Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 50

Ganin ido complete - Chapter 50

Ganin ido complete Chapter 50: Ganin ido complete Chapter 50. "Ba ma zancen kuɗinda suke da shi ba Aunty Beenafah...yanda aka haɗa kai family guda suke…

3,368 words

"Ba ma zancen kuɗinda suke da shi ba Aunty Beenafah...yanda aka haɗa kai family guda suke komai a tare cikin farin ciki shi yafi burgeni...ga ƙamshi dare da rana shi a cikinsa suke kamar waɗanda suke da gonar turare...."

Haɗiye sauran maganar ta tayi duk muka shiga taitayinmu ganin su Khalaty Fattoom (kamar yanda Khairum ta sanar mana cewa Khalaty Auntie yake nufi Khalee kuma Uncle) ita ma Khairum ɗaya daga cikin jikokin gidan ce wanda ita ɗin matar aure ce ba kamar su Suwara ba.

cikin shirin su suke domin suma sun caɓa ado kowa sai walwali yake tamkar wasu taurari a sararin Samaniya.

Bayan Jadda ta fito itama muka ɗunguma muka fita inda muka tarar an jera motoci tamkar wani buki. Rarraba ido na fara domin a yanzu babu abin da nake so da gani irin Dayaa, wallahi na yi matuƙar kewar sa kawai dai na ƙume daɗina ne ban tambayi kowa ba don kada a ga rashin kunyata ace ina tambayar mijina. Babu abin da yake yawo a zuciyata da ƙwaƙwalwar kaina sai kallon da yake min ɗazu. To ko dai fushi yake yi dani akan abin da ya faru shekaranjiya? Ya fa kirani ban ɗaga ba kuma yayi text shi ma ban masa reply ba. Take na ji ina neman rasa nutsuwata domin ni ce bani da gaskiya.

Nayi nisa a tunanin sosai wanda idan ka kalleni zaka ɗauka cewar da gaske kallon kyawawan motocin nake, amma kuma Sam ba haka bane tunanin Mijina ne a raina.

Ban ankara ba kawai na ji an kama hannuna a hankali an sumbata. Da sauri na waigo domin ganin wanene wannan.

Tsaye na gansa cikin suit baƙi ya sha kyau har ya gaji sai murmushi yake min.

Ajiyar zuciya na sauke a hankali tare da ɗora kaina a ƙirjinsa na rungumesa ina murmushi na ce.

"Ina ka shiga tun jiya baka dawo ba?"

Cikin sigar zolaya ya ce.

"Tun da ba ki da Buƙata dani ba dole na kama kaina na shiga duniya ba...."

A ruɗe na ɗago na kalle shi ina mai waro ido bakin gaskiyata na ce.

"Shiga Duniya kuma Dayaa?"

Lokaci ɗaya yaji wani abu ya tsarga tundaga tsakiyar kwanyarsa har zuwa babban yatsan ƙafarsa. Wani irin harbawa zuciyarsa ta shiga yi yana mai jin duk wata jijiya dake jikin sa ta ɗauki ɗumi. Kai! Hatta jijiyar da ke cikin wandonsa sai da ta karɓi na ta saƙon ba tare da ta shirya ba. Wannan wanka na ta na yau da ƙamshinta nema suke su haukatasa.

Ƙara narke murya na yi domin dai kalmar Shiga duniyar da ya furta ba ƙaramin birkitani tayi ba. Mai shiga duniya fa shi ne wanda ya zaɓi ya bar komai nashi saboda wani dalili ya yi tafiyarsa duk inda ya so.

"Tambayarka fa nake?"

"Uhm!"

Abin da ya furta mini kenan tare da jan hannuna muka faɗa mota. A hankali ya ɗora kanshi a bayan seat ɗin yana mai lumshe idanunsa ya yi shiru kamar wanda yake zaune shi ka ɗai ba tare dani ba.

A ɗan tsorace na ƙara matsawa jikin shi da damuwa na ce.

"Lafiya kuwa?"

Buɗe idanunsa ya yi ya kalleni cikin ɗan hasken da ke shigowa na hanya, ji ya yi ta ko'ina ya ƙara ɗaukar ɗumi wanda sosai a yanzu yake jin ba zai iya haƙura ba.

Hannunsa ya kai ya zagaye kwankwasona ya riƙoni zuwa jikinsa sosai ya haɗe bakin mu ya fara kissing ɗin lips ɗina a zafafe har zuwa kwarmin wuyana wanda bai dakata ba sai da yaji ya ɗan samu sassauci sannan ya janye murya a ƙasa sosai ya jinjina min kansa ya ce.

"Kin yi kyau sosai Bibi...ba don wannan fitar ta riga ta kankama ba da babu abin da zai sa naje da ke a haka"

Yana gama faɗar haka ya kwantar da kaina a ƙirjinsa yana mai ƙara buɗe ƙofofin hancinsa yana shaƙar daddaɗan ƙamshina mai ƙara hargitsa masa tunaninsa.

lafewa na yi nima ina mai jin wani irin yanayi na musamman a tare dani, a irin yanda na kasa hana sa kaina hakan shi ya tabbatar min da cewa nima na yi kewar sa kamar yanda yake ji. Haka muka ci gaba da tafiya har muka isa wurin da muka nufa.

KHARTOUM PRESIDENTIAL BANQUET HALL.

A hankali motocin suka shiga suka Parker a harabar babban Hall ɗin, ga motoci nan na manyan en siyasa da en kasuwa da aka jere gwanin sha'awa.

Red carpet ce aka malala ta muka fito daga cikin motocin. Sojoji ne a tsaye suka jera cikin uniform suna saluting ɗinmu ta ko'ina. An shirya wurin sosai wanda ba ƙaramin ƙayatar damu ya yi ba. Hakan shi ya ƙara tabbatar mana da irin matsayi da kuma girman familyn SAMI da suke da shi a faɗin ƙasar.

A hankali muka shiga taka wa zuwa cikin Hall ɗin wanda ya tara mutane cinjim tamkar ba dare ba. Mamaki ne ya cika mana zuciya ganin irin girman wurin da kuma mutanen da aka tara kamar wata kasuwa.

Bayan mun zauna a wurin da aka tanadar mana na musamman Jaddi ya miƙe yazo ya riƙo Hannun Ya Mohaa suka tsaya akan stage da aka tanada domin yin magana ya fara magana cike da alfahari cikin harshen larabci da cewa.

"A matsayina na minister of foreign affairs...na haɗa wannan special dinner ce domin gabatar muku da Jikana MUHAMMAD ATTAHIRU ARAAM wanda ya kasance Jika na farko a gare ni wanda Rania ce ta haife shi. Ya dawo garemu bayan shafe tsawon shekaru ba tare da ya taɓa haɗuwa damu ba. Wannan abun alfahari ne da farin ciki wanda ya same mu, wannan dalilin ne yasa na gayyato ku na musamman domin ku tayamu murna. Shi ɗin ba ɓoyayyen mutum ba ne domin na san da yawa daga cikin ku kusan shi ko don hulɗar kasuwancin sa. Gashi a gabanku ina ƙara gabatar muku da shi cike da alfaharin kasancewarsa jininmu... "

Mayar da kallonsa ya yi wurin Ya Mohaa yana murmushi ya ce.

" Tonight...is your day Hammodi...Sudan is happy to have you back..waɗannan mutanen duk sun taru ne saboda kai..Ina so ka gaishe su kuma ka miƙa musu kalaman godiyarka"

Cikin jin wani irin yanayin farin ciki ya yi masa murmushi tare da jinjina kansa ya ce.

" Thank you Jaddi...Thank you all...haƙiƙa nima na yi farin cikin kasancewata a nan. Na kuma yi farin ciki da Allah yasa na kasance ɗaya daga cikin Ahlin SAMI Allah. Ina godiya sosai."

Hannayensa ya ɗaga sama yana jinjinawa alamar yana musu godiya sannan ya koma ya zauna.

Bayan ya kambala aka gabatar da manyan baƙi suka gabatar da bayanai. Daga nan aka dawo kiran dangin nasa ɗaya bayan ɗaya suka gabatar da jawabi na nuna zallar farin cikin da suke ciki dangane da zuwan sa.

Bayan an kambala aka shiga hidimar ci da sha komai gashi nan gwanin burgewa sai nishaɗi ake musamman mu da su Taimiyyah wacce kusan Ita da Suwara ne ke fassara mana duk abin ake gabatarwa wanda bamu san shi ba.

Bayan an kambala aka dawo sannan aka shiga bada tarihin sa da gwagwarmayarsa tun daga tasowar shi har zuwa karatunsa da kasuwancinsa wanda ni sai a yau ma nake ƙara sanin wasu abubuwan dangane da rayuwarsa.

Bayan an kambala Uncle Mu'aƙƙib ya kira Ya mohaa ya je ya tsaya a gabansa. Wani ne daga cikin baƙin ya taso ya karɓi microphone ya yi bayani sannan daga ƙarshe ya kalli Ya Mohaa ya ce.

"Danginka mutane ne masu matuƙar karamci da daraja, sun iya mu'amala da mutane yanda ya kamata kuma sun ji ma suna hidimtawa wannan ƙasa tamu wanda har da mahaifiyarka, domin bamu manta wa da ita ba kuma har abada ba zamu manta da ita ba domin ta kawo mana alkairai da dama a wannan ƙasa tamu. A yanzu...Kai ɗin ka kasance ɗaya daga cikinmu, saboda haka, mun naɗaka a matsayin Special International Cultural Ambassador Domin kawo haɗin kai a tsakanin ƙasashenmu guda biyu....In Sha Allah, za'a zartar da wannan gobe idan Allah ya kai mu."

Tafi Hall ɗin ya ɗauka ko'ina cike da farin ciki. Takowa ya yi yazo har inda nake zaune ya kama hannuna muka koma saman stage ɗin a hankali ya ce.

"Ni da Matata...dama sauran en uwana. Muna matuƙar godiya da wannan karamci da garin Sudan da kuma mutanen cikinsa da suka nuna mana. Haƙiƙa har abada ba zan taɓa manta wannan ba. A yanzu rayuwa ta ƙara koyar dani wani abu. Ba lallai saika san mutum tsayin shekaru ne za ka samu farin ciki ba...haɗuwa ta ɗan ƙanƙanin lokaci, idan har akwai kyakkyawar zuciya to tabbas ta wadatar. "

Haka aka kambala ƙayataccen taron cike da farin ciki kowa ya watse wanda har dare ya lila sosai ba tare da mun sani ba.

A jere motocinmu suke tafiya tare da juna har sai da muka kusa isa gida ne ya cewa drivern motar tamu ya dakata. A yanda nake kwance a ƙirjinsa ina nan a haka ban motsa ba, domin ban san dalilinsa na cewa a tsaya ba, wata ƙila akwai abin da yake so ya yi. Pressing waya kuwa da gaske naga yana yi da alama shi ne uzurin. Ƙara lumshe idanuwana na yi waɗanda ke cike da bacci na yi shiru ina mai ƙara gyara kwanciya ta a jikinsa.

Sai da suka miƙa sosai kusan 15mnt haka sannan muka ci gaba da tafiya a slow sosai wanda koda muka shiga gidan har kowa ya shige mahutarsa. Muna saukowa na ji ya riƙo hannuna ya ce.

"We are going to our room Bibi..."

Waro idanuwana na yi na kalle sa jin wata iriyar magana.

"Miye kike wani kallona haka kamar wanda ya kauce hanya?"

Still bance komai ba na bisa muka fara takawa. Sai da muka kusa shigewa na kalle sa na ce.

"To ai babu kayana ko ɗaya a nan. Bari na je na ɗauko."

Jinjina kansa ya yi alamar gamsuwa da maganata sannan ya ce.

"Do quick please, nasan kina jin bacci sosai."

Tun da na juya bai ɗauke kallon sa a kaina ba sai da na ɓacewa ganin sa. Har cikin xuciyata na yi niyyan ɗauko kayana na dawo kamar yanda ya ce. Sai dai kuma, ina shiga ɗakin tunanina ya canza, domin gabaɗayan su suna nan a zaune sun cika ɗakin tab yau hadda Khairum da wasu guda biyu. Duk da cewa ba'a nan za su kwanta ba na san cewa zaman fira suke. Kallona suka yi suna min sannu sannan Suwara ta ce.

"Aunty Beenafah sai yanzu?"

Wani irin wiƙi-wiƙi na ƙara yi da ido jin kalar tambayarta,ni duk sai ma naji na shige gashi.

Aunty Labiba ce da murmushi a fuskarta ta kalli Suwara sannan ta kalle ni ta ce.

"Suwara wannan wace iriyar kalar tambayace Mace da Mijinta?"

Dariya ta yi ta ce.

"Haka ne kuma Aunty Labiba. To a gafarce ni, kin san mu tuzurai sai muga kamar kowa haka yake kamar yanda muke, sai mu riƙa mantawa muna da bambanci da masu aure."

Dariya suka fashe da ita suna faɗin.

"To Allah ya aurar da ke."

Wuri na samu akan kyakkyawan gadona wanda bai cika faɗi sosai ba na zauna a gefe na yi shiruna ina sauraren firar su. Tunanin Dayaa ne ya tsaya cak a ƙwaƙwalwata, na san cewa yana can a tsaye yana jirana. Amma kuma sai dai ya yi haƙuri domin ba zan iya wai ɗaukar kaya na ce zan fita na je wurin sa ba. Ai abun da kunya na tsallakesu na ɗauko kaya da sunan zuwa ɗakin da mijina yake.

Muryar Hairi na ji bayan ta taso daga gadonta ta dawo nawa tana faɗin.

"Mummy dole daddy ya riƙe ki a hannunsa yau don wallahy ba ƙaramin wankuwa kika yi ba...kinga ko a hall ɗinnan yanda yake wani kallon ki yana rirriƙe ki kamar wanda akace za'a ƙwace masa ke. Duk wani motsinki ina gani fa akan idonsa, da kin yi zai ce Bibina lafiya. Kai...Wallahy soyayya ta yi a rayuwa."

Hannuna na kai da sauri na toshe mata baki ina mai ƙara zaro ido waje murya a ƙasa sosai na ce.

" Hairi kina cikin saitin ki kuwa? Ba kiga mutane ba?"

Miƙewa tayi tana dariya ta ce.

" To ai bani kaɗai ba...duk wanda yake wurin nan kowa ya lura da ku, shiyasa tun ɗazu muke firar ku."

Ya Allah! Abin da na furta kenan a raina tare da juyawa na kwanta ina mai basu baya domin ni dai ba zan iya da wannan kayan kunyar ba.

Ya Mohaa kuwa, tun yana tsaye yana jiran fitowar ta har sai da yakai ga jinginawa jikin bango yana ta baza ido yana zaman jiran gawon shanu. Mamaki ne fal a ransa ganin har yanzu daga zuwa ɗauko kaya ace bata dawo ba. Ga wayar ta a hannunsa kuma ballantana ya kira. Cikin Seconds ya kamo sabon layin Aunty Labiba ya kira wanda aka sayawa kowa a jiya domin amfani.

Tana ganin kiran ranta ya bata cewa Beenafah yake nema. Tana receiving bai ko tsaya ya ji maganarta ba ya ce.

"Ki bai wa Bibi waya.."

Kallon inda nake kwance ta yi ta ce.

"Mummyn Adeel ungo ga Daddy yana son Magana da ke."

Ƙara lafewa na yi ina mai yin baccin ƙarya kamar bana jinta, kiran duniya tayi min amma ban nuna alamun naji ba. Hakan yasa ta ce.

"Daddy ta fa yi bacci."

Katse kiran ya yi a hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe su kamar ya ɗauke wuta ya rarrafa ya shige building ɗin.

Toilet ya shige kai tsaye ya kunna shower ya sakarwa kansa ruwan sanyi tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ya yi wanka yayo alwala kamar ko yaushe ya zo ya tsayu amma bai tsayu da nisa ba kamar sauran darare ba ya kambala yaje ya Kwanta. Koda ya farka haka ya tashi kaca-kaca wanda dole ba shiri ya fara zuwa yayi wanka sannan ya shirya ya fi ce masallaci.

Ni kam koda na farka na yi lattin tashi sosai domin har sun gama haɗa abin kari duk tare da su Aunty Nadeeyah a kitchen wanda tun jiya muka ce yau damu za'a yi aikin tare da su Taimiyyah da sauran masu aikin su don muga yanda ake yi.

Sai yanzu na cire kayan jikina dana kwanta da su bayan na yi wanka. Ina gama shiryawa na fita na shige ɗakin Jadda.

Turus na yi na tsaya ganin Ya Mohaa a kwance, ya ɗora kansa akan ƙafar Jadda suna murmushi a tare yayin da naga laɓɓanta suna motsawa da alama akwai firar da take mishi.

Sallama na yi musu tare da zuwa gabanta na duƙa na gaisheta cike da ladabi.

Ƙara Faɗaɗa murmushinta ta yi sannan ta miƙo hannu ta shafi gefen kumatuna ta ce.

"Kin ɗebo gajiya daren jiya kam, shiyasa kika jima kina bacci. Da fatan kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau Alhamdulillah!"

"To masha Allah...Daman jira nake ki taso..."

Shigowar ɗaya daga cikin mai aikinta ce ta katse mata numfashi, bayan tayi sallama ta ce ana nemanta a waje. Kallona tayi tace in jira ta tana zuwa.

Lokaci ɗaya na ji gabaɗaya na nemi nutsuwata na rasa, domin Ya Mohaa Sam yaƙi ma ya kalli inda nake zaune ballantana nasan a irin yanayin da yake da ni. Na dai ga shi da Jadda suna dariya da juna to amma tun da yaji cewa na shigo ban ƙara ganin kyakkyawan annuri a fuskar tasa ba.

Cikin rashin kuzari daga inda nake zaune na ce.

"Daddy barka da safiya.."

Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe sannan ya miƙe zaune cikin nutsuwar nan tasa mai ƙara masa ƙwarjini ya ce.

"Zo nan Bibi.."

Tashi na yi jiki sanyaye naje kamar yanda yace. Janyoni ya yi ya zaunar dani akan cinyarsa yana kallon fuskata ya ce.

"Miyasa jiya kika barni Bibi? Kin san a irin mummunan yanayin da na kasance kuwa?"

Girgiza kaina na yi lokaci ɗaya naji hawaye sun ciko ido na na ce.

"Ka yi haƙuri...koda naje ɗakin kowa yana ciki kuma ni ban san yanda zan iya ɗauko kayana ba suna kallona.."

Tun da na fara maganar yake kallon laɓɓan bakina har na dasa aya. Wato duk mai auren yarinya dai ya shiga uku dole ya yi haƙuri da ƙurciyarta da kuma wautar ta. Domin ita a nata tunanin komai tayi daidai ne,Idan ba shi ba, ke da kike matar aure ina ruwanki da cewa wai za'a kalle ki don za ki je gun mijin ki.

Jinjina kansa ya yi yana mai yin murmushi kawai ya ce.

"Shi ke nan, na haƙura."

Hannuna ya kama yana mai bin jan ƙunshin da ke yatsuna da kallo ya ce.

"Ya yi kyau sosai...kin ci abinci?"

Girgiza kai na yi na ce.

"A'a. Ai yanzu na fito.."

Aunty Nadeeyah ce ta fara shigowa da sunan kirana muci abinci amma ba shiri ta koma tana faɗin "afwan" Duk wanda ya shigo sai dai ya Juya ya koma amma shi sam ya ƙi ya sauke ni daga kan ƙafarsa, hankalinsa kwance kamar wanda yake cikin gidansa shi kaɗai.

"Bibi.."

"na'am"

Na amsa masa ina mai ƙure kyakkyawar fuskar sa da kallo.

"Idan har na nemi ki kasance tare dani, please ki tsaya kada ki sake barina ni ɗaya, Idan dai ba so kike wani mummunan abu ya faru dani ba...Miji kike da shi ba saurayi ba. Ki daina damuwa da mutane ki fara damuwa da mijin ki"

Da sauri na jinjina masa kai na ba tare da na fahimci inda maganar tasa ta dosa ba na ce.

"In Sha Allahu ba zan sake ba. Ka yi haƙuri..."

Aunty Labiba ya kira yace tasa a kawo mana abincin a nan dani dashi zamu ci. Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba aka kawo mana tangamemen trayn abinci muka zauna a ƙasa muka ci. Bayan mun kambala ne Jadda ta dawo ɗakin ɗauke da wasu gwala-gwalai a hannunta da wasu kayan al'adarsu na alfarma ta miƙamin tace na je su Suwara su tayani shiryawa shima Ya Mohaa ya je ya shirya.

A bakin gangar shiga parlour na tarar da Suwara Ita da Ya Emraan suna tsaye suna magana wanda alamu ya nuna dukkan su suna cikin nishaɗi ne. Wani mamakin ne ya ƙara sarƙafe mini zuciya ganin yanda suka tsaya kusa da kusa sosai tamkar za su shige cikin juna.

Saukar da idona na yi ba tare da nace komai ba na kama hanya na shige ciki a raina ina tambayar kaina cewa 'kenan soyayya suke ko me?' lokaci ɗaya Aunty Ziza ta zo mini a raina, tuna irin wutar kishin Mijinta da ke balbala a cikin jini da ɓargon jikinta kamar yanda naji su Munira suna faɗa. A yanda suke faɗamin yanda take kishi har suna bani misalai da tsananin kishi tabbas idan har Ya Emraan ta tabbata son Suwara yake akwai gagarumar matsala. Ni ɗin nan ta nuna tsantsar kishin ta a kaina ni da ba kowa ba,ina ga Suwara Babbar Mace er kasuwa, mai tarin ilmi na zamani dana addini, a labarinta da ta bamu ita ɗin jagora ce a cikin gwamnatin kakanta mai babban matsayi, sannan tana da kasuwanci na musamman kuma tana da muƙami a SUQ RANIA mai zaman kansa...Uwa uba gata kyakkyawace ajin farko. Hmm! Lallai akwai case kuwa.

Tunanina ya yanke ganin Hairi ta fito cikin kyakkyawar shiga tasha uwayen gwala-gwalai tayi kyau sosai. Jinjina kai na yi ganin su Aunty Nadeeyah su ma sun shirya kowa cikin kalar laffayarsa mai kyau sosai.

"Mummyn Adeel wai baki shirya ba?"

Cewar Aunty Nadeeyah tana mai kusanto inda nake tsaye.

Jinjina kai na nayi alamar eh, sannan na ce.

"Yau kuma ina muka nufa da safen nan Aunty Nadeeyah? An faɗa muku inda zamu tafi yau?"

Baki ta sake tana min wani kallon mamakin ta ce.

"Wai dan Allah ban ce ki daina kirana da Aunty ba? Daddy fa ba zai ji daɗi ba, dan Allah ki daina."

Dariya na yi na ce.

"Ni wallahy na riga na saba amma ki yi haƙuri Maman Dija."

"To shi ke nan. Kasuwa aka ce zamu tafi daga nan mu shiga gari. Kasuwar da Mama ta kafa (Cewa da Mahaifiyar Ya Mohaa Suq Rania)"

Cike da zumuɗi na ce.

"Gaskiya I'm excited...yanda ake ta bamu labarin kasuwar nan idan muka je nasan ba ƙaramin burgemu za ta yi ba."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull