Ganin ido complete - Chapter 30
Ganin ido complete Chapter 30: Ganin ido complete Chapter 30. "Miye abin Subhanallah sai ka ce na aikata wani zunubi?? Aure fa na ce miki ba wani abu ba…
3,089 words
"Miye abin Subhanallah sai ka ce na aikata wani zunubi?? Aure fa na ce miki ba wani abu ba Hajiya Mulaifa. Nasa ran sake haɗuwa dake akan ya kamata na aureki ko don marayun yaran ki guda biyu, duba yanayin rashin lafiyarki da kuma wahalar da suke ta yi dake babu matallafi, bayan mun tattauna da Matata akan ya kamata na aure ki itama sai ga shi ta amince, da wannan burin na rayu tsayin lokaci sai gashi Allah cikin ikon sa na nemeki na rasa sai yau da Allah ya bayyanar min dake. Saboda haka idan kin amince zamu taso yau In Sha Allahu mu iso Gusaun, gobe idan Allah ya kai muna rai ƙarfe tara na safe sai a ɗaura mana auren, ita kuma zuwa ƙarfe biyar sai a ɗaura na ta...."
Sauke wayar ta yi a hankali tana mai sulalewa zuwa ƙasa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Sai da tayi shi na tsawon lokaci sannan na zauna a gabanta muna fuskantar juna sosai nima da kukan akan fuskata na jinjina kai a hankali na ce.
" Kina Kuka akan Abbie ko?..."
Na faɗa ina mai jinjina kaina sannan na sake cewa.
"Dole ba za ki taɓa mantawa da shi ba na sani har gaban abada, amma kuma ko shi ne yake da damar ganin irin halin da kike ciki a yanzu ba zai so ki ci gaba da zama a haka ba, zai yi miki fata da kwaɗayin samun rangwame akan halin da kika rayu a ciki bayan ya bar duniyar nan...Allah shi ne wanda yafi kowa sanin abin da ya dace da rayuwar bawan sa. Lokaci ne ya juyo mana da abubuwan da bamu tsamma ta ko yin mafarki a kai ba, saboda haka ki yi shawara ki duba yiyuwar abun. Idan har zai yi yu to ki amince da wannan ƙudurin na Dr. Basheer. Lallai akwai hikima a cikin al'amarin Ubangiji, kuma wallahi duk wanda ya dogara ga Allah tabbas ya isar masa. Duk da irin mafarkin auren Mohaa da yake raina, can ƙasan zuciyata tunani nake ina zan barki, duk da cewa kin gama magana domin kin ce Allah ya tsaya miki....niyyar alherin da take cikin raina sai ya kawo mana abin da bamu zata ko yin mafarki akan sa ba. Tun da har bamu nemesa da hakan ba kuma bamu roƙa ba, shi karan kansa ne ya duba yaga cancantar hakan, to don Allah ki duba lamarin Ammie, in sha Allahu zai kula da ke yanda ya kamata."
Ina gama faɗamata hakan na zura hijabina naje na kira Mama da Baba akan wata sabuwar kwamacalar da ta sake tasowa. Ina ganin sun shigo na tashi na koma gidan na su na shige ɗakin Mama na haye gadonta na kwanta shiruuu! Ina nazarin abubuwa yanda suke neman juyawa cikin lokaci ƙanƙani.
********
Aunty Labiba kuwa,ta shiga cikin matsanancin ruɗani, har ta gama shirinta na fita aiki ta kasa yarda cewa wai wannan ba mafarki take ba. Gobe za a ɗaura mana aure! Wannan ita ce kalmar da ke ta amsa kuwwa a cikin masarrafar tunanin ta,duk da cewa kuma ba don zancen ya shige ta ba. Domin an yi haka babu iyaka babu adadi har sai da ya dinga kuka da hawayensa kamar wani ƙaramin yaro yana kiran baƙar ƙaddara ce ke tare da shi. Haka ya sa ƙafa ya bar ƙasar baki ɗaya ba tare da sake marmarin son dawowa cikinta ba. To a yanzu mine ne za ta faɗa masa wanda zai burgesa har yasa ya iya amincewa da maganarta? Ta san kawai ya amsa ta ne ba don komai ba sai don baya son jin sautin kukan ta ko kaɗan, tasan in ba don matsiyacin kukan da ta tartse masa da shi ba na tashin hankali da magiya da komai ba, to ko mai za ta yi ba zai amince ba,tunda hatta Hajiya ta sake yunƙurin neman masa auren har sau biyu daga baya-bayan nan amma kuma ya ƙi amincewa.
Tuno irin waɗannan abubuwan yasa itama kawai ta amsawa Beenafah ne don kar ta ga cewa kamar taƙi amsa tayinta ne. Amma ita tasan har abada Daddyn Raudah ba zai taɓa auruwa ba.
Da wannan tunanin ta samu ta kambala duk abinda za ta yi a sanyaye ta fice wurin aiki. Bayan ta taso da ƙarfe biyar ta dawo gida ta sake shiryawa sannan ta kira Oga Sule ta ce ya zo ya kaita gidan su Beenafah.
Sabuwar mai aikinta ta faɗa mata cewa Emraan ya zo nemanta amma kuma wannan a yanzu ba shi ne a gabanta ba, daman tun daren jiya Hajiyar ta su ta kirata da cewa idan gari ya waye tayi azama taje tana nemanta akan wata muhimmiyar magana domin yanzu haka ma Ziza ta yi yaji ta tafi Kebbi State. Saboda haka ta gaggauta tahowa akwai magana. Da abin ta kwana a ranta amma kuma zuwan Beenafah da wannan maganar sai ta shafe matsalar gidan Auren Emraan da Hajiya ke nemanta a kai.
Sannan ga sharaɗi ta gindiya akan cewa kada wani ya ji zancen auren, hakan yasa ta shirya tsayawa kai da fata, muddin dai wai Yaya Mohaa za a ɗaura masa auren da gaske, to tabbas za ta tsaya akan ganin hakan ta kasance, idan ya so ta je kai tsaye ta cikawa Hajiya gidanta da maganar farin ciki. Abun da ta jima tana mafarki da kuma buri a kai.
Hatta Baba Ustaz da ya iso, ce masa tayi ya samu hotel ya sauka domin ba ta so kowa yasan cewa ya zo.
*********
Gidan namu, dawowa ya yi tamkar gidan mutuwa domin daga ni har Ammie babu wanda ya sake yin wata magana mai tsawo.
Yanzu ma zaune nake a bakin rijiya ina wanke kayan uniform ɗin Bahrain yayin da Ita kuma Ammie ke zaune can nesa dani akan tabarma riƙe da Alƙur'ani a hannunta tana karantawa. Jin sallamar Aunty Labiba kawai da nayi sai da naji ƙirjina ya buga wanda ban san dalili ba.
Wankin na ajiye a gefe na taso na tare ta muka ƙara so ta zauna a gaban Ammie suna fuskantar juna.
"Baiwar Allah sannu da zuwa."
Cewar Ammie tana mai rufe Alƙur'anin da ke riƙe hannunta sannan ta miƙo mini alamar in mayar ciki.
Wani kallon mai alamar tambaya Aunty Labiba ta bi Ammie da shi tana mai jinjina kanta da murmushi shimfiɗe akan fuskarta ta ce.
" Yauwa Hajiya Sannu. Ina wuni."
"Lafiya lau, Alhamdulillah!"
Ba ɓata lokaci ta ce.
"Ni ce Labiba, ni ce nan ƙanwar Muhammad wanda zai auri Beenafah..."
"Allah sarki! Ya gida?"
"Lafiya lau Alhamdulillah. Daman dai ya faɗa mini ne cewa na samo masa matar aure shiyasa na ga cancantar Beenafah..."
Girgiza kai Ammie ta yi tana wani irin murmushi ta ce.
"Ba sai kin sauya magana ba Hajiya Labiba, Beenafah ta faɗa mini gaskiyar yanda abun yake, kuma na amince ne domin ba ni da wani zaɓin. Beenafah 'ƴa ta ce wacce bani da tamkar ta a duniya, duk inda ake neman 'ƴa ta gari to haƙiƙa ta kai. Yanda ta kula dani, bani da wani abin da zan bata face in cika mata duk wani burin ta muddin zai bata farin ciki...."
Jinjina kanta ta yi, cike da yaƙini ta ce.
" Muddin dai alaƙar su da Daddyn Raudah ta tabbata! To bana tunanin matsala Hajiya... "
Fuska cike da nuna alamar tambaya Ammie ta ce.
" Beenafah ta faɗa mini cewa bai taɓa aure ba, to amma ya akayi yake da 'ƴa?"
Murmushi tayi tare da jinjina kanta ta ce.
" Raudah 'ƴata ce ta farko. Ita ɗin ta kasance 'ƴar sa tun da na haifeta ta zo duniya, ita ɗin ta kasance farin cikinsa da walwalarsa, amma kuma ta rasu shekaru kaɗan da suka wuce. Wanda ya na daga cikin abin da ya ƙara gigita rayuwar farin cikinsa....."
Ba tare da ta ɗauke idanunta akan Ammien ba,kai tsaye ta sake jefa mata wata tambayar da cewa.
" Shin zan iya sanin tarihin ku? Na jima ina so in yiwa Beenafah wannan tambayar, sai dai sanin ba hurumi na ba ne yasa dole na kama kaina, amma a yanzu Koba komai mu ɗin mun zamto tamkar en uwa, domin na ɗauki Beenafah da girma sosai a cikin rayuwata, sannan uwa uba ga wani zumuncin babba na neman ƙullawa tsakaninmu zuwa gobe."
Ajiyar Ammie ta sauke a hankali ta gyaɗa mata kanta ta ce.
" Sunana Mulaifa Zayd Hudaif. Na fito daga Aden ta ƙasar Yemen....."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 29*
A gidan wasu bayin Allah na tashi a Aden. Sheikh Zayd Hudaif wanda zan iya kiranshi da Ɗan Aljanna akan irin halin taimako da tausayi irin na sa. Sai matarsa Nana-Zaynab Al-ƙais wacce ta zamto uwa ta gari madubin al'umma. Dalilin da yasa ban kira su da iyayena ba kai tsaye; saboda a lokacin da na fara wayo, tun a lokacin wani mahaukaci yake zuwa ƙofar gidan lokaci bayan lokaci ya ƙwanƙwasa a fito masa dani mu zauna a gefe ya buɗe duk tarkacenda ya zo da shi ya riƙa bani a baki ina ci, wanda yana bani ina ci yana kuka. Tun bana iya fahimtar komai har na zo ina tambayar Ummie cewa wanene wannan. Kin san mi tace min?"
Girgiza kai Aunty Labiba ta yi a hankali tare da share wasu siraran hawayenda suka silalo mata ta ce.
" Sai dai idan kin faɗa mini yanzu."
Itama share hawayen ta yi tana jinjina kanta ta ce.
" Sheikh, da kansa ya zaunar dani ya faɗa mini cewa wannan mahaukacin shi ne mahaifina, shi ne wanda ya sallama masa da kansa ya damƙa masa ni tun ina 'ƴar shekara biyar. Kuma duk bayan lokaci zuwa lokaci yana zuwa ya ganni ya koma, mutumin da duk wanda ya yi ido biyu da shi ko ya ya ne sai ya razana amma ni da mutanen gidanmu bamu taɓa jin tsoron sa ba. Kuma wani abun mamaki, tun da nake ban taɓa jin sautin muryar sa ba ko sau ɗaya. Ina da shekara goma sha ɗaya a duniya ya ɓace ban sake ganin sa ba har yau da nake baki wannan labarin, kuma sheik ya kasa gane inda yake, tamkar walƙiya idan zai zo haka yake zuwa, idan ma zai tafi haka. Na yi kuka na yi baƙin cikin rasa mahaifina wanda har abada ba zan daina addu'a ba akan cewa Allah ya ji ƙansa da Rahma, domin idan ba mutuwa ba, banga abinda yake hana masa zuwa ganina ba, ruwa da iska bai taɓa sa ya ɗauke ƙafa ba.......Iyayena na riƙo ba wasu masu hali ba ne amma dai ni da yaran su guda uku, Lina, Ziyadah, da kuma Fa'ida, mun rayu cikin soyyaya da ƙauna. Duk da kasancewarsa marar abin duniya, shi ɗin ya kasance babban malamin addini wanda ake alfahari da shi a ƙasar Yemen, yana karantarwa a islamiyya da kuma masallaci, sannan yana yawan tafiya wurin Da'awah idan buƙatar hakan ta taso. A dalilin hakan ne yasa mu 'ƴa'ƴansa muka samu tarbiyya mai kyau da ilmin addini, sannan ta dalilin wannan yasa muka samu tallafin karatun boko mai inganci da nagarta tun daga matakin farko har zuwa Jami'a. Bayan na kambala karatuna, ni da Lina muka samu aiki a ma'aikatar jinƙai da tallafi ga mata da yara ƙanana marayu domin goben su...."
Girgiza kanta ta yi da wasu irin zafafan hawaye sannan ta murmusa ta ci gaba da cewa.
"Uhm! Taron farko dana jagoranta a hukumarmu, shi ne wanda aka aika mana katin gayyata na The world Forum on Women and children Empowerment a Vancouver dake ƙasar Canada, inda a nan ne na haɗu da Dr. Bello Wazeer haɗuwar farko. Bayan an kambala taron kai tsaye ya nemi mu tattauna kafin in juya zuwa ƙasata. Bai tsaya nauyin baki ba ya sanar min abinda yake ransa dangane da ni ma'ana yana so mu yi aure. A lokacin ban sanya maganar sa ba a kaina domin a tunani abin ba mai yiyu wa ba ne, domin ni daga Yemen shi daga Nigeria abin da ba zai yiyuba kenan. Amma kuma bayan na koma gida, haka ya cika alƙawari ya zo har gidanmu ya sanarwa da Sheikh ƙudurinsa a kaina. Sheikh ya tsorata ya kuma so ya hana wannan auren namu,duba da cewa ni ɗin amana ce a wurinsa. Amma sai na kafe na ce ni lallai ina sonsa kuma zan aure sa. Hakan yasa Sheik ya nemi Dr. Bello ya turo da magabatansa. Ba'a yi kwana biyar ba, sai gashi sun dawo tare da Alhaji Mudassir da wasu dattijai guda biyu. Da kuma Yayarsa Hajiya Rashida wacce ta zamto ita ce uwa a gare su. Nan aka yi maganar aka kuma ɗaura mana aure, wanda daga ƙarshe, tare da Sheikh da kuma Ummie muka tafi ƙasar Canada domin a can ne Dr. Bello yake aiki kuma a nan yake zaune yana harkokinsa...."
"Kenan ba'a nan Nigeria kuka fara zama ba??"
Girgiza kanta tayi ta ce.
"Ban taɓa zama a Nigeria ba. Gabaɗaya zuwa huɗu na taɓa yi, zuwan farko, aurenmu nada wata shida muka zo wurin gaishe da Hajiya Rashida inda muka yi sati biyu kacal muka koma saboda yanayin aiki, zuwa na biyu kuma bayan na haifi Beenafah ne da shekara ɗaya muka zo bayan Hajiya Rashida ta rasu da sati ɗaya, sai zuwa na uku kuma, bayan na haifi Bahrain Alhaji Mudassir ya matsa akan cewa Dr. Bello ya yasar da shi ya maida shi ba komai ba, alhali kuma shi ne matsayin uba a gare sa. Hakan yasa muka sake wanko ƙafa muka zo. Sai zuwa na huɗu wanda shi ne na ƙarshe, shi ne zuwan da na yi ya sarƙafeni ni da Yarana ya zame mana tarkonda muka kasa fita daga cikinsa...... Zuwan kuwa shi ne, Auren Aysha da muka zo, a lokacin Beenafah tana da 12years a duniya Bahrain kuma yana da 5years, sai tsohon cikin da ke jikina haihuwa ko yau ko gobe. A wannan lokacin na so mu haƙura da wannan zuwan kamar-kamar me saboda yanayin condition ɗina, amma Alhaji Mudassir ya nuna tsananin ɓacin ransa akan cewa auren 'ƴar sa ta farko bai kyautu ace iyalin ɗan uwansa basa nan ba. Ya yi fushi a lokacin fushi sosai wanda har ta kai baya ɗaga wayar Dr. Bello. Ƙarshe don kawai mu faranta masa ransa, na dage na kunna wuta sosai akan dole sai munzo, hakan yasa muka yanke shawarar zuwa, sannan idan munzo zan zauna a nan har sai na haihu an yi suna da wata ɗaya zamu juya mu koma. Don kawai dai in faranta masa rai....."
Kuka ne ya sarƙeta mai ƙarfin gaske wanda har sai da ta tsahirta maganar na ɗan lokaci sannan ta jinjina kai ta ce.
" Ashe duk wannan shirin na juyawar allon ƙaddararmu ne. Muna isowa da sati ɗaya aka yi bikin Aysha da Ahlan. Tun da Aysha ta kambala secondary school a wurina ta ci gaba da zama a Canada, inda a can ta kambala degree ɗinta sannan Dr. Bello ya haɗata da Ahlan wanda yana daga cikin yaran sa a wannan lokacin. Bayan auren da kwana uku, Dr. Bello ya juya zuwa Canada domin nemansa da ake wurin aikinsa cikin gaggawa. Bayan sati biyu lafiya lau muka yi waya da shi akan cewa zai taso da yamma zuwa gida Nigeria domin ya kambala uxurinsa kuma ma ya ɗauki hutun wata ɗaya saboda haka sai ya cika cif zamu koma a tare. Muna zaune a parlour, ni da Hajiya Zaliha sai saƙon mutuwar Dr. Bello muka ji cewa ya samu Accident daga hanyar sa ta Abuja zuwa nan gida Zamfara ya mutu..... Hmm! Haka aka kawo mini gawar sa aka ajiye a gabana, ga tsohon ciki, ga baƙin ciki a lokaci ɗaya na yanke jiki na faɗi. Koda na farfaɗo har an gama yi masa sutura, addu'a kawai na yi masa da ganin ƙarshe aka fice da shi, tafiyar da ba dawowa a cikinta ita Dr. Bello ya yi. Damuwa wasa-wasa ta fara illatani domin Mutuwar Dr. ta zame mini mummunar mutuwa wacce na kusa kwana uku ban san inda hankalina yake ba musamman tun da aka fice da shi a gabana. A ranar da ya cika sati biyu da mutuwa, a ranar naƙuda mai Zafi ta taso mini wacce a gigice aka ɗauke ni zuwa Asibiti, muna zuwa ba jimawa na haihu na haifi ɗa namiji. Sai da na kwana huɗu saboda yanayin jikina yaƙi daɗi sannan aka bamu sallama. Bayan mun dawo, kin san ni ya faru Hajiya Labiba??"
Cikin wani irin Kuka Aunty Labiba ta girgiza kanta tare da faɗin.
" A a?!"
" Ainahin gidanda muke ciki Alhaji Mudassir da matarsa Hajiya Zaliha sun kwaso mana kayan sakawarmu sun dawo damu ƙaramin ɓangarensu wanda bai kai namu girma ba, su kuma sun shige cikin namu gidan sun zauna. Ina zuwa na nufi gidan kai tsaye sai ga Hajiya Zaliha ta tsaya a gabana tana ce mini can ne gidana a yanzu. A wannan lokacin sam ban sa komai a raina ba, domin mutuwar mijina har a lokacin ba ta daina dukan ƙirjina ba. Haka muka koma ɗan ƙaramin flat ɗin na su muka shige inda Beenafah ta yi ta nuna ƙyama a wannan lokacin. Da ƙyar naga na ƙara kwana biyu a gidan daga baya na ji cewa ba zan iya zama ba. Saboda haka kai tsaye na tashi na shiga cikin gidan inda na tarar Alhaji Mudassir yana zaune yana karyawa shi da iyalansa cike da izza da nuna isa. Kai tsaye na ce masa so nake na koma Canada, daga can na wuce Yemen domin ba zan iya zama a nan ba. Daga shi har matarsa, ba tare da sun ko kalli inda nake tsaye ba, yace mini shi ba zai hanani tafiya ba idan na tashi amma kuma babu inda zan tafi masa da yaran sa, hatta Sajjad da yake sabuwar haihuwa a duniya ba zan tafi dashi ba, domin shi bai san inda zai sake ganina ba, kuma ba zai amince naje ko'ina da yaran sa baa..."
Cike da tsananin tashin hankali Aunty Labiba ta fashe da wani irin kuka, jikinta har yana rawa tsabar shock ta ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Amma dai wannan mutumin an yi mugu azzalumin bawa..."
Wani irin murmushin takaici ne ya suɓucewa Ammie, cike da jin wani sabon baƙin ciki a ranta ta ce.