Farrah complete Novel - Chapter 7
Farrah complete Novel Chapter 7: Farrah complete Novel Chapter 7. EPISODE 🔟 Damke wuyan Farrah yayi ganin sotake ta taimaki wannan yaron da sukeda burin…
4,202 words
EPISODE 🔟 Damke wuyan Farrah yayi ganin sotake ta taimaki wannan yaron da sukeda burin samin duniya ta sanadin sa, wani kalan jijjigata yayi yace “kinsan wanene kike shirin kwancewa ke agwai? Kinsan biliyan nawa zamu samu akan yaron chan”? Ihu Farrah tayi da kyar danji tayi kaman zata shide sabida yanda ya damke wuyanta, kokawa tashigayi tana kokarin kwace kanta amman takasa kwace kanta daga hannunshi sabida karfin dayake dashi, Zayn ta kalla da kidnappers biyu suke tsaye kanshi dayan nakokarin daukan igiyan yasake daureshi, bin dan jinin dagefen idanunshi ke fitarwa tayi dakuma karyayyen hannunshi taji wani kalan karfi da kwazo yazomata bazata bari su kashe yaron nan ba, maybe yanada iyaye yanada kannai dazasuyi tunaninshi kaman yanda kusan kullum take tunanin Yar uwanta da aka kashe agabanta, wani kalan ihu Farrah ta yanka. “Eeeeeeeeeeeeeee!” Shi kanshi Oga baisan lokacin daya saketa ba yay baya yana kokarin taushe kunnenshi dan muryanta yay wani kalan piercing dodon kunnenshi, dawani kalan sauri cikin bala’in kwazo da jarumta da ita kanta batasan tanada shi ba tajuya batai wata wata tai kan Oga dake karkade kunnenshi sabida yanda yakejin ihunta har yanzu, gabanshi tasha hakan yadago kanshi zai kalleta tai targeting kwayar idanunshi goran yajin ta danna ta fesama a fuskanshi da bala’in yawa, Ya shiga idanunshi da kyau ya shiga hancinshi atake yashaka da baki, ihun dababu shiri Oga yayi yajuya ahaukace gabaki daya yama zare danjin yajin yayi har kwakwalwa yana tattaba fuskanshi azare yace “ku kamata Lamba takasheni da yaji, wayyo idanuna” juyowa tayi da sauri jin yakira mata sauran, Lamba da dayan sukayo kanta, daganan inda take ta fesa musu dudda suna kokarin kaucewa amman saida ya shiga kwayar idanunsu da jikinsu dan har fatan wuyansu ta watsamawa sukahau ihu suma kowa yay gefe azare wato yaji bala’i ne barinma awajen maza, ganin haka yasa ta arto aguje inda Zayn yake yana kallonta kaman wanda har yanzu bai yarda cewa mutum bace, da duka karfinta takai hannuwanta takama hannunshi mai lafiyan tana ihun kokarin magana with so much force. “Ahhhhh jeh….jeh..…” tana kokarin gayamai suje da baki da hannu, da kyar Zayn ya iya tashi yana kallon yanda hannunshi ke lilo kaman ba hannunshi ba, sakin hannunshi mai lafiyan Farrah tayi tazo ta bangaren hannunshi mara lafiyan ahankali takama hannun saida Zayn ya lumshe idanu hawaye suka zubo sharrrr, daura hannun tayi akan kafadarta sanan takai hannunta daya kan waist dinshi dan yafita tsayi sosai tafara tafiya dasauri dasauri tana waigen bayan su, Oga dasu Lamba na kasa suna fama da yaji kaman wayanda jinnu yabuge, Lamido dasai yanzu ya iya tashi daga wurgan dashi da saniya tayine yashiga gyara bindigarshi da settings din ya birkice sabida barar dasu da akayi, ganin zai harbesu yasa Farrah tawani ja Zayn dawani kalan gudu shima Zayn dayaga bindiga wani kalan karfin gudu ne yaji yazo mai sukahau gudu kaman ba gobe, harbi Lamido yafara yana binsu dagudu shima cikin ikon Allah ko bullet daya bai samesu ba sabida yanda suke famfala gudu, sosai Zayn ke gudu yana kallon gefen fuskan Farrah da kusan itace jagoran gudun nasu tana zufa sosai, dan nauyin hannunshi na kanta, baitaba ganin brave yarinya karama kaman itaba tunda yake in his life, shi baimasan mata can be this brave ba sai dai a tv!
Juyawa baya Farrah tayi dan hakanan jikinta yabata wani abu, wani katon dutse Lamido ya dauka yawani jefo musu yayo saitin Zayn, cikin zafin nama tasaki hannun Zayn karyayye sanan tawani fada kirjinshi ta kankame shi tareda juyarda shi ita tadawo saitin dutsen, dutsen ya sauka akan bayanta wani kalan mugun kara tayi dan har kirjinta taji dutsen ta kankame Zayn sosai dashi kanshi saida yaji yanda dutsen ya daketa akirjinshi sanan ahankali tadago fuskanta ta kalleshi hada idanu sukayi shima kallonta yayi da idanunshi daya dayake iya amfani dashi, ahankali tasakeshi sanan yafita daga kirjinshi sanan tawani juya takalli Lamido dake tahowa yana dariya yace “Au kin tsaya kin ci saa bullets dina sun kare da wlh nai wasting rayuwanki, Shegiya akwai, sai shegen wayau uwa yar dula” dan murmushi tayi da kyar sanan ta tsugunna kasa ahankali dutsen daya jefomata ta dauka sanan ta kalleshi yana dunfaro su yana tafiya yana dan dingishi saitashi tayi tadage da duka karfinta jefamai dutsen tayi dudda yaso ya kauce amman saida dutsen ya sauka akan goshinshi haba sai jini, wani kalan tsalle Farrah tayi tareda mai gwalo dayasa Zayn yadan ware idanunshi cikeda mamaki, dan juyowa tayi takalli Zayn dake tsaye yana kallonta kaman yasami tv baki tabude kaman zatamai magana jin sahun gudu yasa duk suka kalli wajen, su Oga kezuwa but still sunada nisa hannun Zayn mara lafiyan takama suka shiga gudu daga ita har shi wanan karan yamafi na dazu, sunyi gudu nakusan 10min sanan suka kai wajen wani rami da bishiyoyi suka kare bazaka taba sani da rami a wajen ba, tsayawa gaban ramin tayi tana haki sosai sanan tasaki Zayn tanunamai ramin da hannu alamun ya shiga, ramin ya kalla sanan yakalleta dan bola nema cikin ramin, sake nunamai tayi tana kallon bayansu dan yanzun nan su Oga zasu cimmusu ganin inda take kallo shima baison akamasu yasa yashiga ya tsugunna yana taushe hanci amai na tasomai, juyawa tayi da sauri ganin ya shiga ciki zuwa gaban wani bishiyan mangwaro duk Zayn na kallonta wani kalan tsalle tayi tahau bishiyan sanan ta karyo babban reshe dakeda ganyayyaki da mangwaro nunannu ajikinsu, da wasu different itace sanan ta dirko kasa ta taho da gudu fadawa cikin ramin tayi daidai su Oga sun karaso wajajen ahankali tasa reshen tarufe saman ramin dasuke ciki, ganyayyakin suka rufesu sanan ahankali tajuyo takalli fuskan Zayn dake kallonta, hannunta ahankali takai tadaura kan lips dinta alamun yay shiru, samin kanshi yayi da gyadamata kai ahankali kaman wani obedient child, sanan takalli hannunshi dataga yadaura hannunshi mai lafiya akai yarike kana gani kasan hannun azaba yakemai, ijiye itacen data karyo daga bishiyan tayi akan jikinta sanan takai hannayenta ta kwance igiyan hulanta tacire hulan shima ta ijiye akasa, ahankali tasaka hannunta tazame dan kwalin atamapan dake kanta wani kalan zubewa tulin churdadden gashinta yayi daba gyara abaya da Zayn yagani yana taba har kasan wajen dasuke zaune, ko kadan bata damuwa, yaga dan kwalin yaga tayi tararaba shi, sanan tadago kanta takalleshi hada idanu sukayi ahankali takalli monkey jacket din dake saman white shirt din dake jikinshi, da hannu ta nunamai monkey jacket din sanan tamai alamu yacire kallonta yayi dan baigane metake cewaba, hakan yasa ta daura hannunta kan jacket din tadan ja alamun yacire, dan yunkurowa yayi sanan yacire da kyar yabata, karba tayi sanan ta dukunkune rigan takai saman bakinshi duk yana binta da idanu, sanan takama hannunshi mai lafiya tadaura akan rigan asaman bakinshi sanan tanunamai saman ramin dakuma nunamai alamu yay shiru ma’ana kada yay ihu ya taushe bakinshi kada mutanen nan suzo sujisu, sanan ahankali yaga tasaka duka hannayenta kan hannunshi karyayye takama runtse idanunshi gam yayi koyaya aka taba hannun shi kadai yasan yanda yakeji, ahankali take taba hannun ta lumshe idanunta, ta iya gyara karaya awajen maman ta takoya, Mamanta na gyara karaya sosai kusan shine ma aikin datakeyi a birni ana biyanta tana dauri agida, ita kawai gani tayi ta iya a kauyen nan tama mutane biyu dauri kuma sun warke, gano karayan tayi hakan yasa ta bude idanunta tadauki itacen data ijiye akasa ta daura kan jikinta sanan tawani kalan murde hannunshi tahade kashin dayasa yay wani ihu bakinshi taushe gumi na ketomai tako’ina, sanan ta jera itacen tass kafin tasaka igiyoyin dan kwalinta ta daure hannun layi layi tam tam, sanan tasaki hannun nashi ahankali bude idanunshi yayi yakalleta harta dauki hulanta tana daurawa akanta tana kulle igiyan a gemunta, dayan igiyan daya rage ta dauka shi yanada fadi sanan ta kalleshi bayan tagama gyara zaman hulanta, tasowa tayi tazo da gabanshi takalleshi sanan tadaura hannunta daya kan idanumta, kafin ahankali takai igiyan tadaura ma idon mara lafiya tadaure kullin abayan kanshi sanan takoma tazauna, wani kalan dadi yaji da idon namai kaman zai fadi yanzu saiyaji kaman abu yatare idon daga fadi, ahankali yakalli hannunshi dudda yanamai zugi sosai but he’s feeling much better kan dazu……… ”bazasu taba wuce nan wajen ba kuduba dajin nan tass, duk inda za’agan su agansu, inba hakaba saina kashe kowa na kauyen su dan nasan daga rugar fulanin chan take, itane kaje kagani jiya da daddare Lamido” dasauri Lamido yace “a’a Oga, ni wata bazawara nasamu Oga”.
This book is 500 VIP is 2k 3107021073 aisha Muhammad first bank pay and chat me up by clicking on this link; wa.me/+2347012181461?💫 FARRAH💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣1️⃣ Cikin tsananin fushi dakuma tashin hankali Oga yace “Duk inda zaku shiga ku shiga kufito min da yaron nan, that boy life is our golden ticket to paradise” baisan ya akayi ba but jiyayi yasa hannu yakama hannun Farrah gam gam atsorace jin maganan da Oga keyi kirjinshi na bugawa dum dum dum! Ahankali Farrah takalli hannunta dataji ya kama yarike kafin gently tadago manyan idanunta takalli fuskanshi, ko kadan hankalinshi baya kanta fuskanshi na kallon sama dan asaman kansu yakejin maganansu gani yake kaman zasuyi missing step kawai su taka reshen mangwaron su fado cikin ramin dasuke su gansu su kasheshi, zufan dakebin gefen fuskanshi ta kalla dan murmushi tasaki tunda tai wayau yaune rana na farko data taba haduwa da namiji matsoraci, ko Baffa dayake nan siriri baikai Inna kiba ba baida tsoro, rashin mutuncin yake surfafama Inna dudda idanma duka ne zata iya zauneshi ma amman baya tsoron ta balle uban kowa, su Moddibo dabama sukai wannan girma ba suma basuda tsoro amman jibi wanan katon yanda jikinshi ke rawa, tabe baki tayi tadauke kai batare data cire hannunshi daga kan hannunta ba ta jingina da bangon ramin hankalinta kwance ta lumshe idanu dan wani kalan baccin gajiya takeji ko minti uku batayi ba bacci yay awon gaba da ita azaunen, minsharin dayaji taja yasa dasauri yajuyo da kanshi ya kalleta bacci take azaune bayanta jingine da bango tadan dukar da kanta hakan yasa bama ya iya ganin fuskanta sai saman hulanta, mamaki ne ya kasheshi how can she sleep comfortably acikin rami akan wanan dattin? Yana nan inda yake yanajin duka neme nemen shi dasukeyi aka wani kalan tsuge da ruwan sama dayasa yaji sun kwasa dagudu, kalan azababben kishin dayakeji yasa yabude bakinshi ahankali yanajin wani iri but ji yake idan baisha ruwan nan ba zai iya mutuwa, ruwan dake tsiyaya daga ganyayyakin nashiga bakinshi yana hadiya ahaka, saukan ruwan dataji kan fuskanta yasa tabude idanunta ahankali kafin taja hulanta baya tadago kanta ta kalleshi ruwa na fesowa a fuskanta shima kallonta yake, saikuma chan yamaida bakinshi yarufe ganin kaman yanda takeshan ruwan yake kallo, dan yunkurowa kadan tayi taja reshen gefe ta lelleka ganin basanan yasa ta matsar dashi gefe tafito sanan ta tsugunna gaban ramin tamikamai hannu ahankali yakalli hannun nata sanan gently yasaka mata nashi aciki yafito ahankali da taimakonta, mangwaron su ta katse daga jikin reshen sanan tamikamai guda daya kallon mangon yayi sanan yakalli reshen da bolan da aka rufe dasu yanajin amai na zuwan mai tuna ruwan dayasha amman aman yaki zuwa sanan ya girgiza mata kai, maida mangwaron tayi tarike tafara shan nata dan rawa yafara na sanyi dan ruwa ake mai karfin gaske ita ko ajikinta, tafiya tafara da sauri shima yabita yana tafiya da sauri har zuwa gaban dutsenta hawa sukayi sanan suka shiga kogon, waje tanunamai hakan yasa ya zauna akasan ahankali fita gaban kogon tayi sai yanzun nema gabanta yafadi duka tumakan su Shanu daya kawai tagani awajen yana yawo, wani irin kalan mugun faduwa gabanta keyi, dawowa ciki tayi ta zauna sanan ta kalleshi kaman yanda yake kallonta batace mai komi ba.
Ahankali yana kallonta yace “do you have phone please”? Kallonshi ta tsaya tanayi kuri hakan yasa gently yace “kinada waya”? Girgizamai kai tayi alamun batada shi, shiru yadanyi saikuma yasake dago kai yakalleta still tana kallonshi murya chan kasa yace “wani gari ne nan?” Da demonstration tagayamai ganin yanda ya tsaya kuri yana kallonta bai gane abinda take cewa ba yasa tamai alamun tana zuwa tamike tsaye tafice daga kogon bayan riganta yabi da kallo duk jini yabata dutsen da aka buga mata, sauka tayi daga kan kujeran ta kwasa da gudun bala’in sa’i karkaransu ana ruwan nan, direct gidan su Shafa tayi tana shiga taga Shafa ita kadai a kitchen tana soya manja zatai girki, ganinta yasa Shafa tasaki baki tace “yanzu da girmanki kika shiga ruwa kika jike haka Kurma?” Karasawa gaban Shafan tayi tasa hannu ta dagata daga kan kujera sanan tafara gayamata komi a kurmance Shafa nabin labarin tundaga farko har zuwa yanzu, saida tagama tass sanan Shafa ta zaga ta bayanta riganta ta daga ganin taji ciwo sosai yasa tace “waike Farrah maisa bakijin…..” Farrah bata bari takarasa magana ba ta girgiza mata kai sanan tamata alamu itadai tabata wayan, jim Shafa tayi tana kallonta tanason Farrah sama da tunanin Farrah but bataso Farrah taje tasa kanta a matsala, wucewa tayi ta shiga dakin Baban su, wata tsohuwar waya taciro wayan ma akashe tabama Farrah karba Farrah tayi tana murmushi sanan takama hannun Shafa suka fice daga gidan, suna fita ta tuna yanda yakeji tadawo cikin gidan dasauri dakin shafa tashiga ta dauki bargon Shafa dake kan gadon tafito Shafa tabita da kallo sanan tai shiru, gudu sukahauyi nan da nan sukakai wajen, shiga ciki sukayi yana zaune inda Farrah ta barshi sanyin gaske yakeji ya kankame jikinshi warware bargon Farrah tayi ta lullubamai ya sauri yarike bargon sanan tamikamai wayan da Shafa tabashi karba yayi dasauri yana kallon wayan yana dannawa ganin akashe, kugu Shafa tarike tace “kaga Farrah Kurma ce, kuma marainiya ce batada Baba batada Mama, yarinyar nan dakake gani batada gata akauyen nan wahala take, Allah ne kadai gatanta koma wa zaka kira ka kira sabida kafita daga hannunta banson kasamin kawa a matsala” tunda take maganan yake kallonta harta gama, kallon Farrah yayi da itama kallonshi take yanzu daman kurmace, juyowa yayi yakalli Shafa ahankali yace “inane nan?” “Kauyen kudiri” tafadi kai tsaye, murya chan kasa yace “awani gari”? Ahankali tace “garin adamawa” kunna wayan yayi cikin ikon Allah ta kunnu saura one bar, ga service ma kara daya itama rawa take, number Papa yasaka yay dialing yaji ana you have one minute remaining shima ana maganan tana breaking wayan yafara ringing dauka akayi yaji muryan Mami hakan yasa dasauri yace “Mami” muryanta na breaking sosai tace “Hello, Hello” dasauri shima yace “Mami, Mami, is Zayn” duk tsayawa kallonshi suke yanda yake maganan yana fama da wayan yakaita baki yakaita kunne, Shafa tace “ka karamata volume haka Baba keyi idan kawu yakirashi daga binni” da sauri yasa a speaker shima da kyar yagane sabida bai iya amfani da wayan ba “Zayn is that you, muryanka nakej………”. Muryan Mami shi yafito ras awayan daidai wayan ya katse kati yakare, gyadama wayan kai yayi ahankali saiga hawaye sharrrrr yazubo daga idanunshi, ware idanu daga Shafa har Farrah sukayi suna kallonshi, dama kattan maza na kuka, ringing wayan yashigayi hakan yasa dasauri yadauka yasa a speaker wanan karan murya Baban shi yaji kaman ma kuka Alhaji yake dan baya iya magana da kyau yace “Zayn dina kana ina are you okay”? Girgiza kai yayi kaman yana gabansu cikin tsantsan shagwaba yace “I am so scared Papa, please come and get me, I am scared” cikin wani kalan lallashi da so naban mamaki Alhaji yace “stop crying where are you tell me zanzo na daukeka” ahankali yace “kauyen kuduri adamawa state” “adamawa state Innalillahi we are coming with choppers gamunan, kafin nakaraso I am calling the governor na Adamawa stay with this phone okay, wherever you are they’re going to provide you with security, I am coming for you Zayn dina, your father is coming okay” gydamai kai yayi ahankali wani kalan zazzabi na rufeshi jin muryan iyayen shi, suka katse wayan hannunshi yasa akan fuskanshi ya share fuskan nashi tass, sanan ahankali yadago kanshi yakallesu hawaye yagani sun taru a idanun Farrah sosai tana kallonshi, hannunta Shafa takama tace “wuce mutafi tunda za’azo daukanshi wayan idan zai tafi ya ijiye mana anan zamuzo gobe mu dauka” dan kallonshi Farrah tayi kaman yanda shima yake kallonta kafin ahankali tafara tafiya tanabin Shafa dake janta suka fice daga kogon. This is not a free book chat me up directly by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461💫 FARRAH 💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣3️⃣ Direct wani babban asibitin da Mami ke aiki suka wuce dasukakai Abuja, jikin manya manyan likitoci har rawa yake aka wuce wani observation room da Zayn, dakin daza’ayi mai general check up kafin eye Doctors suganshi, Mami kuma scrubbing in tayi dan itace in charge surgeon ma Farrah she just feel this is the least she can do for the small brave girl after saving her son’s life, shikuma Alhaji zama yayi acikin wani executive lounge da only VVIP guest dinsu ake bamawa, Malam dai yadawo dan kallo yana tareda su amman bai zauna akan kujeran da Alhaji da Uncle ke kai ba dan sunmai wani kalan mugun kwarjini yana kujeran dake bayansu, kaganshi zaka dauka wani almajiri ne, ringing da wayan Alhaji yayi yasa ya farka daga zurfin tunanin dayakeyi dasauri yadauki wayan ganin Gwamnar Adamawa ne ke kiranshi, amsa wayan yayi sanan yay murmushi yace “Alhamdulillah, thank you excellency, to to to shikenan” zare wayan yayi daga kunnenshi ya katse sanan ya kalli Uncle dake kallonshi yace “ankama daya daga cikin kidnappers din” dasauri Uncle yace “Alhamdulillahi naji dadi sosai Yaya” shiru Alhaji yayi yanadan karkada kafa yana tunani sanan yace “zan iya yafema mutum duk wani laifi dazai iyamin aduniyan nan dakake tunani amman banda laifi daya shine cutar mini da Zayn” yasakeyin shiru saikuma ya bude malummalum dinshi yadauko wani clean handkerchief yakai kan idanunshi yana share hawayen dasuke fitowa yace “inda sun kashemin Zayn da yaya zanyi da rayuwata eh” kama kafanshi Uncle yayi yace “Yaya dan Allah kadaina kuka nace kuma kadaina maganganu haka bagashi yanzu an ganshi ba” cikeda damuwa da rauni yace “inda yarinyar chan bata taimakeshi ba, da yanzu shine yake kwance a operation room rai a hannun Allah, you know something I am going to reward that girl handsomely wallahi kuwa” sanan yajuyo yakalli Malam dake dunkule waje daya sanyin AC ya isheshi yace “Malam kome kakeso kafadamini zan maka shi dan diyarku ta chanchanci sama da haka awajena mekake so kanason gida a birni”? Wani kalan washe baki malam yayi yana murmushi azuciyan shi yace “inama tamutu su biyani diyya nafi kowa kudi a kauyen mu” anatse yace “a’a Alhaji Baran iya rayuwan binni ba, kawai dai kudi nafiso na gyara gonata da sauran ayyuka” murmushi Alhaji yayi yace “tom shikenan zan saya maka gona dai dai gonaki dari a kauyen ku” wani kalan zaro idanu Malam yayi yakasa gasgasata maganan dayaji gonaki dari yajiance sanan Alhaji yace “zan kara maka da naira miliyan goma kaje kaja jari” wani kalan fadowa yayi daga kujera yay rarrafe yazo gaban su Alhaji, kwanciya yayi flat akasa yana kuka yana musu addu’a, murmushi Alhaji yayi yace “tashi kaje ka zauna” sanan yakalli Uncle yace “jeka kawo cash na 10M kabashi” dasauri Uncle yace “nadauka sai an sallami yarsu za’a bashi”, girgixamai kai Alhaji yayi yace “kawomai miliyan gomanshi a leda kabashi yazauna yana kallo shima yanajin farin cikin da sanadin diyarshi nima inajin kalan farin cikin nan yanzu ahaka. “Kaico! Wayyoo Alhaji, aradun Allah zuciyata zata buga, yau ni Malam nine mai da miliyan goma, Wayyoo Allah na” dan dariya Alhaji yayi sanan yatashi yawuce dakin da Zayn yake ciki shikuma Uncle yatashi fuuu yafice ko kallon Malam baiyiba Malam kuma sai sumbatun kudaden daya samu yake.
Yana zaune awajen Mami tafito tana sanye da kayan operation, tashi Malam yayi dasauri ganinta yace “ta mutu ne”? Turus Mami tayi tana kallonshi tambayan yamata bambaran akunne amman takakalo murmushi tace “bata mutu ba, kuma Alhamdulilah mun samu mucire kwayar bindigan nan da yan awanni zata farka zomuje kaganta” gyadama Mami kai yayi sanan tai gaba yana biye da ita abaya zuwa dakin da Farrah keciki, tana kwance kan gado da kayan operation ajikinta, kanta sanye da hulan operation, an rufamata bargo zuwa cikinta, daga wuyanta kana iya hango katon plasta da aka manna a kirjinta inda akai aikin, ga oxygen a hancinta tana fitar da numfashi tana saukewa, wani kalan bakin ciki Malam yaji daya ganta shi da yanzu zata mutu dayaji dadi daya huta daman ta zamemai nauyi aka, yanzu tamutu zai sami kudin diyyanta sanan yahuta da fitinan Inna, dan kallonshi Mami tayi itadai batasan ko kawai she’s seeing it out of paranoia bane but the man doesn’t look happy to see yarinyar tai surviving surgery, to anya ma uncle dinta ne as he claim kuwa, anatse Mami tace “kace ba kaine mahaifinta ba”? Janye idanunshi yayi daga kan Farrah cikeda kauyanci yace “eh hasalima haryau ba’asan mahaifinta ba duka kauyen mu” ahankali Mami tace “Maman ta fa kace tarasu”? Gyadama Mami kai yayi yanadan tabe baki yace “mahaifiyarta dani kadai iyayen mu suka haifa, tunda tafara fita binni tana saida nono ta lalace, hartazo tagudu muka nemeta muka rasa, rana daya kawai tazomana da durmeme ciki kauye, wai ita tai aure amman mijin ya gudu yabarta todai a kauye ta haifesu yan biyu, yan kauyen mu suka tasata agaba tai cikin shege tazo tana karya cikin sunna ne da aurenta akanta, shine ta tattara ta gudu da yaran tasake barin kauyen, bata kara dawo da yaran ba saida sukai shekaru shadaya aduniya ta dawo dasu gida tana ciwo sosai da kauye yadauka ciwon kanjamau ta kwaso ayawon Duniya shine tadawo, babu kalan kunyan duniya da uwarta bata sakani ba, Toh dai ahaka ta mutu ciwon shine ajalinta, yaran suka dawo hannuna, bata wani dade da mutuwa ba yayan wanan ma ta mutu” yanuna Farrah, ahankali Mami tace “Allah ya jikan su da rahama” hakanan taji Farrah tabata tausayi taga tabon duka daban daban ajikinta yafi akirga wanda kana gani kasan clearly is the case of child abuse amman dai tai shiru, ahankali tace “bari nadan je chan wajen su Zayn naduba shi zaka iya zama da ita, dazaran ta farka bayan kwana biyu idan taji sauki za’a maidaku” “to Hajiya angode Allah saka da Alkhairi, Allah yakara girma” fita Mami tayi security dake gaban dakin tama whispering. “I don’t trust him, keep an eye on him please” yes Ma ya amsa mata sanan tawuce.
Kujera Malam yaja ya zauna yana kallon Farrah, kaman yadauki filon nan yadanne mata fuska tamutu yahuta yakeji, yana zaune ahaka ya saka ya warware shi kadai aka bude kofan dakin, Uncle ne rikeda Leda baka wani irin tashi Malam yayi yace “wayyo Allah kudade na sunzo” kafin ma Uncle yabashi kudin ya karba yana leka ledan saikuma ya rungume kudin yana hawaye wani kallon wulakanci da raini Uncle yamai sanan yawuce yafita daga dakin yawuce dakin Zayn.
Kallon kudin Malam yayi sanan yakalli Farrah yace “tunda yanzu ga miliyan goma na a hannuna chass ni nama yafe gonaki darin na gudu abina ko, Allah yabani miliyan goma daga sama babu abinda nayi tasha kawai zani nakoma kauyen mu, Wanan kuma idan sunga dama su yardata kosu dawo da ita kauyen mu su suka sani koba hakaba” yana gama tunanin yawani mike tsaye ledan ya ijiye kan kujera yadauko bandir daya na kudi yakirga dubu goma yasa a aljihu sanan ya daure bakin ledan ya makaleta a hammata gam gam sanan yabude kofa yafice, fita yayi daga asibitin batare daya hadu dasu AlhaJji ba yana fita motan daya gani yatare yace akaishi tasha.
Imagine yourself kina kwance a comfort na bed dinki kina duba pictures and videos na hadaddun atampopi kina gamawa kawai ki zaba, place an order, make payment akawo miki har gida batare dakin fita kinje kasuwa ba.
Imagine yourself in the middle of stress da kata kata na biki but you don’t have to worry akan atampopin anko dan akwai wacce zata miki supplying nasu har gida?
Imagine yourself kina tunanin that perfect and best gift dazaki bama kawarki be it birthday gift, wedding gift, suna gift or just casual gift, and M Shakur told you Atampa ne!
Just picture it lokacin da za’a kawo miki atampan acikin wata lafiyayyen fine jaka za’a saka miki atampan akawo miki ba abakin Leda ba kaman yanda aka sabayi a kasuwa?? Sweet right? What if M Shakur tagaya muku yau all imaginations, dreams dinan naku can become through by introducing ATAMPA REALM to you guys💃 ATAMPA REALM is an online store dake saida atampopi variety of them, daki bari, masu kyau, masu ado, wayanda ake yayi, akan kudi kuma kalilan don’t you want that?? Atampa Realm are life savers, biki, akwati, birthdays or anything they come through and represent!! Ina gayamuku atampopin su makes statement🌹
All you have to do is give them a call 📞 +2348097573597
Ga wayanda basason kira you can chat them up a WhatsApp by clicking on this link:; wa.me/+2348097573597
You can also follow them on Instagram by clicking on this link; https://www.instagram.com/p/CiQcu1loZ7c/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
You can join their WhatsApp group by clicking on this link; https://chat.whatsapp.com/CUmRWXy4evqLtOoYp3XmNt💫 FARRAH 💫
✍🏻 M SHAKUR