Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 4

Ganin ido complete - Chapter 4

Ganin ido complete Chapter 4: Ganin ido complete Chapter 4. Kwana biyu da tafiyar su Daddy Abuja, muna zaune misalin ƙarfe huɗu na yamma ina tuƙa mana tuwo…

3,367 words

Kwana biyu da tafiyar su Daddy Abuja, muna zaune misalin ƙarfe huɗu na yamma ina tuƙa mana tuwo Ammie na zaune a gefena ta yi shiru wanda ban san mi take nazari ba. Kwatsam ta buga ihu tare da miƙewa a tsaye jiki na rawa tana ta famar girgiza kai tana kuka sosai tana faɗin.

"NO.. NO......This is not happening...Abuja!...Abuja..Yes! Abuja, dole za mu je Abuja muma ko Beenafah?....."

Ƙoƙarin ni ke in riƙeta amma na kasa, domin a wannan karon sosai jikinta ya shiga tsima tana kakkarwa, kafin na yi aune har ta runtuma da gudu ta nufi ƙofar gate,kuma cikin rashin sa'a ni da kaina yau na bar ƙofar a buɗe, shiyasa tana zuwa ta fice da gudu tana ta famar faɗin Abuja a bakinta.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 6*

Tamkar wadda wani mummunan abu ke farautar ranta, haka ta dinga falfala gudu ina ta faman bin ta. Duk inda ta jefa ƙafarta nan ni ma nake jefa ta wa. Ga unguwar tamu tsit! ba mutane tamkar an yi ruwa an ɗauke, wanda tun azal haka ta gada. Kuka nake ina kiran sunanta da kuma neman agajin mutane duk da cewa ban ga ko tsun-tsu ya wulga ba.

Daman daga ka fito titin gidanmu ka nauso kaɗan za ka tarar da corner mai shimfiɗe da wata kwaltar wacce ta miƙe ta ɗauki hanyar babban titi baki ɗaya.

Ina karyo kan corner ɗin, caraf! Idona ya sauka akan Ammie wacce wata mota ta kaɗe ta fit ɗaya ta yi ta mulmula akan titin sanadiyyar buguwar da ta yi.

Kan ta na yi ina mai sake kwaɗa ihun da duk wani mahaluƙin da ya ji ni sai ya tausaya mini, lokaci guda muka isa gareta ni da wani mai Keke-napep tare da Mata guda ukun da ya ɗauko a cikin Napep ɗin ta sa.

A gigice na rungumota jikina ina wani irin gurnanin Kuka na tashin hankali da ruɗewa.

"Ammie... Ammie..! Ammie dan Allah ki tashi.... Ammie please don't do this to me, Wallahi idan kika yi haka baki yi mana adalci ba... Ammie.."

Cike da tausayi mai Napep ɗin ya ce.

"Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki akwai sauran numfashi a tare da ita, gashi.. Duba ki gani..."

Cikin gigita na ɗago na kalle shi tare da Matan da ke tare dashi na ce.

"Kalli Jini yanda yake fitowa ta hanci da bakinta bawan Allah.. Daman ga shi ba ta da lafiya, wallahi ba ta da lafiya...."

"Allah sarki! Ki yi haƙuri in sha Allah za ta tashi..."

Kallon gefen da Matan ke tsaye ya yi yana mai saka hannayensa ƙarƙashin ƙeyar kanta ya ce.

"Malamai dan Allah ku taimaka mu saka ta a napep ɗinnan mu kai ta asibiti ka da mu tsaya ɓata lokaci."

A tare mukayi nasarar sanyata wanda nice na fara shiga sannan aka shigo da ita na rungumeta zuwa jikina.

"Kunga yan da Allah ya yi ikon sa ko? Dan Allah ku yi haƙuri, ku je ku samu wani ya ƙarasa da ku inda za ku tafin."

"Ba komai, Allah ya bata lafiya."

Matan su ka amsa lokaci ɗaya suna ma su juyawa su ka wuce.

Mutumin da ya kaɗe Ammiena duk budurin da muke yana zaune a motarsa wanda nasan yana ciki hankalinsa kwance yana kallon mu, sai dai mu ba ma iya ganin sa kasancewar motar tasa duk tinted ce, gaba ɗaya ba ka iya hango komai sai tsananin duhu sai dai shi dake ciki yake iya hango na waje.

Sosai na ƙurawa motar ido ina kallonta da mamakin da ya kusan sumar dani. Bayan ya ga mai Napep ɗin ya tayar ya hau hanya shima sai a sannan na hangosa a dai-dai lokacin ya tayar da motar ya wuce abin sa.

"Baiwar Allah wace asibiti zan kai ku?"

Wannan tambayar ita ce ta sanyani dawowa daga duniyar tunanin da na abka inda zuciyata ta dugunzuma zuwa ga motar da ta kaɗe mini Ammie na har ta ɓacewa ganina....

"Baiwar Allah na ce wace Asibitin zan kai ku?"

" Daman a Sokoto muke ganin likita duk farkon wata domin tana da matsalar ƙwaƙwalwa..."

"To ai yanzu kinga halin da take ciki dole tana da buƙatar agajin gaggawa, idan ki ka ce za ki nufi Sokoto da ita a yanzu koda a motar gida kuke ai akwai hatsari da kuma barazana ga lafiyarta, kingadai yan da ta ke ta faman zubda Jini."

Cike da gamsuwa da bayaninsa na jinjina kaina na ce.

" To ka kaimu Jan-bulo. Daman can ne farkon inda muka fara jinyarta a lokacin baya wanda daga nanne aka yi referring ɗinmu zuwa Sokoto."

***

Federal Medical Centre, Gusau, Zamfara state, Nigeria.

Har muka isa asibitin hawayena ba su daina tarara ba, ina yi ina hango makomarmu ni da Bahrain idan yau Ammie ita ma ta faɗi ta mutu. Muna zuwa ba ɓata lokaci muka shige Accident and Emergency unit da ita. Bayan sun gama ɗaukar dukkan bayananmu nan take su ka shiga ba ta taimakon gaggawa. Bayan kusan hour biyu sun shuɗe sai ga wani likitan ya fito ya miƙo mana takarda ya ce muje mu biya sannan kuma naje na ɗauko katinta wanda na ce mun taɓa jinya nan a baya.

Cikin nuna damuwa mai napep ya ce.

"Likita da fatan tana lafiya."

Jinjina kai likitan ya yi da murmushi a fuskar sa ya ce.

"Da sauƙi In sha Allah."

Kallon sa ya mayar gare ni ya ce.

"Alhamdulillah! Daman ɗa zu, ina ƙoƙarin karya corner ne sai kawai ta fito ta gabana ni kuma cikin sauri na yi ƙoƙarin na kauce mata, sai wancan mutumin shima ya karya kan motar sa ba shiri, maimakon ta tsaya a inda take sai ta sake komawa hannun sa shi kuma yana ta ƙoƙari amma bai yi nasarar kauce mata ba, domin a tsiyace yake da mugun gudun da ba zai iya tsayawa a lokaci ɗaya ba. To kin san halin mutane a yau, musamman masu kuɗin nan, abu kaɗan suke jira, tun da naga bai fito ba na fahimci cewa sam bashi da niyyar ya taimaka shiyasa ban ma nufesa ba. Yanzu ga wannan... "

Ya ƙarashe maganar yana mai sanya hannu a cikin aljihun wandonsa ya ciro kuɗi ya ƙirga sannan ya miƙo mini yana faɗin.

" Ki yi haƙuri dubu biyar ce ba yawa, wallahi cinikin kenan da na yi. Amma ki ɗauko wayarki ki kira babanki ko kuma mu tafi na kai ki gida ki taho da wani, kada na barki a nan ke kaɗai."

Girgiza kaina na yi ina ta faman share hawayena na ce.

"Ka barshi kawai ai ba laifinka ba ne, ko a hakan ma mun gode sosai Allah ya biya. Ko ba ka bamu komai ba ka fiye mini wanda ya kaɗe ta ya tsaya yana jiran mutuwarta, da wannan taimakon har abada ba zan manta da kai ba. Ina da waya amma ba layi a ciki, sannan kuma a yanzu gaskiya ni ce kaɗai zan iya zaunawa da ita kafin na samu kiran en uwanmu su zo."

"Allah sarki! To muje na kai ki gidan ki ɗauko abin da za ki ɗauko sai na dawo dake."

Sosai na lumshe idanuna a cikin Napep ɗin ina ta lissafin rayuwa har muka iso dai-dai inda aka kaɗe Ammie, daga nan ya tambayeni cewa ina ne gidanmu, sai na nuna masa.

Ina shiga na tarar da Bahrain zaune ya haɗe kai da gwiwa yanata faman kuka. Yana ganina ya taho da gudu ya ƙanƙameni sosai yana faɗin.

"Aunty Beena na ji tsoro sosai, na dawo ke da Ammie ba kwa nan, gidan su Humaida ma ba kowa, mai gadi ma baya nan..."

Ni ma ɗin rungume sa na yi, cikin rarrashi na ce.

"Ka yi haƙuri Bahrain...Ka yi haƙuri. Muna asibiti Ammie ba lafiya, ka dai san yanayin jikinta ba sai na faɗa maka ba. Abin da nake so da kai a koda yaushe ka zama jarumi sannan ka ƙwarara kan ka domin mu samu ciwon Ammie ya warke baki ɗaya.....Mu je na ɗauko katinta da ATM card sai mu tafi asibiti."

" To Aunty Beenafah, ina mata addu'a Allah ubangiji ya bata lafiya. Ai ko a Islamiyya kullum sai na cewa Ra'is ya sanya mahaifiyata a addu'a ba tada lafiya."

"Yauwa yaron kir ki. Zo... Zo mu tafi ana jiranmu a waje."

Ciki na shiga na ɗauko mana duk wani abin da nasan za mu buƙata domin in dai zaman asibiti ne na riga da na saba a yanzu. Wuri na ɗauko na kwashe tuwon sannan na juye miya daban na mayar da komai ciki sannan na janyo ƙofa domin dai ba mu taɓa rufe gidan ba tunda muke. Ko gate ɗin ma haka muka barshi bayan na sakaya muka shiga napep ɗin muka koma asibiti.

Muna shiga aka sake bamu wata takarda again gashi ko ta farkon da akace muje mu biya bamu biya ba.

Wurin biyan kuɗin mukaje wanda nan take aka caji kuɗi kusan dubu ashirin da takwas da ɗari bakwai, ƙuri! mai Napep ɗin ya yi yana kallona domin da alama ya razana.

"Karka damu akwai kuɗi a tare dani zan biya, ko tsaya mana da ka yi kawai na gode sosai."

Bayan mun biya mukaje muka karɓi magani muka koma still tana ciki ba'a fito da ita ba. Muna nan aka shige da case folder ɗinta, sai a sannan na ce mai napep ya aramin wayarsa na kira likitanta. Ina kiran sa yana jin ni ce ya kashe ya kira ni back.

Bayan mun gaisa na shaida masa halin da muke ciki da kuma cewa da suka yi na kawo mu su card ɗinta.

Umarni ya ba ni da cewa na je na kai musu waya ya yi musu magana ko kuma na ba su numbernsa su kira sa. Ba ɓata lokaci na yi duk abin da ya ce wanda su da kan su suka karɓi numbern ta shi su ka kirasa.

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare aka fito da ita zuwa Psychiatric Unit da ke cikin asibitin. Gida aka sake turani na ɗauko magungunanta na dawo. Sai a wannan lokacin Ashiru mai Napep ya yi mini sallama ya tafi gida.

Still a daren ranar nan sai da aka sake bani takarda na je na biya kuɗin wani maganin kusan dubu talatin, na karɓo a pharmacy na kawo musu.

Sai da muka kwana huɗu a asibitin sannan Ammie ta farka,sai dai kuma, farkawa marar daɗi cikin mummunan yanayi wanda ya sakani kuka, kuka fiye da wanda nayi a baya. Domin sabbatu ta shiga yi ba sama da ƙasa, ta ƙarfin tsiya ta shiga neman cisge aikin da akayi mata a hannun damanta sanadiyyar karaya da ta samu. Cikin tsananin ɗaga murya da ƙaraji na shiga ihun kiran likita domin ba zan iya ɗagawa na barta ba.

Halin da Ammie ta shiga a wannan lokacin haƙiƙa ya sakamu cikin tashin hankali da gigita. Hali ne wanda ko maƙiyanta ya kalle ta sai ya tausaya mata.

Nan take likitoci suka shigo suka rufu akanta, bayan sun gama dubata ba jimawa bacci ya ɗauke ta da alama allurar bacci suka yi mata.

Mun share kusan sati Ammie tana cikin wannan halin wanda har ta kai ta kawo ma bana son ta farka gudun kada ta tashi ta nemi fama ciwon ta.

Ga damuwar Bahrain ta wani fannin tana matuƙar sosa mini zuciya, bana son ganin sa cikin halin da yake.

Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. A hankali a kwana a tashi muka shiga cikin sati na biyu wanda Alhamdulillah! Jikinta ya fara sauƙi ciwon ta shima da sauƙi sosai domin a yanzu ta daina farkawa cikin firgici da tsoro ko kuma sabbatu. Sai dai idan ta farka tayi shiru bata cewa komai ba.

Yau ma koda ta farka, a lokacin ina zaune gefenta na ƙura mata ido kawai ina kallonta yayin da Bahrain ke can waje akan tabarma da waya a hannunsa yana sauraren karatu.

"Allah sarki Ammiena! kin farka?"

Na furta mata hakan ganin yanda ta ƙureni da kallo. Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana kallona kamar yanda ta saba sannan daga ƙarshe ta gyaɗa kanta a hankali ta mayarda idanunta ta rufe sai hawaye. Cikin sauti marar tashi ta ce.

" Bani ruwa Beenafah.."

Da sauri na buɗe locker na ɗauko ruwan gora na bata tasha a hankali na mayar a locker sannan na kalle ta cike da wani sabon tausayin ta na ce.

"Sannu Ammie, Allah ya baki lafiya, Allah yasa wannan ciwon ya zamto kaffara. Kada ki zafafa tunani kin ji Ammie,Bari na kira likita."

Ina fitowa na kalli Bahrain na ce.

"Bahrain ka je Ammie ta farka, zan je na kira likita yanzu."

***

Sati Uku mukayi a asibitin, wanda mun kashe kuɗi sun kai dubu ɗari huɗu da wani abu. sai sayen magani muke, yau wannan gobe wannan. Amma Alhamdulillah! Abu mafi muhimmanci shine, ta samu sauƙi sosai wanda wannan shi ne babban burinmu.

Yaya Ashiru, wanda ya zamto Yayana a yanzu domin ya tsaya mana a lokacin da ban yi tsammani ba. Da shi muke duk wannan zirga-zirgar, ko sau ɗaya bai taɓa nuna mana ya gaji ba, kuma duk wani abin da ya kamata ace naje nayi shi yake tsayawa tsayin daka ya yi mana shi, hakan yasa na ji sa wani mutum na daban a cikin duniyata.

***

Ranar Monday da safe likita ya kirani office ɗinsa ya bani takardar sallama tare da takardar refferal zuwa asibitin Sokoto inda muka saba jinya. Amma ya ce zamu iya zuwa gida mu shirya zuwa kwana biyu sai mu tafi, domin condition ɗinta ya yi sauƙi sosai In Sha Allahu babu wata damuwa. Yaya Ashiru shine wanda ya zo ya kaimu gida da kansa.

A daren da muka koma gida ne naje shagon Baba mai shago na bashi katin Daddy na ce ya ɗauki numbern wayarsa ya kira shi ya ce mi shi Beenafah ce.

Na fi minti talatin a tsaye bai kira ba, daga ƙarshe na ba shi ɗari biyu na ce ya saka kati ya kira mini shi.

Sake kiransa ya yi ya miƙomin wayar na kara a kunnena, ƙirjina na dukan uku-uku na yi masa sallama.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*

*FREE-BOOK*

*PAGE 7*

"Daddy ina wuni."

Jin ya yi shiru yasa na ce.

"Beenafah ce Daddy.."

Daga can ɓangaren Daddyn cikin nuna kamar alamun mamaki ya ce.

"Beenafah?"

"Eh Daddy ni ce. Daman Ciwon Ammie ne ya tashi har ta fito titi aka haɗa da tsausayi sai mota ta bigeta, to munfi sati uku a asibitin Janbulo kuma jibi zamu wuce Sokoto domin tana cikin halin jinya sosai har karaya ta samu a hannunta na dama...."

"Allah sarki! Allah ya ba ta lafiya."

"Amin. To Daddy daman..."

Da sauri ya tare numfashina da faɗin.

"Dan Allah ki dakata mini Beenafah! Kin fi kowa sanin ina wurin aikina yanzu haka, yakamata ki riƙa sanin lokutan kirana, mts!"

Daga haka ya yanke kiran ba tare da ma ya tsaya ya saurari maganata ba. Bayan na tabbatar ba ƙara kira zai yi ba yasa na miƙawa Baba mai shago wayarsa a saɓule ina mai tsiyayar da ruwan hawaye masu cike da ɗaci da baƙin cikin daddy na juya na koma gida.

Ina shiga na tarar da Malaman islamiyyarmu su huɗu tare da ɗalibansu rututu suna yi wa Ammie addu'a.

Zaunawa na yi nima tare da su har aka kambala addu'ar, sannan na gaishe da Malaman na kuma yi musu godiya. Wallahi har cikin raina na ji daɗin ganin su da kuma ƙaunar da suka nuna a garemu. Hakan sai ya mantar dani baƙin cikin daddy da na dawo da shi daga shagon da naje.

Bayan mun rako su, a bakin gate Ra'is ya kalleni ya ce.

"Beenafah shikenan dai da gaske kin yafe Islamiyyar ko?"

Girgiza kaina na yi ina murmushin ƙarfin hali na ce.

"Ba haka ba ne Ra'is, nima ina son islamiyya amma kuma dole ce tasa na barta, idan ina da rabo watarana zan dawo."

"To Allah ya taimaka, Allah ya bata lafiya. Kuma dan Allah ina roƙo; Bahrain yana daga cikin yara masu hazaƙa da muke alfahari da su, a daina wasa da makarantarsa, idan yazo sati biyu cikakke sai an samu tsawon kwanaki bai zo ba, kinga hakan dole zai yi affecting ɗinsa, domin da zaran an wuce shi an wuce shi ba za'a dawo baya saboda shi ba."

Jinjina kaina na yi a raina ina jin ba daɗi na ce.

" Haka ne Ra'is, wallahi duk abinda ka faɗa gaskiya ne, to amma ko yanzu ina ƙara baka haƙuri domin uzuri ne wanda ban san ya zan yi ba,amma In Sha Allahu za'a gyara."

" To Allah ya bada iko. Allah ya bata lafiya mai albarka."

"Amin Ra'is, na gode sosai Allah ya saka da alheri."

Akan hanyarmu ta dawo daga rakiyar su na cewa Bahrain.

"Kai ne ka ce su zo duba Ammie?"

Girgiza kai ya yi yana riƙe da hannuna ya ce.

"A'a. Ina zuwa Ustaz ya ce mini miyasa na daina zuwa kwana biyu, shine na ce mishi muna asibiti an kwantar da Ammienmu ba lafiya,shikenan ya ce na wuce na zauna, to ana tashi sai ya kirani ya ce mini za su taho tare dani duba Ammie."

"Allah sarki! Allah ya saka musu da alheri."

"Amin aunty Beena. Ustaz ya ce addu'a waraka ce, indai aka dogara ga Allah akayi ta addu'a ciwo kowane iri ne za'a warke..."

"Wannan haka yake Bahrain, Ustaz gaskiya ya faɗa, muna kan addu'ar akodayaushe, Allah yasa mu dace amin."

Haƙiƙa koda na taso ni ɗin na kasance mai ƙwazo sosai ta kowanne fanni, da hakan na kafe manyan burika guda biyu a cikin raina wanda both Ammie da Abbie suke kan wannan burin su ma. Sai dai kana naka Allah yana na shi iko,ta dalilin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki dare ɗaya,yasa dole na haƙura da nawa mafarkin domin ba zan bar mahaifiyata ita kaɗai ba na fita makaranta, amma kuma na ɗauki alƙawarin bai wa Bahrain cikakkiyar kulawa da goyon baya akan islamiyya da bokonsa, mafarkina da ban samu damar cikawa ba sai ya cika mini shi inda rai da rabo. Ɗan wanda na samu Allah yasa masa albarka ya hore mana hanyar kulawa da na Bahrain.

***

Washe gari Ina zaune a bakin famfo misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe ina wanki na ji ana ta bubbuga ƙofar gate ɗinmu. Cikin mamaki na je ina tambayar waye ne.

"Ashiru ne..."

Kafin ma ya iyarda rufe bakin sa cikin farin ciki na je na buɗe. Turus na yi ina kallon taron bataliyar da yake tare da su.

Murmushi ya yi ya ce.

Shima dai murmushi ya sakar mini tare da kallon su ya ce.

"Iyayena ne da ƙannaina Beenafah. Cewa suka yi suna so su zo su ga Ammie da jiki."

Cikin nuna zallar farin ciki na ce.

"Allah sarki! Sannunku da zuwa....Ku shigo ciki dan Allah."

Tare muka shiga har ciki inda Ammie ke kwance akan katifa saman varendar, ga waya a gefe sautin karatun alƙur'ani yana ta tashi mai taushi da sanya nutsuwa.

Daman a nan na fito da ita kusa da ni domin na riƙa hango ta da kyau kada na barta a ɗaki ita kaɗai. Tunda muka dawo daga asibiti bacci ya ƙaurace mini domin dole nayi kaffa-kaffa kada ta yi ƙoƙarin fama ciwon hannun ta da akayi ɗori. Cikin ikon Allah kuma, tunda muka dawo daga asibitin, lafiya ƙalau take babu alamun motsawar yanayin ta har yanzu, ko don sanadiyyar zafin ciwon da take ciki ne oho! Koda yake kuma babu abin da ya gagari Ubangiji, Allah na gode maka, Allah ka ƙara bata lafiya da nutsuwar ruhi amin.

Tabarma na shiga na ɗauko musu na baza ta a gaban su na ce su zauna. A hankali na taimakawa Ammie ta tashi ta zauna sannan na gaishe da su, bayan mun gaisa na kalli Ammie na ce.

"Ammie waɗannan iyayen Yaya Ashiru ne da ƙannensa suka zo duba ki."

"Allah sarki! Sannun ku da zuwa.."

A tare duk suka amsa suka gaggaisa sannan ɗayar dattijuwar dake gefen Yaya Ashiru wacce da alama ita ce mahaifiyarsa domin sun yi kama sosai ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull