Ganin ido complete - Chapter 29
Ganin ido complete Chapter 29: Ganin ido complete Chapter 29. " To amma miyasa? Miyasa kike neman hanani taimakawa mutumin da ya fito daga ɓangaren ki yana…
3,369 words
" To amma miyasa? Miyasa kike neman hanani taimakawa mutumin da ya fito daga ɓangaren ki yana mai matsanancin neman taimako? Shin ba ki yarda da cewa al'amarin Allah mai juyawa ba ne a duk lokacin da ya so? Shi ɗin fa mai iya juya al'amarin bawan sa ne daga farin ciki zuwa baƙin ciki ko kuma daga baƙin ciki zuwa farin ciki a duk lokacin da yaso....Kada ki ce za ki tsaurara Aunty Labiba please na roƙeki! Ki barni na gwada taimakawa ko Allah zai sa a dace... "
Jikinta ne ya yi sanyi jin irin kalaman da na ɗaure ta da su wanda daga ƙarshe bayan na dire ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ta share hawayenta a tausashe ta ce.
" Ba wai bana so ki taimaka ba ne Beenafah...akwai gagarumar matsala ne idan har hakan akayi yunƙurin gudanar da hakan...domin a neman auren sa na ƙarshe ne, Aljanar ta yi alƙawarin ganin bayan duk wacce ta sake yunƙurin amincewa da auren sa....Dan Allah Beenafah ki fahimce ni."
Cike da gardama na girgiza mata kai na na ce.
" Na ji na gani na kuma amince. Dan Allah ki ƙarfafa wannan abun ya tabbata daga yau zuwa gobe."
" To ai Beenafah shi karan kansa nasan ba zai amince ba.... "
" Zai amince Aunty Labiba, ke dai kawai ki kira shi ki masa bayani.."
Miƙewa ta yi sukuku ta fice ɗaga parlourn tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ta barni nan ina ci gaba da nazarin plan na gaba. Na jima tsawon lokaci ina jiran ta wanda har ta kai ga na cire rai kwatsam sai ga ta ta dawo riƙe da waya a hannunta,ban san ya suka ƙare da ita ba, tana shigowa ba tare da ta zauna ba ta kalleni fuska cike da alamun fargaba ta ce.
"Baba Ustaz zai ta so daga Abuja yanzu, In Sha Allahu zuwa 4pm na san duk daɗewar sa zai iso. Sai dai kuma, wannan sharaɗin naki ba Yaya Mohaa ba, hatta ni karan kaina na girgiza Beenafah....ta ya ya kike tunanin Yaya Muhammad zai yi aure ba tare da sanin Hajiya ba.... "
Murmushi na yi mata sannan na ce.
" Ba wannan sharaɗin ne buƙatar Hajiya ba Aunty Labiba... Iya farin cikin ɗan ta kawai ya ishe ta."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
" Haka ne kuma, to amma yanzu miye abin yi?"
" Gida zan tafi yanzu, ke kuma ki zo gidanmu zuwa an juma idan rana ta yi sanyi."
Fitowa na yi na baro ta kai tsaye ba tare da ta yi wani yunƙuri ba, da alama gabadaya gaɓoɓin jikinta sun sanyaya.
*******
Gidan Daddy kuwa, in banda ƙarar sautin kukan Mummy dake tashi a gigice, babu abin da ka ke ji.
Tun da Daddy ya dawo ya sanar mata wannan mummunar maganar take kuka. Juyin duniya an yi, amma taƙi ta yi magana da kowa musamman Hafiz ɗin, ko kallon in da yake zaune ta ƙi ta yi, ga shi har da Uncle Isma'ila shi ma ya zo tun jiya yana wurin.
Suna zaune a cikin yanayin shiru kowa abin da ya damesa ya damesa, sai ga wayar Daddy security sun kira, cewa ya yi baƙo daga jihar Zamfara.
Cike da zaƙuwa suka ba shi umarnin shigowa har ciki domin suna saka rai da tsammanin cewa, duk wanda zai zo to babu abin da zai kawo shi idan ba zancen Hassana ba.
Kallon shi suke tamkar idanuwansu za su zazzago ƙasa, bama kamar Mummy wacce ta ke jin tamkar ta miƙe ta buɗe zuciyarsa taga miye abun da ke tafe da shi.
Uncle Isma'il yana ganin shi ya wani zaro ido waje alamar mamaki ya ce.
"Kai ne ko? Wato dai duk jan kunnen da na yi maka baka ji ba sai da ka zo?"
Direwa ya yi akan ƙafafunsa ya durƙasa a hankali yana mai jinjina kai ya ce.
"Ni jan kunnen da ka yi mini bai dameni ba, buƙata ta ɗaya ce dan Allah ku amince min ku tausaya mini ku bani Beenafah, wallahi tallahi ina sonta..."
Cikin wani irin takaici Daddy ya kalle shi cike da hargagi ya ce.
"Ashe kai ɗan iska ne!!! Wawa sakarai daƙiƙi...ban yi maka kashedi tun a waya ba na ce kada ka zo nan??"
Cike da magiya ya ce.
"Dan Allah Daddy ka taimaka mini wallahi..."
Wata irin zabura Daddyn ya yi yana wani ihun kiran Security tamkar zai fasa musu dodon kunne yana faɗin.
"Security!! Security!!!..."
Wani irin shu'umin murmushi ne ya suɓucewa Uncle Isma'ila bayan nasarar samowa Mummy mafita da ya yi yanzu-yanzu cikin ƙanƙanin lokaci ya kalli Daddy ya ce.
"Alhaji!! Barshi tukun, ina da wata shawara...."
Tsit sukayi suna kallon shi domin su ji wace irin shawara ce wannan.
"Ba sai ka haɗa shi da security ba,ina so ka bashi sound warning, sannan daga nan ya tattara ya fece kada kuma ya sake nuna maka fuskarsa a nan har abada. Idan ba haka ba kuma, duk irin hukuncin da ka ɗaukar masa shi ya janyowa kansa."
Wani kallon ƙasƙanci Daddy ya jefawa Ashirun sannan ya ce.
" Ai ka riga ka gama faɗa masa komai da ya kamata. Saboda haka, idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira, ka manta da Beenafah....Ka manta da ita har abada, idan ba haka ba wallahi sai na ɓatar da kai..."
Miƙewa Ashiru ya yi jiki a saɓule amma kuma ba don ya haƙura da Beenafah ba ya fice ya bar gidan gabaɗaya. Shi yasan cewa ko zai rasa ransa ba zai iya haƙura da Beenafah ba sai dai idan kuma ya zo a ƙaddararsa cewa ita ɗin ba matar sa ba ce, to sai ya ɗauki dangana.
Kallon Isma'il ɗin Mummy ta yi tamkar idanun ta za su zazzago waje ta ce.
"Isma'il miye shawarar??"
Wuri ya samu gefen da Hafiz yake zaune tun ɗazu wanda ya kasance tamkar mutum mutumi ya zauna ya fara magana da cewa.
"Uhm to! Shawarar tawa ita ce;ai na san dai har yanzu baku sanarwa shi Ameer ɗin da iyayensa cewa Hassana ta tsere ba??"
Da sauri duk suka jinjina kai alamar eh sannan Mummy ta ce.
"Ban cire rai ba har yanzu da cewa za ta dawo kafin bikin nan in sha Allahu. Shiyasa bamu ma yi mafarki gaya musu ba."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"That's very good! Idan har ta dawo ɗin, Alhamdulillah! Hakan aka fi so, idan ma kuma ba ta dawo ba, maimakon rasa waɗannan kadarorin kai tsaye, tun da har ba su san halin da ake ciki ba, to a kira shi Ameer ɗin cikin ɗaki a lallaɓa shi a bashi Beenafah..."
Wata irin uwar zabura Mummy ta yi ta miƙe tsaye tana wani irin girgiza kai ta ce.
" Wane irin zancen banza ne wannan Isma'il??"
" Ai dai kina bari in mutu Hajiya Zaliha kafin ki yi ƙoƙarin binne ni...ina so ki fahimci zancena, a rashin Uwa akan yi Uwar ɗaki! Kuma sai idan dama ta ƙiya ne ake komawa hagu. Ku sani fa; sai idan yaran Alhaji Mansur sun auri waɗannan 'ƴa'ƴan na ku ne sannam za ku iya samun cikar mafarkin ku, idan har kuma daman hakan ta suɓuce muku, to kuwa shikenan kun rasa wannan damar har abada. A madadin yin wannan katoɓarar; a aura masa Beenafahr mana. Ita ɗin mace ce da duk wanda namijin da ya same ta ya cancanci ayi mishi barka,kuma ku sani, dole dai a ƙarƙashin ikon ku take, sai abin da kuka ce za ta yi, muradin shi ne ya aure ta kuma ta haihu a gidan...Namiji ɗaya! Idan ta haife shi a gidan shikenan kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Kinga daga zaran anyi auren,Hafiz ko bai da takardu a matsayin sa na Yayan Su dole za a bashi gurbi wanda sai ma ya tsaya yangar zaɓar inda yake so ya yi aiki,sannan kuma duk wani buri da mafarkin ku zai cika, daga zaran ta haihu kuma, za ki iya yin duk yanda za ki yi kisa a sako ta shikenan."
Wani irin kukan farin ciki ne Mummy ta fashe da shi tare da ɗaga hannu sama tana ta zunduma masa addu'a da godiya akan wannan kyakkyawan tunani na sa.
Kallon shi Daddy ya yi cike da ɗan shakku ya ce.
" To amma fa, ba a nan gizo yake saƙar ba Isma'ila. Kasan an yi ta tallata musu yara iri-iri amma suka ce lallai sai sun samu en biyu kamar yanda suke...baka tunanin ya ƙi amincewa?"
"Na yarda da maganar ka Alhaji, amma kuma ai kowa ya shaida ya kuma tabbatar cewa shi Alhaji Mansur ɗin yana matuƙar ƙaunar yaran nasa, idan har yaron ya amince banga dalilin da zai sa ya ƙi amincewa ba, sannan ga hidimar nan ta matso, tabbas zai zama abin kunya ga irin wannan babban familyn aji labarin cewa wai amarya ta tsere saboda bata son ɗan su da aure. Ko don wannan dalilin, ba za su ƙi amincewa ba."
Miƙewa Aunty Aysha ta yi tsam! Ta fice daga ɗakin wanda ba jimawa Husaina ta bi bayanta suka bar su Mummyn nan zaune suna tattauna yanda za su yi abin ba tare da an samu matsala ba.
Hafiz dai zaune yake a wurin tamkar hoto, domin ya kasa sakin jikin sa dalilin Mummy taƙi ta yi masa magana tun da ya dawo.
********
Ni kuwa, cike da ruɗani Ammie ta shiga girgiza kanta alamar bata amince ba dalilin zancen da na zo mata da shi cike da tashin hankali ta ce.
"Ban amince ba Beenafah....wannan ma wace kalar tatsuniya ce mai abin mamaki? Taya don kawai kinji labarin cewa an ce mutum ya kasa auruwa, mutumin da baki taɓa ganin sa ba, baki san asalinsa ba, baki san ya yake ba wai ki ce kin amince ki aure sa....ai gwanda ma Alhaji Mudassir ya aura miki Ilyas ɗin hankalina sai yafi kwanciya da wannan mummunan abun da kike shirin aikatawa... "
Cikin matsanancin kukan da ban san ma ina yinsa ba na girgiza kaina ina faɗin.
"Ammie! Kika ce gwanda Ilyas akan Mohaa? Wallahi tallahi har abada ba za su zama ɗaya ba. Ai idan na auri Ilyas Daddy zai yi farin ciki akan ya sake yin nasara akanmu, wanda hakan baya nuna komai garemu sai faɗuwa da hasara! Amma Mohaa...ko ba komai, zan samu lada domin na kautar masa da baƙin cikin duniya wanda Allah ya yi alƙawari akan hakan cewa, duk wanda ya kautar wa da ɗan uwansa musulmi wani baƙin ciki to shima Allah zai kautar masa da na sa ranar gobe alƙiyama....Ammie dole rayuwarsa akwai tausai, gabaɗaya Familyn suna cikin baƙin ciki da rashin walwala na tsawon lokaci, hakan da zan yi shine zai zama silar farin cikin su Ammie..."
A zafafe ta jinjina kanta ta ce.
"Ki kautar musu nasu baƙin ciki ke kuma ki fara ƙirga kwanakin mutuwar ki ko??"
"Ba zan mutu ba Ammie, In Sha Allahu ba zan mutu ba sai idan kwana na ne suka ƙare! Ammie, Aunty Labiba ta yi mana riga ta yi mana wando, duk alherin da muke ciki a yanzu ita ce sila, Ammie kin ga irin kwantaccen baƙin cikin da yake fuskarta kuwa? Ammie kin ce wurin ceto rayuwar masoyinka sai inda ƙarfin ka ya ƙare...kenan wannan duk ba haka ba ne?"
" Beenafah! Aure fa aka ce miki! Kin san mi kalmar aure take nufi kuwa? Idan fa an shiga fata ake yi sai mutuwa idan ta raba, cike kuma da soyayya da farin ciki da kwanciyar hankali da 'ƴa'ƴa masu albarka! Wannan shi ne mafarki da burin kowace Uwa ta gari akan 'ƴar ta...To kuwa idan haka ne, kika ce kin zaɓi wannan yaron akan wani dalili kina ganin kin yi mini adalci kuwa?"
Hannayenta na kama na jimƙe sosai a nawa, sannan na yi amfani da su na goge hawayen fuskata still ba don sun tsaigata kwarara ba sake ɗagowa na kalle ta a tausashe na ce.
"Ban san ya zan ce miki ba a yanzu,amma kuma duk abinda nake ƙoƙarin aikatawa, kece sila domin ban san komai ba sai irin tarbiyyarda kika ɗorani a kanta wacce tausayi shi ne mafi rinjaye a cikinta. Ba zan miki alƙawari ba Ammie, domin ni ɗin ba ma'asumiya ba ce ballantana in ce miki na san mi zai faru gobe,ina roƙonki da neman alfarma dan Allah Ammie ki karɓi wannan ƙudurin nawa ki kuma tsaya mini akan hakan sannan ki yi mini addu'a. Da in auri Ilyas gwanda na auri Mohaa da ban taɓa gani ko jinsa ba, domin da shi da Ilyas ɗin duk kanwar Ja ce sai dai shi ko ba komai zan faranta ran 'ƴan uwansa waɗanda suka zame mana bangon jingina."
Rungumeni ta yi sosai tana mai fashewa da kuka tace.
" Shi ke nan Beenafah! Na amince tun da har kin kafe akan hakan, to amma ta ya ya kike tunanin wannan auren zai yi nasara daga nan zuwa gobe? Alhaji Mudassir ba zai taɓa aura miki shi ba kinsa. Sannan Malam Habibu (Babansu su Jafaru) ma ba zai tsaya mana ba Beenafah kin dai gani tun zancen Ashiru da akayi a farko ballantana wannan.. "
Janyewa na yi ina kallonta na ce.
" Mu sake jarabawa wurin Baban mu gani mana, ba dole sai munje wurin Daddy ba domin nasan har abada ba zai taɓa amincewa ba. Dan Allah ki tashi kije wurin Baba ki roƙesa dan Allah."
Da rarrashi da komai na samu ta saka hijabin ta ta fice zuwa gidan Maman Fakiha. Na jima a zaune ina dakon jiran ta sannan sai ga ta ta dawo. Jiki a sanyaye ta kalleni tare da girgiza kanta ta ce.
" Wallahi Beenafah na yi iya yanda zan iya, amma yaƙi ya amince mana. Ni nasan tabbas wannan abun da Wuya, saboda haka ki haƙura da wannan al'amari....."
Cike da ƙwarin gwiwa na ce.
"To Ammie ga wata shawara!!!"
Ɗan Jim ta yi kaɗan tana kallona sannan daga ƙarshe ta jinjina kanta ta ce.
"Wace shawara kenan?"
"Mu kira DR. BASHEER mana....Dr. Basheer likitan ki na Sokoto Ammie. Mutumin kirki ne kuma na san In Sha Allahu zai taimaka mana..."
"Kai Beenafah! Gaskiya a'a. Da muguwar rawa fa akace gwamma Ƙin tashi..."
Matsowa na yi da sauri tare da kama ɗayan hannunta na ce.
"Ammie amma kuma ai da gwaji jirgin sama ya tashi. Dan Allah ki bari mu jaraba ta hannun sa mu gani ko Allah zai sa mu da ce."
"Rabonmu da shi fa tun zuwanmu Sokoto na ƙarshe, ko waya bamu sake yi ba har yanzu..."
Zuruf na ruga na shige ɗaki jikina na rawa na shiga birkita kaya, cikin sa'a kuwa sai ga takardar mai ɗauke da numbern wayarsa da sunan sa na gani. Fitowa na yi na nuna mata takardar na ce.
" Ga numbern shi nan, bari na je na aro wayar Mama mu saka mu kira.."
Juyawa na yi da gudu na nufi ƙofa, kafin in buɗe naji ta kira sunana. Ina waigowa ta ce.
"Kada ki aro ta ta aro ta Babansu."
"Ok"
Ina shiga na tarar da su zaune a wuri ɗaya da alama akwai maganar da suke tattaunawa, bayan na gaishe su na kalli Mama na ce.
"Wai dan Allah Ammie ta ce a aro mata wayar Baba tana so ta kira.."
Kallona Baba ya yi ya ce.
"Waye za ta kira?"
Kai tsaye na ce.
"Likitan ta dake Sokoto."
Yana jin hakan ya zura hannu aljihun gaban rigar sa ya ciro ya miƙo mini, daman wayar mai madannai ce kuma bata da security daman mun saba ɗauka muna game musamman Bahrain da Farisa.
Bayan na fito ne Mama ta kalli Baba cike da rashin jindaɗi ta ce.
" Ni wallahi sam ban ji daɗin abin da ka yi ba. A yanzu na ɗauka tsawon lokacin da muka share da su na zamowa kamar ɗaya za ka iya tsaya musu akan koma mine ne. Amma ka ƙi..."
Wani murmushin ba za ki gane ba ya yi mata yana girgiza kai sannan ya ce.
"Maman Fakiha ba za ki taɓa fahimtar abin da nake hangowa ba sai nan gaba. Kinga waɗan nan mutanen! Jikina yana bani ba ƙananun mutane ba ne, ki duba uwar ta su da kyau ki kalleta da idon basira. Haƙoran maka ne fa a bakinta har guda biyu. Sannan yanayin ta da yanayin maganar ta idan kin yi nazari za su tabbatar miki da cewa akwai wani ɓoyayyen al'amari a tare da ita. Mutum ko shege ne dole yana da dangi domin ba shi ne ya haifi kansa ba. Akwai wani abin da yake ba daidai dangane da su. Ki duba ko gidan da aka kaimu da sunan na wan mahaifinta ne, ba ƙaramin gida ba ne kuma mammalakin shi ba ƙaramin mutum bane,kawai dai kinsan al'amarin na yanzu tsoron Allah ya yi wa mutane ƙaranci, babu abin da ba za su iya aikatawa ba. Dalilin haka ne yasa ba wai taimaka musu ne bana son yi ba, a'a kada in je in yi watarana ina zaunena Allura ta tono garma, ace na jefa kaina cikin masifar da ba zan iya fita ba. Saboda haka, taimako na tare na yau da gobe babu abin da ba zan iya yi musu ba,amma dai taimakon ɗaurawa Beenafah aure, har abada ba zan amince da wannan ba. Allah ubangiji ina addu'a ya shiga lamarinsu ya taimake su akan rayuwar su damu da su baki ɗaya."
Jinjina kai Mama ta yi cike da gamsuwa da maganar sa ta ce.
" Gaskiya ka yi magana, kuma ni sai yanzu na fahimce ka, Allah ubangiji ya zaɓa mata mafi alheri."
Miƙewa ya yi yana faɗin.
" To amin. Shi kaɗai za'a. Ni zan shiga ciki, idan kin kambala dafa abincin sai ki kawo mini a ciki."
"Tau, In Sha Allahu."
Ni kuma, ina shiga na ɗauki takardar na shigar da lambar sa kai tsaye na kira. Sai da ta yi ringing kusan sau biyar wanda har Ammie ta ce na daina kiran kawai sai ga shi ya kira.
Karawa na yi a kunnena ɗauke da sallama a bakina, bayan ya amsa na gaishe shi sannan nace mishi Ni ce ga Ammie tana son magana da shi.
Cike da fargaba da rashin makama Ammie ta amshi wayar suka gaisa da shi lafiya lau sannan ya tambaye ta ya jiki ta ce mishi ta ji sauƙi. Shiru ne ya ratsa tsakanin su na ɗan lokaci, jin tayi shiru yasa daga can ɓangaren sa ya ce.
"Hajiya Mulaifa shikenan lokaci ɗaya kika ɓace tamkar an yi ruwa an ɗauke. Ko wannan kiran ma na san jikin ne ƙila ya motsa ko?"
Girgiza kanta ta yi tamkar tana a gabanshi ta ce.
"Wallahi fa bamu kyauta ba kam, tunda muka dawo wannan asibitin shike nan muka watsar da kai. Amma magana ta gaskiya jikina Alhamdulillah! Na warke gabaɗaya, dama har ana batun ƙara turani Sokoton sai gashi sun ce likita zai shigo nan asibitin ya duba ni daga cikin likitocin da ke dubani,mun ma yi zaton kai ne a lokacin sai ga Dr. Kenna."
"Allah sarki! Congratulations to you. Allah ya ƙara miki lafiya yasa kaffara ne."
"Amin! Daman wata magana ce nake tafe da ita mai nauyi, wacce ban san ma ta ina zan fara yi maka bayani ba, amma ina fata za ka fahimceni...."
Jin ya bata dukkan wani attention na na shi yasa ba ta yi nauyin baki wurin bayyana masa dukkan abin da suke ciki ba, da kuma buƙatar su a gare shi.
Shiru yayi tsawon lokaci wanda daga ni har Ammie, lamarin ya so ya tsora tamu sannan daga ƙarshe muka ji ya ce.
"Na ji dukkan uzurinki Hajiya Mulaifa, to amma what of Uwar ta fara samun inuwar kafin 'ƴar ta samu?"
Cikin rashin fahimta Ammie ta ce.
"Ban fahimce ka ba Dr...."
"Eh, ina nufin da ace an hayo mata mahaifi, ba gwanda ta gabatar da na gasken ba...kamar abin sai yafi zama unique.."
"Still ban fahimce ka ba Dr.??"
Ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce.
"Ina nufin a fara ɗaura mana aure dani dake idan kin amince tukunna, sannan daga baya ita sai a ɗaura natan..."
Cikin mummunar faɗuwar gaba ta ce.
"Subhanallah! Gaskiya a'a!!"
Dariya ce ta suɓuce mishi sannan ya girgiza kai ya ce.