Ganin ido complete - Chapter 58
Ganin ido complete Chapter 58: Ganin ido complete Chapter 58. Zaro ido na yi ina faɗin.
3,367 words
Zaro ido na yi ina faɗin.
"Kenan na jima a kwance, tun 6pm fa."
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Haka ne."
Sallama Hajiya ta yi ta shigo ɗakin tare da yi mini murmushi bayan mun haɗa ido ta ce.
"Beenafah kin farka.."
Yunƙurawa nayi da nufin Miƙewa zaune domin na gaishe ta, sai ga shi ta zo da sauri ta ƙara mayar dani tana faɗin.
"Kwanta abinki kinji. Allah ya inganta ya saukar da ke lafiya."
Mamaki nike na wannan sabbatun da suke na maganar sauka da ingantawa, ni fa har yanzu ban ɗauki haske ba.
Wayar Aunty Labiba da tayi ƙara ne ta janyo hankilana ganin ta ɗauka cike da farin ciki ta kara mini a kunnena tana faɗin Nadeeyah ce.
Karɓa na yi muka gaisa sannan ta yi min ya jiki. Bayan mun kambala ta kira Hairi ta bani kamar yanda Hairin ta roƙeta cewa dana farfaɗo a sanar mata. Bayan mun gama ta kamo numbern Suwara inda a nan suka yi min caa! Kowa na faɗin albarkacin bakinsa harda su Jadda suna ta min sannu.
Kallon Ziza Aunty Labiba ta yi wadda ke sanƙame a inda take tsaye tunda suka shigo da Hajiya ta ce.
"Ziza kin tsaya ba ki zauna ba kuma ba ki ce komai ba."
To me za ta ce? Mamaki ne da al'ajabi suka sanƙameta wanda har ta kasa motsawa tsabar yanda ganina ya dokar mata zuciya. Tambayar kanta take ta yi tun ɗaxu cewa wai daman BEENAFAH ce NANA? Duk labarin da Hajiya ta bata har yau bata taɓa ji ba ko da wasa cewa wai Beenafah ce matar Ya Muhammad ba. Beenafah fa? Cab! Lallai waɗan nan mutanen sai yau ta ƙara tabbatarwa cewa su ɗin ƙwallayen shegun munafukai ne. To miye a ciki da suke ta wani ɓoye-ɓoyen faɗa mata?
"Ziza! Ki samu ki zauna mana, kada ƙafafuwanki su gaji.."
Murmushi ta yi sannan ta ce.
"Uhm! Ai dare ma ya yi tafiya zamu yi...."
Sai kuma ta dawo da kallonta gare ni still da murmushin ta ce.
"Ya jikin?"
Rufe idanuna na yi ba tare da na ƙara kallon inda take tsaye ba na ce.
"Lafiya."
"Allah ya ƙara sauƙi"
"Amin."
Yanayin yanda ta ji na amsa ta shi ne abin da ya ƙara bata mamaki ya sanyata ƙara shan jinin jikinta wanda ko minti biyu bata ƙara ƙwarara ba ta yi mana sai da safe ta fice ta je mota inda Oga Sule ta zauna zaman jiran fitowar Hajiya domin su koma tare, wanda sai da suka ɗan ƙara jimawa sannan suka yi mini saida safe suka tafi.
Suna fita na miƙe na lallaɓa a hankali na shiga toilet na watsa ruwa sannan na yi alwala na fito na yi sallah. Ina nan a zaune da tunaninsa a raina sai ga shi ya shigo ɗauke da ledoji a hannunsa.
Ajiyewa ya yi kan glass table ɗinda ke gefe ya zo ya ɗagoni muka miƙe tsaye yana tallafo haɓata cike da wani shauƙi ya yi kissing lips ɗina da goshina a hankali sannan ya rungumeni a ƙirjinsa, cikin wata irin Murya mai cikakkiyar nutsuwa da haiba ya ce.
"Hankalina ya tashi sosai, na shiga matuƙar gigita,na yi matuƙar ruɗewa, na kaɗu, domin na za ta wani abin ne ya same ki. Idan wani abu ya same ki ban san yanda zan yi ba. Na gode Bibina! Allah ya saka miki da alheri. Haƙiƙa na yi farin ciki wanda ban san ma ya yanda zan misalta miki irin yanda nake ji ba a raina. Wai ni ne yau nike da mata, tana ɗauke da cikina za ta haihu..."
Ɗago fuskata na yi da sauri na kallesa ina murmushi cike da zumuɗi nace.
" Da gaske? Haihuwa zamu yi? Zamu samu ɗa?"
Shiru ya yi yana kallona da wani irin lallausan murmushi dake kwance akan fuskarsa. Yanda ta yi reacting ba ƙaramin ƙara hudashi ya yi ba. Wannan matar tashi Allah kaɗai yasan irin so da ƙaunar da yake mata. Ji yanda take nuna zallar farin cikinta jin cewa tana ɗauke da juna biyu...
"Mijina! kasan me? Wani tafseer da na taɓa saurara malamin yana cewa;Ku yi aure, domin sunna ce ta ma'aikin Allah wanda ya ce ayi koyi da shi. Idan kuka yi aure ku roƙi Allah alheri da albarka, sannan ku yi addu'ar samun 'ƴa'ƴa na gari masu albarka, idan kun samu kuma, ku tarbiyantar da su ku kula da rayuwarsu domin su zamto yara na gari waɗanda za su yiwa addinin Allah hidima, sai rayuwarsu ta yi kyau, kuma kada ku gushe kuna yi musu addu'a da fatan alheri har zuwa numfashinku na ƙarshe...wallahy idan kuka tafiyar da su a haka, kuka sauke duk wani nauyi na su kamar yanda Allah da manzonsa suka koyar... To tabbas za ku yi alfahari da su tundaga duniya har zuwa gobe alƙiyama...Tun daga wannan ranar...babu wani lokaci da zai zo na yi sallah ba tare na roƙi wannan alherin ba..."
Rungume ni ya yi yana mai jinjina kansa ya ce.
" Allah na gode maka da wannan matar da ka bani..tabbas wani jinkirin alheri ne. Allah ya ƙara miki albarka. Ina son ki sosai. Allah ya raya wannan cikin ya girmar da shi cikin aminci. "
" Amin."
Janyewa yayi yana mai leƙa fuskata ya ce.
"Mi kike so ki ci?"
Dariya na yi sannan na ce.
"Ni fa babu abin da yake damuna, komai ma aka bani zan ci.."
Jinjina kansa ya yi yace.
"To kuwa duk abin da na zo miki da shi sai kin ci...bari na yi wanka na fito"
Ya shigewa na buɗe na ci duk abinda raina yake so sannan na sha ruwa wanda kafin ma ya gama abin da yake ni har na daɗe da yin bacci.
Yana zaune yana cin abincin sai ga kiran Jadda ya shigo wayarsa. Fuska ba yabo ba fallasa ya ɗaga tare da yi mata sallama.
Cikin farin ciki daga can ɓangarenta ta ce.
"Barka Hammodi! Ina taya ka murna da wannan kyakkyawan albishir ɗinda ya riskemu. Allah ya inganta ya sauke ta lafiya. Kaga kenan alheri biyu da biyu."
Cikin rashin sanin inda zancen na ta ya dosa yana wani irin murmushi ya ce.
"Amin amin ya Allah Jadda. Na gode sosai, a sakamu a addu'a. A kuma tayani godiya ga Beenafah, tabbas ta gama mini komai a duniya, na gode mata. Ta zamto Mace mafi alheri a cikin rayuwa ta."
"Wallahy kam Beenafah ta gama mana komai Hammodi, Allah ya ƙara muku zaman lafiya da ya ƙara muku fahimtar juna ya zaunar da ku lafiya....Bata wayar na ƙara gaishe da ita."
Kallon inda nake kwance ya yi sannan ya ce.
"Ai ta jima da yin bacci Jadda. Doctor ya ce ta riƙa samun bacci tana hutawa. Jiya ma kinga ga tafiya ga damuwar rashin lafiyar Babanta."
"Allah sarki! To don Allah ka kula da ita yanda ya kamata ka ji ko? A kiyaye da dokar likita. Idan ma ta samu sauƙi kana iya dawowa da ita nan, domin idan tana ganin ta a gida to fa ba za ta daina yawo ba."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"In Sha Allahu Jadda! Na gode sosai Allah ya saka da alheri ya ƙara girma."
"Amin. Allah ya tashemu lafiya."
Washe gari da wuri muka shirya muka je AA master wurin Doctor Osita Wanda ya ƙware sosai wurin yin scanning na ciki da ma duk wani abu wanda ya shafi ciki da haihuwa. Bayan an kambala ya faɗa mana cewa cikin sati shida ne da kwana biyar. Godiya ya yi masa sosai sannan muka baro wurin zuwa gida. Halin da yake ciki na tsantsar farin ciki ni abin har mamaki yake bani. Tun jiya ya kasa tsaye ya kasa zaune kamar wanda aka ce masa haihuwar ta zo. Kwana fa ya yi bai runtsa ba yana ta ibada sai da lokacin sallar asuba ya yi sannan ya fita masallaci.
Koda muka isa gidan na tarar da su Maman Fakiha sun zo tare da Ammie suna zaune suna jirana. Cikin wani irin farin ciki na yi tsalle na ɗale wuyan Ya Jafaru akan tsananin farin cikin ganinsa da na yi.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 49*
"Ke!..Ke!..Subhanallah!"
Ya Jafarun ya faɗa da ƙarfi yana mai tureni daga jikinsa hankalinsa a tashe.
Kallon kallo suka fara sannan suka maido kallon su a kaina tsabar mamakina da ya hana su magana wanda ni sam a gare ni ban ɗauke shi komai ba tsabar yanda na tsinci kaina a farin cikin ganinsa. Sai dai kuma, yanda suka yo min caa! A kaina ne musamman Maman Fakiha shi ya dawo dani cikin hankalina wanda a take na tuna cewa ban yi daidai ba.
Da sauri na waiga bayana amma kuma ban ga Ya Mohaa ba, hakan ya tabbatar mini da cewa komawa ya yi bayan mun shigo. Haƙuri na basu sannan na gaishe su suka yi min ya jikina na amsa da lafiya lau ina mai zuwa na rungume Fakiha fuskata cike da annuri. Itama Fakihar cike da farin cikin ganina ta janye tana mai ƙure fuskata da kallo ta ce.
" Ashe rai kan ga rai Beenafah? Idon ki kenan? Kin shige Ƙasar Larabawa kin zauna kin yi shiru hankalinki kwance...Masha Allah! Kalli kumatunki luwai-luwai! Kin ƙara fari kin yi kyau sosai.."
"Uhm! Haka dai kika ce Fakiha. Ya karatu ya kwana biyu!"
"Alhamdulillah! Komai lafiya ƙalau. Kina can Ammie na ta cika mu da abubuwan alheri. Mun gode Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alheri....kinga ya Hamza an zama Cele..?"
Dariya na fashe da ita kamar yanda ta yi ina mai kallon Ammie na ce.
"Ammie Ina Ya Hamza?"
"Hamza yana Sokoto, exams yake yi shiyasa bai zo ba..."
Bahrain na dariya ya dawo gefena ya zauna yana faɗin.
"Aunty Beena ba kiga idon Ya Hamza ba jiya, tamkar wani ɗan ƙaramin yaro haka ya ɓata fuska sosai sai da Abbu ya dinga masa faɗa musamman akan muhimmancin karatunsa."
Girgiza kaina na yi ina dariyar na ce.
"Ai Ya Hamza har abada ba zai girma ba...." kallon gefen da Ya Jafaru ke zaune na yi ganin yanda ya keta wani kakkaucewa kallona da mamaki na ce.
"Ya Jafaru ina kwana? Sai wani yi kake kamar baka gane ni ba."
Sai yanzu ya ɗago fuskar sa ya kalleni fuskar nan babu ƙiren annuri ya ce.
"Beenafah ya jikin? Allah ya ƙara afuwa."
Daga haka ya miƙe ya nufi ƙofa yana faɗin sai sun fito. Ko kaɗan bai so zuwa gidan nan ba, in banda Mama da Baba da suka matsa da sam bai yi niyyan zuwa ba. Wai har su ce an zama 'ƴan uwa! Bayan an cuce sa kenan. A yanzu tabbas yasan cewa ta fi ƙarfinsa domin ta taka tsani da matakin da ta yi masa rata to amma yasan cewa har abada ba za ta samu soyayya da kulawa ba kamar yanda ya shirya mata idan da ace shi ne ya aure ta. Domin shi ɗin saurayi ne mai jini a jiki, to amma wannan ɗin miye ta gani a jikin sa har ta ji cewa ya burgeta a ranta ta ji cewa ya fi shi? Shi ne fa wanda ya fara sonta tun bata kai haka ba. Amma shi ne za ta zaɓesa dare ɗaya ta barshi. Tsaki ya buga daga ƙarshe ma ya fita ya haye abin hawa ya wuce gida ba tare da ya tsaya jiransu ba.
Ni kuwa, mamakinsa ne ma ya hanani magana. Yanda ya yi reacting sai yasa ni jin ba daɗi a raina kamar na yi masa wani abin ne. Hakan yasa na kasa daurewa na kalli Mamansu na ce.
"Mama! Ko dai na yi wa Ya Jafaru wani laifin ne ban sani ba?"
Cike da takaicinsa ta girgiza kanta ta ce.
"Ƙyale mutumin wofi Beenafah...Babanku ya ce na gaisheki sosai, baya garin ne ya tafi Lagos ɗauko kaya, idan ya dawo kina nan, zai zo ya duba ki.."
Cikin jin daɗi na ce.
" Allah sarki! Allah ya tsare ya dawo da shi lafiya. Ina Farisa?"
Bahrain ne ya karɓe zancen ya ce.
" Ta na makaranta, ai sai da ma na rakata sannan na dawo..."
" Sai da ka rakata? A ina ka ganta da sassafe har ka rakata?"
Ammie ta ce.
"Gidan su ya kwana fa. Kuma Humaida ta yi ta binsa ya kwana a gidansu, amma ko magana ya ƙi ya mata..."
Kallona ya yi yana mai jin wani irin takaicin sa a ranta ya ce.
"Aunty Beena ta ya ya zan kwana a gidansu yarinyar da ta dinga wulaƙantani? A gabana fa take cin abinci ina kallonta yayin da nake jin baƙar yunwa amma ko kallon inda nake tsaye bata yi. Haka lokacin da kuka taɓa tafiya asibiti kuka barni inda Mummynsu ta ce wa Mummy na zageta haka Mummy ta dinga dukana sai da Aunty Biba ta ƙwaceni....Mts! Bana son su Aunty Beena,sam ba su da zuciya mai kyau... "
Lumshe idanuna na yi na buɗe ina kallon sa, a hankali na sauke murya na ce.
" Bahrain! Ita fa rayuwar nan... "
Miƙewa ya yi tare da saka hannu ya toshe kunnensa alamar baya ma son saurarena ya ce.
"Ba abin da za ki faɗamin game da su...i will never listen to you."
Daga haka ya fita ya koma can bakin swimming pool ya tsaya Wanda kana iya hango komai daga ciki. Fira muka yi sosai har kusan 12pm sannan su Mama suka wuce suka barni tare da Ammie.
Ina ciki ina sallah na ji muryar Aunty Labiba ta shigo ita da su Adeel. Cike da farin cikin xuwansu na fito na rungume Hanan ina mai yi musu sannu da zuwa. Mamaki ne ya kamani ganin Biba zaune tana kallona.
"Beenafah.."
"Na'am Biba..da gaske ke ce?" kallona na mayar gun Aunty Labiba na ce.
"Aunty Labiba kece kika zo da ita?"
Jinjina kanta tayi tana murmushi ta ce.
"Eh! Hajiya ce tace a kawo miki ita. Daman kin san ta dawo nan da aiki..."
"Allah sarki! Gaskiya na ji daɗi sosai. Canjin rayuwarmu ya fara ne ta sanadin haɗani dake da ta yi, shiyasa har abada ba zan manta da ita ba...shiyasa duk yanda mutum yake kada raina shi domin baka san wace irin rana zai iya yi maka ba."
Jinjina kai Biba ta yi ta ce.
" Ban san ta wace hanya zan iya taimaka miki ba a wannan lokacin, domin Ammie tabbas ta cancanci in saka mata akan irin yanda ta ɗaukeni ni da Mahaifiyata duk da cewa ba'a nan take ba. Ta yi mana abubuwan alkairai da dama ita da Abbie...Allah Ubangiji ya jaddada rahamarsa a gare shi. "
A tare muka amsa da amin, sannan Biba ta zuba mana abincin da suka zo da shi muka zauna muka ci. Bayan nan muka ɗora da fira. Kallona Aunty Labiba ta yi tace.
" Mummyn Adeel shin Shi Daddy ba zai ci abincin ba ne?"
Ido na zaro ina dariya sannan na miƙe na shiga dube-duben inda wayata take wanda sai da na gama shan wahalar nema sannan na tuna tana cikin Jakata. Koda na ɗauko ya yi min miss call yafi guda ashirin,hakan yasa ba shiri na kira shi back zuciyata cike da rashin jindaɗi.
"Bibi...kin tuna dani kenan?"
Cike da jin kunya na ce.
"I'm sorry."
"Ba damuwa,Ku ci gaba da zumuncin ku sai after magrib zan dawo In Sha Allahu....kin ci abinci?"
Jinjina kaina na yi tamkar yana a gabana na ce.
"Eh. Kai fa?"
"Na ci, Alhamdulillah."
"Ok! Allah ya tsare, Allah yasa a dawo lafiya"
"Ki kula kin ji ko?"
"In Sha Allah."
Ina gama wayar Ammie ta yi mana sallama ta wuce ita da Bahrain. Ya rage daga ni sai su Aunty Labiba har kusan ƙarfe biyar sannan suka tafi suma ta bar ni daga ni sai Biba.
Kitchen ta wuce domin nema mana abinda zamu ci ya yinda na wuce ciki na ɗan kwanta kaɗan.
Bacci sosai nake wanda ban san ma lokacin da ya dawo ba sai da naji yana tashi na.
"Ka dawo? Sannu da zuwa.."
"Thank you. Kin yi sallar magrib kuwa?"
Girgixa kaina na yi na ce.
"A'a. An yi ne?"
"To tashi please, ki lallaɓa ki yi."
Tashi na yi na wuce na yo alwala amma koda na fito baya nan da alama ya sake fita masallaci domin yin sallar isha. Bayan na kambala na je na yi wanka sannan na fito na je ɗakin da Biba take na tarar da ita tana sallah. Bayan ta kambala ta juyo muka gaisa ina murmushi na ce.
"Wallahy na ji daɗin zuwan ki sosai Biba..ina fata tare zamu koma dake?"
Dariya ta yi tana wani girgiza kai ta ce.
"Wohoho! Biba a Dubai! Wayyo daɗi kasheni ni ɗiyar Babana..."
Dariyar nima na yi ina faɗin.
"Kin kambala komai kin jera mana?"
Tsahirta dariyar tayi tana jinjina kanta ta ce.
"Eh, komai an kambala shi Hajiya.."
Wata uwar harara na maka mata sannan na ce.
"Ba Hajiya ba wallahy makawuya.."
"A'a wallahy ranki ya daɗe dole na ce miki Hajiya...yo so kike in ce Beenafah? Uhhh! Ki rufamin asiri in mutu maza su kai ni.."
"Biba ta yaya ki ka baro gidan su Mummy Zaliha?"
Na jefa mata tambayata wacce tun ɗazu ta tsaya a tunanina tsawon lokaci.
Girgixa kai ta yi sannan ta ce.
"Duk wanda ya ce zalunci ne rigarsa to tabbas watan watarana sai ya tuɓeta ba arziki ya dawo tsirara, domin rigar zalunci rigar ƙaya ce wacce har abada ba za ta barka ka zauna lafiya ba. Babu irin wulaƙanci da tozarcin da Mummy Zaliha ba ta mini ba. Ƙarshe sai ga shi rana ɗaya abubuwa sun caɓe musu, haka suka bi mu suka bamu kuɗin mota da cewa zasu nememu daga baya, to fa shiru ba labari, ni kuma kin san 'ƴan marayun yarana guda biyu suna nan sannan ga su Inna. Shi ne na dawo gidan Hajiya Batula na ci gaba da aiki, sai ga shi yau bayan Hajiya Labiba ta zo ta ce na shirya a kai ni gidan Muhammad ɗinta, matarsa tana da sabon ciki in ci gaba da kula da ita."
"Allah sarki! Wallahy na gode mata, na ji daɗin zuwan ki. Allah ya bamu haƙurin zama."
"Hmm! Mummy Zaliha! Mummy Zaliha ta tsula tsiya ita da Daddy Beenafah...Hassana ma ta tsula tsiya. Sai ga shi rana tsaka Hassana ta tsere ba'a san inda ta shiga ba, ashe ta je ta yi auri da wanda ko Tayar Keke bai da ita, hakan yasa Mummy ta kusa haukace wa akan baƙin ciki, ga Hafiz an kore shi daga makaranta..."
Fira muka sha sosai sannan daga ƙarshe na yi mata saida safe na tafi. Koda na je har ya yi wanka yana zaune yana duba wayarsa.
Zuwa na yi na rungumesa ta baya ina murmushi na ce.
" I miss you..."
Miƙewa ya yi tare da juyo dani ta gaban sa yana kallon fuskata ya ce.
"Ke da kika rungume wani a gabana Bibi..kaɗan ya rage na mutu akan yanda abin ya dakeni...amma yan da ya tureki daga jikin sa yana mai jin ba daɗi...shi ne abin da ya ceceni ya hanani mutuwar...."
'Wayyo Allah na!' abun da na Furta kenan a zuciyata ina mai binne fuskata a cikin ƙirjensa cike da jin wata irin kunya sannan na ce.
" Ka yi haƙuri dan Allah! Wallahy Mantawa na yi.."
Jinjina kansa ya yi sannan ya ce.
" Uhm! Na dai ji ba daɗi kam, domin na jima ban daina ganin abin a idanuna ba..."
"Ka yi haƙuri, ba zan sake ba."
Fuskarsa ya kawo saitin Wuyana yana gogawa har zuwa fuskata sannan ya dire laɓɓansa akan nawa ya yi kissing ɗina sai kuma ya janye yana kallon idanuna ya ce.
"Thank you....thank you for everything Bibi. Ta sanadiyyar ki zan zama Uba nan da wani lokaci idan Allah ya amince mana. Ina son ki sosai...irin sosai ɗin nan fa nake gaya miki..bani da haufi ko kaɗan a kan ki domin na san za ki kula da cikin sosai..amma dai duk da haka ki kula sosai kin ji ko..."
Murmushi na yi ina jinjina kai na na ce.
" In Sha Allah zan kula...muje muci abinci, Biba ta shirya komai. "
" Waye Biba?"