Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 27

Ganin ido complete - Chapter 27

Ganin ido complete Chapter 27: Ganin ido complete Chapter 27. "Mummy Hassana fa bata nan! Sannan kalla kiga takardar da ta ajiye akan gadonta...."

3,360 words

"Mummy Hassana fa bata nan! Sannan kalla kiga takardar da ta ajiye akan gadonta...."

Wani irin fisge takardar Mummy ta yi da ƙarfi ta fara karantawa kamar haka.

"Mummy... Daddy... Aunty Aysha...er uwata...Yaya Hafiz da ma duk wani wanda yake da haƙƙi akaina... Ina mai neman gafararku, na tafi wurin da zan samu farin ciki, tunda har baku damu da damuwata ba, ku dukiya kuke so ni kuma farin ciki nake nema,saboda haka ni na nemawa kaina mafita,kuma kada ku ce za ku wahalar da kanku wurin nemana domin har abada ba za ku sameni ba. Na bar ku lafiya...Hassana Mudassir Wazeer."

Wani irin gigitaccen ihu Mummy ta buga lokaci ɗaya tare da zubewa zuwa ƙasa somammiya. Cike da tashin hankali Su Aunty Aysha suka kwasheta sai asibiti.

*********

Ina cikin Kitchen ina haɗawa Hajiya kwaɗon zogale! Na ji muryar Ya Emraan a bayana a hankali ya ce.

"Lady B..."

Waigowa na yi muka haɗa ido da shi cikin sauri na sauke nawa idon a ƙasa a darare na ce.

"Ina wuni!"

"are you sure cewa wuni ne yanzu Lady B..." Ya ƙarashe maganar yana mai duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa sannan ya sake Kallona ya ce.

"11am ce fa yanzu.."

"Ina kwana.."

Murmushi yayi mini har ina iya jiyo sautinsa duk da cewa ban kalle sa ba ya ce.

"Zamu iya fita waje muyi magana?"

Jinjina kaina na yi ba tare da sanin wace wajen yake nufi ba. Ban gama digesting maganar tasa da kyau ba sai gashi ya ƙara so kitchen ɗin ya zura hannunshi ya ɗeba kaɗan ya kai bakin shi ya tattauna a hankali ya haɗiye sannan ya ce.

" It taste good....i will wait outside."

Ɗauka na yi bayan ya fice na kaiwa Hajiya zuciyata cike da fargaba ina gudun kada ta ji ya zo inda nake ta yi mini faɗa.

Bayan na ajiye mata na tashi na koma na ci gaba da aikina kawai na share shi.

Ina nan ina aikin sai ga Haulatu ta shigo tana faɗin.

"Dan Allah wai miyasa kike haka Beenafah? Ya Emraan ya ce mini yazo nemanki..."

Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalle ta na ce.

"Wai dan Allah Haulatu sau nawa zan faɗa muku cewa an yi mini miji a gida..."

"And so! Tun da har ba'a ɗaura ba ai ba za ki hana shi gwada sa'arsa ba..."

Hannuna ta janyo ta kaini wani kyakkyawan lambun da yake zaune a ciki wanda ban taɓa sanin da shi ba a gidan. Wuri ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali.

Jikin wata flower na ɗan jingina kaɗan tare da kama ganyenta ina murzawa a hankali.

" A tsaye kike so muyi maganar?... To ba damuwa..."

Daga haka ya miƙe tsaye ya matso inda nake wanda har ina iya shaƙo daddaɗan ƙamshinsa, a hankali na ji bugun zuciyata ya fara sauyawa wanda har sai da na ja baya kaɗan ina mai ɗago idona na kalle sa.

Kwalin waya ya miƙo mini yana faɗin.

" Ga wayar ki da na fasa...ina fata za ki yafe min?"

Girgiza kaina na yi na ce.

"A'a kabar shi..."

"Ki karɓa mana. Rashin karɓar wayar nan zai sa na ji ba daɗi a raina."

Jin hakan yasa na amsa kawai amma ba da nufin amfani da ita ba.

"Yaushe kike so na zo gida wurin maganarmu? Yau?... Gobe..jibi??"

Shiru na yi ina jin tambayarsa mai kama da tatsuniya domin babu abu guda ɗaya da zai samu daga gare ni.

"Lady B...lokuta da dama a rayuwa, shiru ya kan zama amsar da ba'a buƙatar ƙarin bayani a cikinta. In Sha Allahu ranar Juma'a mai zuwa, za a je nema mini auren ki. Ina son ki sosai, na yi alƙawarin kare ki da dukkan ƙarfina, na yi miki alƙawarin farin ciki iya yanda zan iya..... "

Cike da wani iri a raina na girgiza masa kaina tare da motsa laɓɓana tamkar ana mini dole na ce.

" Kada ka bari hakan ya girmama a ranka, domin an riƙa an zaɓa mini mijin da za'a aura mini nan da wasu kwanaki..... "

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 27*

Cikin rashin ɗaukar zancen na wa da muhimmanci yasa shi murmusawa yana mai jinjina kansa a hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe su a kaina ya ce.

"Lokaci ne kaɗai zai tabbatar da hakan Lady B.....kuma In Sha Allahu dani za a yi shi matuƙar dai ba ke ce za ki ce a'a ba..."

Juyawa na yi na bar wurin na wuce kai tsaye ɗakinmu na jefa ledar wayar a kan katifa na koma na ci gaba da abunda nake.

*********

Tudun Wada, Zamfara State, Gusau, Nigeria.

" Look Ziza! Ni fa ko kaɗan bana nufin ƙuntatawa a gareki.... "

Cikin gunjin Kuka ta katse shi da faɗin.

"Baka nufin ƙuntatawa a gare ni amma kake neman auren House Maid Emraan...Wannan wane irin ƙasƙanci ne da rashin daraja... Yanzu kai baka ji kunyar hakan ba? Miye na yi maka? Auren namu kwata-kwatansa kwana nawa ne? Ni za ka wuƙalanta? a gabana fa ka buɗe bakinka ka ce wai ka samu matar aure, alhali an ce ko mutuwa tana kunya idon mahaifi...Amma haka ka nuna bani da wata daraja ko wata ƙima kenan..... "

" No..no..please Ziza,wallahi that's not what I meant...ko kaɗan ban faɗi haka wai don in tozarta ki ba ko kuma wulaƙanci... I love you... I love you so much Ziza kuma hakan ba zai taɓa canza wa ba, ke ɗin matar rufin asiri na ce kuma ina matuƙar alfahari da hakan domin tsawon zamanmu ban ga wani babban kuskurenki da zan ce Allah wadai ba...please try to understand me Ko kaɗan ban da nufin wuƙalanci a gare ki.. In fact gidanki daban na ta daban...Babu wacce zan wulaƙanta kuma ba zan bari wata ta wulaƙanta wata ba a cikinku,... And kasancewar ki babba, dan Allah let's peace and harmony reigns between us...... "

Cike da jin wani irin sabon baƙin cikin ta girgiza kanta ta katse shi da faɗin.

" Emraan ko a ƙarƙashin ƙasa za ka sakata wannan duk a banza domin ba'a canzawa tuwo suna, muddin ka aureta ta riga ta zama kishiya ta kuma wallahi tallahi na rantse da Allah hakan ba zai faru ba domin baka isa ba wallahi!!!"

Jinjina kansa ya yi yana mai jin wani irin ɓacin rai ya ce.

" Haka ki ka ce ko?"

" Eh haka na ce Emraan!"

Miƙewa ya yi tsaye kamar yanda ta tsaya a kansa suna fuskantar juna ya ce.

" To bari ki ji Aziza...Tun da har na biki da lalama kuma baki saurare ni ba, shikenan! Zan yi aure, kuma zan auri Beenafah, dan Allah idan kin isa ki hana. Zaman lafiya akace ya fi zama ɗan sarki... Da wannan yasa nake so mu yi komai cikin ilmi da wayewa..."

Wani irin matsanancin kuka ne ta sake fashewa da shi tana faɗin.

" Haka ka ce? Haka ka ce ko? Wallahi tallahi za ka gani! Matuƙar dai na amsa sunana ni Ziza Ashraf wallahi tallahi ba za ka aureta ba... "

Zaunawa ya yi a hankali ya janyo glass cup ɗinda ta kawo masa ya tsiyaya lemu da nufin sha amma cikin zafin nama ta saka hannu ta ture kayan gabaɗaya suka watse a ƙasa suka tarwatse.

Miƙewa ya yi kurum ba tare ya ce mata komai ba yasa kai ya fice daga gidan gabaɗaya.

Wayarta ta ɗauko hankali a tashe ta kira wayar Mummy Raliya. Tana jin ta ɗauka a gigice ta ce.

"Mummy na shiga uku na lalace Mummy.... Wai Emraan kishiya zai mini kuma kishiyarma 'ƴar aiki..."

Daga can ɓangaren Mummy Raliyar ta ce.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!....Please cool your mind...Samu wuri ki zauna ki kurɓa ruwan sanyi sannan ki yi wannan addu'ar; ki ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirni fiy-musibati-Wa Akhlufni khairan minha...please ki yi yanda na ce miki yanzu, idan kin kambala sai ki kirawo ni muyi magana. "

A gaggauce ta aikata duk abinda ta ce mata exactly sannan ta sake ɗaukar wayar ta kira ta ta ce.

" Mummy na yi duk abin da kika ce...."

A hankali ta jinjina kanta ta ce.

" Masha Allah, In Sha Allahu ko mine ne zai zo miki da sauƙi... "

" Mummy kishiya fa na ce miki Emraan zai mini kuma da mai aiki..."

"Duk na ji! Amma ki sani, tashin hankali ko wani barazanar ki ba zai sa ya sauya ba, in dai ma namiji ne sai da ya ƙara miki baƙin ciki akan baƙin ciki muddin kika ce ba za ki shafawa kan ki ruwa ba.....Hajiyarsa ta sani?"

Ido cike da ruwan hawaye ta ce.

" Hajiya bata sani ba, na tabbata bai isa ya faɗa mata wannan abun kunyar ba...."

"To Labiba fa?"

Cikin jin wata irin tsanar Labibar a lokaci ɗaya ta ce.

"Ya sanar mata, dole ita zai sanarwa tunda ita ce babbar munafukar da ta kawo yarinyar gidan na su wai da sunan mai aiki, wallahi tallahi wannan munafukar yarinya daman ba ta yi kama da mai aiki ba kawai dai munafurci suka shirya wanda tun farko ban gane ba ma sai yanzu... "

" Duk da haka dai, ki bari abi komai a sannu Ziza, tashin hankali babu abinda zai haifar idan ba ƙarin matsala da ɓacin rai ba... "

Cikin wani irin kuka ta shiga girgiza kanta tana faɗin.

" Ai na san haka za ki ce Mummy....daman nasan haka za ki ceee... "

Daga haka ta yanke wayar tare da jifa da ita a ɗayan kujerar da take zaune.

********

Sai da Mummy ta share kusan kwana uku a asibiti, ta suma ta farfaɗo ta suma ta farfaɗo haka ta dinga yi sai daga ƙarshe suka samu aka samo kanta da ƙyar sannan suka tattara suka dawo gida.

Gabaɗaya ta susuce ta gigice ta fita hayyacinta, ko kaɗan ko a mafarkinta bata taɓa zaton cewa wai Hassana za ta iya bijire mata ba har da haɗa kayanta ta tsere. Wannan wane irin tozarci ne da abun kunya?

Tana zaune Aysha na ta aikin ba ta baki ta ɗago idanuwanta da suka rine sosai suka yi sasul akan kuka ta kalli Ayshar ta ce.

"Aysha duk an bincika ko'ina ba'a ga Hassanar ba har yanzu? Ko ba'a je neman ta ba ne? Ina Alhajin yake?"

Cikin tausasawa Aysha ta ce.

"Mummy ki kwantar hankalinki In Sha Allahu za a ganta..."

Hannu ta saka da ƙarfi ta ture kofin shayin da Husaina take bata tamkar wata mai taɓin ƙwaƙwalwa ta shiga kallon su tana faɗin.

"In kwantar da hankalina kike cewa Aysha?? Miyasa kike yin wasu abubuwan da yasa nake jin kamar bakya ƙaunata? Kin san irin kalar alƙawarurrukan da ke tsakaninmu da gidan Alhaji Mansur ɗin idan har wannan auren ya tabbata? Ni karan kaina akwai wani kamfaninsa da ya yi alƙawarin mallakamin, suma su Hassana akwai abubuwa da dama da za su mallaka na manyan kadarori,...waccan jibgegiyar motar da kika gani fa sabuwa tare da lefen nan aka kawo Alhaji ita kyauta, an ce ta amaren da tawa suna hanya...sannan har cikin shares ɗinsa ya yi alƙawarin mallakawa Alhajin da kuma Hafiz wasu daga ciki da zaran an yi auren kafin nan kuma Hafiz ya iyarda kambala karatun sa ya dawo..."

"To Mummy idan ban ce ki yi haƙuri ba mi zan ce? tun fa ranar Daddy ya aika har garin su Salman ɗin amma ba'a samu labarinta ba, har kulle Salman ɗin akayi sai jiya aka sake sa amma kuma shi kan shi an yi duk binciken da za'a yi amma bai san inda take ba. Gida ma duk su Alhaji Baba su Uncle Isma'il kowa ya ce bata je wurin sa ba... "

Girgiza kanta take tamkar wata mahaukaciya tana faɗin.

" A'a, wallahi tallahi wannan ƙarye ne... Wayyo Allah na! Wayyo ni Zaliha! Hassana ta tona mini asiri, na shiga uku na lalace..."

"Innalillahi! Dan Allah mummy ki yi haƙuri. In sha Allahu za a gano inda take..."

"Ina Alhaji yake??"

"Daddy tun safe ya hau jirgi zuwa Australia an yi mishi kiran gaggawa daga makarantar su Hafiz."

Komawa ta yi luf ta kwanta jikin kujera kamar wata marainiya tana mai share hawaye akai-akai abin duniya duk ya bi ya isheta.

*******

Tun da Daddy ya karɓi saƙon gayyata ta gaggawa through Email ɗinsa daga makarantar su Hafiz hankalinsa ya tashi, gabaɗaya ko baccin kirki ya kasa yi akan wannan dalilin, kwana ya yi yana tambayar kansa miye ya faru da har ta kai aka aiko masa da official letter of misconduct? Miye Hafiz ɗin zai aikata haka da zafi? Yaron kirki mai matuƙar basira miye zai faru haka? Tambayoyinda ya yi ta jerawa kansa kenan daga cikin zuciyarsa waɗanda yasan tabbas ba shi da amsar su sai dai idan ya isa makarantar ya gani ya kuma jiye ma kunnen sa.

A hankali ya taka ya shiga Main Admin block ɗinsu Wanda daga nan reception aka dangana shi da office ɗin vice Chancellor Mai suna Professor Dean Michael inda a nan ya tarar da Head of academic, Register, Discipline committee, sauran head of department da kuma sauran lecturers wanda daga cikin su akwai Mr. Collins.

Gefe ɗaya kuwa, Hafiz ne tare da sauran ɗalibai en uwansa su takwas.

A hankali Daddy ta taka ya je ya samu ɓangaren inda sauran iyayen yaran suka zauna shima ya zauna riƙe da file ɗinda aka bashi tun daga Reception ɗin.

Vice Chancellor ɗin ne ya fara magana cikin harshen turanci cike da girmamawa ya ce.

" Good afternoon all, muna yi muku barka da zuwa kuma mun gode muku sosai da har kuka iya amsa gayyatarmu akan lokaci kuka halarta daga sasassa daban-daban na faɗin duniya. Muna fata kuma za ku bamu haɗin kai domin gudanar da abin da ya tara mu a nan cikin girmamawa da mutuntuwa....."

Bayan sun gama gudanar da duk wasu bayanai da tsare-tsaren su sannan Mr. Anderson daga Discipline committee ya janyo file ɗinda ke gaban sa ya buɗe shi ya fara bayani da cewa.

" Mun kira ku nan ne akan manyan laifukan da aka kama yaranku sun aikata, waɗannan laifuka ne da suka shafi both academic and moral standards na wannan makarantar."

Tsit ɗakin ya yi tamkar ba kowa a ciki tsabar yanda daga yaran har iyayensu suka sha jinin jikinsu, ba ma kamar Hafiz ɗin.

A hankali ya ci gaba da cewa.

"Waɗan nan laifukan su ne waɗanda muka same su da su bayan yin ƙwaƙwƙwaran bincike yanda ya kamata tare da tuhumar yaranku akan laifin kuma suka amsa ba tare da sun musa mana ba, Hafiz Mudassir Wazeer; Laifinsa na farko akwai academic fraud. Hafiz ya haɗa baki da Mr. Collins ya biya sa kuɗi masu yawa ya shirya masa false academic records na fake result ɗin semesters shida, wanda ya nuna yana da high scores amma kuma bayan biyar diddiƙi na ainahin result ɗinsa mun gano ko wace semester GPA ɗinsa is below 1.50 GPA. Laifi na biyu kuma shine;Bribery and corruption. Ma'ana mun samu ƙwararan shaidu da suka nuna cewa Hafiz yana turawa Mr. Collins maƙudan kuɗaɗe akan ya riƙa canja masa result ɗinsa a kowace semester. Sai kuma na uku, wanda dukkan su ne ta shafa har da sauran waɗan nan ɗaliban na Repeated misconduct, An sha kama su ana kawo mana ƙarar su daga security campus a wuraren da bai kamata ba, suna shaye-shaye,lalata da yaran mutane, da kuma gurbata rayuwar salihan ɗalibai zuwa mutanen banza. Sun kasance suna yawan shirya abubuwa waɗanda suke taka mana dokar makaranta,sannan ga rashin girmama malamai da yi musu rashin ɗa a. Na huɗu kuma;Akwai poor academic performances Wanda for the past four semesters Kowanne daga cikin su ya yi failing Registered courses da Kuma missing five official exams without any genuine reasons. Sai abu na ƙarshe kuma;Forgery of official document. Ma'ana, an gano cewa Hafiz yana printing fakes progress reports yana aikawa gida Nigeria yana yaudarar iyayensa da sunan shi ɗin mai ƙoƙari ne alhali ba haka bane."

Cikin tashin hankali kowa ya hau faɗin albarkacin bakin sa, cike da baƙin cikin abin da yaran na su suka aikata musu bayan sun jima suna kashe musu maƙudan kuɗaɗe. Wasu irin hawayene masu matuƙar ɗaci da ƙuna suka gangarowa Daddy wanda ya ƙura ido kawai yana kallon Hafiz.

Wata envelope ce Head of academic ya bi dukkan iyayen na su ya rarraba musu bayan an ba su dama cewa idan akwai mai wani ƙorafi ya yi.

Bayan ya gama miƙa musu a hankali ya ce.

"Wannan ita ce takardar official expulsion, ma'ana;an kore su daga wannan makaranta. Muna fata za ku yafe mana domin dole ce ta sa muka aikata hakan."

Waje suka dawo wanda har yanzu ya kasa buɗe baki ya furta masa wata magana kamar yanda shi ma Hafiz ɗin ya yi tsamo-tsamo tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi. Kwata-kwata Hafiz bai tsammaci zuwan wannan ranar ba a rayuwar sa. Ya ɗauka cewa salin asalin zai gama baza life ɗinsa ya amshi fake result ɗinsa ya koma gida, ashe-ashe rana dubu ce ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya. Yanzu ga shi son zuciya da ganin kuɗi yasa ya rushe rayuwar sa, bama kamar yanda Mr. Collins ya dinga kuka bayan shi ma an kore sa shi ne abinda ya tsaya masa a rai. Duk irin yanda Mr. Collins ɗin ke ta baya-baya gashi sai da ya jefa shi a matsalar da yake gudu.

Suna nan tsaye sunyi cirko-cirko sai ga motar jami'ai ta iso wurin, a gaban iyayen na su aka ɗauke su zuwa office ɗin immigration domin a fitar da su daga ƙasar Australia cikin kwanaki uku da kuma izinin cewa kada su sake dawowa ƙasar har abada kamar yanda dokar ta su ta tanada.

*******

Jafaru kuwa, yana Zaria ƙaninsa Hamza ya kira shi yana ƙyanƙyasa masa halin da ake ciki na cewa, idan bai dawo ba wallahi sai an aurar da Beenafah ga Ashiru domin har sun zo shi da iyayensa wurin neman auren na ta.

A gigice ya baro Lectures ya juyo ya dawo gida.

Ita dai Mama tana zaune ita da Bahrain da Farisa suna ƙulla guggurun da ta gama yi yanzu taga mutum ya shigo mata hankali ta she yana faɗin.

"Yanzu Mama Beenafahr tawa ce ake zancen a aurawa wani ita? Mama wai ko don ban taɓa faɗa muku bane ina sonta?Wallahi tallahi ina son ta, babu wacce nake so a cikin raina idan ba ita ba, dan Allah Mama ki faɗawa Baba wallahi ita nake so na aura..."

Hannu Mama ta miƙa masa hankalinta kwance ta ce.

" Bani kuɗin sadakin ka, lefe, sannan ka nuna mini gidanda zaka ajiye ta...."

Shiru ya yi tare da ƙura mata ido domin ya rasa bakin magana. Kwata-kwata shi bai tsammaci wannan magana daga bakin ta ba.

"Ka yi shiru! Bani sadaki da lefe na ce, sannan ka nuna mini gidan da za ka sakata a ciki, da kuma sana'ar da kake wacce za ka iya riƙe ta sannan kuma ka ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ka...."

Gunguni ya fara ƙasa-ƙasa yana faɗin.

"To amma ai Mama komai na duniya ɗan a hankali ne..."

Jinjina kanta ta yi tare da ƙara tamke fuska ta ce.

"Allah ko! To ai tun kafin a haifeka na san cewa komai na duniya ɗan a hankali ne.... Tabbas da ace kana da waɗannan abubuwan da na lissafa da dani da Malam ko sama da ƙasa za ta haɗe sai mun tsaya akan dugaduganmu mun tabbatar cewa ka same ta....amma yanzu Jafaru magana ta gaskiya ka yi tsaga da faɗi. Da ma ace itama karatu take kamar kai, da na san tabbas za ku iya yin daidai... "

" To Mama dan Allah a sakata makarantar mana, sai mu jira juna ni da ita... "

" Jafaru! Jafaru! Ka wuce ka mayarda hankali akan karatunka ko dan goben ka, ka sakawa kanka salama domin ba za ka taɓa samun Beenafah ba... "

Cike da wani irin ƙunci da damuwa ya ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull