Ganin ido complete - Chapter 42
Ganin ido complete Chapter 42: Ganin ido complete Chapter 42. Cikin azama suka tallafa shi tare da mai gadi da wani mai aikin share-sharen gidan wanda suke…
3,332 words
Cikin azama suka tallafa shi tare da mai gadi da wani mai aikin share-sharen gidan wanda suke kira cika aiki suka sanya shi a mota. Mummy, Humaida da kuma Husaina suka yi asibiti da shi cike da tashin hankali.
Suna isa aka kwashe shi zuwa Emergency unit yayin da suka yi cirko-cirko a reception ɗin suna ta koke-koke.
Husaina na cikin waya da Hafiz taji muryar Mummy a raunane ta ce.
"Husaina wai miye ne a ka rubuta a wannan takardar? Kin kama abu kin riƙe kuma kin ƙi ki faɗamin miye aka rubuta a ciki..."
Tana yi tana share hawayenta ta kalleta a raunane ta ce.
"Mummy ki kwantar da hankalinki, ki bari a fara shawo kan matsalar Daddy tukun...."
Cikin ƙufula ta kalleta cike da masifa ta ce.
"Ƙaramar yarinya kika mai da ni ko me? Ki faɗamin miye a ciki ko ki bani na karanta da kaina.."
Miƙa mata takardar tayi tare da faɗin.
"Kafin ki karanta Mummy ina baki shawara ki zama mai tawakkali da mai da lamarin ki ga Allah..."
*******
Wani ɗakin muka ƙara shiga a tare sannan suka ce ya ɗan jira a nan sai aka shiga dani wani consulting room daga ciki aka ce na hau gado, ni dai ina biye aka min duk abin da za'a min sannan daga ƙarshe muka fito. Nan muka ƙara jira dani da shi na kusan wasu mintuna talatin wanda daga ni har shi ɗin babu wanda ya yiwa wani Magana sannan daga ƙarshe aka kira shi ya shiga wurin likitan sai gashi ya fito yaja hannuna muka fito muka shiga mota muka fara tafiya.
A hankali yaja hannuna ya saƙala a cikin nashi yana jinjina kansa,cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da ƙwarin gwiwa ya fara min magana da cewa.
"Beenafah...You are young, and I'm older....tazarar da ke tsakaninmu tana da yawa sosai...komai a rayuwa yana da sanadi da dalilin faruwar sa. I have met alot of women, masu shekaru, matsayi da girma, but gabaɗayan su babu ɗaya da Allah ya rubuta cewa zan rayu da ita tun ina da ƙananun shekaruna har na kawo yanzu...bayan na cire rai, sai gashi kin shigo rayuwa ta a lokacin da rai bai tsammata ba....and with all this....I don't want any mistake or regret between us in our marital relationship, that's why we have done this Medical check-up...and Alhamdulillah! all the result shows that we are perfectly healthy....but abin da likitan ya bani shawara a kai shi ne, since akwai tazarar shekaru a tsakaninmu,wai I should take things gently......but kin san me na faɗa masa Beenafah..?"
Ɗan rausayar da kaina na yi gefe ina jin yanda zuciyata ke wani irin pumping dangane da irin zantukan da yake mini masu neman su zautar da ƙwaƙwalwata... Ni fa Beenafah ce ba wata ba, amma ji irin abin da yake faɗamini dan Allah sai ka ce wani wanda ya samu tsaran sa.
Ƙoƙarin nike in yi digesting komai a hankali ta yanda zan ƙara fahimtar maganganun nasa da yake faɗa min amma kuma jin na yi shiru yasa shi matsowa da fuskar sa a hankali saitin fuskata ya ce.
"Beenafah!"
Waigowa na yi a hankali na kalle sa sai kuma na saukar da idon na wa ƙasa....a gaskiya ina cikin wani yanayin da ban san ma ta yan da zan fara bayanin abun da nake ji ba a wannan lokacin. Domin kwata-kwata na kasa amsawa, wasu abubuwa na ke ji a ƙirjina har zuwa cikin ƙwaƙwalwa ta.
"Kin ji mi na ce kuwa?"
Murya can ƙasan maƙoshina tamkar wacce aka shaƙe na jinjina kaina a hankali na ce.
"Eh..."
"While...i told him cewa I'm not in rush... I only want love, and Allah's blessing between us...ko ba haka ba?"
"Uhm!"
Na faɗa kawai domin ban san mi zan ce masa ba.
"And for the test also...not because wai I doubt anything Beenafah.....kawai dai I believe health and clarity are the first steps to peace in marriage....idan kuma har wani abu ya faru dake ta dalilin sakacina...to tabbas ba zan taɓa yafewa kaina ba..."
Daga haka ya kalli saitin gabansa inda driver yake zaune ya ce.
" Sidat...Take us to Damas Jewellery."
Jinjina kai Sidat ɗin yayi cike da girmamawa ya amsa sannan nan take ya yi passing ma sauran security ɗinda ke gabansa information ɗin daga nan suka ɗau hanya sai can.
Babban shago ne mai tsananin kyau da ɗaukar hankali wanda babu komai a ciki sai gwala-gwalai da diamond a cikin glasses gwanin burgewa.
Wani dattijo ne mai cikar kamala ya taso daga cikin jerin ma'aikatan da ke ta shawagi a katafaren shagon, sanye yake da jalabiya fara da farar hularsa ya zo cike da girmamawa suka gaisa sannan ya ɗan kalle ni kaɗan sai kuma ya kalli mutumin ya ce.
"I'm looking for something eternal....i mean...something that speaks without words...she's my wife."
Jinjina kai farin dattijon ya yi fuska cike da murmushi sannan ya juya ya zuge wani glass ya ɗauko wani ɗan ƙaramin akwati wanda shi karan kanshi abun kallo ne ya bashi tare da bashi tabbacin cewa wannan zoben zai cika masa ƙudurin da yake cikin ransa,daga haka ya karɓa ya yi godiya muka yo gaba Haroun ya tsaya ya biya sannan ya biyo bayan mu.
A motar ma bai ce min komai ba, kawai ji nayi ya kamo hannuna tare da buɗe ɗan akwatin ya ciro wani zobe mai tsananin kyau yana wani sheƙi ya saka min a yatsan tsakiyar hannuna sannan ya ɗan tallafo haɓata kaɗan da ɗayan hannunsa wanda ba shiri na kalle sa kamar yanda ya buƙata. Yana murmushi ya jinjina kansa sai kuma ya mayarda kallon sa ga hannun nawa dake riƙe a nashi ya ce.
"This ring... Is not about gold or the shine....shi ɗin alama ce mai nuna cewa a yanzu.... I'm not alone, I have a life partner Wanda when ever I remembered or see you around me...sai in ji cewa gabaɗaya matsaloli da duk wasu damuwoyina sun kau."
"Thank you!"
Abin da na iya furtawa kenan tare da ɗora kaina a shoulder ɗinsa a hankali na lumshe idanuwana zuciyata fal farin ciki. Tabbas na yarda akwai daɗi sosai idan mutum na musamman a rayuwarka ya yi maka kyauta ta musamman.
Muna isa gida daman already lokacin sallah ya yi, hakan yasa ya fi ce masallaci ni kuma na shige na yi alwala na fito na yi sallah, bayan ya dawo muka zauna a tare muka ci abinci sannan yace na je na kwanta na huta akwai aikin da zai ɗan yi a yanzu but zai yi joining ɗina daga baya.
Tun da na shige na kwanta ban farko ba sai kusan ƙarfe biyar na tashi na yi sallah sannan na fito parlour na zauna ina kallo wanda ban jima ba na shige na gabatar da magrib da isha sannan na tashi na watso ruwa na fito na shirya cikin wata doguwar maroon sleeping dress har ƙasa sannan na saka net ɗin rigar a kaina tare da ƙara bulbula ƙamƙashi kamar yanda su Aunty Aysha ke jaddadamin na haye gadona na kwanta. Da runtse idona babu abin da ya zo min sai.....'But abin da likitan ya bani shawara a kai shi ne, since akwai tazarar shekaru a tsakaninmu, I should take things gently...'
Shi ne first abin da ya fara zuwa a ƙwaƙwalwata bayan na kwanta na lumshe idanuna wanda sai da na ji gabana ya faɗi. Sosai na shiga recalling maganganunsa na ɗaxu bit by bit tare da sarrafa kowace kalma da bata bigire a muhallin da ya dace har na kambala fassara komai a tunani tirya-tiryan. Gaskiya mutumin nan ba shi da kunya ko kaɗan. Imagine yan da yake magana da ni ko alamar kunya. Yanxu dan Allah ya dace ya riƙa sanar dani waɗanda maganganun? Ni miye nawa a ciki? Mu ɗin aure fa kawai muka yi...and ni ina tausaya masa ne da duk abin da ya faru da halin da yake ciki.....'Idan kuma har wani abu ya faru dake ta dalilin sakacina...to tabbas ba zan taɓa yafewa kaina ba.' A hankali na ji wannan kalmar itama tana dawo min a tunanina wacce ta sakani yin wani murmushin da ban shirya masa ba. Idona na buɗe tare da ɗago hannun da ya saƙala min zoben ina ƙara faɗaɗa murmushina ina jujjuya hannun nawa a hankali. A hakan sai kuma na ji na tsunduma wata duniya ta daban wacce ta saka ni jin kewarsa haka kawai don ɗaukarwa rai. Ina nan ina ta tunani dai har bacci ya yi nasarar ɗaukeni.
Can cikin bacci sosai na ji yana tashina wai na tashi na ci abinci na ce masa a'a ni dai na ƙoshi ba zan iya cin komai ba sai gobe.
Daga nan ban ƙara sanin yanda ya ƙara ta ba sai da na ji mutum ya janyoni jikin sa ya rungumeni tare da janyo duvet ya rufe mu da shi.
Washe gari bayan ya dawo masallaci na gaishesa muka koma muka kwanta. Koda na farka ni ban gansa ba har na gama shiryawa na fito parlour. Nan na tarar da wata matashiyar mata tana tsaye ta kalleni cike da girmamawa ta gaishe ni sannan ta ce min.
"The food for breakfast is ready ma'am...Ko kuma na kawo miki a nan ne?"
"Where is my husband?"
Na tambaye ta tsabar ƙarfin hali ina mai tsatstsareta da ido.
"I'm sorry Ma'am, But I don't know where he is. Wata ƙila kuma ya yi tafiya ta uzuri kamar yan da ya saba....He only told me to bring you food when you wake up."
"Ok. Don't worry I will come and eat later."
Ciki na koma na buɗe ɗakin sa inda na tarar ya bar min wayarsa a kan gefen gadonsa wata ƙila kuma mantawa ya yi da ita.
Ɗaukowa na yi na dawo parlour na zauna na kira Ammie muka sha fira sosai, sannan na kira Mama Asma'u bayan an turo min da numbernta, sannan mummy Sameera, Aunty Aysha da kuma Aunty Labiba. Wanda su ne dai mutane na da nake da su a yanzu. Sosai nake jin kewar su Munira a raina a hankali ina tuna irin rayuwar da mukayi da su. Ko ya suka yi da wayar Emraan da na bar musu a ɗakin su oho!.
Ina nan sai kusan 12pm saura ina ta tunanin rayuwa ina kallo a TV sannan daga ƙarshe na je naci abinci.
A shiririce na wuni ranar har dare, daman ga ciwon ciki a hankali da ya kamani lokaci ɗaya har bana son yin dogon motsi.
Ina ganin takwas ta buga na je na fara cin abinci gudun kada in yi irin na jiya in kwanta ban ci ba. Bayan na kambala na dawo ɗaki na ciro pant da kuma sanitary pad wacce na gani an jera mini kamar a shago na ajiye akan gadon tare da wasu kayan baccin wai don In sauƙaƙa sannan na shige toilet ɗin. Na jima a toilet ɗin ina shiririta Sannan bayan na kambala na fito ɗaure da towel na tsaya jikin mirror ina tsane jikina ina wani ƙarewa kaina kallo da tunanin Yaa Mohaa a raina wanda ya hana mini saƙat. 'Ko'ina ya tafi? Allah masani.
Lokaci ɗaya ya murɗa handle ɗin ƙofar a hankali ya shigo.
'ya ilahiy'
Abun da na yi saurin furtawa kenan a raina tare da runtse idanuna gam tamkar wacce tayi mummunan gamo yayin da jikina ya ɗauki ɓari lokaci ɗaya tamkar zan sume na ɗauke numfashi haka na ji. Gashi na yi nisa da hijab ɗina ballantana in janyo in lulluɓa.
Ƙarasowa ya yi cikin takunsa ya zauna kawai a bakin gado sannan ya kalle ni da mamaki ya ce.
" Miyasa kika rufe idanun ki? Ki buɗe mana ki ƙarasa abin da Kike...i will wait here kada Ki damu...."
Waigawa ya yi gefen da kayana suke a ajiye da nufin ya miƙomin kwatsam idonsa ya kai akan sanitary pad da pant ɗinda na ajiye.
Kallona ya yi sai kuma ya kalli pad ɗin ya ɗauko a hanunsa da pant ɗin ya ce.
" Na ki ne?... Zo... Zo ki nuna min yan da zan yi. I want to help."
Ƙara gimtse idanuwana na yi kawai domin ko gigin matsawa wai inda yake ban yi ba, tun da na lura bai san ana jin kunyar sa ba. Ji wata iriyar tambaya dan Allah wai na ki ne!
"OK... I will follow this instructions and put it for you."
Daga haka ya buɗe pack ɗin gabaɗaya ya ciro ta sannan ya ɗauki ɗaya ya buɗe ta kamar yanda yaga an yi a ledar pad ɗin gradually har ya kambala saƙala ta a pant ɗin sannan ya miƙe ya zo inda nake a hankali ya ce.
" Ina so ki buɗe idanun ki yanzu..."
Jin yan da ya yi maganar yasa na buɗe idanuna cike da jin Kunya na ɗan kalle sa sai kuma na saukar da idanun nawa sannan ya kamo hannuna ya sakamin pant ɗin ya ce.
"Beenafah! Ni da ke fa yanzu abu ɗaya ne.....karɓi ki saka....ko na tsaya na taimaka miki?"
Da sauri na warce ina wani irin girgiza kai na alamar a'a.
Juyawa ya yi ya fita a hankali yana faɗin.
"Ina jiran ki yanzu."
Ban san dalilin hawayena ba,domin na rasa ma mi nake ji a raina dangane da yan da yake min wasu abubuwan a yanzu tsabar yan da nake jin kunya wanda shi sam bai santa ba, haka na share hawayen a hankali sannan na saka pant ɗin tare da sleeping dress ɗin na ƙarasa shiryawa sai Kuma na ɗauki hijab na saka tamkar wata kazar da ƙwai ya fashewa a ciki na fito na tarar da shi jibge da wasu kayayyaki a saman wani glass center table, ga wata Na'ura dake kunne da wani haske tana wata ƙara marar sauti wacce ni dai ba zan kira ta da laptop ba kuma ba zan kira ta da waya ba, shi dai mai abu shi kaɗai ne yasan amfanin ta a wurinsa.
Murmushi ya yi min tare da nuna min inda yake zaune a gefen daman sa nazo na zauna a darare ya yin da ya kalleni cikin natsatstsiyar muryar nan mai saka ni ruɗewa akan nauyin kalamansa ya jinjina kansa a hankali yana kallona ya ce.
"Wannan dress ɗin da kika ajiye akan bed sun yi kyau sosai...kin saka su ne a jikin ki?"
Jinjina masa kaina na yi a raina ina raya tambayar da cewa 'mi yake nufi to?'
Hannunsa ya kai direct ya kama hijab ɗin nawa ya cire kai tsaye ya kalleni murya a ƙasa sosai fiye da ta ɗazu ya ce.
" Kamar yan da na tsammata ne...sun yi miki kyau sosai."
Ni dai wasa kawai nake da zoben yatsana ba tare da na ce masa komai ba, ban wani damu da cire hijab ɗin da ya yi ba domin kuwa, kayan masu kauri ne sosai ga su kuma wandonsu har ƙasa ne, rigar ma mai dogon hannu ce wanda komai ƙwaƙwarsa ba zai iya hango komai a jikina ba domin suna da kauri sosai. Sai dai kuma, har yanxu ban gama dawowa daga shock ɗinda ya bani ba a ɗazu na saka min pad da yayi a pant ɗina.
"Yaushe kika fara wannan abun??"
Wani irin dum na ji, jin saukar tambayarsa da ta ratsa masaraffar saurarona ba tare da na shirya ba. Ƙoƙarin nike in haɗa kalmomin tambayar tasa domin nema yake ya gigita tunanina.
Hannunsa na ji ya sauka a hankali akan cinyata, murya can ƙasan maƙoshi da wasu idanunsa da suka canja sosai, ya kalleni ya ce.
"Uhm! Yaushe ne ya fara?"
"Ɗa zu ne da yamma..."
Na furta masa tamkar zan fashe masa da kuka, kuma tabbas idan ya matsa babu abin da zai hanani saka masa kukan.
Jinjin kai kawai ya yi sannan ya juya naga ya buɗe wata takarda mai ɗauke da zane-zane kamar na Map yana mai ci gaba da aikin da yake, yayinda na sauke wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ina mai resting bayana da kaina a jikin lallausar Kujerar tare da lumshe idanuna ina ji a raina kamar zan nutse akan kunya.
Mun kai kusan 30mnt a haka sannan daga baya na ji ya sake jefa mini wata tambayar da cewa.
"Kwana nawa kike yi ne?"
Shiru na yi masa kamar banji ni yace ba. Jin na yi shirun kuma ban ɗago ba naji ya sake cewa.
"3days?...4days?...ko kuma 5days?...kwana nawa yake ɗaukar ki?...Uhm!"
Hannu kawai na ɗaga masa tare da ware yatsuna biyar alamar 5days ba tare da buɗe idanun nawa ba.
"Can we eat something?"
Girgiza kaina na yi domin har yanzu ni ba zan iya kallon sa ba da wannan kunyar na ce.
"Ni na ci abinci."
Maimakon ya ci gaba da aikinsa, bai yi ba. Ture kayan kawai ya yi ya janyo ni zuwa jikin sa ya ɗora kaina akan ƙirjinsa shi kuma ya jingina a kujerar ya saƙala hannuna a nasa yayi twisting yana Kallon yatsuna ya ce.
"Ki yi haƙuri, ko jiya ma bamu samu munci abinci tare ba, yau ma haka....yanayin aikina yana hana mini sukuni, but zan yi iya ƙoƙarina wurin ganin na sama mana lokaci cikakke kin ji ko, because a yanzu dai kam muhimmancinki ya fiye min komai Beenafah. Yau ma dana fita sosai nake ganin ki a duk abin da nake yi....ni ɗin nan Civil Engineer ne kuma ni ne shugaban kamfanina na gine-gine mai suna Golden Pathways construction...muna aikin gine-gine da tituna kowane iri. Harda ma Bridge Bridge.....main headquarter ɗinmu a nan ne sannan muna da branch a Abuja, Riyadh da kuma London..."
"Allah sarki! Allah ya taimaka ya tsare ka daga dukkan sharri ya ƙara ɗaukaka.."
Ɗago fuskata ya yi ya kalleni na ɗan lokaci sannan ya jinjina kansa da murmushi jin wata irin kyakkyawar addu'ar da bai tsammata ba,ya ce.
"Amin Beenafah. Babu wata rana da za ta zo ta wuce ba tare da na ƙara jin ki da kuma yaba kaifin hankalinki da tunanin ki ba a raina. Ban san ya zan fassara wannan ƙaddarar tawa ba....amma dai kuma,jinkirin ya zame mini alkairi...addu'ar mata zuwa Mijinta....tana da matuƙar tasiri da saurin karɓuwa a wurin Allah..kici gaba da yimin addu'a kinji..."
" In sha Allah."
Hannu ya miƙa ya kashe na'urar sannan ya gyara kayan ya miƙe dani yaja hannuna muka shige ɗakina muka kwanta bayan ya kashe fitilar ɗakin.
Ina jinsa ya jima bai yi bacci ba kamar yanda nima ban yi ba. A yanzu na fahimci wani abu, wato akwai saƙon da baya buƙatar magana ko kuma yinsa a aikace, wani kusanci idan ya yi tasiri, yana isar da saƙo ba tare da furuci ba, to hakan ne a tsakanina da wannan dattijon mijin nawa da na ke jin sa da wani irin muhimmancin da a yanzu dukkan kalaman duniya ba za su iya bayyana abubuwan da na ke ji dangane da shi ba. Ko a yanda yanzu ya ƙware da yi min masauki mai kyau a cikin jikin sa kaɗai yana isar min da wani muhimmin saƙo mai tsananin tasiri da tsayawa a rai.
*********
Gefen su Ammie kuwa. Daman tun da aka kambala hidimar Beenafah Dr. Basheer ya yi alƙawarin kai ta ainahin garinsu inda mahaifarsa take da kuma iyayensa wato Bunza. Kullum sai sun saka rana sai kuma wani abu ya zo ya gifta har dai yau suka yi nasarar shirya tafiyar.
Bayan Bahrain ya fita waje tare da Hamza da Hashi wanda a tare za su tafi domin shi ne wanda zai ja motar sannan Dr. Basheer ya kalli Ammie wacce ta gama shiryawa cikin rantsatstsen lace ɗinta da ya yi matuƙar karɓar jikinta ta ɗauko gyalen ta ta kalle shi ta ce.
"Na gama shiryawa..."
Murmushi ya yi a hankali ya miƙe daga kan gadon da ya zauna zaman jiran ta ya ce.
"Na so mu bar tafiyar nan zuwa wani lokacin musamman kinga Bahrain zai rasa Islamiyyarsa ta wannan weekend ɗin sannan ga boko ma yau ya wuce shi..."
"Haba Dr.! A irin karamcin da su Hajiya suka nuna min bai kyauta ace har yanzu ban je inda suke ba..."