Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 28

Ganin ido complete - Chapter 28

Ganin ido complete Chapter 28: Ganin ido complete Chapter 28. " Dan Allah Mama ki fahimtar da su cewa su mayarda ita a makaranta wallahi na san zamu yi…

3,301 words

" Dan Allah Mama ki fahimtar da su cewa su mayarda ita a makaranta wallahi na san zamu yi daidai.. "

Jinjina kai ta yi ta ce.

" To je ka ka fahimtar da su Jafaru."

A nan ya yasar da jakar sa da yazo da ita ya fito afujajan ya nufi gidan Ammie ransa na masa wata irin suya.

Ammie na tsaye tana shanya kayan Bahrain a igiya ya yi sallama ya shiga.

Kallo ɗaya Ammie ta yi masa ta fahimci kwanan zancen, daman ta san tabbas za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya.

Ido a rufe ya fara masifa da faɗin.

"Ammie miyasa za a nemi bayar da Beenafah alhali ni ɗin ina sonta?? Wannan ba adalci ba ne, babu wanda zai aure ta ya kula da ita fiye dani,..."

Jinjina kai tayi cikin tausasa murya ta ce.

"Na sani Jafaru....amma samu wuri ka zauna mu yi magana."

A nan inda yake tsaye a nan ya darɓe zaune yana mai ƙure ta da kallo alamar yana jira ya ji mi za ta faɗa masa.

Kujera ta janyo ta zauna suna fuskantar juna cikin ƙara tausasa maganarta ta ce.

"Na san cewa kana son Beenafah, na fi kowa sanin yanda kake sonta,kuma idan har Allah ya rubuta cewa Beenafah matar ka ce, to babu wani mahaluƙinda ya isa ya hana, idan kuma Allah ya rubuta cewa ba matarka ba ce duk yanda aka so ba za ka aure ta ba. Abubuwan sun juye fiye ma da yanda muka tsammata Jafaru. Kuma ina neman alfarma a gareka....kamar yadda ka ji tana cewa tana da matsayi a gareka na soyayya, to ina so ka sake bata wani ɓangaren a zuciyarka na zamto wa ƙanwa a gareka, ka ɗauketa tamkar Fakiha wacce duk rintsi za ka tsaya mata a matsayin Yayanta mai kare mata mutuncin ta. Idan har Allah ya nufe ka da aurenta ba ni da ja da hakan, idan kuma ya ƙaddaro cewa wani daban ne za ta aura to za ka yafe mata ku ci gaba da zumunci. "

A hankali kukan da yake riƙewa ya kubce masa da ƙarfin gaske tamkar wata Macce. Tashi ta yi taci gaba da abin da take ba tare da ta yi yunƙurin hana sa kukan ba. Sai da ya yi sosai wanda har sai da ya ji zuciyarsa ta ɗan sanyaya sannan ya sassauta tare da miƙewa a tsaye ya kalle ta murya a dusashe ya ce.

"Na gode Ammie, idan Beenafah rabona ce ina fata Allah ya mallaka mini ita, idan kuma ba rabona ba ce ina yi mata fatan alheri da fatan farin ciki mai ɗorewa har zuwa ƙarshen rayuwarta."

Daga haka ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar ta ba. Jikin gini ta tsaya shiruu! Tana jujjuya al'amarin a zuciyarta, wallahi tallahi ta yi matuƙar tausaya masa a yau kamar yanda take tausayawa Ashiru. Duk irin amsar da shima ta bashi ya ce sam ba zai haƙura ba, ƙarshe ma cewa ya yi ta bashi numbern Daddy da address ɗinsa shi zai je har Abuja ya same shi. Jin ya matsa ya dage akan dole sai ta bashi yasa ta ce yaje tsohon gidanda suka taso wurin Uncle Isma'il ya bashi numbern Daddyn da address ɗinsa.

*********

Ziza kuwa, tun da Emraan ya sa ƙafa ya bar gidan bata sake sanya shi a idonta ba, kiran duniya ta yi kuma ya ƙi ya ɗaga wayar ta. Gashi bata ma son haɗa fuska da Labiba ballantana taje ta koka mata halin da take ciki. Sannan ta yi tsammanin Hajiya za ta zo gidan ta sameta idan ta ganshi a gidan amma kuma ba ta yi hakan ba wanda shi ne abin da ya ƙara tunzura ta. Shawara take na ta kira Baba Ustaz Ƙanin Mahaifin Emraan ɗin ko kuwa ta ɗan ƙara jira ta gani.

Ƙarshe dai haka ta miƙe ido cike da ruwan hawaye ta ɗauki Abeer ta je ta shiga motarta ta wuce gidan Hajiya.

Tana shiga gidan ta wuce har bedroom ɗinta ta zauna a sofa ko gaisawa bata jira sun yi ba kawai ta fashe mata da kuka.

A hankali Hajiyar ta ajiye turarukan da take gyarawa ta zo ta zauna a edge ɗin gadonta suna fuskantar juna ta ce.

"Subhanallah! Ziza Lafiya kuwa?..."

Cike da damuwa ta ce.

"Hajiya yanzu abin da Emraan zai mini kenan? Ga mari ga tsinka Jaka! Sannan Hajiya ace kina ganin sa amma ba za ki masa magana ba..."

"Bayani za ki yi mini yanda zan fahimta Ziza, go straight to the point please."

"Hajiya Emraan ne ya sameni da zancen wai zai ƙara aure, kuma auren ma da Beenafah wanda na san bai faɗa miki ba, to wai don saboda na nuna rashin amincewa ta shi ne ya baro gidan ya dawo nan yau tsawon kwana biyu cikin na uku. Yanzu Hajiya dan Allah hakan adalci ne?"

Girgiza kai Hajiya ta yi tana mai kallon ƙwayar idanunta ta ce.

" Magana ta gaskiya, na san da zancen auren amma kuma ban san cewa yana gidan nan ya yi miki ya ji ba tsawon kwanaki... "

Wani iri dummm! Ta ji a ƙirjinta tamkar an soka mata Mashi jin furucin Hajiya a gareta...Yanzu kenan tasan da zancen auren na shi kuma shi ne take zaune hankalinta kwance?

" Ki yi haƙuri, In Sha Allahu zan mi shi magana... "

Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye ranta na mata wata irin suya a gigice tana kallon Hajiyar ta ce.

"Yanzu Hajiya abin da ma za ki ce kenan, duk irin ƙuntatamin da ya yi ya bar ni tsawon kwana biyu sannan ga zancen auren da ya yi duk baki ga wani laifin sa ba, abin da zaki ce kawai shi ne in yi haƙuri za ki masa magana! Ba za ki kira sa a gabana gani ga shi ki yi mana hukunci ba? Ya rasa wacce zai aura sai Mai aiki? Wallahi tallahi ba zan yarda ba! Wallahi ba zan yarda ba... "

Daga haka ta juya ta bar gidan gabaɗaya ta koma gida ta shiga haɗa kayan ta.

Hajiya kuwa, Wayarta ta janyo cike da al'ajabi ta shiga kiran Emraan ɗin amma kuma bai ɗaga ba. Mamaki take wai ace Emraan yana gidan tsawon kwana biyu ba tare da ta sani ba, jiya ya shigo da yamma, shekaranjiya ma ya shigo da dare amma kuma duk bai wani jima ba ya tafi. Bayan ta yi ta kiran wayarsa bai ɗaga ba, ƙarshe ta fito da kanta ta je ɗakinsa amma kuma baya nan babu wata alama da ta nuna mata ma cewar yana gidan. To ko dai wani wurin ya je ba nan ba?

Da haka ta sake juyawa ta koma ciki ta ci gaba da ayyukanta. Tunani take a ranta cewa tun da har taji hatta Hairiyya bata kira ta akan wannan maganar ba to ta tabbata babu wacce ya sanarwa daga cikin su, daga Labiba har Nadeeya babu wacce ya sanar wa. Saboda haka so take sai ta fara magana da shi sannan ta san irin hukuncin da ya kamata ta yanke.

Ta na nan dai Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, ganin har yanzu bata samu magana da Emraan ba kuma shi bai zo ba yasa ta ɗaga waya ta kira Haula ta ce mata ta faɗa mini cewa tana son ganina yanzu.

Ina zaune bayan na kambala sallah na yi shiru ina nazari. Baccin da na yi ne mai nauyi har yasa na makara wurin gabatar da sallar Zuhr ɗin. Suna zaune a gefe suna cin abinci Hajiya ta kira ta ina ji ta ce tana son ganina.

Kallona Haula ta yi ta ce.

"To tunda kin ƙi kici abinci ta shi kije Hajiya tana neman ki."

Miƙewa kawai na yi na fito waje na samu wuri na zauna tsawon lokaci, sannan daga ƙarshe na tashi na shige cikin gidan ba tare da sanin dalilin kiran ba, sai dai kuma ban kawo komai a raina ba domin tun ina jin ɗar-ɗar na cewa za ta yi mini magana akan Emraan, ko ita ko Aunty Labiba har na zo na daina damuwa domin a tunanina shi ka ɗai ne yake shirmensa ba tare da kowa ya sani ba. Sannan kuma sanin cewa Daddy ya ce zai aurar dani ga Ilyas yasa na daina damuwa da al'amarin Emraan ɗin domin nasan Ihu ne kawai yake bayan hari, domin tun da Daddy ya furta, to kuwa nasan tabbas zai cika.

A hankali na tura ƙofar tare da yin sallama na shiga na zauna a ƙasa ina faɗin gani. Sai dai kuma, ganin mutanen da ke zaune a ɗakin ne ya yi matuƙar ɗaga mini hankali ganin babu mutum ƙwaya ɗaya da na sani a cikin su sai Hajiyar.

Wayarta dake gefe ce ta shiga ɓurari ba ƙaƙƙautawa. Sai da tayi kamar ba za ta ɗauka ba sannan kuma daga ƙarshe ta janyo ta duba,ganin sunan babbar ƙawarta Hajiya Samira dake zaune a Lagos, yasa ta yi saurin ɗaga wayar tana faɗin.

"Ziza ta kawo ƙara ko?"

Dariya matar ta yi daga can ɓangaren ta ce.

"Kamar ko kin sani! Yanzu ta kirani tana shaida mini shi ne na ce ta jira zan kira ki yanzu..."

Miƙewa tayi tare da ɗaukar excuse a wurinsa ta fice daga parlourn domin amsa kira.

Suna ganin ta fice suka juye baki suka yi ta magana da turanci wanda na san hakan ba ya rasa nasaba da wanzuwata a ɗakin domin kada in ji mi suke faɗa.

Sun ɗauki tsawon lokacin da yakai hour ɗaya cikin ta biyu suna magana wanda ban san abinda ya tsayar da Hajiya waje ba har yasa bata dawo ba. Fira suke wacce ta gigitani da kuma ɗaiɗaiɗaita tunanina, firar da ta shigar dani cikin tsananin duhu da ruɗanin neman ƙarin bayani dangane da abubuwan da kunnuwana suka jiye mini, zuciyata ce ta tsinke! Tunanina ya juye! Hankalina ya yi tashin gwauron zabin da ban san ma miye ya kamata na yi ba. Miye wannan suke magana akai? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai miyasa duniya ta dawo haka ne? Miyasa cin amana da zalunci ya zama kamar shan ruwa a wurin wa su?.

Miƙewa na yi jikina na rawa na sulale na bar ɗakin, domin akan maganar ta yi masu daɗi, dariya suke suna ta kekkewa hankalinsu kwance.

Tafiya nake amma a matuƙar gigice nake, domin bana kallon ma inda nake jefa ƙafata tsabar tashin hankalin da nake ciki, har na kai gida na faɗa ɗaki na kwanta ina mai rushe wa da kuka ban san miye yake damuna ba, jikina sai wata ciccira yake tamkar wata mai sabuwar cutar jijjiga.

Ammie da kambala sallar ta kenan tayo kaina da gudu tana mai janyoni jikinta hankali tashe tana faɗin.

"Lafiya Beenafah! Miye ya faru dake?"

Girgiza kaina na shiga yi ina kuka ina faɗin.

"Ba komai... Ba komai Ammie! zazzaɓi ne kawai nake ji... Zazzaɓi mai zafi sosai... Taɓa jikina ki ji ya yi zafi sosai Ammie.."

Da sauri ta kawo hannunta zuwa wuyana zuwa goshina. Cike da tashin hankali ta ce.

"Wai Beenafah dan Allah ba za ki tausayawa kanki ki ɗau dangana ba? Ke ce fa kike mini nasiha akan kada in damu da komai in yi haƙuri Allah yana sa ne da komai..."

Haka ta ɗauki tsawon lokaci tana lallashina tare da bani baki a hankali har ta samu na natsa da kukan da nake yi ba tare da amsa mata ko da magana ɗaya ba.

Duniya ta bani mamaki, matuƙar mamaki wanda har yanzu ba ta daina ba, domin kullum kwanan duniya akan bani sabon darasi take kamar ko yaushe.

Yanda na ga rana haka na ga dare domin ko kaɗan ban samu na runtsa ba, tunane-tunane kawai na ke da neman mafita. In saƙa in warware in saƙa in warware haka nai ta yi har gari ya waye.

Ina tashi na yi sallah na fito da nufin aiki sai Ammie ta hanani ta ce na koma na kwanta, ko gidan aikina ba zan je ba domin rashin lafiya ya kauda komai, sai da lafiyar ake iya yin wani kataɓus saboda haka na koma na kwanta abina.

A yanzu, ba saurarar maganar ta ce a gabana na ba, domin ni sam ban ga ta zama ba. Hakan yasa ban ko bi takan wanka ba na ce mata dole sai na fita domin akwai ajiyar da Hajiya ta bani kuma nice kaɗai zan iya ɗauko wa daga inda na ajiye, ga shi za ta yi asuba zuwa Kebbi, saboda haka dan Allah ta barni in tafi in bata saƙon daga baya sai in dawo tunda babu wayar da zan kira in shelanta musu uzurina.

Ko makaho ya shafa yanayin da nake ciki yasan bana cikin hayyacina, ta dalilin damuwata da ta gauraya da wata gingimemiyar damuwar da ban san ma ta ina zan fara ba. Gidan Aunty Labiba na nufa ba tare da jin wani ƙiren tsoro ba na ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin.

Kallona Mai gadin na su yayi ba tare da ya gane ni ba ya ce.

"Malama ke wacece kuma wa kike nema?"

Kai tsaye na ce.

"Wurin Aunty Labiba na zo, dan Allah kira ta kace ta yi baƙuwa..."

Agogon ƙaramar wayarshi ya duba yaga cewa bakwaice yanzu na safe da mintuna tara. Cike da zallar mamaki ya ce.

"Ina fata dai lafiya?"

"Lafiya lau, ka kirata ka ce mata Beenafah ce."

Wani irin kallon ne ya jefa mini, kamar zai yi magana sai kuma bai yi ba ya ɗauki wayar ya kira ta kusan sau huɗu amma bata ɗaga ba, mita ya fara akan bata tashi ba kuma ƙarshe ma in ja masa ayi masa faɗa. Ni dai ina tsaye na yi shiru duk abin duniya yabi ya ishe ni. Ina nan ba tsammani daga ƙarshe na ji ya ce in shiga tana ciki ta ce in shigo.

Ina tura ƙofar parlourn na sameta tsaye sanye da kayan baccin ta dogaye har ƙasa ta ƙura mini ido cikin tashin hankali ta ce.

"Lafiya Beenafah?"

Hawayen da suka silalo mini ne na share sannan na jinjina kaina na ce.

"Shin zamu iya zaunawa muyi magana ta fahimta Aunty Labiba?"

Da sauri ta jinjina kanta tana faɗin.

"Of course dear...zo mu shiga wancan parlourn..."

Ta ƙarashe maganar tana jan hannuna da sauri muka shige parlourn ta rufe ruf da key muka zauna a kujera ɗaya gab da gab ta ƙura mini ido tana faɗin.

"Miye ya faru haka Beenafah?"

Still da ruwan hawaye a idona ina kallonta kamar yanda take Kallona na ce.

"Wane ne Muhammad Aunty Labiba???"

Wata irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tare da lumshe idanunta ta buɗe sannan ta yi wani murmushi mai gauraye da ruwan hawaye a lokaci ɗaya ta ce mini.

"Yaya MOHAA! Shi ɗin Yayana ne, Shi ne babban Yayanmu..."

Kafin ta iyarda rufe bakinta na gyaɗa kaina na ce.

"To Ina so na aure shi!!!"

Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye har saida na ɗan tsorata ta kalleni hankalinta a tashe ta ce.

"Kin san mi kike faɗa kuwa Beenafah???"

Gyaɗa kaina na yi ina kallonta na ce.

"Na sani!!..."

Girgixa kai ta shiga yi tana faɗin.

"A'a, baki sani ba Beenafah....gaskiya baki sani ba.."

"Aunty Labiba ina sane da komai, a hayyacina nake, kuma shi nake so shi zan aura..."

Wani irin kuka ne ta fashe da shi wanda ya sarƙafe zuciyata da matsanancin ruɗani da tsoro. Shiru ɗakin ya ɗauka na tsawon lokaci wanda daga ni har ita babu wanda ya yi magana sannan daga ƙarshe ta ɗago idanunta waɗanda suka jiƙe da ruwan hawaye ta kalleni tana mai girgiza kanta ta ce.

"Na sani, you are doing all this things don Kawai ki faranta mini kamar yanda na taimake ki ko? Hmm! Kada ki sakawa ranki abin da ba zai taɓa yiyuwa ba Beenafah. Ko ma a ina kika jiyo tarihin Daddyn Raudah, wannan bai dame ni ba, domin ba abun ɓoyo ba ne,amma kuma ki sani, ba za ki taɓa iya yin nasara ba..."

Wani kallon na yi mata na ce.

" Miyasa kika ce haka Aunty Labiba...Miyasa kike ganin kamar ba zan iya ba? A rashin tayi fa ake barin arha banza...ki barni na jaraba sa'a ta mana.!!!"

Wani irin murmushi ta yi mai sauti sannan ta girgiza kanta ta ce.

"Uhm! Beenafah kenan! neman aure sau ashirin da bakwai...goma sha uku daga ciki har ranar ɗaura aure sai an kai amma kuma a fasa, uku daga ciki hour ɗaya ce zuwa biyu yake ragewa a ɗaura amma kuma a fasa. Manyan mata, manyan 'ya' yan attajirai, har 'ya' yan sarakuna ma an nema, amma kuma ba a yi nasara ba. Ƙarshe kunya ce da baƙin ciki da kuma nadama suke mamaye farin ciki da ɗaukin da muke ciki a maimakon murnar auren. Mun haƙura, mun janye, idan har wannan ita ce ƙaddararsa muna fata Allah yasa jindaɗinsa da farin cikinsa su riskesa a aljanna firdaus idan yana da rabo.... Dan Allah kada ki sa ciwon da ya wuce a wurinmu na tsawon lokaci ki ce za ki sake fama mana shi.... "

Hannunta na riƙo cike da ƙwarin gwiwa na ce.

" Aunty Labiba ki yarda dani, in sha Allahu rabbi da izinin ubangiji wannan karon zamuyi nasara...dan Allah ina roƙon ki da ki amince kuma ki bani goyon baya dan Allah... "

" Beenaf... "

" Trust me.... In Sha Allah we are going to succeed.."

"But how??"

"Gobe za'a ɗaura mana aure. Amma kuma da sharaɗi?"

Wani irin kallo ne ta bini da shi mai cike da tsananin ruɗani da neman ƙarin haske ta ce.

"Sharaɗi Beenafah? Wane irin sharaɗi ne wannan?"

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 28*

"Sharaɗin shi ne; Daga ɓangarenku, daga KE sai SHI ɗin sai kuma waɗanda za su nema masa aurena ne kaɗai na amince kusan da wannan har sai an riga an ɗaura auren. Ina nufin ko Hajiya ban amince da ta sani ba....."

Wani kalar murmushi ne ta saki wanda iyakacin sa kan leɓenta sannan ta girgiza kai ta ce.

"Uhm!Beenafah kenan! In dai akwai biyan buƙata, ai rai ba a bakin komai yake ba. Ina ma ace wannan maganar da kike akan Daddyn Raudah ta tabbata Beenafah! Ina ma ace ba zan farka daga wannan daddaɗan mafarkin farin cikin dana riski kai na a ciki ba..."

"Wannan ba mafarki kike ba Aunty Labiba, ki yarda dani ki amince da maganata. In Sha Allahu gobe mafarkin ki zai cika.....you have done so much to me..Saboda haka ban ga wani dalilin da zai sa in kasa tsamo ɗan uwanki daga cikin rayuwar da yake ciki ba..."

"Shin kin san wane ne Yaya Mohaa kuwa? Shi ɗin ya rayu tamkar wani sarki a cikin babbar masarauta. Sai dai kuma ya fara bankwana da farin ciki ne daga lokacinda ya fara neman aure kusan sau huɗu amma kuma baya nasara. Da farko mun ɗauka cewa maƙiya ne ke yi masa zaƙon ƙasa, wasa-wasa har muka gano cewa ashe baƙar Aljana ce ta aure shi,wanda tun daga lokacin ne abubuwa suka ƙara lalacewa, Hajiya ta baza nema masa aure ba ji ba gani wanda ta kasa yin nasara a kai. Magani kuwa, babu ƙasar da ba'a je ba wurin nema masa magani ba..."

Jinjina kaina na yi ina mai bata tabbaci na ce.

" Tabbas a wannan karon zai yi nasara... "

Hannayenta ta haɗe wuri ɗaya alamar roƙo, cike da magiya ta shiga girgiza kai ta ce.

" Beenafah dan Allah! Dan Allah ki daina...wallahi ko a iya nan kika tsaya ba zan daina gode miki ba..."

Miƙewa na yi a zafafe ina ɗaga murya na ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull