Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 43

Ganin ido complete - Chapter 43

Ganin ido complete Chapter 43: Ganin ido complete Chapter 43. "To ai Hajiyar ce ta cika matsala wallahy. Ga gidanta a nan amma tace ita lallai dole sai a…

3,346 words

"To ai Hajiyar ce ta cika matsala wallahy. Ga gidanta a nan amma tace ita lallai dole sai a Bunza za ta zauna, da ta zo garin nan bata cikakken wata ɗaya za ta juya ta koma, komai aka bata ko aka ajiye ta kwashe ta rabewa Al'umma..."

Murmushi Ammie ta yi ta ce.

" Kamar dai yanda Hajiya Asma'u ta faɗa shekaranjiya ne na cewa a godewa Allah da har ya bata zuciyar son taimakawa al'umma kuma har kuma 'ƴa'ƴanta take sanya ku aikata alherin...kuma ma kwana biyu ne kawai zamu yi.."

"Amma dai..."

Hannunsa ta ja suka yi waje ta yiwa su Inna Hansatu da Zairatu sallama da cewa su kula da gida.

Tana cimma Hamza a mazaunin driver ta girgiza kanta tana dariya ta ce.

"Hamza ni dai kasan tunda ba cizon biri ce ni ba, ba zan yarda ka jani a motar nan ba ko?"

Dariya suka fashe da ita sannan Hamzan ya ce.

"Haba Ammie, hannuna fa yabi sosai..."

"A'a wallahi ban yarda ba..." .Kallon gefen da Hashi yake tsaye shi da Bahrain ta yi ta ce "Hashi Idan kana son na yi tafiyar nan to ka amshi motar nan.."

Bahrain na dariya ya ce.

"Abbu ka faɗamata nan gaba kaɗan am the one to drive her when ever she's going out..."

Dr. Basheer na dariya ya jinjina kansa ya ce.

"Sosai kuwa...Hamza fito tunda bata yarda ba kada ka ɓata mana lokaci.."

Fitowa yayi yana gunguni da cewa duk sanda ya ƙware a mota ko ta ce ya kaita wani wuri ba zai kaita ba.

A gaba suka zauna da shi da Hashi yayin da Ammie, Dr. Basheer da kuma Bahrain suka zauna a baya suna tafiya suna fira har suka isa.

Ammie ta samu tarba ta mutunci a wurin Hajiyar Dr. Basheer da sauran en uwansa wanda har sai da taji hawaye tuna irin yanda Hajiya Rashida take yi mata yayar Dr. Bello kafin ta rasu da kuma irin wulaƙanci da tozarcin da Alhaji Mudassir ya yi mata a lokacin da ta rasa inda za ta Kama.

Hajiya sai aikawa mutane take tana kiran su zo su ga matar Basheeru da ta zo daga Sokoto. Haƙiƙa taga yanda ake ƙauna da nuna karamci na musamman. Ko a daren ranar sun kai sha biyu na dare da Hajiya suna ta fira tana bata labarai wanda wani abun Ammie sai ta tambaya sannan daga ƙarshe ta yi mata sai da safe taje ɗakin da aka ware mata mai babban gado wanda ɗakin harda AC akwai ta kwanta.

Washe gari har Gwandu suka shirya suka je tare da Hajiyar wurin ƙannenta su biyu da suke zaune a can tare da iyalansu suka yo zumunci inda aka cikata da kayan arziki suka dawo washe gari ranar Lahadi suka koma Sokoto.

*******

Gefen su Daddy kuwa, Mummy na gama karanta wannan baƙar wasiƙar kamar yanda ta ce ta fashe da kuka tana faɗin.

"Allah ya fi su....wallahi tallahy kowane ne yake bayan wannan abun ba zai taɓa yin nasara ba...idan ma suna wani iƙirari ne ai dai ko'ina aka tafi ko kotun duniya ce kuwa, haƙƙin Bahrain da Beenafah a Hannunsa zai kasance...kuma sai inga uban da zai hana mana kashe kuɗi mu gani... "

Girgiza kai Husaina ta yi ta ce.

"Uh uhm fa Mummy! Hanyar lafiya a bita a sannu. Kin san harkar doka yanda take....ki bari abi komai a sannu dan Allah..."

Kiran likita, shi ne abin da ya katse musu maganar da suke da gudu suka runtuma suka tafi. Bayani ya yi musu da cewa ya samu mummunan heart attack ne wanda ya yi sanadiyyar toshewar jijiyoyin da suke harba jini zuwa ga zuciyarsa wanda idan ba'a yi gaggawar yi masa aiki nan take ba komai na iya faruwa da shi. Saboda haka idan sun shirya za a basu takardar refferal nan take zuwa Babbar asibitin da ake aikin zuciya dake nan cikin garin Abuja. Bayan sun amince ya aka basu takardar magunguna waɗanda aka yi masa amfani da su nan take da suka kama kusan 500k lokaci guda.

Bayan Hafiz ya iso washe gari suka kwashi Daddyn zuwa asibitin inda aka ce aikinki kaɗai a 13M za'a yi shi banda kuɗin magani da sauran wasu abubuwan.

A ranar da akayi aikin a ranar Aysha ta iso lokaci ɗaya da Hassana wanda ita ce ta tsara hakan da cewa dole sai ta zo kuma kada ta damu da duk wani abin da Mummy za ta yi. Lafiyar Daddy ita ce kan gaba da komai a yanzu.

Suna asibitin koda suka koma an bugawa gidan su kwaɗo an rufe, nan suka tarar da masu aikin su sun yi cirko-cirko. Aunty Aysha ta tura musu kuɗi kowa 100k tace su tafi sai sun neme su, haka Biba ta shirya itama ta wuce.

Hotel suka kama tsawon kwana uku sannan daga ƙarshe suka samu wani ƙaramin gida suka siya a wata ƙaramar unguwa.

Mummy ta shiga cikin tashin hankalin da kallo ɗaya idan ka yi mata sai ka tabbatar da cewa ta fita daga hayyacinta. Akan yan da ta zabge lokaci ɗaya, ba ta ci bata sha baccin kirki ma wannan bata iya yi sai kuka wanda a yanzu ya zame mata jiki. Musamman da Alhaji Baba mahaifinta ya zo ya buɗe mata wuta domin bai san komai ba sai yanzu da wannan abun ya faru sannan ya san miyar da ake sha. Haka ya zage ya yi mata wankin babban bargo yace kuma babu ruwansa, duk abun da zai je ya dawo kada ta ce shi ne mahaifinta.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....

*PAGE 39*

Sannu a hankali rayuwa ta shiga tafiyar damu wanda a yanzu mun shafe tsawon wata uku cikin na huɗu a tare. Wata irin shaƙuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu wanda a yanzu na sake da shi sosai ba kamar farkon zuwanmu ba,musamman da na lura shi ɗin mutum ne mai ɗaukar abin da yake so da matuƙar muhimmanci, ya ɗaukeni tamkar wata aminiyarsa da ya kwashe tsawon shekarun rayuwar sa tare dani. Hatta wurin aikinsa sau uku yana tafiya dani da sunan rakiya,haka ma cikin gari mun fita sau biyu mukaje wuraren da suka sakani nishaɗi.

Kullum muna tare da juna sai idan zai yi tafiya ta barin gari irin ta kwanaki haka zai tafi ya barni cikin kewar sa, domin a yanzu idan baya nan ko baccin kirki bana iya yi a yanda na saba da kwana cikin jikin sa, idan ya nisance ni hakan yana mini wahala. Yasa na yi sabon da rashin sa a kusa dani yana sakani kasala,tun ina jin kunyar sa har na zo na saba wanda hatta cin abinci yanzu tare muke yi, dama duk wasu abubuwan rayuwa namu sun zamo ɗaya kamar yan da ya tsara. Gashi kuma Shi ɗin mutum ne kaifi ɗaya wanda bai iya lungu ba,komai kai tsaye yake gabatar da shi, duk abin da yake so na sani dangane da rayuwar sa ko wani abu, kai tsaye yake sanar dani tare da fahimtar dani da kyau yanda zan fahimta.

Yau ma bayan na yi sallar asuba komawa na yi na kwanta ban fito ba sai misalin sha ɗaya na safe. Da Wayata babbar Samsung ɗinda ya siyamin sati uku da suka wuce na fito a hannuna na shige Kitchen kai tsaye muka gaisa da su Madam Amima wacce ita ce ke kula da Kitchen ɗin na duk abincin da za'a sarrafa mana ita da sauran ma'aikatan. Bayan mun gama gaisawa cike da girmamawa ta tambayeni abin da zanci na ce mata ba komai zan duba abin da suka dafa ɗin da kaina tun da ni kaɗai ce a gidan, domin ya yi tafiya yau kusan six days kenan, abun da bai taɓa yi ba, duk ƙoƙuwar tafiyar sa kwana ɗaya ne ko biyu highest Idan ya daɗe ya yi spending 3days ya dawo.

Tea na haɗa kaɗan sannan na zuba abincin da suka dafa shima kaɗan a plate na zauna a kitchen island na ci, Bayan na kambala na ɗauki wayata na kira Ammie muka gaisa sannan na kira Aunty Labiba wacce naga miss calls ɗinta har guda biyu itama muka gaisa da ita. Bayan na gama na miƙe naje bakin fridge na ɗauko bottle water waɗanda basu cika sanyi ba sannan na duba kan fridge ɗin na ɗauko maganina na Folic Acid wanda na fara sha tun farkon dawowarmu daga asibiti bayan ya yi min bayani da cewa Dr. Ashman ne ya bayar kuma ya yi masa bayani na musamman akan cewa yana da matuƙar muhimmanci Macce ta fara shan sa atleast Wata uku kafin ta ɗauki ciki. Dalilin haka kuwa, shi ne;yana zama rigakafi daga hana samun nakasar ƙwaƙwalwa da ƙashin baya na jariri wanda ake kira (Neaural tube defects) kamar cutar da ake kira spina bifida wanda ƙashin baya zai rabu gida biyu ya kasa haɗewa da juna ko kuma Anencephaly wanda za'a haifi yaro babu murfin ƙwaƙwalwa ma'ana babu ƙashin kai. Wanda waɗannan cututtukan da makamantansu suna faruwa ne a makonnin farko na ciki a lokacin da ake haɗa halittar ɗan adam, wani lokacin kafinma mace ta gane tana ɗauke da juna biyu. Hakan yasa ake ƙarfafa Mata game da zuwa asibiti kafin ɗaukar ciki dama bayan sun ɗauki ciki sannan ake ƙarfafa su akan shan folic acid kowace rana.

Sannan shan folic Acid yana ƙara lafiyar mahaifa da ƙarfafa ƙwayoyin halitta da kuma taimakawa wurin ɗaukar ciki cikin ƙoshin lafiya. Yana hana karancin jini abinda ake kira (Megaloblastic anemai) wanda idan akwai ƙarancin jini yana kawo gajiya, kasala, rauni kafin ko bayan samun ciki.

Sannan shan folic Acid yana inganta lafiyar jiki da jini gabaɗaya, yana taimakawa Mace ta samu lafiyayyen ciki ba tare da wata matsala ba. Sannan bayan cikin ya samu still shan folic Acid yana da matuƙar muhimmanci domin yana taimakawa wajen gina ƙwaƙwalwa da kyau da kuma jijiyoyin mahaifa domin ta samu ƙarfin riƙe jariri. Yana taimakawa wurin samar da lafiyayyun ƙwayoyin jini (Red blood cells) ga Uwa da kuma Jaririn. Yana inganta gina gaɓoɓin jiki domin yana taimakawa wajen gina DNA da kyau abinda ake kira Gene( wato ƙwayoyin halittar gado wanda ɗan adam yake samu daga uwa ko uba a lokacin halitta kamar, launin fata, gashi, ido, tsawo, da wasu siffofi dai na daga ɓangaren uwa ko na uba su gini da kyau ba tare da wata nakasa ba).

Sannan shan folic Acid yana da matuƙar muhimmanci domin yana rage yawan haɗarin haihuwar ciki wanda bai kai lokacin haihuwa ba abin da ake kira (premature birth) da Kuma haihuwar yaro wanda nauyin shi bai kai adadin yanda ake buƙata ba (Low birth weight). Ko kuma yawan mutuwar yaro a ciki abinda ake kira (Intra-uterine fetal death). Folic Acid Yana da muhimmanci sosai domin yana bada kariya daga cututtukan chromosal abnormalities musamman ga mai shekaru da yawa da yake buƙatar haihuwa.

Haka ya zauna ya karantar dani amfaninsa daki-daki wanda tun daga ranar ban taɓa tsallake rana ɗaya ba ba tare da nasha ba. A nan na ajiye kan fridge ɗin na musamman gudun kada ma na manta, idan kuma yana gari kullum shi ne wanda yake ɗaukowa da kansa ya bani nasha.

Ina tsaye bakin gangar fridge ɗin bayan na sha riƙe da ruwan a hannuna na shiga ƙoƙarin kiransa da numbern da naga ya yi min text daren jiya kawai na ganshi ya shigo ya tsaya gabana.

Gabana ne ya yanke ya faɗi ganin irin yanayin da yake ciki. Gabaɗaya idanunsa sun sauya kala, fuskar nan ta yi kajin-kajin, kwata-kwata dai Sam baya cikin karsashinsa da ya saba.

Hankali tashe na kallesa na ce.

"Subhanallah! Lafiya kuwa? Miye ya sameka haka??.."

Ƙarasowa ya yi gabana kai tsaye ya rungumeni sosai tamkar wanda zai mai da ni ciki. Shiru na yi nima a hankali na saƙala hannayena zuwa bayansa tare da ɗora kaina akan ƙirjinsa wanda har ina iya jiyo sautin yanda zuciyarsa ke bugawa a hankali. Bayan mun ɗauki tsawon lokaci sai na ɗan zame kaina a hankali na ɗago na kalle shi cikin tausasawa na ce.

"Allah yasa lafiya?"

A hankali ya binne fuskarsa a gefen wuyana sannan ya shiga gogawa yana sniffing ƙamshina har zuwa fuskata ya yi kissing lips ɗina lightly Sannan ya janye cikin wata iriyar murya mai cike da rauni ya kalleni ya ce.

"I'm sorry Beenafah....I'm so sorry da duk irin rayuwar da kikayi a baya....ashe kema haka kika rayu cike da ƙunci da baƙin ciki?? I... I don't know anything about you sai yanzu....na kasa Bacci na rasa abin da yake min daɗi. Ashe da ciwo haka sosai a rayuwarki...a haka kuma kika sadaukar da kanki gareni don kawai irin taimakon da Labiba tayi miki just because kiga ta yi farin ciki...Kin sha wahala Beenafah, abubuwan da suka faru dake sunfi ƙarfin ƙwaƙwalwarki da shekarunki..Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!... "

Bansan lokacin da wani murmushi ya suɓuce min ba akan mamakin yanda ya duk ya susuce ya rikice. Jinjina kaina na yi ina kallon sa still da murmushi da kuma hawaye a idona na ce.

" Wai Kuka kake??"

Jinjina kansa ya yi yayin da ya kafe idonsa a nawa ya ce.

"Da ni kaɗai kika da ce Beenafahta domin nafi kowa sanin muhimmancin ki a duniya...idan zan tuna abun da ya faru dake sau dubu sai na mutu sau dubu akan baƙin ciki da takaicin yanda kika kasance.."

Jinjina kaina na yi tare da sauke ajiyar zuciya a hankali na ce.

"And that's what life is all about....Ɗan Adam ba zai gushe ko in ce ba zai huta daga dukkan igiyoyin ƙaddara ba har sai ranar da akace ya faɗi ya mutu...amma muddin yana raye...to tabbas, arzikinsa, sarautarsa, mulkinsa, wayonsa, dabararsa, ko kuma talaucinsa basu isa su hana faruwar duk abin da Allah ya ƙaddaro masa ba. Duk gatanmu sai da muka wayi gari cikin tsananin ƙunci, yunwa, azaba, da tauye haƙƙi...Kai kuma, duk kuɗin ka, girmanka, dangin ka da duk shaharar da kayi a duniya,hakan bai hana maka shiga cikin matsanancin ƙunci da baƙin ci ba, sannan wacce take zaman uwa a gareka... Sai gashi ta kasance ita ce ƙaddarar ka... "

Sake rungumeni ya yi muryarsa har tana sarƙewa ya ce.

" Haƙiƙa kin cancanci farin ciki da kwanciyar hankali na rayuwa Beenafah... Kuma na yi alƙawari....muddin ina numfashi a doron ƙasa to tabbas zan tsayu akan dugadugaina wurin baki dukkanin wani farin cikin da ya dace da rayuwarki.."

Janyewa na yi da guntun hawayena ina kallon tare da neman yanda zan kwantar masa da hankalin sa na ce.

" Thank you....yaushe ka dawo.?..sannu da zuwa!"

Ganin ya ƙura ido yana kallona baice komai ba yasa na ɗan shagwaɓe fuska na ce.

"Ni fa kasan bana son inga kana damuwa wallahy, hankalina tashi yake yi..."

"Dole na damu Beenafah..."

Hannunsa na kama ina murmushi na katse shi da faɗin.

"Komai ya yi farko yana da Ƙarshe watarana Ya Mohaa...Ubangiji ne kaɗai wanda bai da farko kuma bai da Ƙarshe...amma dukkan wani al'amari na duniya tabbas yana da farko kuma yana da Ƙarshe...kamar dai NI da KAI ɗinnan yanda al'amarinmu ya kasance..Ga shi yanzu ka same ni nima kuma na same ka...."

Kaina na mayar akan kirjinsa sannan na ci gaba da cewa.

" Abubuwa sun yi maka yawa, kullum cikin aikace-aikace kake. Idan kace za ka riƙa saka wasu damuwowi a ranka, to tabbas abin ba zai yi kyau ba. Na gode sosai da yanda ka damuna nima kuma ina alfahari dakai."

Ina gama faɗar haka na riƙe hannun sa muka wuce ɗaki ya yi wanka domin shigowarsa gidan kenan da alama a hanya ya kwana.

Bayan ya gama shiryawa na kawo masa abincin yaci sannan ya tashi ya ɗauki jakar sa ya fice office bai dawo ba sai kusan 9:pm. Sai da ya tsaya ɗakinsa yayi wanka ya shirya sannan ya shigo inda nake wanda ni a lokacin har na yi wankana nima na gama shirin bacci.

Yana shigowa na na sauko daga gadon na ce.

"Sannu da zuwa..."

Murmushi ya yi tare da kallon sleeping dress ɗinda ke jikina, ya ce.

"Beenafah."

"Na am."

Na amsa masa ina murmushi.

"Ya kika wuni? Ya daren? Koda yake kin faɗamin cewa bakya jin bacci...miye naga kina yi lokacin da na kiraki?"

Murmushi na yi na ce.

"Ina ɗakin can wanda muka shiga ranar, wani littafi ne na ɗauko...."

"Uhm. To kinci abinci?"

"Aa..ba kai ne kace in jira ka ba.."

"Ok to, muje."

Dining area muka je muka zauna kamar masu cin wani abincin kirki domin daga ni har shi ɗin ko plate ɗaya cikakke bamu ci ba.

Parlour muka dawo ya janyo table ya ɗora kayan aikinsa kamar kullum ni kuma na zauna a bayansa tare da manna jikina da bayansa na buɗe littafin da na ɗauko daga cikin kayansa wai shi the power of Du'aa.

"Beenafah!"

"Na am!"

Na amsa masa jin ya kira sunana ba tare da na motsa ba.

"I have something important to share with you....juyo ki gani."

Ajiye littafin na yi tare da zuro ƙafafuna na sauko na ce.

"Mine ne wannan?"

Wani babban file ne na fata dake gabansa ya buɗe ya ɗauko wasu takardu sannan ya ɗauko wani abu mai kamar sanda dogo ya warware wanda ashe babban Map ɗin Nigeria ne. Pointer ya ɗauka yana nunawa ya kalleni ya ce.

"Duba nan ki gani.....Da yammar nan na yi receiving business proposal daga multinational company a nan Dubai. They want me to supervise a new pharmaceutical plant construction in Nigeria. And location ɗin a Kaduna State ne..."

Ɗan wara ido na yi na ce.

"Kaduna? Za ka sake komawa Nigeria kenan?"

Jinjina kansa yayi ya ce.

"Yes, but amma ba yanzu ba."

Wata red marker ya ɗauko ya nuna min wani site yana faɗin.

"Suna so ne zuwa next month in tafi in yi inspecting ɗin wurin, Idan naga cewa wurin zai yi kuma na yi accepting...then the contract will run for two years.."

Ɗagowa ya yi ya kalleni yana jinjina kai ya ce.

"That's why I wanted to discuss it with you first...your opinion matters to me more than the offer itself..."

Shiru na yi tare da ƙure takardar da kallo ina nazari da kuma mamakin yanda rayuwa ta gangaro damu har ta kawomu wannan matakin wanda yanzu hatta harkar kasuwancinsa idan zai yi sai ya nemi shawara ta.

"Beenafah.."

Ɗagowa na yi na kallesa na ce.

"To idan ka je kayi Inspecting ɗin kaga wurin ya yi mi za a yi?"

"While....Aiki ne za'a yi babba...Basically, i will be the project consultant....i will design the layout for the research lab,production plant, and quality control unit...and kin san wani abu.?"

Girgiza kaina na yi alamar a'a.

"The payment is 1.2 million dollars for the entire contract."

Jinjina kaina na yi ɗauke da Mamaki a fuskata na ce.

"Duk da cewa ban san lissafin kuɗinba, amma dai daga ji suna da yawa sosai."

"Uhm! It's huge. But you know, money isn't always everything, Kaduna has its own challenges and the work is technical...i might have to stay long wani Lokacin..."

Wani kallon na jefa masa mai nuna zallar kulawa na ce.

"To me...your safety comes first...duk wani abinda zai saka ka wahala ko kuma ya zama barazana ga rayuwarka ko kuma lafiyarka ni ba son sa nake ba.."

Jinjina kansa ya yi cike da alfahari ya ce.

"In Sha Allahu babu abin da zai same ni Matata, addu'arki tana tare dani.."

Daga haka ya ƙara gyara zaman Map ɗin a kan table ɗin ya shiga nuna min wasu wurare da marker ɗin yana faɗin.

"This red zone here...represents the land area they have secured..and the blue lines show the water access for the factory, and this green mark...that's where the main admin building will be....."

Haka ya zage ya bayyana min duk yanda aikin zai kasance idan har abun ya yiyu sannan daga ƙarshe yace.

" Zan iya yi ko kuma kina ganin na fasa? What's your verdict?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull