Kenza eBookz

Farhatul qalbi complete - Chapter 4

Farhatul qalbi complete - Chapter 4

Farhatul qalbi complete Chapter 4: Farhatul qalbi complete Chapter 4. "Mts! Dama na san sai ke wallahi. Tsugudidi kashin o'o. Yanzu banda nemawa kai…

4,482 words

"Mts! Dama na san sai ke wallahi. Tsugudidi kashin o'o. Yanzu banda nemawa kai magana. Akan wani dalilin zaki kashemun radio bayan sarai kinsan ba kida hurumin kashewar? Tukun nama akan wane dalilin zaki ketare ki shigaa cikin daki na iyye? Nace akan wane dalili. Kuma na rantse da rantsuwar ba fashi sai kin gyaro mun radio ta. Yanzu gashi nan kinsa ta denayi baki daya. Dama joganeta nake ahankali na kunna amma saboda tsabar mugunta shine zaki lalata mun. To wallahi sai kin gyaro mun kinji Allah kuwa." Marka ta karasa fada , Hadi da ajiye rediyo din agaban Umma Hadiza dake tsaye tana sauraron Marka ta karasa abunda zata fada.

Doguwar ajiyar zuciyar ta sauke .kafin cikin muryar lallashi da ban girma tace,

"Kiyi hakuri Marka. . Wallahi ba da sani nayi miki haka ba. Wai dan kada batirin suyi sanyi tanata yi ita kadai shi yasa na kashe. Abunda yasa na shigaa tsakar dakin ki kuma dana dawo ne zan gayda ke ba kowa agidan sai Sa'adatu da na hadu da ita a zaure zata fita. Abunda ya saka na kashe kenan wallahi. . kiyi hakuri dan Allah, ki gafarce ni."

"Kinibibin banza dana wofi." Marka ta shigaa mita a kasan makoshi.

"Nace marka kamshin .."

"Dan Allah mai sunan Malam ka kyale ni. Kamshi da kakeji haka nima nake jinsa. Haba."

"Kiyi hakuri Marka. Kamshi kuma gidan dana samu aikatau ne matar gidan zatayi tafiya shine ta bamu kayan miya da taliya da kaji guda biyu. Shine ina dawowa na fara aikin su ban jima da karasawa ba. Ga sunan na zubawa kowa a mazubi."

"Wanne ne nawa?" Cewar Malam NaLado sai wulkita idanu yake yana hangen inda zai gano nasa.

"Gashi Malam naka. Marka ga naki kema. Sa'adatu ga naki ke da yaran. Ke ma Waheedah ga na ku nan."

Malam NaLado ya karba da sauri ya koma kan turmi ya zauna yana ci. Sai gyada kai yake yana lumshe idanu

Hakama marka data karbu nata sai baza hanci take tana shakar kamshin miyar dataji komai ta hadu da dadi. Dama umma hadiza akwai iya girki idan ta samu kayan abinci

Inna Sa'adatu ma data karaci hura hancin ta. Daga karshe bajewa tayi tana ci. Sai taunar kashi kake ji. Kunnuwa na motsawa.

Kamal ne ya fara dawowa. Sai Najibu daga karshe. Umma hadiza ta basu nasu abincin. Tukun sannan itama ta zuba nata tanaci.

Daga ita sai su waheedah dake gefe tana taune kashin cinyar kaza. Alokacin umma Hadiza ke sanar dasu yadda sukayi da Hajia Hameedah. Bata boye musu komai ba. Kwarai matuka sun taya Umman ta su murna. Sai farin ciki ya kara ninkuwa da annushuwa a fuskokin su da zukatan su.

Bayan sun gama cin abincin. Umma hadiza ta dakko dubu daya ta bawa Najibu kan ya siyo sabuwar rediyo ya kaiwa marka. Hakan kuwa akayi ya sayo ya kai mata. Mai makon tayi murna sai ta zo tayi wa Umma Hadizan tatas akan saboda taga ta samu aiki ne zata fara daga kai da nuna isa da izza. Dakyar ta karbi rediyon dan sai da aminiyar ta lawuri ta tausashe ta. Dakyar ta karba

Ranar kukan farin ciki Umma hadiza tayi. Tana kuma sake yiwa Allah godia akan sabuwar rayuwar da suka tsinci kansu ciki.

×××

Haka lokaci yayi ta ja.. Har ranar da za'ai taron wayar da kai akan lalurar sikila)amosanin jini.

Da wuri suka shirya. Kusan dukkanin mutanen unguwar shurah mazan su da mata. Manya da yara duk sun hallara. Kasancewar rana ce ta hutu. Dan haka kwansu da kwarkwatar su sun tumbatsa awajen taron. Wanda wani babban likita zai gudanar da shirin.....

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*

5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:11_

Tunda Marka ta kyallara idanu ita da Inna Sa'adatu akan kaji da yan kayan abincin da Umma Hadiza ta samo a gidan aikinta. Tsangwama, Kyara da tsantsar kiyayyar da suke wa Hadiza da iyalanta suka nunku cikin zukatan su.

Domin Alhamdulillah. Yan sauran canjin da sukayi ragowa awajen Hadizan. Tuni ta auno musu garin kwaki da sukari da kwanon gero. Da kanta takai wa me yar tsala. Zata dinga basu yar tsalan har na tsawon mako 2.

Gashi duk sanda Umma Hadiza zata dafa abinci daga ragowar kayan abincin da gidan Hajia Hameeda taba su. Sai ta dafa ishasshe ta zubawa Marka. Amman duk kyautatawar da takewa Markan bata gani. Sai dai ta cinye ta lashe ta kuma ture kwano tana mitar kadan aka zuba mata. Sam ba godia bare yabawa ga Umma Hadizan.

Baya ga haka kiyayya ce zazzafa ta sake shiga tsakanin Marka da Waheedah. Tunda akayi taron gwaji da kuma wayar da kai akan cutar amosanin jini ta sickle cell Marka ke jin zafin Waheedah a ranta. Musanman da gwajin Na'Ateeku ya fito da matsala.

Tashi akayi da ruwa tamkar da bakin kwarya. Gari yayi luf luf. Bishiyu se kadawa suke suna bada iska mai dadi.

Yayinda ruwan ya yi gyara masha Allah. Wasu gidajen suka cika da ruwa sai aikin kwalfacewa ake.

Gidan MalamNalado da sauran gidajen dake baki bakin unguwar ta shurah duk sun cika maqil da ruwa.

MalamNalado da kansa ya sharce ruwan dakin Marka da nasa dakin. Yayinda dakin Inna Sa'adatu dana yaranta. Su ukashatu da basher suka tsaya suka kwalfe nasu.

Dakin Umma Hadiza kuwa. Waheedah ce ke kwalfewa gwanin ban tausayi. Sai Najib dake tayata kadan kadan domun jikin nasu ya sake motsowa.

Kamal na dakin su. Umma Hadiza na gefen sa tana masa sannu. Dawowar su kenan daga asibitin cikin unguwa.

Sai numfarfashi yake saki yana dartse hakoran sa hadi da tallabo kafarsa ta hagu yana hawaye .

Marka dake wajen dakali a zaune da rediyo a gefen kunnenta tsaki taja mai tsayi tana tabe baki. Kafin cikin kufulewa tace,

"Wai menene haka? Sai wani uban numfarfashi ka ke jerawa tamkar jemammen sa. "

"Kayi hakuri kayi shiru yayan su." Umma Hadiza ta shiga lallabar sa.

"Radadi ne a cikin kasusuwanmu, Misali kafa ko hannu ko baya. Idan a kafa ne ciwon ya tashi sai ka ji kamar ana sara kafar ko ana raba ta biyu Marka, Radadi ne mai wahalar fassarawa." a cewar Najib daya leka kansa wajen Marka

"To uban yan shisshigi da kai na ke?"

"To assalamu alaikum!! Jamaar gidan nan.. wai wai wai. Lalle kuma ruwa ya muku gyara. " Cewar Najan Isubu data shiga gidan tana kwarara sallama hadi da karewa ruwan dake kwarara a gidan da kallo.

Marka na hango Najan ta sauya fuska. Hadi da juyar da kanta gefe tana kara setin rediyonta. Ai kuwa Najan ta zagaya gefen Markan tana daria

"Hajjaju makkatu."

"Najaatu."

"Naam tsohuwa mai ran karfe an buga da ke an bar ki. "

"To ya zaayi da ni.? A haka zaa ganni a bar ni."

"Wannan zance haka yake. Shakka babu. To kar na cika ki da surutu tare muke da maaikaciyar lapia wadda sukayi gwajin jinin mu."

"Ni fa banason tsurfa wallahi. Menene kuma iyye? "

"Kai Marka"

"Ah to yo ai gaskia ne. Karairakin su ne na banza da wofi."

"Dan Allah marka kiyi hakuri kar ta jiyo."

"Gafara can ni. Babu wanda ya isa yayi mum abunda Allah bemun ba."

"Hakane. To dai zan shigo da ita yanzu."

Da sauri Najan ta fita. Nan da nan kuwa sai gashi sun shiga da matar tana biye da ita a baya. Matar suka sbiga gaisawa da Marka da ke yauki kai kace Kashi tagani.

"Fito Hadiza ku koma can. Na tattare nan. Sannu Kamal. Allah ubangiji ya baku lapia."

Umma Hadiza ta share hawayenta. Hannunta daya ta kamo na Kamal suka koma can dakin da shi su Waheedah sun gama kwarfe ruwan cikin sa.

Nan da nan Najan Isubu ta daure mayafinta a kugu ta shiga kwalfe ruwan tana tsane ko'ina.

Sai data gama tukun sannan ta leka ta kirawo Inna Sa'adatu dake kwance akan gadonta tana hambadar ridi.

"Menene ne ake nema na?" Cewar Inna Sa'adatu dake yauki.

"Abunda nagani kenan, Bayan ke da yaran ki lafiyayyu ne, kinga dakta canne dakin uwar marasa lapian ato." Marka ta ce da maaikaciyar lapiar hade da miqa hannu ta nuna setin dakin Umma Hadiza.

Maaikaciyar lapiar ta girgiza kai kawaii. Kafin ta shiga cewa,

"Wato shi wannan ciwo fa Hajia abune daya kamata ace kun bada gudunmuwar lokacin ku da karfin ku kai dama aljihun ku akan wadancan yara masu fama da cutar amosanin jini."

"A saboda me zamu bayar iyye? Bayan shi kansa me sunan malam asirce shi iyayenta sukayi ya aureta. Nan ya tasamun seda na sayar da gonar mahaifin su aka masa auren. Tunda ya aurota kuma gashi nan dansu na farko shanyayye. Ta biyu gatanan kalau akansa amman itama wai seda gilashi take gani. Sai na karshen shima gashi nan a shanye. Baki daya duk abunda mai sunan malam ya mallaka ya kare akan su. Hmm! Wannan yariinya Hadiza wallahi aurota kaddara ne"

"Kash iya kidena cewa haka .. Wato ita wannan cuta, Lokaci mai gajeren zango a dan baya kadan, idan aka yi aure, aka samu juna biyu, aka haihu, bayan kwanaki ko watanni kadan sai kaga yaron ko yarinyar da aka haifa sun mutu, haka ma’auratan zasuyi ta fama da mutuwar ‘ya’yansu, sunata neman magani, je-can, je-can domin samun mafita. Kasuwar bokaye da yan bori sai ta bude, yar-mai-ganye kuwa takan samu wurin baje hajarta a irin wadannan wurare, a karshe abinda za’ace shine, ai matar mayyace, ma’ana ita ce take cinye ‘ya’yanta ta hanyar lashe musu kurwa!

"Sai dai fa, abun ba haka yake ba, “matar ba mayya bace” ba kuma ta “lashe kurwar ‘ya’yanta” Tun farko ba’a tantance kwayar halittar bane, akwai jinsin mutanen da sam bazasu haihu su bayar da da mai nisan kwana ba.Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana dauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su kwayoyin halittar jini masu dauke da ruwa (plasma), jar kwayar halitta (Red Blood Cells, RBC), kwayoyin halittar jini masu kula da garkuwar jiki (White Blood Cells, WBCs), kurgun ruwa (Platelets) da sauransu. Iya

"Cutar sikla ko amosanin jini tana faruwa ne idan aka samu matsala a jajayen kwayoyin halittar jini (red blood cells). RBC yana dauke da sinadarin ‘Haemoglobin (Hb) a cikinsa. Haemoglobin (Hb) kala-kala ne; akwai Haemoglobin A (HbA), Haemoglobin B(HbB), Haemoglobin C (HbC), da sauransu. HbA shi ne lafiyayyen haemoglobin. Sauran Hb ɗin ba lafiyayyu bane.

"Cutar sikila tana daya daga cikin cututtukan da ake iya kauce musu kafin samuwarta. Idan kuma cutar ta samu, to tana da wahalar magani.Idan aka ce mutum na dauke da cutar sikila ana nufin mutum yana dauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurbatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi.A yanzu haka, cutar sikila na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jinin AS da AS ko SS da AS....Iya Ina fatan kina ganewa?".

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*

5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:12_

××××××

Marka ta yatsina fuska tana tabe baki hade da karkace kai ta juyar da shi baya.

Maaikaciyar lapiar ta girgiza kai kawai, Kafin ta cigaba da cewa,

"Cutar sikla mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya. Dubi yadda jikokin ki ke fama.. Wannan cuta musanman, Aka ware ranar 19 ga watan yunin kowacce shekara a matsayin ranar yaki da cutar amosanin jini wato sikila a duniya. Rana ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin fadakar da al’umma kan wannan cutar a matakin kasa da kuma na kasa da kasa. Yau kenan....

"Najeriya ta fi yawan masu cutar a duniya. Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 na Najeriya din nan 100,000 ne ke mutuwa duk shekara Iya..Alkaluma sun nuna cewa ma fi yawan masu cutar suna arewacin kasar ne.

"Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu dauke da cutar sikila a kasar nan. Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna dauke da cutar har zuwa karshen rayuwarsu..."

"Ke dakta kina nufin ki ce me sunan Malam ne me dauke da cutar? Ke ki kiyaye ni."

"Haba Iya .. Ni ba haka nake nufi ba. Ai daga Dan na ki har ya zuwa matar tasa basa dauke da cutar."

"To ai gashi nan yanzu kin fada da bakin ki... Nide nasan wannan ciwo ba daga tsatso na ba ne."

Maaikaciyar lapiar ta dafe goshinta da tafun hannun ta. Dan ba kadan ba Marka ta hada mata zafi. Sam ta kasa gane komai. Gata da tsatstsauran taurin kai.

"Ina mahaifiyar yaran?"

"Tana daka mana."

Nan da nan Umma Hadiza da ke tana sauraron komai ta fita zuwa tsakar gidan ta tsakure daga gefe ta tsugunna.

"Ungo wadannan magungunan... Majalisar dinkin duniya ce suka tattalafawa gidauniyoyi na kasashe da dama kan masu fama da lalurar sikila."

Umma Hadiza ta saka hannu biyu ta karba tana mata godia. Wata leda ce fara mai dauke da rubutun : Health is wealth. Long live warriors. #Spread the awareness. Magunguna ne kala kala aciki masu matukar tsada da kyawu.

"Allah ya saka muku da alkhairi ya biya bukatu Amin. "

"Aamin.... Yauwa, Daga cikin magungunan akwai maganin karin jini, wanda ya ke kara musu jini, saboda kwayoyin halittar jininsu na yawan mutuwa da wuri. Akwai kuma maganin da ke kare su daga kamuwa da cutar maleriya don tana wahalar dasu sosai idan suka kamu. Sai maganin mai kare su daga cututtuka masu alaka da numfashi. Sai wanda ya ke taimaka wa kwayoyin halittar jinin siffarsu ta zama mai kyau, ya ke kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci ana shan shi ne ga wanda ciwon ke masa tsanani. Kamar dai yaran nan na ki. Sannan muna kara ja muku hankali akan ruwa, Yawan shan ruwa abu ne mai matukar muhimmanci ga masu cutar sikila saboda rashin ruwa yana tayar musu da ciwon kwankwaso da na gabobi, Sannan shan ruwan na sa jini ya dinga gudu yadda ya kamata kuma kwayoyin halittar jini su dinga wucewa cikin jijiyoyi, wanda haka ke hana ciwon yawan tashi.

"Tsananin zafin ciwon kwankwaso da masu cutar kan yi fama da shi lokaci zuwa lokaci yana matukar ta’azzara musu. Ƙwararru a harkar lafiya sun ce zafinsa ya fi na nakuda.... "

"Haka yake likita.. Ai aikin ku ne. Kunsan kan sa. Zance na gaskia suna fama wallahi. Allah yasa kaffarane "

"Aamin. Eh , Ai kinga su da ke cikin yanayin sunfi kowa sanin yadda suke ji. Suna jin ciwon kashi kamar ana kwankwatsa shi, jini ba ya isa wasu wuraren don haka idan suka taru a waje daya sai su saka ciwo. Wannan ciwo bai bar masu shi ta bagaren shafar lafiyar jima’insu ba. Ciwo ne da ke hana su rawar gaban hantsi sosai a wasu lokutan ta wannan fanni. Kinga, Ga maza dai yawanci, kwayoyin jini masu kamar lauje ne ke makalewa a gabansu sai jinin ya ki fita ya taru a wajen, sai al’aurarsu ta mike ta ki sauka.A wasu lokutan har sai an yi ‘yar karamar tiyata, wasu lokutan kuma da an sanya kankara sai ta taimaka wajen kwantar da gaban.

"Abunda yasa na ke sanar miki, Saboda jan kunnen da akace muyi don kara wayar da kai, sananin zafin da ciwon ke zuwa da shi kan sa masu yin sa su dinga gurzar kuka tare da gunji da gurnani. Ai kin sani, irin wannan yanayi ba babba ba yaro za a ga sun fita hayyancinsu. Domin da nake tsaye a waje ma ina jiyo kukan sa, Daga cikin wasu abubuwan mamaki dangane da wannan ciwo shi ne yadda a wasu lokutan sai kashin wata gaba ta jikin masu ciwon ya karye bal. Ba komai ke jawo hakan ba sai tsabar zafin ciwon da ke taso musu.....Kina sauraro ko?"

"Eh ,..Ina sauraro likita "

"Yauwa naga akwai yammata agidan ko?"

"Eh akwai biyu..."

"Masha Allah.... Nasan da yardar Allah aure na nan tafe. Abunda nake son sa ni shine, Gwajin cutar HIV/AID, STD da Hepatitis B da C, A kan so kafin a yi aure ayi gwaji na wadannan cututtuka da suke yaduwa ta hanyar jima'i. Wadannan cututtuka ne da za a iya daukar su ko namijin ya dauka ko matar ta dauka daga namijin idan dai akwai mai shi a cikinsu , Don haka idan daya a cikinsu yana da shi sai a ba su magani su warke kafin auren, wadanda kuma ba a warkarwa sai a ba da shawara ka da su yi aure don gudun cutar da daya daga ciki. Ina fatan kuna fahimta...?"

"Ke dakta ni tsegumi ne banaso. Zance dai Najan Isubu ce da Hadiza zasu gayan ki akan Na'Ateeku. Bawan Allahn nan hidima da yake min. Rannan wallahi taliya ta kakkaryawa da tumatirin gwangwani ya aikon. Yarinyar nan wahidin batada mashinshi . Sa....."

"Wallahi Iya bansan komai ba, Bangane kan maganar da kike ba ma. Kawaii dai yanzu zamanin yazo da wasu lalurori da dama wanda kafin auren ya kamata ace an gudanar da su. Kamar su: Gwajin rukunin jini: Gwajin rukunin jini ga masu shirin aure yana da fa'ida, saboda a wani lokaci idan aka samu bambanci na nau'in jini tsakanin uwar da kuma jariri ko jaririya, ana iya samun matsala wani lokaci yara su zo da ciwo. Da su,

"Gwajin cutar HIV/AIDS: Shi ma wannan gwaji ne mai matukar muhimmanci da ya kamata a yi kafin aure, don hana yada cutar mai karya garkuwar jiki ga wanda ba shi da ita. dan har aka samu cikin masu shirin yin auren daya na dauke da ita, to ya kamata su ga likita don samun shawarwarin likitoci kan mataki na gaba da ya kamata su bi don gudun yaduwar cutar. Musanman sikila data zama ruwan dare,

"Kusan kaso biyu ko uku na mutanen Nijeriya suna da ciwon sikila, yana yaduwa ne ta hanyar auratayya tsakanin mace da namiji da suke da nau'in na ciwon da a ke kira career. To su kuma career din nan suna nan a cikin jama'ad. Kowane mutum daya cikin hudu a najeriya yana dauke da nau'in ciwon, wato kaso 25 kenan a yan Najeriya career ne. Don haka kafin a yi aure idan aka gwada aka tabbatar cewa shi namijin career ne matar career ce, wannan sai a ce bai kamata su yi aure ba, kun ga an rage wa al'umma da gwamnati da kowa dawainiyar rashin lafiyar yara masu sikila. Zan sake nanata: Gwajin rukunin jini; Gwajin rukunin jini ga masu shirin aure yana da fa'ida, saboda a wani lokaci idan aka samu bambanci na nau'in jini tsakanin uwar da kuma jariri ko jaririya, ana iya samun matsala wani lokaci yara su zo da ciwon nan da ake kira jondis, wato matsananciyar cutar shawara, wanda idan an haihu za a ga idon yaron ya yi kamar rawaya, sannan kuma jikinsa ma ya sauya launi ya zama rawaya saboda jikinsa yana farfashewa. Wannan yana faruwa ne a dalilin bambanci a tsakanin rukunin jinin mahaifiya da kuma na yaron. Wani lokaci akwai wani rukuni na jini da ake kira RH, idan uwar tana da RH da ya zama korau (negative) shi kuma yaron na shi ya fito tabbacecce (positive). Wani lokaci kuma ana samun matsalar haihuwar jarirai da jondis idan ya kasance uwar tana da rukunnin jini O kuma jaririn ya zamanto yana da rukunin jini A ko B ko AB. ...

"To dika dika daga karshe dai tamkar yadda muka fada a baya. Nan gidan bakuda history na sickle cells sai dai mahaifi da mahaifiya wato Hadiza ta kasance AS, hakama shi mai gidan nan shima AS ne ta haka suka samu yara biyu SS sai guda daya AS. Na farko SS ta biyu AS career na uku SS . Sai bangaren abokiyar zamanta ita AA ce agwajin da mukayi. Don haka yaranta akwai AA da kuma AS amma babu SS aciki ... Wannan shine kawowar karshen bayani na. Ubangiji Allah ya ba wa marasa lapia lapia. Masu lapiar kuma Allah ya kara mana mai albarka , Aamin..."

"Uhm. Kyaji da shi " Marka ta miqe tana Kade zaninta tayi dakinta da sauri ...

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*

*ZAFAFA BIYAR BACTH A*

1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)*

2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)*

3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*

1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)*

_Duk biyar 1500_

*______________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_ *(Mamu gee)*

5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_ *HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_ *_2270637070_*

_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*

*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:13_

"Hadiza.. Ki kula da yaran nan naki, Domin cutar sikla mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya...Bazan manta ba, Farfesa Aisha Indo Mamman ta ce har yanzu mutane na da karancin sanin girman cutar sikila. Ta ce mutane sun dogara da camfi da danganta cutar kan aljannu ko maita.Sai dai ta ce ba a warkewa daga wannan cutar ta sikila har abada, illa dai a samu sauki ko kuma a gujewa kamuwa da ita ta hanyar yin gwajin kwayoyin halitta kafin ayi aure...."

"Likita akance wai ana warkewa?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull