Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 3

Ganin ido complete - Chapter 3

Ganin ido complete Chapter 3: Ganin ido complete Chapter 3. Dubu ɗari da hamsin ne kuɗin tallafin da zamu riƙa samu duk wata idan lokacin zuwanmu asibiti…

3,347 words

Dubu ɗari da hamsin ne kuɗin tallafin da zamu riƙa samu duk wata idan lokacin zuwanmu asibiti ya yi, hakan yasa koda muka dawo iyaka dubu sha biyu ne suka rage a hannuna domin tun kafin ma mu tafi na riga na karɓi kayan Baba mai shago sun kai na dubu takwas.

Addu'a sosai na shiga yi ina fata da saka ran duk inda Daddy yake Allah yasa ya dawo nan kusa.

Sai da muka cika sati ɗaya da dawowa cif, a daren ranar misalin ƙarfe biyu da rabi na dare bayan na raka Ammie banɗaki mun dawo, kamar an ce na leƙa window kwatsam sai ga motar Daddy na hango an yi parking dai-dai inda yake ajiye ta idan ya dawo da dare.

Cikin wani irin farin ciki na kalli Ammie dake ƙoƙarin tayar da Salla na ce.

"Ammie Daddy ya dawo! Wallahi Daddy ya dawo. Zo.....Zo ma ki hango motar sa da idonki ki gani."

Na ƙarashe maganar tare da janyo hannunta kamar wata zararra ina nuna mata.

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana mai bi na da kallo ta ce.

"Allah maji roƙon bayinsa Beenafah. Ni ina ganin kada ma ki yi masa zancen kowane kuɗi kawai ki yi masa zancen abinci, ina ga hakan kawai ya wadatar. Wallahi Ba na jin daɗin yanda mafi yawan lokuta Bahrain yake zuwa makaranta batare da ya sanya komai a cikin sa ba... "

Hannayenta na kama guda biyu ina mai ƙara kwantar da murya, na ce.

" Ba Bahrain kaɗai ba Ammie, har ke kina da buƙatar wadataccen abin Ci da Sha domin ƙwaƙwalwarki ta ƙara samun nutsuwa da aiki yanda ya kamata..."

Cikin kalamai ma su nuna zallar karaya ta ce.

" Ina ma ace Abbie shima yana nan tare damu. Da yanzu komai na nan yanda yake, da yanzu Sajjad ɗina shima yana raye! Da...."

Hannuna na sanya da sauri na toshe mata baki tare da girgiza kaina ina mai fashewa da wani irin kuka, na ce.

"Kash Ammie! Ashe ba kullum ana miki nuni akan yarda da ƙaddara ba? Har abada babu danasani a cikin hukuncin Allah Ammie, Babu fa wanda yake da ikon rubutawa kansa ƙaddara fa ce abinda Allah ya nufesa da shi. Abbie addu'armu yake buƙata akoda yaushe. Sannan a kullum ina so ki ci gaba da sakawa a ranki cewa babu wani laifi da kika aikata, ba ki aikata komai ba. Ki yi haƙuri Ammie na! Ki ƙara haƙuri, Allah yana tare da masu haƙuri."

Ina gama faɗar haka na rungumeta sosai ina mai ƙara lafewa a jikinta yayinda zuciyata ta sake jin wani sabon tausayinta na daɗa huda sassa da ɓargon jikina.

Cikin tausasa kalamai masu ƙwarara gwiwa na yi nasarar sanyata komawa bacci domin bana so abun ya ƙara ta'azzara kada kuma a samu wata sabuwar ɓarakarda ban san ranar fita ba.

Sai dai kuma ni tun wannan farkawar da na yi, ban sake runtsawa ba har gari ya waye wanda ƙarfe bakwai na safe ma a ƙofar Mummy Zaliha ta yi mini.

Ina nan shanye a wurin tamkar wata garar kunya har misalin ƙarfe takwas da rabi sannan sai ga Daddy ya fara fitowa. Idonsa na sauka a kaina ya ce.

"A'a! Beenafah. Ke ce? Yanzu daman nake zancen aje a kira mini ke, kun ji ni shiru kwana biyu ba na nan tafiya na yi."

Wani irin sanyin rahama ne na ji ya ratsa zuciyata wanda har ban san lokacinda na lumshe idanuwana ba tare da cewa Alhamdulillah!.

Mummy Zaliha ce ta fito tare da Humaida da kuma twins ɗinta wato Aunty Hassana da Hussaina. Dukkan su cikin shirin fita unguwa suke da alama ma ba garin za su tsaya ba ganin yanda drivern su da kuma Biba ke ta famar fito musu da jakunkunansu.

Ina ganin ta fito na shiga gaisheta har su Aunty Hassana wanda a daƙile suka amsa min gaisuwar ta wa ba tare da ma sun ko kalli inda shirgina yake ba musamman Mummy har suka shige mota gaba ɗayansu suka wuce suka barni daga ni sai Daddy sai kuma Biba da ta juya ta koma ciki.

"Ki na jina Beenafah? Daman due ta wasu 'ƴan abubuwanda suka ta so, kamar transfer da na samu daga wurin aikina da kuma dalilin makarantarsu Husaina. Haƙiƙa suna shan wahala idan buƙatar zuwa gida ta kamasu saboda nisanda ke akwai daga Abuja zuwa nan Zamfara. Kin ga sai sun hawo jirgi daga can zuwa Sokoto, sannan daga can Sokoto su ƙara hawo Mota zuwa nan kinga akwai wahala. To shi ne muka yanke shawara ni da Hajiya Zaliha cewa yakamata mu koma can domin ni in samu sauƙi su ma kuma su Husainar su samu sauƙi. A taiƙace dai zamu koma Abuja da zama.... "

Zuciyata ce ta buga da ƙarfi har ban san lokacin da na miƙe tsaye ba haɓa na rawa na ce.

"Abuja Daddy! To ni da Ammie da Bahrain fa?"

"Eh daman ku ai za ku ci gaba da zamanku a nan ne...."

Tamkar gilashin da aka rotsawa dutse haka na ji zuciyata ta tarwatse lokaci ɗaya jin cewa wai mu a nan za mu zauna. Cikin matsanancin firgici na faɗa kan ƙafafunshi tamkar wata zararra ina mai fashewa da kuka na ce.

" Dan Allah Daddy ka rufa mana asiri kada ka bar mu a nan na roƙeka. Daddy wa muke da shi da har za ka barmu a nan? Don Allah kar ka yi haka..."

"To cewa na yi ba zan cigaba da ɗaukar nauyinku ba ne da har ki ke wannan kukan?"

"Ba zancen ɗaukar nauyinmu ba Daddy. A duk faɗin Gusau kai ne kaɗai muka sani, ta dalilin ka muke zaune a nan..."

"Ki bari in mutu tukun Beenafah kafin ki yi ƙoƙarin binneni. Ni kin ji na ce miki kuna da wani bayan ni ne? Daman ina nufin ku zauna a nan kafin na tafi can na yi settling, daga baya idan komai ya daidaitar mini sai in aiko a tafi daku. Tsawon shekara huɗu cikin ta biyar nake ɗauke da nauyinku a kaina; Ciyarwa, shayarwa, sutura, magani, hatta makaranta da na kashe kuɗina na saka ki ƙarshe asara nayi saboda daina zuwa da kikayi, na ɗauki nauyin ciwon mahaifiyarki. Duk da haka ban gaji ba sai da na kwashi maƙudan kuɗi na bayar wurin yi wa jaririn da yake cikin zanin goyo aiki wanda sai bayan na gama wahala ya mutu. To yanzu dan Allah Beenafah duk irin wannan wahalar da na yi daku tsawon lokaci mi zai sa na kasa ci gaba da kulawa da ku? Kar fa ki manta har account na buɗe muku ina tura muku kuɗi a ciki. To ko yanzu ba kasawa na yi ba, kuma ba zan fasa yi muku duk wani taimakon da na saba yi muku ba ko don kasancewarku jinin ɗan uwana. Kawai dai idan na koma can tare da ku a yanzu, wahala ƙara maye mini za ta yi domin rayuwar Abuja ta banbanta da ta Gusau, saboda haka ku yi zamanku a nan, ga gida nan babu mai tashin ku a ciki. Daga baya sai in aiko a tafi daku idan na shirya, kuma In Sha Allah zan ci gaba da tura muku kuɗi kamar yanda na saba..."

Tamkar an jefo Ammie daga sama, haka na ganta kwatsam gaban Daddy tana yi mai wani kallon mamaki da al'ajabi na tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta fashe da kuka a hankali kuma ta koma dariya. Tayi kuka tayi dariya lokaci ɗaya tare da nuna shi da yatsa tana faɗin.

"Dr. Bello Wazeer! Alhaji Mudassir Wazeer... Dr. Bello Wazeer... Alhaji Mudassir Wazeer... Bello.. Bello.. Dr.. Bello.."

Girgiza kansa yayi yana mai mayarda kallon sa gareni ya ce.

"Beenafah ki kamata ki mayar da ita ciki please. Sai kun ji Saƙo in sha Allahu zuwa wata ɗaya."

Sake matsawa na yi gaban sa bayan na rirriƙe Ammie cike da magiya ina wani irin kuka mai cike da ƙunci na ce.

"Daddy dan Allah dan darajar Allah karka yi mana haka. Daddy ko yanzu da kake tare damu ya muka ƙare ballantana ace ka yi mana nisa? Daddy Bahrain... Bah...."

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*PAGE 5*

"Kin ga Beenafah.....zuwa anjima idan masu shaguna sun buɗe ki je ki ciro dubu ɗari biyu ne na tura muku. Kin ga yanda hidima dai ta taru ta yi mini yawa, saboda haka sai ku yi maneji tukun mu gani. Kuɗin magani kuma zan yi Magana da Dr. Basheer ko nawa ne zan biya. Sannan ga card ɗina nan, idan kuna da wata matsala za ki iya kirana kai tsaye."

Wai aka ce idan gaskiya ta yi maka ya wa, sai ma ta hana maka yin magana. Muna ji muna gani Daddy ya shiga motar sa Driver ya tayar suka fita.

A dai-dai kan corner su ka ci karo da Aunty Husaina tana cikin keke-napep. Cikin mamaki da nuna tsan-tsan ɓacin rai Daddy ya fito a mota ya kalle ta yayinda take fitowa itama ya ce.

"Miye abin da ya dawo dake? Ina ita Mummyn taku take?"

"Eyyah! I'm sorry Daddy. Wallahi I forgot something ne wanda ba zan iya barin shi a nan ba, kuma Mummy ta rantse tace ba zamu dawo ba sai dai a saukeni na hawo Napep idan na ɗauki abin da zan ɗauka kai sai ka dawo da ni."

"Ta ya har kika yi sake kika bar wani abu mai muhimmanci duk tsawon kwanakinda ku ka ɗauka kuna shiri."

"Daddy ka yi haƙuri, ni ma bansan ya akayi na manta ba..."

"To miye ne wai shi ɗin da kika baro?"

Cikin nuna magiya ta ce.

"Something I can't tell, please dan Allah ka yi haƙuri na ɗauko."

Jinjina kansa ya yi alamar gamsuwa da zancen ta ya ce.

" OK to,shiga mu tafi."

Suna isa ƙofar gidan ya umarci drivern na sa akan ya parker a nan su jira ta ta shiga ta fito.

A inda Daddy ya barmu muna nan a wurin ba mu matsa ko'ina ba munata famar kukan rashin sanin makama akan wannan bahagon al'amarin da ya sake shigowa rayuwarmu ya yi mata karan tsaye.

Shigowar Aunty Husaina ita ce ta yi sanadiyyar jan hankalina na zuba mata idanuna waɗanda su ka rine akan azabar kuka. Har yanzu ban cire rai da tsammanin cewa Daddy zai iya canza ƙudurinsa na barinmu a nan ba, domin bamu da wani da zamu kira namu duk a faɗin Gusau bayan shi.

Rungumeni ta yi sosai a jikinta itama ta fashe da kukanda yake ciciyar zuciyarta tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta janye tana mai riƙo da kafaɗuna murya a raunane ta ce.

"Ki yi haƙuri Beenafah! Wallahi Allah shi ne wanda yasan abin da yake cikin zuciyata. Sam ba na jin daɗi kuma ba na farin ciki da irin halin ƙunci da wahalar rayuwar da kuke ciki. Ba ni da wani iko ba ni da wani zarafi fa ce in tanyaku da addu'a. Mummy ita ce wacce ta haifeni amma na sani Sam! Ba ta kyautawa. Yanzu ki ɗauko mini account number ɗinku zan tura miki da kuɗinda na cire daren jiya a account ɗin Daddy, sai ku samu wata sana'ar da za ku riƙa yi domin kada abubuwan rayuwa su gagareku."

Ban iya na motsa daga inda nake ba har sai da ta maimaita mini kusan sau uku sannan na je na ɗauko takardar da numbern account ɗin ke a rubuce na kawo mata. Bayan kusan mintuna uku sun shuɗe sai ta kalleni ta ce.

"Na tura miki dubu ɗari biyar Beenafah, Allah ya ci gaba da tsare ki daga dukkan sharri ko wane iri ne, Allah ya baiwa Ammie lafiya. Ki kula da rayuwar Bahrain Beenafah."

Wurin Ammie ta ƙarasa ta rungumeta sosai tana kuka na tsawon mintuna sannan daga ƙarshe ta janye ta ce.

" Ke ɗin Uwa ce mai nagarta da kuma sanin yakamata Ammie, I learned so many things daga gareki tun ban iya banbance tsakanin fari da baƙi ba. I love you so much Ammie, har abadan abada kina zuciyata. Allah ubangiji ya baki lafiya mai amfani ya kuma ƙara miki tsawon rai mai albarka."

Faɗin irin halin da zuciyata ke ciki ma ɓata baki ne. Da ana fatan mutuwa idan an shiga matsala da a yau na yi fatan Allah ya ɗauki ranmu ni da Ammie da kuma Bahrain ko don mu huta da duniyar baki ɗaya. to amma kuma sanin cewa hakan baya daga cikin ɗabi'ar musulmi na ƙwarai,Sai na sake fashewa da kuka,haka na dinga mutuwa ina dawowa tsawon lokaci sannan daga ƙarshe na kama Ammie wacce ba zance ga halin da take ciki ba a yanzu muka koma ciki, domin dai ko hawayen naga daga ƙarshe babu su akan fuskarta,Allah kaɗai yasan abin da yake zuciyarta.

Misalin sha biyu na rana ina nan zaune na buga uban tagumi abin duniya duk ya bi ya isheni. Ammie ma tana kwance kurum ban san abin da take nazari ba sai na jiyo sallama kamar muryar Biba.

Jiki ba ƙwari na lallaɓa na fito, ashe kuwa ita ɗin ce dai. Da mamaki na kalle ta na ce.

"Ke ma Biba ba za'a je Abujar dake ba ne?"

Fuska tuƙun-tuƙun ta girgiza kanta ta ce.

"A'a, da ni za'a koma. Na tsaya ne sai da na jira dangin Mummyn su ka zo su ka kwashe komai kab na amfanin gidan wanda zai lalace, sannan kuma na tsaya na ƙara gyara mata komai kamar yanda ta ce. Yanzu zamu tafi a mota tare da drivern Humaida."

Ƙaramar waya ta ciro daga ƙugunta tare da charger ta damƙa mini a hannuna ta ce.

" Wannan wayata ce Beenafah, ki riƙe ta a hannun ki... "

" Biba idan kika ba ni wayar ke fa? Miye za ki cewa Mummy? Sannan ni mi ma zan yi da waya?"

"Zan faɗamata cewa wurin zuwa gidan iyayena ta faɗi a hanya. Beenafah ku yi haƙuri da rayuwa, ni ɗinnan ba kowa ba ce fa ce 'ƴar aiki, kina ji hatta iyayena ta ce idan har wata alaƙa ta sake shiga tsakanin ku da su to daga ranar ta koreni daga aiki, kuma ke ma ba za ki so hakan ta faru ba, domin ni ce nike ɗauke da su da wannan albashin da ake biyana. Abu ɗaya nake da shi da zan iya taimaka miki. Yanzu ki ɗauko hijabinki ki zo mu tafi.. "

Ɗan Jim na yi ina nazarin maganar ta cewa na ɗauko hijabina...

" Kar ki damu, nan ne maƙota ba ni sa."

Ina cikin tunani sai ga Bahrain ya dawo daga islamiyya. Ƙoƙarin saita kaina na yi ina wani murmushin ƙarfin hali, na kalli Bahrain ɗin wanda ya yi ni sa da yin magana da Biba na ce.

" Bahrain! Ka zauna da Ammie ina dawowa yanzu."

Ɗakin ya shiga ya watse littafan sa yana nuna mata karatunda aka yi mu su yau, daga nan ni kuma muka fice tare da Biba.

Wani babban gida ta kaini wanda yake bayan Layinmu. Ɓangare biyu ne, a ciki sai muka nufi ɓangaren dama.

Mun kai kusan minti goma a zaune sannan sai ga wata mata ta sauko daga saman stairs a hankali ta ƙara so ta zauna.

Saukowa Biba ta yi daga kan kujera ta zauna a ƙasa, hakan yasa ni ma na bi ta muka gaishe ta.

Bayan ta amsa ta kalli Biba sai kuma ta kalleni ta ce.

"Biba, wannan fa?"

Kwantar da murya Biba ta yi sosai ta ce.

"Aunty Labiba gidan da nake aiki ne suka tashi za su koma Abuja, to kuma da ni kaɗai za su tafi. Shi ne na kawo miki marainiyar Allah ko kina da wani aikin da za ta riƙa yi miki. Yarinya ce mai natsuwa da hankali, daga ita sai mahaifiyarta da kuma ƙaninta suke rayuwa. Idan Allah yasa akwai dama dan Allah a ba ta wuri."

Shiru ta yi tsawon lokaci tana ƙare mini kallo har sai da cikin raina na ji na tsargu, sannan daga baya ta sauke ajiyar zuciya tare da jinjina kai ta ce.

" Biba kin san fa tun wancan matsalar da aka samu na daina yin mai aiki, ko Hajjo ma zuwa take tana komawa..."

"Dan Allah ki yi haƙuri ki shiga lamarin yarinyar nan, wallahi ita ba kamar sauran masu aikin da kika taɓa yi ba ne..."

"Haka ki ke cewa kullum ai.."

"Wallahi Aunty Labiba wannan ba haka take ba. Dan Allah..."

" Na ji Biba, amma dai kin san ni ba na son aikin kwana... "

" A'a, ai ba aikin kwana bane, suna da gidan su, nan ne baya ba nisa, kina iya ma daga zaran ta kambala aikin ta koma gida abin ta."

Sake jinjina kanta ta yi sannan ta ce mini.

"Ya ya Sunan ki?"

A hankali na furta mata.

"Beenafah."

"Kin iya shara da goge-goge?"

Biba ce ta karɓe zancen da faɗin.

"Ai idan wannan ne kam ba matsala...."

"Biba ba ke na tambaya ba."

Matar ta faɗi hakan ta na mai tsatstsareni da ido.

Ganin haka yasa na gyaɗa kai na a hankali na ce.

"Na iya."

"Ok. Zuwa kwana uku sai ki zo da safe kafin nan In Sha Allah na yi magana da babansu."

"Allah ya kaimu, na gode sosai Allah ya saka da alheri."

Daga haka muka yi sallama muka fito wanda muna tafe Biba na ƙara mini haske akan rayuwar Hajiya Labiba. Muna isa ƙofar gida muka taradda Ilyas yana jiran Biba wato drivern Humaida.

" Biba ina ki ka je haka? Tun ɗa zu Hajiya ke kirana ta ce mini tayi ta kiran wayarki kashe, ban faɗa mata cewa kina tare da Beenafah ba kamar yanda kika roƙa, da ta matsa ma ƙarshe ce mata na yi na shiga kina banɗaki, saboda haka ki amshi wayata ki yi magana da ita kamar yanda ta bayar da umarni."

Salin-alin na yi shigewata gida don kada ma na tsaya ƙarshe na ƙare da jin abin da zai baƙanta mini raina.

Biba kuwa, tana karɓar wayar Hajiya Zaliha ta hau ta da faɗa tamkar za ta cinyeta ɗanye Nama, wai gidan ubanwa ta kai wayar ta. Ta na faɗa mata cewa wai wayar ɓata ta yi ta hau ƙundumomata zagi da cin mutunci wai tunda ba ta san zafin kuɗi ba dole ta sake baki ta yasar da waya, to wallahi ita babu ruwanta sai dai ta sake saya mata wata a cikin albashinta na wannan watan domin ba za ta ɗauki asara ba. Bayan ta gama ci mata mutunci tace ta yi maza ta hau mota su tafi.

Ina zaune ina ba Ammie magani Bahrain ya kalleni ya ce.

"Aunty Beena wai da gaske su Humaida sun koma Abuja?"

Ban san lokacin da na waigo na kalle shi ba domin tambayar ta shi ta zo mini ne a ba za ta.

"Aunty Beena tambayarki fa nake."

Lumshe idanuna na yi sannan na buɗe a hankali ina mai jinjina kaina na ce.

"Eh."

"To mu fa Aunty Beena?"

"Mu za mu je daga baya ne Bahrain, Kaga Ammie na zuwa asibiti, idan muka koma can zai yi mana ni sa sosai har ya kasance ba zamu iya zuwa ba..."

"But Aunty Beena ko a Abujar ma akwai hospital mana..."

"Bahrain! Akwai dalili mai ƙarfi da yasa ba zamu tafi yanzu ba sai nan gaba kaɗan, ta inda aka hau bishiya dole ta nan ake sauka saboda haka sai Ammie ta gama karɓar magani sannan za mu tafi. Ba na son yawan tambaya Bahrain ka sa ni."

Jinjina kai ya yi ya ce.

" Allah ya ba ki haƙuri. Ammie idan ki ka yi bacci ki ka tashi zan ƙara karanta miki karatuna ki ji idan na yi daidai."

A hankali ta gyaɗa kanta ta ce.

" Allah ya kai mu to, kuma yasa ka iya ɗin."

***

Tun da Biba ta ba ni wanna wayar wadda ba simcard a ciki sai Memory only wan da yake cike da abubuwa, waƙoƙi, complete ƙur'an, tafseer-tafseer da sauran su. Hakan yasa Kullum yanzu cikin shan karatu muke, ƙira'a mai daɗi da sanya nutsuwar ruhi, ko kuma wani lokacin tafseer na malamai daban-daban.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull