Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 21

Ganin ido complete - Chapter 21

Ganin ido complete Chapter 21: Ganin ido complete Chapter 21. "Biba....kina nufin Yarinyar Inna Ramatu?"

3,372 words

"Biba....kina nufin Yarinyar Inna Ramatu?"

"Eh, ita fa. Wai ita ce ta kawo mata ita."

Jinjina kai ya yi sannan ya kalle ta ya ce.

"Ki koma Aminiya, ina da wasu baƙin da dole zan yi attending na su."

A nan ta tsaya tana ɗaga mishi hannu ta ce.

"OK amini, Bye."

Ni kuwa, A ɗaki na samu Haula ita kaɗai tana bubbuɗe ɗinkuna masu kyau na Leshi.

Kallona ta yi ta ce.

"Sai yanzu? Kinga kayanmu in ji Hajiya, yanzu Lawan ya kawo su."

Murmushi kawai na yi amma ba don ina jin daɗi ba,domin na ji haushin abin da Aunty Ziza ta mini ba kaɗan ba.

"Miye kuma? Na san dai Hairiyyah ba ta da matsala..."

Ina kallonta na ce.

"Itama 'ƴar Hajiya ce?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Auta Jaja manya kenan, ɗiyarta ce, ita ce auta. Ga taɓara ga kirki ga kuma shagwaɓa. Suna matuƙar matuƙar ji da ita sosai musamman Ya Emraan cewa yake ita ce babbar ƙawarsa Aminiyar sa, kinga yanda take damu? Kamar wa su abokan wasanta,musamman Munira, haka za ta kiramu ɗakin ta muyita fira, sai taga dare ya yi sosai ta ce wallahi babu inda zamu sai mun gyara mata ɗakinta zamu fito......"

"Wannan matar ta jiya fa da ta ce in zo in goge ruwa ya zube?"

"Au! Mummy Na'ima kike nufi wai? Matar Baba Ustazu ce shi ne ƙanin Alhaji marigayin gidannan."

Wucewa na yi na shige na yo alwala na zo na tayar da Sallah.

****

Haka muka yi ta aiki wanda dolena na dinga tsayawa sai Magrib sannan in koma gida domin sai da ta ƙara jaddadawa Su Munira amma bana tunanin su Hajiya sun san da wannan.

Gidan ya cika sosai, mutane babu kalar da babu da masu kirki da marasa kirki, wata idan ta saka ki aiki tamkar ta samu Engine ba bu abunda ya dame ta. Wannan dalilin ne yasa dole bazan iya zuwa bukin gidansu Yaya Ashiru ba domin rana ɗaya ake yi dana Aunty Ziza.

Daren da nake yowa yasa bana samun ganawa da Yaya Ashiru, sannan shi ma Ya Jafaru ya canza mini sosai wanda har abin ya fara damuna. Ko wayarsa na ce ya ara mini sai yace mini bata da caji ko kuma yace wani abokinsa ya ara.

Bayan na faɗawa Ammie cewa ba zan samu zuwa gidan su Yaya Ashiru ba, shi ne ta ce ita dole sai ta tafi ita da Bahrain, ni kuma hakan yasa dole ba zan iya barinta ta hau ƙarfe taje wani wurin ba tare da ni ba, hakan yasa na ce mata yau daga zaran naje sunan duk yanda zan yi zuwa ƙarfe biyar ta jirani zan dawo mu tafi.

Koda na je gidan ya ilahiy! Ya cika maƙil ana ta hidima, wai bahaushe yace masu abu da abun su, ɗan fari a wurin Emraan Attahiru Araam. Su kansu mutanen gidan shaida ne akan yanda Hajiya take tsananin ƙaunar Emraan,da kuma aka zo aka haifo mata jika daga tsatsonshi sai taji ƙaunar da take yiwa jairirin har ta zarce misali, sannan kuma uwa uba ga shi Muhammad. Su Aunty Labiba da yaransu, dangin Aunty Ziza da kuma dangin Hajiya sun taru sai farin ciki suke suna taya murna. Tunda nake da su, yau ne rana ta farko da na taɓa tuɓe kayana nayi wanka a gidan muka shirya a tare cikin ɗinkin da aka yi mana mai kyau. Muna nan dai a ɗakinmu sai zuba uwar fira wanda sai idan za'a yi wani abinne muke ta shi mu fita. Ni daman yau na yi alƙawari na kuma roƙe su alfarma na cewa dan Allah kada su ce na shiga cikin gidan nan domin ba zan shiga ba In Sha Allahu har na koma gida.

Ina nan ma sai ga Adeel ya shigo nemana, nan muka lalace dani da shi yana ta bani labari ina dariya.

Sai da huɗu tayi na yi sallah sannan na kamkanta kayana, duk wani abin da Haula ta kawo mini da sunan nawa ne na tattara gudan kaya na ce musu na wuce gida. Munira sai tsiya take mini wai sai ta faɗawa Aunty Ziza tace na wuce tun ba'a gama bukin sunan ɗan gold ba.

Hijabi na Sanyo na hawo mashin daga can zuwa gida, ina zuwa na cire na sanya gyalen Lace ɗin na ƙara gyara fuskata wacce ba komai sai farar powder da lipstick muka fito mu huɗu da niyyan zuwa mu hau Napep har da Farisa da tace tana zuwa.

Wani irin girgiza Zuciyar Ya Jafaru tayi a lokacin da idanuwansa suka yi tozali dani. Tunda nake bai taɓa ganina da gyale ba sai yau, sannan kuma gashi daman na ɗan ƙara samun gogewa a abubuwa da dama ba kamar da ba.

Take yaji duk wani ɓacin randa na sanya masa ya gafarta mini. Baki kamar gonar auduga ya kalleni wanda da alama ya manta cewa har da Ammie muke yace.

"Masha Allahu! Beenafah ƙarshen kyau kenan...da an ce Beenafah to an kai ƙarshen magana. Ammie bukin ne aka fito? To Allah ya tsare...."

Ina murmushi na ce.

"Na yi kyau dai kenan ko Ya Jafaru?"

"Haba!...."

A hankali muka ga mota ta iso ta parker inda muke tsaye kowa ɗauke da mamaki a fuskarsa.

Wani irin mugun haɗe rai Ya Jafaru yayi ganin Yaya Ashiru ya fito a hankali daga motar yana murmushi ya ce.

"Ammie ina wuni?"

Itama da murmushin ta ce.

"Lafiya lau Ashiru. Ya hidima kuma? Allah yasa alheri?"

"Amin Ammie. Daman cewa na yi bari na zo na tafi daku tunda baku san wuri ba kada kuje kuyi ta wahala."

"Amma Ashiru baka ɗaurawa kanka wata wahala ba? Ai da ka bar shi munzo a Napep.."

Hannu ya miƙawa Ya Jafaru yana murmushi yayin da Ya Jafarun ya gimtse sosai suka gaisa.

Ƙofar motar ya buɗe wanda Bahrain har ya jima ciki tunda ya buɗe ya fito ya shige ciki yace mana.

" Ku shiga Ammie mu tafi yamma na ƙara yi. "

Cikin motar Ammie tashiga, sannan Farisa, sai kuma ni da na kasa ce masa komai sai murmushi nake na shiga sannan ya rufe.

Ya Jafaru dake tsaye ji yayi wani baƙin ciki ya taso ya tokare masa maƙogwaro...wata zuciyar na ingiza shi akan ya shiga motar shima ya bimu, wata kuma zuciyar na ce masa a'a Jafaru! Kai dai yi zaman ka, kana nan zaune zaka ga sun dawo.

Da haka na yi ta ɗaga mishi hannu har muka wuce. Bakin bishiya ya kama ya zauna yana jin a zuciyar shi ba zai iya ɗagawa ko'ina ba sai idan ya ga mun dawo. Shi wallahi a yanzu yama rasa wane kalar tunani ya kamata ya yi. Ko Makaho ya lalaba tsakanin Beenafah da Ashirun nan yasan cewa Ashiru sonta yake... Wata irin zabura ya yi da ƙarfi ya furta.

"Kai! Inaaaa! Wallahi tallahi wannan Ƙarya ce ma."

Daga haka ya sake komawa ya zauna yana mai ɗora hannayensa akan gwiwoyinsa ya buga wani uban tagumi yana tunani.

Duk irin labarin da take bashi akan Ashiru bai taɓa hasko abin ta haka ba, tun ranar farko da Ashiru ya zo suka tsaya suna wannan firar tun a ranar ya tsinci kansa cikin matsanin baƙin cikin da har bacci sai da ya hana shi. Ya hana mai walwala, babu abin da yake gani da ji idan ba firar su ba ta ranar.

Ya kasa zuwa makaranta, tun ranar Kawunsa ke kiran sa amma ya kasa ɗagawa domin bai ga ta tafiya yabar gari ba domin wallahi ba zai taɓa yarda ya yi sake ayi mishi sakkiya ba. To amma kuma ina mafita? Mafita ɗaya ce mafitar da bai san ya ma zai iya fuskantar ta ba a yanzu amma kuma dole ya yi wani abu idan ba haka ba wallahi yana nan tsaye yana kallon ruwa kwaɗo zai masa ƙafa.

****

Yaya Ashiru bai tsaya ko'ina damu ba sai ƙofar gidansu inda muka tarar mutane da yawa sai kai kawo ake masha Allah ana ta hidima.

Cikin farin ciki da wani alfahari yake nunawa duk wanda muka haɗu da shi ni yana faɗin ga Beenafah su gaisa.

Ƙofar Umma aka yi mana shimfiɗa muka zauna wanda ni sam na kasa ganewa, domin mutane sai watsewa suke a hankali suna barinmu a zaune. Ummar ce ta fito daga cikin ɗaki ta zauna a gefena, fuska cike da murmushi ta ce mana.

"Hajiya! Sannu da zuwa."

"Yauwa Maman Ashiru sannu, ya gida ya bayan rabuwa kuma?"

Umma ta ce.

"Alhamdulillah! Sai godiya. Ya kuma jiki?"

"Jiki Alhamdulillah! Sai godiyar ubangiji. Ana ta hidima ashe? Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya."

"To amin amin ya Allah. Mun gode sosai Allah ya saka da alheri..."

Muryar Ashiru muka ji yana ta ƙwala kiran Ayya amma kuma babu ita babu labarinta. Da kanshi ya dinga kiran mutanen gidan muna gaisawa, sai wani kallona suke tamkar sunga wata sabuwar halitta har sai da naji har cikin raina na tsargu.

Abinci aka kawo mana da ruwa wanda gabaɗayanmu babu wanda ya taɓa sai Bahrain ne ma ya ɗauki lemu ɗaɗaɗaya da shi da Farisa suka fasa suna sha.

Kallon Ammie na yi ganin kowa ya kama wata sabgar domin har Umma an kira ta wani wuri, ganin hakan yasa murya a ƙasa-ƙasa na ce.

"Ammie ta shi mu tafi gida."

Gyaɗa kanta ta yi sai muka miƙe a tare muna kiran zamu tafi. Fitowa Yaya Ashiru ya yi daga can cikin wani ɗakin da ya shiga tunɗazu ya ce mu shigo mu gaisa da Ayya.

Ɗakin cinjim yake da mutane wanda ashe har Amaryar tana ciki. Nan muka sake shiga wani babin gaishe-gaishe,daga can ƙuryar ɗaki ƙarshen gado Ayya take yi mana magana ciki-ciki kamar ba ita ce ta taɓa zuwa gidanmu tana surutu tamkar an kunna redio FM ba. Dubu uku Ammie ta miƙawa Ayya tace a sai wa Amarya tsintsiya Allah yasa albarka ya bada zaman lafiya.

Har waje wasu daga cikin su suka rakomu suna mana godiya yayin da wasu kuma suke ta baya-baya damu. Da kanshi ya sake ɗaukarmu ya maishe mu har ƙofar gida wanda har lokacin ashe Ya Jafaru yana nan inda muka bar shi yana zaune.

Yana ganin mun fito motar ya zo yana mai karɓar ledar da take hannuna ya ce.

"Sai yanzu?"

Murmushi na yi na ce.

"Mun daɗe ne Ya Jafaru?"

Jinjina kansa ya yi ya ce.

"Gaskiya dai kam."

Gida Ammie ta shige tabarni ina magana da Ya Jafaru wanda bamu ankare ba muka ji horn ɗin Ya Ashiru.

Juyawa na yi na koma gefen driver na tsaya jikin window na ce.

"Yaya Ashiru mun gode sosai."

Jinjina kan shi yayi da murmushi ya ce.

"Ba komai Beenafah ai ni ke da godiya, na gode sosai. Sai na dawo.."

"Yaushe kenan?"

"Uhm! Ni ko gobe kika ce na dawo zan dawo...beside yau an riga an gama komai kinga na zama free."

"Eyyah ni kuma Kaga Alhamis da juma'a ne kaɗai nake gida domin sauran ranaku ina makaranta."

"To yanzu sai Alhamis kenan?"

Gyaɗa kaina na yi na ce.

"Eh, zai fi."

"To Allah ya kaimu."

"Amin, sai anjima na gode."

Idon Ya Jafaru ƙyar a kaina koda na juyo, gashi ya wani haɗe rai sosai kamar ba shi ne yanzu yake mini murmushi ba.

"Beenafah!"

"Na am"

Na amsa ina kallon shi kamar yanda shi ma ni yake kallo ya ce.

"Wane ne wannan a wurin ki?"

"Uhmmm! Wai Yaya Ashiru kake nufi?"

"Eh"

Ya bani amsa kai tsaye.

"Yaya na mana, wanda ya taimaka mana."

"Bayan wannan dalilin fa Beenafah?"

Ba tare da sanin inda maganar sa ta dosa ba na ce.

"Ba wani dalili."

"Kin tabbata Beenafah?"

Gyaɗa kaina na yi na ce.

"Na tabbata."

Cikin jin wani irin sanyin da ya jima bai ji irin sa a zuciyarsa ba ya lumshe idanunsa a hankali sannan ya buɗe su a kaina yana mai kwantar da murya sosai cikin yanayinda ban taɓa jin muryar sa a haka ba yace.

"Bani da wani zaɓi Beenafah, ya zama dole gobe in tafi Zaria, Kawu har ya yi fushi sosai akan rashin zuwana...."

"To wai ni abinda ya hana ka tafiyar ne ya bani mamaki Ya Jafaru..."

Wani guntun Murmushin ya saki yana girgiza kansa ya ce.

"Ko na faɗa miki dalilina yanzu ba za ki fahimta ba Beenafah... Zo.. Zo mu zauna a nan."

Ya ƙarashe maganar yana mai samun bakin bishiya ya zauna nima ya nuna mini gefen sa yace in zauna.

Wani irin rikitaccen kallo ne ya bini da shi har sai da na ji zuciyata ta tsinke domin a tunanina wani laifin na aikata masa.

" Beenafah ki yi mini alƙawarin cewa daga gidan aikin ki sai Islamiyyar ki kaɗai za ki riƙa bai wa muhimmanci, duk wani mutum ko waye shi ba za ki tsaya kina ɓata lokacinki wurin tsayawa magana da shi ba..."

"Haba! Ka sanni ai Ya Jafaru, ni bani da wannan rayuwar, ko mazan da suke ajinmu a islamiyya babu wanda nake magana da shi in dai ba ta kama ba. Sannan gidan aikina ma su kansu suna da doka,babu wacce ta isa ta tsaya da namiji suna fira koda a wajen gidan ne."

Cikin jindaɗin fahimtar sa da nayi yasa shi sakin murmushi ya ce.

"To na gode Beenafah, zan riƙa kira da wayar Mama sai ta baki muyi magana a duk sanda na tashi, kema kuma idan kina so ki yi magana dani za ki iya ɗaukar wayar ki yi mini plashing kai tsaye kinji ko."

"In sha Allahu Lauyanmu na gobe, Allah ya taimaka ya bada sa'ar abinda aka je nema.."

"Amin. To amma ke baki da wani alƙawarin da kike so na riƙe miki ne Beenafah??"

Cikin seconds na ɗan wawwara ido nayi nazarin maganar sannan na jinjina kaina ina murmushi na ce.

"Alƙawari ɗaya Ya Jafaru, kada ka biyewa abokan banza, kamar yanda Ammie ke yawan gaya mini, abokan banza sune babban jigon da ke taka rawa wurin taɓarɓarewar tarbiyyar yaro duk yanda kuwa ya samu training a gida. ka mayarda hankali akan karatunka kamar yanda kake faɗa mini nima."

Wani abu yake ji yana ƙara girmama a zuciyarsa fiye da yadda yake tunani musamman wannan firar da mukayi, ta tsaya a cikin ranshi tare da sake haska mi shi wata sabuwar hanyar da bai san tana existing ba a cikin duniyar sa.

Muna nan zaune muna ta fira har sai da aka fara kiran Magrib sannan ya ce na tashi na shiga gida.

Washegari koda na fito na shiga gidan wai har yayi sammako ya wuce zuwa Zaria. Fatan alheri na yi musu sannan na sa kai na wuce.

Ko bayan da aka gama sunan Muhammad (Abeer) sai da muka kwashe tsawon sati muna aiki sosai sannan daga baya muka samu sassauci bayan mutanen da suka zo kowa ya watse sai en tsirarrun da suka rage ne ba su tafi ba.

Maimakon Aunty Ziza ta canja daga halin da take nuna mini tunda Hajiya ta yi magana, ko ɗaya ba ta sauya ba wanda sai ma ƙaro sabbin wulaƙancin da ta ƙirƙiro, hatta kofi idan za ta sha ruwa sai ta saka an kirani na zo na ɗauko mata. Ni kuma abin da bata gane ba, ko kaɗan yanzu na daina shakkarta tunda na gano abin ta bana arziki bane, duk tayi abu don ta ɓata mini rai ko kaɗan hakan baya damuna wanda ita shi ne abinda yake ƙara ƙonata dangane da ni, aiki kuwa, idan za ta kwana tana saka ni aiki bana taɓa nuna mata komai, kuma ita ko a gaban waye bata shakkar yi mini haka idan ka cire Aunty Labiba da Emraan. Waɗan nan mutum biyun sune kaɗai idan suna a wuri bata nuna alamun musgunawa a gare ni.

Yauma ina zaune bakin kitchen tare da Haula sai gashi ta kira Haula a waya wai in zo tana nemana. Tashi na yi kai tsaye na shige na ce mata gani.

Flask ta nuna mini tana faɗin.

"Ɗauki ki dafo mini ruwan zafi ki kawo ina jiran ki yanzu."

Ɗauka na yi ina faɗin to,babban kitchen na dawo na buɗe wata babbar tukunyar ruwan zafi ina ta wani mitsitstsika ido akan hayaƙi su Munira sunata mini dariya na cika flask ɗin na ɗauka naje na kai mata na ce ga shi.

Wani kallon sama ƙasa ta mini ta ce.

"kina nufin yanzun nan har kin dafo ruwa?"

Girgiza kaina na yi kai tsaye na ce.

"A'a, a Kitchen na ɗebo wurin su Inna Kuluwa..."

"Did I asked you to go there and fetch?? Cewa na yi kije ki kunna wuta ki ɗora ki dafasu su tafasa sannan ki juye ki kawo mini."

Ɗauka na yi kurum na fice naje waje na juyesu a bakin famfo cikin wani bucket duk su Munira suna zaune suna kallona fuskokinsu cike da alamar tambaya.

Kitchen ɗin ciki na koma naje na kunna Gas kamar yanda Haula ta koya mini na ɗora tukunya na tsaya nan jikin ƙofa har sai da ruwan suka tafasa na juye na kashe sannan na fito naje na kai mata.

"Ɗauki Abeer kije ki cire masa diaper ki kawo mini shi."

Ta ƙarashe maganar tana mai nuna mini toilet. Ɗaukar shi na yi na je toilet ɗin na tsabta ce shi tas cikin lokaci na dawo na miƙa mata shi. Wai ita ƙila a tunaninta zan rikice ne na ce bansan yanda akeyi ba,don ta samu damar ci mini mutunci son ranta. Bata san cewa In Sha Allahu ko ita bata fini sanin yanda ake kulawa da jariri ba, domin lokacin da Ammie ta haifi Sajjad, ni ce na dawo uwar sa ta dalilin halin da Ammie ta tsinci kanta a ciki wanda hatta wanka, bacci, da cin abincinsa duk ni ce, sai da ya bar duniyar sannan na daina kulawa da shi. Saboda haka ni kula da yaro sam baya bani wahala, kuma zan iya jure ƙiriniyar yaro ko yaya yake ko.

Yana da fa Nannynsa ta musamman da aka kawo mata ita kwana uku da suka wuce. Amma don neman fitina ita dole sai ta san yanda ta nemi hanyar musguna mini.

"Ɗauko ga cup can Ki haɗa mini Tea Ki zauna ki fifita mini har sai ya sha iska sannan."

Ina zaune a ƙasa ina fifita mata na ji sautin muryar ta tana faɗin.

"Wai har ke Hairi za ta dinga wani zuzutawa! Ina abin zuzutawa a nan? Mai aiki ana biyan ta har wani abin burgewa ke gareta? Hmm! Wai Pretty! Pretty na inda take ke kam sai dai Pretto..."

Tamkar tana magana da iska haka na yi mata kamar ban san dani take ba. Ina nan zaune Haula ta shigo mata da Lunch cikin wani babban tray mai ɗauke da dishes sun kai kala biyar ta ajiye mata a gefe tana faɗin ga abincin ta nan, kallona tayi ta yi mini murmushi nima kuma sai na mayar mata.. Aiko ina wuta ta ka ɗani, kawai ta hau bakinta tana faɗin wai na raina ta ina kallonta ina yi mata dariya, ita sai na nuna mata abinda na gani a jikinta da yake sakani dariya.

Maimakon in ji tsoro in daina, yanda take ɗin sai ya ƙara sakani dariya wanda har bansan lokacin da wata dariyar ta sake suɓuce mini ba.

Aikuwa jiki na rawa ta miƙe ta nufo inda nake, kallonta nake da mamaki ina jira inga shin dukana za ta yi ko kuma me. Ganin ta juyo gareni yasa Haula sakin dariyarta a hankali tana yi tana toshe baki wanda shi ne abu na uku da ya sake bani dariya.

Ficewa tayi fuu! Sai inda Hajiya tana wani huci ta ce.

"Hajiya! Shin ina so in san wani abu. Waccan 'ƴar aikin bata san matsayina ba ne a gidannan ko kuwa?"

Ajiye remote ɗinda ke hannunta Hajiyar ta yi sannan ta kalle ta ta ce.

"Ziza wacce mai aiki kike nufi?"

"Marar kunyar yarinyar da Aunty Labiba ta kawo mana."

"Beenafah kike nufi?"

Da sauri ta gyaɗa kanta ta ce.

"Eh, ita. Hajiya dariya fa ta dinga mini, sai ta kalleni ta tuntsire da dariya..."

Hankali kwance Hajiya ta girgiza kanta ta ce.

"Ba dai Beenafah ba Ziza, ko Munira da nasan tana iya aikata makamancin haka ba za ta yi miki dariya ba ballantana Beenafah da ba ruwanta...."

"Wallahi Haji..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull