Kenza eBookz

Farrah complete Novel - Chapter 10

Farrah complete Novel - Chapter 10

Farrah complete Novel Chapter 10: Farrah complete Novel Chapter 10. Wuraren 4 na yamma Alhaji yashigo gidan, ana budemai mota ya sauko daga motan yana…

4,414 words

Wuraren 4 na yamma Alhaji yashigo gidan, ana budemai mota ya sauko daga motan yana gyara zaman babban rigan dake jikinshi, direct side din Zayn yawuce bodyguards dake tsare gaban side din Dad yakalla tareda amsa gaisuwansu sanan yashiga flat din Zayn dake wani kalan lafiyayen kamshi ga sanyin AC tako’ina daidai lokacin kuma Zayn dake sanye da bathrobe fari yadaure igiyan agaban rigan kafanshi sanye da bathroom slippers yafito daga kitchen dinshi da glass of milk a hannunshi yana kurba dasauri Alhaji yace “why are you getting milk dakanka bayan kanada masu maka”? Dan yatsine fuska yayi yana shigowa cikin falon, kan kujera yazauna tareda daura kafanshi daya kan dayan ahankali yace “I want to start doing everything myself from now, daga yanzu su daina shigomin cikin daki su tsaya nan bakin kofa” dan murmushi Alhaji yayi yana kallonshi trying to read something yace “ohh that’s new” zama yayi kusada Zayn din yana kallon farin glasses din da akamai na hospital dayake sanye dashi shi, glass din yamai kyau ba kadan ba, baki yabude zaiyi magana Zayn yarigashi ahankali yace “Papa” yay maganan yana ijiye glass na milk din kan coffee table sanan yadago, ahankali Alhaji daya tattaro duka natsuwanshi yace “Na’am Zayn menene me kakeso”? Dan juyowa Zayn yayi yakalli Baban nashi kallon daya dade baimaiba murya chan kasa yace “Dad am I being immature”? Yanayin fuskanshi kadai Dad yagani yagane he’s serious da tambayan baki yabude zaiyi magana cikin yanayi na baison yamai karya Zayn yace “don’t you dare lie to me Dad kafada min gaskiya please, I don’t have anybody, you are my best friend Dad, am I being immature”? Tsayawa Alhaji yayi yana kallon Zayn kalman best friend daya kirashi dashi wanda Zayn baitaba kiranshi dashiba yasa yaji kaman yay kuka, gently ya gyadama Zayn kai yace “yes! But just a little Son, I guess u just 26 still a kid that’s why” girgiza kai Zayn yayi tareda dan juya idanu irin na sangartattun yaran nan yace “no Dad, I think I am being incentive Dad, I am selfish and extremely rude” dasauri Dad yace “noooo Zayn kada ka kara kiran kanka haka, Zayn you are one sweet Human da duk wanda zai zauna dakai saiya soka, you are just being yourself, chasing your likes abubuwan dakakeso, and you are one reserve person baka shiga rayuwan kowa, shiru shiru, you are just the way you are, and being the way one is doesn’t mean he’s rude or incentive or even selfish, you are Zayn, my only son, abin alfaharina, kyautan da Allah yamin” yay maganan yana kama hannunshi mai lafiya trying to assure him abinda yafadamai gaskiya ne, shiru Zayn yayi yana kallon Babban shi na kusan 2min kaman yanda Baban nashi ke kallonshi, ahankali yace “Dad” ahankali shima Alhaji yace “na’am Zayn dina meke damunka haka nafara shiga damuwa wlh, menene talk to me, kome kakeso consider it done” dan ijiyan zuciya Zayn yasauke sanan yakalli hannunshi dake nan adaure yana kallon igiyoyin dan kwallin Farrah data dauremai hannunshi dashi, yatsanshi yakai kan igiyan yana tabawa murya chan kasa kaman mai tunani yace “When those goons kidnapped me Dad I went through a whole lot, I lost all hopes, was thirsty, hungry, ga karaya ga idanuna ga lot of spiders Dad at that point everything was a thing for me, I looked up to the sky nace Allah ya taimaken, then that gurl came from nowhere kaman daga sama aka jefota” yadanyi shiru yana kallon hannun nashi still in a very very low tone yace “Dad that girl protected me with all she got, at first I thought she was an angel, Dad kasan dan kwalinta tayaga ta dauremin hannun nan” yay maganan ahankali yana shafa hannunshi saikuma yadan yatsine fuska ahankali yace “Dad kasan I couldn’t thank her, whenever I looked at her sainaji she’s too small nace mata thank you and I am not use to thanking anybody” yadanyi maganan yana murmushi iya lebe kafin ahankali yace “Dad jikina is telling me I need to do morethan a thank you, she saved my life nima I should save her life and even give her a better life, education, da sauransu, Dad ina Uncle dinta kasa an daukoshi?” Dad na kallonshi right in the eye ya gyadamai kai, ahankali yace “tun around 3 chopper su yasauka, suna biyeda ni maybe ma yanzu haka sun shigo gidan nan” shiru Zayn yayi yana kallon mahaifinshi, lips dinshi ne yashiga rawa kaman yana fighting da abinda yakeso yafadi dan lumshe idanu yayi sanan yabude su yadaura su kan Dad ahankali yace “Dad can you adopt the girl please?”! Shi kanshi Alhaji saida yakara kallon Zayn maganan tazomai wani bagtatan bawai adopting yarinyar ne matsalan shiba ko kadan but this is the first time in history Zayn yacemai please kan wani abu mamaki ma hanashi magana yayi, ahankali Zayn yakai hannunshi yadaura kan na Alhaji yace “Dad lokacin da Mami tace the girl has been abused I felt so so guilty, bansan anything akanta ba but I know batada iyaye, and I know her uncle ran away they don’t like the girl, she’s like a burden, let’s call our lawyer muyi adopting nata idan ma so suke mukara musu wani kudi zamu kara, Dad I want to sponsor her education with my money not your own just to repay her kaji Dad” yakarashe maganan yana jijjiga hannun Alhaji, wani kalan sassanyar ajiyan zuciya Alhaji yasauke yana kallon fuskan Zayn din sanan yace “duk wanda cannot see beyond this your face da ake gani kaman u are rude is blind cus this your heart” Alhaji yakai hannunshi kan kirjin Zayn yace “is made from gold” dan murmushi Zayn yasaki, dan hararanshi Alhaji yayi yace “what are you waiting for, jeka saka kaya karakani nayi adopting yarinya ta Farrah” dan murmushi Zayn yayi yatashi glass cup nashi yafara dauka ya shanye milk din ciki sanan yawuce sama bai wani dade ba wani dark blue hoodie yasaka da gajeren wando iya gwuiwa milk, ya sanya eye glasses dinshi sanan ya feffesa turare yafito kafafunshi sanye cikin wasu navy blue designers crocs simple kayan zama gida but still ka kalleshi saika kara kallonshi suka fito daga side din Zayn din tare.EPISODE 2️⃣0️⃣

Meanwhile lemme all introduce you to supplement da I think we be solution to all problems na jikinmu.

Dukanmu nan munsan ORIFLAME is a reputable brand da aka sansu wajen wallafa abu mai kyau yanzu sunyi Supplement mai suna WELLNESS by ORIFLAME. Kowa dakuka gani mata da maza muna bukatan some mineral, vitamins da sauransu dazai helping jikinmu da system namu, supplement dazai karama defense mechanism namu karfi to protect us from ciwake ciwake, sanan dazai taimakawa organs dinmu yin aiki da kyau.

Idan kina shan wellness zaki kyau, zai karamiki lafiya, zai taimakawa organs naki sosai, akwai so many reviews, wata tace tunda tasha wellness tafara samin ruwa gaba, wata tace skin nata yay fresh, wata tace gashinta daya karairaye yadawo, wata tace nonon ta yakara cikowa, banda haka wellness na bada kariya against cancer.

Wellness is the best supplement da ake dashi right now wanda kasashen duniya da dama sukasha kuma suke recommending ma mutane.

I have good news! Supplier wellness dinan tace namuku albishir duk wanda yasaya akwai FREE DELIVERY to duk inda kake a Nigeria. You will never regret buying wellness, zaki saya sanan kisaima maigida nshi shima. Don sayan wellness contact her by clicking on this link; wa.me/+2349133427208

💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣0️⃣ Side din Mami suka wuce, Mami na zaune a falo tana magana da Mama awaya suka shigo ganinsu tare yasa ta hararesu tacigaba da wayanta zama kusada Mami Alhaji yayi yana kallonta sabida tai kyau taci gayu sosai cikin kace kai kyau, katse wayan tayi takalleshi tace “ne kake kallona haka” cikeda tsokana yace “wai ke baki tsufa ne jibeki saikace ba kene kika haifi wannan gansamemen saurayin ba” yanuna Zayn, dan dariya Mami tayi tace “I take that as a compliment” “ina Farrah”? Alhaji ya tambayeta anatse, murmushi tayi tace “tana sama nabarta cartoon take kallo a IPad dina, you need to see yanda maganan ta ke improving Alhaji, one thing I like about her is she is fearless tanada kwazo da jajircewa” murmushi Alhaji yayi yace “kiramin ita” tashi Mami tayi tai sama bata wani jimaba suka shiga saukowa tareda Farrah, tana sanye da doguwan riga na atampa brown dinkin yamata das das ajiki sai dan kwalinshi data daura aka kanta na kasa wani kunya taji tanaji ita Mami tafiso da Mami kawai tasaki jiki saukowa kasa sukayi Mami ta zaunar da ita kan kujera kusada ita kasa zama tayi tazame jikinta ta zauna akasa da sauri kanta na kasa tashiga wasa da yatsunta Dan dariyan manya Alhaji yayi yace “Farrah yaya jikin? Wajen dinkin yadaina zafi”? Gyadama Alhaji kai tayi ahankali cikin zazzakan muryanta tace “eh…..Ab….ba” jinjina kai Alhaji yayi yana murmushi yace “Masha Allah, ga muryanki nan Tubarkallah Allah kara sauki” “Farrah” yasake kiranta anatse hakan yasa ahankali tadago kanta ta kalleshi, ajiyan zuciya Alhaji yasaki, yace “kingan ni nine mahaifin Zayn, mijin Mamin ku, da Mariya da Fatima da Maryam, Zayn kadai Allah yabani, rana daya kuma Allah yakawoki cikin rayuwan mu, akwai abinda yasa nasaka aka kiraki, inaso na tambayeki ne naji amsanki kafin nai komi” yasakeyin shiru sanan ahankali yace “Farrah kawunki ya sanar damu ke marainya ce, matata nan Maman Zayn likita ce, itace tamiki aiki a operation, taga tabo da dama ajikinki wanda yake nuna na alamun duka ne, yanzu inaso namiki wani tambaya banso kimin karya kinji” gyadama Alhaji kai tayi ahankali, anatse Alhaji yace “wanene yasamiki garwashin wuta abaki?” Shiru tayi gabanta nafaduwa dum dum, dafata Mami tayi ahankali tace “kada kiji tsoro ki yayi gaskiya kinji” gyadama Mami kai tayi sanan takalli Dad, batasan ya akayiba kasa karya tayi ahankali tace “In…na” “Matar kawunki”? Gyadama Alhaji kai tayi tace “eh””ita ke dukanki ma”? Gyadama Alhaji kai tayi takai bayan hannunta dasauri tashare hawayen daya zubomata, shiru dakin yayi Alhaji na kallonta, murya chan kasa yace “akwai abinda ake cema adoption aturence, yana nufin zaki dawo diyata ni da Mami da kotu tabamu mune custodian naki, kula dake yafita daga hannun su kawunki yadawo hannunmu dundundun ki dawo yarmu musaki amakaranta da sauran su, nakira lawyer na halama ya iso yanzu, yanzu hakama kawunki da matarshi na gidan nan chan bangaren baki, amman so naki nafara jin bakin ki kafin nasa akawo kowa nan, Farrah” Alhaji yakirata ahankali murya chan kasa tace “Na’am” ahankali yace “kin yarda ni da Mami muzama iyayenki?” Wasu kalan hawaye ne suka cika idanunta, tunda take baa taba bata daraja da mahimmaci dahar za’a zaunar da ita atamabayi yardanta Awani abu ba sai yau, tunda tahadu da mutanen nan sunada kirki sosai, batada kowa aduniyan nan banda kawu shi kadai gareta amman shima baya sonta baya kaunarta agabanshi aka kashe mata yar uwa baice komiba, dafata Mami tayi dasauri ta kalli Mami, Gyadamata kai Mami tayi alamun tace “eh” ahankali tace “eh Abba” rungumeta Mami tayi tana share mata fuska tace “daina kuka to” sai alokacin Zayn yadan saci kallonta, fuskanta na jikin Mami tana goge hawayen dasuka zubomata kaman ance ta kalleshi hada idanu sukayi da Zayn din hararanshi tayi tareda dauke kai.

Dauke kai shima Zayn yayi dasauri yana regretting kallonta ma dayayi waya Alhaji yayi sanan ya katse wayan yakalli Mami yace “tafi da ita sama”.

Wani Babban lawyer Alhaji ne yashigo falon tareda Uncle, sai Malam da idanunshi sukai zuru zuru da Inna da itama idanunta sukai zuru zuru, Malam yay mamaki dahar gida aka shigo aka daukesu suka shiga jirgi, Inna ihu tadingayi a helicopter wai zata mutu hanjin cikinta zasu zube.

Malam na ganin Alhaji da gudu yataho gabanshi ya tsugunna yahade hannayenshi biyu yace “Alhaji dan girman Allah kayakuri kada ka karbe kudaden daka bani, wlh wlh shairin shaidan yasa na gudu nakoma kauyenmu, to inbama shairin shedan ba ai nasan Kunsan kauyen kuma nakama nagudu, Alhaji dan Allah kayakuri wlh bazaka gane bane, Alhaji nima diyata daya rak, ina fama dakai na, kanwata tazo ciwon datayi shine ya tsiyatar dani tatas banda ko kwandala matata ce keda awakai suma awakan ranan da Farrah ta ceto dan gidan ka duka ta batar dasu, wlh ashirmena naso nagudu ne kawai nahuta inje na karata da matata da diyata guda amman nai kuskure kuya kuri” tunda yake maganan kowa ke kallonshi, cikin fushi Uncle yace “ina miliyan goman damuka baka bamu kayanmu ku dauki yarku amaidaku kauyenk……” tsayar da maganan datakeyi yayi ganin Alhaji yadagamai hannu, nuna kanshi Alhaji yayi yace “kai tun kana dan kankanin ka kataba ganin nai kyauta sanan nadawo na amshe kyautan danayi” sunnar da kanshi kasa Uncle yayi yace “a’a Yaya” maida hankalinshi kan Malam Alhaji yayi da Inna da itama ke zube gaban mijinta jikinta na rawa tunda take bata taba ganin aljannan duniya irin gidan nan ba, murmushi Alhaji yasakin musu yace “ku zauna da kyau dan Allah ni bakamin komi ba kuma bansa adaukoka sabida kudin danabaka ba nariga nabaka gonakin suma nariga nasa anma mai garin ku magana shi gwamnan Adamawa duk sanda ka koma zaka amsa koba komi yarinyar da bakaso yarinyar daka gudu a asibiti kabarta kaga kaci arzikinta” Alhaji yakara murmushi jikin Malam yay sanyi yakoma ahankali ya zauna hakama Inna, gyaran murya Alhaji yayi yace “abinda yasa na nasa akawomin kai nauyin dake kanka kake kokarin gudun mawa nakeso nacire maka shi daga kanka gabaki daya, diyarku Farrah nakeso nazama mahaifinta a shar’ance, cinta shanta, suturanta karatunta duka yadawo kaina, zai zamto Farrah tadawo diyata shine kawai abinda yasa na nemoka zaka bani”? Alhaji ya tambayeshi dasauri Malam jikinshi har bari yake yace “eh eh wlh nabaka Alhaji” Inna ma dan sosa keya tayi azuciyanta tanaji inama ace Rakiya ce ta taimaki yaron, kaman ta chakama kanta wukan bakin ciki takeji, kallon Lawyer Alhaji yayi yace “give him the papers” tashi yayi zuwa wajen Malam dan yabashi papers din yakuma nunamai inda zaiyi signing, dan yatsine fuska Zayn yayi yamike tsaye hanyar stairs yayi yay sama abinshi, shi kanshi baisan mesa yazo saman ba kujeran dakenan falon sama ya zauna yana kallon kofan dakin da yake tunani nan ne dakin Farrah dan shine dakin dake kusada na Mami, yadade yana kallon kofan, kaman akwai abinda ke controlling nashi tashi yayi zuwa gaban dakin yay jimmm yana kallon kofan, ahankali yadaga hannunshi yakai zaiyi knocking kofan dan cizan lips dinshi yayi yasauke hannun kasa ahankali, sake daga hannun yayi zaiyi knocking daidai nan aka bude kofan Farrah ce tabude kofan da saurinta dan ana kiran IPad din Mami dake wajenta zata kaimata saura kadan tafada jikin Zayn ta tare kanta ta hanyar kai hannunta daya ta daura kan kirjinshi daidai saitin zuciyanshi as kariya daidai lokacin kirjinshi ya buga dumm!💫 FARRAH 💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣1️⃣ Yanda taji bugawan kirjinshi a hannunta da sauri ta janye hannun daga kan kirjinshi hannun nata nadan rawa, dauke kai yayi dasauri daga kallonta kaman ance dole yay magana yace “on Monday zan kaiki school ki shirya” yana maganan yajuya da sauri yawuce itama juyawa tayi takoma dakinta da wayan batasan mesa ma gabanta ke faduwa taganshi ba ya chanza mata a idanu gabaki daya kaman bashine mutumin daya bata tausayi ranan dataga za’a kasheshi ba.

Sauka kasa yayi ya barsu suna kan maganganun dasuke yafice daga falon ya sauka yana tafiya a side ahankali zuwa side dinshi. “Hi Zayn” yaji an kirashi dan tsayawa yayi sai alokacin ma yalura da Layla data kirashi tana zaune kan swinging chair dake hanyar zuwa side din Zayn ta sanya wani rigan bacci mai spaghetti hand na silk fari, yanada lace agaban wuyan ya tsayamata iya cinya sai silipas akafanta, dan tsaki Zayn yaja yawuce batare daya amsata ba da sauri ta taso tabiyoshi tana murmushi tace “common Zayn the least u can do is be my friend, am back a Nigeria banda any friend fa bansan kowa a naija ba, at least ni da kai we are related and we live in the same house, I know kaida Mommy baku wani shiri and it’s okay ni baruwana da wanan just be my friend” duk maganganun nan tana yinshi ne tana biyedashi saida yakai gaban flat dinshi ya tsaya hannu yamikama bodyguard hakan yasa bodyguard din yaciro kwalin taba daga aljihun shi da sauri yabashi, budewa Zayn yayi yaciro kara daya zai maida kwalin aljihun wandonshi Layla ma tamikamai hannu tace “at least give me one nima” dan kallonta Zayn yayi for the first time ganin tamikamai hannu, bai dauka tanashan taba ba ko ajikinshi kwalin yamika mata itama ta zare daya sanan yamaida kwalin cikin aljihun shi yasa karan taban abaki, zuwa bodyguard dinshi yayi gabanshi yasa lighter ya kunna mai sanan ya kunna ma Layla ma dake kusada shi, wucewa Zayn yayi ya shiga cikin garden dinshi dan yanada nashi seprate garden dinshi agida banda na asalin gidan kuma, zama yayi kan kujera yana shan taban da sauri itama Layla tazo tazauna kusadashi tana kallon yanda yakeshan taban hankalinshi kwance, murmushi tayi tace “who is your girlfriend Zayn”? Batare daya kalleta ba kai tsaye yace “I don’t have” dan juya idanu tayi cikeda mamaki tace “yaushe zakai aure to” dan kallonta yayi kadan yana fuzo hayaki waje sanan yadauke kai yace “I don’t know” dan dariya tayi sanan ta matso kusada shi saikuma ta sauka daga kan kujeran tazo ta gabanshi ta duko fuskanta na saitin nashi gabaki daya kirjinta awaje dan dama dan yagani tayi kallon fuskanta yayi kafin ahankali yasaukar da idanunshi kan boobs dinta da he could see them da kyau dama kuma dan yagani tayi tsaresu yayi da idanu dan shi dama baisan kunya ba, cikin wani kalan murya dakejan hankalin mutum tace “nima banda saurayi Zayn, and I badly need one” ta mike tsaye tana gyara riganta dan ijiyan zuciya Zayn ya sauke ahankali sanan yadan lumshe ido satan kallon wandonshi dataga yabalain tashi sama Layla tayi dan murmushi tayi tajuya cikeda son jan hankalin Zayn tace “gud night” dan bude idanu Zayn yayi yakalleta tawuce wani kalan juyamai bombom take he don’t think akwai pant ajikin bombom dinma sabida yanda suke rawa still tanashan taba abinta, saida yadaina ganinta sanan yaja tsaki. “F**k” yafadi ahankali, shifa he can’t lie to kanshi bayason mata mace bata gabanshi but he totally loves sex, baya iya resisting sex, mtswwww yasake jan wani kalan mugun tsaki sanan ya yarda taban daya gamasha inama zai iya fita yaje club kawai tsoro yakeji wayanda keson kasheshi suna nan, dakinshi ya shiga har yanzu he’s still very much erect, fridge dinshi yatafi a kitchen yashiga dubawa gabaki daya wines din dayake dashi non alcoholic ne, he’s just looking for something dazaisa shi to be drunk, fitowa yayi yawuce sama closet dinshi yaje inda yake boye wani shisha pot dinshi amman babu yasan Dad ne yafitar dashi komi nashi saida ya hargitsa looking for wani abu amman baidashi wani kalan ihu yayi ya barar da kayan shafanshi yace “f**k this house” fitowa yayi azuciye idanunshi sunyi ja fadawa gadonshi yayi yashiga juyi his tummy hurts kaman zai fice, jijiyoyin kanshi sun fiffito da kyar bacci ya kwasheshi wuraren 2 nadare.

Da Asubahi Alhaji yashigo side dinshi tadashi yayi da kyar da kyar yatashi dan saida yasa Alhaji yay missing first raka’a amman bai damuba haka yatasoshi agaba suka tafi masallaci, tunda yadawo Nigeria yaune yaje masallacin anguwansu yay salla, ana idarwa ya yunkura zai mike dan bacci yakeji Dad yarikemai hannu, fizge hannunshi yayi yace “leave me alone Papa” dasauri Alhaji yasakeshi kafin yan masallacin sujisu fitowa yayi shima Alhajin tashi yayi yabiyo bayanshi dasauri suka shiga gidansu tare, Alhaji yace “good morning Son” “morning Dad” yafadi ahankali yawuce side din Mami batare dayaje side nashi ba, babu kowa a falo hakan yasa yay stairs yawuce sama tun kafin yakai saman yakejin muryan Mami tana biya karatun Al Qur’ani sai chan yaji muryan Farrah na amsawa ahankali, tsayawa Zayn yayi batare daya karasa hawa saman ba yadan lumshe idanu, yanajin muryan Farrah har cikin zuciyanshi, muryanta nada wani kalan secret dadi tana karatun Al Qur’ani dinan dudda muryanta na breaking but voice nata sounds like voice na larabawa and yay mamaki dayaji tana karatun da kyau dan shi yadauka bata iya komiba she’s an illiterate, ahankali kaman baiso yadaga kafanshi yacigaba da tafiya yashigo falon saman daga Mami har Farrah dasuke zaune kan carpet na tsakiyan falon saman suna karatu duka juyowa sukayi suka kalleshi, hanyar dakin Mami yayi yace “morning Mami” mamaki Mami tayi ganin Zayn yatashi da safe hakan yasa anatse tace “katashi lpy Zayn” dan ita bata biyemai da turencin nan nashi, kallon Farrah tayi tace “baki gaida yayanki ba Farrah” dan satan kallonshi Farrah tayi daidai yabude kofan dakin Mami zai shiga tace “Ina kwana Ya Zayn!” Murmushi Mami tayi jin takira Zayn da Yaya abin saiya wani kalan karamata son Farrah azuciyanta, faduwa gaban Zayn yashigayi sosai no one has ever called him Yaya da yarinya nan takirashi da Ya Zayn he really felt something, lips dinshi yadan bude kadan shima sabida kar Mami tamai fada ne yace “fine” daga ita har Mami sunga motsin bakinshi amman babu wanda yaji abinda yace shigewa dakin Mami yayi abunshi ya maida kofan yarufe hawa gadon Mami yayi ahankali ya kwanta yay shiru yana sauraron karatun su, a suratul asr dazu yasame su yana nan kwance yana jinsu wani zubin yabisu wani zubin yay shiru har sukakai suratul naba’i.

Meanwhile lemme all introduce you to supplement da I think we be solution to all problems na jikinmu.

Dukanmu nan munsan ORIFLAME is a reputable brand da aka sansu wajen wallafa abu mai kyau yanzu sunyi Supplement mai suna WELLNESS by ORIFLAME. Kowa dakuka gani mata da maza muna bukatan some mineral, vitamins da sauransu dazai helping jikinmu da system namu, supplement dazai karama defense mechanism namu karfi to protect us from ciwake ciwake, sanan dazai taimakawa organs dinmu yin aiki da kyau.

Idan kina shan wellness zaki kyau, zai karamiki lafiya, zai taimakawa organs naki sosai, akwai so many reviews, wata tace tunda tasha wellness tafara samin ruwa gaba, wata tace skin nata yay fresh, wata tace gashinta daya karairaye yadawo, wata tace nonon ta yakara cikowa, banda haka wellness na bada kariya against cancer.

Wellness is the best supplement da ake dashi right now wanda kasashen duniya da dama sukasha kuma suke recommending ma mutane.

I have good news! Supplier wellness dinan tace namuku albishir duk wanda yasaya akwai FREE DELIVERY to duk inda kake a Nigeria. You will never regret buying wellness, zaki saya sanan kisaima maigida nshi shima. Don sayan wellness contact her by clicking on this link; wa.me/+2349133427208💫 FARRAH💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣2️⃣ Lumshe idanunshi yayi kaman yana bacci yanaji Mami tacemata taje tai wanka itakuma Mami ta taho dakin, bude kofanta tayi tana kallon Zayn daya kwanta akan gadonta ya lumshe idanu kaman mai bacci, maida kofan tayi tarufe sanan ta cire hijabin jikinta ta linke ta ijiye ta taho gaban gadon tana kallon Zayn din barin gemun nan nashi, dan girgiza kai kawai tayi tajuya zatabar wajen hannunta Zayn yakamo dasauri hakan yasa tajuyo tace “ohh dama idonka biyu” tashi yayi yazauna ahankali yana kallonta saikawai ya rungumeta yadaura kanshi akan cikinta yace “Mami yanzu bakida lokaci na” dan murmushi kadan tayi wato har yafara kishi girgiza kai tayi tace “ai kai yanzu ka girma” ciro kanshi yayi daga cikinta yakalli fuskanta dan murmushi tayi sanan tazauna gefenshi tace “wasa nake maka, you will forever be my one and only Zayn” dan murmushi yay saiya koma ya kwanta yadaura kanshi kan cinyarta hannunta tadaura saman gashin shi dakeda taushi sosai murya chan kasa tace “I am proud of you Zayn” dasauri yakalli Mami dan Mami not common takemai magana haka Papa nedai yasaba gayamai maganganu haka, gyadamai kai tayi tace “I mean it, Baban ka yafadamin kaine kace yay adopting Farrah, all I see amaganan is growth you are becoming more and more sensible Zayn dina, Allah yamaka albarka” wani cute murmushi yasaki yadauke kai, hancinshi Mami takama tace “akama mutum addu’a Ameen yake cewa baya dauke kai ba” dan kara yayi. “Auch Mami that hurts” hararan shi tayi tasaki hancin, murya chan kasa tace “Ameen” murmushi Mami tayi murya chan kasa tace “Zayn dan Allah take care of her amana, yanzu legally she’s your sister, Allah yaga zuciyana inason Farrah sosai ina jinta kaman diyan dana haifa, she’s so innocent yarinya marainiya abin tausayi ne, Zayn nasanka nina haifeka, kaji tsoron Allah, kai yanzu babban Yayanta ne, tanada hakki akanka kaga tayi ba daidai ba correct her, kaganta da bad friends or anything dat can harm her karabata dashi, and dole you have to show her good example as an elder brother please Zayn be good, kasan sometimes ina fita for emergency surgery idan kana gida always check on her, dudda yan aiki na nanan, but kai kadubata, kasa ido alamarinta bamu kadaine agidan nan ba, wanan dasu Hajiya sunji Alhaji yay adopting yarinya which has been something da sun dade suna so yamusu amman baiyiba, rana guda sabida kace yayi yayi they might react somehow, so please don’t let any harm yazo inda take kaji Zayn, I trust you nasan duk iya rashin jinka bazaka iya cutar da karaman yarinya like Farrah ba saisa dagakai har ita zan muku kallon yaran dana haifa I will never zargeku kona muku mugun kallo ba, I can do that ko Zayn? I can trust you right Zayn”? Mani tai tambayan tana kallon kwayan idanunshi dan tafi kowa sanin danta she just want to makesure Farrah is safe tareda Zayn karyaje yaci amanarta, ahankali ya gyadama Mami kai yace “yes Mami” murmushi tayi dan taga gaskiya akan fuskanshi tace “tacemin kace monday zaka kaita school”? Gyadamata kai yayi yace “yes” murmushi tayi tana mamaki wai yau Zayn ne zai dauki responsibility wani abu batason tai magana hakan yasa tace “to shikenan” nai magana dawani ustaz zai dinga zuwa Saturday and sundays suna islamiya, dakuma lesson na school sabida tai catching up dawuri, tacemin tayi primary school na gwamnati abirnin chan garinsu da Maman su tazauna kafin su dawo kauye, she understands just little english sanan bata gama iya karatun turenci ba but she can read hausa, gyadamata kai Zayn yayi baice komiba, saikuma yatashi zaune yace “Mami lemme go and workout, ki aikomin da black coffee” murmushi tayi tace “to” .

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull