Kenza eBookz

Farhatul qalbi complete - Chapter 8

Farhatul qalbi complete - Chapter 8

Farhatul qalbi complete Chapter 8: Farhatul qalbi complete Chapter 8. Haj Hameedah ta zura safar girki tana dudduba kayan hadin jikin naman kajin.

4,496 words

Haj Hameedah ta zura safar girki tana dudduba kayan hadin jikin naman kajin.

"Wannan gashi ne.?"

"Eh nayi marinating ne da kayan hadi. Se gasawa kawai."

Waheedah ta kada kai .

"Kin iya girkuna?"

Ta dan yi murmushi kafin ta ce,

"Bakomai ba. Na de fi iya wasu abubuwan . "

"Ah inde kin iya girki ai da sauki. Allah ya temaka. Kai temake ni. Kinsan na manta da tafarnuwa "

"Wai."

"Yi sauri ki dubamun cikin freezer dinnan daga kasa zaki ga tafarnuwar a wani canister."

"Tohm"

Nan da nan Waheedah ta duba ta dakko ta miqa mata. Tafarnuwar a dake take. Haj Hameedah ta diba ta zuba acikin gashin tana cakudawa .

Waheedah ta dauki wasu canisters din na spices tana dubawa. Sai kamshin abincin larabawa suke . Haj Hameedah ta janyo abun grilling din tana dudduba shi. Kafin ta sauke kallonta akan Waheedah. Cikin murmushi tace da ita,

"spices/seasonings ne na larabawa .." Ta shiga daukar kowanne dai dai tana gaya mata sunayen su,

"Wannan Sadaf mint leaves ne, Wannan, Natural sidr leave sai, Pure black seed ( Black cumin seed), Ga Nutmeg, sai cardamom, Wannan sumac, Sai hulba , Fenugreek ,Allspice Cloves, Ginger..."

"Masha Allah.....Gaskia suna da kamshi Maa."

"Sai ma a abinci..."

"Gaskia daga jin kamshin su ma " Ta dauki duster ta shiga goge kitchen cabinets din. Duk kuwa da ba datti suka yi ba .

×××××

A gajiye yake likis saboda gaba daya jiya bai yi wani baccin kirki ba kuma tun kafin asubah bai sake runtsawa ba ya fita. Dawowar sa kenan cargos din kayan su sun sauka a site yaje ya dubo.

Sanye yake cikin manyan kaya. Riga da wando na shadda. Rigar iya gwiwa sai wando. Kalar dark blue. Hular kalar kayan sa ta zanna bukar na hannun sa. Yayinda half covered shoe dinsa da agogon hannun sa kalar aikin kayan sa ne.

Sai kamshin turaren Calvin Klein ne da Rasasi suke tashi a jikin sa.

Yana sallama tun daga bakin kofar kitchen ya samu zuciyar sa da sauya bugu . Bugun mai duka da sauri sauri.

Kamshin turaren da bazai taba mantawa ba ya shiga yawo sosai a kofofin hancin sa.

Ya lumshe idanu ya bude. Ahankali ya saka hannu ya tura kofar kitchen din ya shiga.......

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:23_

===

Yana shiga idanun sa suka sauka akan na Waheedah dake tsaye tana goge hannun freezer.

"Maaaa " Ya fada a ahankali yana takawa wajenta

"Naam Zayn. Ka dawo?"

"Eh.. Yau baki je asibiti ba?"

"Sai da daddare insha Allah inada appointments da Nol da Maxicare."

"Okay Allah ya temaka Maa."

"Amin Zayn. Abincin ka na kan dinning "

Har ya juya zai tafi sanyayyar muryar Waheedah ta doki kofofin kunnen sa,

"Ina kwana?"

"Lapia." Ya amsa ta kasan makoshin sa ya fice.

Sam Waheedah bata jiyo amsa gaisuwar da yayi mata ba. Ta tabe baki tana mamakin da alama shi daya ne me halin shariya agidan.

"Ungo kai wa Zayn cup dinnan na manta."

"Tohm." Waheedah ta saka hannu ta karbi cup din da ke kan wani karamun tray ta tafi .

Kalle kallen inda zata hango sa take. Can ta ganshi akan dinning yana bude food flasks.

Ta je ta ajiye masa tray din agaban sa . Ta juya zata tafi ya dakatar da ita.

"Goge shi da handkerchief ."

"A'ina yake?"

Yai banza bai amsa ta ba. Sai ma sake zuba liver sauce da yake akan soyayyiyar doyar gaban sa.

Dudduba wa ta shiga yi tana mai kaude kauden kayayyakin gabanta. Dogon tsaki yaja ya janyo handkerchief din dake kan despenser.

"Afuwan ban gani ba ne."

Bai kulata ba ya cigaba da yankar doyar yana hadawa da sauce. Gashi zuciyar sa tamkar ta faso kirjin sa ta fado kasa.

Ta dan dakata can ta matsa daga wajen ta koma kitchen.

"Je ki huta Waheedah."

"Da zan dauraye kwanukan ne."

"No kakki damu, Ai akwai masu wankewa "

"Tam. "

"Ki zauna a parlor idan kuma zaki kwanta to akwai daki idan kin haura stairs din bene daga daman ki "

"Tohm Maa "

Tana fita daga kitchen ta zauna akan wani center carpet dake kan wata corner an yi ado da console awajen da wasu vases na decoration .

Tsayawa tayi tana karewa wajen kallo don ba kadan ba ya kawatu.

Ta dora hannunta akan lallausan carpet din tana shafa shi.

Sai ga Ahlam ta shigo cikin sashen bakinta dauke da sallama .

"Wa'alaykm Salam..." Waheedah ta amsata tana murmushi.

"Ahh me sunan yan gayu. Kina hutawa ne?"

"Eh ..."

"Allah sarki, Ina Nadra?"

"Wallahi bansani ba. Ko tana sama? Bari na kirawo ta ."

"No basshi zan hau. .." Har ta kai matattakalar bene na biyu ta hango Zayn ta cikin wani mudubi da akayi kwalliya da shi .

Fasa hawan tayi ta koma wajen sa da sauri tana dariya.

"Zayn Adams...."

"Na'am Ahlam... Ya kike?"

"Lapia kalau ... Shine baka mun magana ba? Ba dan na hangoka ba da shikenan ba zaka mun magana ba... Uhm?" Ta dora hannunta akan nasa tana murzawa.

Ya janye da sauri yana goge hannun nasa da tissue paper. Murmushi tayi me hade da fari.

"Baka ce komai ba ... Zayn."

"Ahlaam. Nagaji ne. I'm exhausted beyond your expectation... Please."

"Nayi lefi ne? Nace nayi lefi saboda nazo wajen ka?"

Ya girgiza kai ahankali . Hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Waheedah na jiyo dik abubuwan da suke cewa. Da sauri ta mike zata haye dakin da akace yana hanyar bene.

"Zo nan Waheedah...."

"Wa...Heee.. Dah.…! " Ya furta kasan maqoshi yadda shi kadai ya jiyo abunda ya fada. Ya na mai satar kallonta ta gefen idanu.

"Ga ni Aunty....."

"Ahh ... Kicemun Yaya dai. Sis Ahlam ko Yaya Ahlam, Kinji yar kanwata ? "

Waheedah ta daga mata kai alamun toh. Kafin tace,

"Tohm Insha Allah.."

"Yauwa! Good girl... Kalle mu muna kama da shi ko bama yi?"

Waheedah ta daga idanunta a hankali. Hade da gyara zaman gilashin idanunta. Ta sauke kallonta akan Ahlam kafin ta sake juyawa ta kallo Zayn. Da sauri tace,

"Kuna yi..."

"Jayyid.. Kaji ko itama tace muna kama. ?"

Bai ce komai ba. Sai ma janyo tissue da yayi ya goge bakin sa.

"Hubba bubba. Tace muna kama... Say something pls "

"Muna yi..." Ya fada badan ya so ba.

Waheedah dai na tsaye a akansu. Tana lankwasa yatsun hannuwan ta.

"Shikenan dear sis .. . Mungode, Hubby na ne." Ahlam ta fada wa Waheedah tana murmushi.

Waheedan ta gyada kai kawai itama tana dan murmushin. Ashe ma miji da matane amman yake shareta? Lalle bashida mutunci. Kuma da alama yana cikin maza marasa darajta matayen su.

"Kije sis .."

"Tohm." Daman ta gajin da tsaiwar da tayi akan su. Ta haye ta shige dakin da Maa tace ta shiga. Bandaki ta shige ta watsa ruwa. Sai da tayi da gasken gaske kafin ta gano yadda ake bude famfon.

Ta dauro alwala jin ana kiraye kirayen sallar azahar na daya saura. Sallaya da hijabi gasunan an shimfida da carbi akai. Don haka tayi sallah da adduoi. Ta dan zauna tana zikiri kafin ta miqe ta koma kasa wajen Maa.

Already Maa din ta kammala gashin da take. Har ta zuzzuba komai a food flask . Maaikatan na dauka suna kai wa Ummimi a sashen Haj. Barr Aisha.

"Sannu da aiki Maa."

"Yauwa sannun mu Waheedah. Ga naki abincin can a cikin plate. Na food flask din kuma na Hadiza ne. Idan zaki tafi seki tafar mata dashi "

"Tohm Maa. Angode Allah ya saka da alkhairi."

"Allahumma Aamin Waheedah, Bara nayo wanka na sakko "

"Tohm sai kin dawo "

Da sauri ta karasa wajen plate din. Fried rice ce lafiyayyiya da taji hanta sai sauce din nama da gasasshiyar kaza a gefe. Sai wani kwano karami daga kasan da aka dora plate akan sa. Soup din catfish ne daya gaji da haduwa.

Ta wanko hannunta da sauri a sink ta shiga cin abincin bayan tayi basmala. Kunnuwanta har wani motsawa suke saboda tsananin dadin da abincin yayi mata .

Kasa boye farin cikin data samu kanta akai tayi. Hawaye suka shiga reto a cikin kyawawan idanunta. Tunda mahaifiyar ta ta haifo ta duniya bata taba haduwa da cima kawacacciya mai madaukakin dadi da gardin dandano irin wannan ba.

Maa ce ta bude kofar kitchen din ta shiga tana sallama.

"Wa'alaykm Salam..." Waheedah ta amsa tana goge hawayenta

"SubhanAllah! Waheedah...kuka? Kukan me kike yi? Fadamun wani abun akai miki? Eh Waheedah? Menene.?"

Waheedah ta kasa cewa komai saboda farin cikin dake dankare a harshenta ya mata nauyin furtawa.

"Menene . Eh?" Maa ta sake tambaya hankalin ta baki daya ya tashi .

"Ba... Bakomi wallahi."

"To kukan me kike yi? Ko ni ce? Kinga wayata na manta nasan kuma zaa neme ni kinganta akan microwave na barta. Sai Kuma zan ce miki soup din kifin ma nakine na manta nace iya abincin plate. Dan Allah menene Waheedah?"

Waheedah kulawar Haj Hameedah tasa ta kara kaunarta a ranta. Da sauri ta goge hawayen dake tsiyaya tace

"Allah maa ba komai. Kawai abincin ne yamun dadi. Gashi kala kala. Bantaba ci haka ba. Shine nake hawayen farin ciki. Allah ya saka muku da madaukakin alkhairi ya kara muku arziki mai albarka Amin. .."

Haj Hameedah ta janyo ta jikinta da sauri ta rungumota . Hawayen itama suka shiga kwarara a nata idanun.

"Ssssh! Kukan ya isa haka nan Waheedah. Nan ai gidan ku ne. Ya zama na ku. Kema din yar gidah ce Waheedah. Allah ya miki albarka ya baki miji nagari inda zaki je ki huta. Yan uwan ki su huta, Na kusa da ke ma su huta. Gidan jin dadi da kwanciyar hankali. Amin, kinji ko?"

"Eh Maaa "

"Yauwa yi sauri ki cinye abincin. Kinji ko?"

"Tam..."

Daukar wayarta tayi. Ta janyo tissue ta goge nata hawayen sannan ta fice. Waheedah ta sake daurayo hannunta ta zauna ta shiga cin abincin tana korawa da ruwa mai sanyi....

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:24_

Tana karasawa ta yi hamdala . Ta nufi wajen sink ta wanko hannunta da hand wash din da Maa ta nuna mata dazu.

Dusters din da suka baci ta diba. Bayan ta mayar da komai mazaunin sa. Ta tattare kitchen din ta yi mopping. Sannan ta fita da moper din da bokitin zuwa famfon baya. Ta wanko su tas ta shanya.

Ta koma kitchen din. Wani spray ta gani na saka kamshin gidah na kamfanin da ta gani a rubuce na (yerwa incense and more) Faffesa shi tayi. Baki dayan kitchen din ya gauraye da kamshi.

Ta dakko food flask din abincin ta riqe a hannun ta. Maa ta shiryo cikin doguwar riga ta rufe jikinta da mayafin rigar. Tana hango Waheedah ta dashare hakora.

"Sakkowa ta kenan ni ma...Sannu da kokari."

"Na dauraye su duster din nayi mopping kitchen. Akwai wani abun da za'ayi?"

"Sannu da kokari yar albarka. A'a babu komai kin gama. Mungode kwaarai. Dan Allah kiyi wa Hadizan sannu. Yauwa ungo ki bata wannan maganin tasha. Har na tsawon sati daya. "

Ta miqa mata wata leda mai dauke da magunguna. Ta cigaba da cewa,

"Na zana yadda zata sha kowanne."

"Tohm. Allah ya saka da alkhairi."

"Aamin. Amin. Nima fitar zanyi ai. Yaran duk suna wajen su Ummimi. "

Sai a sannan Waheedah ta daga kai ba kowa a parlorn da dinning area sai Haj Hameedan kawai.

"Tohm sai da safe. "

"Yauwa Waheedah."

A tare suka fita daga cikin sashen. Waheedah tayi hanyar gate don fita. Ita kuma Haj Hameedah ta nufi sashen abokiyar zamanta inda Ummimi suka sauka.

××××

Tanata sauri har ta kusa karasawa gidah taci karo da kawarta Basira.

"Kawata daga ina?"

"Daga gidan aikin Umman mu nake.. Kawalliya "

"Allah sarki Umma. Dazu naje dubuta ai ni da fannah. Awajen Najan Isubu naji."

"Eh wallahi zazzabi take "

"Allah ya bata lapia mai dorewa. Ciwon da zai sa Umma kwanciya ai babban ciwo ne."

"Wallahi kuwa ... Amin. Ya Innar ku?"

"Alhamdulillahi sunje dubiya unguwar yan Tasha"

"Okay Allah sarki..."

Jerawa sukayi suna tafiya suna hirar su ta kawaye .

Ta majalisar su Ibrahim suka ketare. Sun jeru samarin sunata hira. Wasu na danna waya. Wasu na cin masarar da suka tsayar da me masarar suna saya.

Wasun su na shan shayin cikin wata yar karamar buta dake gaban su. Kamar ko da yaushe. Yayin da wasu daga ciki suke whot wasunsu kuma hira suke mafi yawan su kuma na danna waya.

Matashi Ibrahim na cikin jerin samarin dake danna wayoyin hannun su. Sanye yake cikin yadi mara nauyi me layi layi. Kalar qasa. Ya kishingida yana mai duba wayar sa cikin nutsuwa. Kyakkyawa ne wankan tarwada mai matsakaicin idanuwa da dogon hanci.

"Wohoho...." Wani daga cikin samarin ya furta.

Dayan kuma ya shiga lakato tafun kafar Ibrahim . Cikin rada yake cewa,

'Ga takan, Ga takan...."

Ibrahim ya 'daga kansa a hankali ya sauke akan Waheedah dake tafiya ita da Basira.

Tamkar an tsunkule shi haka ya miqe da sauri jikin sa tamkar mazari tsabar rawa. Yana mutuwar son Waheedah. Wani irin so yake mata wanda ba zaa iya fasalta shi ba.

Ya tsallaka kwalabatin dake gaban sa. Abokan nata masa dariya. Yayi banza da su ya isa wajen su Waheedah dake tafiya.

"Waheedah... Waheedah .." Ya kira sunanta yadda zata iya jiyo sa.

Ja sukayi suka tsaya. Ya karasa yanata dashare baki yana murmushi.

"Ina wuni Ya Ibrahim?."

"Lapia kalau Basira .."

"Ina yini...!" Waheedah ta gayshe shi cikin ladabi.

"Alhamdulillah Waheedateey . Kaif? Ya komai.Tawan.."

Basira ta yi yar dariya kafin tayi gaba ta tsaya daga can nesa.

"Waheedateey....?!!" Ya sake jan karshen sunanta cikin wata siga ta soyayyah.

"Sauri na ke Ya Ibrahim ..." Ta bashi amsa cikin kosawa, Don sam batason kule kulen nan.

"Ance Umman ku batada lapia.... Ina ta son shiga na duba ta. Waheedateey, Kin ki bani chance.. Waheedateey inason naga mahaifin ki don ya bani dama na fara zuwa tadi wajen ki . So nake na aure ki Waheedateey kinsani tun ba yau ba ..."

"Ban gama makaranta ba. Kuma na gaya maka cewar inason na cigaba da karatu ko da na kare sakandire . A yanzu kuma gaskia ban kai shekarun da zan dinga zance ba. Kayi hakuri "

Ibrahim ya dafe kansa. Waheedah na gara rayuwar sa. Yan matan unguwar shura na macewa akan kaunar sa. Duk basa gabansa ita yake so. Amman kwata kwata ita din bata yin sa. Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace da ita

"Zan bari ki karasa karatun sai muyi auren. .... Sai ki cigaba da karatun a gidah na . Kinji ko?"

Waheedah ta sake gyara tsaiwarta da kular abincin da ke hannunta ahankali cikin nutsuwa tace da shi,

"Ya Ibrahim sai nayi istikhara naga alkhairi ne ko akasin haka? Sannan yanzu ba a aure gaba gadi Ya Ibrahim."

"Bangane gaba gadi ba Waheedateey. Ban isa auren ki bane ko kuwa ban kai matsayin auren ba?".

Waheedah ta girgiza kai kafin tace da shi,,

"Babu komai "

"No ban amince ba. Da magana a bakin ki Waheedateey.... Ni bansan me kike jira ba da ba zaki karbar kokon barar soyayya ta ba Waheedateey... Ga ni matashi mai jini a jika. Nayi karatu na har ya zuwa matakin NCE Waheedateey. Ni dan asali ne na fito daga dangi masu dattako da sanin ya kamata Waheedateey. Ina sana'a ta ba zaman banza nake ba. Zan iya riqe ki har karshen rayuwar mu Waheedateey... Ga Zainab yar uwar ki nan tana tadi da samarinta. Gidan ku daya. Yar uwar ki ce ta jini amman ni kinki bani chance ... Meyasa?? Uhm?" Ya fada cikin rada rada. Yayinda tururun numfashin sa ke dukan kofofin kunnenta.

"Kinyi shiru... Wace irin tsana kike mun ne.... Eh Waheedateey?"

"Ban tsane ka ba Ya Ibrahim. Komai lokaci ne ciki harda auren da kake fada. Idan Allah yayi ni mata ce agare ka . Wallahi dole sai na aure ka. Sannan rashin baka damar zuwa zance wannan raayi na ne na fuso na kammala karatu sannan. Don ba zan iya raba hankali na biyu ba... Ni da Zainab ba daya bane. Mu yan uwan juna ne amman masu bambamta halaye. Sai abu na karshe Ya Ibrahim kasan menene matsayin gene dinka? Ina nufin genotype ...Da sauran gwaje gwaje na lapia? Ba a tafiya kai tsaye ayi aure ba tare da gwaji ba."

Ibrahim ya furzar da iskar bakin sa. Cikin kufulewa yace,

"Waheedateey wannan maganar ta genotype yahudanci ce. Wani renin hankali ne yahudawa suka kawo shi don a hana musulmai raya sunnar manzo SAW. Renin hankali ne shiya sa ranar da ake gwajin nayi zamana a gidah ko kofar gida banje ba. Lapiyayye ne ni wallahi. Computer bata isa ta kawo mun karyar kanzar kurege ba.. "

Waheedah tayi murmushi kawai. Ta cigaba da tafiya. Ibrahim yabi bayanta da sauri yana cewa,

"Kinyi shiru .."

"To me zance? Ai ka gama magana. Ni kuwa ko lokacin aurena yayi bazan yi aure ba tare da gwaji ba. Domin cututtukan zamani sunyi yawa masu halakawa ko mutum yayita jinya har karshen rayuwar sa. Musanman ciwon sickle cell na amsosanin jini.... Tun yanzu nasan genotype di na. Don haka ba zan yi auren jelan asibiti ba da yardar Allah...."

"Abar maganar nan.... Yanzu dai yaushe zan zo na duba Umman ku?"

Waheedah ta girgiza kai kawai kafin tace dashi,

"Umma taji sauki... Mungode da kulawa."

"Shikenan sai mun sake haduwa..."

Ya juya ya koma majalisar su . Ita kuma da Basira suka karasa layin su. Kowanne ya shiga gidan su ..

Umma Hadiza ta sake cika da mamakin abincin da Waheedah ta sake kawo mata. Tayita zuba addua tana yabawa Haj Hameedah da kokarin da bata gajiyawa.

Ta zubawa Marka aka mika mata. Dakyar Markan ta karba tana yamutsa fuska.

Yayinda Umman ta rabawa su Kamal da Najan Isubu.

Waheedah ta dauki food flasks din ta kai su waje ta wanke su sau 3 da omo ta dauraye su tas sai kyalli suke. Sannan ta mayar su cikin kwando ta lullube su. Kafin zuwa safiya ta mayar dasu gidan na The Adams family!!

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:25_

_INA MASOYA MATA YAN GAYU DA KE NEMAN GANGARIYAR KAYAYYAKIN GYARAN FATA TAYI LAUSHI, KYAU DA CIRE TABO HADI DA MAYAR DA FUSKA DA JIKI KALA DAYA TA CIRE KNUCKLES? TO KU MATSO KUSA. DOMIN ZAFAFA BIYAR WANNAN KARON MUN LEKA MUN ZAKULO MUKU MAI KAYAN GYARA FATA DA TURAREN WUTA MASU KAMA GIDA DA KAMSHI. WATO: J-SKINCARE PRODUCTS_

_J-SKINCARE PRODUCTS_

_0813 801 1240_

_TANADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA: Black soap, Kiddies Black soap, Sugar body scrub, Body butter, Kojic acid soap Turmeric soap,Goat milk soap,Honey soap,Carrot soap,Face and body cream, Hair growth oil Muna yin contract na sabulun cold process ga masu yin biki ko suna. Akwai spices na girki dana shayi. Kai dama sauran kayayyakin masu inganci, kyau da kuma karko acikin farashi mai rahusa.

_Instgram page:J-skincare products_

_Tiktok:jannatskincare_ _whatsapp/Phone number 0813 801 1240_

_KYAU!! INGANCI, DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN: J-SKINCARE PRODUCTS_

_100% tested and trusted_

========

*WASHE-GARI*

*DA* wurwuri ta karasa dukkanin abubuwan da zatayi ta yo wanka . Daki ta shiga ta zura wata doguwar riga da yayar Umma Hadiza ta dinko mata a sallar bara.

Batayi kwalliya ba. Illa dai ta zizara kwalli ta kuma shafa Vaseline (basilin) a labbanta masu taushi.

Ta dakko yar kwalbar turaren ta ta goga a jikinta da kasan hammatar ta bayan ta shafa alumun mai dauke da lemon tsami.

"Sannu Umma! Ya karfin jikin na ki?"

"Da sauki Waheedah.... Ga biredin can. Akwai ruwan zafi a jug dincan da sukari a gefe."

"Tohm Umma."

Nan da nan ta hada shayin. Ta gutsiri biredin tana ci tana hadawa da shayin. Cikin haka yayan su Kamal ya shiga dakin.

"Umma barka da safiya! Ya jikin naki? Allah ya kara miki lapia mai dorewa yasa kaffarane. Amin.."

"Aamin Aamin ....Ya naka jikin?"

"Da sauki Alhamdulillah..."

"Masha Allahu. Allah ya baku lapia yasa kankarar zunubai ce. Amin"

"Aamin. Yaya ina kwana? Ya jikin?"

"Alhamdulillah Waheedah.. Kin tashi lapia?"

"Lapia kalau. "

"Masha Allah..."

Can sai ga Najib ya shigo shima. Hannunsa kan bakin sa yana hamma.

"Ina kwana Umma ya jiki?"

"Da sauki Najib... Ya naka jikin?"

"Da sauki sosai ..."

"Masha Allahu... Allah ya kara lapia Amin."

"Amin...Yaya Kamal ina kwana ya jiki? Ya Waheedah ina kwana?"

"Lapia kalau Najib ..Ya jiki?"

"Alhamdulillah Yaya .."

"Alhamdulillah Najib. Allah kara afuwa "

"Amin Amin Yaya Waheedah."

"Ga kayan karin kumallon naku nan... Waheedah dakko musu."

"Tohm Umma."

Waheedah ta janyo kayan karin ta ajiye agaban su. Kowanne ya hada shayin sa da biredi. Suna ci. A haka har suka kammala.

Kamal yace.

"Umma bari na tashi na tafi ... Kanin malam shuaibu ne ya rasu. Jana'iza karfe 10. "

"Allahu Akbar... Rai yayi halin sa. Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan."

"Amin Amin..."

Haka dai sukaita yan addoin su. Kafin Kamal da Najib su tashi su fita don halartar jana'izar.

Sai da Waheedah ta tabbatar ta kammala duk wasu aiyuka tukun sannan ta dauki kwandon kulolin abincin .

"Umma zan tafi."

"Tohm Waheedah Allah ya kai ki lapia ya dawo da ke lapia. Tsautsayi da asara Allah ya kiyaye. Sharrin mutum dana aljan baki daya Allah ya tsare. Ki kula dai sosai. Yi nayi bari na bari. Duk kuwa da ba halin ki bane. Amman dai ki tsaya amatsayin ki idan kinje. Ki kauda kai akan komai kina ji ko?"

"Eh Umma..."

"Yauwa, To Allah yayi albarka. Dan Allah ki sake yiwa Hajiar godia sosai. Ki kuma ce ina gaysheta. Dan Allah "

"Tohm Insha Allah Umma."

Waheedah ta fice daga gidan. A bakin zaure ta hango mahaifin su malam na lado. Yana jera rake akan wheelbarrow.

"Baba ina kwana.....?"

"Lapia kalau ... Ya jikin Hadizan?" Ya tambaye ta muryar rada rada yana magana yana kalle kallen kofar gidan da kwanar layin. Waheedah tayi murmushi kawai. Kasan zuciyar ta mamakin ashe Umman su zaman su take. Babu auren mahaifin su akanta.

"Ina tambayar ki kinyi shiru "

"Da sauki .. Da sauki jikin."

"Toh Allah yakara lapia. Ki mata sannu idan kin koma."

"Tohm.." kawai Waheedah ta amsa masa. Da ta dan tsaya ko zai ce wani abun dangane da Umman ta su

Wani rake ya dakko ya miqa mata acikin leda fara.

"Ungo kya sha..."

Hannu biyu ta saka ta karbi raken.

"Nagode ... Allah ya karo kasuwa mai albarka."

"Amin...." Ya amsata , Ya cigaba da gugar bayan raken da wuka.

Cigaba da tafiya tayi tana mai jujjuya ledar raken da ke hannun ta. A haka har ta karasa unguwar ta new gra shurah.

Kanta tsaye ta shige gidan bayan ta gaysar da masu gadin dake bakin gate din a zazzaune.

Ta murda kofar sashen na Haj Hameedah. Kofar gam take a rufe ba a bude ba kamar jia. Wani madanni mai zanen (bell) kararrawa ta gani a jikin kofar

Nan da nan ta danna shi sau uku. Ba jimawa kuwa a ka bude mata kofar. Ta shiga ciki bakinta dauke da sallama.

Nadra ce a zaune da Yayan su da suke kira da Zayn. Sai Ahlam daga gege tana danna waya, Tunda ta yi sallama ta shiga ya zuba mata idanu. Dakyar ya janye ya kauda kansa gefe bayan yaci magani.

"Ina kwanan ku?" Ta durkusa har kasa ta gayshe su

Suka amsa da fara'a lullube a fuskokin su. Banda Zayn daya sake tamke tasa fuskar .

"Ina Maa?" Ta tambaya ahankali cikin zazzakar muryar ta.

"Maa tana asibiti. Ba daddwa aka kirata surgery' na gaggawa ta tafi." Nadra ta fada tana murmushi.

"Allah sarki.. Allah ya temaka, Amin."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull