Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 59

Ganin ido complete - Chapter 59

Ganin ido complete Chapter 59: Ganin ido complete Chapter 59. " Mai aikin Hajiya ce ta aiko mana da ita..."

3,348 words

" Mai aikin Hajiya ce ta aiko mana da ita..."

Ɗan jim ya yi yana nazari na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ya kalleni cike da karaya ya ce.

"Bibi kina ganin zan iya ƙara yarda da wani abu daga gare ta?"

Hannun sa na kama ina mai kwantar da murya na ce.

"Subhanallah! Haba Dayaa! Ya kamata ka tsayar da zuciyar ka wuri ɗaya dangane da Hajiya, kuma ka yarda har abada ba za ta iya ƙara tunanin cutar da kai ba. Hajiya ta yi kuskure a baya...but a yanzu ta gane, dan Allah ka manta da komai. Biba ce ba wata ba, ba za ta taɓa cutar da mu ba.."

Hannunshi na ja muka wuce muka ci abincin sannan muka dawo muka zauna muna fira. Muna nan sai ga wani abokin sa ya zo dubani tare da matarsa da 'ƴa' ƴansu.

*********

Sai da na yi kwana biyar cif na ƙara warware sannan muka shirya muka fita, gidan Hajiya muka fara zuwa inda muka fara tarar da Ziza tana zaune. Sai da ta gaishe da Ya Mohaa sannan ta gaidani wanda ina sane na tsaya ban ce komai ba don gani shin tana gaishe dani ko kuwa? Sai dai bata da yanda za ta yi musamman ta ganmu a tare, saboda haka ko rai ba ya so dole ace da Mijin Iya Baba.

Daga nan muka shige har inda Hajiya take wanda sai da tayi hawaye akan farin cikin ganinmu. Gadonta na kama na haye na kwanta don kawai in ƙara sa ranta ya yi sanyi sannan na ce ina son in ci Wainar fulawa. Da kanta ta fita ta soyamin ta dawo ta kawo min har nan na ci sannan na fita na zaga inda su Munira na bar su ko akwai maganar da suke so su tattauna.

Daga Munira har Haulatu ji suka yi tamkar su goyani tsabar farin cikin da suka ji yana neman kashe su akan ganina da suka yi ba zato ba tsammani.

Kallon Munira na yi wacce ta wani rirriƙeni tamkar wadda akace zan ɓace mata ina dariya na ce.

"Dan Allah ni dai cikani kada ki matse min hancin baby..."

Dariya suka fashe da ita sannan Munira ta wani ja gefe tana min wani kallo ta ce.

"Iyyehh! Lallai yarinyar nan ki ce aure ya koya miki rashin kunya! To ina Cikin yake da za ki ce kada a matsewa Baby hanci?"

Dariya muka yi sannan Haula ta ce.

"Ke ko abu ne ya kawo ga ma'iya. Uwayen zamani...."

Hannu na kai ina shafa cikina ina wani murmushi na ce.

"Ɗan Maman sa da Babansa ne fa! Ɗan dangi kuma. Hmmm! Dan Allah ku saka mu a Addu'a, Allah ya nuna mini na haifawa Daddy ɗa ko ɗiya mai albarka..."

"Amin. Amin yah Allah. Congratulations Beenafah. Wallahy mun yi farin ciki sosai da muka ji cewa Daddy kika aura. Allah ya baku zaman lafiya ya sauke ki lafiya ya baku rayayye mai albarka."

"AMIN Ya Allah Munira....na gode muku sosai..."

Hannuna ta ja tana faɗin zo mu je ɗaki mu yi fira. Bayan mun shiga ne Haulatu ta kalleni ta ce.

"Mai ciki mi kike so ki ci?"

Ɗan wawwara idona na yi alamar tunani na ce.

"Ummm! Mi ma zan ci? Sakwara nike so miyar Egusi..."

Kafin na gama rufe bakina har ta miƙe tsaye da nufin ta fita na yi saurin kamo hannunta ina faɗin.

"Ina za ki je?"

"Wurin cika miki aiki mana Hajiya..."

"A'a. Wasa nikam nake miki, na ƙoshi wallahy..zauna abun ki mu yi fira."

Muryar Munira muka ji tana dariya ta ce.

"Hmm! Ka ji tsoron wanda bai iya soyayya ba, wallahy idan ya iya to fa an shiga uku da shi..."

Wani irin far-far! Na yi mata da ido sannan na ce.

"Wallahy maganar ki dutse...ji nake kamar na haɗiye mijina akan irin ƙaunar da nake masa, domin shi ma yana ƙauna ta, yana kuma so na sosai....Hmm! Allah dai ya barmu da masoyanmu na gaskiya ya ƙara mana haƙuri da juna."

"To a dai yi sai-se sai-se. Kada a zure a al'amarin Rijalu domin ba tabbas ne da su ba. Domin wallahy duk wannan giyar bai hana watarana kina zaune ya kwaso miki wata...ni tun ga al'amarin Aunty Ziza na ƙara tsinkewa da lamarin maza. Ballantana Daddy da ya jima bai yi aure ba. Kada ya fara tunanin aure-aure Watarana..."

Wani irin mummunan faɗuwar gaba na ji lokaci ɗaya wanda a ruɗe na saka hannayena na dafe ƙirjina ina faɗin.

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Gaskiya Munira ban taɓa sanin cewa bakya ƙaunata ba sai yau!....Wallahy da gaske ba ki ji yanda ƙirjina ya buga ba akan wannan muguwar kalmar da kika furta. Kin san yanda nake son Dayaa kuwa? Hmm! Koda yake...ban san iya inda zaren ƙaddara zai kaini ba, amma wallahy kin ji na rantse miki da Allah Munira duk Ya ce zai ƙara aure to zuciyata za ta iya bugawa na mutu lokaci ɗaya..."

" To ke nan Aunty Ziza ba ta yi laifi ba akan yanda take kishin Mijinta?"

Da sauri na Girgixa kaina na ce.

" Ni Wallahy ko sau ɗaya ban taɓa jin ina son Mijinta ba, domin ni asali ma mai mata baya burgeni. To Kuma a wannan lokacin tabbas ban fahimci abinda take ji ba, domin ban da Mijin ballantana in gane yanda zafin kishin yake...Amma yanzu, na fahimta, na kuma gane yanda abin yake, da ni ce a Matsayinta a wancan lokacin da ina iya yi mata fiye da abunda take min. Soyayya gaskiya ce Munira...ban taɓa yin ta ba sai akan Mijina. Ban sani ba ko nika ɗai ce nake jin hakan amma tabbas kishi gaskiya ne. Sannan su ma Mazan ba ki isa idan sun ce za su yi ba ki ce ki hana su....."

Girgixa kai na nayi ina mai jin yanda zuciyata ke wani irin fatfatniya na ce.

" Mts! Munira, mu daina ma wannan zancen dan Allah domin ba shi da wata fa'ida. Barin sa ina ganin shi ne yafi alheri. Allah dai yasa mu dace duniya da lahira.

"Amin. Auren Haula saura wata biyu da 'ƴan kwanaki..."

Ƙara Faɗaɗa murmushina na yi ina faɗin.

"Masha Allah! Ki ce kafin Ramadan kenan kamar su Hairi..."

"Wallhay fa. Haula dai itama Amarya ce, haka za ku shige ku barni nan idan mun haɗu kuyi ta yi mini sabbatun ku na masu aure..."

Dariya muka fashe da ita sannan na ce.

"Ke ma ai yi za ki yi watarana in sha Allahu...amma gaskiya ko da za'a yi kam bana nan, na ji ma ɗazu ya fara mini zancen tafiya har da cewa daƙyar ma zamu isa Sokoton nan tun da su Ammie sun zo. Allah dai ya sanya alheri ya bada zaman lafiya."

"To amin Yah Allah. Ai ba komai,Allah ya kai ku lafiya."

Fira muka ɗan ƙara taɓawa, Munira har da wani ɗauko mini wayata da Ya Emraan ya fasa da kuma wacce Ya kawo suka ba Ziza ta fasa. Bayan na koma ciki na tarar da Hajiya da Ziza suna zaune, ɗaki na wuce na shiryo domin yace yana waje yana jirana sannan na yi musu sallama muka tafi ya ajiyeni gidanmu, ainahin gidanmu inda muka fara zama wanda su Mummy Zaliha suka katanta ne. Ina shiga gidan sai da na ji gabana ya faɗi, hawaye ne suka shiga zarya akan kuncina domin komai haka ya shiga dawowa kai na tamkar yau ne yake faruwa, musamman ƙofar lungunmu inda muka zauna ni da Ammie da Bahrain. Hmmm! Allah kada ka jarabcemu da abubuwan da ba su wuce wa a rayuwarmu.

Komai an can ja shi wanda hatta Fentin gidan sai da aka canja ya dawo kamar ba shi ba.

Ina shiga Ammie ta kalleni ta ce.

"Lafiya? Ya da kuka kuma?"

Rungumeta na yi nasha kukana sannan na janye ina kallon ta na ce.

"Allah ya ji ƙan Abbie da Rahma...Allah ya gafarta masa yasa yana Aljanna. Ina jin kewarsa sosai Ammie...musamman idan ina tuna ranar haihuwata."

Hawayenta ta share tana jinjina kanta ta ce.

"Amin Beenafah. Ina kika baro Mijin naki?"

"Ya tafi, ya ce mini sai idan ya dawo zai shigo. Ina Bahrain?"

"Bahrain yana ciki, yanzu ya shiga wai zai yi bacci."

Cikin rashin jindaɗi na ce.

"Ammie ɗazu fa yake sanar mini cewa wai daga nan komawa zamu yi ba sai munje Sokoton ba tunda dai ga ki kinzo....Ni dai dan Allah ki lallaɓa shi ya bari muje, ina son na ga su Mummy Sameera..."

Da sauri ta wani girgiza kanta tana faɗin.

"Ni zan lallaɓa mijin ki Beenafah akan kina so ya barki ki yi abu? To Allah ya tsare ni nikam, ba na cikin waɗannan uwayen..kuma ma ai banga laifi a nan ba, domin mu ba yanzu zamu koma ba, sai mun gama duk wani abu da ya kawo mu. Yanzu haka Dr. Ya wuce yau ya tafi Lagos zai gana da manajan Abbienku sannan ya dawo nan daga nan mu wuce Canada mu wuce Yemen..."

Cikin jin wasu sabbin hawayen na ce.

" To Ammie kenan ana nufin ni duk ba da ni za'a yi wannan ba?"

" Eh to, gaskiya da farko komai dake muka tsara shi, to amma yanzu kinga ga condition ɗin da kike ciki, ba zai yi yu muyi wannan jiganiyar da ke ba..."

Ai ni kam na yi nisa sosai domin kuma nake mata tamkar wata ƙaramar yarinya. Babu abin da yazo min a rai sai son yin tozali da Sheikh da su Mummy Lina. Sannan ina so in ƙara ganin gidanda aka haifeni na yi wayo a cikinsa na rayu da Mahaifina...tabbas na so sake ganin wannan gidan koda sau ɗaya ne a rayuwa ta.. Ganin da gaske nake duk abinda take faɗa min ba ganewa nake ba,yasa ta dawo rarrashina tana faɗin.

"Ki yi haƙuri, idan kika haihu na yi miki alƙawarin zan kai ki gidanmu, gidan mahaifinki har abada ba zan taɓa siyarda shi ba, yana nan za'a bar shi, duk sanda wani daga cikinku yake da ra'ayi da muradi zai iya zuwa ya buɗe ya shiga. Amma yanzu dan Allah Beenafah ki yi haƙuri ba zan iya wannan tafiya da ke ba, su ma su Hajiya Sameera kiyi haƙuri ki bari sai idan kin haihu, in sha Allahu za ki zo ki gansu watarana, kasa ki damu na riga na faɗa musu condition ɗin ki, saboda haka they won't expect you now sai dai Idan kin dawo watarana..."

Ta shi ta yi ta je ta ɗauko wannan file ɗin ta buɗe tana mini bayanin komai yanda yake tiryan-tiryan har muka kambala.

" To Ammie ba ance har wannan gidan sun siyar ba?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

" Mun nemo wanda ya siye daga baya muka mayar masa da kuɗinsa bayan mun yi masa bayanin yanda gidan yake. Sannan ashe ban faɗa miki ba, cewa Labiba ce ta shigar da shi ƙara, amma Ahlan ne ya shirya masa komai ya je ya yi ta yawo har ya samu aka yi nasarar rufe komai na Alhaji Mudassir ɗin wanda ya ce mini ya fi shekara biyar yana wannan aikin a hankali har ya yi nasara daga ƙarshe."

Cike da mamaki na ce.

" Ammie Ya Ahlan fa kika ce? Mijin Aunty Aysha?"

"Ƙwarai Beenafah. Ahlan ya yi hakan ne ba don komai ba, sai don amanar da ke tsakaninsa da mahaifinku, shi ne fa ya ɗauki nauyin karatunsa, shi ne wanda ya shiga ya fita har ya sana masa aikin da yake a London sannan kuma ya aura masa Aysha."

"Allah sarki! Lallai Ya Ahlan ya cika ɗan halak! Allah ya ƙara dafa masa a cikin rayuwarsa."

"To Amin. Yanzu haka yana can tare da Dr. Domin shi ne yasan kan komai yanda yake. Duk abun da ake ciki, In Sha Allah, I will keep you updated.."

Miƙewa na yi na je na ɗauko ruwa na dawo na zauna sannan na buɗe ina faɗin.

"To ya jikin Daddy?"

"Jikinsa da sauƙi, an yi nasarar fitar da shi jiya, sun tafi tare da Ita Zalihar da Hafiz."

"Eyyah! Allah ubangiji ya bashi lafiya yasa a dace."

"Amin amin."

Muna nan muna fira sai ga su Aunty Ayshar sun zo gabaɗayansu. Nan muka zauna muka sake buɗe wata sabuwar chapter har magariba sannan muka tashi muka yi sallah. Bayan mun kambala na yi musu sallama na fito na cimma sa muka gangara gidan su Fakiha kamar yanda na roƙa. Amma dai cewa ya yi zai tsaya a ƙofar gida na shiga na fito mu wuce.

Da wata irin fara'a na shiga gidan, ganin yanda aka gyara shi ya burgeni sosai,an gyara an saka musu ƙofafi da glass windows an yi Fenti Kamar ba shi ba. Koda na shiga na tarar da Ya Jafaru zaune akan kujera da plate a gaban sa yana cin abinci. Muna kaɗa ido ya wani dire cokalin ya tashi kawai ya fita ba tare da ma yayi mini magana ba,ganin hakan yasa na yi masa banza tamkar ban gansan ba kawai na wuce na shige ɗakin Mama. Sai dai kuma, cikin rashin sa'a sai gashi ban tarar da Baban ba. Gaisawa muka yi da su wanda daga ita sai Fakiha da kuma Farisa ne zaune suna kallo a TV.

Dariya Fakiha ta yi sannan ta kalleni ta ce.

"Beenafah kin ga Ya Jafaru a waje?"

Girgixa kaina na yi alamar a'a, domin ba ƙaramin bani haushi ya yi ba na ce.

"Ban gan shi ba..."

"Hmm! Ke dai mi zan faɗa miki? Ranar nan da muka dawo daga gidanku Ya Jafaru ba sai ya haukace mana ba, sai bala'i yake yana ɗorawa su Mama Laifi wai da gangan sukai masa baƙin ciki suka hana a bashi ke...abu wasa-wasa fa ya nemi ya wuce wuri. Mama sai bala'in faɗa take masa amma fir! Haka ya shafawa idonsa toka ya haƙiƙance yana ta wani faɗan rashin gaskiya...."

Tsawa Mama ta daka mata da faɗin.

"Ke Fakiha! Wane irin shashanci ne wannan? Mi ye za ki zauna kina wani faɗa mata zancen banza haka?"

Miƙewa na yi tsam! Ina mai yin murmushi na ce.

" Allah ya kyauta to? Ni zan tafi sai da safenku...ina gaishe da Baba idan ya dawo."

" Tow Beenafah, Allah ya bamu alheri. Mun gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."

Da amin suka amsa sannan na fito na nufi ƙofar fita, tsoro ne ya kamani ganin akwai Nepa amma zauren da duhu,kuma lafiya ƙalau na wuce shi yanzu da Bolb ɗin shi amma ji wai ba Nepa..

Wata iriyar damƙa ce na ji an kaiwa hannuna wanda ban san lokacin da na buɗe baki domin nufin ƙwallara ƙara ba, amma haka yasa ƙarfinsa toshe min baki da ɗan sauran hasken fitilar ƙaramar wayarsa. Duk da cewa bana ganin sa sosai, ina iya hango yanda Fuskarsa ta wani rine da yanayin matsanancin fushi.

"Wato ke gaki kin je ƙasar waje ko? Ni za ki butulcewa ki je ki auri wannan tsohon saboda kuɗi..."

Cizo na gartsa masa a hannu, sai gashi ya sake ni ba shiri yana mai yarfe hannun cikin wani irin ɓacin rai na ce.

"Ya Jafaru ashe kai ƙaton Wawa ne wagili ban sani ba? Kana cikin hankalinka kuwa...??"

"Ai dole ki ce haka, tunda kin ci amana ta kin je kin auri wani ba ni ba..."

"Ni ban ci amanar ka ba, domin ban san ma mi kake magana a kai ba, tun da muke da kai dai kalmar soyayya bata taɓa shiga tsakaninmu ba ballantana maganar aure ta shigo."

Girgiza kansa ya yi tare da zubo da wasu irin zafafan hawaye ya ce.

"Ai ke ba mahaukaciya ba ce Beenafah! Kin fi kowa sanin cewa son ki nake..da farko na ɗauka cewa da gaske Alhaji Mudassir auren dole ya miki. Ashe ke ɗin munafuka ce mai fuska biyu. Ki rasa wanda za ki aura sai wancan tsohon wanda bai da lokacin ki sai na lissafin kuɗi, daman su kika aura, sai ki je ki yi ta zaman wahala....ina so ki faɗamin Beenafah dan Allah mi na rasa? Mi na rasa da har kika zaɓi wancan banzan..."

Tas! Haka na sauke masa wani marin da ban san ma lokacin da zuciyata ta rufe da har na ɗauki hannu na zabga masa tafin ba. Ban taɓa jin cewa na tsane shi ba sai yau. Wani irin wulaƙantaccen kallo na watsa masa sannan na ce.

" Banza! Jahili wanda bai san ƙaddara ba. A yanda ka ɗauka cewa wai auren kuɗi na yi...to shi na yi Ya Jafaru. Idan kana da yanda za ka yi dan Allah kada ka barni na kai gobe a gidansa. A yanda ka jahilci abin....to mu tafi a haka. Na zaɓe shi , kuma shi na ke so shi ne wanda nake ƙauna. Sannan Na gode Allah da ya kareni daga sharrin ka...Ina so ka sani, Wallahy! ko maza sun ƙare a duniya har abada ba zan iya auren ka ba. Banza shashasha. Kuma idan ka yi yunƙurin sake taɓa ko da gefen mayafina ne...wallahy tallahy sai na sa Mijina ya ɗaure ka...kai! Idan ma aka ɗaureka ai an raga maka, ratayeka zai sa a yi kai tsaye tunda baka da ƙwaƙwalwa a cikin ka. Na tsane ka...na tsaneka Jafaru tsana ta har abada. "

Daga haka na wuce fuu! Na bar shi nan a sanƙame da al'ajabina, domin sam bai yi tunanin zan iya yi masa wankin babban bargo har haka ba.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️

*GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 50*

A daidai bakin ƙofar shigowa Zauren daga cikin gidan Fakiha ta yasar da ledar turaren ƙamshin da Mama ta bata ta kawowa Beenafah bayan ta gama sauraren duk abinda yake faruwa ta koma da gudu ta faɗawa Mama.

Ba shiri ta iso zauren hankalinta a tashe domin ko takalmi babu a ƙafarta, jiki na rawa ta lalubo inda switch ɗin zauren yake ta kunna sai ga Jafaru ta gani tsaye ya jingina bayan sa jikin bango tare da harɗe hannayensa akan ƙirjinsa yana ta wani huci tamkar zuciyarsa za ta fashe saboda ƙunci da takaici.

A zafafe ta ce.

"Wai kai wane irin Yaro ne Jafaru? Uhm! Wace irin zuciya ce Allah ya yi maka haka?..."

"Ni wallahy Mama kawai an cuceni, kuma har abada ba zan daina son ta ba, dole ta rabu da shi ta dawo ta aure ni, saboda Beenafah tawa ce..."

Wasu tagwayen maruka ta sauke mishi a lokaci ɗaya hankalinta a matuƙar tashe ta ce.

"Wallhy! Wallahy Jafaru ka kiyayeni ka kuma kiyayi fushina! Wai kai wane irin yaro ne marar lissafi? Kaga fa ka rufa mini asiri ko Ince ka rufa mana asiri ka fita harkar matar mutane. Wallahy Mutumin nan idan ya ɗaure ka babu wanda zai iya amsoka gare shi. Ka ɗauki ƙaddara, daman can ita ɗin ba matarka ba ce. Muna zaune lami lafiya da iyayenta waɗanda suka kasance masu mutunci da karamci, tunda idan ba dan Allah ya sanyo su a cikin rayuwarmu ba har ta bamu waɗannan kuɗaɗen da ina za ka samu shagon zuwa har ake biyan ka? da kuma tura maka kuɗi idan kana makaranta? Ka yi haƙuri ka mayarda hankalinka a shago da karatunka, In Sha Allahu za ka samu wata wacce ta fita"

"Ni Wallahy....Wallhy! na rantse da Allah ba zan ƙyale mishi ita ba, sai ya sake ta. Ba zan haƙura ba wallahy.."

Daga haka ya yi fuu! Ya nufa ci hanyar waje cike da takaici da baƙin ciki.

Murya Maman ta ɗaga hankalinta a tashe tana faɗin.

" Jafaru! Jafaru! Jafaru kiran ka nake...ka raba kanka da wahala ka manta da Beenafah."

Har wajen ta bishi tana kiran sunan shi, amma ko kaɗan bai saurare ta ba, haka ya miƙe ba tare da ma sanin ina ya nufa ba. Zuciyarsa na yi masa wata irin azalzala da gobarar Son ta, shi sai yanzu ne ma yake ƙara jin wata sabuwar ƙaunar ta da sonta wanda bai ji zai iya rayuwa da wata ɗiya mace ba idan ba ita ba.

Cikin gida suka koma daga Maman har Fakiha mamakin duniya ya ishe su. A raunane ta kallin Maman ta ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull