Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 60

Ganin ido complete - Chapter 60

Ganin ido complete Chapter 60: Ganin ido complete Chapter 60. "Wai an ya Mama Ya Jafaru yana cikin hankalin shi kuwa? Riƙeta fa ya yi....ina jin irin…

3,344 words

"Wai an ya Mama Ya Jafaru yana cikin hankalin shi kuwa? Riƙeta fa ya yi....ina jin irin maganganun da yake ta gasa mata masu zafi kamar wanda aka ce ta yaudare shi...wallahy hankalinta ya tashi sosai domin har da marin shi ta yi...Allah yasa dai kada ta faɗawa Mijinta ko Ammie..."

Hankalin Mama ne ya ƙara tashi jin irin abubuwan da Fakiha ke faɗa mata, nan take ta sake miƙewa tsaye tana faɗin.

" Na shiga uku! Miƙomin wayar nan in kira Babanku...Jafaru ya fara wuce gona da iri. Gwanda a taka mishi burki tun yanzu.."

Wayar ta miƙo mata ta kira shi tace ya dawo gida....nan ta yi mishi bayanin komai nan take yace yana nan zuwa.

*******

Ni kuwa, koda na shigo motar ko gani bana yi sosai akan yanda zuciyata ta rufe da baƙin cikin Ya Jafaru. Dama ashe akwai irin waɗan nan mazan a rayuwa? Waɗan da ba su san ƙaddara ba. Na yarda cewa ya so ni can baya, to amma na kasance ba rabon sa ba sai yayi haƙuri ya manta komai. Amma saboda rashin sanin ya kamata shi ne wai har zai iya buɗe bakin shi ya ce wai auren kuɗi na yi har ma ya riƙa faɗin munanan kalamai akan Mijina wanda ya kasance duniyata kuma rayuwata a yanzu.

Dole cikin daƙiƙu na yi ƙoƙarin sai ta kaina domin idan har ya tuhume akan halin da nake ciki a yanzu ban san ta ina zan fara masa ba. Ce masa zan yi Ya Jafaru ne ya tareni har da riƙe ni yana faɗamin maganganun banza ko me? To idan ma ya turkeni akan mine ne abinda Ya Jafarun ke faɗamin nan ma in ce me? Ko kuma in ce Mama ce da Fakiha suka ɓatamin rai? No..! Babu abu ɗaya da zai faru, domin dole na bar wannan maganar a zuciyata ko don zumunci da amanar da ke tsakanin Iyayenmu a yanzu.

Wayar da na tarar yana yi da Jadda ita ce abin da ya ƙara kwantar min da hankalina sai na karɓi Wayar ina mai kawar da fuskata domin har yanzu idanuna da sauran hawaye a ciki amma ba don na manta da abin da ya yi mini ɗin ba.

Nan na shashashace muna ta Waya har da su Suhaib sai dariya nake jin yanda yake cewa wai ko a Keke ne sai an ɗaurani an kai ni bikin sa, tun da ya ji Ya Mohaa yana faɗin bani da lafiya kuma ina buƙatar hutu.

Bayan mun koma gida, sai da muka gama duk wani night routines ɗinmu sannan muka kwanta. Bayan na kwanta a inda ya fiye mini ko'ina sanyi da daɗi, wato saman ƙirjinsa na ji wasu irin sabbin hawaye sun kwararo mini tuna irin wulaƙancin da Ya Jafaru ya yi mini a ɗazu, da mutuncina da komai wai haka ya riƙe ni don kawai yana marar mutunci wanda bai san darajar aure ba.

"Dayaa!"

Na kira sunansa a raunane ina mai ɗago fuskata na kallesa da sauran hasken bedside lamp.

"Bibi! What's wrong? I notice that you are not ok, tun da muka dawo kamar ba ke ba."

" Yaushe zamu tafi?"

Na tambaye shi kai tsaye domin tsoron Ya Jafaru ya yi matuƙar sanyani a fargaba. Tsoro nake kada ya sake riƙeni watarana duk da cewa yana da wahala ya sake kwatanta irin hakan domin naga kamar ya razana da irin gargaɗin da na yi masa. Gabaɗaya sai naji zaman garin ma ya fice mini a rai.

Hannuna ya kama tare da twisting ɗinsa a cikin nasa yana kallona, muryarsa ya kwantar a hankali yana faɗin.

" Gobe da yamma In Sha Allah nake tunanin mu tafi. Ina so mu koma gida domin ki fara ganin likita cikin lokaci, kuma kina da buƙatar ki huta, idan kina nan ba za ki daina yawo ba. And nima kin ga ayyuka sun taru a kaina sosai, I need to go back..."

Murmushi na yi masa, a raina ina mai jin tausayinsa sosai akan yanda yake ayyuka ba dare ba rana kullum kamar wani Engine.

" Ba fa wani damuwa. Duk ka wani ɗaga hankalin ka sai wani lallaɓani kake...To ai nima so nake mu tafi."

Dariya ce ta suɓuce masa ba tare da ya shirya ba,domin jin irin yanda na amsa shi abun ba ƙaramin dariya ya bashi ba. Bayan ya tsahirta da dariyar ne ya ce.

" Wato in dai na ma wahalar da kaina ina lallaɓaki domin kin riga kin shirya bin mijin ki..."

Hannu na saka da sauri na rufe masa baki ina dariya tare da runtse idanuna na jin wannan maganar da yake furtawa. Yanzu daga yin magana ta har ya juya mata fassara zuwa wani abu daban.

Lafewa na yi wanda ina jin sa yana ci gaba da tsokanata har bacci ya sace ni ban ƙara yi masa magana ba.

Washegari muna zaune muna breakfast sai ga kiran Aunty Labiba tana shaida masa cewa Aunty Ziza ta haihu ta samu ɗiya Mace. Warce wayar na yi cike da zumudi ina ta faɗin Allah ya raya gamu nan zuwa.

Kallona ya yi bayan na ajiye wayar ya ce.

"Gaku nan zuwa a ina? Kin manta yau ne zamu tafi.."

Jikinsa na kwanta a hankali tare da shagwaɓe murya na ce.

"Ni dai dan Allah ka tafi to ka barni,daga baya idan an yi sunan sai ka zo mu tafi.."

"Me ne? In bar ki ki zauna don ki wahalar da kanki da kuma Babynmu Bibi? No..! gaskiya ban amince ba..."

"Eyyah! Please please! Dan Allah mana!...bai kyautu ace an yi haihuwar nan muna gari ba kuma mu tattara mu tafi...atleast ko don kasancewar Matarka karon ta na farko a cikin hidimar gidanku ya kyauta ace na tsaya...and Emraan will be happy ace matakar tana nan a hidimansa, su Aunty Labiba too..please!"

Jin ya yi shiru bai ce komai ba yasa na ɗago na kallesa tare da kama hannayensa na kwantar da Murya na ce.

" Na san ka fini sanin abin da ya kamata Mijina..tunani, hankali, da sanin ya kamata duk ka fini sam ba za'a haɗamu ba. Ban isa na zartar da hukunci ba domin kai ne shugabana kuma kai ne kake gaba da komai. Amma tunanine na yi da ganin kamar hakan zai yi amfani, domin ta hakanne ƙannenka za su ƙara ji a ransu cewa ka zubar da komai ya wuce, Hajiya ma haka. Idan kuma kaga tafiyar tamu yafi ba damuwa za mu iya tafiya..."

Kallona yake a hankali jin irin maganganun da nake furta masa. Sosai ya ji manganuna sun shige sa domin ban taɓa neman sa alfarma irin wannan ba sai a wannan karon. Idan ya ƙi ya amince kuma hakan har abada ba zai barshi ya samu sukunin zuciya ba. Tunanina da iya maganata suna ƙara sanya shi jin akoda yaushe cewa ni ɗin dai ni ce nafi dacewa da rayuwar sa sama da kowace a duniya....

"Ka ce wani abu mana dan Allah..."

"Bibi...lafiyar ki da ta jaririnmu sun fi mini komai muhimmanci a yanzu..."

"In Sha Allahu babu abin da zai same ni. In Sha Allahu Allah zai tsare maka ni a duk inda nake a faɗin duniyar nan, and I promise zan kula maka da kai na sosai da kuma Babynmu babu abin da zai same mu.."

Cikin yarda da kalamai na ya jinjina kansa sannan ya ce.

" Yau wace rana ce?"

Da sauri na ce.

" Saturday ce."

"To zan dawo Sunday, Monday mu wuce..."

Rungumeshi na yi tare da kwararo masa addu'o'i da kuma yi masa kalamai sannan na janye daga ƙarshe ina kallon sa ina murmushi na ce.

"And saura naka alƙawarin da za ka ɗaukar min.."

"Na me kenan?"

"Cewa za ka yi..Ni Mijin Beenafah, Abban Babynmu mai zuwa, I promise to take care of my self kamar yanda Bibina ta yi alƙawarin cewa za ta kula da kanta da Babynmu, zan riƙa cin abinci cikin lokaci, sannan zan yi bacci ma cikin lokaci, kuma na yi alƙawarin rufe idanuwana daga kallon kowace irin Mace koda ta Kara ce...."

Dariya ya shiga yi sosai wanda sai da yaga na ɗan ɓata fuska sannan ya daina yana mai rungumoni zuwa Jikinsa ya maimaita min duk abinda na ce masa ba tare da gargada ba sannan daga ƙarshe ya ce.

"Bibi! Ki yarda da magana ta, duk wata Macen da za ta tsaya a gabana idan har ba ke bace to ni a wurina ba Mace ba. Ke ce komai tawa Bibina...ban san yanda zan iya rayuwa da wata Macen a duniyar nan idan ba ke ba. Ina ƙaunar ki sosai.."

"Uhmm! Ni ma haka fa. Sosai nake son ka,.."

Mun jima a zaune muna ta shan nishaɗin soyayyarmu sannan daga ƙarshe muka tashi muka koma ɗaki muka ɗora sabon zama wanda sallah kaɗai ke tashinmu. Sai kusan 5pm muka fito har Biba muka wuce gidan Hajiya Inda Aunty Ziza take.

Sai da ya gama ganin Babyn sannan na rako shi tare da Aunty Labiba muka fito har bakin mota sannan ta Juya ta koma. Duk budurin nan da muke ban ji hankalina ya tashi ba sai da ya shiga mota zai wuce.

Motar na shige na zauna tare da ɗora kaina a gefen shoulder ɗinsa na fara rera masa kuka..a ruɗe ya juyo da fuskar sa yana kallona ya ce.

"Subhanallah! Miye kuma na kuka?ko kin fasa zaunawa Mu tafi?"

Saurin haɗiye Kukana na yi ina mai jinjina kai na na ce.

" Ni fa bana son ka tafi ka barni.."

Kallon Drivernsa ya yi ya ce.

"Mu tafi kawai Sidat..."

Waro ido na yi da sauri na ce.

"Ni fa ban ce mu tafi ba.."

Dariya ya yi sannan ya girgiza kansa ya ce.

"Bibi rigima...ba za ki je ba, kuma bakya son na tafi na barki...to ki yi haƙuri kinji.. Ni ma ba don na so hakan ba. Amma In Sha Allah kamar gobe ne.."

A hankali na kai bakina na haɗe da nasa na yi kissing ɗinsa har zuwa wuyansa still da ruwan hawaye a idona na janye ina kallon sa na ce.

" Allah ya tsare min gabanka da bayanka. Allah ya taimakeka ya biya maka buƙatunka na alheri."

"Amin Bibina..na gode sosai."

Fitowa na yi daga motar still ina yi ina share hawayena har na koma cikin gidan. Ɗakin Aunty Ziza na sake komawa inda na tarar ida ita zaune ita kaɗai tana kiran su Munira wai su zo su canjawa Baby Pampers ta yi kashi. Karɓar ta na yi kai tsaye na shige na wanke mata na dawo da ita na zauna na canja mata diaper ɗin da kaya sannan na rungumeta a jikina tare da janyo wayata na lalubo numbern Ammie na kira ta.

Duk wayar da nake tana nan zaune da wayar ta a hannu tana chart amma kuma hankalinta yana kaina.

Ina nan ina magana a wayar sai ga Aunty Labiba ta shigo. Wuri ta samu ta zauna suka ci gaba da magana da Aunty Ziza, bayan na kambala na biye su muka ci gaba da firar har aka kira sallar magriba sannan muka tashi muka yi.

Bayan Aunty Labiba ta wuce gida. Wani Ɗaki Hajiya ta buɗemin tace na shiga, idan kuma ina son na ta ne to in zo mu kwanta. Wato yanda take ta wani nan-nan dani wallahy har tausayi ta bani. Hakan yasa na saki jikina da ita komai na yi kamar bai faru ba. Sannan ni ko Hajiyar ma bana kiranta Momma na dawo ce mata kamar yanda na ji Dayaa yana kiranta, wanda na lura hakan ba ƙaramin farin ciki ya sanyata ba.

Washegari, Ammie da Maman Fakiha a tare suka zo barka har da Aunty Aysha wanda na ji daɗin hakan sosai.

Ba su wani jima ba suka fito na rako su har bakin gate na biyu sannan Mama ta jani gefe ɗaya with a pleading tone ta fara mini magana da cewa.

"Beenafah dan Allah ki yi haƙuri da abin da Jafaru ya yi miki kinji. Dan Allah ina baki haƙuri, In Sha Allahu ba zai sake ba...Tun jiya na tambayi Hajiya Mulaifa numbernki ta turo mini amma na kira baki ɗauka ba. Dan Allah ki yi hak'uri, shirme ne kawai irin na shi amma na yi masa faɗa sosai kuma na ja masa kunne..."

Murmushi na yi mata sannan na ce.

" Ai ba komai, In Sha Allahu ya wuce. Wayata kuma wata ƙila bana kusa ne shiyasa ban lura ba, saboda a silent nake barinta. "

" To ba damuwa, na gode. Allah ya ƙara miki zaman lafiya da kwanciyar hankali."

"Amin Mama, Allah ya tsare."

Daga haka muka yi sallama da su na koma ciki. Wurin su Munira na wuce direct muka sha firarmu sosai sannan na tashi na koma ciki.

Lafiya lau muka zauna tsawon kwanaki uku, wanda na ji daɗin zaman gidan ba kaɗan ba, musamman da Ziza ta sake dani sosai tana ta wani ja na a jiki tamkar ba Zizar da na sani ba. Kwata kwata sai naga ta sauya min, sai yanxu ne nake ganin kirkinta da ake ta faɗin cewa tana da shi, tana da kirki sosai tana son mutane, abun da na fahimta shi ne, tana da matuƙar kishi ne wanda yake rufe mata ido yake sanyata yin wasu abubuwan da ba su kamata ba. Kuma a yanzu ni sam ban ga laifinta ba, domin kishi gaskiya ne, kuma a yanda nake jin kai na a yanzu wallahy komai zan iya yi akan Mijina.

A hankali en uwan Ya Emraan ɗin dana Ziza suka fara taruwa. Shi ma sai wani farin ciki yake ya kasa nutsuwa wanda na fahimci sosai yake cikin farin cikin wannan Haihuwar da aka yi masa. Lafiya ƙalau muka gaisa da shi kamar yanda muka yi a waya lokacin da ya kira Ya Mohaa yayi min ya jiki.

Yanda kowa ya karɓeni ba ƙaramin farantamin yayi ba. Duk wanda ya zo sai sun janyoni suna nuna ni suna cewa ni ce matar Muhammad. Addu'ar da suke min itama ba ƙaramin farantamin take ba wanda tsakanina da su sai son barka.

Aunty Nadeeyah ta yi takaicin rashin zuwan ta domin Babansu Dija yace tunda akwai aure nan kusa ta yi haƙuri ta bari sai lokacin ta zo.

Dangi Hajiya suna da matuƙar kirki sosai da kuma nuna kara, Baba Ustaz ma bai zo ba amma Mummy Na'Imatu ta zo ita da yaranta su uku.

Ina nan zaune a ɗakina bayan sallar Magriba ina Azkhar sai ga kiran baƙuwar number na gani, bayan na duba ta a true caller ne naga sunan Maman su Fakiha.

Ina ɗagawa ashe Fakiha ce take shaidamin auren Hafsa wai wannan juma'ar za'a yi. Dariya na yi sannan na ce.

"To Fakiha ni miye nawa?"

Ɓata fuska ta yi daga can ɓangaren tamkar tana a gabana ta ce.

"Haba Beenafah! Hafsa kin san yanda take ƙaunar ki. Wallahy bata san cewa kina gari ba sai shekaranjiya dana sanar mata, kuma ta so zuwa har gidanki ta kai miki kati na ce mata kina gidan Surukanki matar Ƙanin Mijin ki ta haihu. Numbernki kuma na ce mata bakya ɗaukan baƙuwar number. Please ki daure ki zo ko 30mnt ne ki yi. "

Girgixa kai na na yi ina faɗin.

" Fakiha na yiwa Mijina alƙwarin ba zan fita yawo ko'ina ba, ba wai zai hanani ba ne a'a, kawai ya kamata komai mutum zai yi ya riƙa lissafi..amma zan gwada tambayar shi inji idan ya amince zan leƙo ko 30mnt ɗin ne kamar yanda kika ce. Ki bata numbernta ki ce ta kirani, ko banzo ba muna iya riƙa gaisawa koda a what'sapp ne."

"Ok tau, in sha Allah..."

Dariya na yi sannan na ce.

"Oh Allah! Wai Fakiha ashe akwai ranar da za ta zo ki yi hankali ki daina rawar kai??"

Tsaki ta buga tare da kashe wayar baki ɗaya.

********

Jafaru kuwa, duk tsawon kwanakin nan ya kasa zaune ya kasa tsaye, ko baccin kirki baya iya yi gabaɗaya ya zabge lokaci ɗaya kamar wani Naman Miya abin duniya duk ya bi ya ishe sa. Tun jiya ya kamata ace ya koma makaranta amma sam ba wannan ne a gabansa ba, tunda har Beenafah tana garin to wallahy sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi. Tunanin ta da soyayyar ta sun hana masa sukuni, komai yake ita yake gani a idanunsa.

Duk kwanakin nan yana yawan zuwa gidan su wani babban abokin sa Baba Kali amma baya samun shi a gida sai yau ne ya ci sa'a ya tarar da shi.

Baba Kali na ganinsa ya ce.

"Wai daman baka koma Zaria ba Jafar?"

Wuri ya samu a bencin da Baba Kali ɗin yake zaune ya zauna yana faɗin.

"Mts! Ka bari kawai abokina, komai ya kwance mini.."

"Kamar ya kenan? Ba kuɗin registeration ne?"

"Ba shi ba, zance ne akan Beenafah.."

Waigowa ya yi suna fuskantar juna da kyau ya ce.

"Miye ya faru da ita Beenafahr? Ba ka ce an aurar da ita ba?"

Tamkar zai fashe masa da kuka haka ya shiga bashi labarin komai da yake faruwa da abin da ya wakana sannan daga ƙarshe ya ce.

"Wallahy Kalifa ba zan haƙura ba. Ina son ta, kuma ina ji a jikina ita ce Matata..."

Jinjina kai Baba Kali ya yi sannan ya ce.

"To ai kaima dai Jafaru ka yi wauta tun farko da ka bari wannan santaleliyar yarinyar ta kuɓuce a hannunka. Yanda ka raineta kuka shaƙu ɗin nan ai in ni ne wallahy tallahy ko gidanmu za'a siyar sai dai a siyar amma sai an aura mini ita....sannan da kake mahaukaci waye ya faɗa maka cewa yanzu za ka iya janyo ra'ayinta ta ƙarfi? Kuɗi fa aka ce maka Jafaru. Kuɗi manya-manyan kuɗi ba ƙananu ba. To idan baka kwantar da kai ba ta ya ya za ka samu ta dawo hannunka?"

Wani irin abu yaji ya tartsa masa a zuciya wanda sai yanzu da Kalifan ke wannan maganar ya ji dama ce tun farko ya haukace musu da gasken, da yanxu Beenafah tana hannun sa. Ƙara marairaice fuska ya yi yana faɗin.

" Wallahy Baba Kali sai ma ka ganta a Yanxu..Yanda ta ƙaro wani irin kyau da wani shape za ka rantse da Allah ba mutum ba ce. Kyaunta ya ƙara bayyana fiye da da, kuma tana nan da halin kirkin nan nata,...kai ko shi kirkin kamar ƙaro mata shi akayi, domin duk daular nan da take ciki ko kaɗan ba sai ta sauya ba...Wallahy Kalifa har yau har abada banga mai kyau Beenafah ba da duk wasu good qualities da ta tara. Rasa ta ba ƙaramin asara ba ne a wurina, ina masifar sonta, son da ba zan iya haƙura ba..."

Dariya Baba Kali ya bushe da ita sannan ya ce.

" Abokina ba dole ka ruɗe ba, Kaga jinin Larabawa, fata tayi kyau sai walwali take, ai dole ka fice hayyacinka.. "

" Don Allah ni dai ka taimaka mini domin in samu yanda zan yi ta dawo gare ni..Kaga numebrn wayan ta nan na ɗauko a waye Mama tun jiya da dare bayan Fakiha ta gama magana da ita. "

Still da dariya a fuskarsa ya ce.

" To ni dai shawara ta guda ɗaya ce, daman can tun farko ai kasan tana sonka..to muddin dai son nan da take maka na gaskiya ne to yana nan babu inda ya tafi. Saboda haka ba da faɗa za ka je mata ba, ka lallaɓa ta ka nuna mata cewa kafi ta ma son abin da take so...ka kwantar da kanka ka lallaɓa ta ka nuna mata irin son da kake mata, In Sha Allahu za ka da ce.."

Wani uban tsaki ya buga tare da Girgixa kai cike da takaici ya ce.

" Wai har da wani ciki take da shi, su kuma sai wani murna suke..wallahy sai na yi maganin su, gabaɗayansu sai na yi maganin su..."

"Uhm to! Ka dai yi a hankali kam, kada kwaɓarka ta yi ruwa,domin idan Engineer ya kama ko wallahy sai ka yi warin mutuwa..."

Tsaki ya buga sannan ya ce.

"Engineern banza da wofi! Mugu kawai mai raba masoya..."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull