Ganin ido complete - Chapter 57
Ganin ido complete Chapter 57: Ganin ido complete Chapter 57. Washe gari muna ɗaki ina zaɓa mana kaya wanda a wannan karon ni na ce zan haɗa kayan tafiyar…
3,371 words
Washe gari muna ɗaki ina zaɓa mana kaya wanda a wannan karon ni na ce zan haɗa kayan tafiyar kawai ya zauna ya yi kallo. Ina cikin aikin yana zaune shima yana aikin da ya saba aka kira shi akace mun yi baƙi.
Da mamaki muka fito domin ganin su waye waɗannan. Jadda, Suhaib da kuma Taimiyya, su ne muka gani.
Cikin tsananin farin ciki na je da gudu na rungume Jadda ina mata sannu da zuwa, bayan mun gama gaisawa ne, na tashi na je Kitchen wurin Madam Amima na sa suka shirya musu abinci nan take na ji da gani sannan na shiga ciki tare da Taimiyya domin na basu wuri su gana naga kamar Jadda na buƙatar hakan.
Bai gama farfaɗowa da mamakin ganinta ba ta kalle shi tana murmushi ta ce.
"Beenafah mutuniyar kirki ce Hammodi! Ina alfahari da ita."
Murmushi ya yi tare da jinjina kansa ya ce.
"Haka take. Ba ta da matsala."
"Na gani. Kuma In Sha Allahu za su zauna lafiya da Noura..."
Cikin zallar mamaki ya kalle ta ya ce.
"Jadda! Ina tunanin ai an kai ƙarshen wannan maganar domin ita kanta ba ta da ra'ayi."
"Waye ya faɗa maka?"
"Jadda ita fa yanzu tana da right ɗin zaɓarwa kanta miji. Dan Allah kada ku tilasta ta..."
"Hammodi...Noura har yanzu ita ɗin yarinya ce. Tana da ikon zaɓarwa kanta miji na yarda da wannan, to amma idan iyayenta suka ga wani zaɓin da ya dace da rayuwarta shi ma ɗin ba laifi ba ne. Da farko ta yi kuskure...shi ne ma abun da ya taso na ji ba zan iya jira har sai ka zo ba, na zo da kai na. Saboda haka a yanzu ita da iyayenta sun amince muma haka..."
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Abin da ya furta kenan a ransa yana mai jin duniyar na wani irin kewayawa da shi, tamkar zai kifa haka yake ji. Jin alamun kamar tahowar ta yasa ya yi saurin ɗaga mata Hannu ya ce.
" Dan Allah Jadda mu bar wannan maganar a yanzu. Beenafah bata san da wannan zancen ba har yanzu.."
"To ka faɗa mata mana! Idan kuma ba za ka iya ba ni sai na faɗa mata...kana ji ko? Gwanda ka sanar mata tun wuri domin ka sauke wannan nauyin a kanka, kada sai lokaci ya ƙure taga cewar kamar ba'a yi mata adalci ba."
Da sauri ya girgiza kansa ya ce.
"A a dan Allah! Ki bari I will find the right time ɗinda ya kamata na faɗa mata idan ma akwai buƙatar haka."
Ƙara kwantar da murya ta yi ta ce.
"Hammodi,... Za ka ɗauki duk wannan a matsayin takurawa, amma watarana sai ka gode mini In Sha Allahu. Su a yanzu sun riga sun amsa, kai ne ake jira daga ɓangarenka..."
"Idan na amsa na ce sai nan gaba....shin za ku iya jira?"
Cikin farin ciki ta ce.
"Nan gaba? Kamar yaushe kenan?"
Girgiza kansa ya yi kai tsaye ya ce.
"Ban sani ba, amma dai idan na gama yankewa zan sanar."
"To ba laifi...amma dai kamar zai fi idan akayi Lokaci ɗaya. Sannan ko akan Beenafah da Noura ina ga gwanda a yi tun yanzu domin a samu su haɗe kansu komai ya tafi daidai,hakan zai yi matuƙar faranta maka ranka.kaga ga auren Su Suwara...ana ma iya yin sa lokaci ɗaya.."
"Uhm! Nan da wata uku? Hakan ba zai samu ba Jadda, magana ta gaskiya. Bana son na ɗauki alƙawarin da ba zan iya cikawa ba, amma ba zan aure ta nan da wata uku ba, ba zan yi alƙawarin wannan ba."
Shiru tayi tana kallon sa na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Haba Hammodi!! Shin idan aka haɗa auren nan lokaci ɗaya bai fi ba? Kaga za'a sauƙaƙawa mutane wahala, sannan Kaga a lokacin kowa yana nan, amma idan akayi auren su Suhaib ba lallai wasu su dawo daga baya ba domin mun jima bamu aurar ba. Dan Allah ka bari ayi shi lokaci ɗaya komai sai yafi tafiya daidai..."
Cikin jin wani dan irin ɗaci a ransa ya girgiza kai tamkar zai fashe da kuka Ya ce.
"Jadda zan yi nazari a kai.."
"A'a, ba fa wani nazarin da za ka tsaya yi Hammodi, ka je kawai ka fara shiri. Allah ya sanya alheri da albarka yasa ace gwamma da akayi.."
Daƙyar ya yi nasarar jinjina mata kansa amma wallahy ba don yasan abin da yake masa daɗi ba. Babu abinda yake masa yawo a kai da zuciyar sa sai maganganunsa da Engineer Ubaid. Shawararsa da ya bi babu abin da ta ƙara masa sai cakwakiya.
Shiru ya yi tare da zuba ido yana kallonta yana mamaki da irin yanda take ta wani farin ciki kamar ba ita ba. Tunaninsa da damuwar sa miyasa za ta dage akan dole sai ya Auri Noura a irin wannan lokacin alhali matarsa bata ragesa da komai ba. An ya akwai adalci kuwa? Idan Beenafah ta zo tasan wannan bi ta da ƙullin da suke mata mi zai faru daga baya? Shi fa farin cikin matar sa yafiye masa komai a duniyar nan.
Bayan sun gama tattaunawa ya kirani na fito ina murmushi na miƙa mata waya na ce.
"Jadda ga Ammie na za ta miki barka da zuwa."
Karɓa ta yi suka gaisa wanda a nan ne nake jin cewa wai gobe za ta koma. Suna kambalawa na karyarda wuya ina kallonta na ce.
"Ni dai gaskiya ba za ki tafi gobe ba.."
Dariya ta yi ta ce.
"Haba Beenafah! Kwana ɗaya ai dai mun ga juna, uzuri ne dama ya kawo ni kuma na kambala, sannan gashi kuma gobe zaku tafi..."
"To ai ko yanzu akwai kwana biyar kafin fara aikin nasa, kawai dai muna so mu isa da wuri ne.."
"Beenaf..!"
Hannu na ɗaga ina dariya na ce.
"Jadda bafa zan yarda ba sai kin mana kwana biyu. Na gama magana, indan akan tsohon mijin ki kike son ki tafi ki bari ni zan kira sa na lallasar masa zuciyar sa....ta shi mu shiga ciki."
Na ƙarashe maganar ina mai riƙe ta hannun ta muka tashi a tare. Kallon sa na yi tare da yi masa magana da ido alamar miye ya faru da ya ke ta kallona haka? Murmushi ya yi tare da lumshe idanunsa a hankali ya buɗe yana mai girgiza mini kansa alamar ba komai.
Haka muka yi kwana biyu cike da farin ciki, duk abin da take so dama wanda bata ce ba jiki na rawa nake yi mata shi har muka rabu cike da kewa ina mai yi mata lissafin watannin da suka rage na sake dawowa Sudan.
Bayan sun tafi washe gari muka shirya sai Kaduna. Tun da muka sauka kwana ɗaya muka yi ya fara aikinda ya kai sa ba dare ba rana wanda sai da muka yi sati uku cikin na huɗu sannan ya kambala muka yi shirin wucewa Sokoto.
Muna zaune a daren da washe gari zamu tafi Sokoto muna cin abincin dare sai ga kiran Ammie. Ina ɗagawa lokaci ɗaya ƙirjina ya buga jin muryar Bahrain cikin wani irin yanayin da ko bai furta ba nasan akwai wata damuwa. Cikin gigita na yasar da spoon ɗin hannuna na ce.
"Bahrain! Ina Ammie.?lafiya? Miye ya faru da ita?"
Kukan da yake riƙewa ne ya kubce masa yana faɗin.
"Aunty Beena...Daddy...Daddyn gidansu Humaida ya rasu.."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Na faɗa a gigice tare da miƙewa tsaye na ɗora hannuna a kai ina mai fashewa da kuka...
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 48*
Ƙarar faɗowar spoon ɗin hannunsa ne na ji ta karaɗe kunnuwana, da gudu ya yo kaina ya tallafoni wanda kaɗan ne ya rage ban kai ƙasa ba, tsabar yanda maganar ta shiga kaina a lokacin da ban tsammata ba.
Janyoni ya yi zuwa cikin jikinsa tare da saka hannayensa ya rungumeni yana mai bubbuga bayana a hankali cikin nutsuwa ba tare da ya yi magana ba. Sai da ya ji kukan na wa ya yi ƙasa sosai sannan a hankali ya kawo bakin sa saitin kunnena ya raɗamin cewa.
"Ki ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
A hankali na shiga furtawa tamkar wata yarinya ƙarama mai koyon magana na yi ta maimaitawa har sau uku sannan a hankali ya ce.
"Miye ya faru?"
"Dad.. Ddyy wai ya rasu!"
Wayata da ta yi ƙara ne yasa ya janye jikinsa kaɗan ya ɗauko ta, still sunan Ammiena shi ne abin da ya ƙara appearing gaban screen ɗin. Receiving ya yi a hankali tare da ɗosana Wayar a gefen kunnena.
"Beenafah.."
Murya a ƙasa sosai na ce.
"Na'am Ammie."
Sosai ta sassauta murya ta ce.
"Ki bar zancen Bahrain kin ji ko? Ta wayar Dr. Ne aka kira ya ji muna magana bai ji da kyau ba ne shi ne ya ɗauki waya ya kiraki ba tare da mun sani ba..."
"Bai rasu ba kenan Ammie?"
"Bai rasu ba, yana dai gadon asibiti."
Bansan lokacin da na sauke wata irin sassanyar ajiyar zuciya ba ina mai saka hannu na kashe wayar sannan na ɗago idanuna na kallesa a hankali na ce.
"Ka ji wai ba rasuwa ya yi ba."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"OK..Allah Ubangiji ya bashi lafiya."
A sanyaye na ce.
"Amin ya Allah."
Har muka shiga bacci na kasa daina mamakin kaina wai don ance Daddy ya rasu na gigice ina ta uban kuka wanda a can baya ni ɗin nan babu abin da nake masa a koda yaushe idan ba mummunan fata ba, akan girman zaluncin da ya mana. Amma wai yau ni ce nake ta kukan rashinsa.
Washe gari da wuri muka shirya, sai da muka biya wani Company a tare ya shiga ya ɓata kusan 2hours sannan ya fito muka kama hanya sai Gusau. Wani gida muka sauka wanda zan iya kiransa da gidan gilashi domin bayan ginin simintin da naga an yi amfani an kewaye gidan da shi gabaɗaya, gidan gilashi ne ɗan daidai domin bai yi girman wanda su Hajiya suke ciki ba. Ya haɗu ta ko'ina maƙurar Haɗuwa. Ni ko na ce mai abu da abinsa, gidan babban Engineer da kansa.
Kallonsa na yi bayan mun shiga gidan na ce.
"Ba gidanmu inda Hajiya take zamu sauka ba?"
Girgiza kansa ya yi kai tsaye ya ce.
"Bibi ba zan iya zama wancan gidan ba. Kin san wani abu? Har cikin zuciyata na yafe mata kuma komai ya wuce, amma ba zan iya sake zama a inuwa ɗaya da Ita ba. Na auna yafi a ƙirga amma har yanzu ko kiranta na kasa yi..."
Hannunsa na kama a hankali tare da saka idanuwana a cikin nasa na ce.
" Dayaa! Har yanzu shaiɗan ne yake wasa da zuciyar ka, tun da ka haƙura ya kamata ka manta komai ku dawo yanda kuke.."
Wani murmushin gefen baki ya yi yana mai girgiza kansa ya ce.
" Idan aka sake ƙwarya ta baro bigirenta ta faɗo ƙasa ta tarwatse...yana da matuƙar wahala ta iya dawo daidai kamar yanda take...Tashi mu shiga ciki."
Miƙewa na yi tare da bin bayan sa, duk da cewa Ina da sauran maganganu da yawa a cikin bakina, dolena na haƙura na haɗiye su domin bai bani damar hakan ba.
Wanka muka yi muka yi sallah sannan muka ci abincin da ban san daga ina aka kawo ba. Bayan mun kambala muka ɗan zauna domin hutawa wanda sai misalin ƙarfe shida muka shirya muka fito sai asibitin FMC.
Mamaki ne da al'ajabi suka lulluɓeni ganin har da Ammie da Bahrain da kuma Dr. Basheer a ɗakin, bayan su Aunty Aysha da su Mummy Zaliha.
Tsaye na yi ina bin su da ido kamar yanda suma suka kafe suna kallona tamkar sun ga wata sabuwar halitta, musamman Mummy Zaliha da Daddy wanda yake kwance kamar ruwa sai aikin bin mutane da ido.
"Beenafah."
Ammie ta ambaci sunana ganin na yi tsaye ina ta kallon su idanuna cike da ruwan hawaye. A hankali na taka na je gabanta na rungumeta ina faɗin.
"Ammie...Ashe kuma kun zo?"
"Eh,yanzu muma bamu jima da isowa ba."
Waigawa na yi na kalli Dr. Basheer cike da girmamawa na ce.
"Abbu ina wuni! Barka da zuwa.."
"Yauwa Beenafah! Da fatan kunzo lafiya?"
Hannu Ya Mohaa ya miƙa masa suka gaisa sannan shi ma Ya Hafiz ya miƙo masa nasa hannun sannan Uncle Isma'ila. Gabaɗayansu su Uncle Isma'il ɗin babu wanda bai yi mamakin ganin mutumin da yake tsaye a gaban su ba,domin sun san shi farin sani, sai dai har yanzu basu gama fahimtar alaƙar zuwanmu tare asibitin ba kuma gashi mun shigo ɗaki ɗaya a lokaci ɗaya.
Yatsa Hafiz ya ɗaga yana nuna sa still da mamaki a fuskarsa ya ce.
"Engineer Muhammad Araam mai kamfanin Golden pathways...Kai ne aka haɗa da Daddy Bello a lokacin da za'a gina masa kamfaninsa na magunguna, a lokacin ganinka ya yi matuƙar yi masa wahala har ta kai sai da ya janye ya fara process ɗin neman wasu sai gaka ka neme shi daga baya."
Jinjina kai ya yi yana murmushi ya ce.
" Allah sarki! To ya mai jiki?"
" Jiki Alhamdulillah za'a ce, sai dai bamu san abin da ya kawo ka ba?"
Dr. Basheer ne ya ce.
" Shi ne fa Mijin Beenafah.."
Daga Hafiz ɗin, har su uncle Isma'ila, su Hassana babu wanda bai sha jinin jikin sa ba akan zallar madarar mamakin da wannan magana ta Dr. Basheer ta shayar da su.
Muryar Daddy muka ji wacce ba ta ma wani fita sosai yana miƙo wani singilallen hannunsa da ya gama ƙarmashewa yana faɗin.
"Beenafah...Beenafah zo kusa dani ki kawo min mijin ki na gani...kunyar duniya, wulaƙanci da tozarci sun tabbata a kai na Beenafah....Hajiya Mulaifa! Dan Allah ki yafe min.."
Mummy Zaliha na wani irin kuka ta girgiza kanta ta ce.
"Alhaji su yafe maka kodai su yafe mana? Komai mu kayi tare muka yi shi? Amma kai ne wanda ya fara nuna mana ƙofa, domin tun Dr. Bello yana raye kasha faɗamin cewa matar da Bello ya aura baka sonta, duk abun da kake mata kawai kana yi ne don GANIN IDON sa saboda baka da yanda zaka yi da ita tun da ya riga ya zaɓeta. Komai ta yi mana a duniyar nan zaginta kake. Da mijinta ya rasu ma farin ciki ka yi wanda kai ne ka zo min da plan ɗin yanda zamu mamaye komai ni kuma na hau na zauna har na zo na fika nuna musu tsana da ƙiyayya tare da Hassana da Hafiz..."
Hannu Ammie ta ɗaga mata yayin da wasu irin zafafan hawaye suka shiga zarya akan kumatunta, a raunane ta ce.
" Hajiya Zaliha ki daina dawo da hannun agogo baya! Abin da ya faru ya riga da ya faru yanzu kuma duk mun wuce wannan babin, idan mutum ya yi na gari don kan shi, idan ma ya aikata sharri to fa ɗan aike ya aika wanda dole watan watarana sai ya dawo gare sa...abu ɗaya nike so in ƙara Jan hankalin ki akai shi ne;A duk lokacin da muke jin wani yanayin ƙiyayya a tsakaninmu, to mu daina involving yaranmu a ciki, hakan yana taɓa su domin abubuwa ƙara lalacewa suke daga baya wanda ko da an so ayi sulhu, hakan yana matuƙar gagara. Kamar yanda kuka nemi alfarmar mu zo ga shi mun zo, mun yafe muku duk wani abin da yake tsakaninmu. Sai dai ka sani Alhaji Mudassir! Haƙƙin kashe Jaririn da bai san komai ba yana kan wuyan ka, wannan sai idan kun tsayu a gaban ubangiji domin shi ne wanda yasan abin da yafi da cewa da kai..."
Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe a hankali cike da wani irin raɗaɗi, hawaye wasu na bin wasu a gefen kuncensa ya ce.
" Kai Co! Kai co na ni Mudassiru! Astagfirullah Allah! Ya Allah ka shiryeni, ya Allah ka ƙara shiryar dani da iyalina akan hanya madaidaiciya.."
Shiru ɗakin ya ɗauka wanda baka jin ƙarar sautin komai sai na koke-kokenmu musamman Mummy Zaliha mai yin kamar za ta shiɗe tsabar yanda take ji. Haka suka bi mu ɗaya bayan ɗaya suna roƙon gafara wanda ni ce ma mai amsawa domin Bahrain ya maƙale jikin Abbu ko kaɗan ya kasa motsawa sai uban kuka da yake rusawa.
"Aysha..."
Muka ji Daddy ya kira Sunan Aunty Aysha a hankali wacce ke takure a gefe ɗaya ita da su Hassana suna ta kuka. Ɗagowa ta yi ta kalli gefen gadon da yake kwance a sanyaye ta ce.
"Na'am Daddy!"
Wani wahalallen yawu ne ya wuce masa a maƙoshinsa da ƙyar sannan ya ce.
"Ki ɗauko wannan amanar da na baki na ce ko bayan na mutu ki damƙawa Mulaifa hannun ki da nata,ɗauko ki bata."
Tashi ta yi a hankali ta saka key ta buɗe wata locker dake gefen gadon ta ɗauko wani file na fata mai kama da Jaka ta miƙa mata sannan ya ce.
"Waɗannan, su ne kayayyakin mijin ki da na sace da kuma kema kayayyakin ki dana yaran ki, komai yana ciki. Kuma na gode da kuka janye ƙarar, ko a haka kika barni na san cewa ke ce da riba. Duk zakaran da Allah ya nufa da cara, to fa ko ana muzuru ana shaho sai ya y."
Kallon Uncle Isma'ila Ya Mohaa ya yi ya ce.
" Wane irin tsari ake kai da shi na jinya? Na ga yana jin jiki sosai..."
"Ranka ya daɗe magani ana nan ana ta yi, kullum cikin siyen magani ake kuma kullum likitocin suna iya bakin ƙoƙarin su. Ga shi nan dai,sai an shafe sai kuma rai ya dawo, sai an shafe sai kuma rai ya dawo. Haka dai ake a wahalce. Da an so an fitar da shi waje inda aka yi jinyar sa na farko to abubuwan ne sai a hankali..."
Jin yanda yake ta fitar da wani irin numfashi da sauri-sauri yasa hankalinmu ya koma kansa, sosai hankalina ya tashi domin in dai jinya mutum yake a gadon asibiti hakan yana matuƙar ɗaga mini hankali. Da gudu Hassana ta fita wurin kiran likita ni kuma na ƙara matsawa wurinsa ina mai kama hannunsa domin wallahy ba ƙaramin tausayi ya bani ba. Ƙoƙarin nake na buɗe bakina na bashi kalaman da wata ƙila su sanyaya masa zuciya. Sai dai kafin na yi wani yunƙuri har na kai ƙasa somammiya wanda daga nan ban ƙara sanin a ina nake ba sai da na farfaɗo na ganni a gida, saman Gado tare da Aunty Labiba a gefena.
Da kyakkyawan murmushinta na fara yin tozali tana mai ƙara jimƙe hannuna a cikin na ta cike da tausasawa ta ce.
"Beenafah kin farka? Sannu. Ya kike ji a yanzu? Akwai abin da yake miki ciwo? Mi kike so ki ci?"
Bansan lokacinda wani irin murmushi ya suɓuce min ba saboda ba ƙaramin dariya ta bani ba na ce.
"Aunty Labiba ni fa lafiyata ƙalau. Na je kawai zan yi magana da Daddy ne kawai na ga na faɗi..."
Cike da farin ciki ta ce.
"Allah ya ƙara miki lafiya Bibin Daddy...farar mace mai farar aniya, ga farar zuciya kamar zinari. Yanda kika saka Daddy a farin ciki...farin cikin da har sai da ya saka shi zubar da hawaye, ina miki fatan alheri, ubangiji ya albarkaceki ya kuma albarkaci abin da yake cikinki...Beenafah Giwar Daddy uwar gida kuma Amarya uwar 'ƴa' ƴansa. Allah ya ƙara miki farin ciki da kwanciyar hankali a gidan auren ki ya ƙara muku fahimtar juna. Mun gode, mun gode, Familyn ARAAM da Familyn SAMI muna godiya da wannan kyautar..."
"Aunty Labiba ina Ammie.?"
Tambayar da na jefa mata kenan domin ban gama fahimtar ma maganganun da take ba har yanxu. Al'amarin Daddy ya yi matuƙar ɗaga mini hankali, ya gigita ni fiye da zato. Wallahy duniyar nan ba bakin komai ba ce. Ji yanda Daddy gabaɗaya cikin lokaci ƙanƙani kamanninsa suka canja kamar ba shi ba.
"Ammie yanzun nan suka wuce, su ma su Aysha ba su jima da tafiya ba."
Cike da mamaki na ce.
"Hala Karfe nawa ne yanzu?"
Agogon wayarta ta duba tana faɗin.
"11:14pm yanzu..."