Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 22

Ganin ido complete - Chapter 22

Ganin ido complete Chapter 22: Ganin ido complete Chapter 22. "Ziza! Samu wuri ki zauna mu yi magana."

3,369 words

"Ziza! Samu wuri ki zauna mu yi magana."

Haɗiye sauran maganar ta tayi tare da samun kujera wacce ke fecing Hajiyar ta zauna tana kallonta.

"Ki daina shigewa gaban yarinyar nan Ziza, Hairiyyah ta faɗa mini irin abin da kika mata ranar wanda Munira ce ta faɗa mata kuma hakan sam bai kamata ba,ko ni ranar a gabana ki ka dinga yi mata kuma kin san ni bana son haka, ni da na ajiye su ban uzurra musu ba kema banga dalilin da zai sa ki riƙa uzurra musu ba. Tunda kika yi aure gidan nan ban sanki da haka ba, saboda haka dan Allah ki bari, idan ma akan kuskuren da Emraan ya yi ne kema kin san ya faɗa ne kawai, domin kinfi kowa sanin wane ne mijin ki, ko ɗaura mishi ita aka yi a ƙafa ba zai ja ta ba. Ki kama girmanki ki daina shiga harkar yaran nan bana son hakan. Ban hana ki saka su aiki ba, duk abin da kike so suyi miki dole za su yi shi ko basa so domin matsayinki da na su Nadeeyah duk ɗaya ne a gidan nan, to amma ki tsaya matsayin ki dan Allah."

Murya a raunane ta kalli Hajiyar ta ce.

" Ki yi haƙuri Hajiya."

Jinjina kanta ta yi ta ce.

" Ba komai. Kina iya tafiya."

Fitowa tayi jiki sanyaye ta dawo ɗakin wanda har a lokacin ina nan inda ta barni ina fifita mata shayinta. Wani kallon ta yi mini a yatsine ta ce.

"Ki haɗa da kofin ki wuce da shi ki bani wuri."

Cikin sauri na fito riƙe da Tea cup ɗin na cikawa rigata iska. Ɗaki na dawo wurin su Munira. Sai da na shanye lafiyayyen Shayi na wanda ya ji komai yayi zam sannan muka dawo muna cin abinci ina ƙara ba su labarin abin da ya faru sai dariya muke har muka kambala na ta shi na haɗa kayana na yi gida.

Koda na koma na tarar da Ya Ashiru cikin gida zaune da shi da Ammie suna fira.

Ɗaki na shige na ajiye kayan na fito muka gaisa da shi. A nan gaban Ammie ya ciro waya a kwalinta ya ajiye yana faɗin.

"Ammie Waya ce na kawo muku domin zan koma Kano gobe,kuma ina so idan na koma in riƙa ji daga gareku kada a maimaita er gidan jiya."

Ɗan Jim tayi sannan ta ce.

"Waya Ashiru? Kuma Wayar ma irin wannan babba haka?"

Ɗan ƙara sadda kan shi ya yi ƙasa yana faɗin.

"Ba komai Ammie... Ai ba wani abu bane, kunfi ƙarfin haka a wurina."

Daga haka ya miƙe yana mana sallama ya wuce waje. A hankali cikin jin ba daɗi a raina na biyo bayan shi har bakin Mashin ɗinda ya saba zuwa da shi muka tsaya, muryata a sanyaye ba tare da sanin mi nake ji ba na ce.

" Yanzu Yaya Ashiru idan ka tafi sai yaushe kenan?"

Murmushi ya yi ya ce.

"Ban sani ba Beenafah, amma dai ni na san ba zan iya jure nisa dake ba, tabbas dole zan dawo..."

"Allah ya kai ka lafiya yasa a dawo lafiya.."

"Amin. Ina Layina da na baki?"

Zaro idona na yi ina mai jin wani irin ba daɗi a raina na ce.

"Yana Wayar Ya Jafaru kuma ya tafi Zaria."

Wani murmushin gefen baki ya yi yana kallona ya ce.

"Wane ne wannan Ya Jafarun? Ku en uwa ne?"

"Eh to, haka zan ce dai, su ɗin maƙotanmu ne, ga gidan su nan..."

Na faɗa ina mai nuna mai gidan su sannan na ce.

"Tun da muka dawo unguwar nan da su muka fara haɗuwa, kuma suna da kirki sosai, hakan yasa sai muka zama kamar en uwa."

Jinjina kansa ya yi yana wani kalar murmushi ya ce.

"OK. Ba damuwa, akwai layi a ciki na yi mata caji na yi komai, zan riƙa kiran ku ina jin halin da kuke ciki."

"To Allah ya tsare hanya, ina gaida su Ayya."

Daga haka ya haye Mashin ɗinsa yana yi yana kallon gidan su Jafaru tare da tariyo duk abinda ya riƙa yi masa a cikin ƙwaƙwalwarsa. Tun ranar da ya fara zuwa gidan tun daren ranar ya cire Layin ya yasar daga wayarsa, domin duk ya kira ce masa ake a kashe take har yau kuwa.

Ni dai ina nan a tsaye har sai da ya ɓacewa ganina sannan na koma cikin gida.

Cike da zumuɗi na ja wayar na buɗeta,Infinix ce touching screen mai kyau sabuwa dal da ita.

Kunnawa na yi ina ta latsawa cike da farin ciki. En ajinmu a islamiyya kawai nake tunawa su Hafsa waɗanda mafi yawancinsu suna da Waya, sai kuma su Munira. Camera na shiga na fara Selfie ina yi ina dariya kamar wata taɓaɓɓiya.

"Beenafah!"

Waigowa na yi na kalli Ammie jin ta kira Sunana na ce.

"Na'am."

"kina ganin karɓar wayar nan ya yi Beenafah?"

Ɗan jim na yi sannan na kalle ta fuska cike da neman ƙarin bayani na ce.

"mi kika gani Ammie?"

"Ba komai, kawai dai wani abu nake dubawa..."

"Ammie fa kinji cewa ya yi so yake ya riƙa ji idan muna lafiya."

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta jinjina kanta ta ce.

"Haka ne kuma. Allah ubangiji yasa mu dace."

"Amin. Tashi na yi na shirya tsab cike da zumuɗi na fito da jakar Islamiyyata na ɗauko wayar na saka a jaka domin tafiya da ita.

Ammie dake fitowa daga ɗaki ne ta kalleni ta ce.

" Beenafah ina wayar nan take?"

Kallon jakata na yi sai kuma na kalle ta na ce.

"Gata nan a Jakata."

"Ciro ta ki ajiye a ɗaki, daga Islamiyya har gidan aikin ki ban amince kije da ita ba."

A hankali na juya na shige ɗakin na ajiye ta akan Katifa na fito na wuce.

Da dare bayan na yi sallar Isha Ya Hamza na shigowa na ɗauko wayar na nuna masa sannan na ce ya saka mini numbern Ya Jafaru.

Jujjuya wayar ya yi a hannunsa ya jinjina kai yana ƙara kallon wayar ya ce.

"Iyyeh! Infinix! Lallai yarinya kice kin Faso garin..."

Cike da jin ya wani fasa mini kai na fashe da dariya na ce.

"Yaya Ashiru ne ya siyo mini ita."

"Gaskiya ya yi ƙoƙari..."

"Yi sauri ka saka mini Numbern Ya Jafaru dan Allah na kira shi kada kaje ka rigani faɗa masa nasan halinka."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 24*

Yana saka mini numbern ba ɓata lokaci na kira Ya Jafaru cike da farin ciki na kara a kunnena. Ina jin ya ɗaga na buga wani irin ihu tamkar zan fasa masa dodon kunne na ce.

"Ya Jafaru na yi Wayaaa! Yaya Ashiru ya siya mini waya"

Zaune yake akan gadon sa a hostel da tarin Handout a gabansa, daman kuma already an wuce shi a lectures na tsawon sati biyu sannan ya yi joining na su. Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye tamkar wanda aka tsikara da allura jin wata irin mummunar magana...

"Hallo! Ya Jafaru kana jina??"

Cikin wani irin ɓacin ran da har yasa ya kasa controlling kansa ya buga mini tsawa da faɗin.

"Akan me to zai saya miki Waya? Ban ce kada ki tsaya saurarar kowane shashasha ba Beenafah?"

Cike da mamaki na ce.

"Ya Jafaru Yaya Ashiru fa na ce maka..."

"And so! Akan mi zai saya miki Waya? Akan wane dalili?"

"Ya Jafaru ba fa wani abu ba ne, Kano zai wuce shiyasa ya siya mini..."

"Uhm! To na ji!"

Daga haka ya katse kiran wanda ni a tunanina network ne, hakan yasa na sake gwada kiran numbern tasa amma kuma sai aka ce mini wayar a kashe take.

Kallon Ya Hamza na yi sai kuma na kalli Ammie wacce gabaɗaya hankalinta ya ɗauku yana kan Bahrain da Farisa suna magana. Ganin hakan yasa na kalli Ya Hamza na ce.

"Ya Jafaru fa faɗa yake akan Wayar nan. Daga jin yanda yake magana bai ji daɗin ta ba. Ko kuma dai akwai abin da yake damuna? Saboda ba haka yake ba."

Miƙewa ya yi bayan ya gama cin abincinsa ya jinjina kansa yana faɗin.

"Wata ƙila akwai abin da yake damunsa dai kam.....Ni na wuce sai da safe."

Game muka shiga bugawa a wayar ni da Bahrain, bayan kuma wani ɓangaren na zuciyata cike yake da tunanin abin da ya Jafaru ya yi. Muna nan daga nan na ɗan yi wasu aikace-aikace sai muka je muka kwanta domin Yaya Ashiru bai kirani ba, nima kuma ɗin ban yi tunanin kiran sa ba. Washe gari ina tashi na yi Sallah na ɗauko wayar na yi ɗan latse-latsena wanda ko Azhkar ban samu na yi ba akan ɗoki saboda dannar wayar, bayan na ga lokaci ya tafi na ajiye na je wurin shirin tafiyata bayan na kambala duk aikinda ya kamata na fice zuwa gidan aikina.

****

Misalin ƙarfe biyu saura na rana, Mamansu Fakiha na zaune tana zuba musu girkin da ta sauke kawai sai Jafaru ya yi sallama ya shigo gidan.

Ajiye serving spoon ɗinda yake hannunta ta yi cike da tashin hankali ta dafe ƙirji ta ce.

"Jafaru! Lafiya? Miye yasa ka dawo? Miye ya faru?"

Ɗan guntun tsaki ya ja tare da janyo kujerar tsugunno ya zauna akai yana mai yasar da ƙaramar school bag ɗinsa wacce ke ɗauke kala uku ta kayansa gefe ya kalle ta ya ce.

"Ba bu abinda ya faru... Kawai dai na zo ne inji dalilin da yasa wannan Ashirun ya sayawa Beenafah waya.."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Jafaru! Kana da hankali kuwa?"

Yana gunguni ƙasa-ƙasa ya ce.

"To ai hakan ba daidai bane,fisabilillahi Mama kuma ace kuna gani ku bari wani ƙaton banza ya siya mata waya ya bata, wannan hanyar lalacewa ce aka biɗar mata, idan ba shi ba dan Allah Mama Ina Beenafah ina Way..."

Kafin ma ya iyarda rufe bakin sa tuni ta rotsa masa Cokalin miyar da yake Cikin tukunyar gabanta a hasale tana faɗin.

"Ka ci ubanka da kai da dalilin naka.."

Saurin Miƙewa ya yi ya matsa gaba can nesa da ita domin Cokalin ya sauka a daidai, hakan ne ya haddasa masa jin zafi a gefen bakin shi shiyasa ya tashi ba shiri.

Cikin nuna tsantsar ɓacin rai ta kalle shi taci gaba da faɗa tana cewa.

" Yanzu Jafaru saboda baka san ciwon kanka ba, Alhaji ya kashe kuɗi ya saka ka a makaranta amma shi ne zaka wani ɗebo ƙafa sati ɗaya ka dawo gida akan wani dalilinka na banza na wofi? Ina ruwanka don Ashiru ya saya mata waya? Na ce ina ruwanka? Can wan can lokacin baya da ta taɓa yin wayar don ubanka kasan ma da zancen? Inda tana da niyyar lalacewa da tun can bata lalace ba... "

Miƙewa tayi tare da nuna shi da yatsa ta ce.

" To wallahi bari kaji in yi maka rantsuwar Musulmi.. Wallahi tallahi kar in ji kar in gani wai ka yi musu zancen wayar nan da sunan ɓacin rai,ban amince ba ka ji na faɗa maka, kuma wallahi yanda ka ɗauko ƙafa a yau ɗinnan ka zo a yau ɗin nan zaka koma ba sai gobe ba. Sannan mags Garin nan kuma; idan har ba hutu aka yi ba ban amince da ka zo shi ba. Domin baka isa ka zubar mini da mutuncina ba a wurin Alhaji ka ji na faɗa maka.. "

Daga haka ta ƙwala kiran Fakiha akan ta zo taci gaba da raba abincin ita kuma ta shige ɗaki rai a matuƙar ɓace.

Tsaye ya yi kawai yana mai jin wani irin tashin hankalin da bai san ma yanda zai fasalta shi ba. Wai Mama ko tasan miye yake ji akan Beenafah? Jiya sam bai samu ya runtsa ba tunda ta yi nasarar shaida masa wannan mummunar maganar.Wallahi tallahi zai iya ɗaukar mummunan mataki akan koma waye akan Beenafah. Shi kenan kawai don ya taɓa taimaka musu sai a bar shi da ita yayi ta abin da ya ga dama. Idan ba iskancin banza ba akan me zai saya mata waya to?

Ya jima a tsaye tsawon lokaci yana karanta wasiƙar Jaki. Ya saƙa ya warware ya saƙa ya warware ya rasa ma tudun dafawa. Yana nan a haka sai ga babansu ya yi sallama ya shigo. Daga ganin irin kallon da yake bin shi dashi kasan cewa labari ya riga da ya gama kai masa. Cikin nuna ɓacin ransa ƙarara shima yace.

"Mutumin banza mutumin ɗan magori!"

Cike da fatan Allah yasa baban ya Fahimce shi a wannan maganar ya yi ƙasa da murya ya ce.

"Yanzu kai ma Baba laifina za ka gani kenan? Beenafah fa amana ce a garemu bai kamata mu bar ta tana rayuwa kara zube ba a duk yanda taga dama..."

"Beenafahr ce take rayuwar kara zube?? Miye ka taɓa gani ko ka taɓa ji ance tana yi wanda ba daidai ba? Ka faɗa mini shi ni kuma na yi maka alƙawarin ɗaukar mata mataki da kaina"

Ƙasa ya yi da kansa ya na wani turo baki yace.

"To amma dai ai wannan wayar bata kamata ba, idan ma magana yake so yayi da ita ya kira ta wayar Mama man..."

"Kai.. Kai.. Dan Allah banson shirme ka ji ko! Ɗauki jakarka ja juya yanzu-yanzu ba sai anjima ba ka koma..."

Wani irin shock ne ya ji ya ziyarcesa a lokaci ɗaya wanda har bai san sanda ya ɗago ya kalle shi ba yana faɗin.

"Haba Baba! Dan Allah ku bari zuwa gobe..."

"Wallahi yau za ka juyi ka koma Jafaru ka ji na faɗa maka. Idan kuma karatun ne baka so sai ka faɗawa Alhaji Usman ɗin ya daina asarar kuɗinsa a kanka.."

"To ai ni yanzu bani da isassun kuɗinda zan iya komawa yau ɗin..."

"Au! Yanzu ashe ma ba kada isassun kuɗi amma ka yi ƙunar baƙin Wake ka wanko ƙafa ka zo?"

Fitowa Mama tayi daga can varender ta watso mishi dubu biyar tana faɗin.

"Ga su nan ka ɗauka maza da zafi ka juya ka koma ka ji na faɗa maka....Hmm!"

Ta faɗa daga ƙarshe tana mai riƙo daga cikin ƙarfen turakunda suka riƙe verander ɗin ta ci gaba da faɗin.

"Aikin banza aikin wofi! Wannan ai isar baka isa bace kake nunawa. Idan har so kake ka nuna isa to ka je ka fara zama wata tsiya tukunna."

Tsince kuɗin ya yi ransa na yi masa wata irin suya tamkar ya fashe haka ya ke ji. Yana gama tattare kuɗin ya ɗauki jakar sa ya fice. Hanya ya kama wanda sai da ya yi nisa sannan ya juyo kuma ya dawo, ya so ya yi zuciya ya tafi amma kuma ba zai juyawa ya koma bai ganta ba.

Yana dawowa sai gani ni kuma na iso ƙofar gidan...wani irin mamaki ne ya ziyarce ni a lokaci ɗaya na wani hangame baki ina zare ido na ce.

"Ya Jafaru??"

Fuska ba yabo ba fallasa ya kalle ni ya ce.

"Beenafah! Kin dawo?"

"Miye ya dawo da kai kuma? Ba kace sai kun yi jarabawa ba?"

Ga dai bikin zuwa amma babu Zanen ɗaurawa. Ga dai Beenafah yana gani amma kuma bai isa ya yi mata zancen waya ba tunda Mama ta hana, sannan uwa uba ga maganganun da Mamar ta yi masa na ƙarshe sun yi matuƙar ƙona masa zuciya. Wato ga mari ga tsinka jaka! Tuna wannan yasa ya ɗan ƙirƙiro wani murmushin dole ya ɗaura akan fuskar sa ya ce.

"Wani ɗan abu ne ya kawo ni kuma ma na kambala yanzu zan juya in koma..."

"To amma ko shigowa ba za ka yi ba Ya Jafaru??"

Girgiza kansa ya yi ya ce.

"A'a. Ni na wuce sai an jima."

Tsaye nake yayin da fuskata ta cika da maɗaukakin mamaki ina kallon sa har ya ɓacewa ganina. Ajiyar zuciya na sauke tare da girgiza kaina kawai na juya na shige gida ina faɗawa Ammie cewa yanzu naga Ya Jafaru ashe ya zo har ya juya ya koma kuma.

Itama da mamaki a fuskarta ta kalleni ta ce.

"Jafarun?"

"Ƙwarai kuwa Ammie. Wallahi na ganshi yanzu. Amma kuma har ya koma."

Ɗan Jim tayi kaɗan tana nazari, sai daga baya kuma ta jinjina kai ta ce.

"To wata ƙila akwai abin da ya dawo da shi, amma zan shiga gidan na ji."

Da ta je gidan ta tambayi Mama, ce mata tayi wasu takardun makarantarsa ne ya manta wanda dole ana da buƙatarsu shi ne ya zo ya ɗauka ya koma.

****

Gefen su Hassana kuwa;Tun bayan da su Ammar suka zo suka gansu da wata uku aka kawo kayan gaisuwa tamkar za'a buɗe wani super market. Mummy wacce ta ji kamar ta yi hauka akan tsananin farin cikin da take ciki, babu abinda take in ba alfahari ba tana ɗaga shoulder musamman da taga an ɗora kuɗi sama har 5M. Wai kuɗin gaisuwa kawai. Hakan yasa ta ƙara jaddadawa su Hassana cewa gwanda ma ta bada kai bori ya hau, domin kuwa wallahi tallahi aure tsakanin su da 'ƴa'ƴan Alhaji Mansur Anka babu fashi sai idan mutuwa ce ta shiga tsakani.

Hassana tasan Mummy ta san me take iya yi hakan yasa dole ta shafawa kanta ruwa, duk cewa Aunty Aysha sa saurin en uwa sun yi lallashin duk a banza, domin kuwa ba don ta haƙura ba.

Yau ma a makaranta tun da suka fito morning lecture take tare da sabon saurayinta Salman a school cafeteria.

Suna zaune Husaina ta iso wurin a hankali ta yi musu sallama sannan ta tsaya akan Hassana ta ce.

"What you are doing is not right Hassana..."

Miƙewa ta yi cikin azama ta janyo hannunta da ƙarfi suka bar wurin, cikin nuna ɓacin ranta ta ce.

"Hussy miye haka? A gaban Salman ɗin za ki fara yi mini maganganun haukar na ki??"

Girgiza kai ta yi itama ranta a ɓacen tana mai nuna ta da yatsa ta ce.

"Ke ce kike abin da bai kamata ba Hassana... Akan me za ki zo da maganar wani akanki amma kuma ki fara soyayya da wani! Ina jiye miki abin da ke bakya hangowa Hassana..."

"Ina ruwan ki? Na ce miye abin da ya shafeki da abin da nake yi? Salman shi nake so kuma shi zan aura...Wallahi tallahi ni babu wani Ameer ɗinda zan aura..."

Hannunta Husaina ta kama hankalinta a tashe ta girgiza kanta ta ce.

" Please listen to me Hassy... Ka da ki bari hakan ya girmama. Mummy ba za ta amince ba... "

" Dole sai ta amince? Ko kuma ita ce za ta zauna mini a gidan aurena?"

Girgiza kanta Husaina ta yi still ta ce.

"Hassy ina jiye miki kada..."

Hanya ta nuna mata cike da hargagi tana wani girgiza mata kai alamar bata ma son maganar ta ce.

"Kinga Malama dan Allah, ki wuce kije wurin abin da ya shafeki.."

"Hassy! Gabaɗaya yinin yau only morning lecture kika yi attending...Tun da aka tsaida maganarki da Ameer ko sau ɗaya baki taɓa bashi lokacin ki ba, haka zai zo ya zauna ƙarshe ya kakkaɓe rigar sa ya tashi ba tare da kin kula sa ba, sannan yanzu gabaɗaya karatunki ya fara samun matsala duk ta dalilin Salman... Ina shawartar ki da kuma gargaɗin ki; kada ki bari Mummy ta gano duk wannan abubuwan da kike a bayan idonta. "

Daga haka ta juya ta koma class. Mamaki take ta rasa mike damun Hassana, duk abubuwan nan da take tsawon lokaci Hussaina ba ta taɓa yi mata magana akai ba sai yau. Kuma da ace ita ce take wannan da yanzu ta daɗe da kaiwa Mummy labari. Tun da ta haɗu da Salman shikenan komai na ta ya ƙara komawa baya, bata ji bata gani idan ba Salman ba. Ita kuma tana jiye mata masifar da za ta janyowa kanta domin tasan Mummy ba ƙyale ta za ta yi ba.

****

Tun da Hajiya ta yiwa Aunty Ziza gargaɗi akaina tun daga wannan lokacin na samu sassauci. Ba ruwanta da ni irin haka muddin dai ba wani aikin take so ba, kuma shima ba na irin takurawar nan ba kamar na da.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull