Kenza eBookz

Ganin ido complete - Chapter 69

Ganin ido complete - Chapter 69

Ganin ido complete Chapter 69: Ganin ido complete Chapter 69. " Haba Ammah dan Allah! Kada ki tsaurarawa kanki da yawa, a matakin shekarunki, idan kika ci…

3,358 words

" Haba Ammah dan Allah! Kada ki tsaurarawa kanki da yawa, a matakin shekarunki, idan kika ci gaba da kuka haka, wani abu zai iya faruwa dake. Na san ai za su yafe miki...tabbas za su yafe miki. Duk wanda ya aikata kuskure kuma ya nemi afuwa ya kamata a duba masa a manta da komai. Da ace abubuwa ba sa wucewa a rayuwa to da har abada zamu ci gaba da kasancewa a tsagin da rayuwa ta zaɓa mana kenan, wanda walau na farin ciki ko kuma na baƙin ciki. Da ke da Abiyh dukkan ku kowa yana da laifi, ke kin nuna taurin kai shi kuma ya nuna tsananin fushi, wanda da ace baki nuna taurin kai da nuna isa ba, da yanxu rayuwarku ba ta ƙare a haka ba, shi kuma da ace bai nuna zafin fushi da rashin yafiya ba, da yanxu kuna nan a tare, domin da ace ya haƙura ya biyo sawunki, tabbas a yanda zuciyoyinmu suke da taushi mu mata, da tabbas na san za ki iya ajiye ƙudurinki ki bisa ku koma. Rayuwar nan idan har bama fahimtar mazajenmu, bama ɗaukar matsayinsu da girman da Allah ya basu da muhimmanci, to fa tabbas suma za su fito mana da wata fuskarda bamu taɓa sani cewa suna da ita ba watarana. Abu na ƙarshe ni dai da zan faɗa a matsayina na ƙarama sosai a cikin wannan wurin,mu riƙa uzuri wa juna muna yafiya, sai wani abun ya faru a rayuwarmu muke samun damar wani abin. Ban rayu da mahaifina lokaci mai tsawo ba. sannan ɗan uwansa jinin sa ya cutar damu ni da mahaifiyata da ɗan uwana. Mun ɗauka a wannan lokacin cewa wata ƙila a hakan ƙaddararmu ta zo kuma a hakan zamu ƙare...but da ubangiji ya tashi sauya mana rayuwa..sai ya juya mana tamkar wani ciwo bai taɓa samuwar rayuwar tamu ba..."

Cikin jin wata irin ƙuna Sheikh ya kalli Ammie yana zubar da hawaye ya ce.

" Mulaifa halin da kika kasance a ciki kenan? Kai co na! Kai Co na! Sai da na ji a raina kamar ban amince da wannan mutumin ba a lokacin da kika kawo shi gareni...sai dai yanda kika nuna ƙauna a garesa sai na haƙura na kuma yi addu'a, ashe duk da haka ban damƙa ki a hannun da ya dace ba. Ki gafarce ni dan Allah..."

Jinjina kanta tayi a hankali tana kallon fuskar sa ta ce.

" Kada ka taɓa jin cewa wai baka yi daidai ba don ka aura ni ga DR. Bello Sheikh. Tabbas ko kaɗan ba ka yi kuskure ba, domin ka aura mini mutumin da ya dace. Wallahy ya so ni ya kuma riƙeni cikin aminci, wanda ina fata da addu'ar A koda yaushe Allah ya tasheni tare dani da shi a Aljanna. Domin shi ɗin miji ne kuma shi ɗin uba ne. Mutuwa ce wacce tayi mana tsakani, ita ce tayi mana gaggawa a tsakaninmu.....Hmm! na ga lokacin sallar magariba ya ƙarato, ya kamata muyi sallah sannan na ɗora muku yanda na rayu."

Daga haka kowa ya tattara jiki sanyaye aka watse. Nana Maryam, Ammie na ta bi zuwa masaukinsu cike da kewar juna suna ta labari suna farin ciki gwanin tausayi. Gidana na nufa tare da Aunty Nadeeyah, ina ta bata labarin abinda Jadda ta mini kafin zuwansu, muna nan bayan na yo alwala, ina fitowa na taradda Noura ta shigo.

Kallonta na yi kamar yanda itama take kallona sannan daga ƙarshe ta yi mini murmushi ta zo ta rungumeni tana faɗin.

"I'm sorry sis...I'm really really sorry. Dan Allah kada ki riƙeni da komai, wallahy sam bani da ra'ayin auren mijin ki, su Jadda su ne waɗanda suka ga cancantar hakan. Sai ga kuma wani al'amari na ubangiji ya sake bayyana mana cewa, bayan auren ki da ɗan uwana....mu ɗin ashe en uwa ne na jini...please I'm sorry..."

Murmushi na yi mata ina mai share hawayen farin cikin da suka silalo mini na ce.

" Ba komai. Abu mafi muhimmanci shi ne....mu ɗin en uwa ne. Na kasance a da idan naga mutane suna hulɗa da en uwan su, sai inji suna burgeni, a raina nakan ce nima inama ace ina da dangi haka kamar su....sai ga shi ashe nima ina da kyakkyawan family ba tare da na sani ba. Na yi matuƙar farin cikin da wannan. Ubangiji ya ci gaba da ɗaurar mana zumuncinmu har Aljanna."

"Amin ya Allah."

"Mu yi sallah?"

Wuri ta samu akan kujera tana mini kyakkyawan murmushinta ta ce.

"Zan jira a nan."

Zaunawa tayi har muka kambala sallar dani da Aunty Nadeeyah, sai ga wata daga cikin masu aiki ta shigo mana da tray shaƙe da kayayyakin Ci da Sha masu matuƙar daɗi da garɗi a baki tace wai daga Jadda ta ce a kawo mini ko akwai abinda nake son ci a ciki.

Hmmm! Ni ce shugabar cewa idan an maka laifi ka zama mai yafiya. Amma wallahy sam na kasa jin cewa wai zan iya yafe mata duk da kasancewarta Kaka a gareni nima. Duk tsawon kwana biyun nan da take ta wani rawar ƙafa a kaina sam bana jin tana burgeni, daga zaran na kalle ta sai in ji abinda tayi mini yana ƙara dawomin sabo a raina. A duk lokacin da na ɗora idona a kanta sai na riƙa tambayar kaina cewa, wai ashe haka take matar nan, kamar ta kirki. Ko daga sama na faɗo ai yaci ace darajar so da ƙaunar da jikanta ke mini da kuma cikin da yake jikina yaci ace ta tausaya mini. Amma haka ta bushe idanun ta musamman ranar da na iso, ga gajiya ga ciki amma bata yi tunani mai kyau a kaina ba. Allah dai ka haɗamu da mutane na gari, shi kaɗai zamu iya cewa.

Bayan mun kambala sallar Isha ne muka koma parlourn wanda a lokacin har da su Suhaib, Raihab da kuma ƙaramin ƙanin Noura ɗin, Shuraih suka yi joining na mu.

A nan Ammie ta basu tarihin rayuwar da mukayi a lokacin da Abbie ya rasu ya barmu, da kuma irin riƙon sakainar kashin da Daddy ya yi mini da cutar damu da ya yi har sauyinda muka samu da kuma auren ta da Dr. Basheer da kuma yanda aka yi aure na.

Ba ƙaramin al'ajabi suka yi ba jin tarihin aurena da Ya Mohaa. Wanda sun jinjina mini ba kaɗan ba. Kowa sai albarka yake saka mini da fatan kasancewarmu da ni da shi har mutuwa. Sosai idon Jadda ya raina fata domin ko a yanda suke ta zuzuta cancantarmu da irin yaba masa a yanda ya nuna mini ƙauna yasa ta sa jinin jikinta kuma taji har cikin ranta cewa ta yi kuskure.

Cikin wata irin magiya Abiyh ya kalli Ammie yana ta roƙonta shi da Ammah akan ta yafe musu domin su ne sila.

Nan aka hau yafe-yafe ana ta koke-koke. Gefe na koma na amsa kiran masoyina ina ta bashi hint da abinda ke faruwa in brief.

Mai karatu ka kwatanta irin farin cikin da mutum ke shiga idan ya rasa danginsa tsawon lokaci sai kuma dare ɗaya ace ya same su. Alhamdulillah shi kaɗai zamu ce. Amma kowa yana cikin farin cikin da baki ba zai iya misalta shi ba.

Addu'ar kambala taron akayi wanda Sheikh ne wanda ya jagoranta sannan daga ƙarshe na ce kowa ya dakata ina da magana.

Shiru suka yi suna masu kasa kunne domin jin abinda yake raina. Muryar Annie na ji (Nana Maryam) tana faɗin.

"Akwai hikima sosai a kalaman ki Beenafah. Haka nake ganin rayuwarki kamar ta Raihab. Nutsuwarku da baiwar kalamanku iri ɗaya."

Murmushi na yi tare da kallon inda Raihab ɗin yake zaune na ce.

"Daga yau kuwa, kai ne babban abokina, domin duk shawarar da za ka bani in sha Allah na san mai amfani ce."

Dariya ya yi yana jinjina kansa ya ce.

"Tau shikenan Aminiyata, Allah bar mana zumuncinmu har mutuwa."

Da amin duk muka amsa sannan na kalli Sheik na ce.

"Sheikh...dan Allah ina so ka yi wa Ammah da Abiyh nasiha, akan su dawo da auren su su yi haƙuri su manta baya..."

Wani irin kallon suka bini da shi wanda sai da na ji kamar na karaya, amma sai na ƙara dagewa tare da roƙon Allah ya bani sa'a yasa na yi nasara.

Da Ammah na fara na wani kalle ta na ce.

"kin wani ƙuro ido kina kallona. Taurin kai ne kawai kika nuna amma a yanda kike ta kuka kina neman sa gafara dole akwai sauran soyayyar nan a zuciyarki. Kuma ma da ace baya cikin tunanin ki tsawon shekarun nan da yanxu kin auri wani kin manta da shi. Saboda haka, sanadiyyar ki ne ya nemi ya rasa idanunsa, dole ki koma gidansa domin kulawa da shi."

Sai kuma na waiga wurin Abiyh na ce.

"Kai ma sai wani kallo kake mini, da ba ta cikin ranka da ba za ka yi kuka har ka nemi rasa idanun ka ba, sannan da ba ta cikin ranka da yanzu ka yi wani auren ka manta da ita....kuna ji ko? Kun biye wa zuciya kun cutar da junanku. Shawarata a nan ita ce, ɗan lokacin nan da ya saura muku a duniya yana da matuƙar muhimmanci ku ƙarasa shi a tare. Sannan abu na ƙarshe...dan Allah ku dawo da auren ku ko don farin cikin waɗan nan 'ƴa'ƴan naku da kuka ruguza farin cikin su tsawon shekaru."

Nan ɗakin ya ɗauka, kowa ya bayar da goyon baya akan cewa wannan shawarar tawa ta yi daidai. Kawai a mayar da auren tare da na Emraan da za'a yi jibi.

Nan sheikh ya ƙara yi mana jan hankali akan girman haƙuri a gidan aure da kuma lura da haƙƙoƙa da muhimmancin haɗin kan miji da mata a kowane irin abu da zai zo a cikin rayuwar su. Domin da ace akwai haƙuri da biyayya da auren Ammah bai ƙare a haka ba, sannan shi ma Abiyh da ya zama mai haƙuri da rashin biye wa mata da yanzu auren su bai ƙare a haka ba. Da wannan ya samu ya janyo hankalinsu har suka amince wanda a nan Abiyh ya ce zai kira danginsa ya sanar musu, daman daga cikin su sun yi ta bashi shawara tun a lokutan baya akan ya zo ya dawo da ita ya ce baya buƙata. Hatta mahaifiyarsa kafin ta rasu sai da tace ya dawo ita yace baya buƙata.

Kallon Jadda Ammie ta yi murya a tausashe ta ce.

"Jadda! Roƙona ɗaya ne. Mu dai a yanzu family ɗaya ne, Alhamdulillah! Shawarata da roƙona shi ne;tun da har kun ga cewa Noura ta fi da cewa da Hammodi....to gwanda ta bar mata shi domin namiji bai isa ya ruguza mana zumunci ba. A ranar da na iso ƙasar nan naga irin abinda kika mata a gabana, ya sosa raina sosai, domin bani da kamar Beenafah a duniya, zan iya yin komai domin ta, da ba dan wannan zumuncin ba wallahy tallahy har na gama yankewa a raina cewa Beenafah ta gama auren shi har abada, komai zai faru ko. Domin ba zan bar 'ƴata ta rayu a dangin Mijinda basa son ta ba kamar yanda ya faru dani. Har abada ba zan lamunta ba....to amma tunda har abun ya zo a haka, za ta iya bar mata sh..."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku ni Samaahat"

Jadda ta furta a gigice tana mai ɗora hannu a kai tamkar za ta zubo fitsari tsabar yanda ta ruɗe. Sai faɗin take.

"Sharrin shaiɗan ne wallahy NANA Hauwa! Dan Allah ki yi mini gafara. Sam ban kyauta ba,damuwar Noura ta dameni..."

Cikin wani irin takaicinta Aunty Nadeeyah ta ce.

"Gaskiya Jadda kin bani mamaki. A yanda kika mana farkon zuwanmu ko a mafarki akace za ki iya Cutar da Beenafah zan ƙaryata. Amma dan Allah ji kalaman ƙasƙancin da kika mata ko arzikin cikin da ke jikinta baki duba ba. Ai a tunani ko ke ce kike son auren Hammodin za ki ɗaga mata ƙafa... "

Tsawa Baba Ustaz ya daka mata sannan ya ce.

" Wannan wane irin shirmen magana ne? Ina ce an yi komai ya wuce an nemi yafiya kuma komai ya wuce? Miyasa za ku nemi dawo da hannun agogo baya? Kowa ya yi haƙuri wannan magana ta wuce. Hajiya Nana Hauwa sam wannan magana ba ta kama ta ba, duk da cewa nasan ɓacin rai ne. "

Girgixa kai Jaddi ya yi cike da tai ci yace.

" Duk tsuntsun da ya ja ruwa ai dole su yi masa mugun duka Alhaji Ustaz! Wato da na ce miki kibar wannan maganar ta wuce ashe baki barta ba Samaahat??"

Tamkar za ta yi dungure wurin bashi haƙuri haka ta yi, sai kuka take harda wani juyowa tana nemana gafara. Nikam ta shi na yi ina faɗin ba komai ya wuce, sannan na wuce ƙofata, daman ga wani uban fitsari da ya cika mini mara ta sannan ga kiran Dayaa sai shigowa yake, da yaga naƙi na yi picking ne yasa ya turo mini text na cewa duk abinda nake naje na kwanta dare yayi.

Hakan yasa ina yin fitsari na samu wuri na kwanta domin ko wankan na ji ba zan iya yi ba. Kwance nake ina waya da Bahrain sai naji ana nocking door ɗina, ta shi na yi na je na buɗe sai ga Noura na gani wai tana so ta kwana a gidana. Baro ɗakinda nake ciki na yi wanda shi ne ɗakinmu ni da Dayaa na je na buɗe wani muka shiga muka kwanta a gado ɗaya da ita.

Massage ta fara mini ganin yanda ƙafafuna suka ɗan kumbura kaɗan, tana yi muna fira wanda ni duk kunya ma ta gama kamani domin babu yanda ban roƙeta ba akan ta daina ta ƙi. Mun yi rabin dare da ita muna fira sannan daga ƙarshe muka yi baccin gajiya.

Gefen su Ammie ma, kusan tun ranar da suka zo baccin su kaɗan ne, domin fira suke kwanayi da juna cike da kewa. To yau ma tare da mahaifiyarsu suka kwana su uku suna ta firarraki da ƙara samun haske akan rayuwar iyayen nasu.

Washegari, ni kam da wuri na je gyaran kaina na dawo, wanda a can aka mini jan lalle wanda ya yi kyau sosai na ji da gani domin Mijina wanda nasan lokaci kaɗan ne ya rage su iso tare da Amarya Hairi, su Aunty Labiba da sauran en uwansu da kuma Ango Emraan.

✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER*

*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*

*FREE-BOOK*

*PAGE 56*

Muna cikin jera abinci ni da wasu masu aiki guda biyu Suhaib ya shigo tare da Zayn. Wasu kuɗin da ya bani ajiya tun kwana da suka wuce yace na ɗauko masa.

Har na miƙa masa sun juya sai kuma na ce.

"Ko za ku ci abincin ne Zayn?"

Girgiza kai Suhaib ya yi yana dariya ya ce.

"Ke yanzu Uwargida dan Allah idan na ce miki zan iya cin abinci za ki yarda?"

Tsaki na ja ina masa wata harara ta can ƙasan ido. Duniya Suhaib ya gama raina ni, shi kaɗai ke ce mini wai Uwargida. Hakan yasa na ce.

"Mts! Suhaib wannan kalmar ta uwargida da kake kirana da ita bana so fa..."

Dariya ya yi ya ce.

"Miyasa?"

"Da gaske nake faɗa maka Suhaib. Saboda ya kan sa na riƙa ji kamar zai auro wata wacce za ka riƙa kira amarya..."

Daga shi har Zayn ɗin dariya suka yi sannan daga ƙarshe ya kalle ni ya ce.

"Na rantse miki da Allah Yallaɓai ba zai iya ƙara aure ba. A yanxu dai nake faɗamiki, domin ban san abin da gaba za ta yi ba. Wai kin san artabun da ya yi akan auren Noura..."

Dariya na yi na ce.

"Wannan kuma ya wuce. Za ku ci abincin ko a'a?"

"Ni dai a'a. Kin ga tafiyata. Kuma kai idan ka tsaya, to zan yi tafiyata na barka."

Dariya muka yi sannan Zayn ɗin ya ce.

"Na gode Aunty Beenafah. Sai an jima."

Yana gab fita na ɗaga murya ina dariya na ce.

"Ka gama duk wani zumuɗinka. Abinci ne sai ka nemeshi."

Bayan na kambala na je na yi wanka na shirya cikin wata rantsatstsar Abaya baƙa sannan na fito. Suna can suna ta budurinsu ni kuma ina nan na gyara komai na shigowar mijina kawai nake jira.

Ina nan sai kiran wayarsa nake ashe sun fi hour da shigowa yana can cikin gidan tare da su Ammie bayan an shige da Hairiyyah.

Fitowa na yi na je masaukin su Ammien inda a can ne suke zaune tare da su Annie da su Mummy Na'imatu. Rungume ni Hairiyyah ta yi idanun ta cike da hawaye sannan ta janye ta ce.

"I miss you..."

Dariya na yi, ina mai shafa kumatunta na ce.

"Amarya bakya laifi, ko kin kashe irin su Shuraih su Zayn su Taimiyyah."

Dariya suka kwashe da ita, sannan na kalle ta na ce.

"Kin kyau sosai Hairiyyah. Allah ya sanya alheri da albarka ya bada lafiya..."

Hugging ɗina Bahrain ya yi yana mai fashewa da kuka. Bubbuga bayan sa na fara a hankali tare da kalaman rarrashi har sai da na ji ya sarara sannan na kalli fuskarsa na ce.

"Wai duk wannan kukan na farin ciki ne?"

Hannayena ya jimƙe a nasa yana kallon idanuwana yana murmushi. Cike da alfahari ya ce.

"Aunty Beena! Tabbas kina da wata baiwa da ban san yadda zan kwatanta miki ita ba. You are not just a sister...you are a blessing to our family. Ke ɗin Yaya ta gari ce wacce tasan abun da take yi, wacce ta iya kula da rayuwar ƙannenta tamkar ita ce uwar....Thank you for all the effort, for the stress, for the sleepless nights..Allah ya saka miki da alheri. Duk wani alƙawarin da kika mini tabbas ya cika Aunty Beena...tun bani da cikakken wayau kike mini alƙawari, ni kuma a lokacin kece madogara ta kuma duk abinda kike faɗamin ban taɓa ji a raina cewa kina faɗamin ne kawai wai don ki kwantar mini da hankali na ba. Da wannan sai Allah ya dubemu ya cika mana. Ban taɓa tunanin cewa zamu kawo wannan matakin ba a rayuwa, but you pushed it to be real. You are my pride, thank you for being strong for both of us. Thank you for loving and caring for me...Thank you for being the sister that every brother dreams to have."

Jinjina kaina a hankali na share hawayena na ce.

" Na gode da yarda da kayi dani Bahrain. Ubangiji da zuciya yake aiki. Matuƙar niyyarka, mafarkinka ka gina su da yaƙini da kuma kyakkyawar zuciya wacce bata nufin kowa da sharri...to In Sha Allahu watarana wannan burin naka sai ya cika. Mafarkinmu na haɗu wa da en uwa ya cika ba?"

Murmushi yana jinjina kansa yace.

" Eh."

"To yanzu ni ce na biyo ka bashi. Ka tsaya ka yi karatu domin ka cika mini mafarkina na hawa kujerar Abbie.."

Cike da ƙwarin gwiwa ya yi twisting hannunsa a nawa yana jinjina kansa ya ce.

"In Sha Allahu, na yi miki alƙawarin wannan."

Gabaɗaya hankalin mutanen ɗakin ya dawo kanmu. Jansa na yi ba tare da na raba hannayen namu ba. Na shiga nuna masa mutane ɗaya bayan ɗaya yana gaisa wa da su sannan daga ƙarshe na dawo wurin su Aunty Labiba, inda na ganta zaune wuri ɗaya tare da su Ammie, sannu da zuwa na yi mata sannan muka gaisa na gaishe da sauran mutanen na zauna muna ɗan taɓa fira wacce duk akan dai maganar bayyanar familyn namu ne.

Kallonsa nake yanda yake ta dariya da su Ammah a gefe gwanin sha'awa da shi da su Emraan.

Fitsarin da ya dame ni ne yasa na miƙe na ce musu zan tafi gida. Yanzu ban san mi yasa ba, yawan fitsari nake kamar me, kuma idan naje ɗan tsitau nake yin sa, wanda idan ban yi ba neman nutsuwa ta nake na rasa.

Yana ganin ficewata shima ya yi musu sallama ya fito. Ina shigowa na duba agogon wayata na ga ƙarfe shida na yamma ne saura.

Toilet na shige, bayan na kambala na fito.

"Kina fushi ne?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull