Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 17

Ganin ido complete - Chapter 17

Ganin ido complete Chapter 17: Ganin ido complete Chapter 17. Miƙewa Hassana ta yi ta shige ciki kawai ba tare da ta yiwa kowa magana ba, yayin da kuma…

3,358 words

Miƙewa Hassana ta yi ta shige ciki kawai ba tare da ta yiwa kowa magana ba, yayin da kuma Husaina ta yi murmushi ta ce.

"Ba komai Mummy, Allah ya nuna mana."

Jinjina kai Mummy tayi ta ce.

"Amin."

Miƙewa Aysha ta yi tana faɗin.

"To! Mudai kaya kai takalmi hannu, koda bayan mun tafi ne duk abin da aka yanke daga baya zamu ji, Allah ya sanya alheri da albarka ya ba su fahimtar juna..."

Kallonta Mummy ta yi ta ce.

"Shin wai yaushe ne tafiyar ta ku?"

"Next week Friday ya ce mini."

"Tau ya yi, Allah ya kaimu."

Hannu Daddy ya miƙawa Baffa yana faɗin.

"Zo nan Alhajina.... Gobe ya kamata mu fita tare tunda dai za ka gudu ƙasar aro ka barni nan a Nigeria."

Ciki Ayshar ta shige ita da Husaina suka bar Mummy nan ita da Daddy suna ci gaba da tattaunawa.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *ArewaPen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 19*

"Hussy! Yanzu shi ke nan duk tsawon shekara da na share ga shi har zan koma ba zan sanya su Ammie a idona na ba?....da gaske shi ke nan su Daddy sun bar su a can? Anya Hussy Daddy da Mummy sun yi tunani mai kyau kuwa?"

Lokaci ɗaya Husaina ta ji hawaye sun cicciko idanuwanta tana mai girgiza kanta ta ce.

"Haka muka baro su yashe a tsakar gida Aunty Aysha. I don't know where they are.....Har na mutu ba zan manta irin rabuwar da na yi dasu ba. They need help Aunty Aysha, but... Haka na baro su ba tare da sanin wata makama b...."

Tsit! Suka yi a ɗakin lokaci ɗaya tamkar ruwa sun cinyensu ganin Hassana ta shigo.

Ɗan wawwara idanuwa ta yi ta kalle su sannan ta ce.

" Why are you mute?.... And dukkan ku you guys looked worried. What's happening?"

Ajiyar zuciya Husaina ta sauke tana mai lumshe idanunta ta buɗe tana kallonta ta ce.

"Aunty Aysha is leaving tomorrow, and she's afraid kada ki ƙi saurarar wanda su Daddy suka zaɓa miki..."

Wayarta ta ajiye a saman haɗaɗɗen gadonta tana mai taɓe baki ta kalli Aunty Ayshar ta ce.

"A gaskiya Aunty Aysha su Mummy ba su so gaskiya ba, yanzu ke da za ki Auri Ya Ahlan haɗa ku akayi? Ba haɗaku akayi ba, shi ne ya ganki can yace yana sonki babu wanda ya haɗaku. Kuma wallahi bet me Aunty Aysha, da ace haɗaku akayi da Ya Ahlan da yanzu bakwa zaune lafiya, wata ƙila ma da bakuyi aure ba. Sannan yanzu da ma cewa akayi yaje ta ƙarƙashin ƙasa ya nemi aurena wata ƙila idan akwai rabo zamu iya shirya kanmu... "

Murmushi Aunty Aysha ta yi ta ce.

" Wannan ɓaragurbin tunani ne Hassy, sam bai kamata ba. A al'amari irin wannan da ake so a ƙulla alheri ya kamata ki riƙa kyautata za to. Ki bashi dama ku haɗu, ki buɗe zuciyarki ki daure ki bashi matsuguni koda kaɗan ne.."

"Tau ya yi Aunty Aysha, I will try in gani Ko zan iya."

Miƙewa Aunty Ayshar ta yi ta shige wurin wanka ta bar su nan kowace riƙe da waya a hannunta suna danne-danne.

****

A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiyar mini a gidan Hajiya Batula Attahiru Araam. Tun da wuri nake isowa nayi aikina na kambala sannan mu dawo ɗakinmu zaman kashe wando, su yi ta fira suna dariya wanda babu abinda yake ɗaga su sai idan an kira su da sunan wani uzuri. Gida ne mai cikakken 'ƴan ci da walwalar duk wata halitta dake rayuwa a gidan. Idan naga irin abin da su Munira suke yi a gidan ina shan mamaki domin duk yanda nake ganin 'ƴan cin gidan Aunty Labiba to wannan gidan ya fishi 'ƴan ci nesa ba kusa ba, sai dai kuma; abin da na lura da shi shi ne, suna da matuƙar tarbiyya da kiyayewa, domin wurin maza daban wurin mata daban, babu wanda yake zuwa wurin wani idan ba da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba. Duk bayan kwana biyu kwana uku, Haula ta kan je kasuwar tudun wada ita da driver ta amso duk wasu kayan buƙata na cefanen gidan. Itama Munira duk wani aikin da za'a yi wurare da dama ita ake aiki amma kuma babu wanda yake fita ba tare da driver ba. Wani lokacin mu tafi tare da su, wani lokacin kuma su tafi abin su.

Su Munira duk da cewa suma ɗin ba sa'annina ba ne,amma ba su damu da ƙarantata ba, domin sun fi sakin jiki dani fiye da Aunty Hajjo.

Farkon zuwana gidan ina ganin cewa ai ba wani dogon aiki suke ba, sai da na shigo sati na uku a gidan sannan na fara ganin ayyuka tamkar za su yi ajalinsu, musamman dafe-dafen abinci da kuma saukar baƙi kamar ana wani buki kullum haka gidan yake. A nan na gasgata zancen Aunty Labiba da ta ce gidan su gidan mutane ne. Ko en uwan su kawai da suke yawan zuwa sun isheka ciwon kai.

Aunty Ziza kuwa, duk yanda suka so na sake da ita na kasa, kamar yanda itama kullum abubuwanta a kaina ƙara tsananta suke a duk lokacin da zamuyi ido biyu wanda ban san dalili ba.

Yau ma ina cikin goge-goge a parlour kamar yanda na saba sai na ji an zo da gudu an rungumeni gam wanda ba shiri na juyo muka haɗa ido da Adeel.

Tamkar wata sauna, haka na rungume shi gam a jikina yayinda idanuwana suka cika da ruwa hawaye.

"I miss you Aunty Beenafah."

Janyewa na yi ina mai kallon fuskar sa na ce.

"Nima nayi kewarku Adeel.... Ina Hanan?"

"Hanan tana can ɗakin Aunty Hairiyyah tana kuka..."

"Subhanallah! Miye ya same ta?"

Dariya ya fara a hankali ya ce.

"Ni na yi mata Ƙarya na ce mata Aunty Hairi ta dawo, shi ne taje ɗakin wai nemanta take, da bata ganta ba shi ne take kuka....Zo.. Zo muje ki ganta Aunty Beenafah."

Hannuna ya ja muka fito daga parlourn muka ratso wata hanya duk cikin ruffing ɗin muka shige cikin wani katafaren kyakkyawan ɗaki mai ɗauke da kayayyakin burgewa, ga manyan tidy bears nan jejjere, frames ma gasu nan da na real hoto dana zane gwanin burgewa.

Sautin muryarsa, ita ta dawo dani daga duniyar kalle-kallen da na lula ya ce.

" Kin ganta ko Aunty Beenafah?..ji bakinta na kuka..."

Da gudu na yi kanta tare da janyo ta jikina na ce.

"Ke...yi shiru my Hanan ƙyale shi sai na yi mishi duka. Buɗe idonki ki gani ga Aunty Beenafah.."

Shiru tayi lokaci ɗaya tana mai haɗiye kukan ta tare da waro idonta ta kalleni da kyau sannan daga baya, bayan ta fahimci ni ce sai ta wani ƙanƙameni tana dariya. Nima cike da farin cikin ganin su na rungumeta na ɗan lokaci, sannan daga ƙarshe na miƙe da nufin jan hannunta amma sai ta maƙale kafaɗa cike da shagwaɓa ta ce.

"Ni ki goyani.."

Dariya na yi na ce.

"Yanzu kuwa."

Hijabina na cire na goyata tsab, abin da ba za ta samu ba kenan a wurin Hajjo sai dai ni da ta raina, idan tana jin sangartarta. Parlour muka dawo na ci gaba da aikina Adeel na aikinsa na ciwon surutu wanda duk labarin akan abin da ya wuce ne na makarantar sa, islamiyya da boko. Yayin da Hanan ta wani lefe kamar mai bacci.

"To ina Aunty Hajjo?"

Na tambaye shi ina mai ci gaba da abin da nake.

"Aunty Hajjo tana nan, yanzu da ƙanwarta take zuwa suna yin aiki tare..."

"Ke!...Miye haka?"

Cike da jin mummunar faɗuwar gaba na juyo domin in ga wane ne, sannan da wa yake magana. Sai gashi cikin rashin sa'a mukayi ido biyu da shi yana tsaye yana kallona. Cikin rashin sanin abin da na yi kawai na yi shiru tare da kawar da kaina gefe na ce.

"Ina kwana."

"Ba ta da lafiya ne? Da za ki wani ɗora ta a baya haka.."

Sai yanzu na fahimci zancen sa, ai kuwa within seconds na dire ta ƙasa ina faɗin.

"Lafiya ƙalau take..."

"Mts! Yanzu yarinya kamar wannan kike ɗorawa a baya salon kawai ki koya mata rayuwar lalaci..."

"Uncle Emraan ita ce fa ta ce ta goyata.."

Cewar Adeel yana mai nufar inda yake tsaye tare da Hanan ɗin. Wuri ya samu ya zauna ba tare da ya amsa ba. Saman jikin shi Hanan ta haye yayin da Adeel ya zauna a gefen sa tare da riƙo hannun sa ya ce.

"Uncle Emraan wannan ita ce fa Aunty Beenafah, wadda ranar koda ka zo gidanmu har ta riga ta tafi."

"Ok..."

"Kuma ta iya karatu, ita take taimaka mini idan an bani homework..."

Da ido Uncle Emraan ɗin ya bishi sannan daga ƙarshe ya ce.

"Adeel, ta shi su Aunty Dija sun kira suna so su yi magana da kai."

Duk da cewa bana kallon su, murmushi ne ya suɓuce mini domin nasan ya gaji da halin Adeel wanda ni a karan kaina duk na tuno da shi sai naji ina jin kewar sa.

Ji na yi ba zan iya ci gaba da aikinda nake ba, domin zaman sa a parlourn ba ƙaramin takurani ya yi ba,duk da cewa ban san zaman da yake ba. Ga shi itama Munira kamar wani haɗin baki daga zuwa kunna turare ɗakin Hajiya shikenan ba ta dawo ba.

Har na kusa kai ƙofa na sake jin maganar sa a masarrafar saurarona da cewa.

"Ke!"

Juyowa na yi zuciyata na wani irin pumping a ɗan tsorace na ce.

"Na'am."

"Kawo min lemu."

Juyawa na yi na fita na shige babban kitchen ɗin inda freezer take. Tsoro ne ya kamani domin ban taɓa zuwa inda take ba da sunan amfani. Hakan yasa na wuce cikin store inda kwalayen lemuka suke na zaro ƙwaya ɗaya na fito na zo na tsaya a gefen sa na ce masa.

"Ga shi..."

A hankali ya ɗago kansa daga kallon wayar da yake ya kalloni... Sai dai kuma;lokaci ɗaya fuskar sa ta yi wani irin sauya wa tare da nuna zallar ɓacin rai ya ce.

"Miye haka? A gidanku haka aka koya miki yanda ake bada lemu... Infact a ina kika ɗauko shi?"

Kallon lemun na ƙarayi da kyau sannan na kalle shi na ce.

"Daga Store..."

Lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe cike da rigima ya daka mini wata uwar tsawar da sai da na ja baya ba shiri da cewa.

"Mts! Get out from here...."

Jikina na rawa na ce.

"Dan Allah ka yi haƙuri.."

"Leave I said!! Stupid girl kawai... Mts!"

Fitowa na yi da gudu riƙe kuma da lemun a hannuna na yo wurin da su Munira suke wanda hankali tashe kowa ya shiga tambayata lafiya, har Munira na faɗin.

"Aunty Ziza ce Beenafah?"

Da sauri na girgiza kaina ina share hawayena da tafin hannuna na ce.

"Wannan Mijin na ta ne yace in kawo masa lemu,shi ne naje na ɗauko kuma sai ya fara mini ihu.."

Kafin na iyarda rufe baki har Haula ta karɓe lemun da yake hannuna ta taɓa shi, tuni ta wani zare ido tana faɗin.

"Na shiga uku! Wannan ai ba'a fridge ba ne... Ina kika ɗauko?"

Ina mai tsatstsareta da ido na ce.

"A Store ne..."

"To a can kika baro masa abin da kika ɗaura lemun akai?"

Girgiza kaina na yi na ce.

"A'a, a haka na kai masa."

Dariya suka fashe da ita wanda har sai da naji na tsargu na ce.

"Miye abin dariya a nan?"

Tsahirtawa Munira ta yi domin bani amsa ta ce.

"Wai Ya Emraan ɗin za ki kaiwa abu a hannu? To bari in faɗa miki, ko Aunty Ziza ta kai mishi abu haka a hannu ƙarshe kenan, wallahi ba zai karɓa ba, kuma ki ma gode Allah bai faffallo miki mari ba.... Imagine! Lemu a store ba'a fridge ba, mutuminda ko sanyin me za'a yi sai ya sha abu mai sanyi...."

" Ai ban iya buɗe fridge ɗin ba."

"To amma ai akwai wani ta hanyar fitowa, sannan akwai shi a ɗayan parlourn..."

Hannuna Haula taja muka koma kitchen ɗin ta nuna mini yanda zan buɗe fridge ɗin ta ɗauko wasu kalolin drinks sun kai uku, sannan ta ɗauko wani silver tray mai kyaun gaske ta ɗora akai, ta ɗauko glass cup guda biyu ta ɗora ta ajiye a gefe, sannan ta sake haɗa wasu lemukan a kan wani babban tray daban da cups sai ta kalleni ta ce.

"a duk lokacin da akace ki kawo Lemu ko ruwa, to haka zaki yi, kuma sai ki kwatanta da yawan mutanen, don kada yayi yawa ko kuma yayi kaɗan. Ni zan kai wannan a parlourn baƙi, ke kuma ki ɗauka ki kai masa wannan.."

Bansan lokacin da hawaye suka cicciko idona ba, cike da shakku na ce.

"Dan Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan iya kai masa ba.."

Cikin nuna alamun mamaki ta ce.

"Saboda me to? Ya Emraan ba shi da matsala Beenafah, ke ce kika ɓata masa rai. ki daina jin tsoron mutane, idan ba haka ba duk wanda ya kwaso sharar sa wallahi akan ki zai zube ta. Musamman yaran danginsun nan masu zuwa, wallahi ba su da kunya, a gidannan an daraja mu amma su idan suka zo wulaƙanci kala-kala. Kwana biyu don hajiya tayi tafiya ne suka daina zuwa, amma yanzu tunda ta dawo zaki riƙa ganin su kodayaushe, to idan baki ƙwarara kanki ba haka kowa zai rainaki wanda kullum kwanan duniya kika zo sai kin yi kuka. Ki daina kuka, ko abu kika yi ba daidai ba kice kawai mutum ya yi haƙuri amma ki daina kuka. Ɗauki ki kai masa please, idan ya sake miki faɗa ki ce ya yi haƙuri..."

A hankali na ɗauko na dawo parlourn na shigo ɗauke da wata sallamar a bakina, wata irin sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin shi tare da Aunty Labiba suna zaune. Sai da na dire trayn a gabansa sannan na kalli Aunty Labiba na ce.

" Aunty Sannu da zuwa."

Murmushi ta yi tana mai jinjina kai ta ce mini.

"Yauwa Beenafah sannu. Ya kike? Ina fata ba wata damuwa?"

Jinjina kaina na yi ina mai ƙara yin ƙasa da idona kawai ba tare da nayi magana ba.

"Kin yi shiru baki ce komai ba, kuma naga idon ki yayi kamar kin yi kuka, miye ya faru?"

Lemun ya ɗauka ya tsiyaya ya kalleni sannan ya komar da kallon sa ga Aunty Labiba hankalinsa kwance ya ce.

"Na yi mamaki da kika ce wannan matar tawa ta yi zama gidanki amma kuma ba ta iya bada lemu ba.."

"Ka yi haƙuri.."

Na faɗa ina mai ƙara sadda kaina ƙasa sosai.

Muryar Aunty Labiba na ji ta kira sunana.

Ɗagowa na yi na kalle ta ba tare da nace komai ba, ta ce mini.

"Ta shi kije abin ki kinji ko."

Tashi na yi na wuce ɗakinmu direct na kwanta akan katifa ni kaɗai ina kuka har bacci ya ɗauke ni ban sani ba.

Labiba kuwa, Kallon Emraan ta yi wanda ke shan lemun sa hankali kwance ta ce.

"Emraan! Please idan ma kana takura yarinyar nan ne dan Allah ka daina...ko ranar da kace na kawo maka matar aure,I take that as a joke kamar yanda ka saba wani lokacin, but repeating ɗinsa da kayi yanzu na sake kiranta matarka, I don't like it,hakan kuskure ne...."

Ajiye aikinda yake a wayar ya yi ya watsa idanunsa a kanta ba tare da ya ce komai ba. Ita kuma ganin yanda yake mata wani kallon mai nuni da yana buƙatar ƙarin haske yasa ta jinjina masa kanta ta ce.

" Yeah, I'm serious Emraan. Idan kana faɗin haka duk da cewa wasa kake, Ziza won't be happy, and za ka sa Ita yarinyar ta riƙa takura tana shigewa gashi a duk lokacinda ta ganka,and bana so hakan ta faru, I want her to feel at home Kamar yan da su Munira suke."

"OK."

Kalmar da ya furta kenan tare da kauda idanunsa ya ɗauki wayarsa ya ci gaba da abin da yake.

"When are you people leaving?"

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.

"I think in the next two weeks haka...because sai na je Kwara State na dawo wurin wani aiki."

"Ok...Allah ya tsare ya bada sa'a."

"Nadee ta matsa akan za ta zo, na ce ta bar shi har mu dawo ta ce a'a, please talk to her, Ko don karatun su Dija.."

"Mun yi magana a ɗazu, na ce mata ko ni ba zan tafi ba, saboda haka ta bari sai idan Allah ya sauketa."

Miƙewa ta yi tana faɗin.

"Bari na tashi mu tafi, yau kasan ƙurarren lokaci ne kuma ina so muje gidan Hajiyarsu Babansu. Yau kacokam na kashe musu school.."

Sai yanzu ya ɗago ya kalle ta yace.

"To akan me?"

"Sun matsa suna so suga Beenafah, and can gidansu Babansu kuma ana kawo lefen Lailah."

Murmushi ya yi ya ce.

"Lailar da kuka hana a bani ita ko? Saboda kunga bani da kuɗi..."

Dariya ta fashe da ita tace.

"Auntynka Hajiya Marwanatu dai ta san yanda tayi har ta hana a baka ita ni ba ruwana. Kuma ma ai muddin kaga ana so ayi aure ya zo bai faru ba to Allah ya riga ya rubuta tun can babu zanen ƙaddarar aure a tsakanin su mutum biyu ɗin."

"To Allah yasa alheri, zuwa dare dai idan kin dawo zan shigo, domin gobe zan wuce."

"OK, sai ka zo."

*****

Tagwaye masu kama da juna tamkar an tsaga kara, waɗanda ake kira (Identical Twins or Monozygotic) suna fitowa ne daga ƙwai ɗaya na ƙwayar halittar mahaifiya (single Ovum) da kuma ƙwai ɗaya na ƙwayar halittar mahaifi (Single sperm). Bayan an samu ciki, a lokacin haɗin halittar ɗan Adam, idan waɗannan Eggs ɗin guda biyu suka haɗu da juna, maimakon samun ɗa ɗaya da ake yi walau ɗa namiji ko ɗiya mace kamar yanda aka saba, sai a samu ya rabu gida biyu maimakon gida ɗaya a farkon ciki, sai su zamo yara guda biyu wanda komai na su zai kasance iri ɗaya saboda sun fito daga ƙwayar halitta guda, shiyasa suke da DNA ɗaya, genetic material ɗaya, hatta placenta ma ɗaya (Uwa), hakan yasa suke matuƙar kama sosai tamkar an tsaga kara, ko kuma kamar ka samu lemu ne na fata ko kuma Kankana ka raba gida biyu, komai zai kasance iri ɗaya, shiyasa ake shan wahala wurin bambanta su idan ba shaƙiƙansu ba. Sannan su identical twins yana da matuƙar wahala a samu jinsi biyu a ciki,misali; basa zuwa a namiji da mace, 99% ɗin su, ko dai su zo a maza guda biyu ko kuma su zo a mata guda biyu masu matuƙar kama da juna.

Tagwaye waɗanda ba su kama da juna kuma waɗanda ake kira (Non-identical twins or Dizygotic) su tun a farkon samun cikin, Ƙwai biyu ake samu daga ƙwayar halittar mahaifiya (Two Ovum) sannan ƙwai biyu daga ƙwayar halittar mahaifi (Two Sperm). A lokacin halittar ciki, lokaci ɗaya suke zuwa gida biyu-biyu daga kowane ɓangare, sai a samu a yi fertilizing two eggs ɗin by different sperms cell. Ta dalilin hakan ne yasa ake samun tagwaye waɗanda ba su kama da juna sam, idan ka gansu akace maka tagwaye ne zaka gardama saboda komai na su ya bambanta, domin kowa yana da DNA ɗin shi daban, Genetic material ma daban, Sannan placenta ma biyu kowa da na shi (Uwa), sannan a na iya samun su jinsi biyu, na miji da mace, ko kuma maza biyu,ko kuma mata biyu, sannan za'a iya samun su wani fari wani kuma baƙi, ko kuma dukkan su su zama baƙaƙe ko kuma dukkan su su zama farare saɓanin identical da suke zuwa da kala ɗaya, Haka; yanayin murya, magana, tafiya, girma sai ka ga sun bambanta da juna.

Da wannan dalilin ne mafi yawan iyaye masu Identical twins waɗanda ke kama da juna suke kwaɗayi da burin aurawa yaran su twins ɗin masu kama da su domin ƙara ƙarfafa su da kuma ganin sai abin yafi tafiya a tsari da burgewa.

Tagwayen gidan Alhaji Mansur Anka identical twins ne masu kama da juna kamar yanda su Hassana suke kama da juna.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull