Ganin ido complete - Chapter 51
Ganin ido complete Chapter 51: Ganin ido complete Chapter 51. Taimiyyah ce ta shigo a shirye ta kama mini na shirya ta ƙara gyaramin gashin kaina sannan…
3,372 words
Taimiyyah ce ta shigo a shirye ta kama mini na shirya ta ƙara gyaramin gashin kaina sannan muka fito a tare cike da farin ciki muna tafe muna nishaɗi har bakin mota.
Kallon Dayaa na yi wanda yake shirye cikin shigar jalabiya fara irin tasu yasha rawani fari ya yi kyau sosai. Kamar yanda nake kallon shi ina murmushi haka naga Suwara tana kallon Ya Emraan dake cikin shiga irin ta ɗan uwansa tana masa murmushi itama tana jinjina kanta. Yatsar ta babba ta hannuna dama ta ɗaga masa tayi masa thumb up alamar ya yi kyau sosai. Kallonta su Aunty Labiba naga sun yi suna murmushi kamar yanda nake yi nima wanda ban sani ba ko sun fahimci abinda na gani ko kuwa ni ce dai nake shirme na.
A tare muka shiga motocin wanda hannuna na cikin nasa har muka isa babbar ƙofar kasuwar. Masu kiɗi da bushe-bushe muka tarar na al'ada suna ta aikin su, yayin da wurin yayi cinjim da mutane Manya, yara da ƙanana suna ta mana maraba.
Jami'an tsaron da ke wurin ne suka kewayemu suka sanya mu a tsakiya yayin da wasu mutane guda biyu da aka turo daga Office ɗin ministan kasuwanci na ƙasar suka shiga gabanmu domin kasancewa a tare damu mu kuma muna binsu a baya. Hannaye kawai muke ɗaga musu alamar mun amsa gaisuwa muma muna miƙa tamu gaisuwar zuwa gare su kamar yanda Jadda ta ce muyi wanda wannan shi ne yaren da suke amfani dashi, domin ba za su iya game kowa a kasuwar su gaisa da shi ba.
SUQ RANIA (THE WOMEN'S HEART OF OUMDURMAN)
Abin da aka rubuta da kenan da yaren larabci da kuma turanci a saman babbar ƙofar shiga Kasuwar.
Kallon Dayaa na yi wanda fuskarsa ta cika ta da murmushi da alama yanayin ya yi masa daɗi sosai a rai nima ina murmushin na ce.
"Dayaa...it's seem like the whole city breaths her name a wannan kasuwar.."
Jinjina kansa ya yi yana mai ƙara Faɗaɗa murmushinsa baki har kunne yana kallona ya ce.
"She became the air of this Land Bibi..wanda har abadan abada ba za'a taɓa iya shafe tarihin ta ba har sai idan an wayi gari ba kowa a ƙasar Sudan ɗin nan gabaɗaya...every breath they take here...whispers her story."
Takawa muka yi muka shiga kasuwar mai cike da ɗimbin tarihi wacce ta tara jama'a daban-daban na ƙasashen duniya masu kasuwanci bayan mutanen cikinta.
Yanayin Kasuwar ya kasance tamkar wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar gari ne mai zaman kansa. An tsara ta cikin tsarin zamani amma dai tana nan a sifar ta tun wanda aka kafata da shi.
Wasu manyan benaye ne muka tsaya ta gabansu wanda suka saka billboard na dindindin mai hotonta da kuma sunanta. shagu na ne kawai na kayan ado da kwalliya na mata da yara ƙanana a bene na ɗaya. Bene na biyu kuma, cibiyar horar da matasa mata ce a harakar kasuwanci, ƙirƙirar kaya da sana'o'in hannu. Sai bene na uku wanda ke ɗauke da Office ɗin Rania foundation inda ake bayar da tallafi da shawarwari ga 'ƴan kasuwa mata domin dogaro da kai.
Wasu dattijai ne mata guda biyu suka ƙaraso suka gaishe da Jadda sannan suka tsaya a gaban ya Mohaa suna faɗin.
"Allah ya ji ƙan mahaifiyarka ya gafarta mata, Haƙiƙa ta kasance mace mafi daraja da girma wacce ta kawo mana ci gaba da sauye-sauye a cikin rayuwarmu da ma ta 'ƴa' ƴanmu mata baki ɗaya. Allah ya albarkace ka. Allah ya shirya maka zuri'a yasa ka gama da duniya lafiya da kai ahlin ka gabaɗaya."
Wani ɗan ƙaramin kwano wata daga cikinsu ta ɗauko ta miƙa masa, fuskarta cike da murmushi ta ce.
" Kasha wannan madarar daga hannuna Hammodi...Rania ita ɗin ta koyar dani dabarun kasuwanci da hannayen ta da kuma dukiyarta...ita ce wacce ta koyar damu cewa, kasuwanci ba abokin gaba ba ne shi ne abokin rayuwa. Duk wacce ke son ta rayu cikin farin ciki to ta koyi kasuwanci domin ta taimaki kanta da Iyalinta."
Karɓar kwanon ya yi ya kafa a bakinsa ba tare da nuna ƙyama ko tsantseni ba ya sha sannan ya miƙa min nima na karɓa na sha.
Kallon su ya yi yana mai jin wani iri a ransa ya kalle ni yana jinjina kansa ya ce.
" Ita ɗin mata ta ce, suruka ce a gare ku..waɗannan kuma ƙannai na ne."
Wasu irin hawaye ne na ji sun cicciko idona, tabbas a duk lokacin da ya furta wannan kalmar da baya shayin faɗinta ko a gaban kowa yake ta cewa 'Ita ɗin matata ce' tana sanyaya min zuciya na ji na ƙara zurfafa da jinsa sosai a cikin raina.
Hannayenmu muka ɗaga sama alamar jinjina a gare su sannan yayi musu godiya da kuma basu tallafin kuɗaɗe domin ƙara jarin kasuwancin su da kuma kashe wasu matsolalin su na rayuwa.
Haka muka shiga zagaya kasuwar kowane lungu da saƙo sannan daga ƙarshe muka dawo Office ɗin shugaban kasuwar mai ci a yanzu wanda wani ƙanin Jaddi ne a wurin da sauran danginsu.
Manyan hotunan ta ne aka kakkafe har da na Mahaifinsa Alhaji Attahiru da ma sauran waɗanda suka cancanta ace akwai hoton su a wurin.
Bayan mun gaisa ne wani daga cikin office ɗin ya shiga nuna mana abubuwan tarihinta na gwagwarmayarta dake office ɗin wanda a ciki har da litattafan da ta rubuta da Kanta ta wallafa guda uku wanda na ɗaya shi ne; The journey of a market woman, na biyu kuma;women and wealth in Africa, sai na uku kuma; A letter to a young Lady.
Hannu muka miƙa kowa ya amshi copy yana dubawa wanda ni da Ya Mohaa ne muka buɗe letter to a young Lady muka fara dubawa.
Murmushi ya yi ganin babu komai a ciki sai tarin baiwa, hanyoyi da kuma dabarun kasuwanci ga yara matasa mata. Yatsan shi ya ɗora akan wani muhimmin sentence da ta ce.
"Dear Young Lady...never be afraid of carrying your dreams everywhere you go around the world.."
Idanunsa ne naga sun cika da hawaye. A hankali Ya rufe littafin ya rungume sa a ƙirjinsa ya kalle ni yace.
"Her dreams did not dies Bibi...it lives here....in every smile, in every woman selling her hope. Duba Ki gani, kamar yau ne ta rubuta wannan littafin.."
Jinjina kai na nayi cike da ƙwarin gwiwa na ce.
"Ita ɗin jarumar Uwa ce, domin ta bar baya mai kyau. Kowa a kasuwar nan da ma mutanen gari kowa sai faɗin alherinta yake. Yeah! She built a home for every woman..."
Hannuna ya jimƙe a nasa sosai ya ce.
"And now...it's my turn to keep it alive. In Sha Allahu abubuwa za su ƙara sauyawa da sabon ci gaba."
"Allah ya taimaka ya dafa maka ya kuma sanya albarka ga duk abunda ka sanya wa gaba amin."
Bayan mun kambala a nan muka yi sallar Zuhr sannan suka yi ta gabatar mana da kyaututtukan abun da suke siyarwa da yawa, daga ƙarshe muka yi sallama muka wuce Old Oumdurman Heritage Quarters inda manyan gidaje na tarihi suke.
Muna nan muna ta ɗaukar hotuna ana ci gaba da bamu tarihin wurin Sai ga Jaddi ya iso. Murmushi ya yi mana ya ce.
"Kun ganni shiru sai yanzu ko? Ina can ina ji da wasu baƙi da nayi sai yanzu na samu na lallaɓa suka tafi....kunga gidan tarihin gwagwarmaya mazan jiya?"
Dariya muka yi muna jinjina kai kowa na yabawa da abin da ya burgesa a wurin sannan Hairi ta ce.
"To ni ya zan yi na zama Jaruma kamar Mama Rania da ma sauran mata Jaddi?"
Dariya ya yi yana kallonta ya ce.
"Abin ba mai wahala ba ne Hairiyya. Kawai daga zuciya ne, ki saka a ranki cewa za ki yi aiki tuƙuru domin cika wani mafarki na ki, sai ki saka aikin a gaba ki kuma riƙe Allah, da taimakon en uwan ki da mijinki ko iyayen ki tabbas za ki zamo kamar su watarana."
Kallonta Ya Mohaa ya yi ya ce.
" ki kasance komai kike so iyaka ki ganshi a gabanki, abinci, sutura, karatu da kuma kayayyakin more rayuwa....anya za ki iya kuwa favorites...duk fa wanda kika gani a wani matsayi duniya ba haka kawai ya same shi ba, sai da yayi aiki tuƙuru.."
Hannun shi ta riƙe cike da sangarta ta ce.
" Dan Allah Daddy ka goya min baya, wallahi yau an zubarar da tunani dangane da rayuwa, da gaske nake ina so in fara kasuwanci...and I want become like them."
" To shi kenan. Bari mu nutsu sai muga abin da ya kamata."
Bayan mun gama kewaya wurin muka ranƙaya zuwa bakin ruwan teku masu gudana gwanin sha'awa.
Murmushi na yi yayin da kowa ke tofa albarkacin bakin sa na kalli Jadda na ce.
" Yanzu na ƙara fahimtar dalilin da yasa kika ce Mama tana ƙaunar bakin ruwan nan a lokacin da take raye. Wuri ne mai cike da sanyi da sanya nutsuwa, babu hayaniya ba komai sai tarin ni'imomi..."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
"Ta kan zo nan a duk lokacin da take bincike akan wani abu, ko kuma ta ke shirya wani abun. Ta kan zo nan ta zauna ta yi ta rubuce-rubuce wanda Kakanku shi ne ya zamto babban abokinta kuma amininta a wannan lokacin. Domin duk abin ta kawo zai duba shi cikin hikima da basira wanda koda ya kasance abin da ta kawo bai yi ba...cikin lallami da fahimta yake cire abun daga rayuwarta...."
Mun jima ko a bakin ruwan muna shan labarurruka sannan daga ƙarshe muka wuce wani babban masallaci muka yi Asr da magrib sannan muka wuce wani gidan cin abinci na musamman. Bayan mun kambala muka shiga garin inda muka yi ta yaba kyawun garin musamman da ya kasance akwai fitilu masu kyau waɗanda suka ƙarawa garin ƙwarjini da kyawun kallo.
Wannan rana ta yau ta shiga cikin tarihin kowane ɗaya daga cikinmu domin mun samu ilimi, nishaɗi da kuma ƙarin sanin daraja da girman gwagwarmayar Mace. Ba dole sai ka fara da mai yawa ba, kaɗan idan Allah yasa albarka ya isheka mabuɗin rayuwa domin mai ƙarami shi ke da Babba watarana.
Muna isa gidan bayan mun fito mota ya damƙe hannuna sannan naga ya kira Aunty Labiba.
Cike da ladabi ta zo ta tsaya a gaban shi ta ce.
"Gani Daddy..."
Jinjina kansa ya yi in a calm voice ya ce.
"Je ki kawo mata kayan ta....duk abin da kika san na ta ne ki haɗo mata. Wannan building ɗin na gefen dama a nan za ki kawo."
"OK."
Juyawa ta yi ta wuce ciki ta tattaro kayana wanda su dai su Nadeeyah kawai Sun zura ido suna kallon ikon Allah har ta kambala ta fi ce.
Har ta shigo ta ajiye kayan na kasa ɗago idanuna na kalle ta. A hankali tayi mana sai da safe sannan ta sa kai ta wuce.
Kayan jikin sa ya rage sannan ya shige banɗakin ya yo wanka ya yo alwala ya fito. Ganin ina nan inda nake na kasa yin wata huɓɓasa ya kalle ni yace.
"Ki je kiyi wanka...Akwai gajiya sosai."
Cire kayan jikina na yi na ɗaura towel, ba tare da kawo komai a raina ba na wuce kai tsaye na yo wankan sannan na zo nayi sallar Isha da muka ɗauko nauyin ta. Bayan na kambala na buɗe kayana inda nan na tarar har da sabbin turarukan jiki da wasu mata suka kawo mana jiya ta haɗa ta kawo min.
Kayan nawa na shiga dubawa ina neman kayan baccin da zan saka. Ƙirjina ne ya buga ganin irin lalataccin kayan da ya sako min. Idan ban manta ba shi ne wanda ya zaɓomin komai na sakawa ya Shirya mini box ɗina, Kuma tun da muka zo ni ban nemi kayan bacci ba domin a gajiye nake kwantawa kuma ta wani fannin ina jin kunya sosai wanda har bana Iya sake wa da yawa....Lallai Ya Mohaan nan sai yau na ƙara tabbatarwa da cewa ɗan garari ne! to yanzu sabi da Allah muda muka zo ziyara mi zan yi da wannan kayan? Muryarshi na ji a bayana yana faɗin.
"Har yanzu ba ki gama shiryawa ba ne Bibi?"
Waigowa na yi tare da yin narai-narai da ido a darare na ce.
"To ai ni banga kayan sakawa a nan ba.."
Takowa ya yi zuwa gaban kayan ya tsaya ya ɗauko min wata ficiciyar riga mai hannun vex wadda bata da mara ba da tsirara ya ce.
"Ga wannan.."
Ai tuni na ƙarasa ruɗewa na ce.
"Wannan ɗin fa kalli yanda take..."
Ido a ƙanƙance ya ce.
"Na gani.."
"Dayaa ba fa gidanmu ba ne.."
Rigar ya ƙara miƙa hannu ya ɗauko kai tsaye ya zura ta a wuyana yana faɗin.
"Waya ya faɗa miki ba gidanmu ba ne Bibi? Ba ki ga wannan building ɗin mu kaɗai ne a cikin sa ba kacokam. Nan ɗin shima gidanmu ne kada ki sake cewa ba gidanmu ba ne..."
Yana gama maganar ya zare towel ɗin nawa ya barni daga ni sai wannan ficiciyar rigar wacce ta sa na ji duk na koma wata iri daban.
Ni fa gabaɗaya ma wallahy a rikice nake da yanayin sa na yau domin nasan ban isa na hana masa kaina a irin yanda naga wutar fitina na wani irin tururi a ƙwayar idanunsa ba.
"Bibi..."
Ya yi whispering sunana cikin wani irin yanayin da sai da na ji tsikar jikina ta ɗaga.
"Shin ba ki ji ko kaɗan cewa kin yi kewata ba? Na kasa bacci, na kasa yin wani kataɓus...kewar ki kawai ke ɗawainiya dani Bibi...a yanzu bana jin ina iya ɗaukar kwana biyu ba tare da kina gefena ba idan zan yi bacci."
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya shiga birkitani tare da haɗe bakinmu wuri ɗaya ya shiga aika min da zafafan saƙunan da suka gaskata maganar sa da ya gama ta cewar yana matuƙar jin kewata.
Jin ƙafafunmu sun kasa riƙe nauyinmu muna neman faɗuwa yasa ya jani muka faɗa kan gadon muka Lula wata duniyar da muka kwana biyu bamu leƙa ba, musamman shi da ya ji kamar yau ne ya fara sani na. Duk yanda na so in nuna juriya a wannan karon na kasa, domin ba ƙaramar wuya na sha ba wacce ta saka ni dole na fashe masa da kuka. Bayan ya gama da ƙyar ya yi nasarar rungumeni a ƙirjinsa da rarrashi da komai ya samu bacci ya kwasheni sannan ya samu ya rarrafa yaje yayi wanka.
Da wani irin mugun zazzaɓi na farka wanda a yan da nake ji ko kaina ba zan iya ɗagawa ba. Hakan yasa na fashe masa da kuka wanda ba shiri ya bar abin da yake yayo kai na.
Cike da takaici na shiga tambayar kaina wannan wane irin ƙalafuci ne? A garin mutane na wuni ina zirga-zirga amma ya kasa ɗaga mini ƙafa. Koya a jiya ya tabbatar cewa lafiyata ƙalau, to amma yau ta ya ya zan iya fuskantarsu bayan na kwana tare da shi da sunan rashin lafiya.
"Bibi..."
Cikin rashin kuzari na ture hannun sa cikin kukan na ce.
"Ni wallahy ka ƙyaleni..."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 45*
Murmushi kawai ya yi tare da amfani da ƙarfinsa ya riƙe hannayena sannan ya janyoni jikin sa yana mai bani warm hug. Laɓɓansa ya kai saitin kunnena cikin sigar lallashi ya shiga furtamin wasu kalamai masu daɗi da taushin da ban san lokacin da na haɗiye sauran kuka na ba na kwanta laƙwas a jikin sa ina saurarensa har ya yi nasarar lallameni na manta da laifinda ya mini wanda har yasa bana jin haushinsa sai dai yanayin jikina ina jin ba daɗi akan zazzaɓin da nake ji.
Miƙewa ya yi a hakanli ya ɗagoni muka wuce toilet ya barni nan nayi wanka na gasa jikina da kyau sannan na yi alwala na fito. Ina sallah na ji ana ƙwanƙwasa babbar ƙofar shigowa gidan gabaɗaya. Jallabiya ya zura ya tashi ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo hannayensa ɗauke da abincin kari.
Bayan na kambala sallar ya miƙomin alƙurni na karɓa na buɗe na karanta cikakkun shafuka biyu sannan na rufe na je na ajiye masa.
Sai da na gama shiryawa cikin doguwar riga da gyalenta na saka hula bayan na gama ɗaure gashin kaina, sannan na tsaya jikin mirror na ƙura ido ina kallon sa. Wannan mijin nawa a yanzu ya ƙware a tafiya dani, shi ne zai takalo fushina da kansa kuma daga ƙarshe shi ne wanda zai rarrasheni yasa na manta da duk wani ɓacin ran da yake zuciyata. Son sa nake...tabbas ina son sa sosai wanda duk abin da nake ji daga zaran na gansa nutsuwata ma nemanta nake na rasa.
Na jima ina kallon sa wanda shi sam bai ma lura dani ba akan yanda ya duƙufa yana aikin da na san baya rasa nasaba da kamfaninsa na Golden pathways Wanda kullum cikin aiki yake ba dare ba rana.
Da murmushina da kullewar idanunsa cikin nawa lokaci ɗaya ya kasance. Ai ba shiri na saukar da kaina a ƙasa cike da kunya ina neman yanda zan kare kaina idan ma ya tuhumeni da laifin kallonsa ina murmushi.
Kamar kuwa na sani. Rufe system ɗin ya yi ya ture duk wasu kayan aikinda suke gabansa ya taso ya zo gabana ya tsaya tare da riƙa gefen veil ɗina yana leƙa fuskata yana murmushi ya ce.
"Masha Allah...daga ganin wannan kallon da kike min kina murmushi na san cewa an yafe min laifin da na yi ko Bibina?"
Shiru nayi tare ƙara saukarda idona ƙasa sosai ina wasa da yatsun hannuna lokaci ɗaya ina jin wani abu yana mini yawo a ƙirjina.
"Mu je muci abinci?"
Ya ambata cikin sigar tambaya. Jinjina masa kaina na yi sannan na taka muka je muka zauna. Kaɗan na ci abincin domin har yanzu bana jin daɗi ina jin zazzaɓi. Kamar yasan abin da nake tunani domin magani na ga ya ɗauko ya bani, karɓa na yi na sha sannan na kwanta a jikin sa na lumshe idanuna kamar mai bacci.
Bayan ya kambala cin abincin ya tattara kayan ya kira Jadda sai gashi ta turo Taimiyyah ta tsaya can daga parlour ya bata kayan sannan ya rufe ƙofar ya dawo.
Wayata ya ɗauko ya miƙomin yana faɗin na kira Ammie domin ta kira bana kusa. Ina karɓa na kirata tare da yi mata sallama sannan na gaisheta. Duk yanda na yi iya yina wurin ganin na sai ta kaina sai da Ammie ta tambayeni cewa mi yake damuna. Murmushi na yi kai tsaye na ce.
"Ammie yau na tashi bana jin daɗi ne, amma dai na sha magani, jikin ma ya sauka."
Cikin nuna kulawa daga can ɓangarenta ta ce.
"Kin tabbata?"
"In Sha Allahu Ammie. Ina su Mummy Sameera? Na ji duk wurin ya cika da surutu, ina kike haka?"
"Wallahy kin ganmu nan ana ta shiri wai Kebbi zamu je Huda ta haihu..."
Murmushi na yi na ce.
"Allah sarki! Aunty Huda ta gidan Mama Asma'u ko?"
"Ita fa. Ta haihu ta samu ɗan ta namiji kwana biyar da suka wuce."
"Allah sarki! Allah ya raya ya bata lafiya. Duk da su Mama da su Mummy Sameera za ku je?"
"A a. Kin san haihuwa ta uku ce yanzu ta yi, to shi ne Abbun ku yace ta shirya tun da haihuwa ta uku ce ba wani abu ba ne don taje ai za ta ji daɗi idan taga mahaifiyarta a kusa da ita. Shi ne fa ta rantse ta ce ba inda za ta je ai tun da ni gani yanzu ina nan ni ce uwar ta, saboda haka sai dai in je ita ba za ta je ba..."
Cikin jin farin cikin cewa yanzu Ammie na tana zaune cikin jin daɗi da walwala ba kamar can baya ba yasa na yi murmushin da har tana iya jiyo sautina don in ƙara tabbatarwa da kunnena na ce.
" Lafiya ƙalau kike zaune ko Ammie na?"
Jinjina kai ta yi tamkar ina a gabanta ta ce.
"Alhamdulillah Beenafah! Lafiya ƙalau nake zaune da Dr., matarsa, yaransa da kuma danginsa. Kowa lafiya ƙalau muke zaune dasu. Hajiya Asma'u ta mutuntani wanda babu abin da zance sai dai Allah ya ƙara mana hak'uri."