Ganin ido complete - Chapter 16
Ganin ido complete Chapter 16: Ganin ido complete Chapter 16. Bayan na yi musu sallama na gaishe su a hankali na taka naje inda take zaune tayi rashe-rashe…
3,355 words
Bayan na yi musu sallama na gaishe su a hankali na taka naje inda take zaune tayi rashe-rashe a ƙasa na ajiye mata bowl ɗin a gabanta na ce.
"Gashi in ji Haula tace na kawo miki.."
Daman tun da na shigo na nazarci fuskarta yanda ta yi wani canja lokaci ɗaya tamkar ba ita ce ke dariya ba.
Fuska a haɗe sosai ta ce mini.
"Ina ita Haulatun take?"
"Tana Kitchen za ta haɗo miki lemun da kika ce ne..."
Shiru ta yi mini ba tare da tanka ba na tsawon lokaci, wanda daga ƙarshe na miƙe don kaina da nufin tafiya amma kuma sai ta tsayar dani ba tare da ma ta kalleni ba.
Zaunawa na yi na tsawon lokaci wanda har a cikin raina sai da na ji cewar na tsargu sannan daga baya sai ga Haula ta shigo ɗauke da Smoothie wanda ko daga kallonsa kaɗai kasan zai yi taste a baki.
Tunda ta shigo take kallona ɗauke da mamaki a fuskarta har ta ajiye. Bayan ta ajiye lemun ne ta ce mini.
"Beenafah miye kike a nan tun ɗazu?"
Kallonda na jefawa Aunty Ziza shi ya tabbatar mata da cewa ba don kaina nake zaune a nan ba ita ce ta tsayar dani, sai gashi mun tsinci muryarta tana faɗin.
"Ni ce na tsayar da ita. Je ki kira Munira ku zo."
Tashi tayi cikin en wasu daƙiƙun da ba su gaza goma ba sai ga su sun dawo a tare sun durƙusa a gabanta.
"Daman bayan ku biyun nan ana barin duk wanda ya ga damar shigowa ya shigo har nan kai tsaye ban sani ba??"
Kallona suka yi dukkan su a lokaci ɗaya, domin ba su yi expecting wannan tambayar ta ta ba at all, Sannan daga ƙarshe Haula ta girgiza kanta ta ce.
"A'a."
"To miyasa kuka ba wannan yarinyar dama take shigowa? Jiya ma ba nan ba, har ɗakina ta iskoni kai tsaye ba wani neman izini ta shiga,why?"
Sai da Haula ta ƙara Kallona a karo na biyu sannan ta mayarda kallonta gareta ta ce.
"Aunty Labiba ce ta bada damar hakan, ta ce mu ɗauke ta tamkar mu babu wani banbanci, sannan kamar yanda muke da damar shigowa nan a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso itama haka za ta iya shigowa."
Wani irin taɓe baki tayi tare da jan siririn tsaki ta kalle ta tace.
" Bar mini Smoothie ɗin, amma ki wuce da Cake ɗin bana ra'ayi. Sannan kuma ku kawowa baƙina abin Ci da Sha."
Tamkar an zare mini lakka, haka na janyo ƙafafuna a matuƙar sanyaye na yo waje ina mai samun bakin dakalin kitchen na zauna yayinda lokaci ɗaya na ji wata irin kunya da baƙin ciki sun lulluɓeni. Hannun Haula na ji akan kafaɗata ta dafani, cikin sigar rarrashi ta ce mini.
"Ki yi haƙuri dan Allah! kada ki bari wannan abun ya yi tasiri a zuciyar ki, Aunty Ziza mace ce mai sauƙin kai wallahi, na rasa yau miye ya hau kanta."
Munira itama ta ce.
"Sosai wallahi,Aunty Ziza ba ta da matsala ko kaɗan, ni ina ga har da cikin nan yake sakata yin wasu abubuwan..."
Cike da jin wani irin zafi a zuciyata idona tab da ruwan hawaye na kalle su a raunane na ce.
"To amma miyasa za ta ce ba za ta ci Cake ɗin ba? Saboda ni ce na kai mata? Tana ƙyamata ko?"
"Ke Haba! Waye zai kalle ki yace kina da ƙazanta? Dan Allah ki daina ma wannan maganar ba zancen ƙyama ba ne. Duk kwanakin nan fa muma haka take mana. Ko jiya haka ta tada Haula around 11pm ta ce ta yi mata tsire, wallahi muna kitchen har kusan 1am amma da ta kai mata bata ci ko ƙwaya ɗaya ba wai ƙamshin currynda tayi amfani da shi bai yi mata ba. Haka ta fito da shi Hajiya ta ɗauka sannan muka dawo ɗakin nan muna ta mita wanda daga ƙarshe muka cinye muna dariya..."
Jinjina kai Haula tayi ta ce.
" Ƙwarai kuwa, wallahi daren jiya ta ƙular dani ba kaɗan ba, amma kuma na yi mata uzuri saboda yanayin da take ciki a yanzu. Ke ma ki yi haƙuri kar hakan ya dame ki."
Murmushi ne ya suɓuce min da na tuna cewa wai Aunty Labiba tace nima zan iya shiga duk inda nake so a gidan, hakan yasa na gyaɗa musu kaina na ce.
" Ba komai, ya wuce..."
"Yauwa. Bari na kaiwa Hajiya na ta idan zata ci, sannan in kaiwa baƙin Aunty Ziza Abincin in dawo mu cinye kayanmu...Munira ke kuma ki ɗiba ki kaiwa su Inna Kuluwa. Ke kuma ki tashi ki ɗauko mana abincinmu a kitchen kafin mu dawo."
Tashi nayi na je na ɗauko abincin na dawo na shiga toilet na yo alwala na zo na yi sallah sannan na zauna zaman jiran su. Bayan mun ci abincin mun kambala muka zauna suka yi ta firar da suka saba wanda sam na lura basa gajiya ba ma kamar Munira wacce bakinta sam baya gajiya da zuba surutu kamar wata jikar Aku.
Misalin ƙarfe biyu Haula ta miƙe tana kallon agogon ɗakin tana faɗin.
"Bari in tashi, naga ƙarfe biyu tayi,nasan yanzu za ki dame mu da faɗin gida za ki."
Ɗan murmusawa na yi kawai ban ce mata komai ba har taje ta dawo ɗauke da wata ƙaramar Bacco ta ajiye mini a gefena tana faɗin.
"Gashi.....Na saka miki komai a leda idan kinje sai ki zube, zai fi miki sauƙin ɗaɗɗakar kuular nan koda yaushe."
Miƙewa na yi na ce.
"Na gode sosai, sai anjimanku."
Tare muka fito mu uku suka rakoni, a harabar gida muka ga wani ya janyo Mota da alama fita zai yi shima. Da gudu Munira taje ta tsayar da shi tana faɗin.
"Oga Sule sai Ina?"
Ƙara yin ƙasa da glass ɗin motar ya yi ya kallemu ya ce.
"Hajiya ce ta aikeni, idan kuma zan dawo ma sai na biya Eatry ɗin Hajiya Ziza, itama zan ɗauko saƙo a can."
"Eyyah! To dan Allah ka ajiye Beenafah a titinsu dan Allah."
Kallona ya yi don ya ƙara tabbatarwa tunda already yasan Ita Munirar da kuma Haula sannan ya ce.
"Allah yasa hanya ta ce?"
"Kabi ta wurin titin su Aunty Labiba sai ka ajiyeta ko shabanke ne dan Allah, Hayin Malam Ibrahim za ta je."
Shiru ya yi yana ɗan nazari sannan daga ƙarshe ya ce in shiga.
Ɗan waro ido na yi ina mai ƙirƙirar wani murmushin dole na ce.
"Ai da ma kun barshi, zan iya tafiya da ƙafat.."
Hannuna Munira ta ja tana faɗin.
"Dan Allah shiga malama. Waye baya son sauƙi a rayuwa? Sai ki yi ta wani ɗari-ɗari. Oga Sule ba shi da wata matsala shi ne drivern Hajiya."
Daga haka ta buɗe gaban motar ta turani ta rufe ya ja muka fito. Muna isowa bakin gate bayan ya fito sai gashi mun yi ido biyu da Ya Jafaru,daman shi kuma Oga Sulen ya tsaya yin magana da mutanen da ke zaune bakin gate ɗin. Kallon shi na yi na ce.
" Yi haƙuri dan Allah ga Yayana nan ya zo zamu tafi a tare."
Waigowa ya yi ya ce.
"To ba damuwa, Allah ya tsare hanya."
A hankali na buɗe motar na fito na tako zuwa inda yake tsaye. Ganin na yi ya wani haɗe rai yace mini.
"Waye kuma wannan Beenafah?"
Ya ƙarashe maganar yana mai bin Oga Sule da kallo wanda ni ma ɗin shi na kalla sannan na waigo na ce.
"A nan gidan yake, hanya aka ce ya rage mini."
Cikin nuna jin haushi ya ce.
"Kamar ya ya rage miki hanya? Bayan kin san dai dole zan zo na raka ki...."
"To amma Ya Jafaru ai da ma ka daina wahalar da kanka, domin yanzu na san hanya, ko ɗa zu da kaina na zo a ƙafa..."
"Au! Haka ma za ki ce wato?"
"To ya zan ce maka? Daman ai don ban san hanya ba ne, yanxu kuwa tun da na gane ba sai ka ci gaba da wahalar da kanka ba.....Naga sai wani ɓata rai kake, miye aka maka?"
"Mts! Ba komai. Muje.."
Ya ƙarashe maganar yana mai karɓa Baccon hannuna.
Sai da mukayi nisa sosai ba tare da kowa ya sake magana ba, wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya bani ba,domin muddin muna tare da shi to fa bakinsa baya taɓa yin shiru. Amma yau sai gashi yayi shiru kamar ba shi ba. Sai da muka kusa kai gida sannan ya kalleni ya ce.
"Ki daina saurin yarda da mutane Beenafah, musamman irin waɗannan."
Gyaɗa masa kaina na yi na ce.
"In sha Allah zan kiyaye."
"Sannan kuma na zo miki da wani albishir...."
Tun kafin ya iyarda rufe bakinsa na washe haƙorana na ce.
"Masha Allah Ya Jafaru, miye wannan?"
"Na samu Admission a ABU Zaria...sannan kuma babban abin farin cikin shi ne; course ɗinda na fara ne na samu gurbi da shi."
Cikin nuna zallar farin cikina na ce.
"Kai Masha Allahu! Gaskiya na ji daɗi kuwa, Allah yasa alheri da albarka ya bada sa'a."
"Amin. Kin san course ɗin kuwa?"
Girgiza kaina na yi na ce.
"Ni ina zan sani Ya Jafaru idan ba faɗa mini kayi ba."
"Karatun zama Lauya zan yi..."
"Wayyo Allah Ya Jafaru! kamar dai, irin na Aunty Labiba kenan? Na san itama Barrister ce.."
Fuska cike da annuri ya ce.
"Ƙwarai kuwa..."
"Kai masha Allah. Amma fa Ya Jafaru karatun nan kamar ana kashe kuɗi sosai?"
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Eh, akwai kashe kuɗi, amma daman akwai Wan Mamanmu Kawu Usman, shi ne wanda ya biya mini lokacinda na yi diploma ta a nan Zacas, to yanzu ma shi ne ya nemo mini wannan admission ɗin kuma shi zai ci gaba da ɗaukar nauyin komai har na kambala kamar yanda yayi mini a baya in sha Allahu."
Bansan lokacin da wasu zafafan hawaye suka wanke mini fuskata ba. Kallon shi nake tamkar zan kifa na ce.
" Yayan Mama?"
" Eh. Shi ne babba a gidan su, daga shi sai ita,mutumin kirki ne duk yaran en uwansa da ba su da ƙarfi matuƙar dai suna son karatu shi ne yake ɗaukar nauyinsu, hatta su Farisa da kika gani idan term ya yi yana turo wani abu yace a haɗa a musu registeration."
Jinjina kaina na yi ina share hawayena na ce.
" Kenan dangin Uwa idan kana da su suke taimako?"
Girgiza kai yayi ya ce.
" A'a Beenafah. Kowa yana da haƙƙin taimakawa danginsa, walau dangin uwa ko na uba, kawai ya danganta daga hali da kuma zuciya mai kyau. Itama Mama Ko cikin dangin na ta ai akwai masu hali da yawa amma Kawu Usman shi ne kaɗai mai zuciyar taimakawa..."
Hawaye na gudana sosai akan fuskata na ce.
"Duk da haka Ya Jafaru, na san tabbas da muna da su muma da ko yayana ba za su juya mana baya ba kamar yanda Daddy ya mana..."
"To sun yi muku nisan da ba za ku iya zuwa inda suke ba ne?"
Girgiza kai na nayi ina mai jin wani sabon nauyin a ƙirjina na ce.
"Bansan ya zance maka ba Ya Jafaru...Mahaukaci shi ne mahaifinta kamar yanda ta faɗa mini, shi ne ya raineta tare da wasu mutane wanda bayan rasuwar sa suma ta neme su ta rasa. A duk lokacinda ta ce mini na daina wahalar da kaina wurin nema mata magani domin Hauka gado tayi.... sai in ji tamkar na haɗiye zuciyata na mutu....Bamu da dangin mahaifiya,babu wani wanda zamu kira namu a gefen mahaifiyarmu...dangin Uba kuma; Daddy ne kawai kuma ya yafe mu...."
A hankali kukan da nake riƙewa ya kubce jin wani abu da ya taso ya motsa ciwon da yake kwance a cikin akwatin sirri na ba tare da na shirya ba.
Murya kamar zai yi kuka ya ce.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Lallai kina da babban Ciwo a zuciyar ki. Haƙiƙa, na ji matuƙar takaici da baƙin cikin da ba zan iya rungumeki a ƙirjina na rarrashi zuciyar ki ba Beenafah, da ace zan iya da na yi domin na nuna miki irin matsayi da girman da kike da shi a zuciyata. Ki yi haƙuri ki share hawayenki, duk inda kuke Allah yana sane daku, kuma ko Daddy bai taimaka muku ba, akwai mutane da dama waɗanda tarayyarku ta domin Allah da su ba za ta bari ku tagayyara ba...."
Ni dai har muka ƙarasa ƙofar gida ban sake ce masa kanzil ba, domin firar da muka yi tayi matuƙar sosa mini zuciyata da turani cikin mummunan yanayin da na jima ban shige sa ba.
A nan ƙofar gida na karɓi kayana, bayan na gama sai ta kaina, a hankali nayi sallama na shiga gidan.
Koda na shiga na tarar da Bahrain ya dawo daga makaranta yana kwance saman varender da alama zafi yake ji tunda ya kwaso rana.
"Oyoyo Aunty Beena ta..."
"Bahrain ka dawo?"
"Eh na dawo yanzu, sannu da zuwa."
"Yauwa, Ina Ammie?"
"Ta shiga gidan Maman Fakiha."
"ok."
Na faɗa ina mai samun wuri na zauna tare da haɗa kaina da gwiwa na ci gaba da tunanin rayuwa...
"Aunty Beenafah an ce yau kowa ya tabbata ya kawo kuɗin Hadisin sa fa, Malam yusuf yace idan baka zo da kuɗin ba ba zai barka ka shiga ajinsa ba..."
Ɗagowa na yi a hankali na ce.
"Nawa ne kuɗin?"
"Ɗari biyar da hamsin."
"Ok, zan baka idan za ka tafi. Ka ci abinci?"
Girgiza kansa ya yi ya ce.
"A'a, Ammie nake jira."
"Tashi ka ɗauko mini wuri na juye abincin sai na zuba maka."
Tashi ya yi ya ɗauko na juye, ledoji ne da yawa, wanda har abincin safe akwai da aka rage, abincin rana ma ta zuba mini daban, sannan har da Cake ɗinda mukayi sai da ta sako mini da wasu lemukan kwalba."
Da sauri ya tashi ya zuge jakar makarantar sa ya ɗauko empty roba ta Rufaida Yoghurt yaje ya ɗaurayeta ya kawo gabana ya ajiye cike da farin ciki ya ce.
" Aunty Beenafah zuba mini Irish da ƙwai ɗin a nan in tafi da shi islamiyya..."
Zuruuu! Na yi ina kallon sa har ya dasa aya sannan na ce.
"Ina ka samo wannan robar?"
Kallon robar da ya ajiye a gabana ya yi sannan ya kalleni ya ce.
"Su Ramadan suka zo da ita a ciki muka sha."
"To amma miyasa ka ɗauko ta? Bance maka ka daina tsinto tarkace kana zuwa da su gidannan ba? Duk abin da ake baka daga gidanku baka gode ba? Kana fa ganin don kada ka gani ga wasu yaran muke haƙura da wasu abubuwa mu yo maka siyayya, amma kai baka gani ko... "
Sunne kai ya yi a ƙasa a hankali cikin taushi ya ce.
" Ina gani Aunty Beena, ki yi haƙuri.."
Jinjina kaina na yi na ce.
" Ya kamata ka gane cewa kai yanxu ba ɗan ƙaramin yaro bane, nan gaba kaɗan ba jimawa zaka shiga secondary, ka riƙa abubuwa na masu hankali bana son rashin dangana...Kaga waɗannan yatsun nawa?"
Na ƙarashe maganar ina mai ɗaga masa yatsun hannuna na buɗe su na ci gaba da cewa.
" Ka kalle su ka gani,...kai ma kuma ka kalli naka Bahrain...hatta yatsun hannunmu ba tsayin su ɗaya da juna ba, to kamar haka ne, dole a makarantar ku sai ka samu wanda zai zo da abinda baka da shi kamar yanda kai ma kake zuwa da abinda wani bashi da shi. Saboda haka ka riƙa tsayawa ga abinda kake da shi ka dai na sanya ido ga abin wani, kada ka sake ɗauko ko murfin gora ne ka zo da shi gidannan bana so..."
Jinjin kansa ya yi jiki sanyaye yace.
" In sha Allahu ba zan sake ba ki yi haƙuri. "
" Ba komai, tashi ka yi sauri kaci abincin lokaci ya tafi."
Bai yi nisa a cin abincin ba Ammie ta yi sallama ta. Bayan na gaisheta ta miƙo mini dubu uku tana faɗin.
"Kinga Kuɗi Maman Abul ta zo ɗa zu ta kawo su wai dan Allah ki yi haƙuri idan ma wani laifi ta yi miki kiyi haƙuri, idan ma kuɗin ne kuma ya yi miki kaɗan ga dubu ɗaya ta ƙara miki a sama.."
Dariya na yi ina mamakin wautar Maman Abul na ce.
"Allah sarki! Wai ita a yanda ta tsammaci abun kenan?..."
Itama Ammie dai dariyar ta yi sannan ta ce.
"Haka fa ta yi ta roƙona na ce mata ba abinda ta yi miki tsohon gidan aikinki dai kika koma."
"To kam a mayar mata da kuɗinta."
"Babu yanda ban yi da ita ba akan ta karɓi kuɗinta amma ta rantse tace ba za ta karɓa ba, kuma ko ba za ki dawo ba ita kyauta ta baki."
"To,an gode Allah ya saka mata da alheri...bari na tashi na wanke kayan Bahrain don in samu su bushe da wuri. Ga abinci nan, amma kam yayi mana yawa sai dai a rage a kaiwa su Farisa..."
"Hmm! Yanzun nan Jafaru ya gama faɗin a ajiye masa abinci yana nan zuwa idan ya dawo zai ci. Shi ma kuma Hamza kin sani a nan zai ci, saboda haka ki rufe ki ajiye."
Bayan na kambala sallar Magrib, Bahrain na dawowa daga masallaci na karɓi kuɗin hannun Ammie na ce mata wani magani zan siyo kawai na ja shi muka je can Landmark na siyo Rufaida guda biyu da wani ƙaramin Ice-cream na dubu ɗaya da ɗari biyar wanda ba don kowa na yi hakan ba sai don shi.
Ammie za ta buɗe baki ta yi magana, na ce mata dan Allah kada ta ce komai, farin cikin Bahrain shi ne farin cikina.
****
Daddy Mudassir..., akwai wani babban abokin shi, Alhaji Mansur Anka wanda yake da 'ya'ya Maza en biyu kamar yanda Daddy yake da su. Kullum roƙonshi guda a wurin Daddy shi ne; Ya amince da su haɗa auren Yaran na su sai abin ya yi armashi. Kullum akan wannan maganar yake wanda sai yau ya samu haƙarsa ta cim ma ruwa, domin sun samu daidaito da shi da Daddy akan yaran za su zo suga juna, idan Allah yasa sun shirya kan su shikenan, amma kuma auren sai sun kambala karatunsu da suke yanzu nan da shekara biyu cikin ta uku. To shi ne bayan ya dawo ya zaunar da Mummy da Aunty Aysha ya yi musu bayani,to shi ne Mummy ta ce ya bata kwana biyu har ta yi shawara, to a cikin kwana biyun ne ta kira Uncle Isma'il ta ce tana so yaje garin Anka ya binciko mata tushen Alhaji Mansur, daga nan ya dawo cikin Gusau ya binciko mata rayuwar shi da ta 'ƴaƴanshi sannan a wanne mataki suke na rayuwa.
Da yake Uncle Isma'il ɗin ba na wasa bane, take ya cika mata aiki,wanda Daddy na dawowa kamar yan da ya saba bayan sun gama dinner ta hau yi musu bayani.
"Amm! Kamar yanda mukayi da kai Alhaji, zancen yarannan na ce sai na yi shawara, to na amince Yaran su zo su nemesu, idan sun amince fine, idan kuma ba su amince ba to tabbas babu wanda zai musu dole.."
Jinjina kai Daddy ya yi ya ce.
"To ai nima hakan ita ce matsaya ta, kuma ba za'a yi auren ba sai bayan sun kambala karatun su..."
Cike da mamaki Hassana ta kalli Daddy ta ce.
"Auren waye Daddy?"
"Aurenku ke da er uwarki..."
"Amma daddy dan Allah yaushe rabon da irin wannan auren..."
Hannu Mummy ta ɗaga mata sannan ta ce.
"Ya isa! Ai ya kamata ki jira kiji kafin ki yi saurin yanke hukunci. Alhaji Mansur Anka na san kun san shi, to akwai yaran shi maza waɗanda suma twins ne su biyu, shi ne yake neman alfarma da a haɗa ku aure. Ma su kuɗi ne sosai kamarmu kada ku damu, kuma suna da aikin yin su, wanda suma a waje suke zama da kasuwancin su kamar Mijin Aysha. Amma kuma duk da haka, babu wanda zai muku dole, za su zo in sha Allahu kuga juna, idan kun shirya shi kenan ayi, idan kuma baku shirya ba dole a fasa."