Ganin ido complete - Chapter 32
Ganin ido complete Chapter 32: Ganin ido complete Chapter 32. "ALHAMDULILLAH! Yaya MOHAA ya zama Ango.... A Wannan yammar ta ranar Juma'a an ɗaura maka…
3,353 words
"ALHAMDULILLAH! Yaya MOHAA ya zama Ango.... A Wannan yammar ta ranar Juma'a an ɗaura maka AURE da kai da BEENAFAH.... Allah ya amince ya nufa a wannan karon Daddyn Raudah...yau ka zama ango kamar sauran mazajen duniya...Beenafah a yau ta zama mallakin ka,matarka, ƙarƙashinka ikon ka...ƙarƙashin inuwarka Ya Mohaa...Indai da rai da rabo, watarana Jariri ango ne..."
A hankali ya sulale ya zube daga inda yake tsaye rijib zuwa ƙasa ya faɗi somamme...Maƙarrabansa dake daddafe da shi,da mugun gudu suka yo kanshi cikin tashin hankali suna kiran Sunan sa,....
Daga gefen Aunty Labiba kuwa, jin yanda suke ta ihun kiran sunansa ya sa ta fasa nata ihun kamar zata shige cikin wayar ta gansa a gabanta ta shiga kiran sunan sa a gigice...
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 30*
"Na shiga uku na ni Labiba! Miye na aikata haka? Miye zan faɗawa Hajiya akan wannan abun! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!! sai da na ce a'a, amma haka kika dage Beenafah..."
Ta faɗa tana ƙara fashewa da wani irin kukan tashin hankali wanda duk inda ke wurin sai da hankalin shi ya ta shi.
Still wayar har yanzu da ta duba is still on call ba a yanke ba. Hakan yasa a gigice ta sake kai wayar a saitin kunnenta ta ce.
" Hallo Sir Haroun...Hallo Sharath! Please what happened to him?? Please dan Allah ku ce mini Yayana yana lafiya dan Allahhh..."
Muryasa a can ƙasan maƙoshi a hankali ta jiyo sautin muryar sa Calmly yana faɗin.
"I'm safe Labiba....Ki kwantar da hankalinki babu abin da ya same ni..Kin tabbata cewa maganar da kika faɗa mini ba wasa da hankalina kike so ki yi ba kuwa...Ta ya ya ma hakan zai yiyu??"
Wata irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke wanda har su Ammie dake zagaye da ita suna iya jiyo sautin a fili sannan ta yi Hamdala ga Allah, a hankali ta lumshe idanun ta jin wani irin daɗi da ya lulluɓeta tana mai jinjina masa kanta tamkar yana a gaban ta tace.
"Yayana! Ta ya ya zanyi iya yin wasa da hankalinka a irin wannan Issue haka? Tun jiya fa muke ta tattauna maganar nan da kai har zuwa safiyar yau ɗinnan kuma ka amince Yaya. Yanzun nan aka ɗaura maka aure wallahi da gaske nake maka, ban isa na yi wasa da kai ba ai domin kai ɗin ba abokin wasa na ba ne...."
Cikin rashin iya tantance yanayin da yake ciki ya lumshe idanunsa a hankali sannan ya buɗe yana faɗin.
" I were thought cewa komai duk ƙarya ne kamar yanda ya saba faruwa Labiba.....Na ɗauka duk kina wannan ne kamar yanda kika saba domin kawai ki ga cewa na samu farin ciki..Ko kuma dai mafarki nake..."
Muryarta har tana sarƙewa wurin tambayar sa cewa.
"Yanzu kana nufin kana nan ƙalau! Baka jin komai alamar ciwo ko wani abu a jikinka? Baka ji alamun wani abu mai yanayi da alamar Aljanu ba?"
"Calm down Labiba! I'm fine. Bana jin komai fa ce jin kamar maganar da kike faɗa mini wasa kike ba gaskiya bane... Na sarƙe da maɗaukakin mamaki ne Labiba..."
Cike da murmushin nasara ta shiga jinjina kanta tana faɗin.
"Kawai ka maimaita abin da zan faɗa yanxu dan Allah Yaya... Ka ce Alhamdulillahillaziy bini'imatihi tatimmussalihat! Alhamdulillahillaziy an'ama alayya-wa-lam yaj'alni minash-shakirin!!! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!!!"
A hankali ya maimaita duk abin da tace tamkar wani ƙaramin yaro mai koyon magan sannan daga ƙarshe ta ce.
" To Yaya, yanzu kuma za mu shiga plan B Insha Allahu, just stay tune and enjoy your self. I will get back to you soon."
Miƙewa tayi tsaye cike da farin ciki ta rungumoni wanda ni tun da Fakiha ta janyoni muka shigo gidan na kasa yin wani ƙwaƙwƙwaran motsi ganin yanda take kuka na tashin hankali. Suman tsaye na yi jin yanda ta gigice wanda mu duk a zaton mu wani mummunan abu ya faru da shi. Sai dai jin cewa yana cikin ƙoshin lafiya, yasa nima na ji bugun zuciyata ya ɗan daidaita sannu a hankali. Kamar yanda yace yana lafiya, nima haka ɗin ce a gare ni, domin tun da akace an ɗaura har yanxu ko gizau ban yi ba da sunan wai wani ciwo ko kuma alamun aljanu,duk da ina kalle da yanayin Ammie wacce tun da muka shigo idonta ke kaina cike da ƙwarin gwiwa nake kallonta ina jinjina mata kai na alamar ina lafiya ta kwantar da hankalin ta.
" Kin ga mun yi nasara ko Beenafah? Alhamdulillah Allah abin godiya. Ina miki kallon ƙaramar yarinya marar lissafi, ashe-ashe ke ce silar juyawar allon ƙaddarar ɗan uwana...."
*******
Gefen su Mummy kuwa, plan ya hau dai-dai, domin Ameer da iyayensa sun amince da wannan haɗin cikin sauki ba ma kamar yanda suka tsammata ba. Komai ya zo musu cikin sauƙi.
Hakan yasa suka ci gaba da shirin tafiya. Tuni hankalin Mummy ya kwanta tamkar ba ita ce ta shiga tsananin damuwa ba akan dalilin ɓatan Hassana. Amma lokaci ɗaya, wannan plan ɗin yasa ta manta komai tare da ci gaba da abubuwanta. Sai dai kuma, har yanxu ba ta yiwa Hafiz magana tun da ya sauko ƙasar har yanzu ko kallon inda yake ba ta yi.
A yanda suka tsara, gobe Sartuday za su taso daga Abuja zuwa Gusau. Daga zaran sun iso Daddy da kanshi zai je tare da Uncle Isma'ila su ɗauko Beenafah da Bahrain, kuma a wannan karon ya shiryawa Ammie ko shi ko ita, dole ɗaya daga cikin su ne zai yi nasara, ko dai ita tayi nasara akan shi ko kuma shi ya yi nasara akanta, kuma shi ne mai nasarar saboda haka dole cikin biyu ta zaɓi ɗaya;kodai ta bashi yaran shi ya bata kuɗin mota ta koma ƙasarsu, ko kuma ta yi biyu babu. Yana da hanyoyi da dama da zai iya yin shari'a da ita kuma dole kotu ta bashi yara ita kuma taje can ta ƙara ta.
*********
Gefen Ashiru kuwa. La'asar sakaliya ya faɗo gidan tare da samun bakin bishiyar Mangoron gidan ya zube yana kuka wiwiwi tamkar wani ƙaramin yaro.
Fitowa suka yi dukkan ilahirin ahlin gidan suka zagaye shi suna ba shi baki, daman tun yana mota suka tattauna maganar da Yaya Nura da kuma Umma. Ko yanzu ita ce tsaye a gefensa cike da tausasawa ta ce.
"Kamar Yanda na faɗa maka Ashiru tun kana cikin mota;Dan Allah dan girman Allah ka haƙura da zancen yarinyar nan ka sakawa zuciyar ka dangana da salama. Matar mutum a duk inda take ko ana Muzuru ana Shaho sai ya same ta muddin dai Allah ne ya rubuta, idan kuma Kaga baka samu ba to ka ƙaddara tun can ba matarka ɗin ba ce. Saboda haka ka sassautawa kan ka, tunda sun hana maka ka haƙura ka nemi zaɓi mafi alheri a wurin Allah In Sha Allahu zai musanya maka da wacce ta fita. Ka sani fa zafin nema baya kawo samu sai dai idan kana da rabo..."
Jinjina kai Ayya ta yi ta ce.
" Haƙƙun! Wannan maganar taki gaskiya ce, Kaga dai tunda aka fara zancen gabaɗaya mu iyayenka da 'ƴan uwanka babu wanda bai goya maka baya ba. Amma kuma tunda har lamarin ya zo a haka, to ka haƙura, dan Allah ka haƙura Ashiru..."
Wayar shi da ke ta ringing tun ɗazu ya banzarar ne Ayya ta kalla tana faɗin.
" Ka ɗauki kiran nan mana Ashiru! Sai kiran ka ake tun ɗazu ka ƙi ka ɗaga, muma sai magana muke ka ƙi ka buɗe baki ka mayar mana da magana... "
A hankali ya miƙa hannu a aljihun gaban rigar sa ya ciro wayar tare da yin picking murya a sanyaye ba tare da sanin waye mai kiran nasa ba ya ɗaga ya yi sallama.
Daga can ɓangaren ya ji an ce.
" Sunana Jafaru Habib Jika, maƙocin gidan su Beenafah wacce kake yaƙin neman aurenta...na kira in sanar maka cewa yanzun nan aka ɗaurawa Beenafah aure da wani, saboda haka sai ka yasar da makaman yaƙinka ka ɗauki dangana kamar yanda na yi. Ina fata zaka yafe mata domin ba'a son ranta hakan ta kasance ba. A da na kasance ina tsananin jin haushinka akan yanda ka shige gabana ka yi kane-kane a cikin rayuwar Beenafah domin sai nake ganin kamar tafi son ka dani, to ka gani ashe muna namu Allah yana nashi, saboda haka ina mai baka haƙuri a madadin su ita da mahaifiyarta..."
Jinjina kai ya yi tamkar yana a gabansa murya a ƙasa sosai ya ce.
"Na gode."
Daga haka ya kashe kiran sannan a hankali ya ɗago ya kalle su ya ce.
" Daga baro garin jiya zuwa yau har sun ɗaura mata aure..."
Girgiza kai suka yi cike da alhini Umma ta ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu abun da suka aikata kenan? Wato don kada ma su tsaya wani jinkira shi ne suka nuna maka sun fi ka iko da ita, to su je can. Allah ya bata zaman lafiya kai kuma Allah ya baka wacce ta fita...ka yi haƙuri ka tashi ka je kaci abinci kayi wanka zuwa gobe idan Allah ya kai mu ka koma Kano.."
Ayya ta ce.
" To ai dai yanzu ta riga ta faru ta ƙare an yiwa mai Dami ɗaya sata. Tun da dai har haka ta kasance, ka je ya nemi Sabila su sasanta ayi masa auren kowa ya huta... "
Miƙewa ya yi kurum ba tare da ya tankawa maganar su ba ya wuce ya shige ɗakin sa ya kulle da Key ta ciki ya faɗa kan gado ya fashe da kuka tamkar wani ɗan ƙaramin yaro da ya nemi uwar sa ya rasa. Har yanzu ya kasa yarda da cewa wai ya rasa Beenafah. Abu wasa-wasa gashi yana nema ya tabbata.
*********
Muna nan sai gashi a hankali maƙota sai shigowa suke, da masu fatan alheri na gaske da magulmata masu bacci da ido ɗaya duk sun taru suna tayamu murna. Hibbatu ma ta shigo baki har kunne tana wani Allah ya sanya alheri kamar wani da gaske.
Muna nan tare har da Aunty Labiba sai ga Dr. Basheer ya shigo sanye cikin manyan kaya na alfarma sai wani baza ƙamshi yake fuskar nan cike da annuri. Ga shi Allah ya yi shi mutum mai tsayi da jiki dai-dai ba wanda ya wuce ƙima ba.
A parlour Mama tayi masa iso tana da wani tsokanarsa kamar wacce tayi shekara da sanin sa.
Togacewa ya yi a tsakar gida yana dariya ya ce.
"Ni ba maganar shiga ɗaki ce ta kawo ni ba, na zo ne tafiya da mata ta..."
Musayar kallo muka shiga yi tsakaninmu bama kamar ni da na ji duk wata irin kunya ta lulluɓeni. Aunty Labiba ita ma dai murmushin ta yi tare da duba agogon wayarta ta ce.
"Dr. Yanzu fa ƙarfe shida har da mintuna ashirin, kuma kasan dai Amarya tsautsayi ne da ita...sannan ma da kake wannan maganar ai dole sai kun jira kun fara bamu tamu amaryar sannan ka ɗauki taka ka juya ku tafi..."
Girgiza kansa ya yi yace.
"Ba za'a yi haka ba Hajiya Labiba. Itama Beenafah ya kamata tasan cewa Amarya ce kamar kowace budurwar da ake aurar wa cike da gata da soyayyar en uwa da abokanan arziki. Saboda haka yanzu za ta tafi gidan ubanta, sai an yi duk wasu matakan da ake bi na al'ada kamar kowa sannan wanda muka aura mata shima ya zo gare mu sannan zamu ɗauko ta mu kawo ta gidan Mijinta. Yanzu da ba dan Yamma ta riga da tayi ba, da yanzu zamu juya mu koma Sokoton amma zuwa gobe In Sha Allah ƙarfe goma na safe zamu wuce idan Allah ya kai muna rai... "
Cike da jindaɗin wannan shawarar da ya kawo ta jinjina kanta ta ce.
" Alhamdulillah! Hakan ma ya yi. Muma sai muje mu shirya mu zo da duk wani abin da ya kamata ayi duk shagalin da ake so a yi sai mu ɗaukota mu dawo... "
Kallon Aunty Labibar na yi, fuska cike da fargaba na ce.
"Aunty Labiba ko yanzu da hakan ta kasance ina da sabon sharaɗina.."
Fuska cike da alamar tambaya ta ce.
"Wani sharaɗin kuma Beenafah?"
Jinjina kaina na yi na ce.
"Eh! A yanzu idan ki ka koma, ina so ki jewa Hajiya da sauran danginku da zan cen cewa Muhammad ya samu matar aure a Sokoto, saboda haka za ku shirya ku tafi da sadaki da komai domin ɗaura masa aure..."
"Wai kina nufin ko yanzu in rufe wannan ɗaura auren da akayi Beenafah??"
Jinjina mata kaina na yi na ce.
"Eh, shi nake nufi. Kada ki sanar da kowa cewa an ɗaura auren, kice yanzu ne za ku taho tare da duk wanda ya kamata sai a ɗaura aure ku biya sadaki..."
Cikin rashin fahimta take kallona ta ce.
"Amma Beenafah ta ya kike tunanin har yanzu zan iya jure rashin sanar da Hajiya irin halin da ake ciki, Yaya Mohaa fa shi ne babban ɗan ta jigonta, jigonmu na rayuwa..."
"Na fahimta Aunty Labiba, ke dai kawai ki yi yanda na ce miki. Tun da har an riga an ɗaura miye abin damuwa..."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"To na ji... Na yarda ɗin, amma gaskiya ba zai wuce nan zuwa Laraba ba..."
"Sai wata Friday Idan ubangiji ya nuna mana."
Cewar Dr. Basheer wanda ke maganar yana jinjina kai, ganin irin kallon da ta yi masa ya sake bata tabbaci da cewa.
"Ƙwarai kuwa, abin da yasa nace haka;Wannan shi zai sa kuje ku yi duk irin shirin da kuke son ku yi muma kuma mu shirya mata duk abunda ya kamata daga nan sai a juyo a dawo ita."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jinjina kai ta ce.
"Shi ke nan, Allah yasa alheri yasa hakan shi ne mafi alheri."
Da amin duk suka amsa sannan daga ƙarshe ta yi mana sallama ta tafi.
Bayan su Mama sun koma gida, gidan ya rage da gani sai Ammie da Bahrain yayin da Dr. Basheer ya fi ce ya koma ga baƙin sa. Wanka na je na yi, bayan na fito na ɗora alwala naje na da sallar magriba sannan na zauna ina ta karanta addu'o'in suka sawaƙƙa na neman alheri da albarka a cikin wannan sabon shafin ƙaddara da ya buɗe mana. Bayan na kambala na je gaban Ammie na zauna wacce tun ɗazu ta zauna ta yi shiru bayan ta kambala sallar isha.
"Ammie! Har yanzu akwai abin da kike ji yana miki ba daidai ba a zuciya ko??"
Ɗan murmusawa tayi lokaci ɗaya tare da share hawayen ta ce.
"Ƙaddara kenan Beenafah. Bayan rasa mahaifinku da na yi, na yi burin komawa ƙasata na shafe tarihin Nigeria a duniyata. Sai ga shi kuma ƙaddara tasa na sake ƙullawa da wani wanda ban sani ba....Wallahi Beenafah ba don ina so na bari aka ɗaura wannan auren ba, na yi shi ne kawai domin in samu ki cika burinki da kika ƙudura a rayuwar ki. Kin wahala da ni sosai a rayuwa dani da 'ƴa' ƴana, ban san miye zan yi miki na saka miki ba fa ce cika miki mafarkinki..."
Hannayenta na jimƙe a nawa ina yi mata murmushi na ce.
" Haba Ammie... Ke ce fa wadda kika haife ni kada ki manta da hakan, idan kina faɗin cewa wai na wahala dake sai inji raina yana mini babu daɗi...In Sha Allahu hakan shi ne alheri Ammie, Allah ya ji ƙan Abbie ya gafarta masa. Ki kwantar da hankalinki."
"shi ke nan Beenafah. Allah ya yi muku albarka ya sawa wannan aure albarka.."
"Amin. Ina so dan Allah na tashi na tafi gidan su Hafsa na yi mata bankwana, Bahrain zai rakani tare da Yaya Hamza da Fakiha...."
"Uh uhm fa Beenafah,kin san yanzu da can da ba ɗaya bane, idan kika fita babu izinin mijin ki za'a rubuta miki zunubi..."
"Ƙwarai kuwa Ammie, wallahi ko za ki yi kukan jini ba zan yarda da ki fita ba, a matsayina na Yayanki ban amince ba, saboda haka ki faɗamana inda gidansu Hafsar yake sai muje mu ɗauko miki ita."
Cewar Yaya Hamza dake shigowa gidan yanzu.
Tashi na yi ina mai jin wata irin dariyar mamaki na cewa wai matar aure nike sai da izinin miji zan fita. Ɗaki na shige ina jin yanda Yaya Hamzan ke mini tsiya amma na kwanta shiru kawai na shiga nazarin rayuwata ta gaba.
Washegari, tun da wuri muka shirya misalin tara na safe sai ga Dr. Basheer ya dawo da hamshaƙiyar motarsa mai numfashi ya parker a ƙofar gidanmu, kayanmu da muka haɗa tun asuba ne Yaya Hamza ya fito da su, daman ba wasu kaya ba ne kayan jikinmu ne kawai kuma ko su masu sauran amfanuwa ne kaɗai muka ɗauka. Daga nan duk wasu sauran kayan tarkacenmu har mattresses ɗinmu guda biyu Ammie ta saka Yaya Hamza ya kwashesu ya kaiwa Mama ko Allura ba'a rage ba. Daga nan Ammie ta ɗauki takarda da biro ta yi rubuta sannan bayan Yaya Hamza ya rufe ko'ina na gidan ta haɗa da takardar da Key ta ce idan Allah yasa Uncle Isma'ila ko Daddy sun zo nemanmu, to kurum ya ba su waɗan nan ba sai ya ce musu komai ba.
Koke-koke ne ya ɓarke a tsakaninmu musamman ni da naga cewa da gaske tafiya zan yi amma kuma ba bu Yaya Jafaru. Hakan yasa na dinga kuka ina cewa su roƙa mini gafararsa akan abin da ya faru. Tabbas dole akwai kewa tsakaninmu da su domin mun yi zamana na amana na mutunci da har wannan rabuwar ta sakamu kuka.
Daga ƙarshe hannuna Mama ta kama ta kaini har cikin motar sannan ta ce.
"Daina kuka Beenafah, irin zaman da mukayi da irin wannan babbar nasarar da aka cim ma, kuka bai kama ce mu sai dai don Sabo. In sha Allahu zuwa Laraba zamu zo har da Hamza ba.....Hajiya Mulaifa, Allah ya tsare ya bada zaman lafiya yasa ace gwamma da akayi."
"Amin maman Fakiha na gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."
Daga haka Yaya Hamza ya rufe mana motar Ido cike da hawaye yana ɗaga mana hannu har muka ɓacewa ganin su.
*********
Labiba ce zaune a gaban Hajiya tare da Emraan wanda duk ya yi wani iri tsabar halin takaici da baƙin cikin da yake ciki. Ga Ziza tun ranar ta gangama ta wuce sokoto sannan mai makon ace Hajiya ta tausayesa bata yi hakan ba, sai ma wani laifin sa da ta gani wai ai tace masa ya fara shawo kan matarsa tukun kafin ya yi wani yunƙuri, amma wannan abun kunya ne sosai ace wai matarsa ta yi yaji ta tafi gida akan zancen za'a yi mata kishiya. Duk faɗan da Hajiya take shi Sam bai gani ba, ƙarshe ma ce mata yayi zai kira Baba Ustaz akan ya zo yaje ya nema masa auren Beenafah, in yaso idan an yi auren daga baya sai asan yanda za'a yi a dawo da Ziza. Sai dai kuma haƙar sa bata cim ma ruwa ba,domin Hajiya Sam taƙi ta amince masa tace sai an fara dawo da Ziza an shawo kanta sannan an shawarci Labiba tukunna kafin ta yarda ayi maganar aurensa da Beenafahr.
Ita kuma Labiba daman na ta plan tun ranar ta ce musu tana cikin uzururruka shari'a a kotu saboda haka dan Allah su ɗaga mata ƙafa zuwa Saturday.
Kallon Hajiyar ta yi bayan sun gama gaisawa ta ce.
"Shin ni yanzu ina so in san miye dalilin Ziza na yin yaji? Na fa san halin Emraan In Sha Allahu da wuya ya fara kunno da matsala a tsakaninsu..."
Wani kallon Hajiyar ta yi mai sannan ta sake kallon Labibar ta ce.
"To ki ma daina shaidarsa domin a wannan karon shi ne wanda ya fara. Ce mata yayi zai auri Beenafah..."
Wata irin muguwar zabura ta yi ta miƙe tsaye tana dafe ƙirji ta ce.
"Whatt??"