Kenza eBookz

Farhatul qalbi complete - Chapter 9

Farhatul qalbi complete - Chapter 9

Farhatul qalbi complete Chapter 9: Farhatul qalbi complete Chapter 9. "Amin . Tace idan kinzo ga abincin ki nan kusa da wata food flask . Na food flask din…

4,500 words

"Amin . Tace idan kinzo ga abincin ki nan kusa da wata food flask . Na food flask din tace na Umman ku ne "

"Alah sarki. Mungode Àllah ya saka da alkhairi."

"Aamin Amin Waheedah. Je kici abincin ko?"

"Ai a koshe na ke....Sai dai ko na kai na Umman mu."

"Hakan ma yayi .."

Ahlam ta dan daga kai kafin tace,

"Waheedah kin iya dama kunu please?"

"Eh Yaya na iya."

"Okay akwai wai garin a kitchen. Pls ki hadamun yanzu. "

"Tohm Yaya...."

Zayn ya bi Ahlam da kallo. A hankali yace,

"Yanzu ke ba zaki dama kunun ba?"

"Ban iya ba ne shysa..." Ta amsa shi kanta tsaye.

Bai sake cewa komai ba. Ya maida kansa kan tv. Hade da kallon agogon da ke daure a wutsiyar hannun sa.

Waheedah na shiga kitchen ta shiga dudduba inda garin yake. Cikin ikon Allah kuwa ta hango shi.

Kasa kunna gas din tayi. Ta sake komawa parlorn.

"Ya Ahlam... Ko zaa kunnamun."

"Okay Gas cooker din?"

"Eh..."

"Nadra kunna mata please."

"Tohm..."

"Kinga uhmm Waheedah please ki soyamun hadda wainar flour pls "

"Tohm...."

Zayn dake jiyo komai ya tabe bakin sa kawai yana girgiza kai.

"Ya akai babes???"

"Bakomai, Ahlam.."

"Ahlam gatsal? Oh please . "

"Ai sunan ki ne.... Shine sunan ki"

"Koma sunana ne ai be kamata kana fadansa zalla ba. Badan pet names.... Taya zamuyi marital life dinmu ba soyayya ne pls...."

"Sanda ZUKATAN mu suka samu FARIN CIKIN kasancewar mu..."

"Bangane ba... Kana nufin yanzu ba acikin farin ciki muke da junan mu ba?.... Zayn Adams.. Bangane ba...

___ J-SKINCARE PRODUCTS.. 0813 801 1240 NATION WIDE DELIVERIES.

Black soap Kiddies Black soap Sugar body scrub Body butter Kojic acid soap Turmeric soap Goat milk soap Honey soap Carrot soap Face and body cream Hair growth oil Muna yin contact na sabulun cold process ga masu yin biki ko suna Instgram page:J-skincare products Tiktok:jannatskincare Phone number 0813 801 1240

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:27_

=====

Tunda ya dawo daga office yake a gajiye. Kansa har wani sara sara masa yake yi. Abun ka da farar fata tuni har tayi ja. Jijiya katuwa ta futo radau ta wajen goshin sa.

First aid box ya dakko dake kan beside drawer. Ya bude ya zaro panadol pain and fever . Ya ballo biyu ya kurba da ruwa ya sha.

Ya dan jima a bakin gado yana jiran kan ya dan lafa masa. Dan so yake yaje ya dubo mahaifiyar su ganin motar ta a fake ta dawo.

Kan ya na dan lafa masa ya miqe ya shige bandaki ya watso ruwa. Ya sauya kayan zuwa farar riga ta jallabiya. Da dogon wando aciki da singlet. Ya dakko turaruka ya feshe jikin sa da su.

Ya kullo dakin sa bayan ya kammala ya tunkari sashen Haj Hameedah. Bakinsa nata motsawa sakamakon zikirin da yake yi

Da sallama ya shige cikin gidan. Mahaifiyar tasu na zaune akan kujera hannunta da remote control tana kallon tashar labarai ta aljazeera.

Juyawa tayi tana amsa sallamar sa. Yayinda kunnuwan sa suka dauki sautin karatun Waheedah daketa rerawa a daki.

"Maaa!"

"Na'am Zayn .."

"Ashe kin dawo ...? Ya aiki?"

"Alhamdulillah. Munyi mun kammala lapia sai fatan Allah ya bata lapia Amin "

"Amin Yaa rabbi."

"Tunda na dawo ai ko sama ban hau ba "

"Labarai kike kalla... Amma ai ba murya."

"Eh wallahi. Na rage ne. Saboda karatun Waheedah. Qira'ar dadin sauraro. Kai Alhamdulillahi ala ni'imatul Islam and all it entails."

"Aamin Amin.... Karatun dadi kam."

"Wallahi. Karka so kaji yadda nake ji a raina. Beauty with brains. Yarinyar nan tayi kokari wallahi "

Shi dai bai sake cewa komai ba. Illa dai ya maida kansa ga tv da suke kallon kurame.

"Baka da lapia ne."

"Kai na ne yake ciwo."

"Allah ya kara sauki. Ga abincin ka can akan dinning. Na dawo late so spaghetti ce kawai da soyayyen kifi."

"Nagode sosai Maa. Allah ya saka miki da alkhairi."

"Amin..."

Tashi yayi ya tafi dinning din. Kamshin abincin nata dukan hancin sa. Ya ja kujera ya zauna yana mai matso da kayan abincin gaban sa.

Can sai ga Waheedah ta sakko kasan. Caraf suka hada idanuwa da Maa .

Ta zube a kàsa fuskarta dauke da murmushi

"Ashe kin dawo? Sannu da zuwa. Ina wuni. Ya aiki?"

"Alhamdulillah Waheedah. Ai na dan jima da dawowa. Ina zaune anan ina sauraron karatun ki da kira'ar ki mai dadin sauraro."

Waheedah tayi murmushi kawai . Kafin tace,

"Umman mu na gayshe ki. Tace a miki godia, Allah ya saka miki da alkhairi Amin."

"Allahumma Aamin....... Kinci abincin rana kuwa?"

"Ai a koshe nake Maa."

"Ah haba dai . Abincin safe ai baya rike ciki Waheedah. Kije kitchen naki yana nan dana Umman ta ku. Sai ki tafi dashi "

"Mungode Allah ya biya ki da aljanna."

"Amin Waheedah. Tare da ku baki daya.... Ina yayyunki maza.?"

"Suna gidah na baro su. Amman daya ne ya girme ni. Muna kiran sa da Yaya Kamal. Dayan kuma kanina ne Najib."

"Allah sarki.. ... Suma suna wani abunne na aiki haka?"

"A'a saboda basuda lapia "

"Toh pha. Wacce irin rashin lapia ce haka?"

"Sickle cell. Amosanin jini."

"Wayyo. SubhanAllah! Allah yabasu lapia mai dorewa Amin . Allah sarki hadiza. Waye me sickler agidan na ku."

"Gaskia ba kowa. Dan de likitoci sunce da Umman mu da baban mu dik AS ne ko me ne shysa suka haifo sikila."

"SubhanAllah. .. Allah yasa kaffarane Amin. Ke de me lapia ce amman ko?"

"Eh ni AS ce .."

"Yauwa gwara da kukayo gwaji. Saboda fadaawa halakar haifo yara marasa cikakkiyar lapiar da za'ayi ta magani har karshen rayuwa."

"Wallahi..." Waheedah ta fada a sanyaye

"Je ki ci abincin Waheedah. Allah ubangiji yana tare da ku. Ya kuma san komai. Da yardar Allah . Zai kawo muku saukin rayuwa kinji?"

"Amin.. Insha Allah ."

"Allah ya basu lapia Amin."

"Amin"

"Idanun ki short sitedness ne ko long?"

"Short ....."

"Allah yabaki lapia kema kinji ko?"

"Amin Maa."

"Yauwa yalla. Je kici abincin. Allahumma bareek."

"Amin Maa."

Mikewa tayi ta shige cikin kitchen din. Babban plate ne da yaji tuwo da miyar egusi da tasha nama.

Basmala tayi. Ta zauna tana ci. Dadin sa baa magana. Ci take tana kada kai. Tana kuma godia agare su.

Tana karasa ci. Ta dauki plate din ta wanko tas. Ta koma parlor wajen su Maa.

"Akwai abunda za'ayi. ?"

"Kwanukan can zaki wanko kawai Waheedah.... Wanda Yayan ku yaci."

"Tohm Maa."

Ta wuce dinning ta dakko kwanukan. Ta kai sink ta wanko su tas ta jera su a plates keeper .

Ta dakko food flask din da akace abincin Umman su ne. Parlorn ta koma ta durkusa tana wa Maa sallama da ke tare da Zayn. Yana zaune a kujerar da ke gefen ta Maa

Kamshin turaren ta yaci ka hancin sa. Sai lumshe idanu yake, Moment dinsu na kwanaki na kara dawo masa .

"Science ki keyi ne ko art?"

"Science.."

"Masha Allah,.. menene future ambition din ki?"

"Inason zama nurse ...."

"Masha Allahu. Allah yabaki iko. Ya bada sa'a Waheedah .."

"Amin Maa."

"Masha Allah......!!! To shikenan Waheedah, ki gayshe da Hadizan kinji? Ki kuma yiwa yan uwan na ki sannu "

"Insha Allah Maa. Zasu ji baki daya "

"Tohm sai da safe. Allah ya kai mu "

"Amin....." Cewar Waheedah. Ta nufi kofa ta bude kofa ta fice.

Tana tafiya akan hanya tana mamakin kirki da mutunci irin na Haj Hameedah. Har zatabi ta layin majalisar su Ibrahim ta fasa.

Ta layin baya ta ketara ta bi. Ta shige gidah bakinta dauke da sallama.

"Ina wuni Marka?"

"Yana gidan uban ki...🤣 Saboda yanzu kuna cin cima mai dadi ta gidan masu hannu da shuni shine kuke hura hanci kuna wami fankama da dagawa. "

Waheedah tayi shiru. Don sam bataga abun da su kayin ba da har Marka ta dameta taketa fadan maganganun marasa dadi

Ji kake kwas ta sakar mata rankwashi a tsakiyar kanta. Waheedah ta dafe wajen da sauri. Idanunta suka cicciko saboda tsananin zafin rankwashin da Markan ta sakar mata.

Da sauri tace da ita cikin ladabi,

"Kiyi hakuri Marka ."

Marka taja dogon tsaki. Ta fi ce waje ranta na dada sosuwa ganin katuwar kular abincin da ke hannun Waheedah. Babban takaicin ta yadda nasu ne abincin sede su sanmata. Abunnan yana ci mata tuwo a kwarya dole ta nemo mafita....

Waheedah ta girgiza kai kawai ta karasa shiga ciki tana sallama. Ta wuce dakin su da sauri tana yiwa mahaifiyar ta sannu .

Taci tuwon sosai Umma Hadiza. Har dare ya kai musu. Suka karasa cinyewa a abincin dare. Marka ma an zuba mata an kai mata ..

××××

Rayuwa nata garawa cikin aminci da yardar mai sammai da kassai. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha'u.

Sannu ahankali Umma Hadiza sai da tayi kwanaki 10 tana jinya chas. Waheedah ce kullum ke zuwa gidan na The Adams family. Sashen Umma Hadiza.

Sunyi matukar sabo da shakuwa ga dukkanin yan gidan baki daya. Idan ku ka tsame Zayn ku ka ajiye a gefe. Shi kadai ne kaf a The Adams Family basa shiri kwata kwata . Har ta dau rashin shirin su a matsayin tsantsar kiyayya da kyama aganin tah .

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:28_

========

Shirye-shirya ake gadan gadan na bikin dangin Ambassador Nasser Family.

Gaba daya dukkanin yan dangin ciki da wajen sa sun fara hallara a garin na kano. Wadan da suke Kaduna dana Abuja da Lagos duk sun zo .

Yayin da sauran dangi na Sudan dana Egypt duk sun fara sauka a kasar ta Nigeria.

=========.

Yana zaune a bakin gadon sa. Hannuwan sa dafe da kansa.

Ya sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi. Kasancewar asabar ce ba aiki miqewa yayi ya fita kansa tsaye zuwa sashen mahaifin su.

Da sallama a bakin sa ya shiga babban parlorn dake sashen mahaifin su.

Professor Adams Nasser yana daga zaune akan wata hadaddiyar kujera kirar royal chairs samfurin turkey.

Har kasa ya durkusa ya rissina ya fara gayshe da mahaifin na su cikin biyayyah da ladabi,

"Abiey barka da safiya....!"

Ipad din hannun sa ya ajiye a gefe. Ya daga kansa yana kallon Zayn dake durkushe. A hankali yace da shi,

"Kana lapia ..?"

"Lapia kalau Abiey ..... Ya murar? Allah ya kara afuwa, Aamin."

"Na warware Zayn. Ya aiki?"

"Alhamdulillah Abiey. Muna ta hutun weekends ."

"Masha Allah .. Allah ya temaka "

"Aamin Yaa Rabbi."

"Akwai wani abunne Zayn ..?"

Kasa cewa komai yayi duk kuwa da abunda ke damun sa a kasan zuciyar sa.

"Babu komai ... Abiey "

"Ka tabbata?" Professor Adams ya sake tambayar sa cikin kulawa da lurar yanayin 'dan na sa.

"Eh .. Bakomi Abiey "

"Tou shikenan Zayn. ... Allah ya temaka, Amin"

"Amin Abiey. A huta lapia " Ya sake durkusawa yayi masa sallama ya tafi.

Daga can ya hangota a tsaye suna guje guje da auta Moha . Kayan jikinta sari ne irin na indiya dinnan . Kirar riga da wando. Mayafin kayan ta daura shi akanta .

Mayafin ya zume ya fadi. Yalwataccen gashin kanta baqi na larabawan usuli ya bayyana.

Zayn ya samu kansa da tafiya ahankali. Hannuwan sa acikin aljihun sa biyu na wandon dake jikin sa.

Tafiya yake. Yayinda iska na kadawa ahankali. Yadda suke guje gujen da Moha kwarai matuka ya kawatar da shi. Ya saki tattausan murmushin daya kasa gane na menene.

A haka ya karasa sashen na Haj Hameedah. Moha ya tafi da gudu ya rungume shi . Waheedah tayi saurin jan mayafinta tana gyarawa.

"Akieee. "

"Na'am baby brother. " Ya dauke shi yana jujjuyawa dashi

"Me kake ci ne ..? Ka kara kiba tubarkaAllah..."

"Anything flour Akieeey .. Su waffles , Pancakes. Pies and the rest "

"Um dan gayu. Maa na ciki?"

"Yep"

"To muje ka rakani."

Suna shiga ciki Waheedah tabi bayan su. Itama bakin ta dauke da sallama

Haj Hameedah na zaune akan kujera tana rubuta sunaye. Hannunta riqe sa biro da notepad.

"Maa "

"Naam Zayn."

"Barka da safiya. "

"Yauwa ... Ka tashi lapia?"

"Alhamdulillah Maa. Ya aiki?"

"Alhamdulillah yau ina off... Sai yamma."

"Masha Allah! Allah ya temaka Amin."

"Aamin Zayn ."

"Waheedah zo muyi hide and seek ..." Moha ya fada yana tsalle.

"Ka kyelata ta huta baby."

"Ah Maa.. inaso muyi shiyasa."

"Waheedah taga ta kanta."

Waheedan ta nufi wajen sa. Ta kama hannun Moha suka fita waje. Zayn ya bisu da kallo. Maa tayi murmushi kafin tace,

"Ai sun saba sosai. Waheedah ta zama babbar kawar sa. Kwana biyun nan na huta da fitinar sa." Ta karasa fada hade da daga kai sama tana tunani. Can ta mayar da kanta kan notepad ta cigaba da rubutu.

"Maa list din menene kike yi...?*

"Na bikin nan da zaai. Saboda kar na manta ban inviting wasu ba. "

Kada kai yayi can ya nisa yace,

"Maaa . Dama inason magana da ke..."

"To ni kuma?"

Ya 'daga kansa kafin yace,

"Eh .."

"To Allah yasa muji alkhairi....."

"Aamin .."

"Ina sauraron ka .." Ta ajiye biron da notepad din a gefe.

Ta bashi nutsuwar ta baki daya. Zuciyar ta nata waswasi akan zancen da zai fada... Ta kasa gano koma menene..Don tabbas ta lura baya hayyacin sa.

A hankali kuma a nutse yace da ita,

"Maaaa... Dan Allah a fasa auren nan."

Shiru tayi tana nazarin sa. Can ta nisa kafin ta bashi amsar maganar sa,

"Kai ma kasan abune mai wahalar yiwuwa. Wanda ba zaa fasa a kan ka ba. You know that, don't you?"

"Yeah I know right Maa. But ku duba zancena pls . Infact ba wanda na samu akan zancen nan sai ke "

"Eh saboda ni ce marainiyar wayon ka ko? "

Dariya ya kyalkyale da ita kafin yace,

"Maa gaba daya kin koma cikakkiyar bahaushiya wallahi "

Itama murmushin tayi kawai ta gyara zaman gilashin fuskar ta.

"Eh inada gaskia. Meyasa ba ka samu Wanda suke a samana ba? "

"Allah, Maa naje har sashen Abiey na kasa gaya masa. Dama kune options dina shi da kuma ke. Nasan idan na gaya miki zaki sanar masa. Shi kuma ya gayawa Ummimi. Please "

"Toh ai Zayn. Zancen da kazo da shi kasan ko ni bazan amince da shi ba. Ballantana naje har wajen Abiey dinku na same shi da maganar. Ka zauna kayi tunani. Dangi na kusa dana nesa sun fara hallara saboda taron bikin ku ba? Kai kadai zaa yiwa auren ko kuwa sauran duk suna raayi ne? Tambayar ka na ke?"

Ya girgiza kansa kawai yana sauke zuciya.

"Maa ban gama fuskantar Ahlam ba."

"Yo kai ai ko gaba daya lokacin zaa baka ba zaka amince ku fuskanci juna ba. Yarinyar da gaba daya bata gaban ka. Kullum ranka a hade kana muzurai tamkar wani shugabanmu. Kama dauke maganar nan. Maganin kar ayi kada a so ma kaji na gaya maka."

Ya saka hannu ya shafo keyar sa da saman goshin sa.

"Maa. Yarinyar nan is too lazy wallahi. Gashi ta baci da kashe kudi. Beside idanunta sun bude Maa. I can't stand her. Ita smooching a wajenta ba wani abu bane...."

Haj Hameedah ta karasa sauraron sa. Can tace,

"Toh idan ka aureta sai ka tankwarata. Kayi kokarin nuna mata dai dai da akasin haka. Ka mata wa'azi da jan kunne akan haramcin taba wanda ba muharrami ba. Ka wayar mata kai. Sannu ahankali zata dena...."

Ya sake sauke zuciya a karo na takwas kafin yace,

"Dole ne auren dangin nan ne Maa? "

"Dole ne. Kana gani ai ba akan ka farau ba. Junan ku kuke aure, Mutum yanaso ko bayaso haka ze hakura dole yayi. Haka kuma ba kai kadai za'a aurar a wannan karon ba kai da wasu daga cikin yan uwa zaa aurar. Na menene zaka janyowa kan ka ka janyo mun? Salon ace ni na hana ka saboda ban taba aurarwa ba sai akan ka. ..."

"Maa ni fa bansan yadda ake kaunar mace ko so ba. Bantaba ba wallahi "

"To ka fara akan Ahlam... Sai Allah yasa albarka a abun "

"Maa please...."

"Tashi ka fita Zayn. Zan saba maka idan har ka sake tarata da makamancin zance irin wannan wallahi, Kaji na gaya maka "

Dai dai sanda Waheedah suka shiga itada Moha. Nadra na biye da su.

"Tashi ka fita Zayn " ta fada a tsawance

Da sauri ya mike ya fice. Waheedah tabi bayan sa da kallo. Mamakin ganin dazu sunata hira yanzu kuma ga akasin haka .

Ta cigaba da rubuce rubucen da take a notepad. Su kuma suka haye sama.

Dakin Nadra suka shiga. Dakinta mai dauke da kayan gado da furnitures komai purple and white.

Suka zauna akan wasu sofas. Moha yanata tsalle tsalle. Nadra can ta nisa tace,

"Auren su zaai kinsan.!"

"Oh haba?"

"Allah... Shi da Ahlam."

"Allah sarki Allah yabasu zaman lapia."

"Amin... Kinsan mu bama auren bare sai iya cikin dangin mu kawai. Ko kanaso ko baka so ."

"Masha Allah... Allah ya kara muku zumunci "

"Amin. Nima an mun miji . First cousin dina ne .. Dan yayar Abiey dinmu yana Istanbul "

"Masha Allah. ALLAH sa albarka. Amin"

"Amin .. Ahlam ita yar yayan Abiey dinmu ce."

"Kuna kama ma ...."

"Tohm shi yayan namu bayaso. Kuma shine auren farko da zaa fara na dan dakin mu. Kuma ba yadda zeyi sede ya hakura. "

"Tab... Allah sarki ."

"Hmm! Kede bari wallahi. Allah yabamu saa duka kawai "

"Amin.."

"Yauwa na manta..." Ta bude drawer dinta ta dakko wani material ja daya sha dinkin gown da dankwali harda mayafin sa baki sabo ta ajiye wa Waheedah akan cinyar ta. Ta sake ciro laffaya sabuwa pink me torches black ta ajiye mata "

"Na menene wannan?"

"Kayan fitar biki ne .. Na Zayn and Ahlam."

Waheedah ta girgiza kai kawai. Ta kasa ma magana.

"Meye size din takalman ki?"

Waheedah ta sauka daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyin ta. Hawaye daya na bin daya na farin ciki.

"Na rasa bakin godia..."

"Kar ma ki soma sis."

"Nagode Ya Nadra.. Allah ya saka miki da mafificin alkhairn sa. Ya biya miki dukkanin bukatin ki na duniya da lahira "

"Bar kuka please. "

"Ahhh Waheedah ." Moha ya rungume ta shima zeyi kukan

"Ga yaron ki nan zeyi kukan shima.dan Allah ki dena wannan kokekoken meye haka? Ai an zama daya "

Waheedah kuwa sai da ta tabbatar ta karasa godia. Ta sauka kasa wajen Maa nanma ta shiga nuna mata tana godia. Ita dai Maa murmushi kawai take. Ta dakko wani material da ba a dinke yake ba wanda tayiwa dukkanin ma'aikatan da ke karkashinta su. Ta hada da debo kudi yan dari biyar biyar guda 5 ta mika mata wai na dinki.

Nanma Waheedah ta cigaba da godia. Again Nadra ta sake bata takalmi sabo dal. Ranar haka Waheedah ta wuni agidan nan tana farin ciki .

Mai kunshi datazo yi har ita akayiwa. Nadra kuma ta wanke mata kanta ta mata stretching ya sake tsayi.

Sai yamma lis ta koma gidah da tarin kayan. Umma Hadiza ta Yaba sosai ita dasu Kamal.

Har kwanciyar bacci Waheedah bata dena godia ba. Tayi sallar nafila rakaa biyu tanata shararawa su Nadra godia. Da fatan dacewa a rayuwa.

××××

Kamar ko da yaushe a al'adun bukukuwan bikin su. Daurin aure ne yake zuwa farko. Bayan sunje sunyi gwaje gwaje komai nasu kalau zasu iya auren junan su

Ranar alhamis akayi bridal tea party a wani eatery dake kan nassarawa GRA. Iya kawaye mata kawai

Ranar jumu'ah bayan an sakko daga masallaci. Dubban mutane. All the who is who. Suka hallara wajen daurin auren amare da angwaye

Ango Zayn Adams Nasseer da amaryar sa Ahlam Nouh Nasser. Sai amarya da ango na biyu wato: Jannat Adams Nasser da angonta Zaid Nouruh Nasser.

'Yayan Yaya da kanne. Biyu daga yaran professor Adams. Saia daya a yayan su wato Nouh Nasser. Sai daya ta kani gare su wato Nouruh.

Aka daura auren a babban masallaci. Akan sadaki mafi daraja. Daga nan akayi reception a farfajiyar dakin taro da ke gidan na farfesa Adams. Anci an sha anyi hani'an. An kuma yi addoin zaman lapia ga amare da kuma angwayen su....

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ 💞 _NA_

_NANA HAFSATU_ _(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_PG:29_

_____

Tuni mayukan shafawa. Da shower gel na wanka harda night cream da face mask da Nadra ta bawa Waheedah. Sunyi matukar karban jikinta. Kalar fatar ta ta kara haskakawa . Ko'ina luwai luwai na jikinta tamkar kifi tarwada. Very smooth and clear. Gashi cimar da suke ci ta the Adams family ta matukar kara gina jikin su . Dukkanin su sun maro akan da da suke a kandare saboda yunwa.

Ranar jumu'ah din da aka daura aure za'ayi mother's eve. Shine wanda zasu saka red material dinnan.

Don haka tun da safe Waheedah tayo wanka. Ta shiga tsaftace komai da killace su zuwa inda ya kamata.

Tana zaune akan kujerar zama. Tana wanke wanke. Marka ta fito daga dakinta. Ta saki wata bahaguwar miqa tana gantsarewa sosai.

Tayi kan Waheedah tana tafa hannuwan ta.

"Wannan kwailin din da kike narasa na menene.... Karfi da yaji sai kin koma baturiya. Kinata bilicin. Da girman Allah Sa'adatu kalli yarinyar nan yadda ta mayar da kanta "

Cewar Marka, Ta juya tana gayawa inna Sa'adatu. Dake zaune a tsakar gidan tana yankan farce.

"Ai lamarin se kallo kawai Marka... A deyi a hankali . Kuma abu duniya a sannu. Kuna bin kwadayi sannu ahankali zaku faada halaka." Inna Sa'adatu ta fada tana yatsina fuska.

Suka cigaba da bin su da zagi da mugayen alkaba'i. Ita dai Waheedah ta toshe kunnuwanta ta hanyar qin cewa komai.

Ta karasa wanke wanken ta kai kwanukan daaka. Ta sharce inda tayi wanke wanken tanata sauri. Don tuni Umma Hadiza ta tafi gidan aikin nata da sassafe dan kama musu wasu aiyukan.

Kayan da Nadra ta bata da material din wajen Maa da aka dinka ta saka a leda don kai wa wajen guga.

Tanata sauri ta fito daga cikin dakin sanye cikin riga da skirt yan kanti sai hijabi babba wanda take zuwa islamiyya da shi.

"A yawo. A yawata...Sai ina kuma zaa sake harbawa. ?"

"Yawan ta zubar m..." Inna Sa'adatu bata karasa fada ba. Waheedah ta daga mata hannu

Idanuwanta sun kawo ruwa sosai. Don abu kalilan ne ke sakata kuka saboda raunin zuciyar ta. Ta saka hannunta daya ta goge hawayen dake tsiyaya a idanunta.

"Ke ni kike dagawa hannu.?" Ta fada cikin fushi da kufulewa .

"Ki dena aibata ni Inna... Ki dena fadan maganganun da ba haka suke ba .. Ya zaki dinga cewa yawon ta zubar za ni?"

Inna Sa'adatu na daga zaune sai ta miqe tana sallallami hadi da tafa hannuwan ta. Bakinta a bude cikin tsantsar mamakin kalaman Waheedah

"Ke da ni kike? Ni ki ke mayarwa martani dan uban ki?"

Waheedah ta sauke zuciya tana kallon gefe.

"Ni ka..."

Kwas!!! Marka ta zuba mata rankwashi a kwanyar kanta da yasha mai da kananun kitson da Najan Isubu ta yarfa mata.

"Karya ta miki? Ba halin uwar ki bane kika gada? Shegiya da idanuwa tsuru tsuru. Gaskia Sa'adatu ta fada. Kin koma mai kwailin. Jikin ki ko'ina ya cicciko bayan da ba ahakan kike ba. Idanuwan ki sun bude. Kina wani gani gani. Duk iskancin da kike a boye zai fito fili duniya tasan ke kike aikata komai."

Waheedah ta sake fashewa da kuka ganin yadda haka kawai sun tsara zancen su suna magana tamkar suna da tabbacin hakan.

"Zaki bar wannan kukan munafurcin ko sai na tashi na hanbare ki? Kayan meye kike sussunnewa a leda?"

Cikin kuka da rawar murya tace,

"Kayan fitar bikin ce zan kai guga."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull