Ganin ido complete - Chapter 68
Ganin ido complete Chapter 68: Ganin ido complete Chapter 68. " Ga amanar da ka bani a yau na sake dawo maka da ita, ina neman afuwarka da yafiyarka akan…
3,075 words
" Ga amanar da ka bani a yau na sake dawo maka da ita, ina neman afuwarka da yafiyarka akan gazawata..."
Sosai yake kuka yana girgiza kai cike da nadama ya ce.
"Ya sheikh wallahy babu inda ka gaza. Ni ne nan na gaza, ni ne nan na biye wa zuciya na aikata abin da ya dawo ya dame ni daga baya, na kasa bacci, na kasa ci, na kasa sha. Komai na duniya ya juye mini sama ƙasa Nana Hauwa...haƙiƙa ni ne nan mahaifinki. Wannan kuma ita ce SUMAIHA, ita ce mahaifiyarki da ke da Nana Maryam. Mun yi aure da ita dalilin SAMI wanda shi ne mijin twin sister ɗinta SAMAAHA. Kasuwanci ya haɗamu daga nan sai abota ta ƙullu a tsakaninmu. Yana neman Samaaha da aure nima ya nema mini Sumaiha. Sai da suka shekara goma da aure cif, bisa wani ƙaƙƙarfan dalili sannan muka yi aure mu kuma. daga nan na ɗauke ta zuwa Qatar inda can ne ƙasata inda nake zaune tare da familyna. Sumaiha ta kasance Mace mai tsananin zafin kai da zafin zuciya. Al'adunmu da rayuwar matanmu a Qatar tasha babban da rayuwar al'adun mutanen Sudan. Musamman da mahaifiyata ta kasance jinin sarauta. Dalilin da ya hana mini aure tsawon shekaru goma shi ne ƙin amincewar mahaifiyata da auren Sumaiha, hakan yasa na ce na haƙura da aure matuƙar ba ita ɗin zan aura ba. Sai da taga da gaske na yi shekara goma bayan sun buga sun buga dole daga ƙarshe ta haƙura na auro ta ɗin."
" Bamu shekara ɗaya da aure ba ta ce tana so ta ci gaba da kasuwancinta wanda take yi a nan Sudan ɗin. Na san abu ne mai matuƙar wahala mahaifiyata ta amince, domin harakar kasuwanci ta fita kasuwa mu a garemu na Maza ne kawai ba da mata ba. Matayenmu muna matuƙar ba su muhimmanci da kuma kulle su a cikin gida domin a nan suka fi cancanta, koda fita ta kama ayi, to dole a lulluɓe ko'ina hatta fuska da tafukan ƙafa wacce fitar dole sai idan ta kama babu yanda za'a yi, musamman a zamaninmu abun yafi tsanani sosai. Da Sumaiha ta zo, duk ba ta damu da wannan ba. Ba sa jituwa Sam da mahaifiyata da 'ƴan uwana tunda ta fahimci cewa ba sa sonta. Alhali ba son ta ne ba sa yi ba, halayenta ne basaso. Na sha zaunar da ita na nuna mata cewa, idan har ka je Gari ka isko mutane kowa yana da Bindi (Tail) to kai ma ka yi ƙoƙari ka ɗaura naka domin kada ka fita daban. Amma Sam taƙi ta saurare ni. Itama sai excuses take kawo mini na cewa ba dole sai ta kasance yanda dangina suke ba matuƙar dai ina son zama da ita da gaske. A haka nake daurewa ina rarrashinta ina bata haƙuri a koda yaushe ina goya mata baya saboda ina tsananin ƙaunarta. To a lokacin da ta zo mini da zancen kasuwanci, sai na shaidawa iyayena wanda suka ce sam ba su amince ba, musamman mahaifiyata, abu kamar wasa abubuwa suka yi tsamari sosai wanda na yi ta roƙon Sumaiha akan ta haƙura. Haka ta nuna taurin kai ta hau kasuwanci wanda ni ne dai wanda na ke ji da aikina in kuma ji da kasuwancinta. A haka muka yi ta tafiya wanda ko magana wannan sai ta ga dama take yin ta da mahaifiyata."
"A haka har Allah ya bata juna biyu ta haifi yara mata guda biyu wanda muka saka musu Nana Maryam da Nana Hauwa. Mahaifiyata sam taƙi amincewa ta kalli inda yaran suke ballantana ta ɗauka tace Allah ya yi albarka. Hakan ya yi matuƙar yi wa Sumaiha zafi da raɗaɗi wanda nima ɗin karan kaina ban ji daɗi ba, domin hatta sauran en uwana babu wanda ya zo inda take ita da waɗannan jariran. Ban san cewa tsananin ƙiyayya ya girmama a tsakanin iyalina da dangina ba sai a wannan lokacin. Muna nan dai a haka. Abubuwa basu ƙara lalace mana ba, sai da Sumaiha ta zo Sudan ta koma ta tace za ta buɗe shago a kasuwa. Hmm! Nana Hauwa...Matsalar mahafiyarku a wannan lokacin! Ba ta taɓa yarda cewa tana aikata kuskure ba, ita kullum gani take duk abinda take akan daidai take. Da wannan nima na nuna rashin amincewa ta. Na ɗauka cewa duk tsawon lokacin da muka ɗauka ina goyon bayan ta idan nace ban amince ba za ta yarda ta kuma amince kasancewata na Mijinta kuma shugabanta. Amma a haka ta hau shuka min rashin mutunci ta ce ita sam sai ta aikata. Wasa-wasa abubuwa suka ƙi daɗi a tsakaninmu, tashin hankali da rashin zaman lafiya suka zamto abin yin mu wanda muka kwashe tsawon shekaru biyu a haka. A ranar da ta je kasuwa ta sayi Shago da gaske, a ranar na ce mata sai dai ta zaɓa ko ni ko kasuwancinta. Kai tsaye saboda zafin kai da taurin zuciya ta ce mini ta zaɓi kasuwancinta ba tare da tunani ba."
Girgixa kan shi ya yi tare da haɗiye wani wahalallen yawu ya cire glass ɗinsa ya share guntun hawayensa ya na kallon Ammie ya ce.
" A ranar na ƙaryata soyayya Nana Hauwa! A ranar na cire duk wani abu da na taɓa jin ya taɓa burgeni a soyayya daga zuciyata. Domin haka ta zage a wannan ranar ta ci mutuncina da na mahaifiyata tana faɗin wai duk tsawon shekarun da mukayi bata taɓa jin farin cika ba. Kullum cikin ƙunci take da baƙin ciki. Haka ta dinga kuka ina roƙonta akan kada ta tafi. Amma ta saka ƙafa za ta fita, tana riƙe da hannunki dana Nana Maryam, sai na yi nasarar kama hannun ki na riƙe ki. Duk da cewa na janye ki daga hannunta...ko sau ɗaya bata juyo ta kalle ni ba, da ta kai ƙofa ne na ji nima bata da wani matsayi ko wata martaba a idona da zuciyata, hakan yasa na ɗaga bakina na furta mata kalmar saki. Da hakan ma bata juyo ba, kawai ta wuce ta barni dake. Ko kallon ƙarshe bata ƙara juyowa ta yi miki ba...."
Durƙushe Sumaiha ɗin ta yi a inda take tsaye tana ta wani irin kuka tamkar za ta shiɗe. Tsawon shekarun da ta yi da rabuwa da shi babu watarana da za ta zo ba tare da zubda hawayen nadama ba.
Girgiza kansa ya yi cike da takaici ya ce.
" Ku kalle ta wai kuka take a yanxu! Ta ɗauka cewar duk abinda tayi akan daidaita take. Haka ta bar ni dake tayi tafiyar ta, mahaifiyata kuma, itama tsananin ƙiyayyar da take yiwa mahaifiyarku har da en uwa na, tsanar tana nan bata matsa ko'ina ba. Na ɗauka da Sumaiha ta tafi za su manta da komai su riƙeki da amana. Amma suka shiga azabtar dake tamkar kece Sumaiha ɗin, tamkar basu haɗa wata dangantakar jini dake ba haka suka riƙeki. Ƙarshe da na gaji da ganin yanda kike cutuwa, sannan ba zan iya zuwa Oumdurman ba saboda gani nake idan na mayar da ke wurin ta na nuna gazawa, hakan yasa na yanke shawarar damƙawa sheikh ke tun wata da'awa da yazo a Qatar, bayan ya gama gabatar da darussa na tsawon wata ɗaya tare da manyan maluma, haka na shirya cikin wata shigar ta daban na ɗauke ki zuwa ƙasar Yemen na ƙwanƙwasa gidansa na bashi ke...."
Kuka ne mai tsananin ƙarfi ya sarƙesa tsabar yanda yake jin abin na dukan zuciyar sa. Tsawon shekaru ya kasa mantawa, ya kasa manta ranar da ta saka ƙafa ta baro shi. Ya kasa manta ranar da ya ɗauketa da hannun sa ya kaita gidan sheikh..
Cikin wani irin kukan tausayinsu na kalle shi na ce.
"To amma miyasa ka ɓadda kama Kaka? Miyasa sai a shigar mahaukata kake bayyana a gareta? Shin idan ka bayyanawa Sheikh kanka kana gani ba zai karɓeta ba? Kasan yanda mahaifiyata ta cutu kuwa? Kasan tsayin darare da ranakun da ta ɗauka tana kukan rashin iyaye? wanda kullum take cikin waswasi da ƙuncin cewa shin ta ma wace hanya aka same ta?"
Hannayen shi ya haɗe wuri ɗaya yana mai kallona alamar roƙo ya ce.
" Ban san mafita a wannan lokacin. Ni ɗin na kasance sannannen mutum a faɗin Qatar, abun kunya ne a gare ni abun da Sumaiha ta aikata mini sannan ace hatta dangina sun kasa riƙe mini 'ƴata. Sannan zan yi matuƙar baƙin ciki da takaici idan har watarana Sumaiha ta ji labarin inda Nana Hauwa take, domin idan taje ta ɗauketa ba tare da sani na ba, idan hakan ta kasance yana nuna cewa na faɗi, kuma hakan ya tabbata cewa tayi nasara a kaina. Har na koma ga Allah ba zan daina nadamar auren Sumaiha ba, domin ta nakasa min rayuwa da ta 'ƴa' ƴana...bata rasa komai ba,domin koda ta aureni ni ɗin ina da aiki kuma ina kasuwanci. Babu abinda ta nema ta rasa, lokuta dama na so ace mun samu fahimtar juna ta fahimci wane irin mutum ne ni. Amma ba ta yi hakan ba, ita fa a rayuwa...ba dole sai ka samu abinda kake so ba ɗari bisa ɗari. Rayuwar wannan namiji daban ta wannan daban. Abinda mijin ki zai jure ba lallai mijin wata ya jure shi ba, ɗabi'unki da wasu bururruka naki na rayuwa, idan sun sha bamban da ra'ayin mijinki ya ce baya so, matuƙar ba Allah yace ki saɓawa ba to ki yi haƙuri ki yi biyayya. Tun a wancan lokacin na faɗa miki cewa ni banga wani abu mai wahala a nan ba, zamu iya haɗa kai mu cim ma duk wani mafarki naki ba tare da kin saɓa ra'ayi na ba, amma ba ki saurareni ba Sumaiha, kin rusa farin ciki na, kin mayarda mahaifiyata ba kowa ba. kin raba kan 'ƴa' ƴana. Kalli idanuwana ki gani....akan baƙin ciki da takaicin halin da kika saka ni da kuma abinda na aikatawa Nana Hauwa sai da suka kusa makancewa tsabar kuka da..."
Sai yanzu Nana Maryam wato mahaifiyar Noura ta jinjina kai cike da al'ajabi tana kallon mahaifiyar ta su tana kuka ta ce.
" Daman abin da kike ta ɓoye mini kenan tsawon shekaru Ammah? Kema Jadda ko?"
Sai kuma ta juya gun mahaifin na su shima ta shiga kallon shi da hawaye a idonta ta ce.
"Kai ma Abiyh abunda ka ɓoye mini kenan duk roƙonka da nake ta yi tsawon shekaru??"
Kallonta Ammie ta yi ta ce.
"To amma ke taya kika koma gare shi? Bayan kuma dake ta wuto Sudan ɗin."
"Bayan nayi nasarar haddace Alƙur'ani. Na kambala secondary school, wata ƙawata ta taɓa yi mini gorin mahaifi...da wannan dalilin na turke Ammah na ce sai ta kai ni gun mahaifina, idan kuma ya mutu ta faɗa mini in san halin da nake ciki. Bayan na kwana na wuni ina mata bori ita da su Jadda...nan ta shirya mini suka mini visa da komai ta ɗorani a jirgi da address...ta hakan na isa gun mahaifina wanda ya kwana yana kuka da ya ganni. Sam ban samu karɓuwa daga danginsa ba sai kaɗan daga cikin su ne suka karɓeni. Ban sha wata wahalar su ba wanda ban sani ba ko don na je da girmana ne oho! Mahaifina ya nuna mini soyayyar da naji cewa na yi nadamar rashin kasancewata tare da shi tun farkon fari. daman na ɗauke har takardun wanda Ammah ba ta sani ba,hakan yasa ba jimawa ya nema mini makaranta na fara, iyaka idan na ƙarasa semester ɗaya ya mini aure da wani yaron abokinsa, mai suna Abdulmajeed. Na yi mamaki da babu wani labari ko ta mafarki akan Ammah tunda naje, idan na tambayeshi sai yace za ta dawo itama watarana. Sai da na haifi Noura sannan na zo Oumdurman da ƙyar wanda bai amince na zo nika ɗai ba sai tare da mijina, ya ce kuma ya zauna a nan na gama duk kwanakin da zan yi mu koma a tare..Abiyh baya bari ko 'ƴa' ƴana su zo Oumdurman su zauna sam bai amince ba. Na bi duk hanyar da zan bi domin na kamo kan matsalar daga shi har Ammah babu wanda ya bani haɗin kai...yanzu ina amfanin hakan? Na ce ina amfanin hakan da kuka salwantar da rayuwarmu akan ra'ayoyinku na son zuciya musamman ma ke Ammah..!!!"
A hankali na je na rungume mahaifiyar Noura domin yanda take kuka na tashin hankali ba ƙaramin tausayi ta bani ba...kai dukkan su babu wanda ba abin tausayi ba musamman Abiyh wanda shi ne ma wanda ya fi kowa cutuwa.
Maimakon Ammie taga laifin Mahaifinta? Sam ba hakan ta faru ba, laifin gabaɗaya ta ɗauka ta ɗora akan mahaifiyarta da dangin ta ne wanda ta yi mata wani kallon tana faɗin.
"Ke ce wacce kika haifeni...sam shekaruna da tunanina ba su kai na ki ba. Amma dai na san cewa, muddin dai uwa ta amsa sunanta na uwa! To tabbas rayuwar 'ƴa' ƴanta musamman idan suka kasance mata, rayuwar 'ƴa' ƴanta ya kamata ace ta fara ɗauka a matsayin babbar matsalar rayuwarta, wacce za ta iya haƙura da komai matuƙar ba kaucewa Allah ba ne aka ce za'a ɗora ta a kai. Kin zaɓi ra'ayin ki, kin zaɓi kasuwancinki akan mijinki da 'ƴa' ƴanki, bayan Allah da kansa ya kai darajar miji ƙololuwa da har yace da zai ce wani ɗan Adam ya yi Sujada wa wani...da tabbas ya umurci Mataye da su yi wa mazajensu Sujada....Aljannar mace tana tafin ƙafar Mijinta...da roƙo da komai ya dinga roƙonki, amma haka kika saka ƙafa kika bar shi. Sannan yanxu har kike iƙirarin cewa ya ci amanar ki? Anya kinsan wane matsayi mutum idan ya taka ake kiransa uwa kuwa?? Mahaifinmu bai aikata kowane irin kuskure ba...ke ce kika bar ƙofar da wannan ɓaraka ta samu gindin zama Ammah. Hmmm! Koda yake ba zan yi mamaki ba,domin son zuciya da nuna son kai a jinin ku yake...domin a gabana er uwarki ta faɗawa 'ƴata muna nan kalamai akan Mijinta wanda ko condition ɗinta bata duba ba..."
"Ammie please..."
Na ambata da sauri ina mai rufe mata baki da hannuna tare da girgiza mata kaina alamar ta daina.
"Beenafah ki barta...ki barta ta sauke duk wani abin da take jin ya tokare mata zuciya! Tabbas ni ɗin na ruguza kaina a matsayina na uwa, na kasa sauke nauyin da ya rataya a kaina. Na rabu da mahaifinku ba tare da ya yi mini laifin komai ba. Tabbas ya yi iya abinda zai iya wurin ganin cewa ban nemi wani abu na rasa ba. Ni kuma na yi nisa sosai, wani abu nake hange mai nisan gaske....to amma na cim ma wannan abun kuwa? A'a! Ita ce amsar, domin daga lokacin da na watsar da gidana tun a wannan lokacin rayuwata ta samu giɓi. Hatta iyayena da dangina ban faɗa musu gaskiyar rabuwarmu ba. Tun ina saka rai da tsammanin cewa watarana zai dawo gare ni, har ta kai ga na cire rai,domin ya yi fushi mai tsanani. bayan wannan zunubin da na aikata, hakan bai ishe ni ba, da naga cewa tabbas ba zai dawo ba, naji SAMI na gama da iyayena akan cewa zai je Qatar nemansa...a lokacin ne na buɗe baki na juye maganar da cewa shi ne wanda ya wulaƙantani ya koreni yace na tafi ya sakeni,kuma har abada baya so ya ƙara ganina, Nana Hauwa Ita ya ɗauka yace na tafi da Nana Maryam ya yafeta har abad..."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Kalmar da kowa ya ɗauka a ɗakin kenan jin wani irin labari na ban mamaki wanda Hatta Jadda sai da ta girgiza. Haƙiƙa biri yay kama da mutum. Sumaiha bata da wani aiki sai kuka, ta ƙaratar da tsawon rayuwarta da sadaka da kuma ciyar da marayu, aikinta kawai shi ne ibada. Maganarta ɗaya ce, kullum a roƙa mata ubangiji ya yafe mata kuskurenta. Ashe shi ne wannan kuskuren? Taƙi ta yi aure tsawon lokaci tun rabuwarsu har tsufa ya kamata, duk tsawon shekarun nan cewa take ta gama aure a duniya.
Sosai maganar ta girgiza duk wanda yake ɗakin.
Sai a yanzu ne Jaddi ya iya kallonta rai babu daɗi ya ce.
"Ashe kece da laifi Sumaiha? Ki ka rabani da abokina aminina tsawon lokaci? Ina ribar da kika samu a yanzu?"
Ba tare da ta Ƙarya ta ba tace.
"Ni ce SAMI! Dan Allah ku yafe mini. Na tsufa, har na kai ga jikoki amma ciwon da yake raina ko kaɗan bai ragu ba tsawon shekaru. Daga lokacin da mutum ya ɗora rayuwarsa akan wani burin da yake ƙoƙarin cim mawa, musamman ga 'ƴa Mace....to tabbas yana da buƙatar goyon bayan mijinta ko iyayensa akan wannan al'amari, idan ya bijire yace shi lallai sai ya cika wannan mafarkin ta kowace fuska to tabbas zai ƙare a danasani. Kamar dai ni ɗin nan. Na nuna taurin kai da hawa dokin fushi dokin zuciya, wanda nake ganin ko da mijina ko babu shi zan iya cika mafarkina, ba tare da la'akari da irin ƙoƙarin da yake a kaina ba. Ya jure sosai akan irin tsananin da mahaifiyarsa da danginsa suke masa a kaina, a kullum cikin bani haƙuri yake akan cewa in yi haƙuri watarana komai zai wuce. Sai na ɗauka kamar labarin tatsuniya ne domin hakan har abada ba zai samu ba, hakan yasa ganin sun uzzura mini ni ma na yanke rabuwa da shi domin ba za su taɓa sona ba, sannan tunda har ya kai ga cewa na zaɓa ko shi ko kasuwancina to tabbas watarana shi ma ɗin zai iya juya mini baya. A lokacin ƙuruciyata, ni sam ban yarda da yin shawara da kowa ba, domin ra'ayina daban da na wani, abinda zuciyata ke so da hasashe,...ba lallai sun yi daidai da ra'ayin wani ba. Na taso da wata irin rayuwa ta daban wanda sam daga ƙarshe bata amfane ni ba. Babu wata rana da za ta zo ta wuce ba tare da naji kewar mijina da 'ƴa' ƴana ba, na yi ta saka rai da burin watarana ya dawo gare ni, amma bai dawo ba. Nana Maryam ma da nake gani in ji sanyi....tunda taje garesa bai sake bari ta zo gareni ba. Ni ce na ɓata komai, na yarda ni ce. Dan Allah ina neman yafiyarku da gafararku, dan Allah Abubakar ka yafe mini. En biyu na dan Allah ku yafe mini..."
Kamar wani haɗin baki dani da Noura muka yi saurin isa gareta muka rungumeta. Ɗagowa na yi ina share mata hawayenta nima ina kukan na ce.