadawa ba kan na baki waya da sauran su. Ga wani charger nan idan kin bude wajen nan zaki ganta type c ce. Akwai sabon sim aciki. Allah ya bada sa'a ."

Sai jujjuya wayar ta ke. Ba kadan ba wayar ta tafi da ita. Ga ta da kyawu kuma sam babu nauyi.

Ta janyo charger ta rike hade da wayar. Gaba daya dimbin farin ciki ya mamaye mata zuciya da duk wasu gabobi na jikin ta.

"Nagode.... Nagode Allah ya saka da alkhairi. Allah ya kara budi. Nagode "

Yadda fuskar ta ta mamaye da farin ciki ne ya samu kansa shi ma da yin murmushin.

Har suka karasa layin su fannah sam Waheedah hankalin ta na kan wayar ta. Sai danne danne ta ke. Zayn ya yi parking a kofar gidan . Ya zuba mata idanu

"Banda dai kule kulen samari. Ki tsayda hankalin ki akan karatu kinji ko? "

"Insha Allah..." Tana daga kai taga ai har sun karaso

"Laaa" ta fada da sauri ta fice. Ta shige gidan su Basira suka biyawa Fannah.

Waheedah ta zaro wayar tana nuna musu. Suka shiga tsalle suna masu tayata murna sosai suma.

Nan take taji kaso goma sha biyar acikin tsanar da tayi masa ya goge a zuciyar ta.

Suka shige motar ya ja su sai school of nursing.

Har kofar twin theatre da za suyi lectures din ranar ya kai su. Waheedah ta shiga rudani mai tattare da mamakin Zayn .

Ta kasa gane kan yadda yasan komai na daga harkar karatun su .

"Suna jiran ki fa..." Ya fada yana nuna mata su Basira da ke tsaye suna jiran tafuto daga mota su tafi aji.

Ta kasa ce masa komai. Ta fita daga cikin motar tana waiwayon sa. Murmushi ya sa ki kawai. Ya ja motar sa ya fita daga cikin harabar makarantar. Ya yin da su kuma suka shige ajin da zasu dauki darussan ranar.

××××

Sannu a hankali haka kwanaki ke ta tsere mana. Waheedah sunyi sabo kwarai matuka da Zayn. Ta dauke shi tamkar madadin yayanta Kamal.

A nasa bangaren kuwa dakon jidalin kaunar ta ne kullum ke dada tasiri a zuciyar sa da gangar jikin sa.

Yana kaunar Waheedah fiye da yadda alƙaluma zasu rubuta. Zuciyar sa na begen samun Waheedah a matsayin matar aure.

Gangar jikin sa na ingiza da kwadaituwar kasancewar Waheedah a tattare da shi.

Amman gaba daya ya kasa sanar mata. Ta kuma kasa gane inda ya nufa. Ta riga da ta dauke shi a matsayin dan uwan ta na jini. Tamkar babu aure a tsakanin su.

Ganin yadda kullum ya ke dada karewa a tsaitsaye. Gashi Maa ta ki zama ta fuskanci maganar. Ranar da ya sake zubewa ya nemi rokon alfarmar samun Waheedah. Ta wanke fuskar sa da gigitaccen marruka a dama da hagu na gafen fuskar sa.

Bai sake bi ta kanta ba da maganar. Kai tsaye ya samu mahaifin sa ya sanar da shi. Alokacin kuma Ummimi mahaifiyar mahaifin su ta zo .

Zayn ya kasa cigaba da boye maganar. Daman Ahlam ta karasa kai shi karshe da halayen ta. Tamkar zaman haya haka suke yi a gidan na su. Ta tattara shi ta watsar a gefe.

Hakki na rayuwar aure ma sai ya ta rokon ta zata bashi dama. Idan kuwa bataga dama ba sam bata bari ya kusance ta.

Dukkanin abubuwan da ke faruwa daman dangi sun sani. Don haka zuwan da Ummimi tayi ta kirawo dukkanin sauran yaran nata da ke kusa da matayen su. Ciki har da mahaifiyar Ahlam.

Ummimin tace gwara ayi me yiwuwa. Ta yanke ta gille. Ahlam dinma Ummimi ta sa Zayn ya kawo ta gidan na The Adams Family.

A babban parlorn gidan duk suke a zazzaune. Ahlam sai wani fiffika ta ke yi. Ummimi tayi gyaran murya ta fadi komai a takaice. Kasancewar kowa ya san masaniyar tsakanin Zayn da Ahlam .

"To ni Ummimi menene laifi na? Shi ne tun farko dama ai ba kauna ta yake ba. Bayan munyi aure halayen sa suka fito " Ahlam ta fada tana hararar Zayn.

"To naji mu dauka ace hakanne. Ke menene yasa kike tauye masa hakkokin auren sa da ke kan ki? Eh? Tsinke wannan bakya dauke wa karya nayi?"

"A'a..."

"Toh kadan kenan daga cikin sakacin wasu matan akan bai wa yan aiki ragamar komai na rayuwar aurensu......🤸

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_

_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_

💞

_NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:56_

_____

Ahlam ta daga idanu da sauri ta dora akan Ummimi. Kafin cikin bacin rai da takaici tace,

"Bangane ba Ummimi.... Sakacin me nayi?"

"Da fari kafin ma a samo miki me tayaki aiyukan. Ba almajirai kika dauka har biyu ba yara suke gudanar da aikace aikacen gidan baki daya?"

Ba tare da ta ce komai ba. Ta zumbura baki gaba tana mai yatsina fuska. Ummimi ta sake zare mata idanu,

"Tambayar ki na ke kinyi shiru. Haka ne ko ba haka ba ne?"

"To ai aiyukan ne sunyi yawa ba zan iya ba ."

"Haba Ahlam, To menene ladan da zaki samu na rayuwar auren idan har bakya aikace aikacen gidan da mijin ki zai sanya miki albarka? Kullum kina kwance kamar ruwa lamama. Da waya a hannun ki hannu bibiyu. Tunda na ke ban taba ganin me danna waya a duniya irin ki ba Ahlam. Na hane ki tun kafin auren nan ashe baki dai na ba? Kinyi uwar watsi da zance na.... "

"Ummimi please ... Abar zancen nan."

"Ba za'a bari ba. Ummimin kike kalla kina abar zancen nan? Wacece ke? Shashasha, sakarya. " Cewar alhaji nouh mahaifin na Ahlam kuma da ga Ummimi.

"Yi hakuri Baba. Kiyi hakuri Ummimi." Ahlam ta basu hakuri. Kanta a kàsa. Ya yinda kasan zuciyar ta ke mata zugi.

"A mata afuwa Ummimi..." Farfesa Adams ya fada yana murmushi

"Ai ni baki daya ba ni da tace wa... Sai fatan shiriya. Allah ya kuma ya huci zukatan dukkanin mu Amin."

"Amin Ummimi."

"Amin."

"Zayn wane hukunci ka yanke akai eh.?" Alhaji Nouh mahaifin Ahlam ya tambaye shi.

Kan Zayn a kàsa cikin ladabi yace,

"Duk hukuncin da kuka zartar ya yi."

"A'ah ai ba zamu tauye maka hakki ba son. Kuma magana ta gaskia duk wanda ya zauna ya auna rayuwar da kukayi da Ahlam zai ga kana cutuwa aciki sosai. Ba bu kuma iyayen da zasu so haka ya faru da dan su. Dan haka ni de a nawa ra'ayin. Rabuwa da Ahlam shine mafi alkhairi a tattare da kai."

Da sauri Ahlam ta daga idanu ta sauke akan mahaifin ta jin abunda ya ke cewa. Saboda bata taba zato ko tsammanin haka daga gare shi ba.

"No kar ka ce ha ka dan uwa. Ni tunanin da na ke ma Allah yasa laifin ba daga Zayn ba ne. Saboda yanada zurfin ciki matuka." Farfesa Adams ya fada yana kallon Zayn

Shi dai Zayn kanzil bai ce ba. Alhaji Nouh ya girgiza kai kafin cika daga yatsa ya nuna Ahlam yace,

"A'ah zancen nan fa ba sabo bane. Anyi fadan Anja kunnen yarinyar nan yafu a kirga. Ni da kai na gata ba karya nake ba wallahi sai da na kirata waya video call lokacin ina Cappadocia. Na ja kunnenta sosai tace mun ta dai na . Ashe ashe labarin kanzon kurege ne. Don haka babu ruwan Zayn wallahi. Ai dama na sha jiyota da mahaifiyar ta ga tanan tana mata fada akan yin aiki da dai na sangarci saboda aure zatayi. Amman taki yi. Ga banzan halayen data tsira na gayawa kawa komai. Da turawa bloggers neman shawara duk fadin dangin da muke da shi ba mu isheta ba mu sai iyayenta na waya. Na karanta writeups dinnan ba adadi wallahi. Ina mamaki wanda ko a mafarki ban taba zato ko tsammanin haka ba. Kuma wallahi wallahi yarinyar nan ba ta kaunar Zayn."

Baki daya sai akayi masa caaaa jin abunda ya fada a karshe kan Ahlam din bata kaunar Zayn.

"Zancen ka na karshe da gyara ...." Ummimi ta fada tana murmushi.

Alhaji Nouh ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa,

"To bata kaunar tara iyali da shi. Wai kamar Ahlam har ta san ta dinga shan contraceptive pills? Kuma guzurin su tayi ta tafi su da gidan. To Ummimi bata kaunar karuwa da shi ai bata kaunar shi wallahi. "

"Eh to da wannan gaskia..."

"Yauwa ..Ni dai idan ana neman shawara ne. Shawara daya zan bayar itace ta rabuwar su. A raba auren nan dubi yadda yaron nan ya zama fisabilillahi. Tamkar ba Zayn ba. Ita kuma dubi yadda take hawa kamar farashi. Idan aka bar shi ya cigaba da zama da ita tabbas an cuce shi. A cire batun zumunci a dubi hanyar gaskiya. Idan ya cigaba da zama da ita Allah karasa illata shi zata yi. Tunda dukkanin abubuwan da suke faruwa ma ba shi yake fada ba tursashi ake idan an ga damuwa a tattare da shi. Kuma ace kaman Ahlam kuna garin nan unguwa ma kusan daya amman bata san ta zo nan gidan ta gayshe da surukan ta ba? Kafin ku zama surukan natan dan uban ta ai iyayen ta ne ku. Kullum 24/7 yarinyar nan tana online tana chatting. Gaba daya rayuwar auren a wasa ta dauke ta da kuma shiririta. Saboda haka gwara a kawowa tufkar hanci. Dan Allah Ummimi.. ko kuwa Yaya?" Ya juya saitin Yayan su mahaifin su Zaid . Alhaji Nouruh.

Alhaji Nouruh ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya dubi Ummimi can ya ce,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull