Ganin ido complete - Chapter 34
Ganin ido complete Chapter 34: Ganin ido complete Chapter 34. "To su suka sani Haula. Allah ya bata wani wurin wanda ya fiye mata nan."
3,318 words
"To su suka sani Haula. Allah ya bata wani wurin wanda ya fiye mata nan."
"To amin."
Bayan su Hajiya sun wuce. Misalin ƙarfe ɗaya Nadeeyah ta iso gidan ita da yaranta. Isowarta ba'a yi hour ba aka shiga shigowa da kayayyaki ta gate ɗin baya mota tafi uku, kayan abinci ne birjik, kayayyakin aiki, turame da laces komai da suke buƙata na bukin shi ne ake ta jibgowa kamar hauka.
Zuwa Yamma sai ga Hairiyya ta iso itama. Tana shigowa da er Jakarta ta goyawa a baya ta rungume Nadeeyah tare da zubowa da ruwan hawaye ta ce.
"Aunty Nadee wai da gaske auren Ya Mohaa za'a yi a gidannan? It's just looking like a dream to me... I'm scared kada ace za a fasa....."
Cike da yaƙini ta jinjina mata kanta ta ce.
"In Sha Allahu za'a yi. Na siyo mana kaya amma ban kai ɗinki ba, sai ki kira Hazim ki bashi. Zan je in yi magana da baƙin ma'aikatan da suka iso a yanzu."
"OK! Bari na fara yin wanka tukun. Please ki faɗawa Dija ina ɗakina, she should come and meet me."
********
Koda na fito misalin ƙarfe bakwai na safe, na tarar da wata matashiya tana goge-goge da alama ta kambala shara ne, sannan ga wani ƙamshin daɗi yana fitowa daga ɓangaren Kitchen ɗinda ya nuna mana jiya.
" Ina kwana Hajiya!"
Matashiyar ta faɗa da ɗan rusunawa. Hawayen da suka silalo mini ne na share da tafin hannuna sannan na jinjina kai ina kallonta murya a ƙasa na ce.
"Lafiya ƙalau! Sannun ki da aiki"
Hanyar kitchen ɗin na nufa ina mai jin mamaki a raina, wai yau ni ce Beenafah muke da mai aiki a gidanmu har tana kirana da Hajiya cike da girmamawa! Allah sarki! Komai mai lokaci.
Ina shiga na tarar Ammie ita da wata dattijuwa haka na gaishesu a tare sannan matar ta kalleni da fara'arta ta ce.
"Wannan ɗin ita ce Amaryar da Alhaji ya faɗa mana kenan? To Allah yasa albarka."
Ammie ce ta amsa da amin, yayin da na juya kurum na koma tsabar mamakin da har yanzu ya kasa barina. Ɗakin Bahrain na wuce direct wanda na iske ya yi ɗaiɗai a ɗan madaidaicin gadonsa yana bacci ga sanyin Ac mai daɗi yana hurashi. Murmushi na yi tare da samun bakin gadon na zauna kawai ina tunani na cewa 'Shin familyn shi da yace suna tafe Ya ya za su ɗauki Ammie da mu? Idan har matarsa ta amince masa da ya auri Ammie to sauran en uwansa fa? Ya Allah ina tawassali da sunayen tsarkaka! Ya Allah wannan auren da Ammie ta yi don kawai taga cewa na samu cikar burina ya Allah kasa ya zama silar farin cikinta duniya da lahira.'
Ina nan zaune a hankali sai ga Bahrain ya farka. Wanka na ce ya je ya yi nima zanje in yi nawa yanzu domin bamu san wane lokaci ne za su zo ba.
Bayan na kambala shiryawa a tare muka fito har Ammie. Murmushi na yi na ce.
"Ammie kema kin shirya kenan?"
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"Ya kirani a waya yace ƙarfe goma suna nan zuwa..."
Wata er dariyar ce ta suɓuce mini ina kallonta na ce.
"Waya Ammie? Ina Wayar take?"
Hararata ta yi sannan ta yi kwafa kawai ta wuce kitchen ɗin ta kawo mana abincin kari da kanta... Hmm! Wai duniya sabuwa. Muna zaune muna cin abincin Bahrain ya janyo wayar yana faɗin.
"Ga wayar nan Aunty Beena....wayar ma ai ɗaya ce daga cikin wayoyin da na gani a hannunsa."
"Allah Sarki Abbu!"
Ina faɗin haka shi kuma Bahrain ya fashe da wata irin dariya ya ce.
"Shike nan ba zamu ƙara cewa Dr. Basheer ba.."
"Ka sha giyar wake ne da za ka kira shi Dr. Basheer? Ka ɗauke shi ka girmama shi tamkar Abbie ne. Ka tsayu ka yi karatu Bahrain, sannan ka girmama duk wanda ya zo ta gefensa ka bashi muhimmanci...."
Duk firar nan da muke tana nan zaune tana cin abincinta uffan ba ta ce mana ba, muna nan sai gashi ya ƙara kiran ta, nan take ta miƙe kawai ta shige ciki ta barmu zaune a table ɗin muna ci gaba da shiririta muna dariya.
Misalin goma da rabi kuwa muka ji an buɗe gate ɗin gidan, jikin window na je na tsaya ina kallo. Motoci guda uku ne suka shigo jere da juna.
Ina ganin mutane na ta fitowa na kalli Ammie dake zaune jiki a sanyaye na ce.
"Ammie ga suna nan shigowa wallahi da yawa suke har da maza a ciki..."
Miƙewa ta yi tare da zura hijabinta cike da ƙarfin hankali ta je ta buɗe musu ƙofa tana musu maraba.
Hayaniya ce ta karaɗe ko'ina na parlourn wurin gaishe-gaishensu, daman kuma ga yara ƙananu a tare da su.
Bayan sun gama gaisawa da Ammie nima na kalle su na ce.
"Ina kwananku...sannun ku da Zuwa."
Matar Dr. Basheer ɗin wacce daga cikinsu ita kaɗai muka gane ce bayan sun amsa ta kalle ni tana faɗin.
"Ita ce Beenafah, Amaryaarmu..."
Suna cikin tofa albarkacin bakin su ne Dr. Basheer ɗin ya shigo fuskar nan ɗauke da fara'a ya samu wuri ya zauna yana kallon Ammie ya ce.
"Hajiya Mulaifa kin gan su ko?....Wannan ita ce Matata wacce kika sani Hajiya Asma'u, ga Hashi yarona na biyu, Yayarsa Huda tayi aure tana Kebbi, sai ƙaninsu gashi nan Haidar.... Wannan kuma ta gefena Hajiya Sameera kenan ƙanwata da take bina..Ga Zubair wanda shi ma ƙanina ne....."
Haka dai ya shiga lissafamana duk wanda ke wurin da dangantakarsu. A yanda muka ɗauki abin ba haka ya kasance ba, domin mutanen sun karɓemu hannu biyu-biyu musamman Hajiya Asma'u. Yayin da kuma wasu suka ɗan sha jinin jikin su da alama dai bamu yi musu ba. Daman haka rayuwa take Komai zamowar ka mutumin kirki ba za ka taɓa samun so ba 100%, haka zalika ba za ka taɓa samun ƙiyayya ba 100%.
Duk yan da Ammie take ɗari-ɗari sai da suka yi ta janta da surutu suna ta yi mata fatan alheri da fatan zaman lafiya. Suna nan sai misalin ƙarfe biyu sannan suka tattara suka tafi sai Hajiya Asma'u da ta tsaya nan suka shiga tattauna yan da za'a gudanar bukina kamar yanda Dr. Basheer ɗin ya yi alkawari wanda a nan suka yanke cewa za'a yi Kamu ayi Walima da wunin buki, ranar Tuesday, Wednesday da Thursday, ranar Friday Kuma tun ƙarfe tara mu ɗauki hanya kamar yanda su ka yi wa Aunty Labiba alƙawari. Washe da wuri ta sake dawowa gidan namu tare da Hashi da Mummy Sameera kamar yanda na ji Hashi ya kirata. Bayan sun gama tattaunawa suka shirya suka fice har da Ammie wai za su je kasuwa. Dr. Basheer kuwa yana can ya saka aje kama musu Hall sannan ya yi musu order ɗin duk abun da suka rubuta masa na buƙatar kayayyakin amfani.
*********
Tun da Mummy ta farfaɗo take sabbatu kala-kala marasa kan gado. Duk yanda ake lallashinta ta ƙi ma ta kwantar da hankalinta ballantana a nema mata mafita. Sannan duk abin ya cakuɗe musu domin shi ma Daddy dai duk ya shige gashi tamkar wani marar lafiya.
Babu abin da take tunawa taji hankalinta ya tashi irin auren nan gashi ya matso saura kwanaki amma babu wata mafita. Sai dai kuma Uncle Ismaila ya ce ta kwantar da hankalinta ta bashi kwana biyu akwai abin da yake planning akai. Hakan yasa suka dakata da duk wani shirye-shirye suka zauna jiran Uncle Isma'il.
Gidan duk ya yi wani iri tamkar gidan mutuwa. Su Aysha suna nan dai sun zubawa sarautar Allah ido. Idan auren ya faru fine..idan ma bai faru ba sai ta tattara ta koma wurin Mijinta ta huta da ganin wannan baƙin cikin.
Yau ma Mummy tana nan ta yi zaune tana ta rusa uban kuka ta ji ƙugin Motoci suna ta shigowa gidan.
Wani irin ƙuuu! Ta ji sai da Hanjin cikinta suka koka, domin tasan cewa tabbas waɗannan ɗin Su Ameer ne daman sun ce za su zo, to amma Uncle Isma'il ya ce zai san yanda zai yi ya hana musu zuwa amma ta ya ya suka yi nasarar ƙarasowa gidan kenan??
Hankalinta a tashe ta shiga ƙwala kiran Daddy ba ji ba gani tana kiran ta shiga uku, shikenan asirinta ya tonu.
A tare suka shigo har da Uncle Isma'il ɗauke da sallama a bakinsu.
Miƙewa ta yi lokaci ɗaya ita da Daddy suna rarraba ido suna wani yi musu yaƙe amma ba don suna cikin jindaɗi ba.
Bayan sun gaisa Ameer ɗin ya ce.
"Na zo ganin Beenafah ne...naga kamar abin zai yi wani iri ace ana ta zancen buki amma ni da ita bamu tattauna ba..."
"Uhmm! Ka gane ko Ameer....Dadd....daman ana shirya mata ne, tana can gidan gyaran jiki sai ana gobe ɗaura aure za'a dawo da ita.."
Kallon Ameer ɗin Uncle Isma'il ya yi ya ce.
"Ameer! Magana ta gaskiya ita ce; Beenafah an aurar da ita,daman kamar yanda na yi maka bayani tun can cewa marainiya ce, kuma so suke su aurar maka da ita saboda cutarwa to amma sai gashi Allah yasa mahaifiyarta ta samu wani ta aura mata...."
Wata irin tsawa Daddy ya doka masa cike da maɗaukakin mamaki ya ce.
" Isma'il!!! Isma'il kana cikin hayyacinka kuwa?"
Girgixa kai Uncle Isma'ila ya yi ya ce.
" Da hankalina Alhaji Mudassir adalci ne nake nema da masalaha. Daman bayan an nemi Hassana an rasa, na baku shawarar cewa ku aura masa Beenafah, to wani abun da ba ku sani ba shi ne; ni nan da kaina na je har gidan Alhaji Mansur Anka na yi masa duk wani bayanin shirinku da ƙudurinku da kuma cutar da marainiya da kuke da niyyar yi kamar yanda kuka ci amanar uwarta. Shi ne na roƙesu akan su haƙura su jingine burinsu da son auren en biyu su aura masa Beenafah da ita Husaina domin dukkan su mutanen kirki ne, sannan sai da ya yi mini alƙawarin riƙeta komai zai faru na ce kada ya yarda ya sake ta... To sai gashi kana naka Allah yana nasa iko Beenafah da mahaifiyarta sun fice daga tarkon ku..."
Wani irin gigitaccen mari Mummy ta sauke masa cike da wani irin sabon shock ɗinda ya fi kowanne ta ce.
" Isma'il ni za ka ci wa Amana? Ni yayarka uwa ɗaya uba ɗaya zaka ci wa Amana??"
Wani irin malalacin murmushi ya saki sannan ya Girgixa kai yana wani kallonta a sheƙe ya ce.
"Duk wani maci Amana Hajiya Zaliha ai bayanku yake...Mata daga mutuwar Mijinta kuka zalunce ta, kuka haye kan dukiyarsu kuka zauna a kai..."
"Isma'il miye yayi zafi haka da har ka shirya mana wannan cin amanar??"
"Because ni Hajiya Mulaifa ta fiye mini ke! A cikin kayan ta na samu gwalagwalai na kai aka bani milliyan goma sha ɗaya wanda da su ne na fara zuwa Lagos ina ɗauko kaya har yau inda na zama shahararre dukiya ta ninku. Ke fa? Ƙololuwar kyauta ta da ke shegiyar dubu hamsin ce...kin ko ga irin wannan gatan da Hajiya Mulaifa ta yi mini mi zai sa na cutar da ita? Ni sai daga baya ne ma na gane cewa banga laifin da ta muku ba kune azzaluman...saboda haka ni In sha Allahu daman na kuɗura a raina zan mayar mata da kuɗin ta sannan na roƙi gafararta, kuma ko yanzu ba zan sare ba, zan ci gaba da nemanta In Sha Allahu. Sannan abu na gaba da ya kamata ku sani shine... HASSANA ba guduwa ta yi ba kamar yanda kuka ɗauka. Nan garin ta zo inda muke muka aurar da ita ga SALMAN ɗinda take so yake sonta...."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 32*
Wani irin juyawa kanta ya shiga yi har bata san lokacin da ta yi tangal-tangal ta faɗa jikin gini ba tsabar tsananin shock ɗinda ya shige ta.
Ammar dake tsaye tunɗazu da shi da ɗan uwansa ne ya kalli Husaina dake ta rusa kuka ya ce.
"Ki yi haƙuri Husaina....Na yi buri da son kasancewa inuwa ɗaya da ke..to amma kuma halayyar iyayenki ta saka dole na janye ko bana so. Mun ɗauka cewar only dukiyan ne kawai suke kwaɗayi wanda duk munji mun gani a haka, to amma irin abin da suka iya aikatawa ga familyn Dr. Bello da suke jini ɗaya bana tunanin muma idan suka samu wata dama a kanmu za su ɗaga mana ƙafa...Mun barku lafiya cikin amincin ubangiji. "
Daga haka ya ja hannun Ameer suka fice yayin da ransu ke ta yi musu ba daɗi saboda mamaki. Daman tun da Uncle Isma'ila ya sanar musu halin da ake ciki iyayen su suka tattara suka koma Abuja. Su ma yanzu ba jimawa za su tattara su koma. Idan da rabon su yi auren watarana za su yi.
Wani irin gigitaccen ihu Mummy ta buga tare da shan kwalar Uncle Isma'ila ta ce.
"Allah ya isa tsakanina da kai Isma'ila! Allah ya tsine maka albarka ya haɗa ka da bala'i da masif...."
Wayar shi ya ciro daga aljihunsa na gefe yana ta wata dariya kamar ba shi ne ta ci wa kwala tana zagi ba. Kira ya yi tare da saka wayar a Handsfree.... Jin haka yasa Mummy ta sake shi tare da baza kunnuwa ta ji kuma miye abun da yake shiryawa. Cike da sabon mamaki ta ji muryar Hassana tana faɗin.
"Hello Uncle!"
Murmushi ya yi ya ce.
"Na am Daughter Hassana. Ya gida, ina mai gidan?"
"Lafiya lau Alhamdllh. Salman ya fita yana wurin aiki... Ya su Mummy??"
Fisge wayar Mummy ta yi cike da baƙin ciki a zafafe ta ce.
"Suna gidan ubanki...!! Suna gidan ubanki na ce Hassana..."
Daga haka kuma sai ta fashe da kuka tana faɗin.
"Yanzu Hassana cin amanar da za ki mini kenan? Bayan na gama wahala dake, ci, sha sutura da ilmi amma abin da za ki saka mana da shi kenan???"
Murmushi Hassanar ta yi ta ce.
"Mummy ba cin amana ba ce wannan, dan Allah ki yi mini aikin gafara, ina roƙo da ke da Daddy dan Allah ku yafe mini...na auri wanda nake so ina zaune lafiya....sannan ina muku albishir da cewa a duk sanda kuka shirya karɓa ta dani da mijina zamu zo taho gareku... "
" Wallahi kada ki kuskura..... Kuma ki je ga ki ga wanda kika zaɓa, Allah ya tsine miki albarka... "
Da ƙarfi Uncle Isma'ila ya fisge wayar tare da kashewa ya kalle ta ya ce.
" Babu abin da tsinuwarki za ta yi mata Hajiya zaliha domin ba ta aikata miki komai ba. Kuma kada ki ɗauka cewa wai daga ni sai ita muka ƙulla wannan, a'a; Da ni da Alhaji Baba da su Hajiya Ermama duk tare muka haɗu muka yi budurinta a nan, wannan kuma ya rage naki.... Kai kuma! "
Ya faɗa yana nuna Daddy ya ce.
" Wallahi ka ji tsoron Allah tun wuri ka canja takunka tun lokaci bai ƙure maka ba. Ni dai Allah ya sani na tuba da duk abin da na aikata kuma ba zan sake ba... "
Tura shi Mummy ta shiga yi da ƙarfi tana faɗin.
" Fi ce mana daga gida ɗan iska azzalumi. Kuma daga yau babu ni babu kai... "
Ƙwace hannun na Mummy Aysha ta yi daga jikin Uncle Isma'il ɗin cike da karyewar Zuciya ta ce.
" Ki daina Mummy! Enough! Shin wai har yaushe ne za ki daina tsinewa 'ƴa'ƴanki da daina ɓatawa da masu faɗa miki gaskiya?? AMMIE ta riƙe miki 'ƴa' ƴanki cike da soyayya da gata amma haka kika juya mata baya kika ci amanarta. Saboda kawai na faɗa miki gaskiya na ce zan ɗauketa daga nan kika ce kin tsine mini, ki ka yi ta jifata da mugayen alkaba'i kika rabani da dangina....Hafiz ma akan kuskure ɗaya! Wanda shi ma ɗin duk laifin ku ne amma haka kika juya masa baya ba kya ko kallon inda yake, Hassana ma saboda kawai ta zaɓi Mijinda take so itama kin ce taje kin tsine mata, Uncle Isma'ila ma haka!.....Shin Mummy a haka kike so Allah ya cika miki burukanki bayan duk kin bi kin kauce hanya?? Anya ke uwa ce kuwa?..... Daddy... "
Ta furta sunan shi a hankali tana mai ci gaba da zubar da hawaye ta ce.
" Abbie! Abbie ya kula da kai tamkar wani uba da ɗan sa... Amma saboda kwaɗayin abun duniya wanda nasan cewa ko rantsuwa na yi ba zan kaffara ba, da ace kabi hanyar lalama da duk abin da ka nema a wurin Ammie za ta baka. Shin kasan cewa a lokuta da dama idan ka nemi wani abun ita ce wacce ke turo maka da kuɗin kafin ma Abbie ya gama yankewa...bai taɓa yin wani abu ba ba tare da ya shawarce ta ba a kanka.... Wallahi tallahi kamar yanda na taɓa faɗa maka a baya Daddy, idan har ka bari Allah ya ɗauki ranka kana cikin dukiyar marayu wallahi kana cikin bala'i da masifa, domin Allah da kansa ya yi alƙawarin ƙona duk wanda ya ci dukiyar marayu tare da azaba mai raɗaɗi. Tun a nan duniya ya ce duk wanda ya ci dukiyar Marayu WUTA ya ke ci a cikinsa..."
Durƙushewa ta yi akan ƙafafunta tare da harɗe hannayen ta cikin magiya ta ce.
" Dan Allah Iyayena, ina roƙonku da ku canza.... Ku canza tun lokaci bai ƙure muku ba. "
Daga haka ta miƙe ta shiga kai tsaye ta tattara kayan ta ta fito riƙe da hannun Baffa.
Kallonta Daddy ya yi jiki a sanyaye ya ce.
"Haba Aysha! Miyasa za ki tafi tun yanzu? Ki bari mu koma Abuja mana, sannan sai a shirya miki daga baya ki wuce London ɗin.."
Wani irin sabon ƙullutun baƙin cikin ne ta ji ya taso ya sake danne mata ƙahon zuciya. Wato ma ba maganar neman Ammie yake ba, maganar komawa Abuja yake... Hhm! Allah ya kyauta.
" Aysha... "
Idonta a ƙasa ta girgiza kanta ta ce.
" A'a Daddy! Zan koma yanxu, in sha Allahu zan dawo bada jimawa ba. Allah ya kai ku lafiya ya tsare hanya."
Fitowa ta yi ta tarar da Uncle Isma'ila yana magana da matarsa Aunty Suhaila.
Kallonta ya yi ya ce.
" Aysha ina za ki haka?"
Cike da jin wasu sababbin hawaye ta girgiza kanta ta ce.
" Uncle Isma'ila tafiya zan yi...wallahi idan na ci gaba da zama zuciyata bugawa za ta yi..."
"To na ji... Amma ki bari zuwa gobe.."
"Uncle Isma'il ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya ƙara kwana a garin nan ba. Sokoto zan tafi, idan na kwana biyu na wuce."
Kallon Suhailar ya yi ya ce.
"Suhaila! Ki shirya ki wuce gida, zan je na kaita Sokoton na dawo, idan na dawo sai mu tattara mu koma gidanmu domin na san Hajiya Zaliha ba za ta barmu mu ci gaba da zama gidan nan ba."
Daga haka ya janyo motarsa ya buɗe ta shiga da kayan ta suka kama hanya.
********
Duniya sabuwa ta dawo a wurinmu. Dr. Basheer ya zuba mini ɗunkuna na manyan kaya na alfarma. Komai an shirya shi cike da tsari da burgewa. Ashe akwai dangi ma su haɗin kai da nuna soyayya ta tsakani da Allah haka? Gaskiya mun ga ƙauna wurin dangin Dr. Basheer mun gode kuma munji daɗi har cikin ranmu.
Kamar yanda aka tsara ranar Talata aka yi Salalle da Kamu. An ƙawata Hall an kuma tara mutane tamkar mun yi shekaru da sanin mutane wanda duk su Hajiya Asma'u ne suka gayyace su. A jiya kuma Laraba aka yi Walima ta ji da gani a wani kalar Hall na daban wanda yau ne muka wayi gari wacce ta kasance ranar wunin buki.