Ganin ido complete - Chapter 33
Ganin ido complete Chapter 33: Ganin ido complete Chapter 33. "Kin ga ne Labiba, ni ba laifin sa na gani ba don yace yana sonta, a'a, cewa na yi yaje ya…
3,370 words
"Kin ga ne Labiba, ni ba laifin sa na gani ba don yace yana sonta, a'a, cewa na yi yaje ya fara shawo kan matarsa sannan ita kanta Beenafahr ya samo soyayyar ta sannan daga baya sai a tunkare da maganar. In dan ta ni kada ki damu domin yarinyar tana da kirki da tarbiyya... "
Shiru ta yi tare da runtse idanunta ta dafe goshinta na tsawon 5minute sannan daga ƙarshe a hankali ta koma kan kujerar ta zauna ta kalle shi ta ce.
" Kana zaune da matarka lafiya mai matuƙar biyayya, aurenku gabaɗaya fa shekara uku ne. Miyasa maza ba ku da adalci wani lokacin??"
Wani murmushin gefen baki ya yi sannan ya kalle ta ya ce.
"Labiba sha'ani irin wannan fa zuwa yake ba mutum ne ke ƙirƙirarwa kansa hakan ba...."
"To ai kuwa yarinyar dai an nemeta an rasa saboda haka sai ka shafa kanka ruwa ka je ka dawo da matarka..."
Da wani irin mugun mamaki ya yi mata wani kallon yana faɗin.
"An nemeta an rasa kamar ya? Saboda na ce ɗin ina sonta za'a nemeta a rasa?"
"To ni ban san yanzu ya zan ce maka ba, amma dai jiya da yamma Munira ta kirani ta ce mini kwana biyu Beenafah ba ta zo aiki ba kuma ba su da numbernta ballantana su kirata, shi ne na kira lambar maƙociyar su itama take sanar da ni cewa ai sun tashi sun koma ƙasarsu..."
Miƙewa ya yi a zafafe yana faɗin.
" Wannan shiri ne ko ince makirci ne aka ƙulla daga gidansu..daman ce mini da tayi an yi mata miji a gida ba jimawa za'a ɗaura aurenta da gaske ne ba Ƙarya ta yi ba? "
" Oh! Daman haka kuka yi da ita??"
Cewar Aunty Labibar tana wani Jinjina kai.
"Eh, abin da ta faɗa mini kenan ranar da na kirata nake faɗa mata cewa ga jumu'ar jiya zan aika da magabatana.."
"Allah sarki! Allah yasa zaɓin da suka yi mata ya zamto alheri a cikin rayuwarta..."
Cikin jin wani irin tururi a zuciyarsa ya ce.
"Yanzu ke baki san ina ne ƙasar tasu ba."
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"Ni ban san komai dangane da ita ba, aiki kawai take a gidana, bayan Barrister ya koreta a gidana shi ne na dawo da ita nan, kai ni ko gidan su ma ban taɓa zuwa ba. Ka yi haƙuri Allah ya baka madadin ta...."
"Amma Labiba..."
Hannu ta ɗaga masa ta ce.
"Emraan please! Ni fa akwai wata muhimmiyar maganar da ke tafe dani a halin yanzu. Tun da har baka same ta ba ka haƙura mana.... Hajiya! Maganar Yaya Mohaa ce ta kawoni gidannan..."
Jinjina kai Hajiya ta yi tare da ƙure ta da ido ta ce.
"Ina jin ki.."
Ƙara gyara zamanta ta yi da kyau suna fuskantar juna ta ce.
"Hajiya aure ne na nema masa, kuma In sha Allahu akwai alamun nasara a wannan karo..."
Lokaci ɗaya Hajiyar ta ji hankalinta ya tashi domin kwata-kwata ba ta son ma wannan zancen hakan yasa ta katse ta da faɗin.
"Dakata Labiba! Ba na yi warning ɗinki akan cewa kada ki sake zo mini da zancen irin wannan ba? An samu hankalinsa ya kwanta da ƙyar sannan yanzu kuma kike nema ki sake mayar da shi cikin turkensa mai caɓo...kinfi kowa sanin irin mummunan halin da ya shiga da ƙyar da addu'a da magunguna muka samo Allah ya taimakemu ya dawo hayyacinsa...to yau ɗin kuma wace Ƙarya ce ki ka zo mini da ita??"
Cike da ƙwarin gwiwa ta ce.
" Hajiya dan Allah na roƙeki dan Allah ki bani dama! dama ta ƙarshe ita ce nike so ki bani wanda idan har na yi failing to ni kuma na yi alƙawari har abada ba zan sake yi miki zancen auren sa ba... "
Emraan ma, jin wannan maganar tuni ta mantar da shi zancen wani ƙuncin Beenafah da yake ciki. Yayansa jigonsa kuma Uba a garesa wanda har abada ba shi da kamar sa. Farin cikinsa shi ne nasa. Matuƙar dai wannan aure da take iƙirari ace zai yiyu da tabbas sai yafi kowa farin ciki. Hakan yasa ya kalli Hajiyar shima cikin sigar rarrashi ya ce.
"Hajiya dan Allah ki bari a sake trying a gani.."
"Duk fa yanda zaku kalalla meni da wasu kalamanku ba zan amince ba. Nawa akayi? Na ce nawa akayi? The last one ɗinma haka kuka sakani a gaba da kuka da komai amma ƙarshe kunya ce ta dawo daga baya ta lulluɓemu...Muhammad ya samu salama a cikin rayuwar sa dan Allah ku ƙyalesa, baƙin cikin da yake cikin zuciyata ba ya misaltuwa akan wannan matsalar ta Mohaa. Ku kanku shaida ne da duk irin yanda akayi ta nema masa aure amma kuma babu ɗaya da akayi nasara.... "
" Hajiya ki yarda da maganata, IN Sha Allahu wannan za a yi nasara... "
Nan dai suka saka ta a gaba da kuka da komai sannan daga ƙarshe ta amince. Bayan ta gama sauraren ta da bayanin da tayi mata akan Beenafar tare da ɓoye sunanta ta kalle ta tace.
"Yaushe ne zamuje a saka ranar?"
Ajiyar zuciya Labiba ta sauke tana murmushi ta ce.
"Hajiya a wannan karon fa a shirye nake domin ban zo gare ki ba sai da komai ya Kambala. Ranar Jumma'a ta wani sati za'a ɗaura aure a ranar za'a dawo da ita nan a kawo ta ɗakin ta...."
Miƙewa Emraan ya yi cike da zumuɗi ya ɗaga waya ya kira Nadeeyah ya sanar mata, bayan ya gama ya kira Hairiyya...haka ya fice yana ta kiran waya kamar wani zautacce, farin ciki duk ya gama cikasa na zancen auren ɗan uwansa.
A nan suka shiga tsare-tsaren cewa, idan Su Nadeeyah sun zo daga yau zuwa gobe, za su barsu a nan suka ci gaba da gudanar bukin yayin da su kuma zasu wuce Dubai a tare zuwa ranar Wednesday su dawo tare da Mohaa ɗin idan ya amince.
Bayan sun gama tattaunawa cike da sa rai Hajiya ta ɗauki waya baki har kunne ta shiga sanar da mutane.
********
Su Mummy kuwa, koda suka iso an gyara gida ko'ina yayi kyau da sabon fenti fa kuma sabbin furnitures kamar yanda suka bai wa Uncle Isma'ila umarni.
Bayan sun shiga matar Uncle Isma'il ɗin ta jere musu abinci suka ci suka sha bayan an yi sallar la'asar ta cewa Daddy ya tashi yaje ya zo mata da Beenafah.
Hakan yasa ya tashi yaje ya yi wanka ya fito shirye cikin babbar rigar sa tare da Uncle Isma'il suka nufi gidan su Beenafah.
Suna yin parking a daidai ƙofar gidan, Daddy ya kalli Uncle Isma'il ya sheƙe da dariya ya ce.
"Wato Isma'il kace Allah ne ya tarfawa garinka Nono har ka samu gidana ka shige. Da yanzu kana nan sauro da zafi sun kusa yin ajalinka.."
Dariyar ya yi shima yana jinjina kansa ya ce.
"Wallahi kuwa! Sai ga shi Allah ya taimakeni na samu gidan ka na laɓa..."
A tare suka fito motar suka nufi ƙofar gidan, sai dai kuma; Mamaki ne da al'ajabi suka kama su ganin ƙofar gidan rufe da makulli.
GidanSu Maman Fakiha suka aika yaro akan ya yo musu sallama da mai gidan. Sai ga shi kuma Allah ya taimake musu ya dawo yana gida tunɗazu.
Yana fitowa suka gaisa Uncle Isma'ila ya kalle shi ya ce.
"Dan Allah malam Hajiya Mulaifa fa? Sun fita anguwa ne?"
"To wallahi dai ban sani ba. Amma ta bani wani saƙo tace idan ka zo nemanta in hannunta maka wani saƙo... Bari na shiga gida na ɗauko maka."
Shiru suka yi ba ma kamar Daddy da ya wani saki kunnuwa kamar makarantar Zomaye yana jira yaga wannan wane irin saƙo ne. Yana ganin Baba ya fito, tamkar zai kifa ganin takarda a hannunsa ya zuba da gudu ya warto takardar Hannu na rawa ya buɗeta. Wani irin kallo ne ya yi wa Uncle Isma'ila tare da nuna masa takardar ya ce.
"Larabci ne ta rubuta Isma'ila...Wallahi shegiyar da larabci ta rubuta. Oh! Ya subhanallah! Idan ba da take shegiyar muna fuka ba, ta ya ya za ta rubuta mana wasiƙar larabci?.... Amsa Isma'il ka karanta mini dan Allah."
Baya uncle Isma'il yaja yana faɗin.
" Kai baka iya ba Alhaji ni ne zan iya? Ba wannan bawan Allah ya karanta mana. "
Ƙofar gida Baba ya nufa yana faɗin.
" Ni ma dai duk kanwar Ja ce, domin ban iya ba... "
Wani irin cafko hannun sa Daddy ya yi cike da magiya ya ce.
"Haba malam! Dan Allah ka taimakeni mana tunda nasan dole kasan wani a nan da zai iya taimaka mini ya fassara mini ta ce. Wallahi ina cikin uzuri na gaggawa na son jin bayanan da suke cikin takardar nan."
Jinjina kai Baba ya yi yace.
"To muje ga masallaci can mu samu malam yana ciki in sha Allah zai fassara maka."
A tare suka taka zuwa masallacin suka kewaye cikin Islamiyyar Baba ya shiga ya kira musu malam ya fito, bayan sun gaisa Baba ya gabatar masa da buƙatar su Daddy da nema masa alfarma.
" Salam, Sunana Mulaifa Zayd Hudaif. Zuwa ga Isma'ila. Dan Allah idan wannan takarda ta riskeka ina so ka hannunta ta zuwa ga Alhaji Mudassir Wazeer Yayan tsohon mijina Dr. Bello Wazeer....Alhaji Mudassir ina fatan kana cikin amincin ubangiji. Ina so in sanar da kai cewa, Allah ya bani dama da aron lokaci na aurar da Beenafah ga mutumin da ya dace da ita ba ga wanda ka so cutar da ita da shi ba, sannan ina mai farin cikin sanar da kai cewa na juya na koma zuwa ƙasa ta, zaluncin da ka yi mana da kuma girman haƙƙin marayun 'ƴa' ƴana da ka danne, na barka da Allah sarki, shi ne wanda zai yi mana hisabi ranar gobe alƙiyama. Ina maka fatan alheri... "
Wani irin hiri-hiri Daddy ya yi tamkar an tsoma kama a ruwan zafi ya shiga wasu muzuran ƙarya ya na wani ciccika baki cike da kunya ya ce.
" Ƙaƙ... Ƙarya take wannan matar fa! Duk abin da ta rubuta Ƙarya take wallahi.... Ni za ta ɓatawa suna.... "
A hankali malam Nasir ya lumshe idanunsa ya buɗe su tare da bin Daddy da wani kallo ya miƙa masa takardar sa kurum ya juya ya koma cikin makaranta yana faɗin.
" Allah ya kyauta."
Wata irin zufa ce ta shiga tartsowa daddy tamkar wanda ya yi linƙaya a cikin kogi, a gigice suka iso inda motar su take ajiye. Baba na miƙa wa Uncle Isma'ila Key Daddy ya wani shaƙo kwalar rigar sa yana faɗin.
"Wallahi tallahi sai ka faɗa mini inda Mulaifa take...kuma saika faɗa mini uban waye ta aurawa Beenafah..."
Wani irin fizgewa Baba ya yi a zafafe yana faɗin.
"Dan Allah Malam cika min rigata! Ni ina ruwana da rayuwarku? Akan gudun irin haka ne yasa ko kaɗan ban saka kaina a wannan rigimar ba, kuma kada ka ce zaka raina min hankali..."
Hannun Daddy Uncle Isma'il ya janyo gefe yana faɗin.
"Tabbas wannan mutumin babu ruwansa a ciki, ka zo mu koma gida mu nemi mafita."
"Hankalina a tashe yake wallahi Isma'ila..."
"Shi ne nace maka ka zo mu tafi gida tukun, in ya so daga baya koma minene sai mu dawo..."
Sai da ya cire takalminsa sannan ya shige motar tsabar yanda ya ruɗe.
"Alhaji... Subhanallah! Takalmanka fa ka cire,ba fa gida ne za ka shiga ba mota ce..."
"Mts! Na manta ne Isma'ila dan Allah sanyo mini su a ciki."
Cikin sauri ya jefa takalmin tare da zagawa da gudu ya tayar da motar suka wuce.
Suna shiga gidan ko daidaita parking bai gama yi ba Daddy ya fito still ba takalmin ya shige wanda hatta hular kansa a karkace take. Mummy na ganinsa ta ta miƙe tana faɗin.
"Ina Beenafahr take?"
Takardar ya miƙa mata kurum ba tare da yace mata komai ba.... Hannu na rawa ta karɓa, tana dubawa ta mishi wani kallon uku saura kwata ta ce.
"Miye wannan ɗin?"
Uncle Isma'ila ne ya ce.
"Saƙon da Hajiya Mulaifa ta bar wa mijin ki ne, cewa;ta aurar da Beenafah ga wanda ya dace da ita, sannan ta koma ƙasar su, kuma Allah ya isa bata yafe ba haƙƙinta da na 'Ƴa'ƴanta...."
Hannu ta ɗora akai tare da fasa wata irin gigitacciyar ƙara ta zube a ƙasa somammiya. Da gudu Aysha ta rugo hannu na rawa ta ɗauki takardar ta karance tsab sannan daga ƙarshe ta rungumeta a ƙirjinta sosai tana mai fashewa da wani irin kukan farin ciki.
********
Runjin Sambo, shu'uban road, Sokoto North, Sokoto State, Nigeria.
Duk a tunaninmu, gidanda ya taɓa kai mu inda matarsa can zai nufa damu. Sai ga shi hasashenmu bai tabbata ba, domin wani gida daban ya kaimu mai matuƙar girma da haɗuwa. Gida ne abin da ake kira gida domin yana ɗauke da ƙayataccen ginin zamani da kuma kayayyakin amfani iri daban-daban na ƙashashen duniya komai sabo.
A babban parlourn gidan muka yada zango tare da takure wuri ɗaya yayin da muka yi wani iri.
"Haba! Miyasa kuka zauna shiru haka tamkar wasu baƙi?? Hajiya Mulaifa nan fa gidan ki ne...Dan Allah ku saki jikinku.... Ku ta so ku ga wani abu..."
Hannun Bahrain ya janyo ya shiga nuna mana kowane lungu da saƙo dake gidan. Bayan mun gama ya dawo samu parlour muka zauna ya kalli Ammie ya ce.
" Hajiya Mulaifa! Ni ɗin nan fa mutum ne kamar kowa...ba zan taɓa cutar da ku ba. Ni babban likita ne a asibitin da kike zuwa jinya, sannan ina yin kasuwancin motoci ban zauna a haka ba. Ina da mata da yara uku, ina da iyaye da sauran en uwa duk a nan ɗin. Gobe idan Allah ya kaimu ƙwansu da kwarkwatansu duk za su zo, daga nan sai mu shirya bukin yanda za'a kai ermu ɗakin Mijinta."
A hankali hawaye suka shiga gudana akan kumatun Ammie. Ganin hakan yasa na tashi na ja hannun Bahrain muka shige ciki muka bar su.
*******
Jumeirah, Al Waha street, United Arab Emirates, Dubai.
Tun da Labiba ta bashi wannan labarin ya yi cancel duk wata tafiya dake gaban sa kai tsaye ya baro office ɗinsa ya dawo gida.
Wanka ya shiga ya yi ya fito jiki a sanyaye ya shirya cikin jalabiya ya fito ya tafi masallaci domin gabatar da sallar magrib wanda bai dawo ba sai da aka kambala sallar Isha.
Duk ma'aikatan gidan da muƙarrabansa sun tabbatar cewa maigidansu yana cikin wani yanayi na damuwa wanda suka jima ba su gansa a ciki ba.
Yanda aka jera masa abinci haka ya barshi ko kallon inda yake bai yi ba. Tunda ya dawo ya zube kan kujera bai sake jin wani dogon motsi ba, bayan masu tsaronsa da ya bugewa kyakkyawan warning hatta wayoyinsa kama su ya yi ya kashe.
Har yanzu ya kasa yarda da cewa wai duk wannan ba mafarki ba ne..Shekaru arba'in da shida a duniya... Har ya cire ran cewa akwai wani abu makamancin aure a rayuwarsa sanadiyyar munanan ƙaddarorin da suke zagaye da shi waɗanda ya ɗauka cewar shi kenan....yanzu kuma da rana tsaka wai shi ɗin mijin aure ne. Ko Wacce ce wannan wadda ta nemi jefa kanta cikin halaka saboda kawai kwaɗayin girman matsayinsa da dukiyar sa? Ko a ina Labiba ta samo ta?......
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 31*
Yana nan a kwance kan Cushion ɗin ya saƙa ya warware ya saƙa ya warware har misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Yana nan ya ji saƙo ya shigo a private line ɗinsa wanda daga;Hajiya, Labiba, Emraan, Nadeeyah and Hairi. Su ka ɗai ke iya nemansa a wannan line ɗin a duk sanda suka so. Tun kafin ya kai ga ɗauko wayar ya yanke a ransa cewa yasan Wacece ta turo text ɗin.
'Jakadiyar wanzar da zaman lafiya.'
Kalmar da ya furta kenan a ransa sannan ya buɗe text ɗin ya karanta kamar haka:
"Ya Mohaa da fatan kana cikin aminci? Da fatan kana lafiya? If you are awake and safe please let me know....muna hanya gobe tare da Emraan da Hajiya...Muna kan plan ɗinmu kada ka manta, koda mun zo ba'a ɗaura auren ba sai next Friday coming."
"Ina cikin amincin Ubangiji Labiba. Thank you so much. Allah ya tashe mu lafiya."
Tashi ya yi bayan ya tabbatar cewa text ɗin ya shiga sannan ya wuce yaje ya yi alwala ya zo ya yi ta jera Nafilfili yana addu'a kamar yanda ya saba a kowane dare.
********
Washegari, bayan Labiba ta gama shiryawa a tare suka fito ita da Barrister ya kaita har gida. Kafin ta fita daga motar ne ya kalle ta a hankali ya ce.
"Ni na ma rasa wane kalar tunani zan yi Labiba. Emraan ya ce yana sonta, ita kuma ta zo a uzurce ta auri Daddyn Raudah. Sannan shi kuma da akace Aljana ce ta aure shi tsawon lokaci ta hana mishi aure, sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci an ɗaura kuma yana zaune lafiya babu abinda ya same sa......Ta yi gargaɗin kada a sanarwa kowa a dangi har yanxu...."
Jinjina kan shi ya shiga yi still idonshi a kanta ya ce.
" Tabbas! There is something fishy Labiba! Dole akwai abin da ba daidai ba. "
"Ni kai na a rikice nake wallahy Barrister. Komai ya dagule mini wanda har na rasa ma wane kalar tunani zan yi. And kuma na gode Allah da har na ankare na bugewa Oga Sule warning cewa kada ya faɗawa kowa cewa ya kaini gidan su Beenafah, Kaga hakan kuwa ya yi rana."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
" Ba damuwa. Allah ya tsare yasa a dawo lafiya, Allah yasa kuma ya amince ya biyo ku ɗin."
"To Amin. Na gode sosai."
Tana shiga gidan ko ɗosana ɗuwawunta ba ta kai ga yi ba, Hajiya ta kalle ta jiki a sanyaye ta ce.
"Labiba kin tabbata auren nan zai yiyu da gaske? Labiba ni fa ina jin tsoro..."
Langaɓar da kanta tayi gefe a hankali tana mai marmaɗa idanunta sannan ta yi murmushi tana jinjina kai ta ce.
"I'm 100% sure Hajiya....muje ki zage ki haɗawa surukarki lefe. Sannan kuma..... what I suggest is that;tukuicin wannan Amaryar da iyayenta shi ne mun yafe musu kayan ɗaki, a kwashe kayan upstairs ɗin can nasa tunda Allah ya kaimu a zuba sababbi..."
Still zuciyar Hajiyar cike da doubting take kallon Labibar ta ce.
" Labiba kin tabbata auren nan zai faru?"
" Oh Allah! Hajiya Emraan fa ya shirya. Dan Allah ki zo mu tafi kada mu tsaya ɓata lokaci... "
Cikin nuna ƙwarin gwiwa jinjina kanta ta ce.
"Ni kuwa, matuƙar dai wannan auren ya faru da gaske,to na yimiki babban alƙawari Labiba... Amma ba zan faɗa miki yanzu ba sai idan an ɗaura auren kuma ta tare a gidannan."
"Na gode Hajiyata, ina marari da ɗokin jiran wannan lokacin. Allah ya tabbatar mana da alheri."
Suna cikin uzurin fitowa sai ga Munira ta shigo, bayan ta gaishe da Aunty Labibar sannan ta kalleta tare da miƙa mata wata leda ta ce.
"Aunty Labiba ga wayar nan da Ya Emraan ya siyawa Beenafah. A nan ta barta ɗakinmu ko buɗewa ba ta yi ba."
Jinjina kanta tayi sannan a kaikaice ta kalli Hajiya, ganin hankalinta baya nan ta kalli Munirar ta ce.
"ki je ki ajiye wurin ki, duk ranar da Ziza ta dawo ki ba ta ki faɗa mata yanda kika faɗa mini ɗinnan..."
Fitowa ta yi da gudu tana mai fashewa da dariya ta shige tana baiwa Haula labarin abin da Aunty Labibar ta ce.
Itama dariyar ta yi ta ce.
"Ni kuma In Sha Allahu a wannan ranar tare zamu tafi in raka ki muga wane kalar reaction ɗin za ta bada."
Girgiza kai Munirar ta yi tana faɗin.
"Allah sarki!, ko'ina Beenafah take?"
"Hmm! To kin gani dai? Duk abin da nake gudu sai da ya faru, nasan tun da ya furta mata wannan furucin dole sai wani abu ya biya baya. Kuma ni ina kyautata zaton Hajiya Korarta ta yi."